Showing 3001 words to 6000 words out of 108220 words
Chapter 2 - Tantiriya A Gidan Yari Book 3 Complete Hausa Novel
cika da Yan Uwa su Chika,Ikhram duk sunzo,Naila ita barin ma sai murna take kamar wacce ta haihu,sai dare daga Chika sai Ikhram a gidan,Naila tana tsakiyar bed suna ta hira Spark ya shugo bedroom din,zama yayi a gefen Naila ya kalleta dariya ta bashi yanda take faman murna tayi bari,Chika tace wai korar mu zaka yi ne ai ka jira mu tafi kana babban Yaya Sam baka yin yayan Kai,Spark yace wai Yaya manya da wa zanyi wani Yaya wannan Dan iskan mijin naki da ya fini duniyanci,Arham ne ya shugo yace Chika ance ku fito na kaiku gida,Aunty ya Jikin? Naila tace Alhmdllh da sauki,Spark ya kalla yace Yaya Allah kawo wani da wuri,Spark yace a'a ba yanzu ba ai yanzu sabon Ango zan dawo,Naila ta zaro ido,Chika tana jinsu tace Kai Arham dan Allah muje"tafiya suka yi,Naila tace bari nayi wanka Yau bacci har da makara,Murmushi Spark yayi tare da furta zaki murmure ne dole na kwalbe,Naila yau dai bani da amfani ba mamora a jikina sai ayi hakuri Kuma,Spark yayi murmushi kawai.
Annoor kuwa Iman tunda ya samu ta dawo sai da ya lallabata da asuba ya sake Kwalbewa,Iman duk tayi zuru zuru da ita,abinci ma sai daga gida ake kawo musu ai kuwa ta Sha Allurai shine samun saukinta ma.
Iman yini tayi a kwance Bata iya tafiyar kirki sai zuwa yamma da ta Dan ji sauki,mayen Yana gefenta kamar zai cinyeta tace zan danyi tafiya dan Allah ko naji sauki,Annoor ya mike Yana murmushi abinsa shi duniya sabuwa,hannayenta ya rike a hankali ya mikar da ita tsaye harda cewa sama da ikon Allah,dariya ta fara tana dukan damtsensa Shima dariya yake cike shaukin so,ya riketa Yana koya mata tafiya a hankali,Hannu ta yarfe tana cije lips yace daure,ture shi tayi tana murmushi ya fada Saman bed,fadowa tayi kansa tare da sakin Kara,yace sorry tashi aci gaba ya sake riketa suna tafiya a hankali Yana ta faman tsokanarta,yace wai Ina Sunan da kika Sa min na love kin daina fada yanzu,Iman tace ai yanzu ranka ya dade kake wa zai ja da Kai,me gida ran gida baki aka fiku ba aiki ba,kune gaba da mu,yace wash Annoor ka kashe ni,murmushi tayi tace ka daina please,gwara ma ki bar fadi bazan daina ba.
Bangaren Nabeel kuwa shi jinyar Yar matarsa yake sosai kuda baya so ya taba ta,sai bakinta da ya bude sosai tun a ranar surutunta ya baci bata shuru Hidaya,ita first night din kamar an bude mata baki.
Naila ce ta kira Umma ta sanar mata tayi bari,Kubra tace Allah ya sawake ya kiyaye gaba,tace Ina Abba? Zaraf Abba yace gani Ina jinki bari kika yi Ashe to Alhmdllh yafi babu akan ace ko bari bata taba yi ba gwara ace ta taba bari ai Kinga ana sa rai,Naila tace hakane Abba kamar Dan kadangare,Abba yace ke Zubaina sati hudu ai jini ne Ina ya zama kamar kadangare din,Naila tayi dariya tace ai a haka na gane,Abba yace a'a ba da bane gaskiya gudan jini kika gani idonki ya rufe,Kubra tana jinsu Abba yace tunda lafiya kike ai anyi arziki duk wata karya ki ajiye abarki gefe Naila Allah ya baki wani ni kaina na matsu naga kin min jika wlh ki dage tun kafin Dara taci gida na fara miki gori da kaina don kuwa na gaji da Kara da kawaici na kusa fara gori,Naila tayi dariya tace Abba da kanka,to ni dai Kinga na haihu bare ace tunda nayi gori hakki ya kamani bazan haihu ba Nima da yarana,na kusa gajiya zan fara yi muku gori ke da mijinki,Naila tana dariya tace Abba Yana jinka.
