Showing 78001 words to 81000 words out of 155647 words

Chapter 27 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

479

cikin ido.
Murmushi ya khaleel yayi, yajawo iPad d'insa yamik'ama Ak'ilu Abbas.
Kar6a yayi cikeda mamakin mizaiyi da itane?.
"Nasan kana mamakin mizakayi da ita ko?, akwai game aciki, kuma shikad'aine, inaso kaje kayishi, iya inda kasamu game over kakawo min, idankuma kawuce abinda kasamu har sau uku to zan gane zaka iya tafiya".
Cikin rawar murya Ak'ilu Abbas yace, " sir? Nikuma miye had'ina da game?".
''Basai kasaniba, banason yawan surutu jeka".
Duk Ak'ilu Abbas ya rikice, baisan dalilin yin hakanba gareshi, tabbas yasan wanene j!, kuma baya Abu saida manufa.
Koda yak'arasa office d'insu su kusan 20 aciki, sai yake gayama abokinsa wanda sukafi shak'uwa.
"Tab wlhy Ak'ilu kashiga tarkon Oga kawai, shiyyasa naita kwa6arka al0kacin amma kak'i, yanzu wa gari ya waya".
" please Sha'aibu kabani shawara mana".
"Yoni shawarar mizan Baka?, kayi abinda yace kawai".
Shiru Ak'ilu Abbas yayi, Dan yasan shi'aibu ma mutumne mai gaskiya, aransa yace shikenan nashiga uku nikuma, anbani kud'i Na aikata abinda zaiyi sanadin k'ask'antuwata, gashima kud'in harsun zama labari, tunda naje karuwai sun cinye .............
'


Nidai nace, " hummm".



*_Ayya my sweet Xoxo, ALLAH yabaki lafiya, yasa kaffarane, yatashi kafad'a, fan's Ku had'o kayan dubiya tawan babu lafiya=??._*


*_Typing=???_*



>?0? *_CIKI DA GASKIYA........_*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_



*_Bilyn Abdull ce>??


*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_



*_part 2_*
(littafi na biyu=???)


2? 9?

Akwana atashi babu wahala awajen ALLAH, kwanaki nata gudu lamarin tamkar k'yaftawar idanu, kamar wasa saikaga seconds sunkoma minutes, minutes sunkoma hours, hours sunkoma day's, days sunkoma weeks, weeks sunkoma months, months sunkoma years, baka fargaba saikaga kanka amatsayin gawa=?-?. Da d'an Adam yana tunawa akwai k'alubalen mutuwa agabansa dabai aikata wata 6arnarba, hummm kunsan wani abu kuwa?, (wlhy dayawanmu gani muke bazamu mut yanzuba, dukda munsan tabbas mutuwa gaskiyace, Dan inba'a d'auki mamankaba, and'auki babanka, ko yayanka, ko k'anwarka, ko mijinki, ko mataraka, ko k'awarki, ko makwafciyarki, amma lokacin da'akayi mutuwarne kawai zakiga hankalinmu yatashi, kwanaki k'alilan zamu koma dukkan ayyukanmu, wani gani yakeyi shifa k'aramine mutuwa bazata d'aukeshiba yanzu), kai=?I???? @&d'an adamu wanene kai?, mikake tak'ama dashi?, karinga tunawa mutuwa tana d'aukar d'a acikin uwarsa=?I??0??1? @&tana d'aukar masu shekaru biyu=?I? B&=?M? @&, tana d'aukar magidanci. Mai fafutukar Kare martabar iyalinsa wajen cigar dasu da tufatar dasu=?I?????4? Shin miyakaika shagala yakai bawa?, miyasaka mantawa da k'alubalen mutuwa?, miyasa? duniya da kayan cikinta sukafi tasirantuwa azuciyarka fiyeda tunawa kwanciyar kabari daranar hisabi, ranarda kowa aikinsane makaminsa, wane rud'in shaid'anne ke d'awainiya dakai har kakasa jin kunyar ubangijinka daya halicceka danka bauta masa kake aikata zina agabansa, kake shaye-shaye agabansa, kake luwad'i agabansa, kake mad'igo agabansa, kake sata agabansa, kake bin bokaye agabansa, kake cutar da d'an uwanka saboda ALLAH yabaka wata dama ta mulki ko k'arfin iko, miyasa yakai bawa?, shin baka tsoron randa za'a shiryo rundunar mala'iku domin kar6ar ranka?, aranarfa aikinkane kawai guzurinka?, anya kuwa bawa yana k'iyasta kansa amatsayin gawa idan yanutsu, kokayi wannan tunanin, kobakayiba wlhy billahi saika mutu=?I?


