Showing 30001 words to 33000 words out of 108220 words

Chapter 11 - Tantiriya A Gidan Yari Book 3 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

931

bari ne? Naila tace wata biyu da Yan kwanaki Abba,yace Kuma ba komai? Tace ba komai Abba banji komai ba ko ciwon Kai bana yi bare na sa rai,Abba yace to na kusa Kuma fara yi miki kuka Naila abin nan yayi yawa sai tausayinki ya sani kuka Kuma,Kuma mijin naki kalau yake? Naila tace kalau yake Abba lafiya lafiya muke komai,Abba da Yar tasa Naila ba kunya,yace to Allah ya kawo Ina ta Miki addua,jiya ma tsohuwarki bacci na hanata sai da muka yi sallar dare sabo da muyi muku addua,Naila tace na gode Abba amma na karaya da haihuwar nan,Abba ko wacce in aka yi aurenta sai ta samu ciki.

Abba yace to ai lamarin Allah ne ba a Masa dole shi yake bayarwa,irin su Jauro Kuma suce me? Gwara ke kinyi bari Jauro ko Jinin Haila bayayi,Naila ta kwashe da dariya,Abba yace Allah da Jauro mace ne ko Jinin Haila bazai yi ba bare ma a sa rai zai haihu.
Naila tayi dariya kamar me har suka gama waya,suna gama waya yace Beauty tashi ki tafi gida kar Dana ya dawo bakya nan,kije ki kular min da Dana,ga surukanki amma bakya kiyi da ita,Beauty tana dariya ta mike ta dauki Jakarta,tace Abba zan Kara cake din nan,Abba yace ajiye Yar Inna ce zata karya da shi da safe,Kubra tace na bar mata,Abba yace gobe ma rana ce Kubra,Beauty dai ta dauki cake tayi Sallama ta tafi,Abba yace kice Ina gaida me gidan.

Spark ne ya dawo ya samu Nailansa tayi shuru tana tunani,a gefenta ya zauna tare da Dora kansa a kirjinta ya kwanta ya furta duk tunanin cikin ne? Nasan bazai wuce tunanin haihuwa ba,wai ni da kika damu kanki Naila na taba miki complain? Ni wlh ban damu da dole sai na haihu ba,idan Allah bai bawa mutum ba kashe kansa zaiyi,wani yaron ma da masifa ne in aka baka shi,Kuma ko Shekara bamu yi ba amma kinbi Kin damu kanki,damuwarki baza ta Baki ba ko ta hanaki,in ma zaki hakura ki karbi kaddara ki hakura,addua ce kawai taki na mene na damuwa,bana son wannan abin da kike yi,da Allah kike fushi ko da wa tunda shine bai baki ba,Naila tace nifa ba tunanin haihuwa nake ba,bana son karya fada min meke damunki to ko takalma kika samo latest a siya miki a huta tunda ke rayuwarki a takalmin sawa zata kare,dariya tayi tace Allah ba wannan bane kawai yau ne naji bana Jin dadi sai na dinga Jin kunci da haushin kowa,Spark yace ko period ne? tace a'a haka kawai sai naji kamar nayi kuka, Spark yace to yi kukan mana tunda gani ba sai na lallashe ki ba,gidan Rafeeq zaka kaini na Dade banje ba naje naga me ciki Ikhram,murmushi yayi yace dazu naji yace yau bazai bude gida ba Kwalbewa zai yini Yana yi na matsa Masa a Office kwana biyu baiyi komai ba

Muje mu hanashi sakewa,dariya Naila tayi tace ku dai wlh kamar abokai,Spark yace Khalid yazo ma da matarsa suna gari yace zai je can muje kawai,tashi tayi suka shiga wanka tare, Spark duk yanda hankalinsa ya tashi a toilet ya so ya kwalbe Naila taki yarda yau,shi tunda ya aureta bai taba nema ta hanashi ba sai yau,sai ta dinga Wayancewa,kyaleta yayi Bai nuna ya damu ba tunda jiki da jini sai ya rabu da ita suka ci kwalliya suka fito zuwa gidan Rafeeq,itace ke driving dinsu suna ta hirar su ta masoya,yace an dai hanani Kwalbewa,Naila tayi murmushi tace sai mun dawo zan baka Bado karka damu,nasan halinka sai ka fara Jin Haushin mutane.

