Showing 9001 words to 12000 words out of 108220 words

Chapter 4 - Tantiriya A Gidan Yari Book 3 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

673

hanata sakewa taje ta kawo kayan da suka kawowa Mero harda abinci take away lafiyayye,ta mika mata tace mu tafi Spark na gaji kasan ba wata cikakkiyar lafiya gare ni ba,ta kankame hannun Spark mu tafi Dan Allah,ni mu tafi,muje gida kaina ciwo,tana Jan hannunsa,haka suka yiwa Mero sallama suka tafi ya shiga mota driver ya tuka su zuwa airport.

Yanzu muficin Nan ne ya dameta a ranta da Mero ta bayar" Spark yasan baza ta kyale muficin ba" ya bata a hannunta sabo da ya huta da kishin Naila,suna zuwa gidan ta wuce da muficin bedroom dinta,kasan bed ta wulla su kawai tace shegu baza ayi fifitar ba,muna da Ac,ai tunda hannun wata ne ya saka ba me amfani da Kai har duniya ta nade, muficin ma ko kyau,in banda Maita ma irin ta sarakai mene abin so a nan,naga dai Spark ko me unguwa basu gada ba a danginsu bare ace, tsaki ta ja ta shiga safgarta.

Washe gari Spark yace Ina muficin nan mu gansu na Mero,Naila tace naga dai ko me unguwa baku gado ba wlh ba me amfani da shi a gidan nan,na Kone shi ato kaji ka sani,dariya yayi a ransa yace ki dakko min abina,Naila tace wlh akan muficin Nan in banyi yaji ba Allah ya tsine min,sai nayi yaji na tafi gidan ubana,na gaji da ci min fuska da kake yi Ina Maka Kara da alkunya baka gani,mene bani da shi Wanda Mero ta fini,harda hawaye da kuka,Spark ya bude baki yace wai ke tsakani da Allah kishin Mero kike? Ni wlh ko sunanta ka kira gaba faduwa yake bana son zancenta bana kauna ka daina min ahhhhh....har da kururuwa kamar ta zare,Spark yace,to na daina ke Naila haka kike da kishi,yanzu idan nace aure zanyi fa,baza kayi ba...baza kayi ba Inshaallah daga ni sai Kai mutu ka raba takalmin kaza daga nan har tsufa, dariya ta bawa Spark,tace ba abin dariya bane ba a dariya a sharing din Hallare wannan ba abin dariya bane,ni bana wasa da harkar kishi,ta fututtuke sai kyaleta yayi.

Yana Office Yana so ayi aiki ya tsare Rafeeq ya zauna a Office din ya sashi gaba,Rafeeq yace Abu ba Kara ba mutunci,Spark bai kulashi ba Yana ta danna wayarsa,Ikhram ce take ta faman kira,Rafeeq ya Kai hannu zai dauka Spark ya rigashi yace yi aikinka zan kular ma da ita,ai wlh gwara ka koreni na koma wajen Misam na gaji da wannan takura,ace waya ma bazan yi ba,Spark wayar ya daga yace aiki yake fa madam,Ikhram taji Muryar Spark tace a ranta Allah ya so ni banyi subutar baki ba shi yasa ba a so daga daga waya baza ka tsaya Kaji mutum bane sai ka fara sakin zance.

Gaisawa suka yi Yace Yana jinki Rafeeq din,bana ji bazan yi magana ba idan baza a bani waya ba to Yana danna system Yana magana,Dan Allah kayi aikin Nan ba a tura ba har yanzu sabo da su na shugo Office banyi niyyar fita ba,ni wlh gwara ka koma wajen Misam din ma na kawo Arham ko Shaheed better sai kace yaro da matarka da komai aiki sai an tsaya a kanka haba Rafeeq,Rafeeq yace wai ba gashi Ina yi ba,to ci gaba yau sai yamma ba hutu,sai gaf da break Ikhram ta aiko da abincin basket guda,Spark yace Inye kaga masu mata,Rafeeq yace Kai muga naka,ai kasan ana kawowa nine nace kar a kawo yau kaga ma bata Dade da yin bari ba hutawa take,to ga Abinci nan in kana ci,Spark yace ai ni duk Inda naje yanzu bana iya cin abinci da yawa sai dai kadan maganin yunwa In na koma gida banci nata ba akwai matsala hanyar lafiya a bita da shekara,Rafeeq ya dinga dariya yace tsoro kawai kake ji Yaya,Spark yace banyi kuri ba ai ta cancanta a ji tsoronta,Rafeeq ya zuba abincinsa Yana cewa Yaya Anya kuwa Ikhram ba ciki ne da ita ba,Spark yace tooooo...yanzu aka ce har ta samu ciki da na bani sabo da Allah Ina wani amarci da na ci.

