Showing 18001 words to 21000 words out of 108220 words

Chapter 7 - Tantiriya A Gidan Yari Book 3 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

670

danna wannan link din Dan Samun damar shiga group din

https://wa.link/49vn47




Jauro ya Kalli Abba Dolo yace bazan biye maka ba,ni ba Kubra bace itace ya zama dole ta dinga biye Maka Banda ni, Abba yace an dora ka a keken bera,ka Sha amarcinka Jauro ni ba wani Abu nace Maka ba,ya maganar zuwan naku Abuja? Jauro yace so nake sai na koma wajen Habiba itama nayi mata kwana biyun ta sai muje kasan mata sai tace sai da kwananta ya zagayo na takalo unguwa,Abba yace ba tace ta baka sati ba,Jauro yace Kai sai na zauna nayi satin? karya take gwada ni tayi,baka San tsiyar mata ba tunda baka taba yin mata biyu ba?

Abba yace to ka koma kace ka fada baza ka iya har sati ba tare da ita ba,itama ka zuga mata karya tunda yanzu dama Kai munafukin mata ne,ban gane munafukin mata ba,Abba yace to Nan kazo kace Maman Annoor ba wata kamarta,can ka koma kace ba kamar Habiba ai ka zama Dan iska kawai a gari,ni bazan iya Kara aure ba sabo da dole na Fadi gaskiya,idan naji Amarya ta kwace ni zan fadawa Yar Inna gaskiya nace ni can yafi dadi,idan Yar Inna ce ta kwace ni sai na fadawa Amarya kaga zaman aure bazai yuwu da haka ba ni Kuma dole sai na fada shi yasa gwara na hakura ,suje da kyawunsu da komai zan karasa da na Kubra.
Jauro yayi dariya yace dama mata biyu ai sai mu gwarazan Maza.

Bayan sati daya Abba da shi za Azo Abuja yace ko Dan yazo yaga gidan auren yarsa ai yazo,Jauro,Annoor,Iman sai Haidar,Jauro duk ya biya kudin jirgi harda Maman Iman Rahma,Abba me 'ya tuni ya fadawa Naila zasu zo da baki,tare da Yar aiki da su Mufee suka shirya girke girke,Spark yau fasa fita yayi,tace baza ka fita bane yau? Yace Ina zanje surukaina zasu zo ai dole na zauna,Naila sai da suka gama komai suka gyara gidan sannan su Mufee suka tafi gida,Naila yanzu har kannen miji ake sawa aiki.

Spark driver ya tura aka dakko su har gida,Abba yau yaga gidan 'yarsa,yace Allah ya Kara zaunar da ku lafiya baza ki fita daga gidan Nan ba Naila, Aljannar duniya, da nasan abin ya Kai haka ai kullum tsaiwar dare zan dinga yi karki fito daga gidan nan,Iman tana kusa da Annoor dinta,ita da Babar tata sai kallon kallo sabo da rashin shakuwa,Suna shiga Sanyi da kamshi ya dake su,Naila ta musu sannu da zuwa suka zauna,Abba yace Naila ki rage cin dadin nan kar kiba ta miki yawa ki jawa kanki ya dinga hango Yan shawalwalai,dariya suka yi,Naila tace Abba ni Ina naga wata kiba a haka,gaisawa suka yi da juna sannan ta haura sama ta kira Spark tace sunzo wai nayi kiba Inji Abba? Spark yace to kina ta cin kudina kin hanani Tara abin duniya ba dole ba,dariya Naila tayi ta jawo hannunsa ya mike suka fita,Jauro yace Ashe masu gidan ana Nan Kai sai kace Amarya,Spark ya iso ya gaisar da su da ladabi ya mikawa Annoor hannu suka gaisa,Iman tana makale a Jikin mijinta tayi shuru.

