Showing 153001 words to 156000 words out of 236322 words

Chapter 52 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

768

wai a ina kasan Soyayya ma haka Daka ke fadin cewa ina sonta tana sona da karfin Gwiwanka ko ka taba Soyayya ne ban sani ba.,?
Sagir yace"Ni ba irin ka bace..ina shiga Social media ina Hulda da abokai ina Karance karance nasan abubuwa da yawa kan soyayyah ammh ni ban Taba soyayyah ba sai dai irin na yarinta..!
Imran ya saki karamin Tsaki yana Fadin"Shirme kenan..Ni ko na yarinta ma ban yi ba..!
Sagir zai yi mgana kenan akace Mota ta Cika a Hado kudin Mota Dole ya Dakata Imran ya bada Kudim Mota ya Shiga Gidan gaba Key din mashin din Daman yana Hannun Sagir nan yace ma ya riketa a wajensa Har ya Dawo Sagir bai bar tashan ba,Sai da Motar su Imran tatashi Kana ya bar Wajen Cikin kewar Imran din.
Sai da suka Dauki Hanya kana ya Lalubo Wayarsa ya Danna ma Inteesar Kira ammh bata Dauka ba Koda baya son nuna Damuwarsa Dole Damuwar ta bayyana Sako ya Tura mata.

"Zan yi doguwar Tafiya ba Allah ya Kiyaye Hanya..?

Haka ya Tura mata bai saka Ran Zata bshi amsa ba san sai ga Sakonta daman Lokacin Daya Kira suna Lecture ne.

"Allah ya kiyaye Hanya..'
Daga haka bata kara ba,Sai da ya Murmusa daya ga Sakonta ganinsa kawai yayi yana Rubuta mata.

"I miss u....!

Ya tura mata bai kuma damu daman Data bashi amsa ba kamar yadda itama Data gani kamar yana gabanta ta Turamai baki tana fadin"Ba wani nam..Kai da zakaje wajen Wata..!
Ranta kuna yake in ta tuna haka sai dai bata isa ta kankare kalmar Sajida matar Imran bane.

