Showing 18001 words to 21000 words out of 155647 words

Chapter 7 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

450

_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_



*_Bilyn Abdull ce>??


*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
>?2?


*_part 2_*
(littafi na biyu=???)

*_wannan page nawani duk masoyin ciki da gaskiya ne aduk inda kuke, ngd sosai da k'yauna, ALLAH yabar zuminci, inayinku irin million's d'innan wlhy._*
=?
?=?
?=?
?=?
?d'd'd'd'=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?


8?

Alhamdulillahi shirin biki ya kankama, anatama Inda zasu zauna fenti, can baya kusadasu ya Sultan, tunda aka saka ranar auren baffah yasakashi za6en yanda yakeso agina masa nasa wajen, yakuwa za6a.
Tun sannan aketa ginin, hargashi ankammala cikin nasara.
Kaf gidan kowa yanata shiryama wannan biki, dukda uban tafiya yace babu wani shagali daza ayi, acewarsa da kud'in daza 6arnatar wajen wani dinner, lunch, mother day.....etc, gamma ataimakama marasa k'arfi dashi.
Baffa yaji dad'in hakan sosai, kuma yasaka masa albarka.
Hajia babba kam ko a jikinta, da ayi dakar ayi duk uwar ubansu d'aya, yarantama basa wani nuna murnar Auren, saboda anhad'a yayansu da Aysha, amma sunata burin sai lokacin bikinsa da Aleeya, sukad'ai sukasan misuka shirya.

Nidai nace uhhhhmmm.=??


______________________
Aysha kishirya gobe idan ALLAH yakaimu zaku wuce Kano keda gwagggonki.
Lah mama da gaske?.
Eh mana, can zaki koma, nasanarma baffanku ma, nima insha ALLAH ranar laraba zantaho gaba d'aya, kokinje Kano karkiyarda wani yabaki wani abin cushe-cushe ko wani ganyen magani kisha, banason shaye-shayen maganin matannan wlhy, Dan abubuwane masu illah, mutanene kawai suka Gaza gane haka, kingadai anan mamien ku tabaki tsaftatatttu itada Ammah, tunda nonon rak'umine Dana shanu sai kayan marmari dasu aya Zuma kanimfari mazarkwaila dafanfar gyad'a dadai sauransu, wad'annan basa cutarwa tunda damacan ALLAH ya halatta mana shansu koda badan wannan manufarba, shiyyasama nahanaki shan nawajen bintu gaskiya.
Nasan Yaya bazata bakiba itama, tunda bataso, kannena kawai nakeji da asma'u sai matar Ahmad, amma Na gargad'i Hafsat da fadeelah, tunda suma sunsan bamumusu wannan shashancin ba.
