Showing 1 words to 3000 words out of 108220 words

Chapter 1 - Tantiriya A Gidan Yari Book 3 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

664

[2/13, 7:56 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI

BOOK 3
~TAIMAKO~

1-5

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA GARE KI
AIDA MAMAN TASNIM


PAGE NAKI NE
MRS CHIEF


*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*



Washe gari Khadija wato Mero komawa tayi ta cikin dakin da take kokarin lallai sai ta fasa shi,tana zuwa taji sheshekar kukansa ta bangaren dakin da yake,yau taji wani a kusa da shi tayi mamaki Jin ana bashi hakuri,Yana cewa itace wacce zan aura shike nan ta rasu ta barni,Ido Mero ta zaro tare da dafe kirji da hannu biyu tace dama Yana da wacce zai aura ma ashe,ta rasu Kuma to Allah yaji kanta idan tamu tazo Allah yasa mu cika da Imani" shine yake wannan kukan kamar wani mace sabo da soyayya,shi yasa in ba dole ba me za ayi da me kudi Abu kadan Kuka ba juriyar wahala,talaka kuwa ba ruwansa ya Saba da kaddara iri iri,kasa hakuri tayi da karfi tace to a gobarar ta Kone?Wanda suke cikin dakinsa sun zaci Aljana ce tsoro ya kama su Dan su iya tsayin rayuwarsu basu taba Jin maganar wani ta bayan dakin wani ba bare mace ma.

Matashin magana yayi yace ae gobarar har da ita ta Kone,Mero tace sai ka daga Murya banji baaaaa.......tsaki ya ja da gajiyawa yace da karfi da ita gobarar ta Kone,Mero tace Allah yaji kanta tayi Mutuwar shahada,su dai mazan tashi suka yi suka fice basu yarda da mutum yake magana ba.
Khadija taci gaba da magana ka gama kukan ne? banza ya mata,kyale shi tayi taci gaba bula katangarta yau dai taci nasara ta bula Inda ya tsage yatsu biyu zasu iya shiga,idonta Daya ta manna a jiki ta leka taga dakin gashi nan dai wai a haka VIP ne,tace wani abin sai gidan yari.

Maman Wahida tana gidan yari yanzu Kam ta Saba ta zama Yar gari harkar gabanta take yi,iyalanta suna yawan zuwa dubata bata da matsala a vip take zaune,masu hali basa fadawa matsala,bata shiga harkar kowa indai ba a vip kake ba to tasan baka da gata ko kulaka baza tayi ba.
Mero bata San Maman su Wahida kanwar Mima bace tana dai ganinta kamar su daya da Mummy sai ta dinga mamaki, yau dai gaza hakuri tayi ta nufi wajenta da take zaune tana hutawa abinta.
Mero tana zuwa tayi Sallama sanye take cikin riga da skirt na wani tsohon Leshi Wanda suma Azima me kwana ba wando ce ta bata su Ganinta cikin tsumma,Mero tace Ina yini,Maman Wahida da kyar ta dago ta Kalli Mero Khadija Shekeke tace ya aka yi? Dan ma kin samu na gaishe ki ,na saki ki gaishe ni? Khadija tace na kwace gaisuwa ta ba Ina yini ba,dama kama kike da wata Mummyn Spark,da sauri ta Kalli Mero tace a Ina kika sansu kanwata ce uwar mu Daya uban mu daya,Khadija tace da Mima,da Rafeeq,Misam duk ba wanda ban sani ba a cikinsu,Sai lokacin tace zauna,Khadija tace uhm da kika ji nasan Yan uwanki to ni ba me kudi bace shara da wanke wanke nayi a gidan Mummyn Spark,Kuma rannan Spark yazo wajena.

Maman Wahida tace Spark din yazo wajenki? Mero tace ai shi bashi da matsala shi yake bani kudi da komai,amma ni Ina a matsayin kamar uwarsa ya kasa zuwa mu gaisa,Mero tace laifi kika Masa watakil ai ku halinku sai addua kwana Nan Yar uwarki zata zo ku hadu ku zauna kuyi ta zumunci,Mummyn Spark kwana nan zaki ganta a gidan nan,Maman Wahida tace ubanwa ta kashe ke karki jawo mana masifa a dangi,Azima ce ta fito tana rangwada tace Khadija yau baza kije sakar bane? zanje mana muje to,Khadija ta mike tabi Azima suka wuce Mero tace ke Azima karatun Nan da kyar nake ganewa kin San ni dakikiya ce gwara ma na addini Ashe haka ake wankan tsarki,na dade Ina haukata ban sani ba,ai sai jiya na koya,Azima ta dinga dariya tace gaskiya Jahila ce Khadija,Mero tace ta karshe ma, Gani da suna me dadi me asali amma ban gaji me Sunan ba gaskiya iyayena sun cutar Dani yanzu a gidan yari nake wayewa Kai duniya,ni Kuma a gidan yari nake Ilimi Ina wani zama Yar birni,Azima tace gashi Nan kin koma Yar birni na gyaraki tsaf,rashin kunyar ne har yau baki fara gogewa ba Dan Allah kiyi ki koya ki karasa cika sharudanki na gidan yari,ni kin ganni idan na fita a gidan yari duk Wanda ya aureni ya aurarwa kansa tsiya shi yasa bama na so na fita ni karshe ace nayi aure Kuma ni ba Wanda ya isa ya sani ko ya hanani.

