Showing 105001 words to 108000 words out of 155647 words

Chapter 36 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

488


*****

Sam.... Kuwa sarkin naci yana nan la6e har kusan bayan magriba=??.
Harya fara hasashen Barin wajen saiga wata tafito daga gidan su khaleel, cikin dogon hijjab da Nik'af.
Su Samuel sunsan kan aiki sosai, aikam baiyi k'asa aguywaba wajen bin matarnan, saida sukayi nisa da layin tatare taxi tashiga, shima tarewa yayi yashiga, adabara sukebinsu, har zuwa anguwar su hajia khaltum.
Sam....yagane gidan hajia khaltum, Dan shine yasato sakeena lokacin.
Da sauri ya sallami mai taxi, wayarsa yad'auka yakira number sakina, danya kar6i number d'inta alokacin, kuma ta tabbatar masa babu wanda yasan tanada waya agidan.
Saida takusa tsinkewa tad'aga, murya k'asa-k'asa tace, "yalla6ai wlhy kad'an yarage akamani, ina wajen bama bak'uwar hajia ruwa kakirani".
"Yauwa, wace bak'uwace".
" hajia Laurah maman yalla6ai khaleel".
"Da gaske?".
" ALLAH kuwa".
''Yauwa Sakina, kisaka musu ido, idanma da dama kiyi recording d'in dukkan wata hira dazasu kituromin, ki kula sosai".
"To shikenan, dama nazo had'a mata kunune, kuma nagama, zansan yanda zanyi Na ajiye wayar a d'akin idan nashiga".
"Yauwa, saina jiki".

**
Sakina tayi duk dabarar dazatayi ta ajiye wayar, bayan ta danna record, tabaro d'akin.
Su hajia khaltum basusan mike faruwaba suka baje faifan hira kuwa, sosai suka tattauna akan abinda yafaru yau, dakuma meeting dazasuyi Na k'ungiya gobe, kuma duk akan su khaleel ne..
Itako waya babu ruwanta, tanata nad'e komai.
Sai wajen around 11 hajia babba tabar gidan, driver zai maidata gida.
Hajia khaltum tatafi rakata sakina tayi wufff tashige d'akin, ta d'auke waya ta 6oye bayan tayi hanzarin saving d'in recording d'inta.
Tana k'ok'arin fitowa sukaci karo da hajia khaltum, kallon tuhuma Tamata, Dan babu wani d'an aiki da hajia khaltum ta yarda dashi agidan.
" k miya shigo dake d'akinane?".
"Wlhy babu komai hajia, nazo tartare kayan dakukayi amfani dasune, saboda zanyi wanke-wanke".
" shine kuma bazaki jira nakiraki ki d'aukaba, Kodai la6e kikaimin?".
"A'a Ammi, nicefa natasotama yanzu tana barci wlhy".
Babie Ce mai maganar tana fitowa daga d'akinta.
Shiru hajia khaltum tayi tana kallon babie, dawannan Damar sakina tazare jikinta tabar wajen, dama zuciyarta sai dukan 100-100 takeyi.
Saida tagama wanke-wanken sannan tashiga toilet d'in d'akinsu Na 'yan aiki ta turama Samuel record d'in.
Shikuma adaren yaturama Taheer.
Bak'aramin tashin hankali Taheer yashigaba, dan lamarin ya rikitashi, mahaifiyar mutum mai gaskiya da sanin darajar aiiki takasance cikin manyan criminals da suka gagari k'asa, wannan wace irin rayuwace?.
Shiyanzu yaza'ayi ya tunkari j da wannan batun?, kuma aii dolene yasan komai dangane da operation d'in, tunda bak'aramin aiki baneba.
Hakadai yayta k'ullawa da kwancewa, daya kasa hak'uri saiya kira youseef da Joseph ya shaida musu, sumafa zancen ya firgitasu ainun, sukaita tattauna yanda zasu 6ullowa lamarin, aganinsuma gara khaleel d'in yakamata dakansa akan su sukamata.
Sundai yanke shawarar sanar masa tawata sigar, amma ba gaba da gaba ba.


