Showing 126001 words to 129000 words out of 155647 words

Chapter 43 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

459

zaki fita?".
d'agiwa tayi ta kallesa, sanye yake cikin uniform d'in aiki, sunyi masifar zaunamasa ajiki, tajanye idonta ahankali ta maida kan jikinta, " haba sadauki miye aibun wannan shigar tawa?, ko inafa Na jikina arufe yake, tafin hannuna da fuskatane kawai ake gani.
Guntun murmushi yayi, yatako ahankali har zuwa gabanta, jawota yayi jikinsa ya rungumeta, a cikin kunnenta yace, "bazaki ganebane kedai, ina kishin aganemin wannan k'yak'yk'yawar surarne sholyna, ALLAH ya halicceki domin nine kad'ai, danhaka Na haramtama kowa ganeminke."
Cikin jin dad'in kalamansa tashafo fuskarsa, akasalance tace, "ngd Sadaukina, bara Na canja to".
''No barsu, amma next time akiyaye".
"Angama boss", tafad'a tana kanne masa ido d'aya, da salute nashi".
Shima k'amewa yayi yay salute nata.
Atare suka tuntsure da dariya, yakama hannunta suka fice suna cigaba da dariyarsu, idan kagansu dolene su burgeka.
Cikin gida suka shiga, afalo duk suka tadda ahalin gidan, sunyi cirko-cirko suna kallon innah jimmai daketa zuba tsiya, ajiya labari ya isketa, da yamma ta'iso Abuja, saita kwana gidan wata mata dasuke mutunci, shine yau ta k'araso nan gidan domin jin ba'asin kama mata d'iya da'akayi.
Daga Aysha har ya khaleel, babu Wanda ya kalli ko inda take, khaleel ma saiya nufi dining inda su sultan ke zaune suna breakfast shida muhseen da Ramadan.
Duk gaidashi sukayi, muhseen yace, "ya khaleel wai baffah yahana atakama tsohuwarnan birki, please, kamana maganinta mana".
d'an ta6e baki khaleel yayi, yad'au mug d'in shayi yana k'ok'arin had'a shayin, " to inbanda abinka muhseen, tunda baffah yace abarta, aii sai kowa yazuba mata Na mujiya, lokacintane tayi, anjima kad'an koda kud'i aka had'ata tayi tari bazatayiba. kaga mik'omin kularnan tagabanka Ramadan, minene aciki?."
"Fankasunefa yau Anty Mamie tayi agidan, ALLAH nifa banason abinnan".
" saika zauna da yunwa aii, koka saka matarka ta girkamaka wani abun, ai su Mamie nema suka barku, kunyi aure amma har yanzun kuna nane dasu suna wahalar girka muku abinci, Ni kaga Zubamin guda uku".
Dariya mujahedeen dake k'ok'arin zama yayi shida Sultan, Sultan yace, "to ya khaleel kaimafa kana cikinmu, tunda gakanan a tebirin gandu".
Guntun murmushi yayi yana kur6ar tea, idonsa akan Aysha dake zaune kusada Anty Mamie tana 6ata fuska, Anty Mamie nabata abinci abaki, da'alama tsareta akayi kawai.
Ya kauda idonsa yamaida kan Sultan, " aini kasan lalurace yaro, dan matana batada lfyne kawai, amma soon bazaku ganniba anan".
Dariya sukayi gaba d'aya, wadda tak'ular da innah jummai, azatonta da'ita suke.
Dawowa tayi Inda suke tana zaginsu, babu Wanda yama kalli inda take acikinsu, bare tasamu amsa, saima cigaba da firarsu sukayi suna dariyarsu hankali kwance.
Sai kawai innah jummai tafashe da kuka, wai baffah da Ammah Nagani su Khaleel Kecin zarafinta, dama tasan Ammah Ba sonta takeyiba, kaza......kaza...haka taita surutai marasa d'ad'inji, babu Wanda yay koda tari barema ya tanka mata.
Har kowa ya kammala abinda yakeyi suka fito, motoci duk suka shishshiga, ganin haka itama innah jummai tabi ayari.>?#?=?M?