Washe gari Mero ta shirya breakfast,tana tsaye a Palo tana jiran Ihsan ta fito sai ta ganta ta fito daga bedroom a kasa,Haneef ta gani ya sakko daga sama dakinsa,Mero tace a'a lafiya? Haneef yace da aka yi me? tace naga ka fito daga sama dakinka daban,itama ta fito daga kasa dakinta daban fada kuka yi?me ya hada ku kamata yayi ace Kuna Jone ana tashin ku da kyar,ta bude Ido tace Baby kace uhm uhm koma bacci ban gama Jin dumin jikinki ba,amma sai na ganku baram baram,Kai kayi gabas da Kai ita tayi arewa da nata kan,Kai da zanji kace I love you,tace I miss you,ta lumshe ido,kayi mata kallon kauna,ya haka ne bafa mu gane ba mu,Ihsan tace amma ke ban taba ganin Yar shishigi irinki ba,Ina ruwanki to,mata da miji kika sani ko dazu na sakko na shiga wannan dakin.

Mero tace karya ne Aunty tun asuba Ina palon nan Banga motsin kowa ba,Haneef yace kowa dakinsa daban yake kwana Khadija bama hada shimfida,Mero ta bude Baki tace ka kyaleta? Wlh ka Mori sadakinka ko ka Kara aure hauka ake a garin Fir'auna ka taso wlh karka yarda,Haneef ya boye dariyarsa,Ihsan takaicin Khadija ya kamata tace ke na Kore ki daga aiki Yar iska marar mutunci marar tarbiyya Ina ruwanki da aurena,bana shiga harkar mutum amma ke wlh mun sa kafar wando Daya dake,Mero tace Oga ya dakko ni ba ke ba Kuma gyara nayi Allah ya Gani ko a Islamiyya Malam yace in kaga ana ba daidai ba in har kana da hali ka Hana to naga Ina da hali Kuma zan iya shi yasa,Allah ya bamu Ilimi mun nema Kuma mun samu dole mu Fadi gaskiya Mero ta furta kamar gidanta ne,Shi Haneef dadi yaji ta birge shi,dama Ihsan ta dame shi,dining suka zauna,Ihsan ta bude abubuwan sai ta toshe hanci tace wannan wanne irin soye soye ne,Haneef ya kalla yaga shi normal komai ya Masa ya zauna yace serve me,Mero tace ya Maka Kai? Yace yes yayi min,tace an gama ta fara zuba Masa.








