Showing 57001 words to 60000 words out of 108220 words

Chapter 20 - Tantiriya A Gidan Yari Book 3 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

699

ba Yan mata suke kwarewa,idonsa ya bude da sauri Mero ta rufe nata tayi baccin karya.

Yana sani yanda zata ji yace yawwa tayi bacci,Mero da sauri ta dunkule waje daya tare da boye kirjinta wuyanta ya taba ba shiri ta bude idonta,murmushi suka sakarwa juna a haka suna kallon juna ta juya Masa baya tare da furta sai da safe,yace good night.

Washe gari Kwanan Mero daya a asibiti kawai sai ga Ihsan ta zo asibitin da kanta ganin Haneef bai kwana a gida ba,sanda ta zo ya fita siyo magani tana zuwa ta Kalli Mero a kwance Saman bed,Mero Ido ta bude yaga Ihsan ranta a hade,Ihsan tace Shegiya tsinanniya wato a Nan ya tare ya kwana a wajenki shine me jinyarki to bari na Kara rugurguza ki sai ya zauna jinyar da hujja tazo ta kama wajen da aka gyarawa Mero ta murde da hannu,Ihu Mero ta dinga tsalawa a asibiti,Ihsan ta kama Daya kafar ma ta dinga wujijjigata kamar zata cirewa Khadija kafar,Allah sarki Khadija kamar zata suma" da gudu ma'aikatan suka shugo suna rike Ihsan tare da kokarin banbare kafar Khadija a hannun Ihsan,Haneef ya dawo yaga abinda ke faruwa,Yana zuwa ya dinga zubawa Ihsan Mari har bai San iyakar su ba,amma Ihsan tace wlh ba Inda zani sai naga bayanta,Ma'aikatan ya sallama ya damki wuyan Ihsan ta fara kakari idonta ya firfito,Khadija tana kuka ta sheke da dariya me sauti taci gaba da kukanta ta sake fashewa da dariya taga ana Chaskara Ihsan,ya hadata da bango,tana Nishi tana furta a taimako,a....a...Taimaka min...Khadija Taga wani Likita ya shugo dan lukuti tace koma idan maganine na sha ciki kamar an Kifa kwarya,Likita ya rike Haneef dake faman caskara Ihsan yace mace ce fa ka shaketa tana kakari haba Sir, ya nuna Khadija yace wlh ba haka ake kishi ba,kina kallo abokiyar zamanki zai mata illa amma kiyi kuka kiyi dariya abinda kike kenan wato murna kike? Khadija tace ae murna nake ni kasan me tayi min,miji take aure shi nake aure matsayinmu Daya.
Ihsan tana hakki taci wahala fuskarta duk ta Sha Mari ta tasa tace wlh sai ka sake ni Allah ya kiyaye nayi kishi da wannan kazamar,nafi karfin zama da ita ni dama nayi saurayina ka sake ni kawai,Haneef tsaki ya ja yace ke ai mahaukaciya ce baki San me kike ba me za ayi da mace me halinki,Ihsan tace ba Inda zanje sai ka sake ni wlh ta zaro wayarta ta kira Hajji da Maman Haneef tana kuka ta fada musu ku sa danku ya sake ni na gaji da fasikancin da yake da zinace zinace,Karuwa har gida bazan iya ba,Hankalin Mama ya tashi ta zaci da gaske ne tace kiyi hakuri Ihsan gobe zanzo Inshaallah,ni ba ruwana kawai ya sake ni ya auri wacce yake so ni dama na samu wani,Mama tace a'a ban gane kin samu wani ba,da aurenki yaushe kika samu wani? Nidai a fada Masa ya sake ni auren zumunci ne ban yi na fasa kowa ya zauna da Wanda yake so tana fadar haka ta kashe wayarta.

