Showing 6001 words to 9000 words out of 155647 words

Chapter 3 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

445

yace sorry sir.

Kausar tace, "sir! Gashifa yana shirin barin k'asar ta Kano state, jirginsa zai d'aga zuwa k'asar Germany da k'arfe 5pm.
K'arasowa ya khaleel yayi inda suke, yaja kujera ya zauna kusadasu, computer tamatso masa da ita, yasaka siririn farin glass a idonsa yafara dubawa anutse.
Le6ensa ya cije sannan yafara danne-danne, zuwacan yace Adams?.
Da sauri Adams ya amsa da yes sir!.
Kiramin number d'in Captain Salis muzambil.
OK Sir!.
Da sauri yafara laluben number a contact d'in ya khaleel, babu dad'ewa yasameshi, saidai bai d'agaba, yakuma kira a alokaci nabiyu, saida takusa tsinkewa yad'aga, da sauri Adams ya karama ya khaleel a kunne, muryar Captain salis yajiyo yana fad'in sorry j! Wlhy ina wani aikine kana lfy?.
Lfy lau Captain, ya aikinka?.
Alhmdllh, kaima yanaka?.
Munata fama fa.

Captain please akwai jirgin dazai tashi yau zuwa Germany?.
Yes, Of course j!, akwai 5pm, zakayi tafiyane?.
A'a, INA wani bincikene, ngd sosai
OK thanks you j!.
Karka damu.

Cire wayar yayi daga kunnensa tareda turama kausar computer d'in gabanta.
Yamik'e tsaye yana fad'in Adams inaso atura security report zuwa Immigration office yanzu da hanzari, dansuyi seizing d'in passport d'in barau modibbo, adakatar dashi daga barin k'asar.

Ok sir!.

cigaba da musu bayani da dabarun dazasubi wajen tafiyar aikinsu, duk kuwa da dukansu gwarazane akan sanin sirrin computer...



_____________________________

Saida mama tayima Aysha tsiya sannan tad'an saki jikinta, ita mamakima abin kebata, to kodama can hasashenta baiyi daidaiba akan ko Aysha nasan khaleel d'in?.
Duk Wanda yaga halin da ayshar take ciki tun ajiya zai tabbatar batason aurenne?.
Amma tasan yanda zata 6ulloma lamarin kodan ta ku6tar da marainiyar y'arta.

Aysha kam bayan tayi wanka saita d'auki wayarta takoma can bayan d'akunan gidan, Number d'in Anty meerah takira, babu dad'ewa tad'aga.
Tana d'agawa tasaki kuka, cikin mamaki meerah tace k! Lfyarki kuwa? Ko wanine yarasu?.

A'a, Aysha tafad'a cikin shashshekar kuka.
Tomiya faru?.
Aysha Na kuka ta zayyanema meerah komai, a mamakin aysha saitaji meerah ta daddage ta rangad'a gud'a.
Da sauri Aysha ta janye wayar daga kunnenta, saida ta tabbatar Anty meerah tagama sannan tamaida wayar tana kuma rushewa da kukan.
Kai kujimin sakara, tomiye abin kukan kuma, ALLAH ya cika miki burinki, baki ta6a zaton zaki samu khaleel a matsayin mijin aureba, amma cikin sauk'i ALLAH yabakishi, ko yanzu kin daina sonsane?.
Nifa Anty meerah bawai Na daina sonsa bane, amma naso ace koda zan sameshi sai burinmu yacika akansu hajia babba tukunna, yanzu yaza'ayi ina auremsa nasamu damar d'aukar fansa akan abinda mahaifiyarsa tamin?.
Yo aii wannan shinema mai sauk'i Aysha, kada ki 6ata abin farincikin d'aya samemu da bak'incikin mak'iyanmu, yanzudai kibari gobe idan ALLAH ya kaimu zamu dawo Abuja, idan nazo zamu tattauna, harda batun message da aka miki akan gwaggo bintu, danni abin yafa d'auremin kai, nayi iya hasashena nagaza binciko ko wanene?.
Wlhy bake kad'aiba Anty meerah, ina cikin son gano wanene, aka kuma hargitsamin kwakwalwa da maganarnan, yanzudai saikin dawo d'in sannan, agaidamin mom da Raudat dasu Safwan.
OK saimun dawo, zasuji.



