Showing 75001 words to 78000 words out of 108220 words
Chapter 26 - Tantiriya A Gidan Yari Book 3 Complete Hausa Novel
daukansa yuuu yuuuu....mota ya koma ya shiga ya kwanta a bayan mota tare da rike kansa yace da driver juya mu koma gida kaini asibiti kawai,Driver ya fyalle mota da gudu sai birni suka wuce asibiti.
Mero kuwa tun a hanya ta fara kuka tayi sauri ta fada gidan su tana zuwa ta shiga da kuka,Jummai ta gama tace awararta ta saka a faranti zata fara yankawa Mero ta shugo tabi ta kan awarar da takalmi ta taketa tace wlh yau baza ayi ciniki ba,kowa bazai zo siyen awara ba ta wuce cikin daki ta zuge jakar kayanta ta zazzage su a kasa ta fada Saman katifarta ta hau rusa kuka tana wayyoooo Haneef Ina sonkaaaaa......Allah ka Gani Ina sonsa,sai shiga Raina yake kullum.....Jummai ta fita unguwa ta dawo ta samu Mero tana kuka ga awararta kaca kaca a faranti,tace Khadija kece kika min barna haka ko kuwa wani mugun ne daga shiga makwafta in dawo shine kika yi min haka,sabo da baki da mutunci,wallahi wallahi ko ki yarda ko karki yarda Haneef Yana zuwa zansa ya Kai kudin aurenki wajen iyayenki Maza tunda Yana sonki,Khadija tace ni Abdul zan aura nace ma ya turo gobe ko jibi.
Wanne Abdul din? Abdul na gidan Magaji wanzami?Mero tace ae shi,Jummai tace idan kin aure shi Allah ya tsine min Khadija,wlh gwara na mutu,wannan Dan shaye shayen? ga talauci da me zai ci dake da wacce sana'ar? Bashi da sana'a fa,wannan kazamin ma in banda doyi me Abdul zaiyi,ki aure shi ai Kya Sha doyi kuwa,ga me kamshi Haneef wannan kamshin kadai in kina shaka a turaka Rahma ce da Ni'ima,wlh ko ni da zan iya Maida kaina budurwa da na mayar na kwace Haneef din ni ya aure ni,Mero tace a gidan nan wacce kazantar ce ba a ayi, kazanta iri iri badan yanzu ba da nake gyarawa nidai bazan auri Wanda ya lalatani ya cuce ni ba,to zanga wacce zata yarda ki aure Abdulfata din.
Abdul fata kuwa tunda Mero tace ya turo bashi da ko sisi na sigari ma ya gagare shi,ya rasa Inda zai sa kansa,akuyar Tinkiya guda biyu na babansa ya sace cikin dare ya kaisu gidan abokinsa ya ajiye washe gari zasu kai su kasuwa.
Haneef ana wucewa da shi asibiti ya kasa tashi ya fito da kafafunsa sai driver da wasu daga cikin asibitin ma'aikata aka fito da shi tare da Kai shi ciki,Driver Mama ya kira tana zaune tunda Taga kiran driver ta firgita,ta daga yace Mama muna asibiti wlh munje unguwar to ya hadu da yarinyar da yake zuwa wajenta kawai ya ganta da wani saurayin suna zance to sai ta bawa waccen saurayin dama ya Kai kudin aurenta zata aure shi,daga nan ya dawo mota tun a mota yace na kaishi asibiti,wlh muna zuwa ya kasa fitowa da kansa sai shigar shi aka yi,Yana nan ana bashi kulawa,Mama tace wanne asibitin kuke? Global health clinic,Gani Nan cewar Mama,hankalinta a tashe ta nufi asibiti.
Zuwanta ke da wuya ta samu Likita ya fito Yana cewa zaku iya shiga kuga Jikin shock ya samu saura kadan zuciyarsa ta samu matsala amma Allah ya kiyaye,Mama ta shiga tana salati,Haneef ta samu a kwance Yana bacci ta hau kuka a hankali sabo da kar ta tashe shi,Driver ta samu tace Dan Allah kula da shi dole na tafi gidan su Khadija bani address,Driver yace mama ki bari yamma tayi,Mama tace a'a kyale ni yaron nan shi kadai na Haifa duk duniya bani da kamarsa Allah ne gatana shine gatana,Driver ya bata number kuwa ta tafi garin,Bata Isa can ba sai da magriba,da tambaya aka nuna mata gidan su Khadija ta shiga,lokacin Khadija bata nan ta tafi gidan Yan uwan Mahaifinta.