Abba yace ya Banga kayan ciye ciye bane ni bana so a sani gaba da magana ko lemo babu gwara a ajiye min abinci a tafi a bani waje,Naila ta mike ta dinga jera musu abin ci da Sha,Abba ya Kalli Spark yace Allah ya Baki Naila Lada ashe haka kike Shan wahala a gidan miji Yana kallo bazai tayaki ba,dama samun miji irinmu a zamanin nan ai sai an tona,Uwarki ta fiki dace Naila data sameni,da nine bazan zira mata Ido ta dinga aiki haka ba,Jauro yace ai yanzu babu irinmu a kasar Nan sai dai ko a Larabawa, Su Annoor suna ta dariya,Maman Iman tace ku don Allah baza kuyi shuru ba agaban yaran ku,Jauro yace a'a bama shuru mu bakinmu kalau yake fes kullum ga brush ga aswaki ta ya za muyi shuru,Spark shi dai dariya yake kawai dan abin na su Abba Dolo sai Ido.
Ba ruwansu suka bude abinci sai da suka zaba,Naila tace ko a Kai Dining? Abba yace a'a muna da me ciwon baya Jauro kawo mana abin zama mu a kasa zamu zauna.

Naila taje ta kawo musu suka baje a kasa,Iman ta zubawa Annoor su suna kujera,Abba yace ku a sama zaki ci? Annoor yace ya za ayi ta zauna a kasa Iman a'a,Jauro yace Kai yaro munga Habiba ma yanzu ta hakura zama take,Nan wai Kai gyara kake taya matarka? Kayi ka gama,Haidar tunda aka zo aka gaisa baiyi magana ba sai lokacin yace ni ba me zuba min wato ko naci ko na barshi

Naila har ta yunkura zata mike kiri kiri Spark ya jawo rigarta ana kallo ya fuske yace zauna,Haidar yace Allah sarki ai shike nan ya zuba abinsa,Annoor Yana ta Masa dariya yace wlh Kuma matata baza ta zuba Maka ko ruwa ba,Abba yace shi yasa naki zuwa da Yar Inna suka kwashe da dariya,Haidar yace ni me zance matarka tayi min Abba ai uwata ce,Abba yace ake kaunar mahaukaciya ma bare tsohuwa da hankalinta,har abada baza ka samu irin Yar Inna ba,ga Maman Iman kaji tarihinta dai to bare dattijuwa irin Yar Inna a kanta sai ka wulakanta budurwa,Spark Yana ta dariyar Abba da son Yar Inna.

Sai da suka koshi suka huta sannan mazan suka tafi masallaci Naila ta Kai su Iman bedroom suka yi sallah suka kwanta suna hutawa,Maman Iman bacci tayi Iman ta fito ta samu Naila suna gyara palon da me aiki,ta taya su suka yi wanke wanke suka gyara ko Ina har kitchen,Iman tace Dan Allah Naila kice na kwana a nan gidan kar a tafi dani hotel,Naila tace sabo da me? Iman tace to mijina baida hakuri bazai bari na huta ba na gaji wlh duk ya kashe min kugu,Naila tayi dariya tace zaki Saba ne,ni dai Dan Allah kice zan kwana a nan,Naila tace to shike nan zan gwada,harda bawa Iman Yan tsumi na gyaran jiki ta Sha abinta ta bata wasu ta sa a jaka.

Jauro bayan sun dawo daga sallah yace Maman Haidar ta turo min address din gidan su Haidar,Naila tace ni Ina ganin kamar haidar da wani wlh na rasa gidan waye Kuma,sai naga kamar Yana da kanne kamar babu na rasa Inda nasan me kamar sa,Abba yace ai ga address zamu je har gidan,Spark ya karbi Address din ya duba yace a'a to wannan ai gidan su Rafeeq kanina ne,Jauro yace mutumin fa bai taba haihuwa ba,Ae shine fa sunansa Aliyu Shima sunansu Daya da mijin Mummy amma shi ba a kiransa da Aliyu Sunan garinsu ake fada Masa.

Yace bari na kira Rafeeq muje gidan kawai ,Rafeeq ya kira suna tare da Ikhram dinsa ya gaji da halinta ya kaita asibiti cikinta ma yafi na Chika kwanaki a duniya,Spark ya fada Masa dai a gurguje,yace to ku sameni a gidan ai kuwa mijin Mama Yana gida yau,suka tafi Rafeeq ma ya tafi da Ikhram can,Spark suka tafi gaba daya,suna zuwa Suka shiga har Palo, Maman Rafeeq Hannun bibiyu ta tarbe su,Jauro yace wajen me gidan muka zo,tace ai kuwa Yana Nan ta mike taje ta fada Masa ta dawo tace yanzu zai fito,ta kawo musu ruwa da lemo.

