Showing 6001 words to 9000 words out of 108220 words
Chapter 3 - Tantiriya A Gidan Yari Book 3 Complete Hausa Novel
Yankan rago,me Unguwa kiri kiri kiri yace yaga Suhailat da idonsa da mutane sun sauke yarinya a mota karama,ya kira Yan sanda ya bada rahoto kawai bata San zance ba aka kamata Kuma ya dage da hadin bakin wasu dattawan na unguwa tsofaffin banza sai da aka kaita gidan yari bada hakkinta ba,sharri ba Wanda baiyi mata ba,yaje ya bada shedar zirrrr a kotu,gashi yanzu Yana dana sani da nadama,Misam Yana gama saurara yace ahhh da gaskiyar Suhailat a bar sharia sai a lahira
Me unguwa ya dinga rokon Suhailat da kyar da lallashi Chika tace ta yafe Masa a haka ma dole aka mata,Maman Chika ta furta idan Allah Bai baka abu ba duk duniya ba Wanda ya isa ya baka,Me unguwa ka cuceni ka kashe min aure Kuma da na fito ban aure ka ba shine ka koma kan 'yata itama Allah baiyi ba sai da ka kulla mata sharri,wani mutumin babu amfanin saninsa a rayuwa wlh,Me unguwa kansa a kasa yace a yafe min sharrin shedan ne inshaallah zan gyara Halayena,Misam shi dai tunda yaji ance ai ya taba cewa Yana son Chika sai haushin Me unguwa yake ji ya matsu su tafi,Chika ya kira bedroom ya bata hijab yace ungo saka ga tsohon saurayinki nan matsiyaci Dan iska tsohon banza tsohon wofi,ai a haka zai kare rayuwarsa azzalumi wlh na tsane shi tunda yace Yana sonki ni da shi gaba har mutuwa,Chika tayi dariya tace Dan ma baka sani ba lokacin ya zaci bani da wayo naje wucewa watarana ta kusa da gidansa da dare ya taba min duwawu,ai kuwa na saka kuka naje na Kai kararsa sai da aka mana tsakani.
Misam ya rike baki yace fyade zai miki ai da haka ake yin fyade ni kiyi sauri su tafi suma su mama mene na zuwa da shi ko ta waya ai a yafe Masa,Hannunsa taja tare da dorawa a Saman cikinta tace kaji babyn mu,Murmushi yayi tare da shafa cikin yace ko mace ko namiji Allah yayi albarka, suka fito suna zuwa palon Misam yace ai Mama da Kun sani ma ta waya kuka kira sai a yafe Masa ko kuzo ku kadai ba sai da shi ba,gwara dai da muka zo yafi yana ta binmu Yana bada hakuri,Misam haka ya kaisu har wajen Mima suka gaisa suka ce tafiya zasu yi harda sauri siya musu ticket din jirgi sabo da kar ma ace dare yayi zasu kwana,da dai iya Iyayen Chika ne ba matsala,Yana kaisu airport bayan sun tafi ya dawo ya iske Haly da Mufee wai sunzo zasu kwana.
Misam yace me kuka ce kwana? Muna gari Daya ga baki ga hanci" to ba a nan ba ku koma gidan ubanku, Nan ba waje ko Ina a gidan nan lungu da sako sunna muke yi,munafukai haka kuka ce ba bikina kuke yi ba ku anko ma na Rafeeq kuka yi ku tafi gidan Malama ku kwana,Chika tace haba My Prince,yace ba ruwanki ku tashi ku kama gaban ku bana tsarki ba na hanya,Haly ta mike Mufee ma haka suka fice ,Chika tace me kayi kenan Hakan? Misam yace duk naji maganganunsu sun dawo kunnena ki kyale su kawai ko Mima baza tace komai ba,in sun gyara halinsu sai mu shirya.
