Showing 87001 words to 90000 words out of 155647 words

Chapter 30 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

463

dazai zubama mufeedah batajiba bata ganiba, saikawai tarushe da kuka data tuno lalacewar rayuwa irinta Habeeb.
Ba ya khaleel ba, hatta inna jummai mahaifiyarta kukan d'iyarta yad'aga hankalinta, sukai cirko-cirko suna kallon yanda ya khaleel ke lallashinta, dak'yar yasamu tayi shiru.
Bayan tagama shan shayin da ya khaleel ya lalla6ata, ya 6alle magungunanta yabata tasha, baffahma yashigo yadubata, kusan mintinsa 30 sannan yafita, hakama su mama duksun shigo sun dubata, dukda dai k'in amsamusu tayi, danji take kamar takashesu tahuta Dan bak'in cikin sanin sirrinta dasukayi, saidai babu damar hakan kuma.>?*?


***********

Kusan 10pm ya khaleel Yakoma 6angaren Ammah, ya tarar Aysha hartayi barci, Ammah ma zaune take tana kallo da gyangyad'i, Amma dan k'unata tak'i taje ta kwanta, wai film take kallo, gashima ba Hausa akeyiba bare ace tanajin misuke fad'a, kamarma yaren Germany akeyi.
Cikin sand'a yawuce tabayanta yashiga bedroom d'inta, Aysha Na kwance a gadon ta k'udundune da k'aton bargon Ammah, barci takeyi, saidai dagani kamar batajin dad'in barcin, yakwanta ahankali ta bayanta, mannata da jikinsa yayi, yasaki sassanyar ajiyar zuciya, idonsa alumshe ya sumbaci wuyanta yana shinshinar k'amshinta, yasan Aysha dabance a fagen tsafta, ko 'Yar ahekara 100 taganta tabari, gabanta yadawo, yasumbaci goshinta da la66anta data ta6e kamar zatayi kuka, murmushi yayi yana zagaya la66an da d'an yatsansa, kamar tasan miyakeyi tagyara bakinta yakoma normal, wani murmushin yasaki, sannan ahankali yad'ora bakinsa, kad'an yay kissing d'inta yajanye bakinsa, saboda motsi data fara.
Maganar Ammah yajiyo sama-sama, dasauri yatashi Yakoma bakin gadon ya zauna, addu'oi yayma Aysha ya tofeta dasu, jiyake kamar karya barta wlhy, Dan yana buk'atar jinta ajikinsa, amma yasan jarabar Ammah bazata yardaba, gwara yabarta nanda kwana biyu saiya lalla6ata tabashi ita.
Ammah data shigo tarik'e kunkumi=?o?
@&, "kaikuma yaushe kashigo saikace wani Aljani?".
" kinacan kina gyangad'i yazakisan Na shigo".
"Kajimin d'an jakar uba, yo bakaida matarka bane kuka jamin, tunda safe bakubar uban kowa yayi barciba, nitashi katafi saida safe".
" ko bakicebama zantafi aii Ammah, saidaifa ga amanata nan, nabaki kirik'e gam-gam, karki saki baki kita barci taita shan wahalar ciwo cikin dare".
"Ank'i kar6ar Amanar taka, tashi kafita kafin nakira ubanka nasanarmasa".
"A'a aiba'azo nanba Jar wuya, kinga saida safe, nasanki jar wuyace, dolene nayi shakkarki"..
''Kaidai kasani fitsararre dogon banza".
Haka taita mitarta ita kad'ai, saida tayi mai isarta sannan ta kwanta tayi musu addu'a, Dan Ammah akwai kulada addini, shiyyasa ta tsaya tsayin daka jikokinta suka samu ilimin addini, gashinankuwa kowa yanacin ribarsa.
Damma zakkar mufeedah dasuka fitar.



Nace, " itama Jamata akayi aii>?7? @&".