*******
A setetion khaleel yakwana yau, haka suma su Doctor Abraham sunata aikinsu.



*_Monday morning_*

Ranar litinin misalin k'arfe 9am khaleel yazo gida a gaggauce yay wanka yakoma setetion d'insu, babuma wanda yasan yazo gidan, harya fice.
Dama tunjiya babu walwala ga kowa, tamkar anyi mutuwa haka gidan yake, kuma kowa kwana yayi gaban ubangiji yanda mik'a kukansa akan wannan Matsala data tunkarosu.
Masu aiki wasu sunfita, wasu kuma sunata shiri, hakama masu zuwa makaranta.
Hajia babba tana cikin wad'anda suka fita.

Khaleel Na dawowa office yawuce kawai, zamansa dakamar mintuna 27, saiga Dr Abraham, izinin shigowa yabasa.
Dr Abraham yashigo, yay salute d'in khaleel sannan yabashi damar zama.
"Sir! Tabbas bincikenmu ya nuna Madam taci guba da farko, kamar yanda likitocin General hospital suka tabbatar, kuma taci abinne da mintuna 19 kacal yafa aiki ajikinta, saboda kad'an dataci yahana gubar k'arfinsa tasiri ajikinta, munduba raken da'akace tasha kafin meatpia babu komai acikinsa, kuma tsakanin shan raken dacin meatpia yad'auketa awanni 5 dawasu mintuna, sannan meatpia d'in da sauran mutanene gidan sukaci babu guba aciki, hakama Wanda ka kwashe bayan madam ta 6arar babu gubar".
" Amma gurinda meatpia d'in ya6are muka zuba ruwa tareda zuk'ewa ya nuna anan akwai guba, ('Yar zabura khaleel yayi, amma baice komaiba), Dr Abraham yacigaba dafad'in " dalilin dayasa muka gane gubar shine, akwai 6ar6ashin meatpia d'in awaken, Wanda ruwan damuka zuba ya narkar dashi har muka sami damar gane akwai guba. akwai kuma wani guntun damuka samu gabda zamu baro d'akin shima akwai guba aciki. Sannan kwanon shima maik'on mai daya manne ajiki yanuna akwai guba".
"Tabbas abinda nalura dashi Annan shine bayan madam ta 6arar da meatpia d'in, inhar kunbar d'akin to wani yazo yakwashe meatpia mai guba, ya canja damara gubar, Dan kenan wanda mutanene gidan sukaci shi babu guba aciki, Wanda madam tacine kawai mai guba".
" abin kuma mamaki Na uku shine gubar dake cikin meatpia d'in irintace aka bama David yasha aruwa..........
Babu shiri khaleel yamik'e tsaye tsaye, "doctor ka tabbatar hakane?".
" yes sir!, babu kokwanto a cikin aikina, ga dukkan bayanan Na tattara a file d'innan Kaduba kuma, harda Na David ma nasaka maka duk da nasan kanadashi".
Gyad'a kai khaleel yayi, shikuma doctor Abraham yafice.


Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un kawai khaleel yake Ambata, kenan da gaske momyce tabada guba da hannunta dansuci? To Aysha tabamawa koko shi? Yasan Momy batason Aysha, amma baikawo zata iya yunk'urin kashetaba, to mima yasaka gubar tazama dai-dai da wadda Akabama David?.
Komawa yayi yazauna, yana duba file d'in da dukkan bayanan ciki.
Kusan awa 1 ya d'aukeshi.
Saiga Samuel yayi nock d'in door.
Izinin shigowa yabashi.
Bayan ya k'ame tareda salute Na khaleel yabashi izinin zama.
"Samuel yadai?, komun samu wani abunne?".
" yes sir, mai muhimmancima kuwa, akwai wani meeting d'in sirri daza'ayi yau, kuma harda matarnan hajia khaltum wadda taturama barau modibbi sak'o aciki".
" Masha ALLAH, a ina kenan Sam...?".
"Ga dukkan bayanan inda taron zai gudana annan, nima nasamu bayananne a majiya mai k'arfi, tun sanda kabani aikin bibiyar hajia khaltum banyi k'asa aguywaba".
" da k'yau sam..... Da irinku Muke alfahari a hukumarnan".
'Yar dariya Samuel yayi, yace, "aii tarbiyyarkace sir".
Khaleel baice komaiba, yafara duba bayanan.
Sosai yayi farinciki, duk da kwakwalwarsa da tunaninsa suna cikin wani yanayi, amma hakan bazai hanashi fuskantar wannan aikinba shima, tabbas yana kammalawa dashi zai maida hankalinsa kacokan akan Momy, daduk wani mahaluki dake gidansu.