________________________________
Bikinsu Amal nata matsowa, gaba d'aya yau saura kwanaki 6 kacal d'aurin aure, kusan zan iya cewa duk masu aikin gidan da 'yammata harda matansu sultan dasu mama duk suna kichin, chin-chin d'in gara?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? dakuma rabo akeyi.
Aysha ce kawai babu awajen, tana d'akin Anty Mamie kwance, yau kusan satinta d'aya kenan, Dan ya khaleel yayi tafiya zuwa France tun last week, shine yace tadawo d'akin Anty Mamie harsai yadawo.
Kusan kwanakinta uku kenan batajin dad'i, k'irjinta namata ciwo, dauriya kawai takeyi bataso kowa yagane.
Wajen aikin chin-chin d'inma hartaje takasa zama saboda jiri datake gani kad'an-kad'an.
Batacewa kowa komaiba tazaro jiki tadawo d'aki, kwance take shiru tana tunanin ya khaleel, tunda yatafi sau hud'u kacal sukayi waya, ko kiransa tayi saiyace aiki yakeyi, lamarin ya khaleel Na damunta wlhy, ita yanda take karanta novels taga mazan ciki Na tattalin matansu, harma sukan manta da ayyukansu, duk motsinsu yana gidansu, soyayya kaga harta fitar hankali, catake haka zata dinga gani ga ya khaleel, amma yayinda ta auresa saitaga sa6anin hakan, dai-dai gwargwado yana nuna mata kulawa da soyayya, saidai batakai ko rabin wadda ake nunama matan novels ba, shin ko ita bata iya tattalin miji baneba kamarsu? To amma ai matan novels ma girki, iya kwalliya, tsafta, kusan shine sukema mazajen, itama duk tanama mijintashi, hardama biyayya, wadda take ganin mafi yawan matan novels basuda ita, (hummm indai hasashenta gaskiya ne to tabbas zata iya cewa irin wannan mahaukaciyar soyayyar da miji kan nuna ga matarsa, harkiga yana mata kuka to sai'a novels, saboda k'arancin samun irin wannan soyayyar a gidajenmu yasaka mata raja'a wajen karanta hikayoyin marubuta, musamman ma buk na batsa, Dan suna kallon hakan amatsayin soyayya, mukuma yawanci bama samun irin wannan soyayya agidajenmu) "ya ALLAH ka gyara gidajen auranmu", Aysha tafad'a tana share hawaye.
Wayarta tajawo ta dialing d'in number ya khaleel ta France, harta tsinke bai d'agaba, saida takira sau biyu. Ana uku harta kusa katsewa sannan yad'auka.
Cikin dauriya tace, "Assalamu alaika".
Ya amsa yana fad'in "o, nayi laifi fa, jiya nace zan kiraki ban kiraba, amin afuwa aikine wlhy A'eesha".
Danne zuciyarta tayi tace, " babu komai sadauki, Na fahimceka, ya aikin?".
Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke, yakuma jingina sosai da kujerar motar tareda lumshe ido, yace, "Alhmdllh, ngd sosai dakike fahimtata akowane lokaci, haka akeson mace tazama maima mijinta uzuri, Dan itadama rayuwar aure tagaji hak'urine kawai, bakomai ake nema asamu 100% ba".
Aysha tace, " hakane".
"Yauwa ya shirin biki?".
''Gashinan anatayi, duk sunacanma suna chin-chin".
"Tofa, kekuma kina ina".
" ina d'aki kwance, wlhy haka kawai naji inajin d'an jiri, bansan daliliba, amma yanzu yadaina".
"Sholyna kodai asibiti zakije?".
" lah karfa ka damu, wlhy da sauk'i, yanzuma zan koma wajen aiki, yaushe zaka dawo".
"Tom ALLAH yak'ara afuwa, Indai kinji bai tafiba karkiyi shiru, kifad'ama Anty Mamie kuje asibiti, Nima insha ALLAH zuwa nanda 4days zandawo k'asar".
"anafa jibi d'aurin aure kenan?".
"Eh, insha ALLAH, ko kina kewatane?".
Cikin shagwa6a tace, " wlhy sosaima kuwa".
"Humyim, karfa nadawo kice kuma Na gundureki".
"ni wlhy babu waninan, kadawo please ".
Guntun murmushi yasaki, yayinda shagwa6arta ke rura masa wata kasala mai kashe jiki da sanya jini gudu da sauri, muryarsa can k'asan mak'oshi yace, " my sholy karki kasheni da salonkifa, kinga bana kusadake, please karki saka sadaukinki cikin wani hali kinji".
Dad'ine Yakama Aysha, tasaki siririyar dariyar data kuma narkar dashi, aii babu shiri ya Yanke wayar gaba d'aya, yay saurin kifa kansa jikin sitiyari yana sauke numfashi a hankali, tabbas Aysha dabance wlhy, yafad'a cikin furzar da iska daga bakinsa, kashe AC d'in mortar yayi, danshima k'ara sakashi kasala yakeyi, dajin buk'atuwar kasancewa da matarsa.

