Showing 45001 words to 48000 words out of 236322 words

Chapter 16 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

741

Suka Daukesa suka kaisa asibiti aka Dubasa aka bashi mgunguna da Shawarwari da Farko Abun kamar yayi aiki Daga Baya sai Abba ya Kara Rikicewa Bawanda zai Fahimci Halin da Abbanmu ke Ciki}? sai mu da muka Dandanin Zafin Abun,Shiyasa cikin Yan"uwan Abba suka kasa mai Uzuri Ballatana su Fahimci Wani Hali yake Ciki basu Taba Dadanin Zafin Rashin Daya Dandana bane Shiyasa suka Fara ganin Laifinsa suna Fadin bai da Takwalli ne Dagashi har mu da kullum bamu da aiki sai mu tasaahi muna kuka ai ba kanmu Farau Mutuwa da Rashi ba Anni da Asma"u da Salima da Nura Sun Tafi kenan har Abada bazasu Taba Dawowa ba..Daada ce Kadai ta Fahimci Halin da Abbanmu da mu kanmu muke Ciki Baffa Kabiru yafi kowa Daukan Zafi Daga Karshe sai ya Zare hannunsa kan Abbanmu Tunda Likita yace Mgani baya aiki Tunda Abba bai Rage Damuwa ba kuma yaki ya manta da Abunda ya Faru Dashi..? taya zamu manta da wannan Rashin..? Ai har Abada Gidanmu ya Shiga kuncin da Bazamu Taba Fita acikinsa ba.
Tun bamu gane ba Har muka gane irin Yadda yan"uwan Abba ke kallonsa a Saboda Rashin Takwalli Ya koma Mahaukaci bashi da aiki sai Sambatu,Mukuma ya"yansa mu Bar komai nami mun dawo muna Rayuwar kawai Saboda Baffa Kabiru yayi yayi Dani da Imran mu koma Lagos Saboda aikin mu muka ki..Imran ya Nunamai Aduniya Bamu da wani abunda ya Ragemana Bayan Abba Saboda Haka ba inda Zamu muna Tare Dashi Dalilin haka yasa muka kusa Wata Shidda a Dukku,ayyukan mu Duka sun Tsaya an gaji da kiranmu an kyalemu,Munari Tuni Karatunta ya Tsaya Cak itama Bata da wani Sauran abunda Zata Dora.
Ni ban yi Tunanin Dauke Abba mu bar Dukku ba Imu ne ya kawo mana Wannan Tunanin Tun Lokacin Daya iske su Baffa Kabiru sun Tarun ma Abba suna ta mai Fadan yaki ya yarda da Kaddara ya Dawo Daidai ya Zauna yana Biyemana yana kwana kuka Mutuwa ce Dayace kuma wanda ya Mutu baya Dawowa Abba na kuka bayacewa komai Domin alokacin basu san Dacin Dayake ji ba Daada ma kukan Take ammh sun kasa Fahimtarsa,Suna cewa ya zama Mahaukacin karfi Dayaji kamar ba Musulmi ba,Baffa Mustapha baya mgana sai Baffa Kabiru yafi kowa Zakewa wannan Dalili yasa Imran ya mtsamin kan muce Zamu Tafi da Abba Lagos muje Chan muka Cigaba da aikin mu muna kula Dashi..Abun mamaki da muka Furta Daada ce kadai tayi musu ammh Banda Sauran yan"uwan Abba nan da suka amince acewarsu kila zai fi Samun Sauki batare da Rakiyan kowa ba Muka bar Dukku Zuwa Lagos,a mota muka Yi Tafiyar Domin Tun Abunda ya Faru Har Abada muka Tsani Jirgi.
Mun Dawo Gidanmu na Lagos da Zama sai dai Babu abunda ya Sauya Nidai ban koma bakin aikina ba Hakama Imran,Ballatana mu kokarta mu maida Munari makaranta Duk wani Farincikin Gidanmu sai ya Gushe sai kunci da Bakinciki Abba koda yaushe yana Daki yana kuka yana Samabtu mu kanmu bamu da Wata natsuwa.
