Showing 48001 words to 51000 words out of 108220 words

Chapter 17 - Tantiriya A Gidan Yari Book 3 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

684

samu ba haka zan koma gidan iyayena naci ga da agolanci na babu ko bukka.

Naila tace wlh da Spark ya mutu gwara a kwace komai nawa na duniya,ke nifa Ina Jin akan ya mutu gwara mu mutu tare ko na riga shi,Basma tace tab wlh da cewa za ayi na zaba shi zan tura musamman idan na haihu in na mutu mantawa zaiyi ya auri wata ga yarana na barsu ai gwara ni na zauna na kula da abina,Naila tace wlh tunda kike fadar haka Baki fara son Arham ba amma duk sanda kika fara sonsa zaki bani labari da kanki,Basma tace Ina sonsa fa nifa tunda yazo zance naji kwakwalwata ta kwance a kansa sabo da sai naji kamar kar ya tafi,sanda Papa ya Kore shi daga gidan Nan akan nono na" ji nayi kamar nasa wuka na yanke su na watsar,Naila ta dinga dariya,tace nonon naki? Ei ai kuwa na musu addua mace Allah yasa su motse su tamushe,Kullum na dinga ciwon Kai sabo da bana ganinsa tana fada tana mulmulawa Naila cinya da hannu,Naila tace kyale min cinya dan Allah haka,Basma tace Spark Yana shanawa wlh Laushi,Naila tace naji tashi kiyi wanka sai Ango yazo ko so kike ya ganki haka ba gayu? tace a'a bari nayi,ta mike ta shiga toilet.

Su Chika ne da Ikhram suka shugo suna surutunsu har Basma ta fito a wanka,tace sai kallo na akeyi yanzu na shiga uku da kallo wajen mutane,kowa Amarya ce itace Amaryar she.
Ikhram ta mike tace Allah daga surukar General da Mima ta tashi na gaji,nifa idan ba a gidana nake ba takura nake yi,Chika tace yanzu Nan duk yaran Mima sun dirka mana ciki wannan yara Kwai Yan Duniya,yanzu Mima baza taji kunya ba ace 'ya'yanka duk sunyiwa matansu ciki,Naila tace Banda ni,Basma tace wlh harda ke Munji labari,Chika tace da gaske? Naila tace ke daga nayi zazzabi ake min wannan hasashen,idan akwai ai zaku sani ma,Basma tace Kun San girman Allah cike ne da ita.

A gurguje suka zabarwa Amarya kayan sawa Leshi ne fari kwal me tsada yaji dinki hadadde ta shirya sabo ne dal,dama Mima ta Dinka mata bata saka ba,Ikhram ce ta yi mata dauri da Yar kwalliya sama sama ta zuba kyau sosai tana kamshi,Naila tace to muje Palo,Basma tace bazan iya fita ba ni kunya nake ji kawai kawai sai na fita mu hada Ido da Mima shike nan tasan na zama surukarta,Danta zai dinga tabani sai naje ta ganni,dariya su cika suka yi,ke a yaran ma sakarai ce Basma mene abin kunya duk dangi ne waye bai sanki ba.

Da kyar suka yaki Basma ta tashi suka fito,sai buya take a bayan su tana ja da baya tana rufe fuska,abokan Ango da dangi kaf suka shugo lokaci guda da yawansu kuwa sun cika Palo,Basma bayan Ikhram ta tsaya tana buya,Ikhram ta matsa aka ganta kowa ta kiriri, ta rasa Inda zata saka kanta,ta rufe idanuwanta gam,Ango ya kalleta kawai,abokan Ango yara dasu matasa suka fara pics dinsu har family,Amarya sai kunya take je,bayan an gama akace za a yiwa Amarya da Ango su kadai,Basma tace nidai surukaina suna nan bazan tsaya ba,Arham ya harareta tayi shuru ta tsaya ana dauka ta ko Ina,ana gamawa Basma ta zauna tana ta tunanin abinda Naila tace ta yiwa mijinta ita tunaninta tun yanzu zata fara aikin.

Dangin Mima duk da yamma suka tafi ya rage sai surukan Mima sai yaranta su Spark suna gidan suna ta hira,Arham Yana ta sallamar baki,Basma daga ji Mima tace yau Arham tun safe Bai ci komai ba ma,Basma ta tuna tace ance na dinga kula da shi Kuma,tashi tayi sum sum ta shige kitchen ta dinga bincike a kitchen tana zabo kwanika,wani sabon kwali da ba a bude ba ta farke flask ne sababbi masu masifar kyau da tsada,Basma tace irinsu ne na me gida ta zazzabo abinta tace sun da ce da shi.
Sai na samu na gyara Masa gashinsa to ya zanyi ance na chafe shi dole na chafe shi nace cika masakinka Dan Arham,bari ya shugo.


