Showing 15001 words to 18000 words out of 155647 words

Chapter 6 - Ciki Da Gaskiya Book 2 Hausa Novel Complete

06 Jan 2025

452

7?

Tunda suka tafi babu maima wani magana, duk tsoro yacika Aysha, tunani takeyi ina zai kaita.
Yamik'a mata hijjab Fari tas, sai k'amshi yakeyi.
Kar6a tayi tana dubawa, yadin yamata k'yau sosai, batace dashi komaiba tazame gyalenta tasaka, tana k'unk'uni k'asa-kasa akan INA zai kaitane?, batayi zaton yajitaba.
Saidaki zanyi bak'auya kawai, muryar ya khaleel taji batareda tayi zatoba.
ALLAH yabaka hak'uri, tayi maganar a sanyaye, Dan ita wlhy tsoronsa k'aruwa yake aranta, tunda taga yajibgi guys d'innan, dakuma Marin daya mata.
Bai tanka mataba.
Gani tayi sun shiga cikin makarantar A.B.U. zariya, mamaki takeyi mizasuyi anan kuma?.
Guri yasamu agefe yayi parking, d'alibai nata hada-hada, dukda yaud'in ba ranar karatu baceba.
Harya fita Aysha bata motsaba, yalek'o yana hararta, kosaina fiddokine?.
Jiki a sanyaye tabud'e motar tafito, nanfa idon d'alibai Yakoma kansu, y'an mata anga had'ad'd'en gaye duksun rikece, su kallonma ayshar sukeyi amatsayin k'anwarsa, k'ilan yazo nema mata addimetion a school d'inne.
Cikin takunnan nasa Na jarumta yake tafiya, dolene duk mace mai lfy ta k'yasa.=? ?.lol.
Dukda cikin nutsuwarsa datazama tamkar halittarsa yake tafiya hakan baihana ya zarta Aysha ba, ita tanama had'awa da y'an sassarfa atata tafiyar.
K'ofar wani office sukaje da aka rubuta professor Al-hassan ibn Mahmud, Knocking yayi aka bashi izinin shiga.
Dattijone maicikeda kwarjinin kamalar addini, zasuyi sa'anni da baffah.
Cikeda fara'a yake fad'in lale marhababinka Ibraheem bin Abdallah.
Ya khaleel yak'arasa suka rungume juna kamar yanda larabawa keyi, sanan ya durk'usa har k'asa ya gaidashi, ganin haka itama Aysha tadurk'usa ta gaidashi cikin girmamawa.
Cikeda fara'a ya amsa yana fad'in masha ALLAH sannunku dazuwa d'iyata, bismillah kuzauna kuzauna.
Ya khaleel da Aysha suka zauna a kujerun dake gaban babban tebir nasa, Aysha tayi k'asa da kanta saboda kunya.
Mamaki yayi mugun kama Aysha lokacin dataji ya khaleel yajuya harshe suna larabci shida dattijon, dole tad'ago manyan idanunta masu yalwar gashi ta kallesa, suka had'a ido Dan lokacin yajuyo yana gabatar da ita wajen dattijon amatsayin matarsa dazai aura.
Janye idanunsa yayi yamaida kan sheaik Al-hassan.
Masha ALLAH Ibraheem khaleel, masha ALLAH, cikin harshen larabcin yayma Aysha barka dazuwa akaro nabiyu.
A mugun mamakin ya khaleel d'in shima saiyaji Aysha ta amsa da larabcin, daganan tacigaba da amsa tanbayoyin sheaik Al-hasan da larabcin.
Shagala yayi yana kallon bakinta dake sarrafa larabcin cikin kwarewa danuna tabbas ta ilimantu a 6angaren addini, bak'aramin birgeshi tayiba, Dan baiyi zaton hakaba tunda baffah yasanar masa daga k'asar waje tadawo karatu.
Sheaik Al-hassan ibn Mahmud malamin ya khaleel ne, ahannunsa yay karatun addini a Abuja, aikine yadawo dashi A,b,u zariya.
Sundad'e basu had'uba saboda yanauin aikin ya khaleel d'in, shiyyasa dayazo d'aurin aurennan yaga yadace yazo ya gaidashi, shine daya kirashi yasanar masa yasameshi acikin makaranta.
Yakawo Aysharne Dan malaminsa yaganta tunda baida tabbacin zasu sake had'uwa dukda yanada burin malamin NASA yay Iuctures alokacin aurennasa.
Sheaik Al-hasan yaji dad'in wannan ziyara sosai, yayimasu nasiha akan aure da muhimmancin auren kansa, da girmama juna, yanda zasuyi zamantakewar dazasu amfanar dajunansu batareda samun sa6aniba ko k'osawa da junaba, sund'an dad'e sosai a makarantar Dan har saida baffah yakirasa, yasanarma baffah Inda sukaje.
Baffah yace shikenan mukam zamu wuce saikun taho, ka gaidamin da Malam sosai, kace insha ALLAH nima inan zanzo wajensa zuwa Na musaman.
Zaiji baffah, saimun taho, to kutahodai dawuri, karkuyi dare kajiko, Kasan hanya babu k'yau.
Insha ALLAH yanzu ZAMU taho baffah.
Bayan sun Yanke wayar ya isar da sak'on baffah wajen Malam, yaji dad'i sosai kuma ya amsa.
Littatafan addini masu muhimmanci akan rayuwar aure dawasu fannonin yahad'ama kowannensu, sai godiya suke masa.
Ya khaleel ya ajiye masa alkairi mai tsoka sannan sukafito.
Har k'ofar mota Malam yamusi rakiya, saida yaga fitarsu sanan yakoma office yanamai jin dad'in ziyarar, Dan har ransa yana k'aunar khaleel d'in, yarone mai kwazon gaske alokacin daya koyar dashi, ga gaskiya da suffar kamala Na mutanen kwarai batareda yaron, yaga kuma haryanzu halayyar Na taredashi.