**********

Tafiyar mintoci kad'ance takawosu station d'in su khaleel, kowa yayi mamakin miyasa ya khaleel zai kawosu nan?.
Ganin ya khaleel ma'aikatan wajen sukayo caaaa akansa, sai k'amemasa sukeyi da Salutes nashi, suna tambayar ya jikinsa.
Su Aysha dai sai kallon ikon ALLAH sukeyi da girmamawar da khaleel kesamu daga ma'aikata nak'asa dashi, kuma sunsan wannan yana cikin adalcinsa da sassauci.
Su Kansu sai gaidasu akeyi cikeda girmamawa, kuma abin birgewa musulmai da wad'anda ba musulmanba kowa girmamasu yakeyi.
Ana cikin haka saiga Adams, saida yafara k'amewa da salute Na ogansa sanann Yakoma kan surukansa, ya gaishesu cikeda girmamawa.
Suma cikin fara'a suka amsa masa, da tambayarsa yadawo aiki?.
Yace eh.

Su Joseph ma duksun k'arasu, sun gaida su baffa sannan suka maida hankalinsu wajen khaleel dake magana.

Adams akaisu hall d'incan su zauna, ina zuwa, youseef ina buk'atar ganawa da momy".
Yay maganar cikin d'acin murya.
"OK sir".
Youseef yafad'a a girmamame.

Tafiya yake cikin karkashi da sassarfa, zuciyarsa Na harbawa da sauri da sauri, fuskarnan tamkar baita6a sanin miyema dariyaba.
Youseef yabud'e d'akinda hajia babbah take.
Kallo d'aya khaleel yamata ya kauda kansa saboda tashin hankali, dukta fita hayyacinta saboda k'aniyarsu da'akeci.
Daka ganta kasan atsorace take, duk gadararnan da tink'aho yagudu, aii bakin rijiya bawajen wasan makaho baneba, amma kunsan mutuniyar takufa, ganin khaleel saita d'auka yazo fiddatane, danhaka saiwata sabuwar d'agawa ta iso zuciyarta, tawatsa masa muguwar harara maicikeda tsana da bak'inciki.
Kauda kansa yayi yana k'ara tamke fusaka, yajuya yafita ahankaki, da yatsu biyu yayima taheer wata alama.
Kai kawai taheer ya jinjina masa, danya gane miyake nufi.
Tafiyarsa yacigaba dayi ahasale.

Su taheer d'aukar hajia babba sukayi aka fito da ita, saitaji kanta yak'ara fad'i da girma, aidama tasan dolene khaleel yazo ya fiddata, kobayaso tasan sai baffah yasakashi dole.
Wani k'aton d'aki aka kaita, suna ajiyeta suka fito.

................wata bajinta da k'arfin zuciyane ke k'arfafashi, sune suka taimaka wajen maidashi Ibraheem Abdallah d'insa jarumi, wanda baya d'aukar raini, cikin bajinta da jarumta jininsa ke zagayawa adukkan sassan jikinta, babu abinda fuskarsa ke nunawa sai fusata da harzuk'ar fushi.
Tunda yashigo d'akin momy kebinsa da kallo, bata ta6a ganinsa awannan yanayinba sai yau, lallale dolene kowa yadinga fad'in yana tsoron Ibraheem, ita kanta zuciyarta sai bugawa takeyi da k'arfi.
Da k'afa ya shuri kujerar dake kwance ak'asa yamaidata zaune dai-dai, cikin k'asaita irinta gadarar jarumta yazauna tareda crossing k'afarsa d'aya kan d'aya.
Momy takalli kanta ak'asa zaune, wani d'acine ya ziyarci zuciyarta, wai itace a k'asa Ibraheem Na zaune asama cikin sarautar gadara.
Zatayi magana ya dakatar da ita.
"Kinutsu, anan bada d'anki kike tareba, da Ibraheem Abdallah (j) kike tare, shikuma baya d'aukar raini awajen aikinsa, so ki kiyaye".
Cikin kwalo idanu waje momy tace, iyee, lallai Ibraheem, wuyanka ya Isa yanka, ka kalli tsabar idona kafad'amin haka?.
Kauda kansa yayi gefe, yace, " hajia laurah, ina fad'a miki kinutsu!!!!!!".
Yay maganar amatuk'ar tsawace.
Arajane hajia babba tad'anja bawa, baki bud'e idanu waje=?(?.
Saikuma taja tsaki tana watsa masa harara, "kai Ibraheem kashiga hankalinka, wlhy zan sa6a maka kammanni".
" ban hanaki hakanba kuwa, domin har yanzu kinada kimar amsa sunan uwa a idona"....
"Mtsoowww aikin banza, ina amsa sunan uwar takane kakecin zarafina ayanzu?, nagodema ALLAH daban 6ata lokacina wajen rainonkaba, wlhy Ibraheem danasan haka zaka zamema rayuwata, datun randa kazo duniya zan shak'eka kamutu, dabakazo gabana kanamin gadara da d'agawaba kuwa?.
Murmushi khaleel yayi mai ciwo, ya furzo huci mai zafi daga bakinsa, k'ok'arin maida kwallan data cika idonsa yayi, sannan yajuyo yana kallon hajia babba da razanannun idanunsa masu matuk'ar kwarjini da kad'a hantar mara gaskiya.
Aiko hajia babba ta razana ainun, dole tajanye idanunta daga kallonsa.
Cikin kakkausar murya yace, " hajia Laurah! Tabbas da ace kasheni kikayi alokacin sainafi jin dad'in hakan, dace kin kasheni alokacin dabanyi rayuwa da wannan zilwa jahainin fuskar takiba, daban rayu cikin gur6atacciyar tarbiyar azzaluma irinkiba, wlhy hajia laurah, saikin gwammace kasheni kikayi akan barina araye dakikayi, ninan Ibraheem Abdallah, saina sakaki yin nadama keda ire-irenki....
Da k'arfi ya tafa hannayensa.
Saiga Adams yashigo, da ido yamasa magana.
Adams ya jinjina kai yana komawa da baya.
Babu dad'ewa saigashi yadawo shidasu baffa, yajawo table dakecan gefe ya maido gaban khaleel, jakkar hannunsa ya ajiye, yashigo warwareta akan table d'in.
Bindugune dawasu wuk'ak'e aciki.
Su baffah sunyi cirko-cirki suna kallon ikon ALLAH, da tunanin mi khaleel zaiyi dawad'annan makaman.
Shikam har yanzu yana zaune cikin k'asaitarsa, sai hura hanci yakeyi cikin zafin rai.
Bayan Adams yagama khaleel ya kallesa, akausashe yace, "ina buk'atar khaltum anan wajen."
"OK sir!, angama".

