Showing 54001 words to 57000 words out of 108220 words

Chapter 19 - Tantiriya A Gidan Yari Book 3 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

682

Kuma sai Nan da 3days zan dawo,yace ban yafe ba kwana daya na bayar gobe da wuri zanzo na dauke ki da kaina,Naila tace in kayi hakuri da kaina zan dawo,ban yarda ba Baby,kin San Allah ba wai maganar Kwalbewa ba kawai gidan babu dadi ba kowa da ma kin haihu ne sai ki bar min dana ko 'yata muna tare amma ba kowa ni kadai,Naila tana kashe Murya tace Baby,Spark yace Kai Ina Shan Baby Ina morewa wallahi,ga Baby Dan jakar uba Kato,dariya suka dinga yi su Chika sabo da suna Jin wayar me ake yi,tace dama dai kaga ka dade baka siya min komai ba,yace takalmi sabo ya fito kenan,Naila tace ba shi bane fa kamar zata yi kuka,Pleaseeeee....yace uhm Ina jinki,wani turare ne Babynka Kuma yaji kamshin yace Yana so,Spark yace a Ina yaji? Yana ciki ace yaji kamshi Yana so,komai aka tashi ace Baby ne,rannan kika ce yace a baki kudi,ni Gani ubansa idan so yake ya min magana da kansa,ki fada Masa ya sameni ni ubansa muyi magana,Ikhram suna ta dariya a boye an kure Naila,tace ai baza kaji muryarsa ba akwai wani Abu daga uwa sai da suke magana tun Yana ciki babu me Jin maganar sai uwarsa,Spark yace naji wannan karo wata,turare ne na daki Dana jiki,Dana ajiyar kaya,da na toilet etc,duk idan zan siya da dan yawa za a kashe 70k,baya fita kamshin,Spark Yana ji yace shi Dan ya bari a siya Masa ragon suna tukun,yace a yanka Masa ko bashi ne wannan yafi muhimmanci,Ina ATM din Dana baki? Naila tace na siyawa Baby kadara fili na siya Masa,Spark yace Dan Allah da gaske kike ko karya kike? Naila tace da gaske na cinye kudin Nan Amma ba kadara na siya ba,wai nawa ne kwata kwata a ciki,ni bana shanawa a gidan mijina,mene amfanin me kudin,Allah ya hore Maka dole naji dadi wannan kudi baza su dawo ba sisi bazan bayar ba na cinye,murmushi Spark yayi yace idan kin cinye ma ai kanki kika yiwa one Kobo bazan baki ba wlh,gwara na taimaki marasa karfi ke kina ci kina koshi,turare shine matsalarki,kin San ana ta kwana da yunwa wasu yanzu suna Nan suna cewa gari zai waye Ina ma a wuce gobe a tsallake ta a fada jibi sabo da wahala.

Fushi Naila tayi tace kudin ba yawa fa kasan bazan kashe su a banza ba wlh,kaima kasan da dalili,to me kika yi da su fada min,Yan uwana na kauye na taimakawa aka siya musu kayan abinci na raba musu,yace wai kuwa Ina Malam Ya'u Dan caca Wanda ya cinye ki a caca? Naila tace so nake in muka je tare ya ganka,okay idan nazo daukanki gobe sai muje can mu kwana Daya,Naila tace ai su Goggo suna Nan mu bari sai sun koma,yace to ba damuwa,yanzu dai kudin turare zan bayar? Tace ae akwai wani takalmi Shima...bazan siya ba Shima turaren Dan Yana da muhimmanci ne,Naila tace dan Allah in na dawo zan baka bado sau ba adadi,Spark yace ko Baki bani ba ai zan kwata ta karfi, kawai bana so turaren ya wuce ni ban siya ba,Beauty ce ta samo mana me siyarwa,Yace to an gode mata za a siya,Beauty ta siya ma bare ni ko million ne sai na siya miki,Naila taji dadi tana murna tace ai na sani,nifa nayi dacen miji.
Sun dade kafin su gama waya .

