Showing 102001 words to 105000 words out of 108220 words

Chapter 35 - Tantiriya A Gidan Yari Book 3 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

942

tsada Leshi kana gani kasan kayan ba karya a ciki dark green an Golden ne.

Mota suka shiga driver ya kaisu har gidan Mima,Allah yasa duk sunzo Sunan Naila basu tafi ba kowa da kowa Yana gidan Mima,da yamma su Misam,Rafeeq,Arham da matayensu duk suna gidan,suna compound sai kace yau ake Sunan,Badia tazo da Anam,motar Haneef me azabar tsada ce ta shugo gidan sun zaci ma Spark ne,Sai da Mero ta fara fitowa tun daga takalminta da komai na jikinta abin a kalla ne,ba Wanda ya ganeta har takaraso gabansu tayi Sallama suka amsa,tace Mima sai lokacin Maman Rafeeq tace wace haka kamar Mero Yar aikin Maman Spark,Mero tace nice tana murmushi,Mima tace Mero kece haka ai badan kinyi magana ba babu me gane ki,suka hau mamaki,kowa sai da ya kalle ta,tace dama da mijina muke munzo Abuja ne nace bari muzo mu gaisa,Mima tace to ya fito mana ku shugo ciki sannunku da zuwa,oh Ashe kinyi aure ba sanarwa,Mero tace abin ne ba shiri shi yasa.

Arham harda gulma kasa kasa ta furta Mero Yar aikin Mama mutuniyar Spark,Rafeeq yace ni naga dare Daya Allah kan yi bature yau,shi yasa aka ce ko ya mutum yake baka San me Allah zaiyi ba karka wulakanta shi amma su Mama basa ji,Arham yace ei kamar Mamanka wulakantani da take akan Ina soyayya Baki San me Allah yayi ba wlh Kinga dai Mero,dariya Maman Rafeeq tayi tace Dan banza ai Kai sai gyaran Allah.
Haneef ne ya fito ya Sha gezna Yar gasken milk sai shining yake,Sai sa Ido suke yi yaran Mima,mazan ya mikawa Hannu suka gaisa matan Kuma suka gaida shi suka shiga ciki,Anam tace guy din ya hadu ita Mero Dan ubanta Ina ta samo wannan haka ikon Allah kenan daga yau na daina wulakanta Yan aikina wlh naga ishara na tuba,Arham yace kuci gaba duniya ce ai zata bi da ku,ku akan Kuna yaran General sai iskanci,ai da kunce zaku wulakanta min Basma sawa zanyi ta zazzage ku,ki duba dai Maman Spark yau suna Ina,ga Wahida sarkin bakin jini anyi bikinta tana dakin mijinta uwar tana prison,yanzu Kalli Mero dai wannan Mero da ake gani a banza ana mata kallon mahaukaciya ce ma.

Basu dade ba suka fito suka musu sallama suka bar su da Cece kuce,gidan Spark suka je,Naila ta gama gyara kayan gift da komai Baki duk sun tafi har su Zarah sun tafi sabo da makaranta,Naman Sunan ma tace sai dai gobe a Kai musu,masu aiki suna ta soya nama a can compound sabo da sa ne da raguna biyu kamar me layya,Naila tana Palo ita da Goggo Sai taji sallama ta amsa,Mero ce ta shugo,Naila ta ganeta ita" tace Mero kece? Mero tayi murmushi ta shugo tace nice ta durkusa ta gaida Goggo,ta zauna suka gaisa da Naila tace ke Yar gari Ashe haihuwa kika yi? Naila tayi dariya tace ae jiya aka yi suna Mima ce ta fada min da naje,Allah ka sa Nima na sauka lafiya haka,Allah ya raya,Naila tace kema naga kamar kina da cikin Ashe da gaske ne,wai yaushe kika yi auren ba sanarwa? Mero tace Abu ne yazo cikin gaggawa,wlh ujula ujula aka yi auren nan,tare muke da shi ma Yana mota,Naila tace kice ya shugo mana,Mero ta fita ta shugo da Haneef,Naila taga miji rangadeden gaske,bayan sun gaisa tace bari na kira muku shi Yana nan,sama ta haura Spark Yana aiki a system tace kazo munyi Baki Mero da Angonta sun zo,Mero tab aure tayi? Naila tace har da ciki,yace ikon Allah,Naila tace zo kaga Mero ta goge me hali ta aura,Spark yace na tayata murna,ya mike suka fito,ahhhh bai zaici gogewar Mero ta Kai haka ba,mijin ma ya sanshi ashe ya Sha ganinsa a gidan yari in yaje ziyara,suka gaisa Sosai ya zauna suna ta hira,Naila ta kawo musu Abinci da lemuka sannan ta kawo musu Naman da ake soyawa a plate,suka ci kuwa sun Dade kafin su tafi, Haneef 50k ya bawa Naila suka tafi har mota Naila da Spark suka raka su,Naila tace sai mun zo muku muma inshaallah,Mero tace Allah ya kawo ku.