Ta zaci Abba kunya zai ji sai yace bashi wayar ma,ta mikawa Spark Dake gefe Yana dariya Yana Jin Abba,ya karba suka gaisa, Abba yace wai Kai aiki ne yayi Maka yawa ne? ya kamata ka dauki hutu ka samu nutsuwa ance rashin hutu ma Yana hana haihuwa,na gaji da halinku ka zauna ka binciki Naila Anya ba wani Abu ta Sha ba Bata San tana da ciki ba ta gantalar da shi,Spark yace to ya mike zai bar wajen Naila ta rike shi Kam tace wlh ban yarda ba a gabana zaka gama wayar Nan ka karo volume,Spark yaki karo Volume tunda ya rage volume sai da ya gama wayarsa sannan ya kwanta abinsa a gefenta Yana tambaya yau tun safe me da me kika ci?Naila tace abincin da Kaci,wato Abba ne yace ka tambaye ni ai na gane ka.
Washe gari Abba ya bude shagonsa na kayan masarufi harda tiles yace saura katifa,takanas ya siyo katifa Yar Siririya ta Yan makaranta ya saka a can gefe kullum Yana Kai ko a zaune ko a kwance kowa in zai wuce Yana kallonsa ai ta sheka dariya shi kuwa ko a jikinsa yace kanku ake ji bazai yuwu Basir ya kashe ni ba akan Ina so gidanku a tuka tuwo sai dai idan kar a siyi Masara ta.
Rafeeq yau Mima yaje gaisarwa ya samu Arham gososo yayi matashi da cinyar Mima,Rafeeq yace Kai mene haka? Arham yace Kai kaje ka hau ta matarka mana ai kana da ita ni ka barni na hau ta Uwata ni wlh Mima da zata ci gaba da shayar Dani tsaf zan koma baya,Mima ya kalla yace Dan Allah ki Sha ruwan kaikayi su kawo,Rafeeq yayi dariya yace to ke Mima kinji danki shi yasa ya Raina ki Kinga irinta,Mima tace Kai dalla rufe min baki sanda muna talaucin mu kazo ne gudun mu kuka dinga yi sai yanzu zaka dame mu,Arham yace ai yayi mata yanzu ya daina lagawu da baki wlh da a baya ne da yanzu ya mana batsa,Dariya Rafeeq yayi yace yanzu kuwa nake batsa yaro kawai dai an daina yi a gaban ku baku da kunnen ji me kunnuwan ji tana gida,Arham yace muna ji mana me zai Hana ai mu muna Jin dadin wannan batu,Mima tashi tayi ta cire takalminta ta Kifa Rafeeq da gudu tana zage zage,Rafeeq ya shige bedroom tace zo ka tafi gidanka wlh,Mummy tana zaune tana faman kallon takadar sammacinta ta kotu,Arham ya kalleta suka hada Ido bakinsa ya danne da hannu Yana faman dariya,Mummy ta kalle shi tace Kai dan Uwarka da wa kake? Yace ba fa dake nake ba ni,wai Ina Alhaji Baseeru ne? Ina ma kin samu ciki abinki,Mummy tace Dan iska shege ba Yana can Dan wahala,kamar ni zanje bikonsa don a San ya za ayi ko wani auren nayi na fito ya sake aurena wai shi a baya ma kaddara ce dama na Masa tsufa Mamansa ce ni,Arham ya boye dariyarsa yace gaskiya bashi da mutunci duk garar da ya kwasa,Mummy tace ai ya manta,Dan Adam butulu cewar Arham,Mima ce ta fito tace kin biyewa Arham kina Hira Yana ta zurma ki wannan yaran akwai na dauka ciki tashi kaima ta fatattaki Arham Shima.