Aysha ko yana kashe wayar ta tuntsure da dariya, dama da gayya tayi, wai itama sotake tagwada Na matan novels tagani zaiyi tasiri, dad'i kamar zai kasheta, sai juye-juye takeyi agadon ("kai dagaskefa marubutannan suna fad'akar damu wlhy, infa zaka d'auki Abu mai k'yau kagwada ga mijinka zakaga kana canjashi kamar mijinki novels, Kodai bazai lalace akankaba kamar mazan novels to zaka samu farinciki kaima) aii idan akace matar novels tayi wanka sau uku Arana, kekuma saiki kamanta yin biyu, (suma marubutan suna saka hakane Dan ka kamanta ba dole sai d'in kayi kamar ta novel ba, idan sunce 1 akayi, kekuma wataran bazakiyi d'ayan bama, abunda yasa bama amfanuwa da abinda marubuta suka rubuta, saboda muna karanta books d'inne dan kawai nishad'i, burinmu muji soyayya ruwa-ruwa, matsa can kamacan, badukanmune Muke maida hankali wajen fahimtar wane sak'o writer suke son isarwa a buks d'insuba, soyayyarce kawai damuwarmu, amma bamabin matakan mizamuyi musami soyayyar muma agidajenmu, wata Indai ta karanta labarinki yasakata dariya ko haushi anan zata kakka6ar miki da kayanki, bazata amfanu da komaiba, kota gwada danta samu mafita agidanta ko cikin al'ummar datatsinci kantaba, nikam danayi wannan asarar 6ata lokacin, aigarama ace ban karantaba wlhy).
(Yakamata dai reader's sudinga fahimtar writers bamuyita wahalar banza da asarar data ba, ALLAH yasa nun fahimta).


____________________________

Momy madai tanata shirya d'iyarta mufeedah, daka shiga 6angarenta kasan ana bikin 'Yar gata, danma babu Anty zuwairah, Dan baffah yahanata zuwa gidan kusan harna tsawon shekara biyu.
Sosai momy takema mufeedah komai na 'yan gata.
Babu Abu mafi d'auremin kai sai zaman Aleeya agidan, narasa mitakeyi har tsawon watanni biyu da rabi?, kuma babu Wanda yamata maganar barin gidan, gashi bama ta ishi ya khaleel kalloba, amma ko yaushe tana nane dashi.
Komai Na bikinnan da Aleeya akeyinsa.