Tunda suka Fara Tafiyar har suka kai bai yi mgana da kowa ba amotar duk da na kusa dashi da Direba da wasu a baya sai Hiran yadda Harkan Tsaro ya Tabarbare sukeyi a kasar nan namu ya Takura matuka da Hayaniyarsu sai dai ba yadda Zai yi bai Tofa bakinsa ba an Tsaya wasu sun siya Ruwa da abubuwan ci na saman Hanya ammh ko Shi ko abunda ba"a so bai siya ba,Har na Kusa dashi ya Siya Buredi da Ruwa yamai Tayi ya Girgiza kai Sunyi Gudu soaai koda 12pm na Rana tayi suna garin Gombe Daganan ya Hau Mota zuwa Dukku Goro kadai ya Tsaya a gombe ya siyama Daada Tunda tana ci sama sama.
Daya saura na Rana ya iso Dukku Daada na cikin Dakinta taji Baba Asabe nayi ma Imran maraba mamaki ya kamata lokacin Dataji sunansa Bata yarda ba ta Zata bataji Daidai bane Alwala ta Dauro tana Kokarin Tada Salla Imran ya shigo Dakinta da Sallamarsa Cikin Kaushunsa Koda yaushe.
Takalmin kafarsa ya Tsaya ya Cire nan Kofar Dakinta kafin ya kariso baki ta Saki Tana kallonsa Cikin mamakin ganinsa Shi kuma gabanta ya karisa Fuskarsa bata bayyana Fara"a Sosai ba sai dai ya Saki Ransa ba kamar yadda ya Saba ba,Har gabanta ya karisa cikin Dan yakensa yace"Daada..!
Daada data kasa mgana ta shafa kansa Daya dan rankwafa agabanta yana gaisheta tace"Kai nake gani ko kuwa Idanuwana ne suka Fara Rauni ne..!
Mirmishi yayi kafin yace"Nine Daada..!
Daada Farinciki ya kamata ta kamasa suka Zauna saman Darduman Data Shimfida bakinta Har kunne Tana Fadin"Masha Allah Sannu da zuwa yanzu kake tafe Imrana? Ya wajen Malami da sauran yan"uwamka ko ba daga gida kake ba domin munyi mgana da Mahaifin naka da Safe bai ce min kana Tafe ba..!
Yana Sauke Jakar Bayansa yake Fadin"Daga gida nake Daada..Wannan Tafiyar ta takanas ta kano Taki ce Daada..!
Yafada yana Kallonta Cikin Jin Dadin yadda yaga Tana Murna da ganinsa Cikin Jin Dadinta tace"Kai..Aikuwa naji Dadi sosai ka kyauta..Yau ina Zuwaira Allah ya jikanta tazo taga}? yau da kafarka ka tako zuwa Dukku Domin ka Dubani..,!
Kai ya kada yayi kafin yace"Allah ya jikansu da Rahma..!
Daada ta amsa da Ameen daidai Lokacin Baba aasabe ta shigo mai da Faranti shake da Ruwa da ababen sha,Suka gaisa sama sama ta Fice Ruwa kadai ya Tsiyaya yasha,Kafin ya Ciro goron Daya siyama Daada a aljihunsa ya mika mata ta Karba Tana ta Godiya da saka albarka kamar ya bata Duniya Duk sai yaji Tsausayinta ya kara kamashi ba,tun yau ba yasan Daada Tana matukar kaunarsa Soyayyar Datake yi ma Abba ne ya Shafesa.
Mikewa yayi Dauke da Jakarsa yana Fadin"Daada yi sallar ki..Nima bari naje nayi wanka nayi Sallar na Dawo wajenki nazo akwai mganar da nikeso mu Tattauna..!
Daada na Mirmishin Farinciki Tace"Shikenan ina jiranka..!
Daga haka ya Fice Dakin da suka Sauka shi da Sagir wanchan karon nan ya sauka yayi wanka ya Sauya kaya Saboda duk yaji kayan sun Damesa Karamin Wando ya saka 3Quater,da Wata karamar riga yayi Sallah kafin ya Dawo dakin Daada Baba asabe ta jera abinci mai Rai da lafiyan nan ya Zauna gaban Daada Tare sukaci abinci White rice da Miyar kaza Bai wani ci da yawa ba Daadan ma haka Kunun aya dai yasha da yawa suna yi suna Hira sama sama Sai da suka gama Imran ya Kira Abba ya Bama Daada sukayi mgana.
Sai da suka Natsu Daada nacin goron da Imran ya kawo mata ta kalleshi yana Zaune gabanta yadan Kishigida Daga Jikin gadonta tace"To ina Sauraranka Jikana..Allah yasa kan mganar Tarewar Sajida ne adakinta yau da nayi Farincikin da ban taba yi ba..!
Imran kallonta kawai yayi bai yi mgana sai chan ya Mike Zaune Dakyau ya gyara Zama yana kallon Daada kafin yace"Ita ai Tun Washegarin Ranar da aka Dauramna Aure na gama da babinta..,!
Daada ta Kalleshi Cikin Tsoro kafin tace"Bangane ba..?
Dan Mirmishin Saman lebe yayi kafin yace"Manta da wannan mganar Zamu yita Daga baya..Yanzu dai kan mganar yarinyar nan ne ta kawo ni Daada...plz zan Roke ki kada ki aura mata wannan yaron basu dace da juna ba Infact ma bata sonshi kada ki kware ta kamar yadda kika kwareni..!