_____________________________

*_Washe gari_*

Dak'yar ya khaleel ya iya tashi, Dan baisamu barciba sai gab da asubahi, bayan yagama nafilfilinsa kamar yanda yasaba, yay addu'oi da mik'a godiya ga ubangijin talikai, dayay masa gagarumar k'yauta, yayta jero kirari wa ALLAH, harda kukansa. Around 2 yakwanta, Amma sai barcin ya gagaresa, jiyayi yana kewar matarsa, gashi dama tunda yadawo daga tafiyarnan basu sakeba, saboda bak'in Kano dasuka sauka 6angarensu, gakuma hidimomin biki da rashin lafiyar Aysha,, har kusan 3:19am yanata juye-juye, iskar asubace data kad'a barcin ya kwashesa, shinefa haryatashi duk babu dad'i.
Alwala yayi yafita masallaci, bai dawo gidanba saida gari yay shaaa.
6angaren Ammah yashiga, yatarar tana lalla6a Aysha tayi sallah, itakuma tana complain d'in jiri take gani.
Yamatsa yarik'e Ayshan, yace, "Ammah jekiyi azkar d'inki, bara Na taimaka mata tayi sallan".
''To iro", 'Ammah Tafad'a tana sakar masa hannunta Aysha.

Da taimakonsa tayi sallan, tana idarwa tazame ta kwanta awajen, d'aukarta yayi yamaida bisa gadon sannan yafice.
Itama Momy yaje yadubata, sannan Yakoma 6angarensa yay shirin office.
Cikin Suit blue black yafito, yayi k'yau sosai, sai baza k'amshi yakeyi, (duk bin kwankwantonka Baka Isa banbance turaren ya khaleel ba), kullum dakalar k'amshin dazakaji yanayi, saida yashiga suka gaisa da baffah, hakama uncle ma'aruff, yashiga kowanne 6angare Na Matan gidan suka gaisa, sunyi sallama da 'yan Kano yamusu alkairi, Dan yau zasu wuce, kai dukma wani bak'o da biki ya kawoshi yaune zai wuce, harda Na 6angaren Momy, dama kusan dangin babantane dakuma k'awayenta, saikuma innah jummai, Amma yaga alamar itad'in ba yauba, kakarsace Amma babu wata shak'uwa tsakaninsu, Dan bata sakewa dashi ko jansa a jiki, shima shiyyasa ya watsar da lamarinta, saiyaje Jigawa sau uku bai lek'a Inda takeba, gwamma yaje gidan inna mahaifiyar Anty Mamie susha hirarsu, taita masa gata kamar itace kakar tasama ta gaskiya, shiyyasa shima yakeji da ita kuwa.
Yashiga 6angaren Ammah ya tarar har yanzun Aysha barci takeyi, Ammah tamatsa masa yasha tea a tsaitsaye yafice, bayan ya ajiye mata kud'i wai ko Aysha tana buk'atar wani Abu.
Godiya Ammah tamasa tarakashi da addu'a, shikuma yafita yana amsawa cikin jin dad'in addu'ar kakar tasa mai sonsu da k'aunarsu.

Yana fitowa suka had'u da Ema... sai Samuel, yaukam babu Adams, yanacan yanashan amarci.>?*?.lol
Samuel ne yau amazaunin Adams, bayan sun gaisheshi da salute nashi Sam...yabud'e masa mota yashiga sannan yamaida yarufe.
Sauran securitys nashi suma duk suka shiga mota sannan suka tafi.



___________*
Yakamata kibar kukannan haka mufeedah, ninama rasa miya kaiki aikata hakan batareda d'aukar wani matakin kare kaiba, haba mufeedah, ba'a bama namiji kai hakanan babu tsaro aii".
Cikin share kwallan mufeedah tace, "wlhy Anty kubrah bansan hakan tafaruba, dan saida nad'auki kowanne mataki, nibanma San miyaja ra'ayinaba wajen aikata zina?, dukda nasan buk'atar aure da yaudarar beeb guy ta tataka rawar gani wajen zirmani, bawai abinda Na aikata bane yasakani kuka, asarar miji mai k'yak'yk'yawan hali irin Ameenuddin danayine yake ta6a zuciyata, wlhy inasonsa Anty Kubrah, Amma kowa yakasa fahimtar hakan".
Rungumeta kubrah tayi tana lallashi, saida mufeedah ta tsagaita da kuka sannan tace, ''ki kwantar da hankalinki, da yau zanbar k'asarnan, amma saboda matsalarki Na dakata, yanzu zanje Lagos insha ALLAH agobe zan dawo miki da maganin dazaisa wannan cikin yabi rariya, karki damu dabatun Ameenu, dakansa zai dawo gareki kinji".
" amma Anty tayaya kenan?".
Cikin murmushi kubrah tace, "karki damu ki zuba ido kedai".
" shikenan Anty ngd sosai da kulawarki gareni, ALLAH ya dawo fake lfy".
"Ameen".