Wani satin Mero da Haneef sai prison wajen Maman Spark,tayi girki lafiyayye suka Kai,bayan Mama ta fito da Yar uwarta da kyar suka gane Mero,Mama ta nuna ta da yatsa tace me...me...Mero tace nice Mero da kika ce ban dace da suna Khadija ba sai dai Mero,to ga Mero Allah ya azurtata tayi sama ke Kuma gaki a wani hali,ni bazan miki abinda kika yi min ba,albarkacin naci na Sha a gidanki baki taba hanani abinci ba bazan manta da wannan Alkhairin ba,ko nama kika ci Ina ci,tace gashi ta mika mata Daya abinci da ta kawo mata,Maman Wahida ma suka gaisa suna ta mamakin ikon Allah,Azima ce tazo suka rungume da Mero sannan Mero ta bata nata abincin,Haneef harda kudi ya basu duka,sun Dan dauki lokaci sannan suka tafi,Mero tana cewa Azima ki gaida su Goje su Scola kice bazan manta da su ba,Azima tayi dariya tace zasu ji.

Naila tana yin Arba'in Spark ya dauke ta da Baby da Arham da Basma suka bar kasar suka tafi Germany,Arham sai murna yake zasu Shana,Rafeeq yaji haushi an bar Masa aikin Office a hannunsa,Misam kuwa ya biyawa Mahaifiyar Chika da Mahaifinta Makkah,ya canja musu gida me kyau.
Spark amarcinsa yake Sha kawai sai da suka kwashe watanni kamar baza su dawo ba suna zaga kasashe,suna dawowa Kuma Jauro ya biyawa Yar Inna da Abba Dolo Umrah da shi kansa Jauron da iyalansa kaf,suka tafi wai za ayi addua har su Haidar da matayen su.

Lokacin aikin hajji ya kusa Iman ta haifo Yarta mace kyakyawa,ba a Dade ba Hidaya ta haifi Danta Namiji itama,an Sha suna anyi shagali,Yar gidan Iman Sunan Maman Annoor aka sa mata tana kiranta da Nihad,ita Kuma Hidaya suna kawai danta ya ci Na'eem.
Naila da Spark,Rafeeq da Ikhy,Basma suka tafi sauke farali gaba daya Spark ne ya biya musu,Chika alkawari yayi zai biya mata dama,can suka hadu da su Abba Dolo,Abba Dolo da Yar Inna kamar Larabawa suna makale da juna.

Bayan Sallah suka dawo Mero ta Haifo Yan biyu mace da namiji kyawawan gaske kamar yaran Larabawa,kowa sai murna ake taya su,Spark ma yaje da Naila da Sha Tara ta arziki yara sunansu Nawwar da Nawwara ,su Mima sun je,Mufee da matar Kamal ma da yaron cikinsu.
Sai da Basma ta Shekara biyu sannan ta samu ciki,Arham ana ta murna da kamar baza ta haihu ba itama, lokacin su Chika ma yaransu sun fara tafiya dagwai dagwai,na Naila Yana Rarrafe ko Ina,ga matar Kamal ta haihu itama