Yafada kai Tsaye yana Kallonta Daada Tayi Sagale tana Bin Imran da kallo Tana auna Wasu abuubuwa acikin Ranta,
Cikin Karin Haske data ke so Daga Wajensa tace"Wata yarinya kenan..?kuma dame na kwareka..?
Imran kai Tsaye yace"Inteesar mana Daada..Da yaron nan na wajen Baffa Kabiru wachan zuwan namu kina cewa ya nemi yardanta..,!
Daada tana kara Nazarinsa tace"To menene mtsalan Imrana..!
Imran ya Dakuna Fuska yana Fadin"Mtsala Daya Daada bata son sa kuma bai dace da ita ba..!
Daada ta dade shuru batayi mgana ba ganin haka yasa Imran ya Rike duka Hannayenta yana Fadin"Daada kada ki yarda da mganarsa..Wlh inteesar bata sonsa koda yazo yace miki wani abu karya yake yi..kada ki Saurareshi..,!
Daada ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Naji bata sonshi..To wa take so..,?
Imran ya tabe baki yana Fadin"Ni bansani ba abunda kawai na sani bata sonshi kuma amtsayina na Dan"uwanta bazan so hakan ya kwareta ba..!
Daada ta Kallesa ido Cikin ido kafon tace"Kai kake sonta kenan shiyasa kace kada na yarda da mganar mai sunan megidana Hamisu..?
Abazata yaji mganar da Sauri ya Kalleta yana Nazarin mganarta meyasa Daada itama tace ko yana son Inteesar ne Hade rai yayi yana Fadin"Nifa ba sonta nake yi ba..Ni fa ban ma sani ba ko ina sonta ko bana sonta..!
Daada Tayi mirmishin su na manya akallah dai a shekarunta Zata iya gano Inda Imran ya dosa domin ta ma Lura Shi kanshi baisan yana son Inteesar din ba Zuciyartsa ke jansa yana aikata wasu abubuwan baisani ba.
Saboda ta kara Tabbatar da Zarginta ta gyara Zama Tana fadin"Naji bata son Khamis kai ma baka sonta..To na yarda da mganarka ature mganar khamis daman akwai wani yaro dan kawata Aina"u tuni take son mu Hada Zuru"a da ita sai nayi mata mgana yaje ya ganta su Sasanta nasan Zasu Daidaita..,!
Ai kamar Daada ta Zubamai Wuta haka yaji mganar nata,Kallonta yake kai tsaye yana jin Zuciyarsa na suya Daada na Lura dashi Tana Dariya acikin Ranta.
Bata rai yayi yana Fadin"A"a daada baza"ayi haka ba gaskiya..!
Kai Tsaye tace"To ya za"ayi.?ko kana da wanda za"a hadasun ne nifa bana son na Mutu ban aurar da duka jikokina ba Daga Mazan har matan..!
Imran yayi shuru yana wani Tunani Kafin kai Tsaye ya kalli Daada yana Fadin"Ni zan aureta Daada shikenan..!
Daada ta saki Dariya aranta tace Dan kwal uba kama Dawo Hanya ne..
Kai Tsaye tacemai"Sajidan fa..?kasan bazaka Hada jini Daya kishi ba ko..!?
Tabe baki yayi yana Fadin"Daada matso kiji..!
Kunnenta ta kawo ya rada mata mganar da baisan kome yace mata ba Naga dai Daada ta Zaro ido Tana kallonsa kafin tace"Innalillahi wa"inna Ilaihirraju"un Imrana meyasa kayi hakan..?
Batare da Shakka ba yace"Saboda Hakan kadai ne mafita Daada..Kiyi Hakuri ban iya cika Miki Burinki ba..Ammh ki bani Auran Inteesar na miki alkawarin bazan baki kunya ba..!
Daada Cikin jimami tace"A"a itama ai baka sonta bazan baka ita a maimaita abunda ya Faru ba..!
Da Sauri yace"Bazai faru ba Daada..Nifa ina son ganinta kusa dani ban Tsaneta ba..Kinga ai zan iya Zama da ita ko..!?
Yafada batare ma Daya sani ba Daada Tayi Shuru batayi mgana ta shiga wani Tunani,acikin Ranta bata isa tace ma Imran A",a ba kodomin ta gyara Kuskuranta na baya na Auramai Sajida Domin gyara Zumunci sai dai abubuwa sun Faru marasa Dadi.maimakon Zumuncin ya gyaru sai abubuwa suka Lalace a mganganun Imran ta Lura yana son Inteesar wannan ne karo na Farko Daya nemi wami abu a wajenta bazata hansa ba Tunda ya kasa Rike abunda ke Ransa yazo ya gayamata kuma Tabbas Zatayi amfani da wannan Damar ta nuna ma Mami Asma"u kuskuranta ta kuma Nuna ma Kabiri sakacin da ya aikata,
Duk da abunda Imran ya aikata bataji Dadinsa ba Da Sajida da Inteeaar duka nata ne,Sai dai gwara hakan gwara ayi abunda za"ace gwara da akayi da Abunda Daga baya za"a zo ana nadama ita kanta Daga wannan Datayi bazata kara aikata irin wannan Kuskuran ba.