Washe gari da safe a masallaci kafin ma Mohsin yazo Abba yasa an radawa yaro suna Hasheem,Naila tace ai dai baza a Fadi ubanmu ba sai a samo suna a Dan makala Masa na saka Masa Ashraf ai akwai ma'ana me kyau,Chika tace ba gwara Misam ba,Beauty tace duk kunci ubanku sunansa Annoor shi nake so,ba Annoor mijin Iman ba kawai sunan ne ya min tun da dadewa Ina son Sunan shi yasa,Iman tana zuwa taji ana cewa jariri Annoor tace Annoor Dina? Beauty tace ba shi ba a wanne dalili so kawai nake na saka Masa abina,Allah ya Masa Albarka,Iman tace a kasar Nan naga alama kowa a cikin fushi yake amma sai a dinga nuna a farin ciki ake kowa pretending yake Yana yake,Ina shugowa wata mata ta dinga masifa zan take ta wai,Naila tace Goggo ce fa suna dariya,Mohsin ko zuwa gidan baiyi ba ya barwa Abba komai a hannunsa an radawa yaro suna an yanka raguna uku manya.

Sai da Beauty ta tsala wanka yazo gidan Abba yace sai yanzu kaga damar zuwa wai Kai me gida ka haihu ko,sai an jira ka nufinka?Mohsin yace to Abba gani nayi ka Isa komai a wajen shi yasa ban zo ba sai yanzu,Allah ya shiryeka Mohsin ga raguna Nan an yanka anyi komai,Kai Mohsin yanzu duk wannan ragunan na Beauty ne? Ina na sirikin Beauty? Zan fara hassada gaskiya,Mohsin dariya ya shiga yi yace ta Sanwa Siriki ko a plate ne,Allah ya kiyaye ai wlh da bazan karba ba,Allah sarki Yar Inna da kyar ta samu aka yi yanka a haihuwar Hidaya data Naila,lokacin muna tsananin babu sai babanta ne ya bamu rago,a haihuwar Hidaya,Naila kuwa Tinkiya aka yanka,Kai lokacin kana da gata an bar min gado rago biyu na yanka Maka,Mohsin yace shi yasa nake da Albarka,Abba yace ba wani nan,wlh idan Jauro Bai zo min Suna ba babu ni ba shi ko gidansa bazan sake zuwa ba naga har yanzu bai zo ba,
Annoor kuwa da shi aka rada suna a masallacin mutumin da ban sa rai ba yafi surukin nawa ma Nabeel,sai na ganshi yazo shi da Haidar,sun kyauta ai cewar Mohsin,ciki ya shiga ya gaida Umma,Naila tana zaune tana kwalliya a tsakar gida da mudubi a hannu,gaisawa suka yi ya shiga dakin me jego kasancewar Safiya ce babu mutane sai yamma.

Jauro da wuri yazo ya dauki Abba suka bar gidan suka tafi gidan Amaryar Jauro,Abba Yana zuwa yace shi yasa nake son Habiba wlh tana can ta tafi gidan Sunan jikanta amma ke kina nan gida, Jauro yace ban gane kana son Habiba ba wlh ko na rigaka mutuwa ka auri matata ban yafe Maka ba,Abba Dolo yayi dariya yace Allah sarki Habiba ba ajina bace duk matanka ba ajina a ciki,haba Jauro ai sai dai in na mutu kazo neman auren 'yar Inna Kuma wlh fatalwa zan Maka baza ka taba Jin dadi ba sai na dinga fito Maka a horror,duk Wanda na mutu ya auri Yar Inna ya gama Jin dadin duniya,bazan taba mutuwa gaba daya ba sai na dinga yin fatalwa,Jauro yace ka gaji ma ka mutu gaba daya din,yace in banda ma abinka Habiba ai Bata waye ba ko ka mutu ba abinda zanyi da Habiba sai dai na dinga kawo mata tallafin kayan abinci.
Maman Annoor abinci ta kawo musu Jauro yace munci a gidan suna Yar Inna ta zubo mana girki,ga waina ga sinasir,ga tuwo ga shinkafa dafaduka ga Soyayyar shinkafa ta Sha koron wake da yelluwar Masara,girkin da su Habiba da Maman Annoor har a koma ga rabbana baza a iya ba cewar Abba,Maman Annoor