Rayuwa na ja kowanne suna zamansu lafiya sai sabani Wanda ya zama dole da sauran kaddarorin rayuwa domin bawa baya zama babu kaddara da jarabawar rayuwa,cikin Basma ya tsufa itama gida ya dauke ta suka koma gaban Mima,satinta biyu a gidan da tsakar rana ta fara nakuda Arham Yana wajen aiki,Mima Bata fada Masa har suka Kai Basma asibiti ta haifo yarta mace kyakyawa,duk ba a fadawa mutane ba sai yamma likis aka sallamo su,tazo ma tayi wanka aka yiwa jaririya wanka suka shirya tsaf ta gwada bashi nono,Arham sai wajen dare yazo gidan ganin matarsa yaya take,Mima ya gani yace Basma fa ya jikin nata? Mima tace tana daki shiga mana ka ganta,Yana shiga ya ganta da jariri a hannu tana cin Abinci,Arham yace wai haihuwa kika yi? tana dariya tace gashi ka gani kuma,ya dafe kirji yace wayyo dadi, Alhmdllh Alhmdllh,Mima tana jinsa Yana hauka iri iri,na zama Daddy wannan yarinyar zata ga muzurai ince ke shiga gida,dariya Basma tayi tace ni Kuma nace wato baza ki shirya ki tafi school din ba sai kin makara wannan yarinya Allah ya shirye ki bari na fadawa Daddy,sai na kwala ma kira Daddy Daddy,Arham harda kausasa Murya na'am lafiya,ka zo taki ta shiryawa ta tafi school,sai na fito na mata wani kallo tuni Zata kama gabanta,dariya suka yi sannan ya zauna ya dauke ta yace a'a Kai nayi 'ya kuma
ni,Anya zan iya bacci ma,Basma tana ta dariya,Mima ta sanarwa dangi da kowa.
Su Arham sunga jama'a kullum cika akeyi yayye da sauran dangi da abokan arziki,ranar suna yarinya taci Sunan Mima suna kiranta da little Mima,Mima an Maida sunanta sai farin ciki take yi sosai yarinya tana gani gata,Papa yace matarsa guda ai sai abinda take so a duniya.

Azima kuwa ta Jikin katanga ta fadawa su Scola sakon Mero har yanda tayi kyau da Wanda ta aura,Goje yace mu dai mun shiga uku ko wacce muka Shaku da ita sai ta bar gidan yari ta auri me kudi daga yau baza mu sake kula ko wacce ba duk kuje Yan iska Shegu,'ya'yan mutanen banza ,kana shakuwa da mace sai kaji fit ta fice tayi aurenta,Dan Indo yace abin bakin cikin ma sai kaji Dan prison ne,yanzu dai ji Tantiriya da wannan Dan iskan Spark shege Dan giya,Scola suka sheke da dariya yace Spark dinne Dan giya? Da mene idan ba Dan giya ba Yana magana Yana lumshe Ido kamar zaiyi bacci in ba giya yake Sha ba ubansa Soja yake Sha? Marar neman Albarka,suna ta dariya Scola yace kaji ance ta haihu ma Naila,Dan Indo yace ta haihu? aka ce tsohon zance yace a gidan yari a Nan ya mata ciki,da abinta ta shiga gidansa,daga Dan auren har ta haihu a nan yayi mata ciki karya suke,scola suka dinga dariya da ihu,Dan Indo yace ana kallonta a namiji Ashe shi harka kawai yake Kwasa Allah wadaran Spark kaji, ban taba ganin Dan iskan yaro ba irinsa,suna ta dariya,Malam Jilani Yana zaune yace wallahi Haramun kake aikatawa ranar lahira wlh sai ka Bada shedar abinda ka fada an rubuta,Dan Indo yace Kai rufe mana baki munafukai duk ba da ku aka hada baki ba,Kun fake da karatu,kasan kana fadar gaskiya kazo ka fada mana macece tun farko mana,sai anyi magana ka makale Murya kamar zaka yi amai wai ke Balarabe munga Sudais da Shuriem ma karewa,gashi Nan sauran Yan uwanka malamai sun fita sun barka,su Malam Garzali Kai kana Nan sai ka Kara wata uku sabo da bakin hali,Malam Jilani yace Kai yaushe zaka fita? Kai da aka yanke Maka hukuncin daurin rai da rai,shuru suka yi Dan Indo Yana Jan Kwafa.