AsmaBaffa
[2/24, 9:10 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI

BOOK 3
~TAIMAKO~


41-45


Official

By
AsmaBaffa


Page naki ne
Mrs Muhammad


*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*



Abincin ta zaba iri iri ta zuba Masa a flasks ta shirya komai abinta,Mima ce ta shugo ta Kalli abinda Basma tayi tace wa yace ki dakko wannan flask din? Wa ya aike ki? Kin San na mene ne? satin nan fa na siye shi zan kaiwa wata matar Senator gudun mowa zata aurar da yarta shine kika dakko kika wanke tare da zuba abinci,wa zaki bawa? Wanne baki kika yi?Basma tayi shuru,tambayarki nake yi nidai nasan a dangin ki ma ba wanda yazo,Basma tace dama Arham ne yace a bawa Yar aiki ta kaiwa wani abokinsa yazo daga nesa shine na zuba a nan sabo da ya fita kunya,naku ne flask din? Ki bari in aka kaiki gidanki sai kiyi Iko da kayanki,juye ki bani flask Dina,Basma kuka zata yi tace wlh idan aka kwace sai nayi zuciya a gidan nan,ko na fadawa Papa a bar min shi flask din,shi Papa sai ya biya kudinsa shike nan ya zama nawa,wlh da haka aka yi ma na huta ya biyani kudina cewar Mima,Basma tace to mun karbi bashi Mima zan karbi kudin sai na baki,Hakan yayi Ina jira Mima ta furta,tace to.

Masu aiki ne suka shugo suka fara sabon girki,Basma ta juye waccen abincin tace wannan dama ya tsufa ayi sabo a zuba min a Nan,ta wanke flask dukkansu tace gashi wannan duk abinda ya dace a zuba min daban special,suka ce to Amarya.
Tana fita taga yan mata sun cika Palo wai duk Yan secondary school da Yan University din su Arham ne suka zo Masa murna,sun ci wanka ga abokai Maza suma Yan makaranta,Basma ta zauna tana cewa nidai bani da kawaye a garin Nan,friends din mijinki ne suka zo muku murna,Basma ta tabe baki a ranta tace Allah yasa dai bai taba musu nono ba,gaisawa aka yi aka nuna musu Amarya,suka dinga yabawa suna Allah ya sanya Alkhairi,Basma tana amsawa tana murmushin yake.

Arham ne ya fito" Basma tana ganinsa ta mike tsaye,Yan mata suna tsokanarsa Ango wlh munyi mamaki wai aure aka yi Maka,duk abokai har mata ba Wanda yayi aure cikinmu mu da muke mata ma sai muka ji Abu katsam,Basma kusa da Arham ta tsaya ana kallonta ko kunya,kishi take,kafin ya basu amsa tace farin jini ne da shi yayi kasuwa,baiyi kwantai ba shi yasa,Kuma shine baya ji shi yasa aka zarge mu da igiya sabo da na gyara shi ya zama mutum,dariya suka yi Dake Yan matan birni ne wayayyu ba mace ba namiji taba Jikin juna suke su tafa su rike hannu wai duk normal ne su ga yan Abuja,Basma tana kallo a garin abinda akeyi shi yasa baza a taba mata miji ba,wata a friends tace da Arham Dan duniya ta Miko hannu zata rike shi,Basma ta janye hannun Arham,tace wai ku bakwa tsoron zunubi ne,duk irin wannan Yan kana nan laifin da ake Gani a ba komai bane wlh sai su taru su yiwa mutum yawa,ana magana kuce Kun waye,duk wayewar da ba ta bin hanyar Allah bace aikin banza ce,nidai ku taba wani wannan an bada shi ato.

