Showing 102001 words to 105000 words out of 155647 words

Chapter 35 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

471

komai, babu abinda sukace sai ALLAH ya k'yauta.
Babu Wanda yay tunanin tafiya gida yahuta acikinsu, Dan isowarsu kenan daga islands uk, sunsami nasarar kamo glory da yaranta su Lola, amma john basu sameshiba.

Kusan awanni biyu likitocin suka d'auka aciki, sannan ne suka fito kowanne yana yarce gumi, ya khaleel ya taresu da tambayoyi.
"Cool down mana j! Zomuje office zanmaka bayani". 'Cewar Dr Faisal'.
Yajuya yakalli sauran doctors d'in, inason a ajiye security a k'ofar d'akinnan yanzunnan Doctor Ahmad".
"OK sir".

Ya khaleel yajuya yana kallonsu Taheer, wannan aikinmu ne bana doctors ba.
Atare suka jinjina masa kai.
Tsurewa Momy tayi, dandanan tafara k'yak'yk'yafta idanu.
Saurin bin bayan khaleel tayi office d'in doctor Faisal.
Amma tana shiga doctor Faisal yanemi alfarmar tafita, da khaleel kawai yakeson ganawa, sai baffah.
Kamar hajia babba tashak'e doctor Faisal haka taji, tafice tana dalla masa harara, aranta tana fad'in zanyi maganinka ne aii.
Tana fita doctor Faisal yakira baffah awaya.
Baffah yashigo yazauna akujerar dake kusada ta ya khaleel.

Kusan mintuna 3 doctor Faisal Na 'yan rubuce-rubucensa, saida yagama yad'ago yana kallonsu baffah, ''maganar gaskiya Alhaji akwai wani 6oyayyen Al'amari dake faruwa, ajiya duk na duba mutanen gidanka babu wanda yaci guba, munkuma bincika meatpia d'in da Ibraheem yabamu, shima babu komai acikinsa, to amma ita matar khaleel tabbas inhar taci wani Abu ko yayane to shine aka sakama gubar, shinema yafara aiki ajikinta jiya, Dan tabbas ta had'iya, kodai abisa kuskurene kokuma bayan zubar da meatpia d'in bakinta bata wanke bakinba ta had'iya yawu, dan gubar tanada k'arfi sosai, cikin mintuna 20 kacal take fara aiki ajikin mutum, Alhmdllh kunyi azamar kawota asibiti jiya, muka samu nasarar ceto rayuwarta, saboda gubar batada tasirin dazata hallakata, dama cikin jikintane abin damuwa, amma Alhmdllh yanacikin k'oshin lafiya".
"Abinda kuma yafaru yau, tabbas akwai Wanda yashiga d'akin datake kwance yabata wata gubar.......".
Zabura ya khaleel yayi daga zaune, jikinsa har rawa yakeyi yace, "nurse d'inku biyu sunshiga d'akin, kuma ina zargin ta k'arshe, dan alamun rashin gaskiya sun bayyana tartare da ita, harna tsaidata amma tacemin zataje kirankane A'eesha ta farka".
"Ni!, no nurse d'aya natura d'akin da take kwance, kuma bana zarginta, sister Ruk'ayya ce, kuma tasanarmin taje tadubata tana barci har lokacin, bayan ita ban tura kowaba, babu kuma wata nurse datazo wajena saikai Daka kiramu,
Amma ina zuwa, waya ya d'auka yakira wani doctor, yana d'auka yace, "doctor Hambali inason a tattara dukkan nurses d'in asibitinnan".
" no dukansu, harda masu aikin safe dasukazo yanzun".
Yana ajiye wayar ya khaleel yace wannan ba aikinku baneba, namune.
Waya ya d'akko shima yakira Joseph, "hello Joseph, kunemi Dr Hambali inason a atattara min dukkan doctors da nurses dake cikin Hospital d'inan, harda ma'aikata cleaners".
"OK sir".