Bayan Dawowarmu da Wata Daya Baffa Kabiru ya zo ganin mu Cikin Wannan Halin ya kara Bata ransa yayi ta Zaginmu yana mana Fada Abbanmu kuwa kamar ya Dakesa Daga karshe yace yaje yayi ta Haukansa In ya Haukace ni da Imran sai mu kaisa Gidan Mahaukata ko Zama bai yi ba ya Juya shima zuwan da yayi Daada ce ta matsamai yazo ya Dubamu.
Awannan Ranar Ran Imu ya baci ya Fita,Fitan da bai Dawo ba sai da ya kwana Biyu yana Dawowa na gansa ya iya Busa Sigari,shi kuma ya ce Dole ne muyi Nisa da Komai namu in muna so mu Cigaba da Zama Lafiya Inda ba wanda yasan Labarin Gidanmu Ballatana akira Abbanmu da Mahaukaci muyi nisa da komai nanu asali,Nasaba Dukiya aiki da Komai na Rayuwa Ni kuma na amince Domin Lokacin na Fara Tsorata da komai kada Imu ya Fada wani Hanyar Banza.
Bamu saida komai namu ba Gida Motoci Duka suna Lagos sai dai mun kai Takardan Barin aiki Daga Ma"aikatanmu da Muke aiki sai muka Tattara kudi Katin bankin mu Dana Abba dana Nura dana Asma"u da Takardun makarantarmu Dana Munari sai kayan sawanmu,muka Diba iya wanda Zamu iya muka Baro Lagos Bayan mun Sallami mai Gadi mun kulle Gidanmu bamu ma Tunanin Zamu Dwo Watarana ba sai Domin yin hakan Shine Mafitarmu Mun Taho da Abba Kano bai Cikin Hayyacinsa a Hotel muka Sauka Ni na Fita Na Bincikamana Gida Cikin kwana Biyu muka kara mallakan Wani gidan,Shine wanda muke Ciki,Muka Tattaro muka Dawo Domin Gina wata Sabuwar Rayuwa Bayan mun bar Duka Layukan mu da Wayoyim mu a Lagos Da komai inda Za"a Same mu saboda bama Bukatar Taimaakon kowa Tunda ankasa Fahimtar,Radadin Dake Cikin Babban Rashin da mukayi.
Ganin in na Zauna Haka Rayuwar Gidanmu Zata kara Lalacewa Cikin kunci,Sai na yanke Shawaran Fita Neman aiki Duk da bamu rasa komai ba Muna da Kudi,ammh ban Zauna ba Cikin ikon Allah na samu aiki a hukumar Inec ta nan Reshen Jahar Kano,Ni ne na Zama Uwa da Uban Imran da Munari na Zama Garkuwan Abba na Daukan Mai likitan Dake Zuwa Gida yana Dubasa Duk Bayan Wata Daya,koda Abba ya Fara Dawowa Hayyacinsa ya Fahimci Abunda muka aikata yayi ta kuka sai dai Bai Da Cikakkiyar Lafiyar da Zai iyq Tambayanmu meyasa mukayi hakan..?
Da albashina na Siya Motan Hawa na Siya ma Imran Mashin Tunda yace bai Bukatar Mota aiki ma yace bazai koma ba,Shi Baahi da Sauran wani Buri kuma,nayi nayi na Rabashi da Shan Sigari na kasa Saboda ya Riga ya Zama Jikinsa bazai iya Awa Daya bai Sha Sigari ba,duk Wasu Sabbin Halaye Rashi ne da Rayuwa suka maida Imran haka,Ni nayi Tunanin Inganta Rayuwar Munari Tunda ita Kadai take Ragemana na maidata makaranta..
Da farko ban Yi niyyar Fara Neman aure ba sai nayi Tunanin auran nawa Zai Tamaka ma Rayuwar Imran da Munari Sai dai kash Duk inda na Nemi aure sai mgana ta kamkama sai ta watse duk inda akayi Binciken Gidanmu aka gano wani abu duk da bama Hulda da kowa abun mamaki labarin komai sai ya fita, bamu da kowa kuma Abba bashi da lafiya yana Ciwon Hauka Dalilin haka Imran ya karya Hannun Kawun Wata Asma"u Dana Nema aka Hanashi Daga Karshe shi kawun nata yaci Zarafin Gidanmu Shari"a Dakyar na iya kasheta Na nemi aure kusan sau uku bana samu sai a kanki kema din da kokarin Imu na Sameki Tun kuma Bayan Tafiyarmu Har yau wani Daga Cikin Ahalin mu baisan inda muke ba bamu sani ba ko sun neme mu mudai bamu nemi kowa ba Har Rana mai kama ta yau..Ko naso mu nemi gida Imran ke Hanani Domin shi yafi Daukan Abubuwan da suka Faru}? Fiye dani Kaina.