Suna fitowa Haly tace ai da kunya mu koma gida muce an Kore mu,Yaya Rafeeq Kuma in kaje ma ya dinga wani cin magani kenan,Mufee tace cikin kwanciyar hankali mu tafi gidan Naila tunda tayi bari muje kawai muce aiki zamu dan dinga tayata,ai kuwa can suka nufa sai kace dole,Suna zuwa suka same su a Palo sun saka kana Nan kaya wasu silk silver iri daya riga da wando,na Naila na mata na Spark na Maza,ba karamin kyau suka yi ba,Naila ya aika yace je ki kawo min wayata,Naila tace na gaji wlh Baby sai juyani kake yi yanda kake so,yace to na taba cin bashin ki ban biya ba? tace a'a,yace na hanaki ci Sha da sutura? tace a'a,yace ya batun Kwalbewa? tace Nan ma zam zam,kin taba cewa na baki abu na hana? tace a'a,yace ki taba bani sisinki kyauta? Naila tace Ina naga kudin baka,yace to ta ya bazan juyaki ba,Dan ma kin rainani ne Ina kyaleki shi yasa kike fadar haka,in wata ce jiki na rawa zata yi kafin nace anyi duk da kema kina kokari,Naila tace karfa ka manta Nima Yar gata ce a wajen Kaka,Inda na girma ban San babu ba duk abinda nake so shi ake min,Kuma Allah ya bamu rufin asiri bare kace kudinka na bi ato kana min zan maka,Kai kasanni wlh ko so kake na dawo Maka Naila ta ne ta farko,dariya yayi yanda take zazzare Masa Ido,yace kwana biyu ai kina Off ban saki a corner ba shi yasa kike haka,Naila tayi fari tace na saka dai a corner badan Ina tausaya Maka ba sai na Maida Kai Baseeru na Kone ma ruwan jikinka,dariya Spark yayi sosai yace Allah ya baki lafiya wlh na daina tausaya miki,Naila da kuri tace ni dama bana so ka dinga daga min kafa, a yini a kwana digir digir zaka gani...su Haly ne suka yi sallama tare da kwankwasa kofa,Naila ta ce Spark tashi ka bude kofar nan murmushi yayi ya jawota ta fado jikinsa"kissing dinta ya shiga yi a lips sannan ya mike ya bude kofar ta tafi dakko Masa wayar.
Haly ne suka suka shugo da fara'a,Spark yace kune ashe,suka ce ae Yaya, Mufee ta mika Masa hannu wai su tafa,ya Kalli hannun yace sa'anki ne ni? tunda muke na taba handshake da ku? Kuna mata au kin manta uwar mu Daya uban mu daya dadina zaki ji Mufee? Baki suka bude da sauri Mufee tace sorry wlh gani nayi muharramina nane Kai,Spark ya kalle ta yace uhmm to ki fito da miji a muku aure sai kuyi ta handshake shine karshen kusanci Bada ni ba wannan iskancin na koma Dan kauye dankwali ya ja zakara matata ta Jani duk wannan iskancin bada ni ba,dariya suka yi Haly tace kawai dai fada kayi Yaya ba wani Dan kauye Itama ai ba Yar kauye ce ba,au na zaci ai zaku ce itama tayi clean yanzu kuci ubanku yanzu,suka ce a'a, Alright ya furta ku zauna.
Naila ce ta fito da dan gudu da wayar tana taka steps tana kawo Masa tana yiwa su Haly barka da zuwa,Da wayar da hannun ya hada ya rike tare da jawo Naila ta zauna a tsakiyar cinyoyinsa,su Haly ya saci kallo yaga sunyi sauri sunyi kasa da Kai,yace dama Mima ta haifi masu kunya? film suka koma kallo ta dole,Naila tace akwai komai fa a kitchen kuje ku zuba kuci abinda kuke so,Mufee tace a kawo mana mudai kar ace munyi shishigi,to baza ta tashi ba sai dai in baza kuci ba ku barshi" ku baki ne ko gidan bakon ku ne,Haly ta mike Mufee ma ta mike suka nufi kitchen,Bayanta ta kwantar a kirjinsa Yana shafa gashinta yana danna waya,Spark yace gobe ranar ziyara ki shirya muje wajen Mero,Naila fuska ta bata Nan take,kishi ya cika mata zuciya,Jin shurun yayi yawa ya leka fuskarta yace Allah ya shiryeki Naila,tace Ameen zanje ai Allah ya kaimu.
Fitowa suka yi da plate da lemuka Naila tace Kun min ta'adi fa amma ai duk daya tunda jininsa ne ku amma plates din bana kowa bane duk kalolin nasa baku ga na musamman bane,Haly tayi murmushi tace to ayi hakuri amma miji ma komai nasa ba a tabawa? Naila tace Kai Baku sani ba? to spoon ma kala kala sunfi kala goma duk irin nasa daban ne wlh Kuma kullum da kalar da za bashi ya ci da shi,plates ma haka nasa irin iri ne Kuma kullum da kalar da za a bashi komai da kuka sani nasa ba a tabawa na daban ne,Kai Sallaya ma sai da izininsa wani zai hau Masa,Haly tace ai Kinga mun karu shi yasa kitchen din kamar ana siyar da kaya,Naila tace ba a wasa,Spark Yana jinsu Yana danna waya har wani dadi yake ji shi Kam ana girmama shi ya Dade Yana mamaki ko cokulansa gasu da yawa iri iri amma baza a bawa wani irin nasa ba,yace bala'i da masifa ya kare akan Wanda baiyi dacen mace ba.
