Showing 78001 words to 81000 words out of 108220 words

Chapter 27 - Tantiriya A Gidan Yari Book 3 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

692

a gabanmu idan ka dawo,sai ni daga an samu matsala,ai Naila ta girmi Basma,Arham yace da Shekara nawa? Nailan yarinya ce fa a gidanka ma ta Kara girma ai ko zata girmi Basma sai dai da Shekara daya ko biyu,Nailan da take kanwar kanwata....

Spark yayi murmushi yace wai yaushe ka fara son Basma din? Kace baka sonta? Na canja to Ina sonta yanzu ba shike nan ba,Ina son abata Kuma inshaallah zata warke da wuri,Spark yace baka ji ba kenan? akan me zanji tunda Allah yace gona ce mu shiga ta Inda muka ga dama,ai shine na shiga ta Inda naga damar, ni bazanyi noma a layi layi ba wlh,idan na faro ta gefen yamma,sai na tsallaka kudu,na dawo arewa a haka zanyi ba wani a layi,Spark yayi dariya sosai yace to shike nan in ta fara yoyon fitsari yace nayi a haka Ina so,Spark yace Allah ya taimaka,yace Ameen ya ma taimake ni,Naila zata zo anjima,kar tazo ta ziga min mata muna zaune lafiya Ina mata wayo tazo ta ziga min ita amma dai ai Aunty Naila ce tazo,da matar Rafeeq ce ko Chika bazan yarda ba,Chika fa chiki ya tsufa haihuwa ko yau ko gobe Kuma,Spark yace ai kuwa saura kadan,jeka ni zan wuce,Arham ya fita ya Masa Sallama ya koma ciki.
Mima abinci ta shirya aka Kai gidan Arham.

Basma tana zaune me gidan Arham ya shugo,kunyarsa take ji yanzu ita Kam,Bata so ma su hada ido,kallonta yayi suka hada Ido da sauri ta janye idonta,yace shike nan an daina kallona ma bare muyi Hira,ga chewgum Ina ci zan dawo dan barikinki fa, dariya tayi kadan ta kalle shi tare furta to ci mu gani chewgum din,a gefenta ya zauna ya dawo da Kafafunta Saman cinyarsa Ya fara mata tausa, ana lallaba Basma ga chewgum ana ci tana ganin Dan barikin ta, harda cewa baza ki Dade ba zaki koma school so nake PHD kiyi Inshaallah,Basma taji dadi tace na gode Allah ya Kara budi,Arham ya furta ke zan yiwa godiya da kika bani shashshaka da mai,dariya ta kama Basma tace nidai ba ruwana Allah,motarki tana Nan anjima zan are ta na fita,tace na baka aro ka dauka,tace ai ka bani ma kudin accnt dinka haka kace harda kudin Dake accnt dinka duka,Arham yace kaiii yaushe? Wannan baram baramar ko da wasa bazan yi ta ba,Basma ta saka jaraba tace wlh an Bata sai ya mata transfer ko ta kai kara wajen Mima,Arham yace to in an baki kudin da me za a ciyar dake,ko baki nayi ai baza ki karba ba na sani kina da hankali,Basma tace ni bani da hankali wlh sai ka bani kudina mota dai ka dinga aro amma banda kudi sai ka bani,kin yarda baki da hankalin ke? Basma ta furta ae dama bani dashi ni bana ma fata nayi hankali kawai ka bani kudina da kayi min alkawari,ta fara fushi akan kudinta,Arham tashi yayi yace Banga ta zama ba ya shiga kitchen ya buya sannan ya kira Spark yaji wuya yace ya Banga Aunty Naila bane har yanzu? tayi tazo mana,Kai fa kace kar tazo,Dan Allah tazo,ai zata zo na kaita school zata yi signing wasu takardu jibi zata fara lecture na gaji da masifar Nan ta cikin Naila gwara ta zama Busy,wannan zaman da take a gida tana hutawa taci ta Sha shine yake sata wata tabarar.