Momy dai an ajiye girman kai taje ta rok'i Ammah akan tabama baffah hak'uri yabar zuwairah tazo, da farko Amman shareta tayi, saida tayita mata magiya sannan Ammah tace taje zata masa magana.
Ilai kuwa dasafe yazo gaisheta tarok'eshi akan yabar zuwairah tazo, tunda komai ya wuce, da angama biki saita tattara tatafi.
Badan baffah yasoba ya amince, sosai Anty zuwairah tayi murna kuwa.
Taitama Ammah da baffah godiya acikin waya, harda kukanta akan baffah ya yafe mata, hakan bazai sake faruwaba.
Amma dukda haka bawai tanason Aysha baneba, haka kawaidai batason mahaifinta tayi fushi da itane.


__________________________
Biki bidiri bired'e, gidafa Alhmdllh yacika da al'ummar Annabi, dangi tako ina sun cika gida, yo kikam harfa 'ya'yan mutum hud'u, momy zata aurar da mufeedah, Anty Mamie, Ramadan, zunnuarain, Amal. Ummie amarya, Shahudah, sai matar uncle ma'aruff k'anin baffah, Naseeba da Hamdiyya, (Dan itama nangidan tadawo za'a had'u waje d'aya ayi kawai.
Aikam gida dai ba'a magana, mama ma dabazata aurar dakowaba danginta dank'am da gida, su Yaya fadeelah, hafsat, Ummah, Anty nasarah matar ya Qaseem duk suna nan, harda matan kawu bilyamin, da babbar 'yarsa, saikuma Rufaidah da Safiya amare, kowacce da cikinta, su Rufaidah anata zubar da yayu.
Aiko Aysha tatasosu gaba da dariyar mugunta, wai daga yin aure harsun sami ciki.
Yaya Hafsat tayi dariya tana kallon ayshan, tace, "hummm Aysha kema wannan k'yawun naki aii inkaji gangami da labari, kinga yanda kika k'ara 'Yar k'iba kuwa, harda wasu hips na musamman, gawani bala'in k'yau dakikayi, anya ya khaleel Na kallonki kuwa?.
Kwa6e fuska Aysha tayi, tatashi daga d'akin mama tafice, dama anan suke hirar, tun isowar mutanen kanon da safe Aysha tadawo tsakkiyarsu anatashan hira, tayi kewarsu sosai.
Maganar Yaya Hafsat tasakata fita, danta Sosa mata inda yake mata k'aik'ayi, tun jiya yakamata ya khaleel yadawo gidan, amma shiru, har tayata su maleeka sukayi tagyara 6angarenta, suna shirya masa abinci. Amma har dare babu labarinsa, tasha kuka kuwa da daddare, da safennanma haka tatashi cikin bak'in rai, zuwansu yaya fadeelah nema yasakata d'an sakin jikinta.
Tunani yatafi da hankalinta wata duniyar baki d'aya, jitayi anyi sama da ita kawai.
Zaro idanu tayi waje, cikin matuk'ar firgita, wanene ya d'auketa, jikinta sai 6ari yakeyi takai dubanta kansa.
Wata wawuyar ajiyar zuciya tasaki, ''sadauki! Yaushe kadawo?".
Kashe mata ido d'aya tayi, yana wani k'asaitaccen murmushi, saida yatura k'ofar 6angarensu yashiga sannan yabata amsa.
"Yanzunnan nadawo".
Shiru tayi bata tankaba, saima hawaye data kamayi.
Harsuka isa 6angarensu tana kuka, shikuma baice mata komaiba, tana rik'e a hannunsa yasaka key d'in yabud'e k'ofar falonsu.
Bai ajiyeta a faloba yanufi d'akinsa kai tsaye da ita, yasan yayi laifi dolene yayi lallashi.
Ko ina tsaf yanata tashin k'amshi, saboda gyaran dasukayi masa jiya, kuma yauma batareda sanin Aysha ba Anty Mamie ta turo tasleem takuma gyara Inda k'ura ta sauka.
Saman gadonsa kawai ya d'ireta, takara k'arfin kukanta tana bubuga k'afafu yanda yara sukeyi Idan ansakasu kuka.
Bai kulataba nanma, yaje ya kulle k'ofar yahau cire kaya, Aysha kam bata gajiba tacigaba da ta6ararta=??.
Toilet yashiga, kusan 20minute yafito d'aure da towel, alamar wanka yayi, jikinsa kawai ya goge yad'an fesa turare yasaka boxer ya haye gadon.
Jawo Aysha mai kukan shagwa6a yayi jikinsa, tanata tureshi itakuma alamar karya ta6ata.
Cikin sigar tsokana yace, "o, Sholyn sadaukinta bagani nadawoba to, kema kinsan aikina aii, sai kinamin uzuri, haka Nike kullum tamkar kud'i, koda yaushe acikin yawo nake".
" amma inda bakada mata kake wannan yawon, aii yanzun saika tuna Kannada ita ko......
"Umh hakane kuma, yakatseta da Sauri, zata k'ara magana ya d'ora bakinsa akan nata>?+?...
@& @&.



