Showing 15001 words to 18000 words out of 108220 words

Chapter 6 - Tantiriya A Gidan Yari Book 3 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

934

kwana zanyi,Spark yace a Ina? Kana da gidan Uba wai ni na haife ku ne? Kun takura min fa,Arham yace wlh sai na zo tunda kayi gida da dakuna ai da baka son mutane sai kayi 2room and parlo,in Kun gaji dani ayi min aure,babu me sake aure a gidan nan sai Nan da 4yrs mun gaji,Arham yace za kuwa kuji bikina kwana nan,Mummy tace wannan Kai banda sakin aure me zaka iya,wa zai Maka aure yanzu me ka sani a duniyar 26yrs in banda ma kayi saurin girma yaushe amma gaka Nan Kai da Rafeeq kanku daya,Shima Shaheed din haka,Arham yace abin ne ya matso ya za ayi dani,Junior ne kawai ba ruwansa,Me balagar zuci cewar Arham ai ya Dade da balaga a zuciyarsa,Spark yace Arham zo na aikeka,Ni bani da zuwa a karami ba kowa ya taso da aikensa sai dai yace Arham,an haifo ni a karami Mima me yasa ba ayi kwazo ba a kaina,Mima ta mike tace Kai ni wai sa'arka ce,wai ni wannan yaro kuwa shine kuwa a mahaifata sanda Ina da ciki ba canji aka min ba,Mummy tayi dariya tace ato in kin San babu addua aka yi dai kiyi magana tun wuri,Mima ce ta harari Mummy tace Allah ya sawwake miki a gaban danki,Spark yace a'a'a'a tayi maganarta me za a boye min nasan white and black,Naila tuni ita tabi Arham sun tafi wajen Papa.

Suna zuwa a bedroom suka same shi,Arham yace Papa gata na kawo Maka samfur ka gani irinta zaka samo min,Papa baiyi niyyar dariya ba sai da ya Dara yace to Arham ni da aka bani zabi sai an kawo min samfur,gwara da samfur ku yanzu idonku yayi dishi dishi kar a dakko min wata Choco milo ace ana so nayi biyayya wlh bazan yi ba,Papa yace to dama Bada zuciya daya kace ba ko,nidai irin wannan Papa irinta Inda hali har Sunan so nake na nunawa Yaya Spark Nima fa yes ae,sannan Papa ka bani jari na kirki kaga dai mu a gabanka muka taso Dan Allah kar a barmu da talauci,Papa a dube mu a bamu jari,Papa yace to Arham za a duba ka dinga tuna min yace to Allah ya Kara arziki,Naila tana dariya kasa kasa tana durkushe ta gaisar da Papa ya amsa da fara'a,yace bakya zuwa kwana biyu ki dinga zuwa kinji,Naila tace to,shi Papa ba ruwansa dan tashi kullum azo gidan,Arham yace Papa Dan Allah ka yiwa Yaya Spark fada ya barta tayi karatu,ko bata yi aiki ba ai karatu Yana da dadi tunda dai zamani yazo a barta tayi ko part-time sai ta gama degree dinta a saukake Friday,Saturday Sunday ai yayi,Kuma ma yanzu ga private da yawa ba wahala an gama karatu in da kudi,gaskiya ka fada Masa ya barta,duk su Ikhram tayi degree ita,Chika ta kusa gamawa ga Misam naji yace zai maidata ta karasa ita sabo da mayata ya hanata,Papa yace bai kyauta ba zan Masa magana.
Naila taji dadin maganar Arham ya taimaketa sosai yau ya birgeta,suna fitowa tace Inama Zarah kanwata ta girma da na baka ita wlh,Arham yace Bada ni ba baza ku Kara mallake ni ba Kun mallake Spark Nima a shanye ni,a wajen ku zamu kare,wani Jinin zan dakko daban can dangin wasu zan samo tawa,Zarah a auren kauye ta Isa mana amma Bata da kudi,kudin kirjinta basu girma ba wannan ana tabawa zata fara kuka wayyo ka fama min,ka fama min,Naila ta dinga sheka dariya tace Allah ya shiryeka Arham ta juya zata tafi suka ci karo da Spark,yace me kuke cewa haka sai faman dariya kuke Allah yasa ba batsa yake koya miki ba,Arham yace na koya mata ko ta koya min,wurin Papa ya wuce,bayan sun gaisa Papa yace me yasa baza ka bar Naila ta koma makaranta ba ne? Spark yace ni bana so wani Boko,Papa yace a'a ka barta tayi makaranta part-time ma ta Isa a hankali sai ta gama tunda zamani ne ba sai anyi aiki ba, shi Ilimi dadi gare shi,Ya dinga lallaba Spark da kyar ya yarda yace shike nan tunda kace zan sata amma in ana so a bata tsaro, a bani sojoji nata daban su kaita su dakkota,idan Ina free na dakkota na kaita,in sun kaita Kuma su jira a tashi a dakkota,Papa yace wai matarka kai tafi ta kowa ne? ni tafi ta kowa a wajena,karya kake bata fi tawa ba,Spark yace to ka sa Mima na sa Naila aga wa zai cinye zabe,tashi kaje karka dameni Kai kullum bakinka baya rasa magana,ka tabbatar ka sata a school,Spark yace to ya fito Yana Harare Harare ance ya sa Naila a school,yayi niyya su yini amma ya fasa yace taso mu tafi gida ke,ana so a hanani Kwalbewa ko wanne time shike nan kullum na dawo gida matar tana makaranta mene amfanin haka.