*Shakira...*
3/22/22, 23:04 - Ummi Tandama???i: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:JanaftyB??0
{*

*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*

}? }? }? }? }? }?}? *??T??14*

"Kinji irin kaddaran Data Fadama Gidanmu Babe..Tun bayan Faruwar Al"amarin Komai namu ya tsaya Cak Kawai Rayuwar muke gamu nan bawani Jin dadi ba Farinciki ba Walwala.
Kinji Kuma Dalilin daya sa muka Baro komai namu kinji kuma irin Halin da muka Shiga da wanda Abba ya Shiga Da Dalilin mu na barin Komai namu muka Dawo muna Rayuwa inda ba"a Sanmu ba kuma kinji Irin Lalauran Data samu Abba Shi din ba Mahaukaci bane yanayin Rayuwa da kaddaran Allah ne suka Maidashi haka.
Ya karishe Fada yana Tsiyayan Hawaye,Safiya ma Dake Jikinsa Hawayen Take,Cikin Sarkewar Murya tace"Allah ya jikansu Anni..Allah yayi musu Rahma Allah ya kyautata Makwancinsu.Hakika kunga Babban Rashi..Tabbas kun Hadu da Jarabawa Mai girma Mutuwar Rai har Guda Hudu a Lokaci Daya dole Zuciya Zata Raunana..Allah ya karbi Shahadarsu..!
Yusuf na jan majina yake amsa mata da Ameen Ameen..
Safiya ta Cigaba da Fadin"Tabbas su Baffa suma basu kyauta ba..kamata yayi su ja ku ajiki da Lallashi da Nasiha da komai sai kuFara manta abunda ya Faru..Su Rika Nuna muku ku Fauwalama Allah komai su Nuna muku Hakan bashine Karshen Rayuwar ba akwai Wasu agaba..Ya kamata ace sun Zauna sunfi Kowa Fahimtar Halin da kuke Ciki..Abba kuma ya kasance koda yaushe Suna Lallashinsa da kokarin Nuna mai Komai Daya Faru da Sanin Allah kuma Mutuwa Dayace Muma Jiranta Muke,su da suka Tafi basu yi Sauri ba Muma da muke Duniyan Jiranta Muke na Tabbata da yanzu baku kai ga Daukan Wannan Matakin ba My Dear..!
Yusuf Dake Sauraran Safiya yace"Gaskiya ne Babe..! Yafada Cikin Sanyin Murya mikewa Tayi Daga Jikinsa,Tana Fadin"My Dear Tashi muyi mgana..!
Bai mata Musu ba ya Mike Zaune ya saka hannu ya kunna Hasken Dakin Suka Kurama juna ido Kan kirjinsa ta koma ta Lafe Tana Fadin"Ina da Wata Shawara My Dear game da Situation din Abba He Need a Help..ba na kai ka dai ba..Taimako yake Nema Awajenmu Dukkanmu matukar muna so ya samu Lafiya ya Daina Tuna Abunda ya Faru.!
Da Sauri Yusuf yace"Wata Shawara ce Babe na..?
Dagowa tayi Tana Kallonsa Hannunsa ta Riko Duka Biyun Tana Fadin"Bai Kamata ku bar Abba yana Fuskatar wannan Abun shi Kadai ba..Kada kuyi Treeting dinsa kamar su Baffa My Dear..Bai dace ace Abba yana Rayuwa acikin Daki ba ko Falo baya iya Fitowa Ahalin yana da lafiyar Kafarsa..Bai kuma Dace arika barinsa Shi kadai ba..Sai Tunanin Da ba"a so Sai yaRika Samun Matsugguni acikin Zuciyarsa ..Masu irin Laluransu suna Bukatar Wani a kusa Dashi a Koyaushe..Ba kamar yadda kuke Barinsa ya Wuni Shi kadai ba Hakan yakan Kara Haifar da Ruruwan Raunin Dayake Cikin Zuciyarsa..Abba yana Bukatar ya Riks Fitowa yana Sakewa yana Walwala,Ya Chanchanci yayi Farinciki..Duk Abunda Zai sakashi Farinciki Shi zAmu Rika Kokarin Yi agabansa muyi Keeping dinsa Yadda Tunani da Damuwa baza ma su samu Damar Nukurkusan sa ba..Kaga Ta hakane kadai Magungunan Likita Zai yi Amfani ajikinsa amfanin na Har Abada ba na dan Lokaci ba..!