___________________________
Hajia babba kam gidan hajia khaltum taje da sanyin safiyarnan.
Koma barci basu tashiba, itace ta tashesu, Aminiya lfy kuwa da farra safiyarnan?.
Inafa lfy aminiya, inacikin tashin hankali wlhy, wai Alhaji yarasa da wadda zai had'a Ibraheem aure sai jinin fad'ima makiyyata.
=?3?bangane mikike nufiba.
Mtsowww wataran kemafa sai ahankali, to Alhaji ne jiya da daddare yataramu shida munafukar tsohuwarnan, wlhy dabadan yayar mahaifiyata baceba dasaina saka an6atar min da ita............takwashe duk abinda yafaru tasanar mata.
Humm lallaima Alhaji Abdallah, mijinnan nakifa shima akwai taurinkan tsiya, to inbanda abinsa yama za'ayi yahad'a jinin kura da kare a rami d'aya? Ke baki fad'a masaba Ibraheem d'in yanada wadda zai aura.
Na nawa kuma?, nafad'a shegiyar tsohuwarnan tace aure babu fashi, yakikeso nayi? Wlhy kullum addu'a nakeyi ALLAH ya kashe jemammar tsohuwarnan muhuta, danni itace kawai matsalata agidan, tashigemin hanci, narasa yanda zan fyatota tafito wlhy.
K'yakkkkh aii insun San wata basu san wataba, kibarsu suyi auren kawai.
Kamarya nabarsu aminiya? Kinsan kuwa mikike fad'a?.
Hhhh nikuwa nasani aminiya, kawo kunnenki kiji.
Da sauri hajia babba tamik'a kunnenta, hajia khaltum ta gwargwad'a mata maganar, dariya suka kwashe da ita harda tafawa, hajia babba tace wannan shawara tayi aminiya, kinga daga baya sai ayi bikinsu da Aleeya.
Yauwa kokefa, dad'ina dake akwai fahimta wlhy, da duk kinbi kin tashi hankalinki abanza.
Hummm kibari kawai, wlhy jiya ko barcima banyiba, yanda naga rana haka naga dare, amma yanzu zuciyata sakayau wlhy.
Hhhhhhh to mud'in Na wasane aminiya.....suka kwashe da dariya suna tafawa=??=ؐ? saikace wasu k'ananun yara=??.


___________________
Gwaggo bintu nad'akinta Na 6angaren mama, zaune take abakin gado ta rabga uban tagumi, abin duniya dukya isheta, mamaki takeyi duk yanda ta k'untata rayuwar Aysha abaya amma yanzu taketa Neman hanyar kubtar da ita, anya kuwa bawani abu Aysha ke shiryama rayuwartaba? Kai Lamarin da mamaki gaskiya.....da sauri tad'ago kanta danjin alamar shigowar mutum.
Mamace tashigo d'akin NATA.
A'a bintu lfy kuwa?.
Cikin kame-kame tace babu komai fad'ima, amma Dan girman ALLAH kiyafemin abubuwan danamiki lokacin kina gidan Yaya, wlhy sharrin shaid'anne, tabbas ke mutuniyar kirkice, tunda baki dubi halayena Na bayaba kika taimakamin, ngd sosai.
Murmushi mama tayi tareda zama bakin gadon itama, babu komai bintu, aii yarigaya yawuce, nayafe miki, kowa yana kuskure arayuwarsa aii.
Gwaggo bintu ta jinjinakai tana share hawaye, dasake jinjina k'yak'yk'yawar zuciya irin ta mama, dukda tanada fad'a amma mutumce mai matuk'ar sauk'inkai idan ka iya zama da ita.
Nikam bintu wai Dan ALLAH waye yakai Aysha karatu k'asar waje agidanan?...............
'










One Love my Fan's=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?d'd'd'd'd'd'
[9/6, 5:54 AM] Aysha Galadima: *_Typing=???_*



>?0? *_CIKI DA GASKIYA........_*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_



*_Bilyn Abdull ce>??


*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
>?2?


*_part 2_*
(littafi na biyu=???)


4?