Nace hummm, khaleel kenan, kwantarma da hankalinka, ALLAH ya sauk'ak'a maka.>?*?.



__________________

*_4:30pm_*


*_IDAN KERE NA YAWO?#?>?#?._*

Su khaleel sungama shiryawa tsaf, anyima bindugu saves da bullet, hakama handcuffs and'iba dayawa.
Motoci kusan 7 aka d'ibi ma'aikata aciki, amma duk sai suka rarrabu, ko'a cikin setetion d'in bakowa yasan inda zasujeba, saboda tsaro, amintattunsune kawai aka d'iba.
Nesa dawajen taron suka ajiye motocin.
Duk sanye suke cikin Uniform d'in aiki, babu mai fuskar rahama acikinsu kuwa.
Cikin hikima suka sami wajajen mak'alk'alewa, Dan wajen meeting d'in cike yake da tsaron 'yan ta'addah.

Tsitt d'akin meeting d'in yake, su Momy duksun nutsu suna sauraren jawabin shugaban k'ungiyarsu............
'




To yaudai kam, zamuce k'arshen tika-tika tik, masoyan hajia babba sainace amin afuwa, dominfa gobe itace ranar bankad'ar sirrikan 6oye, ranar bayyanar abubuwan mamaki, Wanda bakowama yayi zaton hakanba, mutane dayawa dazasu bayyana muku ta sigogi da dama=?A?.
Tabbas akwai abubuwan mamaki, al'ajabi.
Nikaina bilynku nak'agara gobe tayi aradu>?8? @&>?8? @&>?8? @&>?8? @&>?8? @&=??=??.


Happy day fan's

*_Typing=???_*


>?0? *_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_


*_Bilyn Abdul ce>??

*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu=???)_

*_ASSALAMU ALAIKUM MASOYANA!!_*

_Awannan ga6ar kam zan baku hak'uri, amin afuwa sosai, nasan wasu basajin dad'in yanda sukemin comments a groups amma bana magana, wlhy abubuwan yawa sukemin, zaka kula da Oga da safe, kafin yafita, yana fita aikin gyare-gyare zakayi, sannan nafita islamiyya, nadawo 12, wlhy ina dawowa typing kawai nake zaman yimuku, wahalar typing takan d'aukemu lokaci mai tsawo, saboda abune Na nazari, wani lokacinma saikin kusa gama page kiji baiyiba, ki goge kiyi wani kuma, kunga kafin mutum yagama kansa yad'auki zafi, sauri kake kagama ka fuskanci aikin gida kuma, wani lokacin kiyi bak'i, ko fita takamaki kekanki, ALLAH akullum ina gamo da messages Na PC samada 150, rasama ta ina zan fara nakeyi, gakuma Na groups, groups yakai 40 wanda nake a ciki, wasu kunyarsu take hanani fita kawai wlhy, lokacin dazan gama typing kaina yad'auki zafi sosai, saina dingajin gandan duba sakwannin PC, amma dankarkuga kamar inamuku wulak'anci nake daurewa naduba, shiyyasa nake d'auke idona ana groups, amma wlhy inajin dad'i sosai, kuna sakani farinciki ainun, badankuba banga amfanin rubutubba, tunda bazan rubuta danna karanta nikad'aiba, duk inda masoyina yake nima ina matuk'ar sonsa da alfahari dashi, babu abinda zance daku saidai ALLAH yabar zuminci, k'aunarkuce ke sakani wajen 6ata lokacin yin typing kullum da siyen data, I love you so much my fans, babu marubucin dabaison masoyinsa, duk muna k'aunarku wlhy=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?d'd'd'd'd'd'd'._
Amin afuwa please, kuna raina wlhy=?A?=ؘ?.