Damu zauna 6ata lokaci wajan baku wannan shirmen da 6ata kud'inmu gamma mu nutsu wajen koya muku zaman auren da biyayya, maganin mata baya hana d'a namiji ya wulak'antaki idan yaso, idanda matanmu nada hankali dasun gane hakan, (wlhy naga matarda tahad'a kayan mata ta kwankwad'arma cikinta da yamma da daddare mijin yaji dad'insa, washe gari da safe sa6ani yashiga tsakaninsu ya sheshshek'ama fuskarta marika), shin Dan ALLAH maganin mata yayi riba kenan?, alokacinfa dasuke tareda sune kawai sukejin dad'in har miji yamiki wani sambatun banza, dazarar buk'atarsa tabiya shikenan anwuce wajen, wannan bazai hana yaci ubankiba, bazai hanashi cin zarafinkiba, bazai hanshi ya sakekiba, bazai hanashi yimiki kishiyaba, shin mata nawane suke amfani da kayan d'a'a amma basu fita daga cin kashin d'a namijiba, ga cututtuka dakiketa tanadama kanki wanda bazasu bayyana agarekiba sai lokacin da tsufa yazo miki, shin Dan ALLAH miye abin birgewa duk inda kika zauna kika tashi aganshi jik'e da ruwa, wannan wace iriyar masiface?, mutanan da maganin mata sukesha?, bama su sanshiba, amma suna zaune lafiya da mazajensu, wani aurenma sai anyi mace zata San mijinta, miji yasan matarsa, amma saikiga aurensu ana kiran shekararsa 80-70-60, kuma suna zaune lfy, ko sa6ani zakiga baya yawan shiga tsakaninsu.
tsakaninku da ALLAH awannan zamanin aure nawane kekai shekara 10 kacal babu tashin hankali da masifu acikinsa, awannan zamanin inhar mace sukai zaman lfy Na kwana uku da mijinta acikin sati, to wlhy kwana hud'u cikin fad'ane, mafi yawancin abinda ke faruwa kenan, kuma koda yaushe kud'inki nagidan dillaliyar kayan mata, bakiciba, bakiba y'ay'anki sunciba, bakiba iyayenki sun sakamiki albarkaba, baki taimakawa marasashiba, saikije kisha abinda zai ruguza rayuwarki batareda kinsan hakanba, kedai kawai mijinki yaji dad'i, yaringa zunduma ihu lokacin dayake taredake, indan anhad'u gidan suna ko biki kiringa bama sauran mata labarin sambatun dayake miki da ihu, mata suna dariya ana cafkewa da miki jinjina kinci gari.
Haba mata, wannan wace iriyar asarace haka, sirrin aurenkine agidan biki? Kaiconmu wlhy, ALLAH kuma ya tsinema duk ma'auratan dake fallasa sirrin aurensu, wlhy mugyara, keba karuwaba amma rayuwar aurenki tafi ta karuwai fita fili, wa'iyazubillah, Dan ALLAH mu kiyaye mata.
Aysha karki yarda koda da kuskure hakan takasance dake, kada naji kada nagani.
Kuka sosai Aysha keyi, tana jinjinama mama kai, kidaina kuka dan bama ayi komaiba, abinda yasa nabarki saboda kina kusadanine, akoda yaushe zan ringa nuna miki kuskuren abinda ke hana rayuwar aurenmu k'arko awannan zamanin.
Tashikije ki kimtsa komanki, Dan duk za'a maidasu 6angarenku kafin natafi.
To mama, ngd, tafita tana cigaba da kuka.
Mama tabita da kallon tausayi, tana tausayama d'iyar tata da dududu bata wuce shekaru 18 ba, gata da k'aramin jiki, bandama karatun kasashen waje ba irin namu baneba da saifama yanzu ayshar zata kammala Secondary nata, amma gata ayanzu hartana bautar k'asa (NYSC) d'inta