Sai da suka dawo ya sauke Naila a gidan Arham ya wuce,tana shiga Basma tace Oyoyo ga Aunty Me darasin aure ,ke fa sai kace dillaliya haka kike, Basma wai wani Aunty me darasin aure.
Basma tace wlh ki fada Masa ya bani kudina da ya min alkawarin ranar first night yace ya bani duka kudinsa na accnt yanzu Kuma wai ya canja,ni nace yayi min alkawari,motarsa ma yace ya bani zai dinga aronta a hannuna amma ita mota nace ya dinga aro ai sai ya bani kudin ko.

Naila tayi dariya tace ke shashasha ce ai wannan wasa ne,dadinki ne yasa ya fada Kinga ya zauce kenan ai sai kiyi murna a kanki ana Sambatu,ko baki yayi ai sai kice ya barshi kawai tunda kin San dalili,Basma tace Ohhh Nan dama dadi ne yasa? Naila tace ae kema in kika fara Jin dadi haka zaki Masa kyautar baki sani ba,ai ni har gidan Abbana nace na bawa Spark,Basma tayi dariya tace tab Inama Abba zai ji kin Masa kyauta da gida,Naila tace ai bazai ji ba ma,Nifa gaskiya da naga Arham yanda ya susuce Allah na zaci aljanun ruwan maliya ne gaba daya a kansa,tunanina Yana da Aljanu masu yawan gaske cewar Basma,Naila tana dariya da wasa da dabara ta dinga Dan ganar da Basma tana koya mata abubuwa.

Abba ne ya fito da tabarma waje kofar gida sabo da irin mugun zafin da ake ya shimfida ya kwanta Yana Shan iska a gindin bishiya yace kaiiiii...Abu marar kyau ma Yana da ranarsa,Zafi ma da ranarsa,ba iya su Mohsin dina bane suke waje,Nima gashi duk tsiya cewa zanyi Ina waje,Mohsin ana can ana labbaika kana kiransa zai ce ai Yana waje Yana kasar waje,duk Wanda suke wata kasar zasu ce Ina waje,Nima gashi duk uban da ya kirani Ina waje Nima, ko ta wannan bangaren ai zafi yayi amfani,Beauty ce ta fito yanzu saura kwana biyar tayi arba'in,ana sa rai da dawowar mijinta shi yasa take ta faman gyara jikinta,Abba yace Ina zaki je Kuma? Kullum sai kin fita wai Ina kike zuwa ne haka? Beauty tace Abba gyaran jiki nake zuwa fa,yace au to jeki a dawo lafiya,tana tafiya Abba yace ana jiran miji kenan Kai yaran zamani karku kashe irin su Jauro da gyaran jiki,Jauro ne kuke birge shi.
Yana haka sai ga wayar Jauro ta shugo,ya daga yace dan halak kaki ambato yanzu nayi gulmarka ni da zuciyata,munci namanka,Jauro yace ai sana'arka ce kana Ina yanzu kana gida? Abba yace a'a bana gida wlh Ina waje na fita waje,Jauro yace ban gane ba kasar ka bari ga number dinka tana shiga,Abba yace Ina waje mana kazo ka ganni Dan Kaine kawai zan fada Maka gaskiya amma Ina waje wlh nima,Jauro yayi dariya ya kashe wayar kawai ya nufo wajen Abba dolo suka Sha hira.

Washe gari Abba da rana ya shiga gidansa cin abinci ya iske Beauty ta hada gumi kamar me ana masifar zafi,yace ke kuwa Beauty sai kace kin fada Swimming pool ko kin fada teku,Beauty tace Abba fanka din ma zafi take hurowa baku da ac bari ya dawo a sa muku AC gaskiya zafin yayi yawa,Abba yace a sa mana har a kitchen sabo da watarana in na shiga taya Yar Inna girki Kinga na huta da hucin gas.
Beauty tace duk za a sa,Abba yace har tabbaci kike bayarwa wato dai ta tabbata kin mallake Mohsin dina Kuma sai abinda kika ce,Beauty tayi murmushi,yace Ina sa rai shi zaiyi mata biyu Ashe mu zuriar mu sai mata daya,Allah yasa Aslam in ya girma shi ya rama min.