Bindiga khaleel ya d'auka, yad'auki bullet hud'u yazuba acikinta.
d'akin yayi tsit, kowa fargabace ta kamashi, kardai khaleel yakashe hajia babba, su Anty zuwairah duk sunyi k'asa da Kansu suna kukan zuci, kokad'an basuga laifinsaba, sunsan akan dai-dai yake, tunda akan aikinsa yake, summafi jin zafin momy da laifin data aikata, Su Hasnah ma sun kasa kallo, duk cusa Kansu sukayi acinyoyinsu suna kuka ahankali.
Zuciyar inna jummai tashiga tsitstsinkewa dan tsoro.
Ana haka saiga Adams yataso k'eyar hajia khaltum, ita harma tafi hajia babba jigata, duk raunukane ajikinta, sai layi takeyi ahanya tamkar mashayiyar giya.
Rakwam tazube gaban khaleel kusada Aminiyarta.
Khan khaleel na a d'uk'e.
Kusan mintuna 3 sannan yad'ago idanunsa dasukayi jajur saboda 6acin rai, yazubasu akan hajia babba.....
Nunata yayi da bindigar ya d'ana kunamar, cikin kauda kai yace, " zan kiraki da momy akaro Na k'arshe, momy miyasakaki aikata dukkan wad'annan abubuwan?. wlhy inhar baki warware wannan k'ullinba saina tarwatsa kanki da wannan bindigar, bawasa nakeba, bakuma burga nakemikiba ko tsoratarwa, abinda ke raina nake fad'a.............
'



_please kuyi manage da wannan, yau ina busy sosai wlhy._


*_Typing=???_*


>?0? *_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_


*_Bilyn Abdul ce>??

*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of expert & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu=???)_


*_Gaisuwarku ta dabance sister, ALLAH yak'ara haske a rubutunku kuma, yasaka albarka arayuwar 'ya'yanmu baki d'aya, ngd da bibiyar buk d'innan dakukeyi, ALLAH yabar zuminci._*

Aysha Manshat (Ummu Zunnurain) Ummu Basheer, Maman Khady, Kdeey, Reefat yahaya, Aysha Umar Abubakar, miss xoxo (tawan nikad'i=? ?) Aneesa Abubakar rimi, Ummah shehu (Mrs Hameesu Taura) Maryam (Ummu Affan), Bily Sarki, Bily s fari.