____________________
Yauwa Amatullah, kune y'an zamani, dama zuwanki nake jira, bud'e d'akincan Na bak'i muje kiduba kayancan idan sunyi, idan kuma akwai abinda za'a k'ara ko za'a sake kinga zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu saimu shiga kasuwa, Dan yakamata akaisu ranar alhamis ko.
To Anty Mamie kayan miye haka?.
Mujedai kigani mana.

Woow Anty mamie! Kayan auren ya khaleel ne?.
Sune Ama...
Masha ALLAH, akwati shidda, wlhy sunyi k'yau akwatinan, zama sukayi bakin gado, anty Ama.... tamasu fillah-fillah, kai wlhy komai yayi Anty, komai dama ayishi dai-dai misali yafi, amma nuna fariyarnan bata birgeni nidai.
Aii Ama...ita rayuwa basai ka nuna kaid'in maishi baneba, koda kanada kud'inda zakayi abinda fiyeda nak'asa dakai yayi, karkace saikayi Wanda ya ninninka nasa, wannan shike saka Wanda k'arfinsa bai kaiba burin yin kamar nakan, wannan fariyarce tasaka zaman y'anmata da zawarawa yawa, kowa burinta sai anyi mata abinda akama k'awarta lokacin aurenta, hakama iyayenmu burinsu Aueen y'ay'ansu yafi nakowa, Idan ankawo lefen auran d'iyar makwafta sudinga hura hanci aina d'iyansu yafi, sukansu samarin burinsu suyi bajinta tamkar ta auren wane, shiyyasa saikiga fitintinu sunyi yawa acikin bikin auren, da rayuwar auren kanta bayan anyishi, zakiga ma'aurata burinsu ayi events kala-kala Na k'awa da birgiyewa awajen shagalin aurensu, ad'akko mawak'a masu zamani da tashe su wak'esu, alik'a y'an dubu-dubu bugun Abuja ana takasu, amarya da Ango su d'au k'yalk'yali cikin kayan kece raini Na alfarma, wuyan amarya da hannunta kaga ruwan gwal k'irar Dubai nata k'yal-k'yal, k'awayen amarya da abokan ango da dangi ank'ure wanka cikin kayan birgewa, ga camera man agefe yanata k'yastu, washe gari dukwata kafar media tad'auka anyi auren wance da wane, abinda ke 6atamin raima wai kayan lefen aurenki dazarar ankawo zakifara ganin ana yawo da hotunansu a social media, y'an group ga kayan auren>?#?.
Sukuma saisu d'auki shewa, kai amma wance kingama morewa, ALLAH dai ya maidamu danshinki, kai wacece addu'a gareki haka, muma abamu Dan ALLAH=??=??=??, kujifa wawanci.
Kekam anfasa miki kai, kinacan dad'i kamar yakasheki kayan aurenki sun birge mutane=??.
Sai ank'are biki kaf ango yayta sace kayan da d'aid'aya yana maidawa shagon daya aro>?#?.
Inkuwa siya yayi dagaske ma da sauk'i, amma dasun k'are kikace wane kayana sun tsufa zaice duk kayan Dana saka miki alefe kice sun kare, kinsan wahalar danaci natarasune? K'ilama y'an uwankine suka kwashe anga banza, to banidashi nikam=??.
Wlhy tundaga k'aryar biki ake fara samo matsaloli a aure, please mukula Dan ALLAH.
Hakane wlhy Mamie, ALLAH dai yasa mudace, amma yanzu wannan baffah ne yasa ahad'a ko ya khaleel.
A'a Ama... Gudunmawa tace, babana yamin magana akan lefen, amma nace masa yad'an saurareni, shima baffan naku dayay maganar haka Na sanar masa.
Yanzu saiki nemo su Amal Ku kwasa kukai wa Ammah kawai tunda komai yayi.
Kai amma kinsha kud'i Anty Mamie, ALLAH yak'ara bud'i Na alkairi, lallai ya khaleel d'an gatan Anty Mamie.
Fita Anty Mamie tayi tana murmushi batace komaiba.

.............................................
Ohni Halima, yanzunan duk bilkisunce ta had'a wad'annan kaya haka? Ya ALLAH ka albarkaci wannan yarinya da zuri'arta, ALLAH yakareta daga dukkan wani sharri itada zuri'arta.
Su Amal sunata amsawa da ameen cikin jin dad'i.
Bayan baffah yadawo Ammah tasaka aka kaimasa kayan, dakanta taje tamasa bayani, shima yaji dad'i sosai, sai albarka yake sakama matar tasa.
Yace amma gawata shawara.
To inajinka.
Mu 6oye kayannan, akuma gargad'i yarannan suyi shiru dabakinsu, inason naga lefen da laura tace zata had'o itakuma, hartake masifa kar wanda yamata shishshigi.
Ah wannan shawara taka tayi d'annan, aii babu matsala, amaidasu 6angarena to.


*_Washe gari._*

Hajia babba zaune da bataliyarta, dansu Anty zuwairah ma duk an iso, harda y'ay'anta, hakama Anty shukurah, akwatunane guda 3 agabansu, said'an kit karami, daga ganin akwatunan kasan irin wad'anda sukayi muguwar dad'ewar nance ashago ba'a samu masu siye da wuriba, Dan harsun fara tsufa.
Shukurah tayi tagumi tareda zubawa momynsu ido da y'an uwanta, ganin yanda suketa d'aga kayan suna shewa da dariyar mugunta, gaba d'aya kayan ciki babu ko fasali, duk irin atanfofinnane leda aka zuba, saiwani shegen leshi da kalarsa kamar kagudu Dan muni kala uku, sai shadda d'aya dadai sauransu, ko'a k'auye baza'a had'a wad'annan kayanba.
Komaidai babu tsari da mutunci aciki.
Hajia babba ta ta6e baki, yo dakuke dariya badan gidannan banebama zata samu kamar wad'annan d'inne? Kuhad'asu akaima babanku da kakarku su gani.

