Showing 33001 words to 36000 words out of 108220 words

Chapter 12 - Tantiriya A Gidan Yari Book 3 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

675

dakin Mero taji kofar gam,key din mota ta dauka ta fita kawai ta wuce eatery lafiyayye taci acan,tana cin Abinci wani matashin mutum talaka,kana ganinsa kasan sai dai rufin asirin Allah amma kyakyawa ne Siriri bai ko kama kafar Haneef a kyau ba.

zama yayi a gefen Ihsan Ganinta babu mayafin kirki bata Masa kama da matar aure ba,sannu yace mata tayi murmushi ta amsa tana cin abincinta,order yayi ta fruits salat kawai sabo da baida kudin cin abincin,kallonsa Ihsan tayi tace ya fruits kawai? Murmushi yayi yace ba komai shi nake so ma,tace a kawo Maka irin wannan rice din akwai dadi,yace bata dame ni ba ne,tace a'a Kaci mana zan sa a kawo sai na biya Maka,yace nace miki bani da kudi Hajjaju? tace nidai nace ka dandana Kaci,okay fine ya furta Yana murna a ransa yau yayi gam da katar,tasa aka kawo Masa yaci ya koshi abinsa.

Yana gamawa ya mike yace thank you Hajiya ya fice da sauri,Bai tsaya ko Ina ba sai Dan gidan da yake rabawa dakinsa me dauke da toilet da dan gado irin na gwauraye.
Murmushi Ihsan ta saki ta mike ta wuce cikin rantsatsiyar motarta.

Spark suna zuwa gidan Rafeeq a can suka samu Khalid Yana zaune a Palo tare da Rafeeq da Ikhram,Rafeeq yace ya Lagos din? Spark ne ya zauna ya hakimce Naila ta zauna a gefensa suka gaisa da Khalid da su Rafeeq,Khalid yace Lagos tana can Ina Barack a daure Ina hutawa Allah yasa ma tare da matata nake,Rafeeq ya furta har yanzu bata sake haihuwa ba? Khalid yace akan me zata haihu yanzu ana zaune lafiya,Soja in kaga Bai nemi mata ba sai kiyayewar Allah,saura kadan rannan na afka,na tuna Dan bariki Misam yanda ya kasa dainawa sai na fasa na ja abata na Maida ta ciki,Ikhram da Naila sai da ya basu kunya amma su ko a jikinsu.

Spark tunda kayi aure banji ance kayi tafiya ka bar kasar ba bare kaki fadawa mutane,da kuwa kawai sai dai aji baka kasar Kuma baza ka fadawa kowa ba,Spark yace da kenan bani da nauyin kowa Gwauro ne ni Amma yanzu ko zan tafi kafata kafar me daki,Rafeeq Yana zaune Yana Shan fruits,Ikhram tazo ta kawo musu kayan Sha da na ci,Spark yace Tantiriya ga fruits Nan,murmushi Naila tayi tace bana son sha ni yau bana son cin komai,Why? ya tambaya tace haka kawai bana so.

Yau me kika ci kwata kwata? Daga fadar haka sai taji haushin Spark wai har taji haushi nan da nan mood dinta ya canja da kyar ta daure sabo da mutane bata ce ya dameta ba,Spark tunda ya kula da haka sai ya kama kansa,bai sake yi mata magana ba,suka ci gaba da hirarsu da su Rafeeq,Nan ma sai haushi anki kulata ta mike tana cewa mu tafi gida,Ikhram tace ke Naila kalau kike kuwa? Naila tace kalau nake tunda baza a kulani ba mene amfanin zuwana,nazo kin wani share ni ke da nazo wajenki,Ikhram tace yau naga ta kaina ni yanzu duk maganar da nake miki kina shareni banji haushi ba sai ke,Naila tace eh ai Kya ce haka mana yanzu bazan sake zuwa gidanki ba,Rafeeq Ido ya zaro yace wlh da kin kyauta min ni dama Kun isheni Allah raka taki gona,Khalid dariya yayi yace madam dai yau ba kalau take ba gaskiya Spark ba haka na Santa ba,Naila ta fice tayi waje,Spark bai ce komai ba bai tashi ba bare ya bita,horn yaji tana ta yi Masa yaki fita kawai suka ji ta fice da motar tayi tafiyarta,Rafeeq yace yau kaga ta kanka Spark,dariya Spark yayi yace rabu da ita taje na koma a taxi,Khalid yace sai na saukeka a gida,ka lallashe ta Dan uwarka maybe wani abin kayi mata,Spark yace ba abinda nayi mata ni.