________________
Tunda suka d'auki hanya babu Wanda yace uffan, har sunshiga cikin kaduna.
Shi yanata tuk'insa dajin wa'azin sheaik Jafar Mahmud Adam, itama Aysha wa'azin take saurare, yayinda wani 6angaren zuciyarta yatafi wajen tunanin ya khaleel d'in, komai nasa na burgeta, tako ina ya khaleel cikakken mutumne, saidai abinda ba'a rasaba, Dan d'an adama Tara yake bai cika gomaba, babu yanda za'ayi kace wane yakai 100%, dolene saika samu wani d'an taumashe koyaya ataredashi.

Awajenwa kika iya larabci haka?.
Maganarsa ta sauka a kunnenta.
Batareda ta kalleshiba tace a islamiyyar abbanmu, shima yana koya mana.
Alkur'ani fa?.
Nayi sauka, ina izufi 37 a hadda.
Yanzunkam saida yajuyo ya kalleta, banason k'aryafa.
ALLAH ka tanbayi mama.
Kansa ya jinjina, yacigaba da jeho mata tambayoyi akan sauran littatafan addini, sosai take bashi amsa daki-daki, saidai abinda ba'a rasaba, Wanda tasamu rauni akansa saboda rashin tunatarwa, tunda ba islamiyyar take zuwaba yanzun, jiyayi k'aunar iyayenta da kimarsu tak'aru azuciyarsa, dama haka yake burin samun matarsa mai ilimin addini, dukda har yanzu baita6ajin son yarinyar aransaba.
Daganan baikuma cewa komaiba.