Spark yace duk watannin da ka kwashe,Anfi 4mnths Ina laifi ai ka dangwali arziki,Dan tayi ciki mene a ciki ai sai tafi dadi ma kana hauka,Rafeeq yace Kai inaga ciki ne da ita Allah Kare ni bana so yanzu,baka so kaje kana kwanciya da ita, Rafeeq yace to gani ga Allah amma yau bata son kamshin kaza gobe Yalo zata ci,jibi tace wancen abincin ma ta daina ci ko ta dafa sai irin wannan ciye ciyen,ga masifar son sex,yanzu yau hakkinta ka dauka ka rikeni a Office ,Spark yace ta Nan ka bullo uban wa zaka yiwa wayo,tayi ta cikinta ba ruwana,Rafeeq yaji dukul a ransa yaso yaci nasara ya gaji,yace ka taimaka min Yaya Dan Allah,wlh ba Inda zaka sai 5pm ka gama aikinka.

Basu tashi ba sai 5pm sannan ya kyale Rafeeq,basket dinsa ya dauka ya nufi gida abinsa Yana shiga Ikhram ta tarbe shi ta rungume shi yace yau Spark ya kusa halakani yau mine,fuskarsa ta shafa tace kayi hakuri ai nema ne muje kayi wanka ka huta, daukanta yayi suka shiga bedroom,wankan ma itace ta tayashi ya gama shiryawa cikin jallabiya ruwan Zuma,tace abinci fa? Yace na koshi sai anjima ya haura Saman bed ya kwanta Yana hutawa Ikhram ta hau yi Masa tausa daga tausa ya fara bacci tace nifa ba bacci nace kayi ba,I think i need you,Rafeeq ya bude Ido a hankali yace Anya ba ciki ne da ke ba kuwa wifey, yau ya kika yi da bana nan? Ikhram tace na Sha wahala sai addua nayi,Dan Allah ka tashi muyi,Rafeeq ya zaro ido yace da kin bari nayi bacci na tashi zanfi samun nutsuwa,Ikhram tace to yi baccin zan jira,ya koma ya fara baccinsa ta tasa shi gaba kamar mayya tana ta kallonsa tana kallon agogo.

Minti talatin tana cika ta fara murna tace lokaci ya ja,tana zaune a tsakiyar gadon a gefensa tana kallonsa kwanciya tayi ta shige jikinsa tana ta Allah Allah ya tashi itama tayi baccin,har magriba ya rigata tashi ma,ya tashe ta yace lokacin Sallah yayi ya wuce masallaci,bayan ya dawo abinci ta shirya musu suka ci suka koshi sannan suka fara Kwalbewa abinsu,Ikhram yanzu bata gajiya,jinta yake kamar sabuwa ta Kara sweet shi yasa kullum sai Kara nacin masifa,ko bata nema ba sai ya kunnata bare ma kullum a cikin bukata take.
Washe gari sabo da Spark yaki kunna wayarsa bai fita ba,Spark har gida yazo daukan Rafeeq yana mota driver na tuka shi,yasa me gadi yaje yace Rafeeq ya fito,Rafeeq daga wanka ya fito ya shirya a gurguje ya fita Yana cewa a kawo Masa breakfast Office,mota ya bude ya shiga Yana fushi,Driver ya ja suka tafi.