Naila tana jinsa tayi mukus,yace kinyi shuru,tace ban San akan me kake magana ba,karya ne kin sani kunje Kun hada min makarkashiya wajen Papa,Naila tace ta me? Ni ba ruwana gaskiya,suna komawa gida taga motar da ta zaba dazu a waya,tace wai har an kawo motar, Suna fitowa me gadi yazo ya bashi key din sabuwar motar,budewa yayi ya shiga ya kunna motar yaji zam zam,Naila ta zaga ta shiga gaba tana murna tace munyi mota gaskiya tayi kyau,key din ya cire ya riko hannunta ya sa mata key din a tafin hannunta yace gashi taki ce halak Malak na siya miki,Naila tace na'am? Yace ae taki ce,Naila rasa me zata ce tayi,tace ni Tantiriya yau nice da mota ta fada Jikin Spark.

Tace Innalillahi.... Tantiriya tayi mota,Naila da mota,Jamilu Terror wayyo Abba,Yaya Mohsin kuzo,Umma Yarki tayi car sulluwa,Abba Yarka tayi sulluwa,Spark Yana Jin dadi ya gama birge Naila yau,jikinsa ta fada ta kankame shi tana murna,tace babbar yarinya a Abuja za a gatabara kowa ya Adana yaronsa ba ruwana horn da gadara in na sha kwana duk Wanda bai matsa ba babu ruwana,ni da nake da Ashraf Spark,Spark yace ni daina wannan sambatun muje ki bani Bado shine kawai nasan kinji dadin kyautar, Naila tace Kutmar....kai...muje ciki,Spark yayi dariya sai ya tuna sanda take prison yanda tayi maganar sak yanda take yi a prison,tace muje yau har fish style sai munyi,Spark yace a Ina kika taba ganin na kifi? Naila tace na gano ni yau zaka gani,muje yau bado idan zai koma ragadada ba ruwana,Nima yau bani da hankali kawai.

Maman Wahida ce ta kira Mero tace zo da Allah ki min wanki,Mero ta kalle ta tace wanki? tace ae ke ba yar aiki bace a gidan Yar uwata,a cikin salary din data biyaki zaki min,Mero tace wannan marar mutuncin Yar uwar taki yo ai ko a iya zagina da tayi ta cinye salary dinta,ke Gyatumar Wahida wlh ko Bata zagina bazan miki aiki ba,bari kiji ko kudi zaki biya ni nafi karfin na miki aiki yanzu,wuuu ni rufa min asiri Ina matar Hanif a nan gidan wa ya isa Dani,ke nifa tun yanzu kallon banza nake wa gandrobobi ma bare ke, kin San da wa kike magana? Kina magana da millionaire Khadija,kina magana da me arziki,Maman Wahida tayi murmushi tace a Hakan? Mero tace da ke zan fara na gane fuskarki duk sanda na tashi maganin mutane Dake zan fara,kin san zan iya kulleki na jefar da key din a kasar nan?