Shukurah batace komaiba, amma saida tayi kuka dan bak'in ciki.

_____________,,,
Baffah yagama ganin kaya tsaf yace ALLAH ya sanya alkairi, hakama Ammah abinda tace kenan.
Su Anty Mamie ma duk sun gani, umme amarya data kasa shiru saida tace amma alhaji ba kayannan za aikaba dai?.
To basu uwarsa tahad'aba Saudah?, suza'akai kuwa.
A'a Dan ALLAH alhaji, wlhy bai daceba, gsky acanja shawara, nidai gatamu gufunmawar nida yaran d'akina, ayi hak'uridai babu yawa, 1.5million ne.
Aii sune masu yawan saudah, ALLAH yasaka da alkairi kinji, amma tashiga saka mata albarka itada baffah, hakama Anty Mamie tanata godiya.
Baffah yakira ya khaleel dake tsaka da aiki a office.
Bayan sun gaisa yace dasafe naga baka shigo baneba lfy dai ko?.
Wlhy lfy lau baffah, muna dawowa sallar asuhi nafita saboda akwai aikin danakeson kammalawa, yau da daddare jirgina zaitashi zuwa saudia kuma inagama sai ana jibi d'aurin aure zan dawo, shiyyasa nake had'a ayyukan dasukad'an cushemin.
OK, tom zaka shigo gida dai ko?.
Eh insha ALLAH, yanzuma Dana gama wannan aikin zan taho.
To saikazo.



Bayan la'asar yashigo gidan, saida yashiga ya gaisa da dakowa, sanan yaje wajen baffah, bayan sund'an tattauna akan bikin yanuna masa kayan auren, Na Anty Mamie Dana momynsa.
Baidaice komaiba gameda kayan Momy amma fuskarta tanuna alamun 6acin rai, yakumayi godiya sosai akan Na Anty Mamie da umme amarya.
Baffah ma baice dashi komai akan kayan momynba.




4days ago.
Bayan tafiyar mama da kwana d'aya aka kai lefen Aysha Kano.
Anmusu tarba ta mutunci da girmamawa, a 6angaren haiya babba Anty shukurah Ce kawai taje, saida sukaje Kano taga bakayan da Momy tahad'a baneba, tayi farinciki sosai Dan dama Abin nata damunta azuciya.
Sunso ganin Aysha amma tak'i yarda, Dan bamata gidan, suna gidan Anty zainaba d'iyar kawu bilya itadasu Sadiya sauran amaren.

Aranar suka juyo da shatara ta arzik'i, kowa yanata yaba lefen Na Aysha, suma sauran duk ankawo nasu Dama.


Abinda kecin zuciyar Aysha baiwuce ya khaleel ba, musamman intaga yanda sauran y'an uwanta keta shirye-shirye da angunansu, amma ita banda ita, indama tad'anji sauk'i d'ayane Taheer yakirata akan zaizo kanon gobe danyaji abinda suke buk'ata Na y'anmata shidasu Joseph.
Wannan ne yad'an rage damuwar tata
kad'an.............
'










=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?d'd'd'd'd'=?
?=?
?=?
?=?
?
[9/7, 1:21 PM] Aysha Galadima: *_Typing=???_*



>?0? *_CIKI DA GASKIYA........_*
_{=?*?wuk'a bata hudashi=???}_



*_Bilyn Abdull ce>??


*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
>?2?


*_part 2_*
(littafi na biyu=???)

9?