3? 9?

Su khaleel sunada yawa sosai, amma dukda haka su hajia babba sunfisu yawa, danma ankama wasu aciki, sauk'in d'ayane bakowa keda makami acikinsuba.
Dukda jikin ya khaleel a sanyaye yake, kuma baisan daliliba, amma hakan baihanashi aro jarumtaba ta musamman ya k'arfafawa kansaba, daboda gudun Matsala.
Acikin kwarewar aiki suke shiga wajajen, duk wanda akayi karo dashi kuwa cikin dabarar aiki suke gamawa dashi, basuda mafitar data wuce kashesu, saboda suma suna samunsu kashesun zasuyi tunda akwai nakamai a hannunsu.
Bawai k'aramar k'ungiya baceba, k'ungiyace data tara manyan mutane, masu muk'amai kala-kala, ga dukiya sun tara, saboda business kala-kala dake gudana cikin k'ungiyar, kuma Na manyan kud'i.
Karya wuyan wani da khaleel yayi bayan nannad'e kansa aleda yasakani rintse idanu, sosai tsoro yashigeni, danganin yanda zukatansu khaleel suka gama bushewa, basajin komai wajen kisan garatan nan.
Matsalar da aka samu shine cctv camera dake aiki acikin d'akin taron, wadda su khaleel basusan da itaba.
Wad'anda suke kulada cctv camera d'inne suka ankarar da 'yan k'ungiyar.
Tashin hankali kenan, wai Wanda ba'a saka masa rana, kusan shekaru 29 k'ungiyar Na aikinta. Amma basu ta6a gamo da makamancin tashin hankalinnanba, saidai amusu tsinci d'ai-d'ai badai gaba-da gababa, don ko kad'an basu aminta wani yafidda sirrinsuba, komai cikin ilimi ake yinsa.
Hargitsewa hall d'in yayi, masu makamai suka fara d'ana kunamin bindugu, irinsu Momy kam sai neman wajen 6uya.
Musayar wutane yafara gudana a tsakaninsu, bakajin komai sai k'arar harbe-harbe.
'Yan jarida kam dasu khaleel sukazo dasu sai d'auka sukeyi, lamarin kaikace film ne wlhy.
Shirin ma'aikaci da d'an ta'adda bazaizo d'ayaba, dukda gawurtar k'ungiyar su hajia babba takai taringa bama matasa training saboda gudun zuwan rana irin wannan ta kota kwana.
Tiyagas su khaleel suka fara jefawa cikin hall d'in, dama su sun d'auki matakan kare kai, dandanan wajen yakacame da tari da atshawa, gashi hayak'in yana saka hawaye, masu ciwon asma kuwa saidai addu'a kawai.
Jefa tiyagas yaba su khaleel damar shiga hall d'in, dukda haka akwai masu taurin zuciya dake harbi har yanzun.
Amma haka su khaleel sunata samun nasarar cafke wasu, Dan k'ungiyar ta tara maza da matane, harda wad'anda tunaninka bazai ta6a kawo maka ganinsuba awajen, saboda Girman milki ko dukiya.
Akwai k'ofofin fita da dama acikin hall d'in, wannan ne yabama wasu dama sulalewa, amma ina, wannan shine angudu ba'a tsiraba, dankuwa cikinsu khaleel wasu sun bisu.
Acikin masu guduwa kuwa harda hajia khaltum da hajia babba.
Lamarifa yaci tura, komai yagama hargitsewa, acikinsu khaleel dayawa sun sami harbi, 'yan k'ungiyar kam ba'a magana, bayan wad'anda aka antaya barzahu akwai masu harbi a sassa daban-daban.
Kusan awanni 3 aka d'auka ana Abu d'aya, lamarin kamarma bazai k'areba, kowa yafita hayyacinsa, Dan babu Wanda baiji jikiba, ansami cafke mafi yawa acikinsu, wad'anda suka samu raunuka akafiddosu waje, gawawwakinma haka duk an fiddosu, wad'anda suke k'alau kuwa handcuff aka saka musu, duk aka fito dasu waje, 'yan jarida sunata aikinsu.
Ya khaleel yafara bin ma'aikatansu yana dubawa, Dan a tantance wad'anda suka mutu, dakuma rauni, duk a wahalce suke.
Khalee yace, "amma akwai wad'anda babu acikinmu?".
''yes Sir! Wasu sunyi yunk'urin guduwane, shine suka bisu".
"OK!, yakamata azuba wad'annan amotocin da aka kawo, suma akirasu aji?".
" OK sir".