Abba kwance yake a katifarsa ta shago Yana Jin radio,Kubra ta leko tace kaji kunya wlh ko ni mace bazan yi wannan lalacin ba,Abba yace na zaci ma zuwa kika yi ki tayani kwanciya nafi Jin dadin auna hatsi,bazan zauna a benchi ba ga zafin rana so kike cutar rana ta kamani na dinga kashin majina wlh bazan yi ba,bazan zauna a rana ba sai Rumfar kwano me shegen zafi,ke yanzu ba ci gaba bane a Ganni a killace a cikin shago amma a rumfa kowa Yana kallona tsirara iska tana bushe ni da rana,idan ana ruwan sama Yana min feshi,Nan kuwa a cikin sutura,Yar Inna ko dai kin daina so na nane ban sani ba? in kin daina kaunata ki Fadi gaskiya sai na Kara aure babu Bata lokaci,naga kwana biyu wani gani gani kike min,Kubra tace me yayi zafi daga magana daya,yace to kija baki kiyi shuru, dubu biyu nazo karba,Abba yace to ana sana'a Kuna korafi sai Kuma a baku-a baku gashi ya mika mata" ciki ta shiga ta samu buhun Masara ta zauna

Abba yace ahhhh....ta mike da sauri Dan taji tsoro ma yanda yayi yace abincin ci ne fa ki zuba Masa wannan mazaunai ai ba tsari tashi gaskiya in baza ki zauna a katifa ba ki tafi gida,Kubra tace bazan tashi ba wlh na zauna,Dan Allah ki dawo Nan Kinga Sha wuya ya nuna mata katifar da yake zaune,tace bazan dawo ba a nan zan zauna.

Abba ya kalleta harda harde kafa yace to ya soyayya ta Yaya tunanina ? Dariya Yar Inna tayi ba shiri ka fa girma ka daina irin wannan ka barwa su Mohsin,Abba yace sabo da sune mutane ni ba mutum bane soyayya ba tsoho ba yaro kowa ya ji da tasa ai bakya kunyar ciki sai soyayya,in ciki ne yanzu zaki ta amai a gaban mutane ki ta asarar abinci kici ki amai,Bai fa kamata na yafe miki ba da aure na kike tafiya wajen gardawa amma na yafe miki Dan Kinga nayi shuru da zancen Ina sane,dariya Kubra tayi tace rana tana yi bari na tafi girki zanyi,Abba yace ke rabu da girkin nan yau a siyo abincin, mu nawa ne kwata kwata a gidan zauna muyi soyayyar mu,Yar Inna tace dama na gaji wlh,Abin nema ya samu Abba yace ba shegen da zan siyarwa ko da gero ne bazan siyar ba yau tunda kika kawo min ziyara,Kubra tace a gida fa muke wannen shagon a Jikin gidanka yake Ina wata ziyara a nan,Abba yace duk da haka idan ba haka ba duk Wanda ya siyi kwano Daya biyu zan bashi,Kubra tace a'a ai gwara karka siyar ni tafiya zanyi,yace kina tafiya zan rufe na dawo gida.

Jauro ne ya kira Abba,ya daga yace hello" kana magana da Hubby,Abba yace waye Hubby? Hubbyn ubanwa kamar wani Dan Daudu ni bana Daudu Allah ya tsare ni,Jauro yace Kai dalla daraja na Kara na samu Karin suna,ai duk suna Daya in ka samu Kari to darajarka ta karu,Amaryata ce take fada min,Abba yayi dariya yace to sai aka yi me? Kai dadi kake ji nufinka? Karya take" fada tayi Dan kaji dadi wannan lokacin soyayyar an wuce lokacin ka gama abarka da Habiba tun da jajayen sawunka,itama ta gama soyayyarta da me Yalo uban Annoor ka daina murna Jauro,ni kaga nawa kowa yaji yasan ba karya a ciki Abban Mohsin Kuma ni na haifi abina akwai wani shege da ba ni ba,Abban Naila, mutane suce mijin Kubra,Yar Inna in soyayya ta Kai mata tace Dan siriri na kaga duk ba karya siririn ne ni,Kai kuwa wlh ka kiyayi Hubbyn nan da gemunka da furfura a dinga fada Maka Hubby ko dacewa baka yi da Sunan ba,ai gwara me gida ma ya fiye Maka.