Fitowa tayi asibitin tana sharbar kuka da kururuwa azo a taimake ni mijina ya kawo karuwarsa asibiti,Mutane da Yan zaman jinya aka taru aka cika, Ihsan tana musu bayani Yar aiki ya kawo min gida Ashe karuwarsa ce sun dade da sanin juna,bayin Allah ashe a boye dakinta yake kwana,da rana idan na tafi wajen aiki suna tare suna sabon Allah,tun suna yi a boye ya fito da shi fili,Ina zaune Yar aiki da ita yake Hira,da Yar aiki yake kallon film komai Yar aiki karshe har tayata girki yake a kitchen yanzu Bata da lafiya ya taho Yana jinyarta,ba iyayenta ba danginta babu mace shike jinya tare suke kwana ta ya bazan damu ba?

Wata mace ta dafe kirjinta da hannaye tace wannan yayi asara,ai ni tuni na dawo daga safgar Maza,basu da hali tsaf zaiyi abinda yafi haka,wata ma tace amma wannan anyi matsiyaci,wasu kuwa suka ce sai hakuri mazan duk haka suke,Mace daya ce a ciki tace to ke duk kina me? Ya kamata a bincika maybe baya sonki ya aureki,ko Kuma kece bakya abinda ya dace har ya fada wannan safgar Allah dai ya kiyaye,mazan suna ji ba Wanda ya bawa Ihsan gaskiya a Maza sai ma cewa suka yi ke dai ba matar arziki bace ba matar rufin asiri bace,da matar arziki ce baza ki iya yiwa mijinki fallasa da tijara haka ba,mene birgewarki da cinyewa,wannan halin naki yasa yake kula wata,wani yace tab wannan bashi da mata ya Kara aure kawai,idan nine sakinta zanyi cewar wani,Ihsan motarta ta ja ta ware gida ranta fes ta fashe haushinta.

Khadija da Haneef suna Jin abinda Ihsan tace da mutane,Khadija tace karka ji komai duk Wanda yayi Maka kallon banza kayi min kiss a gabansa ko uban waye na yarje Maka,dariya Haneef yayi yace banyi niyyar dariya ba fa Ina bacin rai,oh to ci gaba ke dariya koma ta furta, karka saki Ihsan Dan Allah,Haneef ya Kalli Khadija tare da sa hannunsa cikin nata yace zaki aure ni? mamaki tayi Jin abinda ya fada ba zato,tace Ina Yar aiki kalleni fa Ina ni Ina Kai me kudi, answer me" zaki aure ni? tafin hannaye tasa tare da rufe fuskarta ta furta ae,murna yayi yace na gode,su Hajji da dangina zasu iya hanawa indai ban saki Ihsan ba zasu ce bazan Kara aure ba,zanje da wasu da abokaina a daura mana aure ko basu sani ba indai Mama ta sani shike nan,ita nasan zata amince,Mero taji tayi nasara sai murna take a ranta.