Bak'aramar fad'uwa gaban gwaggo bintu yayiba, tuni har zufa tafara ketowa a sassan jikinta, tuna gargad'in daya matane yasakata saita kanta da sauri, murya adake tace fad'ima Wanda ya kai Aysha karatu yace karna fad'a.
Bara namiki dallah-dallah yanda zaki fahimceni, lokacin danazo da Aysha gidannan kowa ya tausaya mata, sannan kuma Aysha tacigaba da tayani y'an ayyukan gida nakeyi, wannan yasakashi kirana gefe yamin tanbayoyi akan Aysha, ban 6oye masa komaiba Na sanar masa, shine yace zai taimaka mata taje makaranta, abinda yasa aka danganta tafiyar tata da taimakon mai ciki danku barine, nasan kai tsaye Yaya bilyamin bazai yarda Aysha tatafi karatu wata k'asaba.
Amma Dan ALLAH ki fahimceni, shi yace domin ALLAH yayi, shiyyasa bayason kowa yasani.
Ajiyar zuciya mama ta sauke, danta yarda da zancen Na gwaggo bintu.
Tace, "to amma miyasa tunda Aysha tatafi karatu bakizo kano ba? Har bikinsu Hafsat amma babuke?.
Hakane, hakan tafaru sakamakon Lagos danaje kulada zuwairah d'iyar hajia babba, tasamu ciki yana bata matsalane daga Bayama ta haifu d'an babu rai, wlhy fad'ima nasha wahala awajenta itada y'ay'anta, wannan dalilinne yasaka harnayi jiyyarnan a asibiti.
To bintu rayuwa sai hak'uri aii, gashi yawuce kamar ma ba'ayiba.

Aysha dake jikin k'ofa la6e tasaki ajiyar zuciya tareda fad'in Alhamdllh.
Da sauri tabar jikin k'ofar danjin alamun mama zata fito...


_____________________
Hankalin barau modibbo atashe yake sosai, Dan antabatar masa jirgi bazai tashi dashiba, hukumar shigi da fici ta k'asa tayi seizing d'in passport d'insa.
Baigama fita daga wannan rikitarba yaga alamun rufe asusun bankunansa da akayi gaba d'aya, zuface tafa keto mata addukan sassan jikinsa, cikin sassarfa yake fitowa daga airport d'in tamkar zai kifa k'asa, yaransa biyu nabinsa abaya, sukansu akid'imen suke>?#?.


_______________________
Muna saurarenka j, tund'azun ka kiramu amma kayi shiru ka kasa magana, shin meke damunkane haka? Nifa tunda safe nafuskanci bakada walwala gaskiya.
Ajiyar zuciya ya khaleel ya sauke, cikin cije le6ensa yace hakane Taheer, inacikin matsala gaskiya.
Joseph yace matsalarmi j!?, idan akan kama barau modibbo ne aimun d'akko hanya, ko yanzu mukaso kamashi zamu kamashi.
Ba wannanne matsalarba Joseph.
To miye? Cewar youseef?.

Aure!.

Aure!! Kuma? Kakeson yi?.
d'an Harar Taheer d'in yayi, ya gyara zamansa sosai, muryarsa cinkushe da d'aci yabasu labarin komai daya faru, dan ya yarda dasu, bashida abokan dasuka San sirrinsa sama dasu d'in, suma duk kukansu shi suke fad'amawa.

Gaba d'aya suka kwashe da dariya, sai faman ta6awa sukeyi, tsantsar farinciki ta bayyana a fuskar kowannensu, Youseef yace alhmdllh j!, gaskiya mundad'e bamuyi makamancin farincikin nanba, dama kullum damuwarmu zamuyi aure mu barka, abin Na matuk'ar cin zuciyarmu, lallai Ubangijinmu ya kar6i addu'oinmu, ALLAH nun gode maka.
K'aramin tsaki yayi yana Harar youseef d'in, kai Malam bamaganar wasa nakeyibafa, ya ina fad'a muku damuwata zaku maidani wani shakatafi?.
Nifa banason aurennan, kuma bansan hanyar dazanbi Na yakiceshiba saboda baffah, please kubani shawara mana.
Amma miyasa baka son auren j!?.
Saboda bana sonta Joseph.
Tab, nifa kana bani mamaki wlhy, tokai wa kakeso kuwa arayuwarka? Banta6a ganin kayi budurwaba tunda nake, shin bazakayi aure baneba arayuwarka, kome? Katuna addininkufa yabaku damar auren har mata hud'u, kaiko ko d'ayarma ka kasa kayi, badole baffah yaza6a maka da kansaba.