Jummai tana ganin Mama taga suna yanayi da Haneef,hannu bibiyu ta karbeta a dakinta ta kawo mata ruwa da tuwon daren data kwashe,Mama Sallah ta fara gabatarwa sannan tace nasan baki sanni ba,ai nice mahaifiyar Haneef,Jummai tace ai kuwa naga kamanni, nasan kin San mene ne ya faru tsakanin Khadija da Haneef,kaddarar data fada musu,wlh sharrin shedan ne,Dan Allah ku yafe masa,Khadija nazo na bawa hakuri tayi hakuri ta yafe Masa Dan Allah,tace a sanadin wannan abin Haneef yana kwance a asibiti,Mero ce ta shugo gidan ta tsinci Mama tana cewa Haneef yazo ya samu Khadija tace wani ya turo wlh bai koma gida da lafiya ba sai asibiti aka kaishi Yana can bai San Ina yake ba,zuciyarsa ce ta samu shock saura kadan ta samu matsala Allah ya tsare,Dan Allah kuyi hakuri ku yafe Masa,Sallama Khadija tayi kamar bata ji zancen ba amma hankalinta a tashe yake.
Ciki ta shiga tace laaa Mama kece? Mama taji dadin yanda Khadija ta mata tace nice Khadija nazo baki hakuri har gida,Dan Allah ki yafewa Haneef,Khadija ta furta ai na yafe Masa ni tuni,Mama taji dadi tace na gode, Dan Allah ki aure shi Khadija,Mero tace ai ni wani nake so Mama,Dan Allah yayi hakuri,Jummai tace Kinga Maman Haneef na bashi ita rabu da ita,a kawo kudin aure wlh ko a gobe a daura indai kun kawo kudin aure da sadaki a ranar za a daura,Khadija zata yi magana Jummai tace kina magana wlh sai mun raba gari,Shuru Khadija tayi ta tashi ta fice,Mama tace kar ayi mata dole dan Allah,Kyaleta karya take tana sonsa wlh cewar Jummai,suka gama Kus Kus dinsu da Maman Haneef sannan taci tuwon kadan tace ta koshi a daren ta samu me taxi dan garin ya kawota birni drop.
Asibitin ta koma ta samu Haneef a zaune Yana cin Ayaba,farin ciki tayi ta zauna a gefensa tana tambayarsa ya jikin? yace da sauki,Yana cin Ayaba Yana Jan tsaki shi kadai,Mama tace Haneef ka kwantar da hankalinka Inshaallah gobe sai an daura Maka aure da Khadija,Haneef yasan ma bazai yuwu ba,yace hmm kawai Allah ya kaimu,ka shirya gobe da kawunka zasu zo har abokinka Isma'il ka gayyato tunda Kai naga baka fiye abokai ba,Haneef ya kalleta kawai dan bai San taje garin ba ma Kuma bata fada Masa ba.
Washe gari da safe aka sallame su Mama ta damu sai Haneef yayi shiri,cikin sababbin kayansa ya saka wata tsadajiiyar shadda fara kar,bai sa hula ba tace ai dole sai ya saka,haka ya saka ya shirya sosai ya fito a angonsa,jikinsa a sanyaye yasan tatsuniya ce,ita kuwa Mama har ta fara Shirin hada Lefen ma,Su Kawu su biyar suka iso daga Adamawa suka tafi a mota biyu har abokin Haneef Isma'il suka tafi garin su Khadija,Munnir shi ya raka su har gidan dangin Sani ubansu Wanda Jummai taje ta fada Masa Khadija ta samu miji na kirki amma taki yarda,ita ta gaji da girman Khadija a gida,zasu kawo kudin aure da sadaki kawai a daura aure.