Naila gidan Misam ta wuce,tana zuwa tayi parking kofa ta kwankwasa,Chika ta bude kofar tace au Ashe kece shugo,Naila ta furta mu gaisa a nan wucewa zanyi fa na biyo bai ma sani ba,Chika tace bai sani ba? baki Naila ta tabe tace ai namiji ba dan goyo bane ke rabu da shi duk ya sire min ma, halin Maza ai sai su,Chika tace Spark din? Naila tace me aka yi aka yi shi dan Allah canja zance,Chika tace to da dalili ko fada kuka yi? Naila tace ko daya ni wlh da zai barni na tafi gida sai nayi wata ban dawo ba ya ishe ni,Chika tace tab shi kuwa Spark lallai ba karamin laifi yayi ba tunda Naila dai tace haka,Naila tace ai mu dai mata sai dai Allah ya saka mana abinda Maza suke mana,babu na gari duk sun kare,na gari sun kare yanzu.
Chika ta rufe baki tace ai sai hakuri Naila dama watarana dole a saba,Naila tace hakurin da nake da bawan Allah Nan ya isa,badan Ina hakuri ba Chika da yanzu zuciyata ta buga,Ki Kara hakuri kinji,ya zanyi na hadu da kaddara,sai anjima ta juya ta tafi abinta,Misam Yana Palo Yana Jin komai.

Mamaki ya kamashi yace ke Honey Anya Naila kalau take kuwa tun kwana uku da suka wuce na je gidan naga tana ta fushi,Abu kadan sai ta fara fushi ta fusata,Chika tace Ina zan sani laifin Spark ne gaskiya duk yanda aka yi,Naila haka kawai baza tayi haka ba da dalili,Spark ba abinda zai mata tab wannan yanda yake sonta kamar ransa me zai iya tsinanawa bare ya bata mata rai,Chika ta furta dan kawai dan uwanka ne shi yasa.
Misam Spark ya kira a waya yace wai me kayiwa Naila ne? Kai a Ina kaga Naila din? Yanzu tazo nan ta tafi tace badan tana hakuri da Kai ba da yanzu zuciyarta ta buga,dariya Spark yayi yace kyaleta fada take nema ni Kuma baza tayi da ni ba,Misam yace dama me zaka iya Kai kam akan Naila ai tubabbe ne.

Naila tana komawa gida tayi parking ta fito ta shiga bedroom dinta ta kwanta haka kawai ta fashe da kuka take ta faman kuka a kwance a haka Spark ya dawo ya same ta,mamaki ya kashe Spark,yace Allah ya kaimu gobe mu tafi asibiti Ina zan iya wannan abu haka,Ina ganin wannan abin ai sai na rame ai, tana jinsa tana ta kuka,a haka tayi Sallar Magriba da Isha,girkin ma taki yi sai take away ya musu ya dawo,da ya kawo ma da kyar ya lallashe ta taci,yace tashi mu tafi to mu kwanta,kafada ta makale tace naje ka taba ni bazan je ba,Spark Ido ya zaro ba shiri yace kamar wata Amarya,Au dattijuwa ce ni wato na tsufa kenan,kawai kace na tsufa,yace ba haka nake nufi ba,ni a nan zan kwana,yace to ai da nan da can duk daya,ni dai za a dameni ta furta,Wanka ta shiga ta fito tayi Shirin bacci har da saka wando tight dogo da riga t-shirt da bra da komai kar a taba ta,Spark ma Yana Shirin baccinsa ya kashe light bai kulata ba ya kwanta abinsa gwanin tausayi yau ba Kwalbewa,Ido ta bude tace haka muke bacci Kai baka iya kula da mace ba,Ina Shan wahalar aure nidai,kowacce da Mijinta lafiya ni banda ni,ta Hana Spark bacci sai korafi take Masa baya kula da ita,hakurin da nake a gidan nan shi yasa ake min wani abin,sabo da anga Ina hakuri bana cewa komai,Juyowa yayi yace taho to dan Allah idan baza ki bani komai ba ki rabu dani nayi bacci,Naila tace ai ba abin arziki kake shukawa ba ,shi yasa kasan me kake min duk zaluncin da kake min hmmm ba komai,rungume shi tayi ba riga a jikinsa,ta dinga shafa bayansa tana cewa bayan nan zaiyi dadin cizo,wlh kamar na cije ka,bayan nan naka da cizo ya dace gaba daya,ban taba kula ba sai yau,Spark tun Yana dariya marar sauti har ya saki abarsa,ci gaba tayi tana shafa bayansa tace da gani ma duk Wanda ya cijeka zai ji dadi,hakoranta ta saka na kasa tana Masa susa da su,tace dan dai zaka ji zafi ne da na gwada.