Abba da Yar Innar sa suna zaman su lafiya,sana'arsa sai yaga dama ma yake yinta yau rana tana takewa ya gudo gida yayi kwanciyarsa,yaki fita sai Aslam ne ya zauna a shagon ya siyar, Yar Inna tace baza ka fita ba kenan? Yace bazan siyar ba na gaji Wanda ya dogara Dani ma a unguwa ya dogara da aikin banza,in zai kama me sana'ar arziki ya kama ya dinga siyen kayan masarufinsa a can,ni na gaji da auna hatsi nauyin tsiya,sai ka jawo buhu ga nauyi ka zuba a daro,wajen kamfatowar ma ba arziki sai nauyi duk kasusuwana sun fara budewa,sai damatsa nake ajiyewa sai kace Dan dambe,Yar Inna tayi dariya kamar me tace Ina kaga wasu damatsa,in ma kayi damatsa ai haka ake so,ke Yar Inna ki rage budurwar zuciya so kike Naila da Hidaya na auren masu damatsa kema kice irinsa kike so na koma,shi yasa wato naga kin yarda da sana'ar lokaci guda,Yar Inna tace Allah ya kiyaye Kai yanzu ko Gym kake zuwa Ina zaka tara damatsa,Abba ya kwanta ya mimmike yace wayyo Hashimu kwanta ka huta.

Annoor da Iman dinsa suna joint na Shan Ice cream da shawarma,aka kawo musu suna zaune,Baby tana cinyarta ya shiga bawa Iman a Baki tana ci suna hirarsu ta masoya,Ice cream din yake bata tana Sha,sai wani ya fado fuskar yarsu har da rige rigen lashewa a fuskar yarinyar,ya riga Iman lashewa,hannun ta doke tana shagwaba tace ka min wayo Allah dariya yayi yace ni da 'yata kin tsaya kina yanga,wajen kida na tashi harda rawa da hanu Yana bata tana cin shawarma abinsu sharr.
Nabeel tare da Hidaya suna gidan Haidar,Haidar dinma Yana Nan suna ta hira abin su a gidan suka yini.
Su Nabeela ma sun haihu suna zaman su lafiya da mazajen su suna zumuncinsu.

Mero tana Jikin mijinta a bedroom suna hutawa,tace wai Ina Yar uwarka Ihsan ne?yayi murmushi yace tana Nan Kano tana aikinta ta rasa mijin aure har yanzu,ita Kuma auren take so yanzu hankalinta ya dawo jikinta amma ta rasa mijin,taje Adamawa ta dade ta dade ko zata dace amma Ina,ta dawo Kano duk yawan Al'ummar Kano ta rasa mashinshini duk ta rame to karshe dai abokina Yana sonta yanzu zo Kiga murna zai Kara ta biyu da ita,Mero tace maganin marar hankali kenan duniya makaranta,shi yasa in mutum yace shi duniya ya sa a gaba to zai ga duniya,dariya suka yi yace Allah ya kyauta ya raba mu da aikin dana sani ya ja musu Bargo suka shike suka fara soyewa.

Spark kuwa Naila tana samun hutu ya dauke ta suka bar kasar tare da Baby dinsu,suna jirgi suna daukan pics cike da nishadi,Baby Yana ta kiriniya gwanin sha'awa,Naila wata ta Gani a jirgi babbar mace tace Dan Allah dauke mu ta bata wayar matar ta dauke su pics da videos sunyi kyau,Naila tace Kalli yanda muka yi kyau ya Kalli pics din ya mata rada a matse nake Baby uwar Baby matar Baby ta Baby da Babynta Kuma gata Baby itama muna sauka a bani bado,dariya tayi tace Ina Jin wannan kirarin nasan me ake so dai, yayi dariya Yana tuna masifar Naila lokacin tana da ciki ya dinga dariya Yana tuna mata itama dariyar take,tace wlh in na tuna dariya nake yi,Kunnenta ya ciza kadan sannan yace Allah ya barmu tare,tace Ameen Baby Mijin Baby Baban Baby,dariya suka yace Ameen Ameen Allah yasa ko wata na Gani idan zanje zance nayi makuwa nayi batan kai na dawo gida wajenki,Naila ta sheke da dariya tare da furta Ameen.

INA BAWA FANS DINA HAKURI BISA MATSALA DA AKA SAMU A WAJEN POSTING.

WANNAN LITTAFIN NA SAMU MATSALAR TYPING WLH BAN YI SHI CIKIN DADI BA,SABO DA YAZO MIN A BANI DA LAFIYA,GA ZUWA ASIBITI LOKACIN DA AKA SHIGA BOOK2 HAR KUSAN FARKON BOOK3,A BOOK3 KUMA UZURI YA SHIGO MIN DA YAWA BA ZATO WANDA YA JAWO DELAY DA YAWA A LITTAFIN,BAN JI DADIN HAKAN BA SABO DA KOWA YA SABA BANA BOOK HAKA A DADE BA A GAMA BA SANNAN BANA FASHIN POSTING SAI DA DALILI ME KARFI,WANDA A WANNAN BOOK DIN HAR NA GAJI MA DA BADA UZURI,BANA FATA NA SAKE TYPING ME DELAY HAKA,NI KAINA BANA JIN DADI WLH AMMA DUK DA HAKA
ALHMDLLH

INA GODIYA GA ALLAH DA YA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFI LAFIYA DA NI DA MASOYA WANNAN LITTAFIN TANTIRIYA A GIDAN YARI.