__________________________
Biki kam dai ba'a cewa komai, gida yagama. rikicewa, baka ganin kowa ba'a ganinka, duk son d'aukar rahotona Na tsiya dole Na hak'ura, nakoma gefe nazuba idanu.

Karfe 10am aka d'auro auren Zunnurain da Amaryarsa Maryam, sannan aka d'unguma misali 11am aka d'auro Na zunnurain da amaryarsa Samha.
Tom angwaye saimuce ALLAH ya sanya alkairi=??=??=??.

Misalin 1:30pm bayan idar sallar Azhur aka d'aura auren mufeedah & Ameenudden, sai Hamdiyya & Abdul-Hakem, Amal & Adams, Shahudah & Anwar, Naseeba & Najeeb, ubangiji ALLAH ya sanya alkairi amare da angwaye, su babban Yaya ya khaleel sai baza babbar Riga akeyi, angwaye kam aii ba'a cewa komai, su Adams da ya Ramadan baki kamar ya yage=??, hakama amare sunsha k'yau acikin gida, kamar zasuje gasar sarauniya k'yau.lol.
komai yana cigaba da gudana cikin tsari, acikin gidama mata nata shigi da fici da shagalinsu.
Amma banda Aysha da zazza6i yarufe, su Rufaidah na 6angarenta tun jiya, a can suka kwana, hirar family d'insu sukeyi, dauriya kawai Aysha dake kwance a 2seat takeyi tana jefa magana a first tasu, Sadiya ce ta fahimci kamar ayshan batada lfy.
Tace, "Aysha lfy kike kuwa?".
" eh mana sadiya mikika ganine?".
"Naga sai hura hanci kikeyi, kamar kuma a wahalce kike magana?".
''A'a wlhy, kawai gajiyar aikice".
Hararta Sadiya tayi, tace, " aikinmi kikayi agidannan Aysha?, tun d'azun kina like da ya khaleel a d'aki, sai 9 kuka fito, kijimin 'Yar rainin senses ".
Dariya duk sukayi. Amma banda Aysha data harareta itama, to gwaggo mai tsari, sokike nabarsa shikad'ine? Ke haka kikema mijinki da har kika k'unso ciki?".
Hhhhhh mi kowa zaiyi ba dariyaba, dama Aysha da sadiya inhar suka had'u sai anyi tsiya, kamar sakone da sako aii (like nida Anty Ruk'ayya maikan goruba=??=??>?-?).

Abinci suketaci, Aysha na kwance tana kallonsu, babu abinda ke bata sha'awa a abincin, sai wani kallonsu takeyi a yatsine kamar taga gotta.
"K dallah malama kidaina mana wannan yatsine-yatsinen, idan bazakici bane babu dole, ki d'auke kanki mana". 'Rufaidah tayi maganar tana harar Aysha'.
Baki Aysha ta ta6e, ta kauda kanta daga kallonsu, tajuya kwanciyarta tama basu baya.
Babu Wanda yasakebi takan Aysha, sukaita shagalinsu da abinci. Ita daga nanma barcine ya kwasheta.
An idar da sallar la'asar ya khaleel yashigo gidan, bayan yasamu mutane sund'an lafa musu, saidai cikin gidan dank'am yake da mata,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login