Maman Wahida tace Dan Allah jeki karki dameni,Mero tace kin yiwa Kanki gata zan iya zaginki tas wlh ba ruwana ni,Yan uwan naki Yan wulakanci wani dadinsu naji da zan zauna ki more ni,ke nifa me morar jikina yanzu sai Hanif, zan iya tubewa nace Dan Allah Hanif zo ka More ni,Maman Wahida tayi dariya tace ya dirka miki ciki kuwa Kiga mora ta gaske,Mero tace to mene indai Hanif ne ba komai ko yanzu zan iya in haka-in haka ince wuce,Maman Wahida tace ya wuce Ina? ke Yar nan baki tafasa ba zaki Kone" ke Khadija ki kiyayi Maza da soyayya,Mero tace ku sanda kuka yi taku waye yace ku kiyaye? wlh bazan kiyaye ba in tazo kaina na sani na koya daga lokacin na gane karatun duniya,a bari jikina ya fada min,bana so kowa ya fada min gaskiya a kyaleni naji a jikina, Tinkiya aka yanka min da aka haife ni da ita aka rada min Suna Khadija shi yasa dole ku ganni haka to aikin gama ya gama sai addua kawai amma ni ba wani nutsuwa zanyi ba,in kuka ga na nutsu to Tinkiya tayi hankali,kudi ne suka yi gardama maimakon a yanka min ragon da ake layya da shi ana samun Lada sai aka nemo Tinkiya itama tinkiyar tayi ce Bata fara Dan sanin kan duniya ba ta Ina za a ga Khadija dai dai,shi yasa nake wata gilmo gilmo,Maman Wahida tayi dariya son ranta tace Allah ya gyara to,Mero tace Ameen amma a daina neman wani sai na nutsu ni gaskiya,ta juya ta tafi can Inda su Goje suke hada Majalisar su.

Mero dakin data fasa ta shiga ta leka ta hango Hanif daga shi sai dogon wando,Jikin Nan mashaallah mulmul,komai me kyau gwanin birgewa,yatsa Mero ta sa a baki tana kallonsa galala,Bai San tana yi ba har ya saka riga,a ranta tace kallo ya kare,a fili sallama tayi taji ya amsa amma ya daga waya Yana magana yace Dan Allah Hajji ka daina maganar Ihsan,ita bata da hankali komai sai an mata,dama ni ba sonta nake ba kune kuka daura aure,tunda abin Nan ya sameni ai bata zo Inda nake ba kuma bata min waya ba,dama wacce nake so zan aura ita Kuma Allah yayi ikonsa,ku kyaleta tayi abinda take so duniya ce,ni dai bazan sake ta ba amma akwai lokaci,Ido Mero ta zaro tace Allah ya Kamaka wlh mugun bakin halinka ya fito fili,dama Kai ba mutumin kirki bane kullum sai mummunan halinka ya fito?

Hanif yace ban gane ba?ae ai kace haka mana tunda gashi rannan na zaci baka da aure sai naji budurwarka ta Kone a gobara wannan ban damu ba Alhmdllh tunda ta mutu,yau Kuma na zaci sungul (single)ne Kai" ashe wai sabo da wani abu ma har aure ne da Kai,ai tabarar tayi yawa,lalacewarka har ta Kai haka kayi aure haka.
Hanif yace Dan nayi aure shine na lalace ai shiriya ce,idan wata ka aura ba shine yake shiriya amma Ihsan fa,Hanif ya bude baki kamar ta San Ihsan din,yace kin Santa ne? tunda ta aure ka ai dole na ganeta na ganeta,dariya yayi yace to shike nan yanzu me kike so ayi? Mero ta goge kwallarta tace a taimaki ni idan na fita ka kaini gidan Ihsan na zama Yar aikinta,Hanif ya zaci Mero bata San me take harda dariya Yana kallonta a bagidajiya wai zata zama Yar aikin Ihsan,bai san Mero wayo ta hada Masa ba,yace Indai wannan ne wlh zan Taimake ki,Mero tace yawwa na gode ni dama taimakon kawai nake nema kenan,yace an gama zamu je in mun fita ko kin rigani barin gidan nan ai na Baki number ta jiya ki kirani a waya zan sa a aiki aikatau gidan Ihsan matata,Mero tace na gode ta juya ta fito zuciyarta ba dadi tace zaka gane kurenka a kaini can yanda muna tare sai na kwace ka.