Kunga duk wannan cecekucen baima tasoba, j! Kafad'a manane danmubaka shawara?.
Khaleel ya jinjina kansa.
To inhar shawararmu kake nema, kama iyayenka biyayya, tunda kagadai bawata kakesoba barema kace saboda soyayyartane, insha ALLAH darajar biyayyar dazakaimusu nangaba saika sota fiyema da tunanin mai hankali.
Kaga saura 4weeks kawai bikin Joseph, daga nan saina youseef, nima Dady yasanarmin zuwa jibi za'a saka ranar aurena, kai kad'aine dama damuwarmu, to ALLAH ya yaye mana, kawai kayi hak'uri musha biki please, dukda bansan yarinyarba, nasan baffah bazai maka za6in banzaba wlhy, eyeeee angonba, harfa kafara k'yallin goshi Na angwanci.=??=??.
Taheer yak'are maganar da tsokana.
Gaba d'aya suka kwashe dadriya, amma banda khaleel Wanda yaja tsaki yana fad'in d'an iska kawai, aikai matsalarka kenan mtsoww!.

Hhhhhhhh karka wani doje wlhy, nasan muna funcika j!, akwaika da taku akan Abu, saikayi kamar baka damuba, amma k'asan ranka kana son abin.>?(?
Azumin dakakeyi wani lokaci namiye?.
Na k'aniyarkane mara mutunci, tashi kabarmin office d'an iska kawai.
Hhh ai wlhy babu inda zanje sai ankai k'arshen maganar nan dani, dolene shirin yazama Na musamman, dukfa d'aurewar nan taka ranar saikayi shaku-shaku da babbar riga Alhaji.
=??dariya suka kwashe da'ita suduka, harda khaleel, zan iya cewa yaune karan farko danaga yayi dariyar da har hakwaransa suka fito fili.
Wlhy yaronnan bakada kirki, cewar ya khaleel yana nuna Taheer. Bayan sun tsagaita da dariyar khaleel yace kud'in abokaine Na gari, wad'anda suke taka rawar gani a sashen tarihin gwagwar mayar rayuwar Ibraheem Abdallah, babu abinda zan cemuku saidai naita mana addu'ar cin ribar abota har a aljanna.
Ameen suka amsa gaba d'aya.
Joseph yace, "ansaka rana kenan?".
Kwanciya khaleel yayi jikin kujera, muryarsa a sanyaye yace basu sakaba, amma yau uncle ma'aruff nacan Kano zasu tattauna da iyayenta.
To ALLAH ya sanya alkairi. Yasa ayi damu kuma, wlhy harna k'agara naga mai sa'ar data samu wannan jarumin jarumai, mai k'yak'yk'yawar zuciya da rik'on gaskiya, mai martaba k'asarsa da kare mutuncin al'ummar cikinta, koda basusan dashiba.
Wlhy zancenka gaskiyane youseef, boss nadabanne acikin mutane, samun irinsa saida kwakkwaran bincike irinna masu hikima, da'ana samun ma'aikata jarumai marasa tsoro da kwad'ayi irinka da kasarmu bata lalace hakaba, saidai kash ru6a66un dasuke saida mutuncin k'asar tamu saboda kud'u sunfi nagartattun masu gaskiya irinka yawa, gashi kuma har yanzu al'ummar dake cikin k'asar basu fargaba, saboda *_KABILANCI DA 6ANGARANCI_* n dayayi tasiri aruhinsu, ga saka mana k'yamatar addinin juna da'akeyi, koda yake ba laifinmu baneba, laifin manyanmune, suna haddasa mana fad'ace-fad'acen addini saboda cikar gur6ataccen burinsu akan siyasa, mafi yawan fad'a da'akeyi ak'asarnan y'an siyaysane ke shiryashi, amma da tafiya tafara nisa saiya zama fad'an yazama na addini, wannan wace iriyar masiface, mund'auki amanar kanmu mun dank'a ga siyasa, wadda dama an kawo mana itane danta wargaza kanmu,, sai d'an siyasa ya d'auki mak'udan kud'i yabama Malamai da pastors, kaga sunata 6a6atu da cusawa jama'arsu mummunar ak'ida azukata, amma da tashin hankali zaizo duk kwashe y'ay'ansu da matansu zasuyi da kud'inmu subar k'asar, wad'anda suka kasance malaman kwarai acikinsu sai adinga binsu d'ai-d'ai ana kashe manasu, shin jama'armu bazasu farka daga nannauyan barcin daya d'aukesu baneba? Su nutsu wajen gano nagartattu irinsu khaleel a k'asarmu? Duk mutum mai gaskiyade zakaga bashida Pawer d'in hidimtawa al'ummar kasarmu, saboda mak'iya masu gur6atattun halayen dasuka raba hanya da halayensa na warai sune zagaye dashi.