_ALLAH yasaka albarka da haske arayuwarku._

_ban manta dakuba kuma 'yan groups d'in. *ZAMA NA AMANA* Na Admin Umar a Facebook da group d'insa Na WhatsApp, & *DEEJAH ABDUL NOVELS* da *UMMEE and AYSHA GARKUWA NOVELS*._

_nagode sosai da k'auna, wlhy nima ina k'aunarku aduk inda kuke, I love you wujiga-wujiga narantse>?8? @&>?8? @&>?8? @&>?8? @&>?8? @&=??=??=?
?=?
?=?
?d'd'd'=؋?=؋?=؋? '

4? 5?

"Ibraheem!! Kana nufin zaka iya kasheni?."

"Ba Ibraheem ba, Ibraheem Abdallah, kokice j! domin samun sauk'i, kisa aranki baki ta6a sanin wannan Ibraheem d'inba kawai, yafi miki sauk'i".

" iyeee, lallai d'an zaki yagirma".

"Young tiger! Baya ja'inja da kowa". 'Yay maganar yana harbin gefen hajia babba".
Rud'ewa tayi ta gigice daga ita har hajia khaltum d'in, su baffah kam duk rintse idanunsu sukayi, duk zatonsu khaleel ya harbi hajia babbane.
Saiga mutuniyar taku jiki Na rawa, har taune harshe takeyi wajen fad'in " zan fad'a maka komai wlhy yalla6ai, bama saika harbeniba, ALLAH ya huci zuciyarka Oga".
Wani murmushin mugunta khaleel yayi, yagyara zamansa yana wasa da bindigar a gefen kumatunsa, idonsa k'yam akan hajia babba.