Babar Iman tuni ta tare a gidan sahibinta suna cin duniyarsu da tsinke ita da Sudan,amma hankalinsa yaki kwanciya sai bikon Maman Rafeeq yake zuwa yi sabo da ya samu ya gyara kuskurensa,da kyar Papa da dangi suka shiga maganar aka sasanta itama Maman Rafeeq ta koma gidan part din kowa daban, Maman Iman taji dadin Hakan Kuma tana bata girmanta.
Kudin Auren Haidar aka Kai Papa yace a kaiwa Spark,Spark ya kira Papa a waya yace ko haihuwa banyi ba ni gaskiya baza a dora min girma da wuri ba a kaiwa Yan uwanka ka fada musu su Kai can,Naila tace yawwa kana karba shike nan ka tsufa ko Da bamu ajiye ba,furfura ce zata feso Maka da wuri in kana shiga irin wannan sabgar ta manya,Papa Yana jinta ta waya,yace wato matarka ce ta ziga ka ko? Ince kayi Abu kace baza kayi ba,ba ruwanta papa jikanka ne yace kar babansa ya tsufa,Mamansa ya fadawa suka yi communication suka tattauna sannan suka fada min muka yanke shawara,Papa yace ka gama Karyarka ai tunda ba a gabana kuka girma ba ai Kuma sai ta Allah ni,Allah ya shirye ku ya kashe wayar ya kira ya basu address wajen Yan uwansa suka Kai kudi aka yanke rana wata daya tal.

Hidaya kuwa bata da lafiya ta samu ciki sai amai take Shekewa kawai ko me taci amai amai kamar me,tana Amai Iman ma tana nata gasu makwaftan juna sunyi anko sai su hadu suyi ta tattaunawa,Hidaya taje gidan Iman tace ke ashe ciki ne dani,na zaci malaria ce ashe babbar malaria na dauka,ana zuwa asibiti wai ciki,shi kuwa murna yake fa kamar me,ni Gani nayi nayi saurin dauka,Iman tace kin hadu da mugun sauro wlh nima sauron shi ya cijeni,mijina likitane Ina samu tun kafin na fara laulayi ya fada min ashe da gaske yake
inda kisan maye,Hidaya tace har ga Allah bana son cikin nan da wuri haka,Iman tace Ina so ni murna nake wlh,ai ni da shi so muke.

Ihsan tunda ta samu gidanta ta kama me tsada Yan uwanta suka sata gaba basu yarda ba sai dai ta dawo gida tayi Idda a gabansu,ba yanda ta iya haka ta koma Adamawa ta dole ma saurayinta me kurkura Bai sani ba ta fada Masa a waya ta tafi Adamawa,Bai san tana da aure an sake ba ma Sam,suna waya sosai kusan kullum ne sai tura Masa kudi take kamar me.

Mero kuwa ta Sha gyara wajen Jummai,saura Kwana biyu akai Mero gidan mijinta Yan uwan Haneef Maza suka kawo Lefe akwati Sha biyar set uku,an zuba kayan masu tsadar gaske kamar banza,Kauyen sai tururuwa ake ta zuwa kallon kayan Lefen Khadija Maza da mata yara da Yan mata,Jummai ana ta alfahari ana Jin dadi,Jummai ta fashe da kuka tace oh Inama uban Yar nan yana nan yaga duniya,Kai jama'a mutuwa me Yankan kauna Kai rayuwa abar tsoro ce,Sani ya tafi ya barni ni kadai har abada na gama farin ciki tana hawaye ta yagi cinyar kaza tana ci wacce tayi ragowa ta saukar baki,tace bazan sake nishadi ba a duniya,murmushi ko dariya in aka ga nayi a dole nake yinsa ba yanda zanyi ne,Wasu mata suka shigo suna guda suna duba Lefe,Jummai bata San sanda ta washe baki ba tana dariya tare da furta Alhmdllh yarinya ta tayi goshi.