Spark yace bari ki gani dai naga kamar Kinga na kyale ki yau shi yasa,kayan jikinta ya hau cirewa tana hanawa suna kokawa sosai Naila harda kuka da cizon da yakushi baza a taba ta ba,Spark Kuma yace wlh bazan biye Miki ba,da tirje tirje da masifa da kukanta a haka Spark ya kwalbe yau yaci wahala,duk ta yakushe shi,sabo da fada yau Bata gamsu ba shi ya gamsu ta dawo Kuma tace sai anci gaba,yace ba abinda zanyi na gaji duk kin yakushe ni kin ji min rauni,ai Kaine da naci Spark naci ne da Kai baka Jin magana sai da nace bana so,to Kuma yanzu me kike nema? Ai ni ban kawo ba yau sai yanzu nake so,Yace bazan yi ba,Hallare ta gaji baza ta iya komai ba,wlh sai tayi haba haba tace baza tayi ba ai sai a tsine mata tabi duniya,please Baby,to fada min me na miki kike kuka yau kina fada da mutane me aka miki? In kin fada min shike nan,Naila tace domin Jin dadin zuciyata nayi,yace shine kika je gidan Misam kika zazzageni ko? Ka yafe min haushi naji Kuma wlh ban zageka ba nace dai baka min adalci Kuma nima ban San me yasa na fada ba ai kana min kai,Misam shine ya fada Maka sabo da gulma.

Komawa tayi jikinsa tana cewa please,Spark yace duniya sabuwa ni ai yanzu zan kwalbe kwantar da hankalinki ke da harijinki.
Washe gari Spark Yana niyyar Kai Naila Asibiti sai ya ganta ta dawo normal kamar da sai ya share yace ai mood ne dama ana samun haka,sai da yaje Office ya dawo wurin magriba ya dawo ya sameta a turbine Kuma ba mutunci.

Arham ne yayi wanka ya zuba kyau shadda yasa fara,ba karamin kyau yayi ba,ya fito Yana goge takalmi sai kamshi yake,Mima tace Ina zaka je? Yace birthday party,amma kasan abinda Papan ku yace ko baka Jin magana kenan,cewa yayi fa yau kaje kuyi zance ku fahimci juna da Basma Kuma na fada mata ta sani,wanne irin iskanci ne wannan, wani ne yasa kace a zabo Maka kana son aure,sabo da Kun Raina mutane ba a isa a fada muku kuji ba kenan,indai kana son ranka ya baci ka tafi birthday party,Arham yace a gida take fa gobe sai na nemeta,ai ba gobe yace da kai ba,ka sani Kuma,Arham hakura yayi yace shike nan kice mata tazo,'Yarka ce ni da zaka aikeni ta juya ta bar wajen,Arham yace kai sai kace wata yarinyar azo a Gani,su Mima an Mima yabi yace to a Ina zamu yi zancen? gidan ubanka sai na fada Maka,shuru yayi ya kira Mufee a waya yace Ina Basma take? tace gata Haly tana shafa mata powder, kice Ina jiranta a palon baki na sama,Mufee tace uhm Ashe zance za ayi bari muzo muga wankan,yace wlh ba ita nayi wa ba,party zanje Mima Kinga yanda take fada akan yarinyar nan,laifinka ne ai gata nan zuwa yace to ya kashe wayar ya koma palon da yace taje ya zauna Yana danna wayarsa.