Duk hirar da kubrah da mufeedah keyi a kunnen Aleeya ne, amma batace uffanba, tadayi shiru tana kallonsu, har Kubrah tabar d'akin.
Kobayan fitar kubrah Aleeyan batacema mufeedah wani abuba, saima harkokinta datakeyi...............
'








*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu ameen_*=?O?

*_Typing=???_*


>?0? *_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_


*_Bilyn Abdul ce>??

*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu=???)_


_bilyn Abdull bata manta dakuba 'yan *BBC HAUSA NOVELS* wlhy ina k'aunarku kamar yanda kuke k'aunata, ngd sosai da comments d'inku, ALLAH yabar zuminci, I love you wijiga-wijiga Alkur'an sisters._
=??d'd'd'd'd'd'>?8? @&.


3? 3?

Su ya khaleel Na isa office aiki kawai yafarayi, yakwana biyu baizo office ba, saboda tafiyar dayayi, dukda dai akan aikine shima, amma baihana yatadda jibgin aikiba dake jiransa a office.
Zamansa dakusan mintuna 40 kiran Taaheer yashigo wayarsa, harta kusan tsinkewa yad'aga.
Bayan sun gaisa taheer ya tabbatar masa da wadda zasu kama tafito.
"A'a mikuke jira, Ku kamata mana, damani banaso akamata cikin gidanmune kawai ne".
"OK sir".

Duk suka yanke wayar suduka.

Aiki ya khaleel yakeyi amma zuciyarsa tarabu gida biyu, rabi akan Aysha rabi wajen matar dasu taheer zasu kama.
Yana tsaka da tunaninnan akayi knocking d'in k'ofar office d'in, umarnin shigowa yabada, youseef yashigo hannunsa d'aukeda takardu, saida yayi salute nashi, ya khaleel yanuna masa kujerar zama sannan yazauna, hannu yabashi sukayi musabaha.
Yauseef yace, "sir, gashi munsami mutum kusan 16 masu tambarin kunamarnan".
Da sauri ya khaleel yakar6i takardun yashigo dubawa.
Saida yagama tsaf sannan youseef yacigaba da maganarsa.
" tabbas barau modibbo yana ciki, sannan akwai yaron Alhaji bishasha Lazarus shima yanada ita, akwai yara da'aka kama agidanka suma duk sunada ita.
Cikin mamaki ya khaleel yake kallonsa, kallo irin Na tabbatarwa.
Youseef ya jinjina masa kai alamar gaskiyane.
Huci mai zafi ya khaleel yafurzo daga bakinsa, gaskiya wannan lamarin yafara d'aure kansa, shin miyasa hakan kuma?, kenan da gaske akwai mai alak'a da wannan k'ungiyar acikin gidansu?, (zuciyarsa tana karkata ga zargin Aysha ne, musamman idan yatuna da lokacin da'aka sanarma barau modibbo zuwansu, ya tabbatar Aysha ce kawai taji hakan, amma to mizai sakata tiromusu 'yan Daba kuma? Bayan harda ita zasu cutar?, tokuma ya'akayi tasan talatuwa mai aikin Hajia khaltum ce?, kenan tanada alak'a dasu?, musamman idan Yakuma tattara bayanan matashiyar budurwa sakeena.
Kai, bai yarda da zuciyarsaba, yabibiyi Aysha amma haryanzun bai kamata dawani Abu dayashafi wannan k'ungiyarba, yakamata gakuma sato masa Sakina, zaimata wasu tambayoyi.......
Youseef ne yad'an buga table yace, "sir!, lfy kuwa?."
Da Sauri ya khaleel yakawo numfashi, kuma furzar da hucin yayi sannan yace, "babu komaiba youseef, cigaba ina saurarenka".
Ajiyar zuciya youseef ya sauke shima, yacigaba dafad'in sannan akwai wasu 'yammata biyu damuka kama kusan 3years kenan da cocaine a airport d'in Lagos, suma sunada wannan tambarin kunamar."
Cikin jinjina kai ya khaleel yace, ''kunyi k'ok'ari youseef, kuma kucigaba da aikinku cikin kulawa, ina alfahari daku sosai".
Murmishin jin dad'in yabon da ogansu yayimusu youseef yayi, yace, "duk wani kwazonmu yanadaga cikin tarbiyarka Sir".
Murmushi kawai ya khaleel yayi, yace, "babu damuwa kaje, zuwa anjima zan nemeku kaidasu Joseph".
"Ok, thanks sir".
Ya khaleel ya jinjina Kansa yacigaba da aikinsa.