Jauro Yana Jin Abba yace hmm wlh da zan iya daina Aboki da Kai da tafiya ta zanyi na daina kulaka kaddararren Aboki ka dame ni ka dami iyalina,Abba Yana Jin Jauro Yana surutu yace Jauro ka tuna Baffanka lokacin yana jinsa da jini a jika yace Habiba yake so,Jauro yayi dariya yace muka dinga takara muna fafatawa da Baffa akan Habiba,Abba yace an Dade ana abin kunya a duniya,Jauro yace na dinga gaba da shi nace da Habiba idan yazo zance kawai kar tayi tunanin Uba nane ta fasa Masa Kai,Ashe ya fini target ni Ina zuwa zancen yasa yaran unguwar suka Kwada min Mari yafi biyar,ranar da za'a daura aure naje na sace Habiba muka gudu,sai gashi ana rokona na dawo a daura Dani,lokacin ana tsoro kar na lalata ta,Habiba Kuma ita ga virgin me tsoron Allah,Komai aka yi Jauro ba kyau Allah ya hana,Miko min takalmi Allah ya Hana Jauro ni ba matarka bace babu kyau ka sa wata mata tayi Maka hidima,Maman Annoor tana dariya tana saurarensu.

Sai yamma likis Annoor ya biyo daga wajen aiki ya kira Iman ta fito su tafi gida,sallama ta musu,Beauty ta bata kayan suna wani cake da tarkace a cikin wata jaka me kyau,ta shiga kwalawa Naila kira..Nailan Spark.....Nailan Spark nake nema ta leka wani daki...dai dai lokacin Spark ya shugo gidan tare da Mohsin,yaji ana kwalawa Naila kira Nailan Spark,yace ko wace wannan ta iya kiran Sunan, ya furta da kansa Nailan Spark sweet name,Iman ta sake kiran sunan Nailan Spark zan tafi,Spark yace ga dai Spark din Naila,murmushi tayi suka gaisa,yace kin iya saka suna,Naila ce ta fito tace Iman wai har tafiya? Yazo fa yana waje,Naila tace to ki gaida gida muna godiya In na dawo zanzo,Allah ya kawoki Beautyn Mohsin ta shiga wanka kice na ware na gode ta juya ta fita,tana zuwa Annoor yace Ina Hidaya? tace yau ana suna gidansu ai baza mu tafi tare ba,ban gane ba Dan Allah je kice ta fito mu tafi sauke ta zanyi a gida.
Iman ta koma ta kira Hidaya tace ki taso mu tafi inji Sweet,Hidaya zata yi musu Naila tace in kin zauna uban me zaki wa wani ke ba aiki kike ba sai kwanciya, tashi ki tafi,Hidaya zata yi magana Naila ita a dole babba tace ki tashi ki tafi wlh wai wanne irin Abu ne wannan,tashi tayi kawai ta gaida Spark tace Umma na tafi,tun yanzu? to ya turo a daukeni ya zanyi Abba ya riga da ya bada ni,to ki gaida gida, ta fita suka tafi Iman tana gaban mota Hidaya tana baya suna ta hirarsu har Annoor.
Amare kuwa Nabeela da Rahma shirye shiye suke yi Abu Yana ta tahowa kusa.

Naila Shirin tafiya ta wuce tana yi,su Chika ma haka,Beauty tace Ina ma Nima a can nake tare da ku,Spark Yana wajen Umma bayan sun gaisa ya fita Yana jiran su,sallama suka yi suka tafi Zarah da ta rako Naila tace Aunty ki tafi dani,ki bari ayi hutu da kaina zanzo na dauke ki cewar Spark,Chika,Ikhram,Naila da Spark airport suka wuce,Spark ya gansu a hanya zasu jera da shi yace bazai yuwu ba kuyi gaba ku biyu ko baya ni da Baby muna tare,sai kace me mata uku sai kallona ake yi,Ikhram da Chika suka yi gaba Naila da Spark suna baya a haka suka shiga jirgi zuwa Abuja.