Fitowa yayi cikin shiga ta alfarma Yana tafiya ta manyan masu kudi yanda ya Saba,har ya bude baki zaiyi masifa me ya kawo Maza har palon matarsa baza a jira shi a waje ba sai suka yi Ido biyu da Maman Iman,Baki ya bude mamaki ya kama shi,yace Rahma me zan gani kece? Rahma ta mike tsaye tace nice nan Sudan,Spark yace dama na fada muku da Sudan aka sanshi amma sunansa Aliyu.

Rahma ta dafa Iman tace ga Yarka,Maman Rafeeq da Rafeeq suka zaro ido waje,Jauro yace ga Danka Kuma bakin Dan iska tambadadden dattijo,Abba yace a'a Jauro yaransa suna ji kana zagar musu Uba ba dadi,Haidar yace mene amfaninsa ni wlh a Kara Masa wani,a wajen Aliyu Sudan ya durkushe yayi zaman dirshan a kasa ya Dora hannaye a Kai Yana kuka,yace Rahma ki yafe min na cutar dake son ki ne ya sa na aikata miki haka,har lokacin kina halin ciwon hauka Ina ta bibiyar Inda kike har na ganki a kango na da nake ginawa daga nan zuciyata ta kasa hakuri Dake har naci gaba da amfani dake,dalilin sonki na kasa kula da matata ta aure Ina zaluntarta,farko da na fara bataki Baki samu ciki ba sai dai lokacin da kike halin ciwo na hauka tabbas wlh wannan 'yata ce,Jauro yace Kai rufe mana baki algungumi ko kunya baka ji duk mutanen unguwa sun San kaine ka aikata tunda ana ganinka kana fita da ita,Kai rashin Imaninka yayi yawa mace tana ciwon hauka,Rahma ce tayi magana tace sharrin shedan ne laifin kaka ne data Hana shi ni,ni nasan Yana so na,duk ita ce ta jawo min,Aliyu Sudan yace kwarai kuwa.

Abba yace to shi Kuma Haidar din fa? Jauro yace ai kasan matar da tazo aiki gidanka Yar wanke wanke da shara Binta,kayi mata ciki kuka koreta Kai da matarka,Jauro ya nuna Maman Rafeeq, kece da laifinki wai ku son miji son aure kar asiri ya tonu Kuna kallo mazajenku suna aikata fasadi sai ku Goya musu baya ku kare zancen to yanzu gashi ke ba take yake ba Kuma gashi ya tara yara har biyu ba yaran sunna ba,ke Kuma Allah bai baki naki ba,mutane baza su hakura da jarabawar Allah ba,Kun cuci yara kawai.

Maman Rafeeq tana ta rusa kuka mijinta yayi abin kunya bayan itace ta Kori uwar Haidar tace ta yiwa mijinta sharri,Aliyu Sudan yace yanzu Ina Binta take? Haidar yace tuni ta koma Fatima tana England ta samu hadadde tana aure" jiranka zata yi?,ka daina ce mata Binta" Fatima ce yanzu,Kuma ko tana Nan baza ta aure ka ba,me za ayi da miji irinka,shi yasa kullum na dinga tsallaka katanga kullum son Bariki nake ashe gado nayi ni nasan da dalili,Allah ya kiyaye Yan tabe tabe nayi banyi babban ba adduar Kawu tana bina,Aliyu Sudan yace Nima tawa zata bika,Haidar yace a'a'a ko kayi baza ta karbu ba,irin wannan laifi naka munana Ina zaka sa min albarka ta bini Kai kanka inaga sai da aka sallamaka ka gudo daga Sudan din, nidai kawai ka cuceni,cuta ka gama damu Allah ya yafe Maka,bamu muka yi laifi ba da sauki,takaicin ma da banyi aure ba" da nayi aure ne ma da sauki to ban aure ba wace zata ji Dan shege ta aura,Spark yace Kai in da kudinka ko Yankan Kai kake mata yanzu aureka zasu yi,ni da nake da kanne na baka daya a ciki ko Mufee ko Haly wawarka zasu yi.

