Showing 60001 words to 63000 words out of 108220 words
Chapter 21 - Tantiriya A Gidan Yari Book 3 Complete Hausa Novel
biki a gidan Nan to gashi matarsa ma bata haihu ba anyi wani,Kuma fa namu Albarka zaiyi ko ganga Daya ba a buga ba,ko kwano bai ce kwal ba bare a tara mata da Maza a gwamutse,Mima tace kar dai ka zauce,Dan Allah ka kula da yarinyar mutane,ka bi komai a hankali yace nine fa Mima Arham dinki guda karki ji komai.
Arham ya shirya an fesa wanka na gaske kamar yau aka daura auren,Papa ya sa Driver ya kaisu,Arham yace to gobe na sa a kawo min motata,ba Wanda aka fadawa Kai Amarya daga Ango sai Amarya suka tafi.
Amarya tana bayan mota tare da Angonta da hantsi gatsai gatsai.
Maman Haneef washe gari tazo tare da Hajji da wasu Dattijai Maza dangi su biyu sun taho sulhu,Haneef Yana asibiti ,Khadija ta dingiso daga toilet tayi wanka ta fito ta zauna da kyar tana dafe bango,wayar Haneef ce tayi ringing,ya daga,Mama cikin fushi tace yazo gida suna Nan,sun samu Ihsan tayi girki ta kula dasu ta sake fada musu karya da gaskiya sun hau sun zauna,shi yasa cikin fushi tace yazo gida,Salamatu ya kira a waya tazo ta kula da Khadija sannan yace Khadija zanje naji,tace duk tsiya karka saketa Dan Allah tace ai tayi saurayi naga ta yanda zata auri saurayin nata mu gani,duk so take yanzu a sake ta sabo da ta samu Wanda zata iya juyawa son ranta,irinsu haka suke basa aure Dan soyayyar tsakani da Allah sai in zasu juya mutum son ransu sannan suke aurensa,ai yanzu taga baza ka juyu ba,karka saketa kace ka fasa auren in sun matsa daga baya sai suji a salansa,dariya yayi yace haka za ayi sai na dawo ya fice Salamatu tazo suna ta hira da Mero.
Haidar sabo da ya samu kafar zuwa zance gidan su Mufee ya nace sai da aka daura auren Sudan da Rahma Maman Iman,ita kanta Iman sai labari taji,sannan Haidar ya dage wai biko zai Masa na Maman Rafeeq sabo da kawai ya fake da zuwa can,ana daura aure Jauro yace tunda miji a shirye yake itama in ta shirya za a iya sa rana su Habiba su rakata,tace Nan da sati zata tare,Iman sai labari taji ma,tace Allah Sanya Alkhairi.
Haidar kamar uwarsa ce ta tare harda kiran Ikhram yace wani satin muna hanya zamu kawo Amarya,tace Allah ya kaimu,yace Ina yarinyar nan kuwa me hankali ta gidan su mijinki kanwar mijinki? Ikhram tace Mufee? Ai tana nan lfy,yace yarinyar nan Inda take birgeni akwai hankali ga ladabi,tayi a rayuwa Ina son mutum me hankali da nutsuwa,ga gaisuwa tana ganinka zata gaishe ka,Ikhram tana ta dariya a ranta tace bai san iskancin da suka tsula ba duniya ce ta bi da su,Ikhram taci gaba da zuga shi tace ai duk tafi matan gidan hankali,yace gata kyakyawa,tafiyarta kawai abar kallo ce wani chafe chaf chaf....zanzo ki jawo min ita,duk da Ina da number dinta amma kwarjini take min gashi tana ta ja min rai,haka nake son mace me aji...Ikhram tace ai indai kana ciki zan Maka campaign,yace Dan Allah ki taimakawa Dan gaba da fatiha,irinku sai an tsaya mana muke samun aure,tausayi ya bawa Ikhram tace a ranta Iyaye suna cutar yara irin wannan,mutum har mutum irin Yaya Haidar,tace Inshaallah Yaya Haidar kamar ta zama taka,su basu da matsala wuyarta na fadawa Spark wlh sai an baka,ko Rafeeq sai Inda karfinsa ya kare akan wani nawa ya samu ci gaba ba abinda bazai min ba,yace na gode sister Allah ya bar zumunci Mama ta kusa zuwa gari tace nan da sati inshaallah tare zamu zo Abuja,tace Allah ya kaimu dan Uwa" ya kashe wayar tare da furta Ameen.
Masu Sharhi Wanda basa gajiya Ina matukar godiya.