Sunkusa fita Kaduna yatsaya wani wajen saida snacks agefen hanya, baicema Aysha komaiba yafita tareda saka mata luck.
Baidad'eba sosai saigashi yafito da leda guda biyu a hannunsa.
Yabud'e motar yashigo yana fad'in Alhmdllh.
Kamar yanda yanuna ya manta da ita a motar haka itama ta shareshi har suka fice daga cikin Kd.
meatpie dake nad'e cikin tessu yafaraci tareda fad'in bismillah.
Aysha tasaci kallonsa ta gefen ido sannan tace a'a ngd.
d'an juyowa yayi ya kalleta sannan yamaida hankalinsa ga tuk'insa, baisake cewa uffanba har suka shiga tsakkiyar dajin tsakanin Abuja da Kaduna.
Wayarsa tayi wringing, saida ta tsinke aka sake kira sannan yad'aga.
Ango kasha k'amshi, har yamzu baku shirya dawowa wajen aiki baneba kaida youseef? Kunbarmu aiki yamana yawa nida taheer wlhy.
Joseph yayi dariya, karka damu my guy, end of this week zanshigo Abuja tareda madam.
OK saikun isoto, agaidasu papa da joy.
Zasujika da k'au, ina amaryarmu?.
Waye amaryarku?.
Hhhh madan Aysha mana.
Aini bamma Santana, kaga sai munyi waya ina kan titine, yay maganar yana yanke wayar batareda ya saurari mi Joseph zai fad'aba.
Abin yak'ule Aysha. Dan taji dukkan wayar tasu, amma tana mamakin dama yana wasa da mutane haka?.
Sun isa jere aka fara kiran sallar magriba, tacikin jere yabi saboda gudun go slow d'in dazai samu idan yabi ta babbar hanya, musamman awajen dei-dei d'innan.
Ganin lokacin sallah zai kwace masa yatsaya a bwari wani masallaci zaibi jam'i.
Harya taka zai fita wayar Aysha tayi wringing, dakatawa yayi yafasa fitar, atare suka kai hannu kan wayar, shiyayi nasarar d'auka yayinda Aysha tayi saurin janye hannunta saboda d'orawa datayi akan nasa.
Ya d'auke wayar daga cinyarta yaduba, Anty meerah yagani a screen d'in, saiya mik'a mata yafita.
Baki ta murgad'awa bayansa sannan tad'aga wayar, harta tsinke ansake kira.
Anty meerah Na I missing you wlhy, kin manta dani kusan 1week bamuyi wayabafa.
Sorry lil sholyna, babynki ce batada lfy, amma tasamu sauk'i.
Wayyo my Raudat shiyyasa nayita mafarkinta, yajikinta?.
Kwantar da hankalinki da sauk'ifa, hak'orane.
To duk kuna lfy? Ya Canada?.
Gatanan k'alau, saidai muna kewarki wlhy, tunda muka dawo kullum sai munyi hirarki agidanan.
Wlhy nima ina kewarku Anty meerah, wani lokacin jinake kamar nayi tsuntsuwa nazo gareku, karki damu, aimun kusa zuwa tunda ga bikinnan nata zuwa ko.
Uhhm, ni Anty meerah kibari kawai, ALLAH yanzun banason aurennan, ya khaleel lamarinsa tsoro yake bani, saboda halin ko inkula dayake nunamin, yanda kikasan ba aurensa zanyibafa.
Karki damu daduk wata shariyarsa, kowane namiji danasa salon, wani bazai ta6a nuna miki color d'insaba saikunyi aure, wasu kuma sununa miki soyayya awaje, idan kunyi aure kiga bahaka baneba.
Shikenan Anty meerah.
Yauwa sweet lil d'ina, yanzu ya'ake cikine?.
Humm abubuwa kam sunata faruwa, kuma Alhmdllh ina k'ara samun bayanai akan su hajia babba, kinsanma wani Abu?.
A'a saikin fad'a.
Hhhhh wlhy mufeedah nakama shekaranjiya around 1:30am Na dare zata fita, batasan nagantaba, nafito d'aukar ruwa nasha, har tsakar gida nabita, naga tanatama d'an gwari maigadi jaraba, yabud'e mata gate kuwa tafita, rok'onsa nayi akan yabarni naga inda zataje.
Kinsan minagani kuwa? Tana fita tacire hijjab d'in jikinta, wlhy daga ita sai bra da pant, saiwata shegiyar riga wadda da'ita da babu duk d'aya.
Motar wani guy tashiga, inanan zan kafa mata wani tarko, ALLAH sanadin haka sai hawan jini yakama uwarta.....
Hango ya khaleel natahowa yasaka Aysha fad'in kibari nakoma gida zamuyi waya, tayanke da sauri.
Motar yashigo suka cigaba da tafiya.