Jauro yace bakin ciki kake min Hashimu na gano ka,ni ban San ma wanne kuskure ne yasa kazo a abokina ba,gaba daya abota da Kai kaddara ce ma,Hashimu yace to ya zaka yi Dani baka da kowa sai ni sai na zo cin girkin Amarya,Jauro yace Dan Allah kazo kaji dadi,Kai kaga wani Yankan salat me sifirin kamar ba hannu ne yayi ba yir yir yir indai yanka kayan lambu ne a barwa Ruhina,Abba yace ita Kuma Habiba fa mece? Jauro yace ita zuciyata ce Amarya Kuma Ruhina an barka a baya ka zauna da mace daya tilo kullum Kubra Yar Inna wai Dan Allah baka gajiya? Abba yace ka ganta tana jinka tana shagona zance tazo ma yau nace ta huta mu soye bana gajiya da abata ko? Abba ya Kalli Yar Inna,murmushi tayi tace Jauro ta Allah ba taka ba inshaallah baza a min kishiya ba,in naga dama sai na raba abotar taku,Abba yace wannan Kuma kinyi karya karki mike kafa dai ba a bawa namiji Amana Nima ba wata Amana zan rike ba ko yaushe zaki iya Jin kishiya ta taho" karki yarda dani bani da tabbas,Kubra dai tana jinsu suna ta surutu.

Misam ne ya Kai Chika asibiti daga Nan ya kaita gidansu,Kamal suka samu da Spark a kofar gida suna ta hira da tsare tsaren bikin Kamal da za ayi Nan da sati daya,Misam ya budewa Chika mota ta fito ko kula su baiyi ba ya sa Kai zai wuce,Kamal yace Amma baka da mutunci yaron nan,Misam yace to Kunga real namiji sai na tsaya Ina kula ku Kai baka da mata a kwararo kake kawai,shi Kuma wannan yayi auren Dan cikin ma ya kasa ba rashin kunyar da basu yi ba an kawo Amarya amma ni zuwa daya kawai har ta karba,Dariya Kamal yayi Chika ta gaishe su, Spark yace masu ciki gashi Nan duk kin dashe mu kuwa dama karkar muke ko da shi ba a ganewa,Misam yace wlh a'a kasan dama ba Wanda ya isa ya kirata da baka ato,matar taka fin ta wani tayi,Spark yace Allah ya baka hakuri masu Hallare da Madara,Chika tuni ta wuce ciki tana dariya, Misam yace Ina Rafeeq? Yana Office na bashi aiki yanzu ma wajensa zan koma nasan halinsa yanzu sai ya tafi gida.

Annoor yau Iman taci sa'a ya kyaleta ta kwana lafiya,suna zaune Jauro ya kira Annoor yace Ko me kuke ku bari muje asibitin mahaukata Maman Iman ance ta dawo hankalinta,Annoor yace to bai fadawa Iman ba sai yace ta shirya suje gidan mahaukata su gano mamanta,sai murna take yi ta shirya,Annoor bayan ya shirya ya saka Shadda wata sky ya zuba kyau harda dora Yar hula a Saman kitsonsa yace zanje wajen surukata tunda ta warke ai taga surukinta kamili,Kansa ya kalla a mudubi ya juyo ya Kalli Iman yace ya kika ganni? tace Kamilu Sunan wani,dariya yayi yace tambaya nake nayi kyau please? tace to Kai akwai ranar da baka kyau ma ai kullum kyau kake yi,mudubi ya sake lekawa yace wow Allah yayi kira,dariya tayi ta ture shi tace kalle ni fa,me zan saka ne ma na sutura? Yace Abaya,ai kuwa ita ta zabo wata maroon Egyptian ta saka tayi kyau sosai kamar a sace ta.