Yace ai dama kune kuke kyaleta duk garin Nan babu sa'an Khadija Allah ya kaimu za a daura indai kin gamsu da tarbiyyarsa da Halayensa da gidan da ya taso ba matsala,Jummai tace na gamsu,sun San masifar Jummai sannan sun gaji da ganin Khadija taki aure a kauye ko wacce ana mata aure banda ita,Yan uwa ya fadawa,kowa yaji sai murna za a aurar da Khadija a daina musu gori a gari.
Washe gari tun kafin suga angwaye suka Tara mutane a masallaci ana jira,Munnir yasa Yar wankakkiyar shaddarsa ya rakasu masallacin,Haneef ji yayi kawai ana cewa ga angwaye sunzo,mamaki ya kamashi dan bai zaton hakan ba,su Kawunsa ne akan komai sune suka Bada dubu Dari biyu kudin aure sannan Kuma aka Bada sadaki dubu dari biyu Shima,Dangin Khadija suka ce yayi tsada gaskiya su a rage,Haneef yace baza a rage mata ba ai sunyi ma kadan,Isma'il Yana ta mamakin auren Haneef haka Emergency,Nan take Liman yayi Khuduba mutane suka sheda aka daura auren Khadija Sani da Haneef.
Ana gamawa Haneef yaji hankalinsa ya kwanta nutsuwa ta zo Masa,wani irin farin ciki da nishadi ne suka lullube shi,ji yayi a duniya Kam baida Matsala shi dai,yace Anya kuwa da gaske ne ba mafarki nake ba? Isma'il yace da gaske ne duk mun sheda sai mu tafi gida sai an kawo Amarya,Haneef yace ni a nan zan yini kabi su Kawu ku tafi driver na muna tare, Isma'il ya zaro ido amma Haneef shi ba komai Aboki ke sani nasa ba shi yasa Isma'il bai San komai ba akan Haneef sai kadan.
Su Kawu yabi suka tafi Haneef da driver dinsa suka je gidan Khadija,yaga ana ta shiga Allah Sanya Alkhairi yace ashe dai da gaske ne,yaro ya tura gidan yace a kira Khadija inji Angonta,Khadija tana ta kuka an daura aurenta da Haneef,tana daki ta boye kanta,itama Jummai bata nunawa mutane ita,Yaro ne ya shugo yace Khadija tazo inji Angonta Jummai tace kace gata nan,da kanta ta shiga dakin Khadija tace tashi ko na ci ubanki,Kuma wlh in Baki je ba Khadija sai na tsine miki ki tashi kije tun wuri saura ki Masa fitsara,Khadija ta tashi tana hawaye,wanka ma da kyar tayi,taki yin kwalliya ta zauna daga ita sai vest da skert na atamfa,Hijab Jilbab ta dauka har kasa dogo me hannu ta saka tana goge hawayenta Wanda ya kasa daina zuba.
Yana ganin ta fito ya sallami driver yace zan kira ka,Driver ya Kalli Khadija yace ki shiga bayan mota Yana ciki,maganar mahaifiyarta ta tuna dole ta bude motar cikin fushi ta shiga ta zauna bata Kalli Inda yake ba ta sake fashewa da kuka,Haneef ko a jikinsa shi hankali kwance,yayi murmushi tare da riko hannunta,da sauri tasa hannu ta make Masa hannu ya saki ba shiri,yace kiyi hakuri Khadija,ba laifina bane na miki dole ki aure ni, Dan Allah kiyi hakuri ya kwantar da kansa a kafadarta ta janye jikinta da sauri tana harararsa,Kyaleta yayi yace zan tafi,mota ta bude fuuuuuu ta shige gida abinta,driver ya kira suka wuce,sai bayan ya koma gida Mama ta bashi labarin yanda aka yi har aka daura Masa auren da Khadija.
Godiya ya shiga yiwa mahaifiyarsa,Mama tace to sati me zuwa za a kawo ta sai kabi komai a hankali har ta huce Nima yau zan koma gidan mijina sai munzo kawo lefe,yace mama akwai kalar kayan da nake so zan saka da Kuma dinki,ai dama komai na bar Maka ka siya da kanka abinda naga zan iya ko ya kamata zan tuna Maka yace to na gode.yau Haneef sabo da murna har da zuwa wajen abokansa ya Kai musu ziyara,Jummai Kam ta aurar da yarinya murna kawai take abinta tace in da rai sai a Ganni watarana a saudiyya ko a Ganni da yarona Munnir mun koma birni,duk Wanda ya shugo sai ta Masa zancen Inda rai da rabo sai a jini a saudiyya ko mun koma birni ma gaba daya.