Hakane Taheer, amma aii mungodema ALLAH, tunda Anfara walk'iya munkuma fara tsinto k'asurguman munafukai, kuma tabbas y'ar manuniya zata cigaba da nuna manasu insha ALLAH, talakawanmu kuma dasuka kasa gano gaskiya haryanzu saboda rashin sanin ciwonkai ALLAH ya farkar dasu kafin lokaci ya k'ure musu.
Ya khaleel dabaice komaiba Tun d'azun yace amin Joseph, saidai akullum ina tuna muku duk abinda zanyi da taimakonkune, kuma bazan ta6a amsa sunan waneba saida sunanku aciki, wannan zancen naku saiya tunamin dawani Abu mai muhimmanci dayake araina tuntuni.
Atare sukace wane Abu kenan?.
Saida yad'ago daga kwancen dayake akujera sannan yace yakamata mu kafa kungiyar taimakon matasa, wasu sun kammala karatu babu aikinyi, mukar6i takardunsu mu nema musu guraban aiiki, wasu rashin gata yasaka ko karatunma basuyiba, mu koya musu Sana'a dabasu jari, wasu kuwa karatunne ya yanke saboda babu kud'in k'arasashi, mu taimaka musu su gama, yakamata mu juya akalar zukatan matasanmu su farka daga ra'ayin karatu nayi danhaka sai aikin gwamnati, gwamnatin k'asarmu batada k'arfin d'aukar dukkan matasanmu suzama a k'ark'ashinta, amma idan ana jansu ajiki, danuna musu basaita silar gwamnati asiri ke rufuwaba, k'asar zata zauna lafiya, ataimakesu wajen ciremusu burin sainayi kud'i nima kamar wane, wannan zairagema k'asarmu cin hanci da rashawa, ta'addanci da k'abilanci harma da fad'an addini, za'a daina wawaso akan dukiyar y'an k'asa, wadda zakaga mutum shikad'ai yatara biliyoyin kud'i, kama rasa mizaiyi dasune? Ga gidaje da hannayen jari, jikokin jikokinsama bazasuyi talauciba, kaga mutum d'aya da mota ashirin shikad'ai, sannan duk y'angidansu kowa nada sama da biyu, kai wlhy idan kaje wani gidan saika d'auka anan ake k'era motoci saboda tsabar fariyya, to ba kud'insa baneba, hak'in al'ummar k'asane, shiyyasa baisan ciwonsuba, yawancin zakaga y'ay'ansune y'an cocaine, kuma sune ke shigomana daduk wani kayan maye ak'asarmu, saboda inama talaka yasamu abinda zaici? Bare yazama d'an safarar miyagun kwayoyi?.
Abinda ke matuk'ar tada hankalina shine, bayan satar kud'inmu dasukayi, sukabama y'ay'ansu sukaje suka siyo kayan maye da kud'in, saikuma adawo dashi cikin y'ay'an talakawa ana saida musu domin gu6ata tarbiyarsu, baza'a barmu muji da zafin talaucin daya ishemubama.
Sometimes idan kaga d'an talaka yazama d'an ta'adda wlhy zafin talaucine da bak'incikin zalincin da manyan k'asarmu keyi akanmu, ko shaye-shayen nan da y'anmata sukeyi duk silar masifar da'aka jefamune, kuma wlhy wasu sunkoyone wajen y'ay'an manyan, k'awaye ko samari, saboda shegen kwad'ayinsu, Dan muma talakawan wani lokacin bamusan darajar kanmuba wlhy, bamusan ciwon kanmuba, kowa burinsa ace dashi wane. Why!!!!?.
My friends why!!?.
Wace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login