Fitowa tayi tana Jin kunya tana bin Jikin bango akan an mata kwalliya yau ta sa sabuwar doguwar riga ta atamfa Mima tayi mata dinkuna kala kala,Haly har dauri tayi mata,shine take Jin kunya bata saba ba.
Bata taba yin zance ba sai yau,yanda kawayenta sukeyi ta tuna,daga ance zata yi zance shine sai kace yaje gidansu tazo tana kasa da Kai ta durkusa a gaban Arham tare da furta Ina yini,Arham yaga ta tsula kyau kamar ba ita ba,a ransa yace ashe fuskar ma abar yabawa ce ba iya gaba da baya ya dace a so ba,muryarta yaji tace Ina yini,Shima ta Yan kauyen yayi mata yace lafiya kalau kalau Alqur'an,tace an yini lafiya? Yace lafiya kalau,ya mutane gidan? Yace gaku an lafiya,tace ya....latseta yayi yace ke kin isheni da gaishe gaishe ban Saba ba,tun Ina biye Miki Ina miki Kara Abu Kuma sai Nisa yake,in kika ce Ina yini ko ka yini lafiya kawai kiyi shuru haka,tace to ai Ummati tace haka ba tarbiyya bane,yace ni a wajena tarbiyyar kenan,tace to bari na kawo Maka ruwa,Arham ya bude baki yace ni da gidanmu,ai wajena kazo,Kuma ance bakinka Annabinka yace to jeki,tashi tayi tana gyara mayafinta ta tafi taje ta dawo dauke da ruwan da lemo a faranti su Mufee suna ta boye dariyar su har leke suke yi.

Tana kawowa ta ajiye Masa ta zuba Masa lemon a cup tace kasha Dan Allah,Arham a ransa yace ubana ya zuba abu a dinga rokona na Sha karfin hali,dauka yayi ya Sha,yace ke baza ki Sha ba? tace a'a an hanamu cin Abu a gaban saurayi ance ba tsari,Arham ya Sosa gashinsa yace na shiga uku zanga rayuwa a gidana.
Yace to zauna,ta nemi kujera daban zata zauna yace a nan zaki zauna ya nuna gefensa,ta ja gefen gyalenta ta sa a baki tana wasa da shi tana Jin kunya tazo ta dan dora duwawun ta kadan a gefensa,ga kujerar 2seater yace zauna sosai,zama ta gyara,Arham a ransa yace to ni me zan ce mata ma ne,tambayar ta yayi tunda yaga ita daga Waka sai shiririta ta iya yace ya Dan maliyo maliyon naki? Murmushi ta saki tace ai acan muke yi da shallu da reriye reriye me gudu ya gudu marar gudu ya tsaya sai a buya,Arham yace hmmm sai me? Sai tirke wasa da marmari fita da hawaye Idan aka Kamaka yaro wlh duka zaka ci sai dai kaji tas tas an hada ma jini da majina,Arham yace nine yaron? da mene to Kai?,ni na taba zaton a duniya zan auri kamarka ma,ana ganinka ai an San saurin girma kayi girman birni ne da nawa zaka girmeni ma,ai tun farko da Papa ya nuna min Kai aka ce Kai zan aura tun daga lokacin gwiwa ta tayi Sanyi,da farko na zaci mijin wannan Naila dinne kaga shi shekarunsa dai dai Dani,amma sai wai aka sake cewa ba Misam bane ba Rafeeq duk sunyi aure nace Papa to suyi ta biyu dani mana,yace a'a ai Kaine tun a lokacin na rike baki nace Kaine aka ce Kaine wlh ba karamin mamaki nayi ba nace zan karba da hakuri,Arham yace 5-0 ,kin min 5-0 yafi karfin 1-0 wannan sai biyar da kan Jaki,nufinki mijin Naila ya fini kyau? Murmushi tayi tace ba kyau nake nufi ba ai kaima kyakyawa ne duk Kuna da kyau wlh Allah shekaru nake nufi,Kuma ma namiji Ina ruwansa da kyau,neman kyau a namiji ai sai dan Daudu tunda dai an min kyautar ka shike nan,Arham yace ke zaki aureni ko ni zan aure ki? Aka dai bani Sadakar ki,Basma tace wlh ba sadaka aka baka ni ba sai ka biya sadaki cab, Arham yace to ke yanzu kina so na? da kika ganni kinji kina so na? Basma tace to ni dai ban San gaskiya ba, bana ganewa Ina so bana so ni ban sani ba kawai nidai rayuwa ta nakeyi ko da Kai ko ba Kai yo zan rayu mana,babu batun in ba Kai sai rijiya wlh ba ruwana ko bakin pampo bazan tsaya ruwa ya Jikani akanka ba balle ta kaini ga fadawa rijiya guda akan ka wallahi Bada ni ba,Arham yace 20-0.