Yan hassada sai tsinewa Jummai suke uwar son kudi wai Dan me kudi ya auri yarta wai zata tafi Makkah ko ta koma birni,ana ta zuzuta auren Khadija yanda tayi tsada a kauyen.
Abdul ya saci tinkiyoyin ubansa ya Kai kasuwa Yana dawowa da kudinsa zai Kai na aure yaji an daura auren Khadijansa da wani,Abdul takaici ya kamashi yace wlh sai dai in Khadija baza ta fito ba sai ya nada mata duka yayi mata tsirara a cikin mutane,Bai San Jummai ta Hana Khadija fita ba wai gyarata take yi,kullum sai ya tare hanya ko zaiga Khadija amma ba labari.
Kudin auren Khadija a ciki ake mata gyaran Jikin skin ne kawai ba a gyara ba sai taje birni.
Munnir yace na Dade da gama secondary nasan ma kwana Nan zan koma birni mijin Khadija ya sani a makaranta sannan zan zama Dan gayu Nima ya bani aikin yi itama Inna a dauke ta mu bar kauye jaraba sarakan hassada da gulma,Jummai tace Allahumma Ameen Allah ya amsa maganarka,yo ai ni nayi farar haihuwa da abani na haifi Dan Majalisar tarayya ai gwara da na haifo Khadija yanzu zaka ga tausayi da taimakon iyaye da Yan uwa,Mero sai da tayi dariya yanda gaba daya suka Dora samun arzikin su a kanta,Munnir yace shi yasa nayi ruwa nayi tsaki akan auren nan sabo da ni Inna na hango ci gabana,Inna tace kwana Nan Munnir ko a hanya aka bani awara bazan kalle ta ba bare ma naci to ballatana Kuma ace nayi ta siyarwa,to mun koma birni ma Ina zanyi awara na dai siyar da wani abin amma Banda awara.
Mero tana zaune tana jinsu tana dariya sai da suka gama tace to wannan baida Imani baya kyauta Kuma baida tausayi in zaku cire rai ma ku cire,baza mu cire ba wlh cewar Jummai.
Mima tana zaune Mufee sai waya take tana Kus Kus Kus waya ba dare ba rana da Haidar,Mima tace Kinga nifa na gaji da wannan abin wlh zan sanarwa papanku kawai Haidar ya kawo kudi bazan iya wannan masifar taki ba Mufee,ke a duniya baki da aiki sai waya,Shaheed da Junior suna zaune,Shaheed yace uhm ai gwara ayi mata auren,kina dai ji har kalan kayan da tasa ta fada Masa wlh idan pant ne a jikinta fada zata yi tace pant ne a jikinta red da bra,Yana jin haka me yayi saura sai wani abu ya darsu a ransa daga nan sai a fara zancen iskanci,Junior yana jinsu yace tab rannan ma kalar kayan bacci ta fada Masa,harda cewa bata Sa masu nauyi Ina jinta,Mima tace ya turo kawai ni wlh na gaji,yara kamar zasu kashe ni kowa da kalarsa,Maman Rafeeq ce ta dawo sai Ganinta suka yi afjajan,Mima tace ya haka ke da kika ce sai sati yau da safe a ganki kin dawo,tace uhmmm kema kin sani ai wlh ni Kam bazan sake zuwa gidan Arham ba,iskanci a gabana da kalaman banza,na fito na dawo parlo ya dakko Amaryarsa a hannu ya dawo parlon da ita wai gidansa ne baza a hanashi shanawa ba duk Inda yaga dama a nan zai kwanta da matarsa,ya dawo parlon wai a nan zasu huta,Mima tace ke wayo ya miki ya Kore ki fa" ke Kuma sai ki taho,ki nuna Masa Yar zamani ce banza sokuwa sai ki taho,Maman Rafeeq tace a'a Dan duniya ne wannan wlh baku ga abinda yake ba a gabana yake taba ta,Junior yayi dariya yace ai kune ku kyale shi sai ta ginshe shi kuka wani tafi,Mima tace wace zata ginshe shi? badai Jinina ba,Khalil ya riga kowa aure amma har yau mace bata isarsa bare Arham, dan Allah ku kyale su mana cewar Junior, Shaheed yace ku fadawa Spark ya bashi shawara watakil ya gyara,Mima tace ai Arham yace Spark ma bai iya yiwa matarsa komai ta Ina zai bashi shawara ya yarda,tsokanar su yayi kawai amma zaiji indai man to man ne,Mima tace wato mu ya raina mu ai shike nan.