*_2month's ago_*

Kwanaki nata shurawa, bikinsu ya khaleel yamatso gab.
Aysha tanashan gyara wajen Ammah da Anty Mamie, harma da gwaggo bintu ( nace wannan bazai hana ya khaleel dakakiba=?? gwaggo bintu=??).
Ga Anty Mamie tatsaya akanta wajen koyamata girke-girke dazama da miji, abinda ya khaleel keso da Wanda bayaso danta kiyaye kuma taci ribar zama dashi.
Tayi k'yau harta gaji, Ammah ma Na koya mata dabarun zama da miji irinna zamaninsu, sosai Aysha take fahimtar komai daki-daki.


A6angaren hajia babba kam batawani d'auki bikin da muhimmanciba, ko kayan lefe da Shukurah tace zataje Dubai tahad'o hajia babba cewatayi uban Dubai d'in, y'ar talakawar za'a had'ama kaya asu tsada?.
Bazai yuwuba.
Kai Momy, itamafa tazama d'iyarki, yakamatafa kugane khaleel shikad'aine namiji acikinmu, yakamata kuma a auransa mu nuna masa gata, kodan d'awainiyar dayakeyi damu, hakama Anty zuwairah nace nawa zamu had'a masa gudunmawa tace ko sisi bazata badaba, Momy kimata magana Dan ALLAH.
yo maganar ubanmi zan mata, wlhy ina bayanta gara tasiyama y'ay'anta kayan sakawa, idan zaiyi auren gaskiya saita masa, Dan wannan auren rusashshene, kwanakin Dana bashi nacika zan wargazashi.
Inzaki Adana kud'inkima sai aurensa da Aleeya ki Adana, inkuma zaki bashi kekika Sani, dama aii kema salla mammiyarce tamkar shi, karkuma kisake kirana akan bikinnan, dama zakiyi zamanki wajen y'ay'anki yafi miki alkairi basai kinsaka mijinki kashe kud'in jirgi abanzaba, ato kindaiji nafad'a miki.
Hummm amma Momy.......
Ya isheni haka Dan ubanki.
Shiru Anty shukurah tayi, tace shikenan Momy sai anjima, insha ALLAH ana saura sati 1 zantaho.
Kekika Sani kuma.

Ya khaleel dake tsaye abakin k'ofa yanajin wayartasu yajuya dabaya, Dan baya buk'atar momyn tasan yashigoma, wajen aiki zaije shine yashigo gaidata, maybi da yama zaije Gabon, amma dasafe yake sakaran dawowa.
Ko amma bai gaidaba yafice, saboda wayar Momy ta Sosa ransa, su Kansu su Adams sunlura ransa a6ace yake, yarasa miyasa Momy take masa hakane?, yakanji alabarin mutane idan mutum yanada y'ay'a maza dayawa, ya haifi mace 1 tak acikinsu takan samu gata fiye da kowa, hakama idan ya haifi mata da yawa, namiji yazama shikad'ai yakan samu gata fiyeda sauran y'ay'an, amma shi agaresa ba haka baneba, Momy tafi nuna soyayyarta kan y'an uwansa mata, mawuyacine suyi rayuwar sati d'aya Momy batayi abinda zai Sosa zuciyarsaba agidannan, Anty Mamie daba ita ta haifeshiba, nononta kawai yasha, amma yafi samun kulawa da kwanciyar hankali agareta.
Yanzu kokan aurenan itace ta zaunar dashi tamasa nasiha da Nuna masa muhimmancin biyayya ga iyaye, da alkairin datake hango masa a auren, kullum tsaye take Kansu wajen kwantar da hankalinsa itada Amman akan auren, amma ga Momy bahaka baneba.
Wanan wace iriyar rayuwace, shidai basain dad'in uwaba wlhy, gata da ranta amma maraya yafishi jindad'i......
Adams yak'ara magana akaro Na hud'u, sir! Munzofa.
Firgigita yabud'e idonsa, tareda yin k'aramin tsaki, Natafi wata duniyarne Adams, bara naje wajen Oga nafito, kafin nafito kasanarma su fharuk ina nemansu a office d'ina.
OK sir!
Adams yafad'a yana masa salute.