Su Haly a gidan suka kwana abinsu sai abinda suka ga dama suke yi indai baza su taba mata kayan Spark ba to suyi komai ma,sun sake sun samu waje sai suka fasa tafiya suka yi zamansu a gidan, a gidan Naila da Spark suka barsu suka tafi Kano wajen Mero.
Naila burinta taje taga su Goje ko zasu ganeta.
Har da cewa amma zamu fara ganin Maza Wanda muka dan sani a Dan musu alheri ko ka samu Lada kaji please,Spark ya kalleta a jirgi yace kice kawai kina son ganin samarinki,Naila ta wayance tace daga nace kayi sadaka Dan Allah,banza ya mata yace kin ma rainani Ina kallo zan barki ki wani gaisa da kartan banza wlh idan kika kula wani a ciki ranki sai ya baci ya hade rai,Naila tayi shuru Yana ta faman tsaki har suka sauka.
Haidar ne ya samu Jauro a gidan Amaryarsa Jauro Yana Palo Yana hutawa,Haidar ya shiga gidan,bayan sun gaisa ya gaida Maman Annoor ma yace Kawu dama fada Maka zanyi gobe zan koma gidana na zauna a can,Jauro yace aure kayi? Aure Kuma Kawu zanyi baka sani ba,to baza ka koma ba kana gida dadin kaje kana baligi ba kowa Kai kadai a gida ka dinga kawo yaran banza to ban amince,in kana so ka koma ka Nemo matar aure dama ka isheni,dariya Haidar yayi yace Inshaallah zan kawo matar auren Allah kawo ta gari, Jauro yace Ameen ko Kai fa kaima ai ko Dan Hubby ka samu me fada Maka amma kullum Haidar Haidar ba canji ko Hashimu ai an canja Masa suna shi da yake local ma ana fada Masa Abban Mohsin,mu kuwa da ba Da ba jika kamar samari muke ai mu sai Hubby,Honey,Sugar,Haidar ya dinga dariya yace Kawu yanzu in aka kiraka da Hubby sai ka amsa? Kawu ya furta na dade da amsawa ma tuni,yaro sa wasa ana ta ci gaba Banda kai gaka kyakyawa sankacece sai bulayi kake yi a gari,Kunkumar ma taki samuwa,Haidar dai ya Dade Jauro yana ta babatu akan ya samo mata shima,sai da ya gama fadan sannan ya Kalli matarsa Amarya yace a karrama min Dana da kayan motsa baki,dariya suka yi taje ta kawowa Haidar kayan ci da Sha sosai.
Naila kuwa suna zuwa lokacin Maza ne duk,driver da ya kaisu yayi parking suka fito,Spark yace kinji me nace ai karki kula wani ko da wasa muje ya rike hannunta suka shiga,sai kallonsu ake yi kowa ya gane Spark Naila sai kallonta akeyi duk mazan Nan kallon sani suke mata sun rasa Ina suka Santa,Naila kamar tayi kuka tana kallon su Malam Jilani duk gasu Nan anzo musu amma Spark yace in ta sake tayi magana tam,su Goje suna ganin Spark da mace suka tabbatar Jamilu ce ba karya tunda shi ya aureta Kuma gata sun zo tare ma kowa ya kalleta yasan itace sai dai ta Kara kyau,ta Kara haske da kiba ta goge gata Kuma a shigar mata ta alfarma domin shadda ce a jikinta peach color.
Masu Sharhi Ina godiya matuka.