_kamar yanda kowa yasani sunana Laurah, innah jummai k'anwace ga Halima (Ammah), uwarsu d'aya ubansu d'aya. ayanda innah keban labari tun suna k'anana tafi Ammah k'yawu sosai, amma abin bak'inciki mutane sunfi son Ammah, sukance Ammah tanada nutsuwa da girmama mutane, innah jummai kuwa akwai rawar kai, ga rashin kunya, ko iyayensu sunfi nunama Ammah soyayya fiyeda innah, kafin innah jummai tasamu Abu sai Ammah tasami ukunsa, tun alokacin innah jummai tatashi da k'iyayyar Ammah aranta, kullum burinta tayaya zata fi Ammah komai, aganinta tunda tafi Ammah k'yau, ita yakamata tafara samun komai kafin Ammah tasamu, amma ina, kullum Ammah ce asamanta._
_haka suka cigaba da rayuwa cikin rashin jituwa, kowa yana d'aukar hakan amatsayin fad'an sako, amma ita innah jummai har ranta takejin k'iyayyar Ammah, gidansu bawani karatun boko akeyiba alokacin, sai makarantar Allo, wata rana sundawo daga makaranta da hantsi, saisuka gamu dawani bak'o akan besfa=???, Ammah ce kawai ta gaidashi, amma innah jummai ta6ige da k'are masa kallo, saboda lokaci d'aya yasace zuciyarta, bak'onnan ya tambayesu gidan wani mutum dayazo nema, cikin ladabi Ammah tamasa kwatance, yamata godiya dasaka mata albarka, sannan yad'auki taro da sisin kwabo yabata, amma sai Ammah tak'i kar6a, yay magiyar duniya tak'i amsa, caraf sai jummai ta kar6e kud'inan, murmushi kawai yayi yaja besfa d'insa yatafi, itakuma Ammah tashiga yima innah jummai fad'a akan kar6ar kud'inanan, tun a hanya fad'a ya sark'e tsakaninsu, har sukazo gida._
_ALLAH yajik'an baba mai d'anwake mahaifiyar su innah, ta tambayesu abinda yahad'asu, Ammah ta sanar mata komai, fad'a baba tayima Innah jummai, sannan ta kwace kud'innan, ta aiki Ammah gidan da bak'onnan ya tambaya taje ta maida masa kud'insa. Wad'annan abubuwa dasuka farune suka saka Rufa'ee k'aunar Ammah, baiyi k'asa a guywaba yasamu Malam Saminu yayan mahaifiyarsa da wannan batu, shikuma yazo har gida yasanarma Malam yahuza babansu Ammah. Mutananda sunrigada sun gina 'ya'yansu akan tarbiyya mai k'yau, dan haka babu batun jin ra'ayin Ammah Malam yahuza yabadata. Saidaga baya aka sanar mata._
_wannan aure shine yazama sanadin k'arin k'arfin k'iyayya tsakanin Ammah da inna jummai, domin ita sosai takeson Malam Rufa'ee aranta, gashi awannan karonma Ammah takuma kwace abinda takeso a hannunta, daga wannan karon Innah jummai tad'auki aniyar tarwatsa Ammah dadukkan farincikinta, tadad'e tanamata bitada k'ulli amma babu nasara, har itama tasamu miji tayi aure, wato mahaifina, ALLAH ya azurtasu dasamun haihuwata, alokacin Ammah Nada 'ya'ya biyu, Abdallah da ma'aruff, Innah jummai Ce tayima Ammah asiri haihuwarta tatsaya, acewarta bazai yuwu Ammah tayita haihuwar mazaba itakuma gashi da mace tafara, ALLAH ya hukunta kwayayen haihuwar Ammah biyune kawai a duniya, shiyyasa bata sakeba, domin asiri yana tasirine da izinin ALLAH. Saidai kuma ubangiji ya nunama innah jummai iyakarta, domin itama tundaga ni saitaita haihuwar mazan suna mutuwa, wannan yasakata d'aukar burun ruguza 'ya'yan Ammah biyu._
_Tunda nafara zama budurwa ALLAH ya jarabceni dason Abdallah, har d'oki nakeyi idan yazo gidanmu, amma kullum innah jummai Na kwa6ata akan naciresama azuciyata, Dan bazata amince Na auresaba, bana saurarenta ko kad'an, dukda kullum karatunta naburin nayi kud'i yana tasiri azuciyata, Dan innah jummai batada burin daya wuce Na auri mai kud'i nima nazama hamshak'iyar mace, kodan ta nunama Ammah cewar tafita, ALLAH yatsareni daine kawai banta6a aikata siyar da mutuncinaba, amma ansha biyana kud'i nasamo budurwar daza'ayi iskanci da ita, idan nasamo kud'in kuma innah jummai bazata ta6a tambayata ina a samosuba, saima taita sakamin albarka da min kirari, *Laure, lauratun babanta, farar haihuwa adon kowace uwa*, kullum kirarinda Innah jummai kemin kenan idan akawo mata kud'i, wani zuwa da Abdallah yayi gidanmu gaida innah jummai na rud'e daganin yanda yazama cikakken mutum k'yak'yk'yawan saurayi San kowacce budurwa, tundaga wannan alokacin natada billi sai shi, inba hakaba kuma zan gudu daga gida, innah jummai namatuk'ar sona, alokacinne kuma taga yakamata ta yadda da aurenmu kodan mu mallake dukiyar da Abdallah Muke tunanin yanada ita, alokacinma shi bawani kud'ine dashiba, rufin asirin ALLAH ne kawai._
_nasan Abdallah bays sona, an tursasashi aurenane kawai, domin yanajin maganar iyayrnsa, itakuma Ammah tayarda da aurenmune domin k'arin k'arfin dank'on zuminci itada 'Yar uwarta, batasan burin 'Yar uwartata tarwatsata baneba. abinda ya tada hankalina nida innah jummai shine haihuwar mata Dana fara, domin burinmu bai wuce nahaifi 'ya'ya mazaba danmu mallake dukiyar Abdallah, bayan haihuwar Zuwairah inada cikin shikurah muka had'u da hajia khaltum taje sibiti ganin likita itama, tundaga nan muka kullah k'awance, tacemin a Abuja take aure, yanzuma tazo Kano bikine zazza6i yakamata tazo ganin likita._
_bayan haihuwar shukurah babu dad'ewa sai Abdallah yazomin damaganar k'arin aure, ankai ruwa rana sosai saboda Innah jummai da Khaltum suna zugani akan karna yarda nabar Abdallah k'ara aure. ALLAH ya rubuta fad'ima saita zama matar Abdallah, saigashi anyi bikinsu, tunda fad'ima tashigo gidan nahana kowa zaman lafiya, sannan duk cikin data samu saina zubar dashi ta hanyar bata magani batareda tasaniba, Dan banaso tahaifi namiji kafinni Na Haifa, bazai yuwu tagaji dukiyarsaba bayan nafita shan wahalar zama dashi, wannan rashin zaman lafiyar tamu yasaka Abdallah auro Bilkisu, nanma ansha fama kam sosai, zuwan Bilkisu gidan naso muhad'e kai da ita, danna samu nariga 6arar da cikin daduk zata d'auka cikin hikima, saboda aringa jingina hakan ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login