AsmaBaffa
[2/20, 2:14 AM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI

BOOK 3
~TAIMAKO~


26-30

Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM


PAGE NAKI NE
Chuzahraumar



*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*




Ihsan Ido ta zaro tana mamaki yanda yake sakewa da Yar aikin da jiya tazo ma,farfesun ya fara dandawa,tunawa yayi da kazantar gidan su Mero masu tace gasara da Skirt,yace ya batun tsafta kuwa nan dai ba skirt Kuma ba koko bane ko? Mero kamar ta sani tace ai tunda naje aiki Abuja na goge bana biyewa babar mu yanzu ma kullum gyara nake mata Ina so na koya mata yanda ake lamarin duniya,Ihsan tace uwar taki? Ae mana iyaye ma a ilimince idan anga suna ba daidai ba ta siga me kyau da tausasawa zaka fahimtar dasu,akwai wata kissa ta Sahabi na manta,Ihsan tace ke Jahila kice baki sani ba me kika iya kazama,Haneef ne yayi magana ya isa,itace kazama ko ke? Wanda yake gyarawa da Wanda Yana zaune sai dai ya zuba Ido ciki waye kazami?,Ihsan tace Yar aiki ce fa karka manta Haneef,yace to ita ba mutum bace,cin fuska ne wannan ai,ke baki aikin fari bare na baki Kuma ki damu mutane, Ihsan fushi tayi ta mike ta bar wajen tana cewa bazan ci ba bana ci,Mero tace ikon Allah Innallaha ma'assabrin Aunty Ihsan,Aunty Ihsan tawalkaltu alallah bazan biye ki ba Ina da hakuri ni,Haneef ya kalleta yace sit,na'am me kace? Zauna nace muci,Ido ta zaro tace muci fa kace,Uhum muci mana nace" zubawa kanki,Serve your self,Mero tace kana da kirki gaskiya,yace girkin yayi dadi kwana nan zan Kara miki salary double,kinyi abinda banyi zato ba,yanda nace zan biya ki ba haka zan baki ba zan Kara miki,Mero ta Sosa Kai tace na gode tana ta Jin dadi tana murmushi

Farin ciki ya kamata tace yanzu aka fara harkar girki Oga,tunda haka ne zaka ga Abinci iri iri dama na koya a Abuja zaka Sha dadin girkina iri iri,dariya yayi, tace Allah sai nazo na fara zuba Maka Egusi soup,da miyar waterleaf Alaji ya Sha wata tarwada an gama,mu muka iya sarrafa abinci,ni da kitchen yake a tafin hannuna,Kuma nice wacce nasan sirrin tukunya babba da karama,tukunyar kasa data karfe duk nasan kalar dandanon girkin su,Haneef yace yana murmushi to zauna kici,zama ta gyara ta fara ci,suna cin abincin su,Ihsan leken su take yi ta bedroom,tana ci Yana satar kallonta, Mero duk da a kauye take abubuwanta na birgewa take yi.
Sai da ya gama ci ya kwashe wayoyinsa yace Office zan tafi,Kallon film dinmu fa? Maybe na dawo kafin lokacin idan Kuma ban dawo ba ki kalla Kya bani labari

Mero tace to an gama a dawo lafiya Honorable mijin Ihsan Yar wanka sai dai babu mamora,wlh ka dinga morar ta shi yasa take ma gani gani,kamar zaman maguzawa,shi yasa aka ce me shi ya Kara aure sabo da irin haka,yanzu da kana da wata matar da yanzu Ihsan ta kawo kanta tana make ma Murya Darling Ina Kwana,amma yau ko gaishe ka banga tayi ba,haba ko Fir'auna sai da ya zabo mace ta gari Asiya ya aura bare Kai Musulmi,Haneef Yana dariya yace haka ne Khadija zaki tayani zabowa na Kara ni kaina naga Ina bukatar mace ta gari,Mero ta washe baki tace in kayi aure zaka Kara lafiya da nagarta da daraja a idon duniya,amma wannan Ihsan ni da ita ai daya muke,Nima da zaka siya min kayan daukan wanka wlh haka zan dinga cakarewa a gidan nan bamu da banbanci,to yanda nake kwana na tashi haka take kwana,Dan Allah Kai baka ga ta Raina ma hankali bama,ka kashe kudi ka biya sadaki ta zauna a gidanka,Kaci da ita ka shayar da ita ga sutura sannan baka amfanar komai Kuma,ai cikin biyu ayi daya kodai ta dinga karbar Ijakala ko Kuma ka dauki mataki,a kirata ayi maganar nan a gabanta.