Mummy ce zaune tare da Yar uwarta a gidan yari tace har yanzu Spark bai zo ya duba uwarsa ba tun Ina Jin wahalar rayuwa a gidan Nan har na fara Sabawa ma,Maman Wahida tace wannan yaro baida hali,Ina gidan nan yake zuwa wajen wata banza bazai neme ni ba,danki ba Dan mutunci bane,Mummy tayi murmushi ta furta haba Yaya duk yaran Mima akwai kamar Dana?gaskiya nasan da dalili amma zaizo ne,tunda Yana min aike ai da sauki,tabe baki Maman Wahida tayi,su biyu a gidan yari basa safgar kowa sun hade kansu suyi fada su shirya ba sa kula kowa su masu kudi ne,Mummy ma tafi saukin Kai sabo da ta canja hali sosai kafin a kawo ta gidan yari,Maman Wahida kuwa har yanzu da akidarta ta kudi ita me kudi ce.

Naila suna komawa gida tace ya kamata Muje wajen Mummy har yanzu baka je ba fa,Spark Yana kwance yace Ina sane da ita bana so naje na ganta cikin damuwa ko naje na ganta a wani hali zan iya kuka,dariya Naila tayi tace Kai kuka baya Maka wahala a yanda Maza suke da karfin zuciya,kin taba ganin kuka na in banda akan Mummy? to yanzu a kaina baza kayi kuka ba kenan sai iya Mummy? Kishi kike da uwata dama ko,a'a ni na isa na hada kaina da ita ni a wa dorin dofino kunu bayan ludayi,rufa min asiri na mutu dakin uwata, akan me zan hada kaina da Iyayenka ai ko da Yan uwanka bazan hada kaina ba,ni da nake macen aure ko yaushe za a iya sakina,su kuwa fa Yan uwanka ne har abada Kuna tare,ni kuwa a gobe kace na tafi gidan ubana ya zama dole na tafi, ni dama bance na kaita ba,mu da aka auro mu a sama,ana ganin kamar taimaka mana aka yi mu gamu talakawa kullum kallon mu akeyi a taimaka mana aka yi ai,iyayen mu basu da shi,Spark tsayawa yayi Yana kallon Naila da mamaki,dakatarta yayi yace wait wait...yanzu Nan har kinyi fushi wai? daga Yar magana shike nan kin Fadi tafi Hamsim,komawa tayi jikin mudubi ta haye kan Inda ake jera kayan kwalliya tasan ba a zama a kan irinsa ba Dan kamar glass yake ai kuwa nan take ya fashe rukukus,ta tashi hankalinta sai neman masifa take, kayan ne babu Quality,ance za a min kayan daki akace ai an zuba komai gashi yanzu ko Shekara banyi ba sun fara fashewa,Spark ya kalleta kawai yace Allah ya shiryeki,tana jin haushi kamar an mata wani Abu,ficewa tayi taje kitchen ta dauki tire ta shirya abubuwan ci ta zauna a Palo tana ci,Spark ne ya ya fito ya Kalli tire din duk tarkace ne a ciki rakwacam,Bread take ci da kifi,ga Kuma Ayaba guda uku,lemon bawo Daya,ga ruwa ga lemo Mineral roba har biyu,ga Madara peak ta ruwa.

Dariya ta bashi ya Kalli tire din yace wannan duk ke kadai zaki cinye? ya dauki kifin yana cewa duk yaushe kike soya kifin Nan ne baya karewa,Dan Allah ki rage ai sai cikinki ya lalace ya dauke madarar da lemo Mineral,kuka Naila ta fara,Dana Yana so yaci Kuma baza a bashi ba,Spark yayi dariya Don Naila yanzu ta haukace sai anyi hakuri da ita,yace cikin nan fa ciwon hauka ya sa miki Naila,Ina zaki Kai wannan tarkacen kin kula shi tayi tace Ina zaka je? fita zanyi yanzu zan dawo,ba Inda zaka je ka zauna tausa zaka min waye yace kayi min cikin wato Kai kullum sai dai kayi wanka ka fita fes ni ka barni a gida da katon ciki Kai ka gama aikinka shike nan,bazai yuwu ba ayi min ciki a dinga wulakantani an gama Dani an lalatani,Spark Yana kallonta yace ai na daina fada Dake ni tunda kika cijeni rannan,idonki ya rufe kika manta nine kika cijeni sai da kika fasa min fata a ranar na tabbatar wannan yaron na cikinki ya haukata ki,ni wannan yaron ban San irinsa ba,Almajiranta zan kaishi can,Kin fasa min mudubi Baki bani hakuri ba,tsokanarta yayi,hakurin me zan baka kana da kudi ka siyo wani mana ai dama kace zaka canja furniture,ni din nace zan canja furniture? yaushe? ni nace to,ai ka canja min kafin na haihu,zo ka zauna a nan na jingina,Spark idan baiyi ba dama yasan ba son sex take ba yanzu ya shiga uku baza ta yarda ba"