Mero tace uhm Azima ke kam ai baza ki fita bama sai kaddara tunda laifinki ba sharri a cikin,Azima tace thank God nayi nadama ni wlh na Saba da zaman gidan nan ko gida na koma ma bazan ji dadi ba,Mero tace gashi mun hadu wai Azima kin San su Chika da Beauty,Azima tayi dariya tace daina tuna min su,ke gidan da kike aiki baki yi dace ba wlh wasu Yan aikin suna dace acan suke samun Ilimi amma suka barki a Jahilarki Khadija,Mero tace su ai Yan boko ne da karatun Boko suke aiki na addinin suna da shi dai dai gwargwado amma sun manta ma kudi da duniya yasa sun manta ma da wani Ilimin addini bare su koyawa wani,sannan duk talaka baida daraja a wajen su ta ya zasu koya Maka Abu suka San ma me kake ciki bare wacce nake gidanta a cikinsu itace ma tafi kowa lalacewa.

Azima tace itace Danta yake auren Naila Inye lallai Naila tayi prison mijinta yayi prison ga uwarsa zata yi prison su uku rigis duk prison sai kace gado,Dariya suka yi Mero tace gashi nima daga zuwa aiki gidan na fado Ina tsoron Naila karta haifo Dan Birsina,karasawa suka yi Inda ake koya musu sakar,Azima ta wuce bangaren nata ta kayan Sanyi ita kuwa Mero bangaren mificin sarakuna irin na fadar sarki masu kyau da tsada su ta iya,tayi mugun iya saka su tunda tazo ta koya,gashi in sun saka baza a basu kyauta ba sai dai ka siya in kana da kudi,Mero sai da ta siyi biyu wai sai ta yi kyauta.

Bangaren su Malam Jilani suna zaune Dan Indo ya shugo idonsa jajir yace kai akaramakallas gaba dayan ku Jiya Mafarkin Jamilu nayi ya dawo gidan nan,Malam Garzali ya tuntsire da dariya yace wai Dan Allah baza ka manta da Jamilu ba,tayi aure ance tuni,Dan Indo ya jawo tarkacen kayan Naila data bari ya kalle su,ya daga wani katon bujen wandon ta ya furta Allah sarki duniya yanzu wannan Jamilu ta saka shi,Malam Jilani Yana boye dariyarsa yace Matar wani ce dai yanzu,haramun kake aikatawa,Dan Indo yace Allah ya tsinewa yaron nan Spark,zuwansa ba alheri bane ya cuceni,yanda nake Son Jamilu na tabbata baya sonta haka,duk sanda na sake ganinsa a gidan yari ko ziyara yazo sai ya yabawa Aya zakinta,Malam Jilani suna ta dariya,Dan Indo ya sake Jin Haushin su yace ai kune manyan munafukai dama karya kuke Kun San macece shi yasa kuka riketa a dakinku,Kuna fakewa da karatu Yan iskan banza Yan iskan wofi,Malam Sharu yace mu mene namu a ciki yaro dai Jamilu da hannunka kayi Masa hanya ya bar gidan Nan sabo da haka laifinka ne,mu karatun mu muke da addua,ai ba karatun Allah kuke ba ya ja tsaki ya fice.

Schola ne ya tare Dan Indo yace ya akayi ne Dan Maza? Dan Indo yace jiya mafarki nayi Jamilu ya dawo gidan nan,Schola yace wai Jamilu Terror? yace ae,dariya Schola ya dinga yi yace tab sai akace Maka gaskiya ne sannu waliyyi to Kai da Jamilu har Abada tana can tana ta Shan madarar Nido yanzu haka ma an samu Rabo ka samawa kanka lafiya ka hakura,Kaga ni na tafi wajen kawata Khadija nasan anjima kadan zata bayyana a Jikin katanga mu Sha hira Ina dalili ka likewa mace daya,Jamilu ai ya zama old version,ga new Version latest Khadija Ina laifi kana Jin Muryar mace ma a'a mu munyi can" ya wuce yana rangwada.