Ihsan dama tana labe tana ji tace to munafuka algunguma Ina jinki,Kuma wlh sai kin bar gidan Nan na Kore ki dole ne aikin wai,oh my God kina sani magana,Mero tace ai ba wani Abu aka ce ba fada za a miki ni bazai yuwu na dinga ganin ogana Yana da mata Kuma Yana kwana ya tashi shi kadai ba,kije ki dinga bashi hakkinsa salary na nake ji,ya samu nutsuwa yafi Jin dadin bamu akan lokaci,yau da fushi ya tashi a gidan Nan so kike watarana ya kore mu sabo da rashin samun nutsuwa,in kin San hakane me yasa kika aure shi ai sai ki barwa masu sonsa,kullum cikin fushin ubangiji kike,Ihsan tace ya neme ni ne naki zuwa,sai ya neme ki zaki je,ba hakkinsa bane a bashi mana kayansa,Baki Ihsan ta bude galala tana kallon Mero,tace are you normal?oh bagidajiya ce ke dole kiyi,Mero tace me zaki nuna min ai na fiki ko kina da Ilimin bakya aiki da shi ke,me zaki nuna min kina Kashi kina fitsari wanne kwambo zaki yi, ki bawa Oga hakkinsa kawai a samu salama,bazan bayar ba idan Jikin na ubanki ne kizo ki dauka ki bashi

Mero tace Allah ya kiyaye ma Ubana Sani yayi irin jikinki ai babu lafiya Kuma namiji da jiki irin naki,ke yanzu Dan Allah bakya ganin asarar man shafawa kike da kayan kwalliya? Miji baya yabawa ba ruwansa Dake kema ba ruwanki da shi,ai wlh in nice ke ko Mai bazan shafa ba,ko dangwali yaba bazan shafa ba bare Mai me kamshi,to asara ce babu me yabawa,ni da ke ba banbanci,Haneef Yana jinsu Yana latsa waya suna ta fama,ya fice abinsa,Yana fita Ihsan ta zazzaro ido tace ke ko uwar data haife shi ko uwarsa Hafsatu bata Isa ta fada min magana ba ki shiga hankalinki,bana hayaniya bana shiga Uzurin wani bana so Kuma a shiga nawa,in kika ce zaki shiga gonata wlh iyayenki sai sun bar kauyen ku tsirara,ki kama kanki bana shiga safgar rayuwar wani,Yar aiki ce ke ki tsaya a matsayinki duk da shi Haneef ya daure miki gindi,Mero tace a'a karki Masa sharri ta Ina ya daure min yanzu ma fitsari zanyi abina.

Ihsan ta tsaya tace ke...ke...ki shiga hankalinki wlh na fiki rashin mutunci,Mero tace nawa rashin mutuncin degree ne dan Cotonou,naki kuwa bazai wuce na nan Benue ba,ki bashi jiki ki huta,wlh indai Ina gidan nan sai ya latse ki ya taba kudinsa bazai yuwu ba a dinga ci da rabonsa,naga uban da zai sa ya tabani to,kanin ubanki ne shi Haneef din,Yar iska marar tarbiyya berar kauye.

Mero kalamai ta tausasa da lallashi tace Aunty Ihsan....Auntyna...kiyi hakuri haka zaki hakura ko dukiyar fulanin naki basu da girma ki daina Jin kunya,wai zai ganki kiji kunya ko ai abin kunya ne a gansu ba girma ba haka bane,nooo inji Spark....aure ne sirrinku ne ba wani zai fadawa basu yi masa ba,Kinga ko mu sai dai muyi hasashe cewar ba wasu manya bane amma bamu da tabbas tunda a riga kawai muke ganinsu,Ihsan tace na shiga uku yau Allah ya tsinewa uwarki,Mero ko a jikinta tace Kinga ki nutsu hakuri zakiyi haka Aunty kina so kema fa,Haneef fa ga kyau ga kamshi yanzu wata macen in ta ganshi sai ta fara zaucewa amma ke ana nuna miki hanyar arziki kina runtse Ido, kije kici arzikin Hallare Aunty,ki tuno farko farko sanda kika Kai kanki ya kika ji? Ki koma ki sake karbowa wlh,Ihsan gani tayi Mero kawai bata da Kai ta ja tsaki ta juya tana cewa idan ma hada baki kuka yi shi yace kizo ki lallabani to ki koma ki fada Masa jikina ban bayarwa in Yana so ya kawo kansa,ta juya a ranta tana murna cewar lallai Haneef da Khadija suka hada baki sabo da taje ya kwanta da ita,wata dariya tayi tace wlh tukunna ma Haneef,wasa kake da mata sai ka gaji ka kawo kanka kana roko na.