Shaheed ne ya dawo Yana shugowa tace juya kasan Inda dare yayi Maka,me nayi Kuma ni daga dawowata school fa naje,Mima tace kasan Allah wlh zan fadawa Papan ku,ka wuce part dinku kawai bana son magana,Mummy tace yawwa haba yara duk sun addabi mutane,Mima tace wlh ni da zasu samu mata ma duk a musu auren yafi min ai sun Isa,Shaheed ya fara murna Yana Shoky ahh Shoky ai bamu sani ba ni wlh a daura ma data Annabi,ko wace a bata ni sadaka 9mnths sai jikoki ta ko Ina,Junior ne kawai Bai Isa aure ba cewar Mummy,Shaheed yace ku bashi yarinya ku gani a kulle su a daki wlh sai ta haihu,Rafeeq ne ya fito yace daga zuwa gaisuwa ni ku tsaya na fice na tafi ya lallaba ta gefe ya fice,Shaheed ma ya tafi abinsa Yana murna ance za a musu aure.
Hanif Usman Dan asalin Adamawa ne,Fulani ne gaba da baya,tun Yana dan 3yrs Babansa ya rasu sai mahaifiyarsa a gabanta ya taso ya girma ta tsaya Masa yayi makaranta har masters a kalla zai Kai 33yrs,kyakyawan matashi ne na gaske,fari ne amma ba irin Kal Kal ba,Yana da dogon hanci,bakinsa dan daidai ne me kyau,hakoransa masu matukar kyau haka idanuwansa,Yana da yalwar gashi baki wuluk me kyau,shi bai cika tsayi ba Kuma dole a kira shi da dogo,komai na Hanif me kyau ne,haka gashi ko wanne sutura ya saka sai ya zuba kyau ta amshe shi,baida hayaniya sannan ba a fiye fada da shi ba kawai harkarsa yake, har Mamansa ta auri kanin babansa suka yi Yar gida,bayan Alhajin nasa Yana da mata da yaransa biyar amma duk mata ne Kuma duk an musu aure a yanzu suna da yara ma ko wacce.
Hanif tunda ya taso yake da kashin arziki Ya fara aikin gomnati Yana kasuwanci sai kasuwancin nasa yazo ya danne komai,kudin da yake samu har da na hauka ma Allah ya sa Masa Albarka,Yana da kudi matuka sosai,Business dinsa yafi karfi a Kano state a Nan ya kera gida na karshe a GRA Yana zaune shi kadai iyayensa suna Adamawa da dangi,Yana da kadarori sosai matashin me kudi ne.
A Yan uwansu Adamawa akwai wata Khairat wacce Alhaji kanin babansa ke riketa,tun tana karama Hanif yake son Khairat kamar ransa,wacce Kuma a sanadin gobara data kama gidan Umminsa wato gidan kanin babansa tayi ajalin Khairat wacce ya Sha kuka kullum a cikin damuwa yake sabo da ita.
Dalilin zuwansa prison kuwa a cikin Yan uwansa ne bangaren Umminsa mahaifiyarsa ta samu Dan gidan Yayarta wacce ta Dade da rasuwa ana ce Masa Sudeis zai Kai 25yrs ta turo shi Kano wajen Hanif akan zai koya Masa business zai Maida shi yaronsa,kaddara tasa satin Sudeis biyu aka neme shi aka rasa daga fita kasuwa ba a sake ganinsa ba,Hankalin Hanif ya tashi matuka sabo da a gidansa yaron yake zaune Kuma wajensa aka turo shi,dangin uban yaro suka ce baza su yarda ba dama Hanif Dan mafia ne kudin mafia yake da su matsafi ne,iya nema da cigiya an rasa Sudeis,Uban yaro ya Kai Kara bazai yarda Wanda aka kama Hanif aka tsare shi a prison bangaren Wanda ake tuhuma ana sauraron kararsu,Alkalin ma nasu yayi tafiya yaki dawowa shi yasa har yanzu ba a yanke hukunci ba,Yana Nan a ciki shima kamar Mero basu San zaman da suke ba.
Umminsa da Alhaji suna zuwa ko yaushe sannan Hanif abinci me tsada ake kawo Masa kullum,haka sutura da komai nasa classic ne,kana ganinsa kasan babu maganar wahala a tare da shi,shine Kuma Wanda Mero take kallo a TikTok tana sonsa.