AsmaBaffa
[2/28, 7:36 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI
BOOK 3
~TAIMAKO~
51-55
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM
Page naki ne
Sailuba Abdullahi Sani
*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*
Arham suna mota ya Kalli Basma yace tunda nake ko a film banga biki irin namu ba sai kace a America ba kowa ba gata,Murmushi Basma tayi tace ko a jikina an tsikari kakkausa ni dama so nake na huta sai abinda naga dama,Arham yace abinda kika ga dama? abinda dai naga dama ai sai abinda nace,Basma tace na girki fa nake nufi da zaman gida,Arham yace sai abinda nake so zanci,sannan na baki uhm uhum hum ya rufe bakinsa yace bari nayi shuru sai lokaci yayi zai nuna,Basma tace na San me kake nufi fa,mu ba wani yare da za ayi mana bamu gane ba,hannun Basma ya riko Yana Murza yatsunta masu kyau,tace ko lalle babu,yace rabu da su zan kaiki ayi miki, wai ba gyaran Amaryar maganin Infection ne ba da na ni'ima ba? tace haka aka ce yace rabu da su zamu yi abinmu,idan naga dama sai nayi zuciya na fasa komai sai anyi gyaran,kyale su Mima haka ma za ayi,zan basu sample, I just wanna have fun to night amma zan iya hakura ko dan bakin cikin Maman Rafeeq so nake sai tayi kuka tunda bata son mu Arham ya furta.
Gidansu me kyau Madaidaici Driver ya kaisu,gidan ya tsaru matukar gaske,Arham suna parking ba kowa a gidan shi da driver suka fito da kayan suka shigar da su sannan ya aiki driver ya fada musu Inda zai je ya siyo musu abinci lafiyayye,Basma sai murna take komai na gidan yayi mata an kashe mata kudi,Ango kuwa da kansa duka akwatuna goma cif ya Kai mata bedroom dinta ya kwashe nasa ya Kai nasa dakin,sannan ya dawo Palo ya gwada tv da komai normal,kitchen ya shiga ya jona su gas duk an hada,ya duba Store tare da kiran Basma da ke aikin kalle kalle yace duba ki gani komai yayi ko akwai abinda kike bukata,Basma harda iyayi tace akwai wani curry kala uku da nake bukata,yace sai gobe sai a kawo Yana kare mata kallo Yana murmushi Yana tauna chewgum,Basma tace yi poster a haka kayi kyau,ya tsaya kuwa a haka Yana tauna chewgum din sama sama, tana murmushi tace kamar dan bariki ni dama haka nake son miji,da Papa talaka ne wlh sai ka Shekare baka yi aure ba,Allah ya taimakeka dai,yanzu ma rashin kunyata ta jawo aka yi min,ki duba gidanki ki gani idan da abin gyarawa naga dai ko mai neat ne,tace sai kayana zana shirya,muje to mu shirya,suna zuwa suka bude kayan lefe suka hau shiryawa suna fito da na fitowa,Arham ya ciro wasu material English gown yace ga wannan zaki saka? in kana so mana,duk abinda nake so shine a Lefen nan,Basma tace tab masu karamin karfi Kun shige su baza ku samu kwancen kayana ba mijina ya naso,dariya ta sake yi tace Allah abin dariya kusan fa mate Dina nane Kai da kadan ka girme ni,yace Kuma a haka zan baki kuka ba,ki rufawa kanki asiri abinda nayi niyya ya tabbata zan fasa wlh nayi maganinki yanzu gashi mu Allah ya hore mana Hallare tabarakalla mashaallah akanta sai kiyi yaji,dariya Basma tayi tace ku kuke da abu daya ai mu mata....Kinga wannan jambakin Ina sonsa a dinga shafa min Ina shanyewa,sai da suka gama shirya kayan tas sannan ya dawo kan inners ta zaba Shima ya zabi wasu,yace wannan bra din sunanta yi shurunka nono,dariya suka yi ta daga kafadarsa.
Yini suka yi suna shirya gidansu Inda baiyi ba suka gyara komai,har kujerun ya kalla yace basu yi ba aba ta Kalli kofa ya juya ya canja mata position,gashi sunci sun koshi abinsu,Basma tace saura me gyaran jiki,yace karki damu za ayi,fes za a gyara min wajen zan bawa su Mima mamaki,Basma tace ai Gani suke mu yara ne suna kallon jikina wai kake so,Arham yace kyale su zasu ga yaro abokin tafiyar manya,Rafeeq ne ya kira shi da niyyar aikensa kana Ina Arham? Ina dakin me dakina,Rafeeq yace bana son wasa,yau fa aka Kai mu dakin aure ka tambayi Mima,to ai yanzu ba abinda kake yi,yace tab wallahi yanzu ko Papa ne bazan fita ba bare wani Yayana,sanda. nazo auren nawa me kuka bani Papa ne ya min komai sabo da haka ba Wanda zai aike ni naje ,Rafeeq yayi murmushi yace sabo da kayi Amarya? ai Amarya ba karya bace abinda kake yi shi zanyi nima,Basma ce tayi magana kaga wannan a dauke su? Yace ae sunyi" su zan saka da dare ko? Arham yace ahhh na tuna a canja su ba yanzu ba,Rafeeq yace ashe dai da gaske ne Arham,zauna wasa Rafeeq asirinka ya karye,dariya Arham yayi kawai ya kashe wayarsa.