Kwana uku na cika Haneef da yamma ya tura motoci harda danginsa mata guda uku Yan dakko Amarya,gidansa ya Sha gyara an canja furniture da komai na gidan an canja shi,ya Sha gyara sai kamshi yake ta ko Ina ga Salamatu ta dawo bakin aikinta.
Amarya tayi kyau sai haushi take ji tace wlh sai ya gane kurensa in naje gidansa zamuga matar da zai taba,ta shirya ta zuba kyau cikin kayan lefe ta sanya dakakken Leshi blueberry ,abin ba a cewa komai,Maman Haneef tana gidan tana jira a kawo Amarya tayi musu nasiha su wuce Adamawa,Jummai tasa Mero gaba tana ta lallashinta tana mata fadan aure,tace idan kinwa kanki gata kin zauna lafiya ke kika sani idan kin watsar wlh kinwa kanki Khadija kafin kowa ya shiga damuwa kece zaki shiga,ki zauna ki rike aurenki ki rike mijinki,kiyiwa Allah biyayya ki yiwa mijinki,aka yi hakuri da wasu ma banzaye ga wulakanci,ga fasikanci,shaye shaye,barayi sannan ga talauci amma matayensu suna hakuri da su bare mijinki,in zaki nutsu ma ki nutsu, ke har wata ce,wacece ke Kalli gidanku fa na gado,ba abinda aka mutu aka bar muku,baku da gata sai Allah.
Sai da ta gama tace Allah ya bada zaman lafiya,Allah ya kade fitina sai nazo gidan ganin gida kuje Allah ya bada sa'a,aka fita da Khadija ana guda motoci biyar amma sabo da hassadar karamin gari da mata suka ki zuwa,wai su birni tayi Nisa baza su je ba aje aki dawowa da su,sai iya mota uku aka cika aka tafi,Wanda suke mutunci da Khadija Yan mata ne mutum biyu ne rak Rahina da Shamsiyya sune kawai.

Gida ya bawa kowa mamaki yanda duk Yan kauyen suke zato ya zarta haka,bayan sun shigar da ita basu dade ba aka kwashe su da abinci ruwa da lemo carton carton aka zuba musu a mota aka Maida su kauye,Mama ta zauna daga Yan uwanta mutum uku sai ita suka yiwa Khadija Nasiha sosai sannan suka shirya tafiya gaf da magriba suka tafi Adamawa,Mama a waya ta fadawa Haneef sai Khadija kawai a gida sai Salamatu me aiki.
Bai nufi gidan ba sai 9pm sabo da yasan Khadija ba kulashi zata yi ba shi yasa ma shi dai tunda ta zama tasa an gama Masa komai kawai.
Khadija Kuma ko kuka bata yi ba Sam Sam.
Tace me nake jira ma Haneef har wani ango ne na kirki da zan rufe Masa fuska sai ya bude" ta fitowarta Parlo ta hakimce tare da kunna Kallo abinta.




Masu Sharhi Ina godiya




AsmaBaffa
[3/6, 3:46 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI

BOOK 3
~TAIMAKO~


71-75


Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM


PAGE NAKI NE
Mmn Zee




Haneef ne yayi Sallama tare da shigowa dauke da Leda katuwa a hannunsa,Ganinta a parlo ya sashi farin ciki da nishadi a zuciyarsa,baya so ya sameta tana kuka dama,da kyar ta amsa sallamar,a gefenta ya zauna ta matsa da sauri gefe,tace hmm me kike matsawa na riga nasan komai naki fa? Khadija wani haushi ya kamata ta kumbura,ya kalleta yayi murmushi dama tsokanarta yayi yace ke bakya tuna ranar dan Allah baki ji dadi ba?,takaici ya kama Khadija ta mike zata bar parlon ya fisgo ta tare da bata rai ba wasa,Bata taba ganin bacin ransa ba sai yau,yace Ina magana zaki tashi sa'anki ne ni,Ina mijinki Ina magana and you are walking out of me,wai tunaninki jikinki na damu da shi? ki rike abinki indai Haneef ne bai Kara zuwa ya nema,me zaka ce ka riga ka nema ai dai kaji kunya tunda ka iya fyade,nifa bari kaji ba wani muzurai da zaka min bari in fada maka
Kaga a kasar nan kowa Yana da degree"kowa akwai Inda degree dinsa yake Alhaji Ashawo,naka degree din Yana Hallare nawa Yana kwakwalwata sabo da kaina ba dai dai yake ba,kabi a hankali bani da kai,Haneef yace nine Ashawo? da mene to nifa ba dai dai kaina yake ba shi yasa ni degree dina na rashin mutunci ne,ba ruwana da wani me gidane kai.