Baffah dai yayi shiru Danshi gaba d'aya ma tunaninsa ya kulle.
Ya khaleel Na ajiye wayar yace, "yanzu ya jikin matata doctor?".
"Alhmdlh, mun sami nasara, yanzu hakama barci takeyi, amma cikin jikintane dai kamar.........
" kamarme? Doctor karkacemin dai ya salwanta please...... "
Yanda yay maganar sai tausayinsa yakamasu, doctor ya girgiza masa kai, ''bahaka nake nufiba j, ka kwantar da hankalinka, cikin yana nan lfy, saidai muyita addu'a ALLAH yasa gubar karta shafi wani sashe Na lafiyar yaron/ko yarinyar kawai".
Huci mai azabar zafi ya khaleel yafuzar daga bakinsa, yarintse idanu da k'arfi yana dukan tebir d'in gaban doctor.
.
Please j ka kwantar da hankalinka, bawai inada tabbacin za'a haifi babien da dawata nakasabane, kawai hasashene".
"Haba doctor yazakace haka? Karkayi k'ok'arin yimini yawo da hanakali akan abinda kakeda tabbas akansa, wlhy ko wanene wannan mai aika-aikar saiyayi nadamar shiga gonata........
Ganin yanda ya birkice sai baffah yajawoshi jikinsa, rungumesa yayi, jinsa ajikin mahaifinsa sai kawai yasaki kuka mai tsanani.
Bubbuga bayansa baffah yashigayi, shikansa jiyake tamkar yay kukan saboda tausayin d'an nasa, amma saiya dake, yashiga k'arfafashi.
" haba Mu'azzam kaifa namijine, kuma ma'aikaci mai kare rayukan al'umma, mizaisa ka karaya hakane?, karka bari abinda yafaru da matarka ya raunanaka, kamata yayi yak'ara maka karfin guywa, kowaye ya aikata wannan abun tabbas sanadin tonuwar asirinsane, kuma hakan yana nuna yadad'e yana cutar damu, yanzune ALLAH ya nuna mana hakan, banaso ka zargi mahaifiyarka, dan batada dalilin kasheku, sannan mutane dayawa sunci meatpia d'in, amma baimusu komaiba, wandama mamanka tabaku an bincikashi babu komai acikinsa, amma miyasa aka samu gubar ajikin Aysha?, kuma shine last Abu dataci ajiya?........"
Zumbur ya khaleel yatashi daga jikin baffah, danya tuna masa abinda yamanta, kuma yakamata kowa yayi nazarin hakan awannan ga6ar, shikansa?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? shaidane Aysha bataci komaiba jiya, daga rake sai wannan meatpia d'in, amma miyasa babu gubar acikinsa?, wannan lamari da d'aure kai gaskiya.
Wayarsa yazaro, kiran wasu doctors yayi cikin ma'aikatansu, yasanar musu yana buk'ar ganinsu a General hospital yanzunan.
Cikin girmamawa duk suka amsa, bai kuma sauraren bayanin doctor faisalba yatashi yafice.
Daga doctor har baffah da kallo kawai suka bishi.....
Harya kama handle d'in k'ofar zai fita doctor yace, "j!".
Cak ya khaleel yatsaya amma bai juyoba, Dan allurar 'yan mazan tamotso.
Doctor Faisal bai damuba yace, " please bamuson kowa yasan matarka nacikin k'oshin lfy, anunama kowa tana cikin halin k'ila wakala, inaga hakanne zai dakatar da masu harinta, kuma zai bamu damar aikinmu atsanake".
Jinjina kansa kawai yayi batareda yace uffanba yafice.
Baffah ya sauke ajiyar zuciya yana kallon doctor, "doctor ngd sosai, amma Dan ALLAH ak'ara bama yarinyar nan kulawa sosai".
"Insha ALLAH alhaji, Na yanzunma kuskurene, bakuma zamu bari yasake faruwaba, kuma babu Wanda zai sake shiga d'akin datake kwance, dagani sai kai da Ibraheem".
" masha ALLAH, hakan yayi".
Baffah yabashi hannu sukayi musabaha yafito...........
'