Wata Majalisar ce guda suke kafata a wajen sabo da Mero tana zuwa ta Jikin wajen suna Jin Muryar mace,Mero da Azima suka zo ta wajen Mero ta kwala da karfi Salamu Alaykum harda rige rigen amsawa,Goje yace Kai Muryar mace duniya ce wannan yarinya Allah ya mata albarka tana kwantar min da zuciya tana sani nishadi,rabon da naji Muryar mace tun Jamilu Tantiriya tana nan,Mero tace Kai Yan Maza har naji warin ku na gardawa ta nan,irin na ubanki cewar wani me Suna Balarebe,Mero tace Ubana Yana can Babata ta takura Masa shine ka zage shi ai abin yayi Masa yawa Allah ya isa,Ina ma zaki iya shugowa gidan nan bangaren mu,Mero tana dariya tace uban me zan muku in na shugo,Schola yace madarar Nido za a Baki iri iri harda me bulkodi ahayye ni dai Allah ya tsare ni neman Yar uwata mace,Mero da Azima suna ta dariya,Azima tace wayyo gashi bana kwana da wando,Goje yace ku jefa ni ciki Dan Allah,I love you a jefa ni ciki,Hanif ne yazo wucewa ta wajen yaji suna ta ihu da dariya,da izzarsa ya dan tsaya yaji Muryar Khadija ta daki dodon kunnensa tana cewa a gidanmu ga shimfidita ga Kaza taka kyankyasar 'ya'yanta a kauye,ni fa a birni na koyi tsafta a gidanmu sai mu gama wanke wanke mu wanke kafar mu da soson wanken Kwanon,su Goje suna ta dariya sabo da Fadi ba atambayeka ba din da Mero ke yi kullum sai ta fada musu abinda suke yi a gidansu na kauye.

Balarabe yace tab Allah yasa bakwa abincin siyarwa,Mero tace cab ai kuwa wallahi muna yi awara da Koko,tsohon dankwalina babata ta dauka da shi take tace gasarar Koko da awara,har skert dinta na ciki mun taba amfani da shi,Schola yace wayyo kunya ku matsa na boye kaina ni Schola Ina zan sa kaina Yar uwa tana ta bankada,Goje yace to ke Khadija baki da kanne ne? Me kace bana ji sai kayi da karfi,da karfi yace Baki da kanne? Mero tace daga ni sai kanina Yana kauye wani Dan banza shashasha nake ganinsa yanzu Kuma a haka sai kaji watarana wata har kasa bacci zata yi a kansa Allah ya kiyaye wacce taso kanina Muneer tayi asara,Azima tace ke muje dalla lokacin makaranta Kinga ke kike koyon Addini muje ko Kya samu ki daina wannan iskancin zancen naki,Dan Allah karku tafi cewar Muler muna Jin dadin mu kamar mu rungume ku,Mero tace wayyo Dan ma Baku ganni ba,Goje yace Allah? tace Allah da kunji a cike muke kamar ana bamu kaji,Goje har da dafe Kai yace Kuma fa da gaske ne Yana magana da sauran mazan,Hanif kallon su yayi kawai wani takaici ma ya kamashi mene abin dadi a nan,yace gaskiya ku Baku San ma mene abin dadi ba,Goje yace Kai ai sabon zuwa ne baka wani Dade ba shi yasa kake fadar haka da ragowar turirin mata a jikinka ka shugo bai gama barin jikinka ba shi yasa,ka kyale mu Muji dadin mu,Hanif yace Goodluck,Yana kudu Dan uwarka Yana Niger Delter, Goodluck ma ya sauka daga mulki karewa cewar Schola Yana ta faman cakaki,yace tun yaushe nake binka Ina naci Ina sonka ka zama budurwa ta kaki yarda wai Kai me tsafta shine yanzu zaka zo ka takura mana, Kai kudin naka ma ba kyauta kake ba, tunda kazo gidan Nan sai girman Kai sisinka ba Wanda ya taba ci,Hanif yace Allah ya kiyaye irinka Dan neman takashi yaci kudina,taka dai da alama baza tayi haske ba tunda dai ba irin mugun farin nan bane Kai ato farar takashi sai Spark,dariya Hanif yayi yace ko waye wannan Spark din oho da an tashi gori da shi ake kwatance.