Annoor Yana jinsu takaici ma ya hanashi magana,yace mudai kawai an cuce mu,yanzu Haidar Kai ubanku Daya da Iman kenan? Yace to ya zaka yi na zama surukin ka,shi yasa muke kama ma,Annoor ya Kalli Haidar ya Kalli Iman yace Kai ya Akai ban kula ba sai yau Kuma Kuna yanayi fa,Haidar yace sa wasa yaro,Haidar ya Kalli babansa yace to yanzu Kai Baba zamu ce ko me kasan bamu da gadonka sai a bamu rabonmu tun a duniya,in kana so mu ce Maka Baba wlh in baka so to kaje da kudinka ni dai ba sake Ganina zaka yi ba dama can Ina da Ubana daban me zanzo nayi Maka,uwar tawa da ka koreta Gombe garinsu,Aliyu Sudan yayi mukus kunya ta isheshi.

Rafeeq yace abin kunya ya bar gidan su Spark ya dawo gidanmu,'Ya'ya biyu rigis ba aure aka same su,sai nayi wata ban zo gidan Nan ba,dama Nima ba kaunata yake ba tunda aka kawo ni riko ka tsaneni,kwana a gidansa bana yi sabo da ba shi ya haife ni ba,matarsa duk kyan gidan Nan abinci wahala yake mata,badan ni ba da yanzu ta canja kamanni,dama shi yasa ake so mutum ya shuka Alkhairi in kaki Kuma duk sanda Allah ya Kamaka to wlh shike nan Kuma,yanzu gashi iya wannan ya isheka,ba duka ba zagi asirinka ya tonu a idon duniya,ga hakkin yaranka,hakkin matan daka zalunta,hakkin matarka ta sunna gani ni kaina Dan riko hakkina kadai sai yasa asirinka ya tonu,yanzu ni uwata zaka sakar min mu ware tunda ba sonta kake ba dama ga Rahma ta dawo ka aureta ka sakar min uwa wlh.

Spark yace wlh kuwa ka saketa kawai kanwar uwar mu a saketa mu tafi da abar mu,Rahma tace in aka saketa Nima bazan aure shi ba Dan Allah kuyi hakuri zai gyara halinsa sai mu zauna lafiya mu hada kanmu,Maman Rafeeq takaici ya kamata tace wato ita wannan kawai ma tunaninta aurensa zata yi ta shugo gidan sabo da so,ni na hakura da Kai Aliyu Sudan ka Aiko min da takarda ta sai na koma gidan Rafeeq,Rafeeq yace gidan Mima zaki zauna gidana bazai zaunu ba,gidana ba gidan zama bane Mama, mu kin San ba a rabamu da Uhum hum,daki ta shiga Aliyu ya bita Yana Bata hakuri ta fito da akwatinta.
Spark yace ni Ashraf na kashe auren kanwar babata yau mutafi gida kina da gata muje ku hadu ku uku a gidan Mima kwana Nan uwata zata tafi babban gida,Haidar yace ku tafi da ita wlh kar ta zauna karku yarda sai ya bata Jan kati uku.

Abba yace Dan Allah ku zauna,Kai Ashraf ku tsaya,suka tsaya Shima Aliyu Sudan din ya zauna ya nutsu Yana kwalla,Abba yace duk wannan abin babu abinda zai gyara ayi hakuri a tattara a yafi juna babu abinda ya Kai hakuri riba,Kai tunda kasan baka son matarka na mene zaka takura mata ka barta ta samu Wanda ke sonta,ka auri wacce kake so kaima shine zaman lafiya,da ka auri wacce kake so duk baza ta kaika ga aikata wannan cikin shegen ba,yace Nima iyaye ne suka hada,Maman Rafeeq tace Nima na tsane shi ba sonshi nake ba sabo da abinda yake min bana kaunarsa" kawai ya sake ni ya auri wacce yake so final