Haneef yace me za ayi da jikinki ko dadi babu,ba ni'ima kamas tunda na fara ma ba kwanciya kika yi ba motsin kirki kinyi ne,kuka me dadi ma a danji sexy sound baki iya ba dalla matsa ya ture ta zai wuce,Mero ta tare hanya,zai wuce ta karfi ta rike hannunsa Kam da hannaye biyu tace Kai Abar taka dadi ne da ita? in banda azaba me ta iya tsinanawa,komai baka iya ba,ai baka cika namiji ba tunda kayi releasing a waje kamata yayi kafi karfina ka koma ciki kayi ciki shine kake namiji amma ka kasa kayi half Zina,ai Kai Zinar taka bata inganta ba half kayi,Haneef yaso yayi dariya ya fuske yace a half din kika kwashe satikai kina kuka tunda half ce me yasa kika Dade kina fushi,ai idan ace full complete Zina kayi ni da Kai har abada,yanzu ma da ka ga anmin dole an kawo ni gidanka to Dan half Zina kayi ne,ka daina kuri Kai ba namijin kirki bane.
Ai gwarzon namiji shi ke tare budurwa su fafata ta amince da shi ya biya bukata Kai kuwa sai fyade.
Koma mene ni naci riba akanki nayi fyade Kuma na aura ki godewa Allah ya wuce sama ya bar mata take away din,farin ciki yake yi akan ta dinga shuru tana kuka gwara su dinga fada kullum yafi Masa.

Ledar Mero ta bude Taga kaza, fruits,snacks da abubuwa,ai Mero ta zauna tace dama ita nake jira tun safe Ina gida naki cin abinci,alkawari nayi duk ranar aure na to in za a kaini dama bazan ci komai ba tara yunwata zanyi sai nazo naci kaza ta na koshi,dama yunwa take ji ta zauna taci kaza taci kaza sai da taji kamar zata yi amai sannan ta koma kan fruits ta Sha son ranta sannan ta mike ta shiga kitchen sauran ta juye duk ta adana tare da wanke hannunta ta dawo Palo,Haneef ta samu a Palo a zaune Yana kallo,komawa tayi kitchen ta tattaro ragowar abinda ta taci kaf ta kawo Masa a Leda tace gashi naci nawa ni kanta na gefe,yace ai dama naki ne ba nawa ba ni ba irinsa naci ba,oh dama irinku ne masu cin dadi a waje ku bar iyalinku a gida,tashi yayi yace biyoni muyi Sallah,sai dai muyi a Palo ba Inda zanje,fine ya furta taje tayi Alwala ta sako hijab tazo Palo suka gabatar da Nafila a parlo sannan yayi addua

Mikewa yayi tare da furta mata good night ya wuce ba tare da ya jira ma ta amsa ba,haushi taji tace wato yanda suke yi da Ihsan haka zai min bai ma damu da ni ba,duk Ango Yana zumudin Amaryarsa amma ni ko a jikinsa" wato ni ya riga da ya tsotse zagin ba ruwansa,Ina ganin cin fuska a gidan nan,tashi tayi tare da haurawa sama ta shiga bedroom dinta hadadde tayi addua ta kwanta,baccin gajiya da kaca kacar biki ya kwashe ta,Shima haka sai asuba ya tafi masallaci,Mero akwai Sallah akan lokaci bata wuce ta,Sallah tayi da Azkhar,ta duba bata ga Salamatu ba ashe Haneef yace taje gidan sai ya gama amarci zata dawo.
bacci ta koma sai wurin 9pm ta tashi tare da shiga kitchen,Shima ya dawo Yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login