Arham daga kwanciyarsa Haly ta kira Mima a waya ta fada mata, Mima tana dakin Papa tace kaga ka samu Arham da kanka kayi Masa magana wlh tun kafin a Kai yarinya ko ayi mata ma gyaran Jikin yaje ya nace mata,gaskiya in baza ka Masa magana ba a basu gidansu su tafi kawai yafi,ai ba tsari kowa yasan me ake yi,Papa yace Inshaallah wani satin za a kaita ku fara shiryata,ai kafin wani satin ya gama da ita kaje ka yi Masa magana da kanka tunda mu ya Raina mu,Papa yace muje suka fito da Mima dakin Basma Muryar Papa suka ji Yana magana Kai Arham zo Ina nemanka yanzu a part dina,Yana fadar haka ya juya suka tafi,Basma tace kaje za a Maka fada,Arham yace ni Banga amfanin wannan aure ba,na kasa gane kan wannan aure,Basma tace asiri aka yiwa su Papa da su Mima, mahassada sun mana asiri,Arham ya furta naga alama Rafeeq ne yayi min asiri naga yafi kowa bakin ciki Dani sabo da nine sakonsa kar na kamo shi,Basma tace ko Kuma Kawuna ba kana gani Sadakin nan da kyar ya bada su,Arham ya furta ba abinda bazai iya ba sabo da yaga matarsa ta tsufa nononta ya zube yayi yaushi shine yake min bakin ciki,Basma tace Kai wlh da sauranta yarinya fa ya sake aure daga baya sabo da hadama,Papa ne yayi tsawa Arham baka ji ne,Basma itama ba wasa tace gashi nan dama wayarsa ya manta Papa ta furta kamar Soja mace,Arham ya gama saka kayansa ko wandon nasa bai kulle Zip ba kamar zai fado boxers a waje ya fito,Papa kamar ya fashe da kuka sabo da rashin kunyar Arham ta gallabe shi,kallo Daya ya Masa bai sake ba,yace muje marar mutunci,dariya Arham yayi,Papa yace kace baka sonta bata da kyau ban iya zabe ba,Papa subutar baki ce na gane gaskiya,idonka Yana Gani Allah ya saka da Alkhairi Allah yasa a Kara Maka matsayi a wajen aiki,komai yayi perfect,Papa yace kar na sake ganinka a dakin Basma ko tazo dakinka Kun rufe kofa,Kai baza ka bari a kaita ba,Baka sonta fa jikinta kake so wlh in na sake ganinka kaje dakinta ko tazo Kun rufe kofa zaka yi wani Abu sai na Saba Maka,in baka son albarka ka sake zuwa ku rufe kofa ko tazo ku rufe kofa,in kana son albarka Kuma ka kiyaye taba ta,duk wata mu'amula ban hanaka ba amma banda wannan safga,indai kana so in Maka baki dan Allah ka sake azo a fada min,Arham yace har da Baki,ai Allah ne yace Dokar Allah ne wannan,to shike nan kaje ka Kuma tafi ka bani waje,Arham ya juya ya tafi Yana mamaki yace a daura ma aure ace kar kula matar ni na taba Jin haka,shike nan zanyi biyayya.

Komawa yayi wajen Basma ya bar kofar a bude,Basma tace ya barka ne? Arham yace yace yayi min Baki in na sake tabaki sannan kar na rufe kofa in muna tare sai an kaiki gidana,Basma tace har da baki? Arham yace kwarai,tace tab asiri ne,Allah ya karya shi ko waye cewar Arham,yace sabo da bakin ciki a aure ma sai an jefi mutum sai da safe ya juya ya fita,Basma ta rako shi bakin kofa tace Good Night bye ya wuce.

Yana komawa a Palo ya samu Shaheed,yace Mazaje ya aka yi ne? Arham yace uhm Papa ne yayi min baki kar na sake taba Amarya,Shaheed yace illar zama gida Daya da iyaye kenan,Basma tana ganin rayuwa zama da sirikai,Arham yace duk Maman Rafeeq ce take wannan zigar,ka kiyayi matar data kashe aurenta ta dawo,ana tausayinta ashe ita bata Tausayin kanta,Allah ya kawo mata bazawari ko irin Baseeru Kusa ne cewar Shaheed,Junior Yana jinsu yace gaskiya Papa bai kyauta ba a nan ya dace ace ya bari ka dan more,Arham yace kaima dai ka fada ni basu gane nufi na ba ma bazan yi sex da ita ba wannan in ta dinga kuka ai sai kowa ya sani Dan Tabesting a hana mutum wlh duk Wanda naji ya kirani Ango a gidan nan sai na taka Masa birki ni ba Ango bane,Arham ya zauna yana ta surutunsa kamar me.
Bangaren Basma kuwa kwanciya tayi abinta tana tunanin Arham dinta tace mutum Yana son Mijinsa a hanashi sakewa.

Washe gari Misam yazo gidan Mima Yana gidan Rafeeq yazo shima Spark ya shugo suna zaune suna hira da Maman Rafeeq"Arham ne ya fito Yana Jin Haushin kowa Yana Bata rai,Misam yace Ango Ango ka Sha Mai,Arham yace duk Wanda yasan yayi min asiri yaje ya karya abinsa tun kafin ya dawo kansa Yana magana Yana kallon Rafeeq,Papa sun min aure an hanani taba Amarya,sai kulla min tuggu ake yi a gidan Nan Kuma bakin da suke gidan nan ne suke wannan hadin,Maman Rafeeq tace ni kenan? tunda nice bakuwa a gidan nan,Arham yace Nidai ban kama suna ba Baki nace karki fadawa yayarki tazo ta tsine min,Rafeeq yace baka da hankali ka zare Arham,ni dai ba ni nayi Maka aure ba...