Chika ce tace ki kyale bawan Allah da abokansa Basma,Arham kallon Basma yayi ta cukule ta turo baki,murmushi yayi yace gyara bakin to yanzu zasu tafi ma,Basma tace ni yanzu nayi course a wajen Siriki na muzurai zan dinga yi,Arham yace Papa? tace ae mana Ina da siriki Soja ace bana muzurai ai nayi asara,Mima ce ta fito da sauri Basma ta koma kujera ta zauna tare da fuskewa,Kawaye suka ce to taso ayi pics Amarya,tana shagwaba ta mike kamar sune Angon a haka aka yi pics,sun dan dade sannan suka tafi.
Mima ce tace Kaci abinci kuwa? Arham yace kika ce baki damu dani ba,tambayarka nayi ni,Basma tace na zuba da zan Kai Masa sai naga suna yin sabon abinci shine na fasa bashi tsohon abinci, yanzu sabon nake jira,Mima tace yayi masu iyawa shike nan da abinci gasu Nan iri iri duk baza a bashi ba sai anyi sabo,haka zai ta zama da yunwa kenan? Basma tace sai da na tambaye shi ai idan Yana da ulcer yace kalau yake shi,shine yasa nace a bari ayi me zafi,dariya Rafeeq yayi yace wani ya shiga uku,Arham ya harare shi da wasa ya wuce ciki,Basma ta mike a ranta tace bari naje na chafe shi,Maman Rafeeq ce tace gidan uban wa zaki je Kuma? Wannan yarinyar idan ba a taka mata birki ba wlh kafin a kaita gidansa tayi ciki,Basma a hankali yanda ba me ji tace ke kin kashe aurenki kinki zama zaki kashe mana namu auren za ace baza muyi biyayya ba,Ikhram tace Kinga Basma jeki ki Kai Masa abincin naga kina mimimi da baki,Basma tace ko minti biyar bazan ba zan dawo,sabo da iyayensa kar su ga bana kula da dansu suce baiyi dace ba Nima ala dole zan Kai,Spark yace Dan Allah jeki kina ta surutu wa ya hanaki ne,ta tafi abinta ta shige kitchen tana zuwa an gama wani girkin ta zuzzuba sai ga Arham ya shugo kitchen din da kansa,tace kaga abincin fa yanzu zan kawo,Arham yace abinka da baka Saba ba ni a barni na eba da kaina,Basma tace wlh bazai yuwu ba kace wani baka Saba ba,yace duk wannan abubuwan wa zai cinye? Basma tace Kaine muje ta tura shi waje muje,Arham yace dole zaki min,ni karki shugo min rayuwa na tabaki kije ki fadawa mutane,Nayi Dan hankali zan iya kin fadawa Papa da Mima amma banyi alkawari ba zan iya canja ra'ayina kana bani haushi zan fada,Arham yace zan saita miki bakin ai wlh,ta dauki abincin suka tafi suna zuwa dakinsa taga Junior a ciki,tace Kai junior ka daina zuwa Nan yanzu kowa yayi zamansa a dakinsa yanzu ba sa'anka bane Arham Kai da Shaheed ku dinga taka tsantsan da shiga dakin nan,Junior yayi dariya yace dama yau dinma tsautsayi ne,to tashi ka tafi naka,yace to ba musu,tace ka samo taka a Mami market dinku ta sojoji tunda Kai dole sai ka zama Soja,Junior ya dauki laptop dinsa ya fice Yana dariya.

Basma ta fara tunanin ta ya zata chafe shi tace gashi Kato ne ashe,tsaki ta ja a ranta,tace ita Naila ta ya take chafe Spark ne ita,Arham Yana kallonta Yana tsince tissue da aka watsar a dakinsa,Basma ta koma kusa da shi ya mike ya juyo zai tafi ta Masa kamar zata dauki yaro karami hannayenta a saitin hammatarsa tayi tayi ta iya ko motsa shi ta kasa,ta fara cika...ci ..cik...cikaaaaaa.....uhmmmm...
ta durkusa a kasa zata daga shi wai ta kafafunsa,tayi nishi ta dage ta kasa,gumi ta hada nan take,Arham Yana kallon ikon Allah yace mene haka? dagowa tayi tace na kasa Cika masakinka zan Maka na dagaka na cafeka shine na kasa,Arham yayi dariya yace kin makara Mima ta Dade da yi min abina tun Ina jariri har aka yaye ni,kawai kace kana min bakin cikin shiga Aljanna baza ka nuna min yanda zanyi ba,Arham yace ai sai an kwanta akeyi,Baki ta tabe tace to yaushe za a kwanta? yace yanzu ma tace to ci abincin Dan wallahi yau sai na kaddamar zan tafi.

Arham ya zauna a gefen bed harda zuba Masa abincin,yace yarinya ta fara cin Sadakin ta ashe dai da alama zaki ci kudinki 200k,wai haka aka biya dama? Arham yace ba a Baki ba? tace ae ni ba a bani ba ko sisi,yace tab tsaya naci abinci wlh baza ta sabu ba a baki abinki so ake auren ya dinga rawa ba a bawa Amarya sadaki ba Ina aure,Basma ta zauna a gefen bed tace lallai ma Kawu Dan Yana kanin ubana shi aka aura ko shi za a yiwa ciki,Arham ya sheke da dariya,yace kura da Shan bugu gardi da kwashe kudi,aje a bi min hakkina kar Kawu ya tafi kauye ba mutunci ne da shi ba,sanda Babana ya mutu ai kasa rike ni yayi,yace bazai iya ba sai yanzu anga na girma an bani sadaki na zai cinye min,sanda Ina yarinya ko fitsari nayi sai ya dinga dukana dole babata ta tafi dani agolanci shine yanzu yaji kudi yayi shuru Yana so ya samfe da su gida aje a siyi Masara a ci tuwo ni Ina nan an yi min ciki yau yawu gobe amai wlh bazan yarda ba.