Khadija Sani Uba Mero kenan Yar kauyen Kano ce cikin wani kauye dake Danbatta,Khadija su biyu Iyayensu suka Haifa,Khadija itace ta farko sai kaninta Muneer,Babar Khadija Bata da tausayi gata da masifa kamar me Wanda ba boka babu Malam ta mallake mijinta sai abinda tace kasancewar Sani shi wani gashi nan ne dai sanyin Hali ne da shi sai abinda aka ce da shi,duk Inda akace Yayi to Hakan zaiyi kuwa,bashi da gidan kansa,Yana kallo tana cutar da yaransa ba karatun addini bare na Boko sai talla da aikatau baya so amma bazai iya magana ba,komai tace an gama kawai.
Gashi duk Inda zata je kamar jaka sai tace sai ya rakata idan da kayan shi zai daukar mata har Inda zata je kawai umarni take bashi,Kuma shi zai fita ya Nemo,banbancinsa da su Abba Dolo shi Yana da zafin nema amma Kuma sai abinda aka ce da shi,matarsa Hajiya Jummai ta hanashi rawar gaban hantsi ga masifa,su Khadija haka suka taso suka ga tana yiwa ubansu,taci kwalarsa ta zazzage shi ba abinda zasu iya.
Yau ma gidan ya shugo ya Kai wani gero kasuwa Yana dawowa ya fito da kudin ya zube mata a gabanta yace gasu ki duba kiyi abinda ya dace ni na dauki dubu uku ciki,Baki ta bude ta ajiye tire din dake hannunta gata kyakyawa da ita sai masifa,tace ban gane ba akan wanne dalili zaka dauki dubu uku zube ka dauki dubu daya ta isheka,Muneer Yana zaune Yana cin tuwo yace haba Inna mutum da amfanin gonarsa ya siyar duk ya Baki kudin akan ya dauki dubu uku shine zaki ce bazai dauka ba,Kai rufe min baki ko nazo na taka wuyanka,Sani Wanda suke kira da Uba yace kyale a bata Muneer ba komai dubu dayan ma ta isheni" ya dauki dubu dayansa kawai ya koma dakinsa ya kwanta.
Zuwa yamma ta fito zata je gidan suna ta gama shiryawa tace Sani fito ka daukar min kayan barkar nan muje,haka ya fito ya karbi Yar ledar suka fice da yadinsa brown ishirunka maraya,ita Kuma ta Sha atamfa blue da hijab,suna tafiya suna Hira sai kace wasu matasa,abinda take so ita kenan duniya ta San ta mallake mijinta sai abinta tace,ana ta gulmar su ita kuwa tana Jin dadi,yace yaushe zamu je wajen Khadija ne? tace sai an siyar da Masarar da zata zo kwana nan,kasan kudin mota tsada rayuwa tayi tsada.
Yace ke da yarki kamar ba ke kika haife ta ba,fuska ta bata ya ja bakinsa ya tsuke Yana tsoro,nesa da ita ya matsa Yana tafiya tace dawo wannan hanyar,yace ta Nan tafi sauri mubi ta nan,to bazan bi ba ta nan nake so" haka ya dawo Inda tace suka ci gaba da tafiya.
Yau abokin Sani ya gaji ya sake dawowa har gida ya kira Sani,yace gaskiya ka canja hali abinda kake yi Sani a garin Nan bai dace ba Sam,ace mace ta Maida ka kamar Rakumi da akala wlh mu Maza bama Jin dadin Hakan Sam,ka duba yau fa wai gidan suna ka rakata,Sani fuska ya Bata yace Dan na raka matata laifi ne? Shi yasa ku mutanen kauye har kullum Jummai take fada min na fita sabgar ku baza ku waye ba,tace dama na daina kulaka nine na nace nake Maka alfarma,amma mene aibun Hakan? Ko Jummai ta fada min tace a Makkah ma haka ake yi karewar garin addini kenan haka Maza suke wa matansu,to Kai Sani Balarabe ne ko al'adarmu Daya? Koyi nake da su karku dameni Kuma duk Wanda ya zageni ko yayi gulmata da gulmar Iyalina ban yafe ba,Abokin Sani ana ce Masa Malam yace yanzu yau fa har hannu ka rike mata a titi haba yara suna kallo ba tsari,matar tawa Dan na rike mata hannu koyi nake da Larabawa ko a gaban yarana na cikina zan rike mata hannu,baya ga haka ma ba yin kaina bane itace tace na rike mata shike nan bazan yi ba sai na watsa mata kasa a Ido.