*_wasu sun zata yau asiri zai Tonu kai tsaye ko?, ai idan hakan tafaru labari yasamu rauni kenan, kuma kanku saikunji babu dad'i, amma Ku k'ara hak'uri kam, Dan dolenen komai yafito fili awannan ga6ar, tunda Aysha tabasu bakin zaren, yanzunkam fad'an Na manyane>?#?>?#?._*




*_masu had'a fitina tsakanin writers kuji tsoron ALLAH wlhy, karku d'auka hakan kamar k'aramin abune, kuji tsoron addu'ar Wanda aka zalinta, shin miye ribarku wajen cewa wasu na amfani da fasahar wasu?, wlhy idan kin had'a kinci riba yau, aranar gobe kiyama zakiyi Dana Sani, Dan ALLAH baya barin hak'in wani akan wani, kudaiji tsoron ALLAH, akwai mutuwa, akwai hisabi, duk Wanda yake k'irk'irar irin wad'annan fituntunun ya ALLAH kayi gaggawar tarwatsa al'amarinsa, kahanashi barci mai dad'i, kasaka bak'inciki da k'unci a zuciyarsa, ALLAH kamana maganin munafukain fili dana 6oye dake la6ewa abayan writers suna kunna musu wuta ameen._*=?-?=?O?





*_ALLAH ka gafarma mahaifina, da dukkan sauran musulmai baki d'aya.=?-?=?O?

*_Typing=???_*


>?0? *_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_


*_Bilyn Abdul ce>??

*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu=???)_

*_Na gaisheki k'yauta Anty Ruk'ayya maikan doya>?-?=? ?, saura kicigaba da gulmata nahanaki page>?+?>?#?=??_*


3? 8?

Yana fita a can baya wani d'aki da doctors kanyi meeting yanufa bisa jagorancin Taheer, dukkan nurse's d'in da doctors anhad'asu awajen, shigarsu babu dad'ewa doctor Faisal ma yashigo.
"Amma zaka ganeta j!?".
"Zan iya ganeta insha ALLAH, saidai inbata nan".
" d'aya bayan d'aya nurse ke tasowa mazansu da matansu, ya khaleel Na kallonsu, amma harsuka k'are babu komai kama da ita, sai wadda tashiga Na farko kawai, danhaka aka tsaidata ita.
Bayan kammala dubawa babu ita aciki ya khaleel yamaida hankalinsa kan d'ayar nurse d'in, yayi masifar had'e fuska.
yace, "k wace nurse ce tashiga bayanke? Nasan kin santa?".
" wlhy yalla6ai ban Santaba, danni inagama dubata nafita kuma duk kuna tsaye, saida nasanarma doctor cewa barci takeyi, amma wlhy bansan wacece takoma d'akinba bayan fitata".
Ran ya khaleel bak'aramin 6ace yakeba, ya maida hankalinsa akan doctor Faisal. "Doctor tabbas kowacce wadda ta aikata tana cikin ma'aikatan asibitinnan, dan haka nikoma wacece nabada awa 50 kacal anemomin ita".
Yajuya yafice daga d'akin.
Kowa da kallo yabishi, tabbas kowa yasan yau ma'aikatan asibitinnan sunshiga tarkon khaleel saidai ALLAH.
Dayake su Anty Mamie ma duksun ganta, dole saidaisu aka cigaba da duba har masu shara da goge-goge, tunda abune Na laifi, cikinsuma za'a iya samu.
Khaleel kam yama bar asibitin shida doctors d'insu nawajen aiki, su doctor Abraham, amma saida yakuma saka tsaro mai tsauri azagayen d'akin da Aysha ke kwance sannan suka tafi.
Gidansu sukaje, su Ammah duk suna harabar gidan, shirin tafiya asibitin sukeyi saiga motarsu khaleel, dakatawa sukayi harya fito.
Suduka babu wanda bai tsorata da yanayin khaleel ba, har Ammah, Dan sunsan idan yana cikin irin wannan Fushin komaima zai iya faruwa, sannan komin kusancinka dashi bazai d'aga maka k'afaba, kuskure k'ad'an wani zaimasa yaci dukan banza.
Babu Wanda ya isheshi kallo acikinsu yaja zugarsa suka wuce 6angarensa.
Afili Ammah tace, " lallai gidannan gab yake da kamawa da wuta, tabbas inaji ajikina akwai gagarumin Abu dazai faru".
Kowa kallonsa ya maida kanta, amma batasake furta komaiba, kujera tanema ta zauna.
Suma duk sai suka nemi wajen zaman.