Wad'anda basa wajen aka shiga kira, wasu suce sun kamasu, wasukuma suce sunadai binsu binsu abaya har yanzu, amma suna buk'atar k'arin ma'aikata.
Taheer dai cayayi ahad'ashi da khaleel.
Faruk yamik'ama khaleel wayan cikin girmamawa.
A kunne yakara batareda yayi maganaba, daga can Taheer yace, "sorry sir idan bazaka damuba kazo da kanka, wasu mutane hud'u sun shiga gidanka, bazai yuwu mushiga babu izininkaba".
" gidana kuma Taheer?".
"Yes sir?".
''OK ina zuwa, kubani k'ank'anin lokaci".

Saida khaleel ya tabbatar anzuba sauran a mota, wad'anda suke buk'atar k'arin ma'aikata aka tura musu, wasu kuma suka tafi da motocin wad'anda aka kama, ma'aikatasu kam tuni anyi gaba dasu Dan basu taimakon gaggawa.
Ya khaleel kansa yasamu raunuka, amma bai damu da kansaba, Na k'asa dashi kawai yake son abama kulawa.
Key d'in mashin yakar6a ahannun wani ma'aikacinsu, yanufi gida zuciyarsa Na dukan 100-100 saboda fargabar abinda zai Tatar, kenan zarginsa yazama gaskiya, acikin gidansu akwai mai mu'amullah da k'ungiyar? jiyake tamkar zuciyarsa Zata kama da wuta saboda bak'in ciki da fargabar wanda zai tarar amazaunin d'an k'ungiyar.
Ak'ofar gida yay gamo dasu Taheer dake tsaitsaye, basu shiga gidanba, saboda girmama ogansu.
Bai tsaya garesuba, horn kawai yayi d'an gwari yabud'e masa gate yashige da mashin d'in, suna su Taheer duk sai suka shiga.

Tunda su hajia babba suka sami nasarar baro hall d'in kaitsaye nan gida suka nufo afirgice, sunyi imani da cewar idan anan gidan suka fake khaleel bazai ta6a kawosu aransaba, tunda bai gansuba, amma hajia babba da idanunta taga khaleel.
Babu Wanda yasan sun shigo gidan, sai mutane kh'alilan, gaba d'ayansu arud'e suke, hajia babba kuka takeyi da idanunta, takasa zaune takasa tsaye, khaltum kam ba'a magana, dama kunsanta afagen tsoro, sai mutum biyu dasuka gudo tare, suma duk matane, d'ayama budurwace, d'ayar kam zata iya zama sa'ar khaleel.
Ko kafe mashin d'in baiyiba yasakeshi anan, sai cikinsu Taheer ne wani yagyara farking d'in mashin d'in.
Taheer ya nuna masa motar dasu hajia babba sukazo, khaleel baisan motarba, Dan bata gidan baceba, saikace mayunwacin zaki haka yanufi d'an gwari datun shigowar su khaleel yake arud'e, Dan yasan tabbas babu lfy yau agidannan, cikin daka tsawa khaleel ke tambayarsa waye yashigo da motarnan gidannan?!!.
Hargowar khaleel ce tafara jawo hankalin mutanenen gida, suka fara fitowa d'ai-d'ai.
Jikin d'an gwari rawa yakamayi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login