Basma ce ta fito sanye cikin doguwar riga fitted tayi kyau sosai,Arham ya bita da kallo Yana cewa Allah ya Kai damo ga harawa ranar kawai ku taho daukan patient zuwa asibiti,Basma ta karaso ta gaida su suka Amsa, Arham dake tsaye ta dan kalle shi ta rike hannunsa ta saki ta wuce, Maman Rafeeq tace nidai bari na tashi daga nan bazan iya Jin wannan Abu ba,Arham yace wlh yanzu na fara batsa a gidan man kowa ya gyara kunnensa ko a bani matata ko aji zancen Hallare da bado,haka kawai ba dama na kebe da iyalina na,Arham yayi Iyali inji Spark Yana dariya,Arham ya bi Basma,Misam yace Dan iskan yaro Hallare ta motsa Kai na tsorata da yaron nan Spark ya gado,Spark yace Kai baka ga iskancinka ba sai ni zaka ce ni ya gado Rafeeq ya gado,Rafeeq yace kwarai ni haka nake lafiya ce,inyi In Kara in sake yi bana gajiya haka nake,ni da naga Ikhram ma ba zaman lafiya,Spark yace tab sai kace Mima ya Kalli kofa yace kar ta jini suna dariya,Misam yace Allah yasa ta jika wlh yanzu Mima ta musulunta fada take yiwa yaranta.

Arham Yana shiga kitchen wajen Basma ya samu Mima a ciki,Mima ya kalla ya Harare shi tace Ina Nan to,yace dan Allah Mima magana zan mata,ba ruwanka da ita na fada maka ayi mutum kamar ayu wai meke damunka ne,Arham yace gado masifa ne musamman irin na kaka Zeenatu,Basma tana jinsu tace Ina so in kulaka Sunshine to kar Baki ya bika na hakura ya jiya din?Dan kadan me Albarka cewar Arham,Mima ta dakko ludayi ta biyo shi da gudu,tana dawowa wajen Basma tace ke ana so a kwato miki yanci kafin a kaiki ya fara sonki na gaskiya kina shirme,Yana nunawa jikinki yake so ke Baki fahimta,Basma tace ai duk cikin so ne a so Jikin mace ma ai so ne yanzu idan wata ce bazai taba ta ba,ni kuwa nayi Masa na birge shi,ai kune da Kun San haka Mima sai ku bari kar a daura sai ya fara so na,kina biye Masa din Yana tabaki ba dole a daura ba,nidai tausayinsa nake ji gaskiya cewar Basama,jiya ma haka yace yace sirikai sun hanashi sakewa,kice dai sirikai sun hanaki sakewa,Dan Allah ki bamu hadin Kai Basma ya fara sonki da gaskiya,Basma tace abi ta shortcut Mima yafi,zaki ga Shortcut ki sake kulashi ki gani a gidan nan ana kwatar miki yanci bakya gani.
Basma tayi shuru a ranta tace Ina naga wani yanci tunda aka yi min aure,a fili tace da dai an barshi ya karasa ragowar yancin dama babu ai Mima,Ina yanci ga macen aure,Mima Bata sake magana ba,tana kallo ta dakko sabon flask a kwali Shima zata farke,Mima tace wannan na Maman Rafeeq ne ta siyi abinta,ai bata da miji me zata yi da shi zan siya ya min kyau,Fisgewa Mima tayi ta Maida ta boye,Basma ta fito tana kuka indai ba a wannan flask ba to yau sai dai in Arham ya kwana da yunwa wlh baza ta Kai ba,Mima tace na Kai Masa da Kai na ta zuba Masa ta ba me aiki ta Kai,Arham yace Ina Basma fa kika kawo? tace baza ta kawo Maka ba sai a sabon flask,to a Bata sabon flask din mana bazan ci ba Nima a bata sabon tunda tana so,yanzu na kwace Sunan abokin Baban Naila Jauro bawan mata Nima na cancanci Sunan sai abinda mace tace wlh, Yar aiki ta koma ta fadawa Mima" tace ajiye a kitchen yunwa ai ba kanwata bace da kansa zaizo.