Tayi min komai na gidan ta tuka min tuwo na ci da yarana Dan kawai tace rike min hannu Sani sai na kasa sabo da ni Dan iska ne ko me? Ko a garin Fir'auna aka haife ni,karku sake shiga harkarta da iyalina,gaisawa dai mu gaisa amma Banda shiga lamarin auratayya ta,gaisuwar ma ba dole In Kuna ganin da matsala ku kyaleni,amma ni sai me Dankwali sai abinda Jummai tace yawwa.
Malam yace Allah ya ganar da Kai,yace Ameen ya shige gidansa
Yana shiga gidan ya kwashe zancen ya fadawa Jummai,Jummai tace ai na Dade da fahimtar Malam munafuki ne rabu da su makiya mahassada.
Chika tana zaune a Palonta ta mimmike Misam Yana mata tausa sabo da tana da ciki,sai langabewa take tana Nishi,Me unguwa Maman Chika da Baban Chika mahaifi ne suka zo,Chika tayi mamaki babu Sanarwa,Misam ne ya bude musu kofa suka shugo Sanyi da kamshi ya daki hancin su,Chika tana ganin Me unguwa ta hade rai tace me ya kawoka gidana,Abban Chika yace Suhailat bana son shashanci ki nutsu,Misam gaida su yayi a mutunce Yana musu sannu da zuwa.
Chika ta zauna ta hade rai ganin Me Unguwa,Mamanta ce ta kalleta ta Harareta sannan ta gaishe su ta mike taje ta kawo musu kayan Sha da ci tace kar wannan ya sake ya Sha min lemo na,Kin San Allah zan Saba miki me yasa bakya ji ne,Misam ne ya mata rada yace calm down su Abba ne fa,Abba ne yayi magana yace dama Me unguwa ne yayi nadamar abinda yayi yazo baki hakuri akan ki yafe Masa,bazan yafe Masa ba kuwa sai dai a bar shari'ar nan ayi ta a gaban Allah.
Abba ne ya share Suhailat ya Kalli Misam yace Kai nasan kana da hankali,Suhailat da kake Ganinta bata Jin magana,ni na haife ta amma nasan halinta sarai,lokacin Ina auren babarta Ashe Me Unguwa tsohon saurayin Maman Suhailat ne" to ni ban sani ba Ashe haushina yake ji na kasa shi na aure Masa budurwa,tunda na aureta ta haifi Suhailat yarta ta fari kenan muna zaune lafiya ashe me Unguwa shi kullum budurwarsa tana ransa burinsa ya kashe mata aure ta fito ya aure ta.
To bayan Suhailat ta girma ta Kai 13yrs Bata sake haihuwa ba,da ta samu ciki sai bari,Ashe Me unguwa ne yayi mata asiri ake zubar da cikin bamu sani ba,karshe da yaga dai baza ta fito ba sai ya hada baki da wani ya bashi kudi ya shiga dakin matata da dare lokacin tana kitchen ni Kuma na shiga Ina shiga na iske Kato a kan gadona na sunna a tube zigidir,kuskure na banyi bincike ba sai na saketa saki uku,ta koma gida katsina kenan Inda Me Unguwa suke dake duk unguwar su daya,da Suhailat ta tafi,cikin ikon Allah data fito shima bai aure ta ba sai ta auri wani,daga Nan ya fara Jin haushi Yana binta da sharri,ita Kuma Suhailat haushinsa take ji Yana son uwarta tunda taji Labari.
Ganin bai samu uwa ba sai ya dawo kan Suhailat tsofai tsofai wai ita yake so,tayi tayi ya daina kulata yaki,sai sharri ma da yayi mata duk abinda ya faru sai yace Suhailat tana ciki,Kullum tana wajen Yan sanda,karshen sharri wata yarinya aka tsinta a bola an mata