Washe gari da yamma saiga Taheer da Joseph, dukda babu angon nata taji dad'i sosai, batada wasu k'awaye dasuka wuce y'an uwanta, sai maleeka da Tasleem, komai a hannunta suka damk'a, dukda tasanar dasu babu wani Abu dasuka shirya.
Kafin tafiyar nasune ya khaleel yakira wayar Taheer, bayan sun gaisa da maganganinsu yasanarmasa suna Kano.
"Kano kuma? Mikukajeyi a kano?".
Taheer yace, "Munje wajan amarya mana, kaibaka cemana komaiba gameda shirin biki, shiyyasa mukaga yadace muje".
"Uhmm OK, to yanzu yakukayi?".
"No babu komai, Gatama muna atare".
"Bata wayar".
Aysha dake magana da Joseph Taheer yamik'ama waya, ta amsa batareda sanin dawa zatayi maganarba Dan sanda aka kira Taheer matsawa yayi daga wajensu.
Asanyaye tace, " Assalamu alaikum".
"Wa'alaikissalam!, muryarsa tadaki dodon kunnenta, maganarsa takatse tunaninta"...
"Kinajina? Banason wani shirmen day day d'inan, karnaji ance kunhad'a wani events na banza da wofi, dan bana buk'ata, nabama Amatullah sak'o tabaki, tundasu ranar Friday zasu zo nan kano, ni saima ranar zan dawo dasafe".
Muryar Aysha a sanyaye tace, " ALLAH yatsare hanya".
"Ameen ya amsa" yana yanke wayar.

Su Taheer sukamata sallama suka tafi.


_________________________,_
Ranar Alhamis aka sakasu Aysha a lalle, bawani taro akayiba, irin al'adar Malam bahaushe tada akamusu, matar yayansu Qaseem ta feshesu da turare da fauda, aka rangad'a gud'a akansu, shikenan.
Sukad'an cigaba da sabgoginsu Na a are da k'awayensu.
Aranar su Ameerah suka sauka daga Canada, Aysha tayi murna sosai tamkar anyi mata bishara, baby Raudat tayi girma sosai, yarinyar abin sha'awa wlhy, ifteehal tashige cikin k'awayen amarya anata abubuwan arzik'i, meerah kam tanataredasu Hafsat fadeeala dasu amal.
Washe gari su Anty Ama... Suka iso suma, harda Anty Mamie da Ammah, su inna ma y'an Jigawa sun iso.
Gidafa yayi dank'am dajama'a, abin ba'a cewa komai.

Ranar juma'a aka d'and'asama amare k'unshi, gaskiya sunsha k'yau abin har ba'a cewa komai, sunje wankin kai da yamma, sanda suka dawo gidan ko'ina bak'ine, anata aikin gyaran kayan miya dadai sauransu.
Aysha tafad'a jikin Anty Mamie tana murnar ganinsu.
"Eyee kaga d'iyata amaryar kamshi, k'unshin yayi k'yau sosai wlhy, waye yamukune?".
"Anty Mamie wata k'awar Anty Nasara ce".
"Wacece Anty Nasara?".
"Matar ya Qaseem.
Kai gaskiya ta'iya sosai, kunsha k'yau kuduka".
"A'a amaryar Yaya babu magana?"..
"Hannu Aysha tasa tarufe fuskarta, kai Anty Ama....ALLAH ban gankiba, dama kinzo?".
"Wai Aysha babumu abikin babban Yaya aii gayya ta 6aci, kintaho da kwana biyu Na iso, randa muka kawo kaya kuma kika 6uya mana, ya hidima?".
Y'ar dariya Aysha tayi kawai batace komaiba.

Nan dai abokan wasa suka cigaba da tsokanarsu.


_____________________________
10:23am jirginsa ya sauka Nigeria, su Adams sukaje suka d'akkosa, yana bayan mota zaune, sai amsa calls na jama'a yakeyi, musamman abokansa dasukasan da dawowar tasa.
Bayan ya cire wayar akunnensa Adams yace, "aii Oga bak'ifa suncika tab wlhy, bakaga jama'aba, abin ba'a cewa komai, saidai ALLAH ya kaimu gobe a d'aura aurennan lafiya kawai".
"To ameen Adams, yanzuma youseef ke sanarmin su Sameer sunkusa sauka suma, yazata bamubar airport d'inba mutsaya mutafi dasu, nacemasa mun baro".
"Ai wlhy oga tunjiya babu abinda mukeyi sai kwaso jama'a kawai, a ciki da wajen Nigeria, aii mutum mai jama'a yamore arayuwa".
Murmushi kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login