Spark ya kira yace wai kaji Arham ya tare yau? Spark yace na sani ni ai,yaron nan sai gori yake ba a bashi komai ba Kuma gaskiya bamu kyauta ba,Spark yace uban me zan Masa bayan gidan nasa ni na zuba musu komai na ciki,papa ya gama gini nayi kayan ciki bai sani bane rabu da shi yayi ta Jin haushin,Rafeeq yace wannan gorin na Arham bari na fadawa Misam mu tura Masa kudi,Misam ya kira ya fada Masa,Misam yayi dariya yace bamu kyauta ba gaskiya Nan take suka Masa transfer ta kudi na kirki,Arham Yana Gani yayi dariya yace sunji gori sun turo kudi,saura matan gidanmu masu aure su Anam.
Basma tace sun baka kenan tana taba gashinsa,yace sun bayar sun wanke kansu saura Spark babban nasan Naila ce bata yi magana ba,amma tana cewa turawa Arham kudi zai bani,Basma tayi dariya tace nima haka zan koma,yace ai zaki iya tunda kina da abin bayarwa,kina da Bado sai dai yanzu ba a San kansa ba tukun.
Basma tace ni nasan kan abina ai,murmushi yayi tare da furta an gama gyaran? tace ae an gama,yace to yanzu bari kiji ko Ikhram bazan kira ba akan gyaran Jikin akwai Babar abokina Yar Sudan ce me kyau take yi,ciki da waje zata gyara min ke,tace to ayi mata magana,a waya ya kira abokinsa yace Dan Allah hadani da Mama,yace to ya bata waya suka yi magana ta fada Masa abinda za a kashe,Nan take ya tura kudin tace a kawo ta yau.
Sai da kowannen su yayi wanka Arham yace driver yazo ya kaisu unguwa,ba bata lokaci yazo suka je wajen me gyaran,a ranar ta fara yi mata ta bata wasu magungunan ta fara amfani da su sai skin da ta gyara mata ta taba wasu subulai da sauran su.
Suna kan hanyar su ta komawa gida ya musu take away suka wuce gida.
Maman Rafeeq suna zaune da Mima tace Basma yau zata yabawa Aya zakinta,Mima tace yanda Arham yake ai sai ta ji jiki Kinga bakin rashin kunya ya mutu an huta,gobe da wuri zan bawa su Haly abinci su Kai daga nan su gani lafiya take in tana bukatar agaji sai kije,Maman Rafeeq tace bazan je ba wannan marasa kunyar yaran naje na ganowa idona,in Baki je ba waye zai je to,shike nan Allah ya kaimu.
Arham Shirin bacci suka yi cikin kayan bacci masu kyau,ya damu Basma mu kwanta,suna kwanciya kamar zata narke ashe Basma an iya kissa da shagwaba,bargo ya lulluba musu yace gida yaji rufi ga kwano ga ceiling duk sabo da kar a ganmu,Basma ta fara Masa shagwaba haka kawai,Arham yace Nidai na shiga uku da duniya yau din nan har an tafi da Imanina an gama Dani,bazanyi karko ba Yar Aljanna da wuri zaki mallake ni,gwara Spark Dani ashe,dariya Basma tayi tare da shigewa kirjinsa sosai tana wata sabuwar shagwabar,Arham yace na bar miki motata na dinga aronta a wajenki Ina fita,Basma tace a'a ni dai....ka rike watarana idan ka bunkasa da kudi sai ka siya min tawa kajiiiiiii.....ta karasa da wata shagwabar Arham yace Dole na bar miki ita sai kin karba ni Kuma sai na dinga aro Ina fita,Yana magana Yana cire mata rigar baccinta a hankali har ya zare ta,Arham ya furta abu haka mashaallah,Basma tace ai ko ni na Kalli jikina na gansu sai nace Allah na gode ma na fita kunyar mijina,Arham da sauri yace ahhh kin fita tass,ya shiga shafe su yana murje su
Haneef gidansa ya shiga Mama tace sai yanzu kaga damar zuwa kana can wajen kanwar uwarka ko? Hajji yace abin naka Kuma yayi yawa fa,meke faruwa ne wai,Haneef ya zauna yace Ina Kwana Mama,karka Raina mana hankali rike gaisuwarka tukun,Ihsan tana ji ta fara hawaye da kuka tace ni na hakura da aurensa ya sallame ni kawai,Mama tace duk abinda kaji mace tace a sake ta to ba karamin abu bane,yanzu Haneef har ka Kai matsayin ajiye wata banza a gidanka? Yaushe ka lalace ban sani ba? Tarbiyyar da na baka kenan Haneef, rasa ma me zai ce yayi,Mama tace to tun muna sheda juna ni da Kai ka sallami Khadija ta koma gidan iyayenta ko Kuma ta koma wani gidan aiki" bazai yuwu ba.