Arham Yana ta dariya yace wai ke shekarunki nawa ne? tace 17yrs da wuri na gama makarantar secondary sabo da karatun kauye sai a hankali,Arham yace a dawo maganar sadaki fa,tace ai dole na karbo abina Kuma a jikina zan cinye ba wata kadara da zan siya in samu in ta siyan kayan dadi,Arham yace wanne kayan dadi gashi kullum kina ci,tace ni dai a jikina zasu kare kudin,yace uhm uhm Basma dollar tayi tashin gwauron zabi,ba ruwana ni cewar Basma" ta sa hannu ta goge masa gefen bakinsa da dan abinci ya bata, suna zaune ya ci abincinsa ya shiga wanka,Dan kwanciya tayi a gadon tace bari ya fito sai naje na nemi Kawu ya bani sadaki na,kwanciya tayi daga rufe Ido sai bacci,baccin tsiya ne da Basma kamar me cutar bacci.

Yana fitowa ya ga tana bacci ta Kalli sama,Maman Rafeeq kuwa zuwa tayi ta fadawa Mima tace tunda Basma ta tafi Kai abinci taki dawowa wlh tana can Kuma kin San yaran Nan musamman Arham din,Mima ta idar da Sallah tace jeki mana ki Koro ta ko gyaran Jikin ba a yi mata ba,Maman Rafeeq taje dakin Arham ta dinga knocking yaki magana Kuma yaki budewa kamar ba mutum,tace Arham Kai ...shuru yayi Yana Jikin mudubi Yana fesa turare tace baza ka bude kofar ba,magana yayi yace bacci nake na gaji da sallamar baki,Ina Basma ta fito,yace ai ta fita,karya kake ka bude tun kafin ranka ya baci na kira ubanka yazo da kansa,kofar ya bude ta hango Basma kalau tana bacci,tace tashe ta ta fito ke Basma ta shige ciki tare da jijjiga ta,Basma ta mike ta fito,Mama ta taso keyarta gaba.

Ba ayi miki gyaran jiki ba kike wani Kai kanki wajen namiji daga aure,ai Kya bari shi ya nemeki,Basma tace to na bari Allah ya kawo shi tunda bakwa so nayi biyayya shike nan na fadawa Papa kawai,Mama tace sabo da shi ya kawo ki ana miki Abu sai kice zaki fada Masa to dukan mu zaiyi ko me, Basma tana jinsu ana mata surutu ta wuce dakinta.
Tun daga ranar bata Kuma kula Arham ba,Mima tana kallonta ko ance Arham baici abinci ba bata magana,idan yace tazo baza ta je ba,har aka kwashe kwanaki hudu zuwa biyar,Mima da kanta taga zata raina Arham,ba abinda ake sa Basma tayi indai na Arham ne to kuwa baza tayi ba.

Tana zaune a Palo yau duk su Mima suna nan Arham yace Mima ya naga ba a gyara min bedroom dina ba? na manta ma ban sa an gyara ba, ga Basma taje ta gyara,Basma tace to kawai taki tashi tayi zamanta,Mima tace ba Dake nake ba wai me kike yi haka mijinki ne fa amma ba a isa a saki aikinsa kiyi ba.
Basma tace cewa fa kuka yi Ina Kai kaina wajen namiji na daina zuwa,in naje abinci zan Kai sai an biyo sawu na an Koro ni ana min fada Ina dalili ba sai na barshi ba tunda bakwa so,dama ni fada Aunty Naila ta min shi yasa nayi kokarin yin abinda tace Amma tunda kuka ce Ina zubar da ajina shi yasa na daina yi.

Mima tace au Ashe zuciya kika yi kenan? Ae zuciya nayi,duk yanda na Kai ga sonsa bai kai ya ku ba kuka ce bakwa so a kula da shi a barshi yaci gaba da gwaurantakarsa shine nace to na huta,Arham yace banga laifinka ba kinyi dai dai Ina bayanki,Mima ta kalle su tace shike nan Basma yanzu ba ruwan mu ki kula da mijinki,komai kece zaki dinga yi Masa a gidan nan baza a sake bin sawunki ba,Basma tace a ranta sunji wuya sunga zan raina dan su,lallabata Mima tayi tace yanzu kije ki gyara dakin amma karki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login