Mero harda wasu Yan matan su biyu ta ja suka je,tace yau Yan Maza Raina a bace yake harda kwalla,tace kishiya aka yi min,Scola yace ke kuwa wanne Iftila'i ne yake samunki haka Khadija rannan kikace gidanki anyi gobara yau Kuma an miki kishiya, wanne Dan iska ne yake bugo miki waya haka ne?
Mero tace sunanta Ihsan yace itace uwar gida saurayina nane,Goje yace shi bai San a cike kike ba,kika ce a cike kike ta ya zai miki kishiya?

Mero tace yace sun tsotse kamar alalar Leda tayi gardama a tukunya,Suka dinga dariya,Goje yace ni Ina so da za a jefo ni nan Khadija da a haka zan murmure dake,Mero tace wlh Ina komawa gida sai na sa Babanmu yayi aure,In Allah ya yarda sai anwa Inna kishiya tunda suka ki zuwa kawo min ziyara gidan yari, yarsu guda tana gidan yari sunki zuwa akan kudin mota,Scola ya sheke da dariya yace bankada ta fara, yanzu Babar taki kike wa fata? Mero tace ai duk nasan sirrinta wlh sai na fadawa Amaryar ta kwace Babanmu ya koma wajenta ya juya mana baya duk ya tsane mu kowa ya huta,Goje yace Allah dai ya biya wlh zan so na ganki muyi Ido hudu,Mero tace Kai kwarto ta ido ma ma sai kayiwa mace ciki ni dai ba ruwana da Kai bazan hada ido da Kai ba,idan na fita daga gidan Nan Ina ruwana da ku ma dukkan ku babu na gari i Kashi,kowa Dan iska ne da mummunan laifinsa, yaushe zan hada alaka da ku kuzo Kuna min ture ,Scola yace Jamilu ma ya fita lafiya wlh an kasa yi Masa komai bare ke,Allah sarki Yar uwa Terror Kai mun Sha kallo jiya,Goje yace wayyo Allah ya kwashewa Spark albarkarsa tasss data duniya data lahira duk Allah ya kwasheta,Dan iska Jan banza Jan wifi,fuska kamar kosai,Kai kaga Jamilu Terror lutsu lutsu komai,Balarabe yace ni kadai fa na fara vibration,Ina tunowa na taba rike a hannunta a gidan Nan sai naji wata ni'ima wai nine na taba rike wannan kayan halitta haka, nace ni a barni haka ma ya ishe ni nayi dace a gidan duniya,Ashe ni Balarabe a gidan yarin ma da sa'a nazo.

Scola yayi dariya yace ai jiya sai dana ji kamar na tuba daga Daudu wlh da za a bani ita sai na tuba amma tunda bazan samu ba Ina wajen su Hajiya mu'awiya ta.
Washer yayi shewa yace jiya idona wlh sun washe ,Mero tace wai Ina Dan Indo ne? Goje yace cab ai Dan Indo yanzu na lahira ya fishi sukuni,Yana can Yana cin ubansa,ai sai ta Allah Kuma,gashi yanzu an bazama neman yaransa cikin sirri duk sai an kamo yaransa da yake sawa aiki ta nan gidan,Sabon hukunci ya tabbata akan Dan Indo,Kaunar Jamilu ta jefa shi a halaka,dariya suka yi Yace ni kaina yanzu buya nake Khadija Baki San case din ba da ni a cikin masu Zane gandrobobi,Mero tace daina buya sunci ubansu,uban gandroba,Kai nifa ba ruwana cin uban kowa nake na baka dama Goje ka zagi duk wani Gandroba kace nice na saka,Goje yace Billahillazi ba ruwana kina katsina Ina daura ko tare muke uban me zaki iya" baki da ko sisi sai surutu.