Sai dare Mero ta gama surutunta zuwa dare ta koma dakin da bama a shiga Inda ta fasa,Hanif an kawo Masa take away hadadde da nama Yana ci Yana ta jira yaji muryarta sabo da da ta Saba zuwa Yana Jin surutunta Yana samu Dan sauki a ransa,sallama tayi ya amsa da kyar,tace me kake ci ne? yace nama,masu kudi Allah ya Kara budi,Ameen ya furta yace ba waje da na San miki,tace ga kafa dinga sako min Yan siri iri ta wajen zanci haka,yace to ya mike ko wanne Yankan nama sai ya raba shi gida uku ko hudu sannan ya samu ya Dan turowa Mero kamar wata tururuwa ta karbe ta cinye Kuma.

Naila ce ta fito tana rike da mara tana Nishi ta samu Spark a palon sama Yana kallo tace wash Allah Baby wayyo marata,zan mutu ta durkushe a wajen tana murkususu,a firgice Spark ya mike ya rike Naila yace me ya faru? Yanzu naji ciwon mutuwa ne wannan, Spark ya rude ya dauketa da sauri sauri suka tafi asibiti,Naila tana kuka tana bige bige a mota da kyar ma ya iya driving.
Suna zuwa aka karbeta aka fara bata agaji,sai da aka Dade Sannan mace Likita ta fito ta samu Spark hankali a tashe Yana jiran amsa meke faruwa.

Likita tace Sir Alhmdllh taji sauki amma kayi hakuri ciki ta samu baifi 4weeks ba Kuma ya zube,Spark yace ke likita ance bari yafi nakuda azaba kalau matata take? Indai matata kalau take shike nan Dan ciki taje gobe ma nayi sabo,dariya ya bawa likitar tace kalau take yace to Alhmdllh nan da jibi ma zan mata sabo Inshaallah,yanzu me ake bukata? Likita tace ai tafi karfin Pad sai dai pampers babba ake siyawa matan da suka haihu ko bari,Spark yace ban gane ba nufinki yanzu Jinin jikinta zubewa yake baku da hankali kuka ce kalau take,Likita tace ya gama fita cikin amma ai dole zata danyi jini kafin a samu ya dauke a hankali duk abinda ya dace anyi,Spark yace nifa shi yasa bana son matter din Nan ta ciki-ciki,ya fita yaje ya siyo abinda tace ya kawo mata,ta bawa nurse Dake asibitin kudi ne ko ba Yar jinya akwai masu yi.

Naila jikinta ta gyara ta shirya ya kawo mata wasu kayan ta canja ta fito kamar ba ita ba fes,waccen kayan Kuma data cire sabo da wadata sai tace ban taho da me wanke min ba ni na bar miki ko ki zubar,sai da ta fito Spark yace Ina kayan da kika cire? Ni wlh bazan iya wankewa ba na barwa nurse in bata so ta zubar.

Spark yace kut kayan da nake so nace dinkin Yana miki kyau yau fa ni nace ki saka su shine kika bayar wlh ba Yar iskar da zata saka,Naila tace sun baci fa sosai,yace ma wanke,sabo da baki San zafin nema ba in siya miki Abu me tsada kice a zubar kin San nawa ce atamfar? Kudin banza gareni,Naila kuka ta fara Dan kar a karbi kaya tasan halinsa ba kunyar uban kowa yake ji ba,kaina Yana ciwo kana ta min fada,Spark ba yanda ya iya yace sorry muje amma indai naga Nurse din nan sai na kalleta tunda ta sa min kaya ta shiga uku kurwata baza ta kyaleta ba,Naila tace ka kalleta Kuma? Tace kwarai ai asibitin nan sun shiga uku sun dinga ganina kenan,juyawa Naila tayi ciki da sauri tace Nurse kiyi hakuri ki bani kayana mijina yace bai yarda ba,Nurse tace ba komai gasu ma an zuba su a Leda in kinje gida Kya wanke,Naila ta karba ta koma mota a boot ya saka ledar kayan suka tafi gidan da magungunanta,suna zuwa gida ya bawa me aiki yace a wanke su tas in anyi normal da hannu a zuba su a washing machine tace to tana ta yiwa Naila sannu gata babba dama tasan komai

Tana gamawa ta hadawa Naila ruwan wanka ta gasa jikinta tayi wanka sosai tare da gyara kanta sannan tazo tayi kwalliya cikin wata fitted gown ta Leshi brown,abinci taci ta koshi Sannan ta Sha magani ta kwanta ta hau kiran waya Hello Ana gaisawa zata ce wlh bari nayi yanzu amma da sauki Alhmdllh mun dawo gida, kowa sai da ta fada Masa tayi bari,Spark ma haka har da kiran Mima yace Naila ce tayi bari, subhannallah Kuna asibiti yanzu? ai Abin yazo da sauki kalau take muna gida,to bari muzo cewar Mima.
Kafin wani lokaci gidan Spark ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login