Jauro da Abba suka zauna suna ta sasanci Abu yaki yuwuwa,Maman Rafeeq tace ita tana jiran takarda,Ikhram tana ta kallon Haidar tasan tarihinsa yayi kama da Wanda akace sun hadu ta bangaren uwa,magana tayi tace Haidar Dan Allah a Gombe su waye danginka? Jauro ya karbe zancen ya bata labarin dangin tace to wlh shine cousin dina da babata da babarsa uwarsu Daya ubansu daya ita babata ta rasu a prison,ka kira Mamanka kaji,Haidar yace Kai karfa a dinga gayyato min Yan uwan da ba nawa ba sabo da ni Dan gaba da fatiha ne kowa sai yace Dan uwana nane,ya kira Mamansa tace Haidar kunje kuwa? Yace ae an gama komai zan Baki labari ga wata Ikhram wai yarki ce Yar gidan Sarah wai wacce ta rasu a prison,Maman Haidar harda kuka tana Allahu Akbar Allahu Akbar bani ita 'yata ce,Rafeeq yace to fa Yan uwantaka ta tafi tayi naso harda Ikhy dita.

Sun Dade suna waya da Ikhram,Jauro ya mike yace ku tashi mu tafi sauran bayani ya rage gareka Sudan in ka yanke hukunci ka tuntube mu,suka mike suka fice ya biyo su ya karbi number waya kunyar duniya ta ishe shi,Abba yace ba Sudan ba ko Makkah ne Kai ba ruwan mu.

Gidan Mima suka dunguma,Mima Taga sabuwar masifa Kuma again kanwarta itama wata ta afka wani hali,Mima tana Jin komai ta dinga salati tana sallalami,Mummy tace ni gwara ma na bar garin Nan na huta da wannan masifa,Arham yace saura kis ai jibi za a fara zama,tace zanci ubanka wlh,suna zaune Mufee ta fito cikin atamfa fitted gown ta zuba kyau gasu da kyau dama,Haly ta fito suka gaishe su Mima an koyawa yara gaisuwa,suna tafiya Haidar yace a ransa ba ruwana Ina Dan shege wa zai bani yarsa,kuje da kyawunku bazan so kowa ba,Jauro ya Kalli Haidar yaga Yana kallon Mufeeda,Jauro yace karka bada mu mana,Haidar ya fuske yace ni me nayi suna Kus Kus,Mufeeda Kuma su Haly anga zuka zukan samari harda nutsuwa,ana nuna halin kwarai.

Mima sai yau taga Baban Naila,tace Inshaallah zamu zo har gida a gaisa,Abba yace Allah ya kaimu,Papa yazo suka gaisa a ranar su Abba suka ce sai dai a kwana suka koma gidan Spark kafin su tafi hotel,Naila ganin su Jauro sun fita sai Haidar, Annoor,Iman Spark da ita tace amma a Nan zaki kwana ke Iman,Iman tace ae mana ai ni Ina Nan,Spark da bai San zance ba yace mata da Mijinta ki raba su Ina ruwanki wannan ai shishigi ne ko ke kadai kike kwana ke? Annoor yaji dadi yace so take ta rabani da ita yau Yana dariya,Spark yace a'a idan anan zata kwana Shima ya kwana anan,Annoor yace shine maganar gaskiya,Iman takaici ya kamata da bakin cikin Spark,tayi shuru tana fushi,Haidar Yana jinsu yace ni yanzu Yaya ne bazan ce komai ba kanwata ta rainani,kaji da shi dan iska cewar Annoor.

Naila ce tayiwa Spark rada tace Kai baka gane ba Baby hutawa fa zata yi ya dameta da naci baya bari ta huta shine zata kwana a nan yau,Spark baiyi kasa kasa da Murya ba yace to kawai sai ta huta? akan me zata huta?..Baki Naila ta rufe Masa da hannu,Annoor yace na gane kan zancen Kuma ai,ya leka fuskar Iman Yana dariya yace baki kuka hada ashe, Spark yace karka biye mata Dan Allah indai mata ne haka suka ke,kafin ayi abu suna wani nokewa ana farawa Kuma sai....Naila ce ta rufe Masa baki tana dariya tace wai mene haka Dan Allah ka kyale yarinya a barta ta huta,Annoor Yana dariya yace bamu zo duniya Dan mu huta ba,bauta aka turo mu muyi sabo da haka ita muke yi.

Washe gari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login