AsmaBaffa
[2/14, 8:52 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI
BOOK 3
~TAIMAKO~
6-10
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM
PAGE NAKI NE
Mariamsanee50
*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*
Dan Indo Yana zaune wajen abokinsa kasurgumin Dan iska ne ya hango Naila ya saki salati sai da abokin ya Kalli Dan Indo yace lafiya? Dan Indo Naila kawai yake kallo yace wayyo Jamila wannan tafi karfin Jamilu sai dai Jamila, mikewa yayi Yana kallon Naila ya taka suna tafiya ya Sha gabansu,ko Spark bai kula ba yace subhannallahi kayyasa Chau Allah dai ya biya,Innalillahi wa innailayhirrajun,walahaula Wala kuwwata haka kike da kafirin kyau ban sani ba Ina Nan mun zama kartan banza,Naila tayi mukus ita tsoro ma abin ya bata,Spark fuska ya tamke ya Maida Naila bayansa sai ga Goje ta baya yace Dahara....Spark yace wannan wanne shirme ne? are you out of mind? Kun San wace kuwa she is my wife,Dan Indo yace and so? Ina ruwanmu da aurenta mu Jamilu Terror muka sani a bamu abinmu muyi ciki,dama Ina nemanka Dan wulakanci shine kaje ka aure ta uban waye ya saka ka aureta? Spark yace ubanka ne yasa ni stupid,Kai in ba jahili ba matar wani zaka kula,Ya ja tsaki ya fisgi hannun Naila yace muje,Dan Indo ya tare hanya yace wlh ba Inda zaku je sai ka bamu abar mu,Naila tace zanyi magana Dan Allah please hannunta ya matse da karfi ta saki ihu sai da ya ja hankalin Mutane,Scola ne ya tashi Yana taku da sauri Yana karairaya yace wayyo kawata Yar uwata haka madarar Nido ta Maida ke wata fresh and Beauty,gaskiya ne ai kin samu ta me kudi wlh abinki Shar yo Yar Nan kullum kaji da kayan marmari ba dole a fitar da Madara me inganci ba ,Spark yana Jan Naila,laaa Tantiriya ga Tantiriya,Shege Jamilu Terror Kaine haka? washer ya tafi da gudu Yana Jamcy Jamcy kamar zasu cinye Naila haka suke yi,Malam Garzali daga nesa yace Allah ya sanya Alkhairi amma kin dauki hakkin mu,ragowar bujenki suna Nan muna kallo sun zama kayan tarihi,
Spark samawa kansa lafiya yayi ya Maida Naila bakin gate ya sata a mota ya shiga shima ya rufe,yace wannan ai sai su cinye ki duk ga mata nan ke kadai ce mace,Naila tayi shuru yace da ke nake fa,tayi shuru,yace wlh sai na sa an Kai Dan Indo dakin duhu an gana Masa azaba,Yana ta faman masifa Naila tayi shuru yace bana son raini,tace Kai fa kace nayi shuru kar na sake nayi magana sabo da haka nayi shuru.
Dan Indo sai ashar yake durawa a filin ana rirrike shi,Yana cewa Dan wulakanci da cin hanci yarinya Bata gama wa'adinta ba ta gudu Kuma gashi tazo ana kallo ma'aikata suna kallo,Kuna kallo baza ku kamata ku dawo da ita ciki ba,sai na tona asiri yau nine Nan na fitar da ita ni na sa ta gudu,sabo da ta auri me kudi Yana Baku cin hanci shine aka kyaleta,ai nine na gayyato yarana yan Daba suka bude wuta a bakin gate da su Goje ta ciki muka samu bulalai muka Zane kowa,muka hargitsa kowa ta fice a sanadinta mutane da yawa sun gudu yau na fada kowa yaji nine....
Nan take securities suka kama Dan Indo suka ce zaka yi bayani,aka yi ciki da shi,Goje yace tab Dan Indo ya kira ruwa zai ci ubansa a gidan yari sai sun kusa kashe shi,Scola yace Allah na gode maka da ka sa min basira na koma mace.
Spark kuwa Kallon Naila yayi ya ja Kwafa,sai da aka gama da Maza kaf suka koma sannan aka fito da mata,Spark ya kira Mero ta fito sannan suka karasa,Naila fuska a hade tana kishi da kyar tayi kokari ta danne,suka gaisa da Mero,Mero tace Naila Ashe kin San su Azima, Naila tace la na sansu amma a sanadin su Chika, ni Maza na sani a cikinsu na zauna a can muka hadu da my love ta furta,Mero tace kinyi dace Nima nayi dace,Naila tace ban gane ba,Mero tace to Nima Ina da nawa a prison,sai lokacin Naila taji dadi tace Allah yasa da shi za ayi kema in kinyi aure karki sake a Miki kishiya Kinga dai ni kiyi koyi Dani,Spark Yana jinta wai Mero take gayawa irin ta San mijinta ba aure zai Kara ba,duk ya gane hirar ta,a ransa yace Ina ma Ina da ra'ayin aure da na bawa Naila mamaki,Mero tana ji tasan ma da ita Naila take,ta mikawa Spark muficin da take sakawa tace gashi na iya? Spark ya karba yace sunyi kyau mashaallah na gode,tace nice da godiya,naso ace yau Innata zasu zo da ka gansu amma sun fasa wai sai gaba,kaga a ciki Ina zuwa makaranta na iya karatun Hausa yanzu na fara iya na turanci,ga addini,Kai na fara zama Malama yo duk su wankan haila,wankan janaba,wankan juma'a,Idi duk na iya ai inaga Nima watarana sai na bude makarantar koyarwa,Spark yace naga alama kinyi kokari sai ki dage Dan kin kusa fita an kusa fara shariarku,Naila kishi ya