Yace to yanzu idan aka daura aure gado daya zamu dinga kwana,baki ta bude tace ni ba Yar iska bace ko babata dakinta daban dakin mijinta daban,Arham yace ke banza sai dare ya tsala take miki wayo tana tafiya,ai arcewa suke cikin sanda,Basma ta tsura Masa Ido tace babata Yar iska ce kake so kace? Yace iskancin aure ba,da bata je ba za a haife ki ne,ke wai cikin kogon dutse kike rayuwa? A karkashin dutse kike? duk iskancin mutanen kauye na zancen banza da labarin aure baki san me ake yi ba,Basma tace na sani mana ai hauka na manna Maka Kaine baka gane ba,ka gwada min iya duniyanci,mu mene bamu sani ba,mun San komai,dariya yayi yace haba? yanzu naji sanyi to me akeyi? tace ai in anyi auren Kaine Jagora Shugaba sai ka koya min ka sani a layi sai nabi,Arham a ransa yace ashe Yar duniya ce a haka kamar sakarai,yace uhm Lissafa min me miji da mata suke yi in anyi aure?

Kai ta daga sama ta rike yatsanta daya tace na daya girki,na biyu tsafta,kwalliya,gyara gida,tattausan lafazi,fari, kisisina,wankan tsarki shi yasa aka ce kar a fiye yin kitso sabo kullum sai anyi,Arham yace wa ya fada miki? Kawata ce Karima dan kaji in fada Maka da aurenta yaranta biyu tana fari da Ido tana fadawa Arham,tace uhm to Ina ji sai me? Yin wanka da ango ai Karima ma mijinta Yana cudata nidai ban dani wlh bazan iya ba ni Kam haka kawai ai sai Hawan jini na ya tashi,yace to Ina jinki,da bacci shike nan,yace bacci ma akeyi?to da Kai me zaka yi? In baka yi bacci ba me zaka yiwa wani ko gadina zaka dinga yi? Arham yaga dai Basma duk yanda ya Kai ga son iskancinsa sai ta dakko wata tashar tana ta faman raina Masa hankali,yace bacci nake ji,tun yanzu zaka tafi ko goma fa bata yi ba wlh sai na fadawa Papa nace minti biyar kayi,Arham shuru yayi ya fasa tafiya yasan sai ta iya fada ta hada Masa sharri.

Shuru yayi Yana danna waya tace kunno mana,kanta ta leko ciki,Arham ya fisge mayafin ba zato ya cire ya rike yace a gida ma sai kin fito da mayafi a Nan kike guje guje a gaban mutane,Dan Allah ka bani mayafina wlh zan fadawa Mima...ta furta da shagwaba,hannu ta Kai tana ja Yana ja,ga kwaro nan ya shigar miki riga,wayyo ta wajen Ina tana tambaya tana tattaba wuyanta,kawo na cire miki gashi ta bayanki ya furta ba wasa,ta juya da sauri yaga jela gashinta doguwa har baya an tufke yace a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login