Malam Jilani suna zaune yau a daki yace ohh Kai kaga Jamilu,Malam Garzali yace idan arniyar ce tsab namiji zaiyi ridda a kanta ya koma Krista,ai Ina cikin zikiri Ina zaune na ganta manta me nake karantawa nayi sai dai bakin kawai dake motsi cewar Malam Sharu,ta samu kiwo me kyau,Spark Yana kiwatata gaskiya mashaallah,Kai Kai carkwadi gaskiya ana ci da rabonmu idan wa'adinmu ya kare mu dage mu rangado mata,Malam Garzali yace Kai waye zaiyi sake ai sai na zaba bazan sake ganganci ba irin ta farko salamatu sai na hango fuskar nan tata kamar ta birin turawa wannan Yan karamin,fuska kamar an damko gari.

Abba yau gidan Amaryar Jauro yazo,ya iske Jauro an harde a kujera da glass fari medical idonsa Yana karanta jaridar Hausa,Abba yace su Hubby ana ta hutawa,Jauro yace sai yau kaga dama kenan,Maman Annoor ce ta fito ta Sha doguwar rigar atamfa tayi kyau matuka,ta zauna a gefen Jauro tace sannu da zuwa babban aboki,Abba yace yawwa Amarya ya gida ya aka ji da abokina?
Tace gashi baka ga ya canja ba ya dawo wani matashi,Abba dariya yayi yace har abada ai yanzu sai dai ki ta tafasa Masa maganin ciwon baya,yau kafa gobe baya na ciwo,Maman Annoor tace a'a banda shi dakau yake shi,Jauro yace fada Masa,ni na taba ganin Aboki Dan bakin ciki irin Hashimu,Suna ma bakin ciki yake an canja min,Maman Annoor tace wai da nace Noori na? Jauro ya sake Jin sabon Suna yace kaji latest ya fito Hashimu,kullum upgrading dina ake,Maman Annoor ta mike tana dariya tace Qalbina bari nazo,Hashimu ya tuntsire da dariya,bayan ta tafi yace wlh yaudararka take idan gaskiya ne Allah ya Maida ni wajen Yar Inna lafiya,kasan Allah Jauro kayi kaffa kaffa da kudinka kodai tana so ta lashe ma kudade ko Kuma akwai manufa ta daban.

Jauro ya ja tsaki yace Dan kawai Kai Yar Inna bata fada ma ne mu ai mun Saba Jin sunayen soyayya,Yar Inna nata ba irin wannan bane wlh Yar Inna ta sake tace min Qalbina to lafiya ne,amma na auri Amarya sama ta Kai tace Qalbina to kullum wlh da Ido daya zan dinga bacci nasan da wata a kasa,kaima da Habiba ce ta fada zan yarda amma haka kawai karya take kawai dai so take ta susutaka tunda naga tana da hankali,abinci ta kawo shiryayye iri iri,Abba ya duba yace Amarya me dadin tuwo Ina kallo sai na tuna da girkin Yar Inna na jiya haka tayi min shi, Jauro ya bude baki" yace wlh karya kake Yar Innar Yar kauye me ta iya,teacher ce fa cewar Hashimu,ko ka manta ne teacher ce Kuma tattalin gida take koyarwa har yanzu.







AsmaBaffa
[2/16, 8:24 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI

BOOK 3
~TAIMAKO~


16-20


Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM


PAGE NAKU NE
Binta Abba
~Teemah

Hey lovelies

Ke matar aure ce kuma kina neman business din dazakiyi daga gida da kuma baya bukatan jari?

Kai dan makaranta ne kuma kana neman inda zaka ringa samun kudin kashewa?

Ko a'a ke kinada business dinki Amma kina neman wani side hustle haka da zai Kara Miki extra source of income?

Ko kinada business idea da kikeson kifara Amma Babu jarin farawa?

Toh duk ku tarkato wannan training din, dan ga solution nan nasamo muku, kawai ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login