Mima dai Papa ta samu tace Dan Allah tunda an gama komai a bar Arham su tafi gobe a Kai Basma haka sunfi karfina tun kafin ya fara danneta a gabana,Papa yace Allah ya kaimu ni kaina naga yau ko gaishe ni bai zo ba alamar fushi yake,kyale su a kaita haka ta gane kurenta a can, washe gari Papa ya kira Arham yace babu bikin da za ayi Arham zo ka dauki matarka ka bar min gida,an hada komai ku tafi,Arham yaji dadi kamar me yace ai yanzu Safiya ce sai yamma,Papa yace a'a ta ebo kayanta ga Lefenta suna wajen Mima ku dauka ku tafi,Arham yace da safe? Ae da safen fa ku tattara ku tafi karka Kara 30mnt a gidan nan,amma ai ba fushi kayi ba ko Papa? Ba fushi nayi ba Arham ai kasan fushina tunda ka matsu ku tafi ai ya fi,yace to mun gode ayi min nasiha,Papa yace a'a ai Kuna da hankali Kun fimu sanin ya kamata wacce nasiha,Arham yace ni ba a so na kowa an Masa nasiha ban da ni ,amma ai ita dai Basma din ayi mata nasiha ta kula dani sosai,Papa yace itama tana da hankali ai,ka karasa ladanka Papa in ka barmu haka sai muce fushi kayi, amma dai ko ayi hakuri da zaman tare ai kace.

Basma da safe taji Mima tace tayi wanka ta shirya ta zabo mata sabon kaya cikin na lefe riga da skert na Leshi fari tace ki sa wannan,ta zaci unguwa zasu je ta shirya abinta sosai,Mima ta zauna dake ita uwa ce tayiwa Basma nasiha da fada na zaman aure,Basma tace wai ina zamu je ne? gidan miji za a kaiki,Basma a ranta tace sun ga haazaa,wa ya gaya muku barno gabas take,a fili tace tun yanzu za a kaini ai da yamma ake Kai Amarya,Mima tace ku yanzu za a kaiki shi zai tafi Dake daga baya zamu zo ganin gida,Basma tace to Allah ya kawo ku.
Tana fitowa ta zauna a Palo ana ta Kai kayan Lefenta mota,Mufee suna zaune suka ce Basma kin dakko shanyarki kuwa? tace na manta na gaji ne ni an kusa kaini gidan mijina ma na huta da wahala,ga Inda zanje na huta na harde kafa daya kan daya" Nan kuwa duk an dameni ,Haly tace Allah ya taimaka Basma Allah ya baki hakuri Kuma,Papa yasa aka kira Masa Basma ya mata nasiha Shima a haka ma Mima ce ta dage sai anyi amma wlh yace bazai wa Arham ba,Ita Mima ta samu Danta tayi Masa nasiha,Arham sai da yaga an bashi matarsa sannan ya kwanta a cinyar Mima yace zanyi missing dinki yau Allah ya nuna zan koma Shan abincin yara,Shekara ashirin da Yan hayaniya da yayeni,Mima ta durma masa duka ya saki Kara,ni kake fadawa haka Dan ubanka? Kishi kike? Ke kika yayeni sai dai kiyi hakuri,Mima tace sai naji bana so ka tafi,Arham yayi dariya yace ya zama dole kuwa ai namiji Dan gidan wata ne,ya mace ake cewa Yar gidan wani ce inji Mima,yace Shima namijin haka Mima tunda ai dole ya bar gidan su,tace shike nan gobe kazo da wuri na ganka,to zanzo ai ko baki ce ba ma,za a kawo muku abinci? Arham yace Papa yace an hada komai na girki idan naga normal sai tayi in baza ta iya ba Kuma an samu matsala sai na kiraki a waya,amma na rana Dana dare kar a kawo da safe dai nasan za a iya samun matsala gobe da safe akwai matsala za a iya kawowa,tace to shike nan babban magidanci,dariya yayi yace kayana kadan na eba zan dawo na tafi da wasu gobe,tace to,yace Spark Yana cewa sai Nan da 4yrs za a Kara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login