__________________________

Cikin nasarar aiki su Taheer suka sami damar cafke kubrah, a babban filin jirgin sauka da tashi Na Abuja, ankamatane tana k'ok'arin tafiya Lagos. mamaki yayi matuk'ar kama Taheer, Dan yasan kubrah sosai, tadad'e tana kamun k'afa dashi akan yashawo mata kan khaleel yasota. Yamzu har yarinyarnan zata iya ta'addanci haka?. Kai yanzukam ya gama yadda ba'a shedar mutum.
Kallon-kallo kubrah da Taheer sukayi, sai gumi takeyi da rawar jiki. pretending tafara musu, akan mitayi daza'a kamata?, tanayin hakanne kuma saboda taga Taheer, atunaninta zata samu sassauci daga gareshi. Amma abin mamaki saiya nuna halin ko inkula da ita, saima ka rantse baisantaba.
Cikin yaran taheer wani yadaka mata tsawa da zabga mata lafiyayyen maruka, tuni tadafe kunci tana hawaye, bakinta kuma yayi gum, danta gane rijiya bawajen wasan makaho baneba. kad'an daga aikin masu bak'ar fuskarnan su suburbud'a mata alburushi atsakkiya kwalwarta yanzunan.
Hankalinta baigama tashiba gaba d'aya, ta tabbata inhar ya khaleel nawajen zai kubtar da ita, tunda baita6a kamata dawata 6arnaba, koma hajia babba tasaka ya fiddota aii.


Nidai nace hummm.


********
Ya khaleel Na tsaka da aiki su Taheer suka dawo, ko d'agowama baiyi ya kalli taheer ba, yadai amsa gaisuwar da Taheer d'in kemasa tareda jinjina masa kai.
"Sir! Munsami yarinyarnanfa, amma abun mamaki da d'aure kai kubrah ce fa".
Babu shiri ya khaleel yad'ago kansa, yace, " kubrah kuma? Wace kubrah?. "
"Kubrah dai daka sani, mai zuwa gidanku, Dan haryanzun bansan dangar takar zumincinkuba".
Azabure ya khaleel yamik'e, lokaci d'aya kansa ya sara masa, yay saurin dafe kansa, yama rasa wane tunani zaiyi. Miyasa zuciyarsa ke alak'anta mutanan nan da matarsane?. ranar dinner d'insuce tafad'o masa arai, tabbas aranar hankalin Aysha da meerah yatashi saboda ganin kubrah dawasu mata biyu, idanma bai mantaba meerah barin wajen tayi baki d'aya, kuma Aysha batada wata aminiya sama da meerah. Sannan washe garin ranar lokacin su Sameer sunje musu sallama kubrah da wata mata sunshigo yima Aysha sallama, harya basu damar shiga inda take a bedroom, kuma yashiga d'akin kiranta saboda tazo suyi sallama dasu Nawaff, saiya taddasu cirko-cirko, tabbas akwai alamar tambaya akan matarsa.
To amma idan yace haka kuma, miye alak'ar Momy da kubrah, sannan hajia khaltum kuma?.
''Ya salam!! yafad'a da k'arfi yana dafe kai".
Da sauri Taheer yamatso kusadashi, "j! Miyake faruwane haka?".
Kansa ya girgizama Taheer, cikin k'unar zuciya yace, " Taheer ina zargin wasu abubuwa biyu, kuma akan mutum biyu, amma bana fatan hakan ta kasance, domin duksun shafi katanguna, ya ALLAH!".
kamashi yayi ya zaunar, yaringa kwantar masa da hankali, saida yaga yad'an nutsu sannan ya idamasa bayanin yafice.
Gaba d'aya yau ya khaleel yakasa ta6ukama kansa komai, tunani yafaracin k'arfinsa, yanaso yakira gida yaji yajikin Momy da Aysha amma haushinsu yahanashi, kuma yayi alk'awarin inhar suka kasance cikin abinda yake zarginsu wlhy billahi bazai d'aga musu k'afaba, saiya hukuntasu, kuma da hannunsa zai kamasu.
Wannan alk'awarine, bazai ta6a barin mai laifi a k'ark'ashin inuwarsaba.
Idonsa yayi jajur saboda 6acinrai, zuwa can maganar yarannan tadawo masa arai itama, lokacin dayake tambayarsu waye ya turosu, (sunce matar babansa hajia Bilkeesu) kai jama'a miyasa zuciyarsa take karkata dukkan zarginsa akan wad'anda ya yadda dasu? Mafiya kusancu agareshi kuma?, zai sakama dukkan wani dake gidansu ido kawai, Dan yanzu ba Aysha kad'aice abin zarginsaba, harda Momy da Anty Mamie.>?%?