Suna kamshi suka fita shi ke driving a wata sabuwar motarsa da ya siyo,Kawu suka dauka suka tafi can.
Suna zuwa aka kaisu wani daki na daban,sannan a kirata ta fito sanye cikin riga da zani na atamfa har da Hijab,kana ganinta kasan yanzu da hankalinta,shuru tayi tana kallon su,Nurse tace gata Hajiya ki musu magana su suke zuwa dubaki,Jauro yace sannu tace yawwa Dan Allah ku su waye ku kaini gidanmu,Iman farin ciki ya kamata,Maman Iman tace ni Yar kauyen Libiya ce tallan maganin gargajiya ne ya kawo mu kasar Nan da iyayena,Jauro yace zauna Dan Allah ki nutsu ki bamu labarin naki ko zamu San Inda zamu kaiki.

Zama suka yi sannan tace sunana Rahma,Jauro yace yawwa ko kefa Rahma suna me asali,taci gaba Babana sunansa Mahmood tun Ina karama ya rasu,Mahaifiya ta ma Ina karama ta rasu a wajen kakata na girma wacce a kauye muke da zama,tana bada maganin gargajiya,tana amfani da Aljanu,kasa kasa muke zuwa,watarana muka sauka a Nigeria a Daji muke zama da dabbobin mu shanu da rakuma,akwai wani bawan Allah Dan asalin Sudan ne zai wuce Abuja ya ganmu a hanya ya tsaya ya karbi maganin haihuwa a wajen kakata,ta bashi yace Yana so na sai tace baza ta bashi ni ba ya nace a haka dai sai da yasan inda muke zaune a Daji.

Watarana yazo wajena ya samu Kakata bata Nan ya bani wani abinci me dadi da nama tunda na ci ban sake sanin Ina nake ba Ashe magani ya bani yayi amfani dani ya lalata min rayuwa,Sai da kaka ta dawo ta sameni cikin wani hali na fada mata komai amma sabo da taurin Kai Ina sonsa yana so na tace baza ta bashi ni ba,ni Kuma nace tunda Hakan ta faru ai gwara kawai ya aureni a huta,shi Kuma dan Sudan Marwan kenan yayi min haka ne Dan Kaka ta bashi ni ya aureni amma taki yarda.

Ana nan watarana na dinga kuka nace wlh sai na bishi mun gudu,tace indai na sake na bishi sai ta Sa Aljanu sun haukata ni,ban yarda ba watarana muka hada baki da shi muka gudu ya dauke ni a mota,kwana daya tsakani na fara ciwon hauka ban San Inda kaina yake ba,da kansa ya dawo dani wajenta,ranar da ya kawo ni ranar Kuma ta bawa wasu Yan fashi magani sun gwada bai musu ba suka dawo a ranar a gabana suka yiwa kaka Yankan rago suka fece,har a lokacin bana gane abubuwa da dama hankalina ya fara barin jikina,daga nan nidai ban sake sanin Inda nake ba sai yanzu da Allah yasa na warke jiya kenan.
Jauro yace iKon Allah to ko dai Marwan din Dan Sudan shine uban yarki? Tace wa? Ya nuna mata Iman ya kwashe labarin komai ya fada mata,Rahma tace ya kamanninsa suke? Jauro yace Yana da haske dogo yana da gashin Baki goshinsa da tabo,Rahma tace wlh shine masoyina nane Ina sonsa har yanzu a Abuja yake zaune cikin gari yanzu Ina zan ganshi.

Jauro yace Yan uwanki fa? tace bari tukun wannan duk suna Libiya Kuma ma duk sun tarwatse bada magani yanzu burina a Nemo min Baban wannan da kuka ce Yata ce,yanzu wannan 'Yata ce?Jauro yace yarki ce gashi Nan Kuna kama ma,Iman sai murna take yi tace Kinga mijina surukinki ne wannan ta nuna mata Annoor, Annoor yace Ina Kwana harda kasa da Kai.

A ranar aka gama komai aka sallami Rahma suka wuce gidan Habiba aka Kai mata ita ta zauna a nan,sai Iman ake tayawa Murna.
Jauro yace Haidar ya shirya dama za aje wajen ubansa mahaifi a Abuja sai a tafi da Rahma ko za a ga uban Iman a can,Habiba tace ya kamata a bari ta murmure sai a je.

Mahaifin Annoor ya dawo daga US ya samu Yarsa Maryam tana cuta ta gaske an rasa dalili ta rame ta fike,ga wasu kuraje da suka cika mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login