Su khaleel suna shiga yace, bincike mai k'yau nakeso, Dan tabbas akwai abinda bamu saniba, ajiya A'eesha bataci wani abuba agidannan, kowa ya shaida haka, amma dai ina zuwa.
Waya yaciro yakira Ammah, babu dad'ewa saigata tazo.
Suna zazzaune, itama saita nemi waje ta zauna. khaleel yace, "Ammah kamar yanda bincike ya nuna a 6angarenki Aysha take kwana, kuma kinfi kowa Sanin dukkan wani motsi akanta, shin jiya ko taci wani abinci kafin meatpia?".
Ganin yanda khaleel keyin magana ya tabbatarma Ammah ba fagen wasa ko sanayya akeba, yana fagen aikinsane, danhaka itama taci Serious.
" tabbas yalla6ai a 6angarena Aysha take, kuma saboda juna biyu datake dashi bakomaine takeciba, wanima idan taci amai takeyi, ajiya bataci wani abuba, idanma ban mantaba da rake ta karya, kuma har kaje kataho da ita bataci wani abuba a 6angarena, ban saniba ko zuwanku anan d'in taci".
"Anan ma bataci komaiba, koda mukazoma barci tayi, sai around 1 tatashi, meat pia ne kawai nasan ankawo taci, shima gutsura d'aya kacal tamasa, bama ta had'iyaba, ta furzar dashi. Kamar yanda doctor Faisal yace k'arfin gubar yana fara aikine cikin mintuna 20 kacal ajikin Wanda yaci, daga barinmu nan zuwa 6angarenki zaikai minti ashirin kafin A'eesha ta suma. Abinda Yakuma d'aure kammu shine, babu wata guba ajikin meatpia d'in Dana kwashe atsakar d'akinnan, Wanda A'eesha tazubar, kuma acikinsane taci. Wannan shine yarud'ar damu, akan son Sanin mi A'eesha taci?".
Dr Abraham yace, " sir, inabuk'ar ganin raken datasha".
Da hannu khaleel ya nunu masa ledar rake da fleet dasuke a falon, Wanda suna nan Inda suka barsu tun a jiya.
''Yauwa, kozamu iya ganin inda aka 6arar da meatpia d'in?".
Nanma Kansa ya jinjina musu, yamik'e suka bishi baya, harda Ammah.
'Dakimsa da abin yafaru sukaje.
Tangaran d'in d'aya fashe yana nan, Dan khaleel meatpia d'in kawai yatsince yabar fasashshen kwanon.
Wata Na'ura suka saka, wasu Na haskawa, Dr Abraham kuma nasaka wani d'an tsinke, kusan mintuna 7 Dr Abraham yace kozamu sami ruwa?".
Ammah Ce tafita da Sauri, babu dad'ewa saigata tadawo da ruwa.
K'ar6a Dr Abraham yayi ya yayyafa awajen daduk suke zaton meatpia d'in yazuba, sannan yasaka wani Abu kamar sirinji yazuk'e ruwan, aka tattara fasashen kwaonon aka zuba a Leda, d'an lallek'awa sukayi kozasuga koda wani guntun meatpia ne ad'akin, amma basu ganiba kuwa, sai can wani acikinsu yatsinto wani d'an mitsit a akusada wardrobe, shima da Alama dije bata Ganshi baneba, dukda dai k'ank'antarsa takai akasa ganinsa musamman idan mutum ba'a cikin nutsuwa yakeba.
'Daukarsa sukayi suka saka awata Leda aka d'aure.. Yo bandama dai binciken tsiya irinna ma'aikaci mizasuyi da wannan 6allin abun, saikacefa yaro mai k'yuya yabaka Abu da k'yar=??, gaba d'ayafa baifi Girman wannan gyad'arba=?I??T?).
Amma haka suka d'auka Dan zai iya Zame musu wani madubin dubawa.
Daga Nan fitowa sukayi, raken fleet Dana ledama Duk suka d'auka aka tafi dashi.
Asibiti suka koma, suma su Ammah asibitin suka tafi.
Sai lokacin Ammah taji cewar ankuma zuwa har Inda Aysha take kwance anbata gubane.
Kutt Amman iya bala'i kuma, aikam tashiga zazzaga masifa asibitinnan, catake ALLAH ka tona asirin kowanne tsinanne ke keson kashemin jikata, ALLAH katona asirin matsiyaci.
Bak'aramar sukan zuciyar Momy adu'ar ammah keyiba, jin Adu'arnan take tamkar tana k'onata da garwashin wutane, Dana tun d'azun arikice take, tarasa hanyar dazata bar asibitin, Dan tafa kula kwa6arsu zatayi ruwa, sotake taje su tattauna plan F, kafin agano yanda Aysha taci guba dakuma wadda aka bata, dije takirata tasanar mata su khaleel sunje gida dawasu doctors kuma taga bincikene Na bin kwakwkwafin tsiya sukeyi, ALLAH ma yasota sanda dije takira wayar tata tasami k'arfin dakewa kamar babu komai ta amsa mata, bama zaka ta6a zargin dawani take wayaba, saboda iyafis dake kunnenta, sauraren dije kawai tayi, amma batace uffanba.