Tunda ta Fara mgana ya kafeta da Ido Zuciyarsa ta Cika da Farinciki Da Alfaharin Samun Macen Kirki kamar Safiya DAmam ance Duk Tunanin Namiji Ita mace Tamkar Garkuwa ce Garesa Gashi Cikin Lokaci Tana Warware Musu mtsalan da Shekara da Shekaru suka kasa mganceta.
Girgizashi Tayi ganin yana ta Kallonta bai yi mgana ba tace"Bakace komai ba My Dear..?
Yusuf ya Lumshe ido Kafin yace"Ina Jinki..Zuciyata ce ta Cika da Girma da alfaharin Zamowa Miji gareki Babe na..Ina jinki cigaba da Fadamin yadda komai Zai Tafi Wlh har na Fara Ganin Abba ya samu Lafiya na Har Abada..!
Safiya tace"Insha Allahu Abba zai Samu Lafiya indai muka Taru muka Tallafamai..!
Na farko Abba zai Daina Zaman Daki Zai kasance yana Wuni a Falo,sannan Zamu samo mai Abubuwan da zasu Debemai kewa kamar su Karatun azkar da karatun Karamin Qur"ani wanda Zai Rika Karantawa koda yaushe....Ko Jaridu Domin yarika karantawa yana Sanin Abunda Duniya take Ciki..Littafan Karatun Daya Shafi Fannin sa Wato Physchology,Abu na gaba kuma ya Daina Salla agida ya kasance yana Shiga Cikin mutane ko da bada Wata Mu"amala ba,Ya rika Sallar Cikin Jam"i hakan ma zai kara Taimakamai sosai Wajen Rage Damuwa da Tunani Sannan ya kamata Mu Rika Haduwa dukkanmu Da Daddare muyi Dinner Tare,Bayan mun gama kafin kowanne ya Shiga Barci mu Zauna dashi muyi Hira Labarai na ban Dariya wadanda Zasu Sanyashi Nishadi sannan kuma ya zama Dole ya rika ganin kowa Cikin Walwala ta hakane Shima zai yi kokarin manta komai sabi da ku..Masu irin Laluran Abba suna Bukatar taimakon Mutanen Dake kusa Dasu...!
Bata gama mganarta ba tajita a Jikinsa Ya Rumgumeta Kamkam Kamae wani Zai kwaceta Cikin Farinciki yake Fadin"Tanque so Much Babe na..Allah yayi miki Albarka..U are a Bleesing From Allah..!
Safiya itama ta saka Hannuwa ta Rumgumshi Tana Fadin"My Pleasure My Dear..Is My Duty Amtsayina na Matarka na Tallafeka a Dukkan Komai na al"amuranka Shine Zamantakewar..!
Kamkameta Kawai ya karayi yana Fadin"Alhamdulillah..Allah ne Abun godiya..!
Sun Dauki Tsawon Lokaci ahaka kafin ya Dagota yana Share Mata Guntun Hawayen Dake Idanunta Itama ta Saka Tattausan Hannunta ta Gogemai Nashi a Tare suka Sakarma Juna Mirmishi Hancinsu ya Hada Waje Daya yana Fadin"I love u Babe na..!
Itama cikin Wani Shauki Tace"Love u More and More My Dear..!
Komawa sukayi suka kwanta Bayan ya Dauketa Gabadayaanta ya Dorata Saman Jikinsa,Ya Kashe Musu Hasken Dakin Lokaci Daya ya ja musu Blanket yana Fadin"Oya Barci..Zamu karisa mganar dq Safe..!