Yad'an dad'e a office d'in ogan nasa, suna tattaunawa akan abinda zai kaishi Gabon, dakuma mutuwar David Wanda khaleel d'in ya tabbatar da anbasa gubane aruwa yasha, kuma anhad'a kaine dawani makusancinsa, tunda bakowane ke shiga inda David yakeba, ya khaleel yace sir!.
Inazargin wasunmu Na taredasu David, Dan a shekaran jiya nafara tatsar wasu bayanai agaresa, Yakuma tabbatarmin zai fad'amin jami'an tsaron dake basu taimako akan harkokinsu, shine jiya muka wayi gari an kashesa, nasaka anrufemin masu tsaron k'ofar, har sai sun sanarmin Wanda yayi aika-aikar, dansunsanshi, amma sunk'i fad'a saboda wani dalilinsu nadaban.
Ha...ha..hakane, yakamata mu tsananta bincike akan kisan nashi, dan.... Dan babu wani bare dazai shigo yayi wanan aika-aikar.
Wani murmushin kasaita ya khaleel yayi, cikin izzarsa yace karka damu sir, y'ar manuniya zata nuna, kuma wlhy kosu wanene saisunyi Dana sanin 6atamin aiki, sannan mutuwar David bashine zaisa su ku6ta daga farautata ba, saima hanya dasuka nuna mini, alk'awarine saina gurfanar dasu bisa guywoyinsu agabana!!.
Y'ar zabura Oga yayi, Dan maganar khaleel d'in tashigeshi.
Batareda sauraren komaiba ya khaleel yay salute nashi yafice daga office.
Ajiyar zuciya Oga yayi (babu zancen fad'in matsayinsa, saboda tsaro=??=?M? Miye mafita yanzu??....



A office d'insa yatarar dasu Solomon, atare sukayi salutes nashi, yazauna akujera yana binsu da kallo.
Mahmud ya'ake cikine?.
Yes sir, mun kammala komai, kamar yanda kabuk'ata mun tankad'e da rairaye wad'anda sukeda kusanci sosai da barau modibbo, so aranarma da kukaso kamashi akwai wata number da'aka masa massege da ita, cewar gakunan zuwa garesa.
Inaga wananne yakawo matsala harya farga yagudu bayan yaga messenge d'in.
OK wanene mai number?.
Macece gaskiya, yasaka mata hajjaju kawai.
OK. Yanzu mutane nawane kuka tace acikinsu?.
Faruk yace su 37 ne sir.
OK.
Yakamata abisu d'aya bayan d'aya amin bincike akan sana'oinsu, da address nasu, har ita macen da tamasa massage d'in.
OK sir.
Solomon yace amma sir kana ganin lokaci baiyiba dazaku kama barau modibbo?.
Hakane Solomon, zamu kamashi, amma inason kama Alhaji Aliyu bushasha ne first, danshine ogansa nalura, kokuma nace babban dila d'insa, to kafin kuma nakamashi dolene mucigaba da bibiyar barau modibbo dansamun wasu bayanan sirri daga garesa batareda shima yasaniba.
Muna kamashi barau modibbo yanzu, Alhaji Aliyu zai gudu wlhy, kumashi mutumne mai wayon tsiya, baya hud'd'a da wayar tafi da gidanka, saidai yaransa..
Lallai yanada wayo, cewar kausar.
Sun tattauna sosai gameda wasu ayyukan sannan ya sallameshi suka tafi.

Shikuma yacigaba da 'yan ayyukansa, yana son kammala komai akan lokaci, saboda nanda 2weeks binkin taheer, tsakaninsu sati uku ne acal.
Ga aiki yamusu yawa, ad'an tsakaninnan, hankalinsa yarabu biyu. Ga shirin bikinsa shi kansa, damma k'annensa suna tsaye akan komai da baffansa.
Shi satin bikinma yana Saudia, sai ana 3days d'aurin aure zai dawo Nigeria.



Akwana atashi, babu wuya wajen ALLAH, biki saura kwanaki 10 kacal..............
'











=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?=?
?=؋?=؋?=؋?=؋?d'd'd'd'd'
[9/6, 8:54 PM] Ay??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????sha Galadima: *_Typing=???_*



>?0? *_CIKI DA GASKIYA........_*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login