*********
Su doctor Abraham sun kar6i dukkan bayanan hannun su doctor Faisal, suka tattara suka koma setetion d'insu, harda ita Ayshan, wadda aka d'auka kashir6an tamkar mara rai, babu Wanda baimata kukaba a 'yan gidan kuwa, duk da basusan barcine takeba, dansu anfad'a musu har yanzu tana cikin damuwa.
Khaleel yace, "baffa yakamata duk Ku koma gida, yanzun mundawo da case d'in hannunmu, sannan kukula sosai, Dan yanzun koma wanene zai iya d'aukar kowanne irin mataki".
Jinjina kai baffah yayi yana murmishi, yadafa kafad'ar khaleel yana fad'in " haka nakeso kadawo jaruminka, banason karikice kazama mai rauni, dan sun cutar da itane dama dansu raunana zuciyarka, ka karaya gaba d'aya, nikuma sonake hakan yazama allurar k'arin k'aimi suka maka yarona, ALLAH yabada nasara, ya kareminku baki d'aya, kaje, karkayi sanya, ka tabbatar kakama azzalumai Ibraheem!!! ".
Karo Na farko dakowa yaji wannan sunan abakin baffah, kuma yanda yay maganar saida kowa ya tsorata, Dan cikin daka tsawa furicin k'arshe yafita daga bakin baffan.
Kowama awajen da addu'ar samun nasara yabisu, dakuma tasamun lafiya ga Aysha, Momy ma ta daure tayi, amma dukkan mai hankali ya kalleta yasan bata cikin nutsuwa, su Taheer kuma duksun lura da haka, amma basuce komaiba, Dan basu ta6a kawo zarginsu akan Momy ba, tunda sunsan mahaifiyar Khaleel Ce.
Amma Samuel yad'auki alk'awarin bin kwakwkwafin Momy, Dan tund'azun duk wani motsinta akan idonsane, haka kawai yaji zuciyarsa bata amince da itaba, yana kuma kallon sanda take waya, dukda batayi maganaba wasu alamomi sun nunata.
Koda suka tafi shidasu khaleel shi dawowa baya yayi.
Cikin dabara yaytabin moticin gidansu khaleel abaya, wani guri nesa dagidan yasamu ya zauna, ya tabbatar inhar Momy batada gaskiya saita fito daga gidan.

__ __
=?A? =?A?
=?C? =?D?
Nima ina nan sainaga fitowar hajia babba=? ?>?#?=??.


__________________
Yinin yau zumbur su khaleel basu hutaba, dukkan wata kulawa ta musamman kuma Aysha tana samunta, lokaci-lokaci ya khaleel kanje d'akin datake kwance Wanda keda fasifar tsaro ya dubata.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login