Tana Dariya tace"Ok..My Dear..!

*****
Washegari Wasu Zukatan sun Tashi ba Dadi yayinda Wasu Zukatan suka Tashi Cikin Farincikin,Cikin Wadanda Suka kwana Cikin Bakinciki Imran ne Farko Kwata kwata Barci Barawo ne kadai ya iya sacesa Daya Runtse ido Sai ya rika ganin Inteesar Sanda Take Tofar da Miyau Lokaci Daya da. Toshe Hancinta In kuma ya yi Shuru kunnuwansa Amon Muryanta suke ji Inda Ta Kallesa Tana Kiramai Ta"awizi kamar Taga Shedan kwana Yayi Busa Sigari sai da ya karar da Kwalaye uku kana ya Saurara Gabadaya Bakincikin Yadda bai Sauyama Yarinyar nan kammani bane ya kamashi,Daya sani ko Mari ya Tsinketa Dashi ya Tattakata Wanda nan gaba bazata Kara Raina wani bama Shi ba,Ammh Takaichinsa Daya Da ya bari ta Subucemai ya Zama Dole ya Nemi Sagir ko wacece zai Santa Koma Daga ina take yana da Masaniyar komai ya Zama Dole ya Nemota ko domin yaci Ubanta ya Nuna Mata Karyanta Imran Ba wajen Wasanta bane.
Bangaran Inteesar kuwa Tayi kwanan Farinciki Hankalinta kwance Tuni ta manta da wani Imran Ballatana Abunda ya Faru Daman koda Mama ta Dawo Ta gaji ta Fara jin Barci Sama Sama Sukayi mgana tace mata ta Shiga Makota ne,Daganan Ciki Ta Shige.Bayan Ta Tatarra Littafanta,Tayi Sallar Isha"i tabi Lafiyan Gado Barci ya Fara Daukanta Taji Mganar Sagir din nan Falon Mama Ita dai bata kara Samun kanta ba sai da asuba da Mama tasheta Sallah.
Bayan ta idar da Sallar ne Tayi azkar ta Fita Tsakar gida Taga Mama na Shara ta gaisheta sai ta amshi Sharan Mama bata Hanata ba tunda Umma tace ta rika bata kowani aiki ne Saboda Ita Macece Domin amfanin kanta Watarana.
Ita ta Share Tsakar gidan Tas ta koma ta Gyara Cikin Dakin da Falo ta Share ta Goge kafin ta gama Mama ta Dafa mata Ruwan Zafi sai ta Juye tayi Wanka Koda ta Fito 7:30am na Safe kuma ta Kira Classrep dinsu yace mata 8am suke da Lacture,Shiyasa Take Sauri Ko Tea da Buredin da mama ta Hadamata bata Tsaya Sha ba Complex Kadai ta sha..Sai Cake Data Diba ta saka ajaka ta Dauki Littafanta ta Fito Tana yima Mama Sallama ta Dauki Kudi ta bata taki amsa tace Tana da Kudi a Hanunta Jin Haka yasa Mama Ta kyaleta ammh Sai ta Buga ma Sagir Kofa tace ya Fito ya Raka Intee ta samu abun Hawa Zuwa makaranta.
Haka kuwa akayi Shi ya Rakata Har Bakin Titi suna Tafe suna Hira sai da ta Samu Abun Hawa Zuwa Cikin makaranta Sannan ya Dawo yayi wanka ya karya ya Fita Zuwa Shago yau bai da Shiga makaranta sai Gobe.
Bangaransu Yusuf da Amaryansa Safiya Lafiya kalau suka Tashi Cikin Farinciki ba domin ya Hanata Fitowa da Wuri ba da Tun Safe taso ta Fita Kitchen Ta Taya Munari Hada Breakfast,yusuf ya hanata sai dai ta Tayashi Shirya wa zai tafi Wajen aiki Domin ya Sanar da yayi aure ko Zai Samu koda Hutun Sati Daya ne..Dukkansu sunyi wanka Safiya ta Shirya Cikin Daya Daga Cikin kayanta na Gida,Shi kuma Yusuf yana Sanye da kananun kaya ne,Sun Fito Falon kenan Sukaci karo da Munari ta Fito Daga Dakin Abba itama Cikin Shirin Fita Tana ganinsu ta Washe baki Tana Fadin"Mr and Mrs Yusuf Abubakar Malami.. Gud Mrning..!