Bata Jin Tausayinsa yanzu,bayanta ya Koma ya zauna tana tsakanin cinyoyinsa ta Dora bayanta a kirjinsa ta mimmike kafa a Saman kujera,tire din Yana Saman cinyarta,tace yawwa ko kaifa amma kawai sai dai ka fita,da ka fita mana na Gani,yace ni na Isa Yana dariya, ai ni gaba ta kaini Baby ki dinga sani Ina miki haka kullum,rigarta ya dage ya shigar da hannunsa ya shafa Dan cikin kamar ta fara ajiye tumbi haka yake,yace bari na fara branch a wajen Baby, sai yayi sama da hannayensa ya koma kirjinta,Naila tace ai dama baka kaunar Dan nan ba ta tashi kake ba,Spark yace Nima ba kauna ta yake ba,tunda aka same shi yake takura min tun Ina sonsa har na gaji,dariya tayi yace yanzu yau da na biye Miki da yanzu munyi fada yafi sau goma a gidan nan,na fasa mudubi kayi hakuri ai akwai kudi ka siyo wani,yace ai kayanki ne Dan mutum ya fasa abinsa ai ba damuwa,yanzu tunanin da nake ko zan samu irinsu a canja mudubin, Naila tace to ka bincika dai barna dai danka ne yayi ba ni ba,da Yana ciki yaushe ya fito yayi barna.
Suna hira Yana Murza Naila a nutse,tun bata so bata ji sosai har ta fara shiga Mood,hannayenta ta goge da tissue tace bari na wanke hannuna,tunda yaji haka yasan yayi nasara.
Hannayenta ta wanke da bakinta ta dawo ta furta Allah yasa bana karnin kifi,yace ai kece da ba ruwanki da kifi amma yanzu kullum ne sai kinci abinki,tace to ya zanyi Ina so.....bakinta ya rufe mata da nasa ya shiga tsotsa sai kace mayu duk kayan jikinsa sun tashi daga aiki sunyi mutsu mutsu,sun Dade suna Abu daya kafin ya samu shiga hanyarsa ya dinga kwasar gara a Palo, samu nutsuwa hirarsu suka dora cike da nishadi.

Mero bayan tayi Sallar Isha a zaune a Saman bed, kwanciya tayi Haneef Ya sa ta a gaba Yana danna wayarsa sai da ya gaji tace baza ka kwanta ba? Kinga gado ne? ba gado,Mero tace oh gashi mu ba arna ba bare na matsa Maka ya kenan,dariya yayi ba tare da ya kalleta ba, har bacci ya kwashe ta Yana zaune,gajiya yayi da zama kafafunsa sunyi tsami,gashi bazai iya kwanciya a kasa ba shi,ta juya baya ya matsar da ita gefe can karshe ga gado Dan karami,Mero farkawa tayi kadan tace tace wash ciwona....sorry ya furta ya tsaya Yana kallonta,sai da ta koma bacci sannan ya kwanta a haka a bed din kowannensu kamar zai fado kasa.

Juyowa Mero tayi da kyar taji ko Ina ba waje da kyar ma ta juya a Jikin mutum,idonta ta bude a hankali ta ganshi suna facing juna,murmushi tayi ta zubawa kyakyawar fuskarsa Idanuwa tana kallonsa sai da ta kalle shi son ranta tace yau Ina morewa,Dan ubanki Ihsan dawo ki sake fasa min Kasusuwa na,yatsa ta saka ta taba hancinsa ta cire hannunta da sauri,duk abinda take ba bacci yake ba Yana jinta,Mero tace fuskar gata da Dan fadinta ya kaga an Mari Haneef, marin ta gwada kamar zata sharara Masa Mari ta fasa,tace bari Muji gashin da Laushi ko karza ne ta shafa tare da lumshe Ido tace ba banza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login