INA MIKA GODIYA TA GA DUKKAN WANDA SUKA SIYI LITTAFIN NAN MAZA DA MATA,SUKA SA KUDIN SU SUKA SIYA INA MATUKAR GODIYA ALLAH YA BIYA MUKU BUKATUNKU BAKI DAYA,ALLAH YA YANTA KU CIKIN YANTATTUN BAYINSA A WANNAN WATA MAI ALBARKA DA ZAMU SHIGA.
CIKIN SAURI NA KARASA WANNAN LITTAFI KASANCEWAR AZUMI YAZO WATAN IBADA.

WANDA SUKA JAJIRCE DA YI MIN SHARHI KO YAUSHE HAR MUKA GAMA NOVEL DIN NAN WLH BAN SAN MA DA BAKIN DA ZAN GODE MUKU BA MUSAMMAN

BABY AK
AMINA YUSUF BAWALE
HAJJORA INVESTMENT
MURJANATU ABU NA BANGA
DA DAI SAURAN SU INA GODIYA.

SANNAN WANDA SUKA JAJIRCE MA FARKO HAR AKA YI NISA UZURI YA SHUGO MUSU INA GODIYA,DA SAURAN WANDA BASU SHARHI BA KUMA INA KAUNAR KU NA GODE MATUKA.
MASU JIRAN COMPLT KUMA DA KUKE GEFE NA GODE.
ALLAH YASA MUYI IBADA KARBABBIYA.
ALLAH YA BAMU LAFIYA ME DORARRIYA ME AMFANI BAKI DAYAN MU

INA YIWA KOWA FATAN ALKHAIRI MASOYA.






AsmaBaffa
[3/10, 12:24 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI

BOOK 3
~TAIMAKO~


91-100

Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM



PAGE NAKU NE.
Oufadi
Raliyaisah615





Spark ya kashe kudi na kirki Naila kaya masu tsada kamar me hada lefe haka ya mata su gaba daya ta zabe kayanta wasu duk ta cire kwance da marasa karfi Dake kusa da gidan Abba,da wasu na kauye gaba daya ma duk ta ware musu za a tafi musu da shi,ga gift kala kala tun kafin suna ana ta kawo mata,ko Kamal kayan da ya kawo na jariri ba a magana, saura kwana biyu suna Hidaya,Iman,Mufee,Beauty,Zarah da Aslam duk suka zo sai su Tani daga kauye,Spark ya kama musu Event center suje can suyi taron suna ba a gida ba,har anko su Chika suka yi.
Naila anje gyaran gashi saloon an Sha uban lalle me kyau kamar Amarya,haka su Ikhy ma.
duk sun gama shirya komai abinsu sai 12am ta shugo bedroom din Spark tayi wanka tayi Shirin bacci,yace ki kwashe kayan Nan na jariri da naki sun cike min bed,tace na gaji Allah ta fara kwashewa ya tayata suka Adana ta canja sabon bedsheet ta gyara bed din sannan ya Sha shayin na'a na'a ya kwanta tana gama shafa turaruka masu kamshi na musamman,Spark Yana kallonta sai kace maye,Juyowa tayi taga ita yake kallo,dariya ya bata ta murmusa yace nifa kyawun naki sai mamaki yake Kara bani zo mu kwanta,light ta kashe musu Baby Yana ta baccinsa a bed,Spark ya shigar da ita jikinsa,yace Hallare agaji take nema a taimaka mata ko da mouth ne,Bata Masa musu ba haka ta murje mijinta tass ta jiyar da shi dadi ba tare da anyi wani sex ba ta gamsar da shi.
Washe gari suna ba Wanda yazo gidan Naila a masallaci aka radawa yaro Ahmad,Papa yace kawai a dinga ce Masa Muhammad kar a canja Masa wani suna tunda shi da Ahmad aka sanshi,amma duk da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login