Tafada Tana yar Dariya Yusuf ya Kalleta Lokaci Daya yana Lakuce mata yacw"Mrning How was ur Nite..?
Safiya tace"Lilsisy kin Tashi Lafiya..?
Munari tace"Lafiya Lau Anty Safiya..Ya yusuf Yanzu Abba ke Tambayanku..!
Yusuf yace"yanzu Wajensa Zamu Shiga..ya karya..?
Kai ta gyada mai kafin tace"Eh yau kunun Gyada nayi mana Sai na Soya Dankali..Yanzu na gama bashi yasha na bashi mgani Sauri nake tayi Yaya Zan Shiga makaranta 8am muke da Karatu..!.
Yusuf yace"Sannu da kokari..Bazaki jirani na Sauke ki ba..?
Agogon Fatan Dake Hannunta Ta Kallah Kafin tace"A"a Ya Yusuf bari na Tafi in na Tsaya jiranka Zan makara..!
Bai mata Musu ba ya Ciro 1k Cikin Aljihun Wandonsa ya Mikamata yana Fadin"Take Care..!
Ta karba Tana Fadin"Tanque Ya Yusuf..Anty Safiya Bye..!.Tafada Tana Daga mata Hannu,Hannun itama Safiyan ta Dagamata Tana Fadin"Sai kin Dawo ki kula da kanki..!
Mirmishi Tayi musu kafin ta Fice su kuma suka Shiga Dakin Abba suka Iskeshi yana Zaune kan gado yana Tunani Kasa suka Zauna suka Gaisheshi ya amsa yana Saka musu albakar.
Yusuf ya Kalli Abba yana Fadin"Ya karfin Jikin Abba..?Hope dai ba Wata Mtsala..!
Abba ya Girgizq kai kafin yace"Ina Samun Sauki..!.
Atare Shi da Safiya suka amsa da Allah ya kara Lafiya Kafin Yusuf ya Muskuta yana Fadama Abba Shawarwn da Safiya ta kawo Abba ya Dade kansa na Kasa kafin ya Dago ya Murmusa yana Fadin"Cikamakon Mutum Shine Samun Mace ta Gari...NAgode sosai yata..Kuma nayi Miki alkawarin Zan baki Kowani Hadin kai Domin Tamkar Munari nake kallonki..Sannan ni kaina Ina son na Warke Ko Domin na Koma ga Yan"uwana da Mahaifiyata..Itace araina Domin In har ina da Rai akwai Hakkinta Daya Rataya a Wuyana..!
Yusuf ya kalli Safiya itama ta Kallesa suka Gyada kai atare Kan Safiya na kasa Tace"Insha Allahu Zaka Samu Lafiya Kamar baka Taba wannan Laluran ba. !
Abba yace"Allah ya amsa..!.
Suka amsa da Ameen sun Dade Zaune Abba yana ta Tambayan Safiya matakin Karatunta Tana Fadamai sai ga Abba na Hirar Karatu da Safiya Data gayamai Fannin Data Karanta yake Fadamata abaya Daman yace in bai Zama Malami ba zai zama Masanin Na"ura ne .
Sai ga Yusuf Farinciki yaki barinsa Ransa Har sukayi ma Abba Sallama suka Fice,Su Biyu Suka yi Breakfast Saman Dining sunayi suna Hira Bayan Sun gama Safiya ta Rakashi Har Haraban gidan bata koma ba sai da Taga Fitar sa Daga Gidan kana ta Koma Cikin Gidan.
Dakin Barcinsu ta koma ta gyara Shi Tsaf kana ta koma ta Tatttara Abunda suka Bata Daga Dining zuwa Kitchen Tana ganin yanayin Kitchen din bai Wani Samun gyara Saboda Munari ce Ita kadai kuma Saboda makaranta Bata Samun Lokacin kanta Ballatana ta Tsabtace Kitchen din
Ga kwanukan Wanke wanke nan Kamar sun fi na kwana Biyu Munari bata samu Damar wankewa ba,Nan Safiya ta Zage ta wanke komai ta maidaahi a Muhallinsa,Ta kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login