Mima ta tambaya to ya Basma din? tana nan itama bankadaddiya shuru take bata korafi sai yanda yayi da ita cewar Maman Rafeeq,Mima tashi tayi ta shiga daki tare da kiran Spark,bugu biyu ya dauka tana Jin Naila ta ciki tana kuka,tace Kai naji kamar kuka?Spark yace sirikarki ce da jikanki suke kuka,Jikanki ne yace tayi kuka,ni na taba ganin ciki haka kullum sai anyi kuka,Spark yace Ina ganin ta kaina Mima,danki Yana Jin jiki a rayuwa,Jikanki Yana abinda yake so,Naila ce tayi dariya tana goge hawayenta,Mima tace maganinku dama irin wannan cikin ai a saku a gaba shine dai dai,Spark yace Kuma Baki San tsiyar ba bana iya ko yi mata fada bana iya tsinana komai sai dai na lallabata,Mima tace to tsoronta kake ji ai wani iskancin ma na mata ai sai ana biye musu suke yinsa,Spark yace uhm uhm baza ki ja min salala n arziki ba,Mima tace kace kawai salalan tsiya yafi,murmushi yayi yace Baby ga Mima ya mikawa Naila waya ta karba suka gaisa da Muka tace ya jikin? Naila tace kalau nake Mima Alhmdllh,Spark yace Ina fa kalau ga me ciki.
Sai da suka gaisa sannan ya karbi wayar Mima tace Dan Allah Arham zaka yiwa fada ya kula da matar nan kar ya kashe musu Yar mutane mu shiga uku,sannan ka dinga Kai Naila tana bata shawara tana dorata akan layi,Spark yace Arham yafi karfina kina Gani yace ban iya komai ba cikin matar tawa ma rabo ne yasa aka samu,Mima tayi dariya karka Kara Masa sharri Spark to haka yake nufi mana tunda ba wata uwa na iya tsinanawa ba Kinga kuwa ai rabo ne kawai yasa,to ayi hakuri ai wasa ne,Ina Jin dadi Ina murna kanku a hade Kun hade kanku Kun zama abokan juna,matan ma haka nake fata su kasance dan Allah ku kokarta,Spark yace to zan gwada tace yawwa ta kashe wayar.
A ranar Spark ya fita da mota har kofar gidan Arham ya Masa waya ya fito,Yana fitowa yace idan aike ne nifa bazan je ba Ina da aikin yi,Spark ya bata rai ba wasa yace shugo mota Dan Allah karka bata min lokaci,budewa yayi ya shiga gaban mota,Spark ba alamar wasa a fuskarsa,Arham ya kalle shi ba mutunci yau,yace yau Allurar ce ta motsa? kaga Raina a bace yake wlh ka kyale ni kawai bana son wasa,yanzu Kai Arham haka ake yiwa Amarya? Dan Allah ka kyale ta a samu ta warke karka cutar da ita,Arham yace wai ni da matata Azo ana bani doka,in ka lalata ta har ta fara yoyon fitsari ai Kai ka sani,Baki Arham ya bude yace yoyon fitsari? Abin har ya Kai haka? Spark yace kwarai ka tambayi likitoci shi yasa muke jiye Maka tsoron hakan Dan ya tsoratar da shi ya fada masa,kar a cutar da yarinya,Amana ce fa,mudai muna fada Maka gaskiya ka barta ta warke idan ba haka ba Kai ka jiyo ko me ya faru,Arham yace tab Kai fa naga ai ba kyale Naila kayi ba,har kana da bakin magana yarinya har kuka take