Salamatu tana gefe ta Dora hannaye a Kai tana tsoro da mamakin Mero,sai da Ihsan ta bar palon Mero ta dinga dariya kasa kasa tace ai wlh sai bakinki ya bude Ihsan,aikin banza baki san ni ba so nake ya kwanta dake ba kawai Dan na hanaki sukuni ne Kuma gashi na saki magana,sai na koya miki masifa a gidan nan, Kya fada mana aji,aji indai bana makaranta ba bane ai aikin banza ne,Salamatu tafiya tayi ta buya kar ma Mero tayi mata magana ace suna gulma.

Haneef kuwa har yaje Office Yana tuna Khadija Yana ta dariya shi kadai Yana Jin dadi,yace gaskiya fa yarinyar take fada na Kara auren nan yafi kawai,dama Mamana tana fada min ko waye ya bani shawara indai na duba naga ta kirki ce kawai nayi aiki da ita,kullum Ina bukatar mace amma ba dama,gaskiya zan dauki shawarar Khadija wannan ai me kaunata ce,Allah sarki tana so na samu nutsuwa Kuma gashi madarar Nido fa ta taru,wannan Yar iskar kuwa ko bata da lafiya wa ya sani ma ko aljani ya aureta oho,ba komai bari na dawo gida.
Mero tana kitchen ta dora abincin rana Ihsan ta shugo ta bangajeta ta wuce ta dauki lemo a fridge ta fita,tukunyar Mero ta sauke tace yau sai yamma zanyi girki kowa yaci nade da Mai yau kin jawo wa kanki,sai Haneef zai dawo nayi masa,ta kashe gas ta fito ta wuce dakinta da biscuits da Madara,taci ta koshi tayi Sallah ta kwanta ta dinga baccinta har da cire kaya daga ita sai vest da pant .

Yunwa ce ta damu Ihsan taga abinci shuru shuru gashi so take taci ta fita ta Sha wanka cikin material me tsada,fitowa tayi kwas kwas tana kwalawa Khadija kira,tafi karfin ma ta kira sunanta sai dai Yar aiki...Yar aiki ....Salamatu ce ta fito da gudu tace dalla ba ke ba ta gasken Yar aiki nake nufi,tsaki ta ja ta wuce dakin Mero da kanta ta ganta tana bacci daga ita sai dan guntun wando da vest,mamaki Jikin Mero ya bata kyau haka kamar ba Yar aiki ba,duka ta dannawa mero a cinya,ta bude Ido da sauri,Ina abincin dan uwarki? Me kika dafa nace? Mero tace nade da Mai,tsaki Ihsan ta ja tace Allah ya taimakeki kinyi girkin,wlh da baki dafa ba da Kinga rashin Mutunci,Mero dariya ta kamata wai Ihsan bata San mene nade da Mai ba,yunwa ce nade da Mai bata sani ba ta zaci wani lafiyyen girki ne.

Tana fita Mero ta sawa kofarta key ta koma baccinta,Kitchen Ihsan ta shiga taga tukunyar ba komai,ta buda flasks duk wayam,dining wayam,Salamatu ta kwalawa kira ta fito tana hammar yunwa,tace Ina abincin da tayi? Salamatu tace ban sani ba Hajiya,tace min ta dafa nade da mai cewar Ihsan,Salamatu ta shiga tafa hannaye tace Hajiya ai yunwa take nufi,ai in kika ji ance nade da Mai to ba komai naci yunwa ce,Ashar Ihsan ta dura ta koma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login