____________________
Yauma dai haka Aysha tayini duk babu dad'i, komai taci kamar jira saita amayar dashi, zogalene kawai dataci ya zauna, haka 'yan Kano suka tafi suna tausaya mata.
Bak'in 6angaren Momy ma duksun wuce, inna jummai Ce kawai tarage.
Misalin 10 Na safe baffah yashiga duba hajia babba, bayan sun gaisa da inna jummai yashiga d'akin.
Duk 'ya'yanta suna zagaye da ita, har mufeedah dake raku6e gefe d'aya.
Ganin baffah suka fara yunk'urin fita amma saiya dakatar dasu, kujerar madubi husnah tabashi yazauna, Momy Na kwance dukta kuma janga6ewa saboda dagaske batada lafiyar, k'arfin haline kawai, da k'yarma tasha tea da magungunanta takwanta yanzu.
Sannu yamata cikin tausayawa, da tambayar k'arfin jikinta, tace, k'irjintane kemata ciwo yanzun, amma tasanarma doctor dasukazo yanzun shida sultan, yace zai kawo mata magani.
"To shikenan ALLAH yak'ara afuwa, sannan kuma ki kwantar da hankalinki, Dan kinsandai kinada hawanjini. Idankuma hankalinki ba'a kwanceba ciwon bazai barkiba".
Kanta ta jinjina masa, wasu siraran hawaye suka zirara a idonta na dama, suka gangara har cikin kunnenta, Anty shukurah ce ta goge mata.
Baffah ya maida kallonsa ga mufeeda, "k kuma kishirya kayanki, 6angaren Ammah zaki koma harki haihu, rashin ganinki zai sassautama mahaifiyarki rad'ad'in datakeji".
Mufeedah kuka tafashe dashi, Dan tasan inhar takoma 6angaren Ammah bata Isa zubar da cikinnanba, tasan jarabar Ammah da k'unatar tsiya.
Cikin daka tsawa yace, " kobak'ya jinane?".
Azabure tace, "to baffah".
Yayi tsaki yana maida kallonsa ga Momy dake yunk'urin tashi zaune, Anty zuwairah da Shukurah suka taimaka mata tatashi.
Muryarnan ta Momy duktayi low, tace, " Alhaji kana ganin ita Ammah baza'a takurataba?, nida canayi tabi inna Jigawa kawai, idan ta haihu saita dawo, koya kagani?".
"Eto kema kinzo da shawara mai k'yau, amma abani nanda kwana uku nagani".
Murmushin samun nasara Momy tayi, tacigaba dafad'in " to ALLAH ya kaimu, sannan sai kayanta, yakamata akwasosu aii".
"A'a baza'a kwasosuba, Dan zamu maida auren kan Nafisa d'iyar k'anen Bilkisu Hameesu, tunda ta isa aure, dadai tasleem ko maleeka zan bashi, tokuma duk sunada manema ashe, Dan haka baza'a kwaso kayanba, mungama magana da innah za'a d'aura auren k'arshen satinnan, shukurah keda Amatullah kuje Ku d'akko kayan sawar Mufeeda kawai, sannan karku d'akko akwatinan lefen, kubarshi can, sadakintama za'a maidashi Na Nafisane".
Tunda baffah yafara magana Momy take zabura, haryakai k'arshe, " Alhaji ban gane wannan zancen nakaba?, daga INA kuma wannan annamimancin yafito?, asaki 'yata agida, bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login