Haneef yace Mana bani da da laifi ni,lokacin da nazo muku da abinda take yi....kuka Ihsan ta saki ni ka sake ni na fada Maka,Nan take Haneef yace ya na sakeki saki daya dama ni kin isheni na gaji da rashin mutuncinki,kowa ya sheda nayi a gaban ku na saki matata saki daya,Ihsan ta saki kururuwa wallahi saki uku nake so sai kayi min saki uku idan uwarka ta haife ka da jini ka karasa min Sakina,Mama ta bude baki tace a gaban nawa? a gabanki ai ba uwata bace ke,Haneef yaji dadi da tayi a gaban su suka gani,tace duk ba kune munafukan ba sai da kuka gama waya da danku zaku zo nan Kuna mana wani kaza kaza,Haneef Yana ji yaki magana ta dinga cin mutuncinsu,Mama ta fashe da kuka ko yi shuru Haneef bai ce ba,yace ai ku kuka jawo Mama sai dai ayi hakuri Kuma.
Ihsan ta mike ta shiga dakinta,duk da haka taji ciwon sakin matuka,Mama ta gama kukanta tace rayuwa ce idan da ranmu zamu Gani,Hajji yace Haneef kayi gaggawa ba a biyewa mace,Haneef yace ni biye mata zanyi wlh bazan dauki wannan ba,hakuri sai ku mutanen da Banda mu yanzu,akwai abinda ma Bai kamata kayi hakuri a kansa ba,matar da ko hakkina bata bani ai nayi rawar gani ma,in wani ne wlh tuni ya sallameta a iya case daya na Ihsan yaci ace na sake ta,bana sonta ni zuciyata wata take so,Mama tace ni Kuma baza ka auri Khadija ba idan ma sabo da ita kayi sakin,Haneef yace to ba damuwa gwara na zauna a Gwauro nasan a Gwauro nake yafi min mutunci,amma mace irin Ihsan me za ayi da ita kirjinta baza a taba ba duk da ba sonsa nake ba ai tayi min Kara tace gashi,shike nan ni a haka zan kare komai ace Yan uwa,zumunci dai zumunci bazan iya ba.
Mama tace to na fada Maka Khadija ta San Inda dare yayi mata tunda zuwanta ba Alkhairi bane tasa ka rabu da matarka ta hada ku fada wannan ai shedaniya ce kawai,Ihsan tana daki tana waya da wani tace a samo mata gidan haya me kyau na gaske Kuma a GRA.
Mama kwana zaku yi? Haneef ya tambaya? tace Allah ya kiyaye mu yanzu zamu tafi tunda a gaban magabata kayi saki mene amfanin mu,dariya Haneef yayi yace Allah ya tsare, sauran dattijan kuwa basu iya cewa kala ba sabo da Haneef Yana da kudi, fadan ma sai talaka ake iya yiwa shi.
Kudi ya basu ya sallame su suka wuce shi Kuma ya kwanta bacci,Ihsan ta zaci baya Nan ba kowa ta fitar da kayanta ta siyo kanarzir zaka Kone Masa gida,ta shigo Palo da galon a hannunta sai gashi ya fito ya Sha shadda Sky Yana kamshi da alama fita zaiyi,tsoro taji ta fara kame kame,Galon din Dake hannunta ya kalla ya tako ya fisge tare da budewa ya gani hannunta dayan ya kalla yaga harda lighter,yace gidana zaki Kone zaki sa min gobara? juyawa tayi ta fice da gudu ta bude mota tare da zuba akwatunanta ta shiga ta fice daga gidan,Me gadi yayiwa Warning yace kar ka bari wannan yarinyar ta shugo min gida ko da wasa,idan na ganta watarana a nan a bakin aikinka.
Bai koma asibiti ba Office yaje sai dare ya kira wayar Khadija yace kicewa Salamatu ta tafi gida yanzu zanzo,ko da ya Koma bai cewa Mero wani Abu ya faru ba