Daada na chan na Nazarinta ita kadai Imran ma nayin nasa shi fa a Tunaninsa zai yi Taimako ne Tunda Inteesar bata son khamis bazai bari a aura mata shi ba,Kuma bazai yarda Daada ta kawo wani ba Shiyasa yace Zai aureta ba domin ya yarda da mganarsu na cewa ko yana sonta bane baiyi Beleving kan wannan abun ba.
Daada ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Zan yi mgana kan auranka da Inteesar kuma bamai Tada mgana ta..Sai dai kaima ina so kamin wani abu Guda Daya..!
Kallonta yake yi bai yi mgana ba Daada ta gyara ZAma Tana Fadin"Da Farko Dole zaka Dawo Imran din ka Dana sani..Ka daina shan Taba ka koma aiki ka zama Mutum wanda zai iya Rike mace saboda Nauyi ne zai Hau kanka Ina so don Allah ka Dawo Rayuwarka ta baya komai yayi Tsanani Saukin sa na wajen Allah indai zakamin wannan alfarman nayi maka alkawarin Karshen Wata Zan kira kowa da kowa kuma baza"a Watse ba sai da auranka da Inteesar da yardan Allah..!
Kamar Daada tayimai gafara haka yaji Cikin Farimcikinsa Daya kasa Boyuwa yace"Insha Allahu Daada..!
Daada taji Dadi sosai ta Rika sakamai albarka Kiran La"asar ya tadasu ya tafi yayi sallah Daya dawo ya shiga ya kwanta yana Barcin gajiya bai tashi ba sai gabda mangariba Ya tashi yaje yayi salla ya Dawo barcin yammah Cikin kunci ya tashi ga kuma Fushin Inteesar bata Kirasa ba sai shima ya Shareta.
Da Daddare sun sha Hira Daada Shi kanshi yana ta mamakin kansa ko Saboda Rabi Hirar Daada ke yinsa kuma Duka Labarkn Anni ce shiyasa yake jin Dadin Hirar kuma bama Haka ba Zuwansa Dukku yazomai da Sauyi sosai yaji Dadin zuwansa Wajen Kakarsa sai alokacin yake jin Dadin da Sauran mutane ke ji in suka zo wajen kakkaninsu bai taba Samun kusanci da Daada ba sai wannan karon.
Washegari daya tashi da Safe yaga Kiran waya da bakuwar lamba ba adadi,ga Sako yayi mamakin wanda ya Kirasa,sai dai sakon Daya gani ya bashi amsa Sajida ce.
Tsaki yaja yayi Bloking dinta ya Share Sakon nata Domin baya Bukatar Wata mu'amala da ita bashi da akala da ita
Ita kuma Daman Umaima ta saka Ta Tambayan mata Munari ita kuma ta Turo ma Umaiman ta Tura mata,Shine ta Dinga Kiransa bai Dauka ba ta Turamai sako Daga baya ta Dinga Kira bai shiga ba ta Fahimci ya Kulleta ne Tayi kuka sosai kamar Ranta Zai Fita kuma ta Dora Bleeminng din komai kam Mami Tama ganin koma menene ya Faru itace Sila,Shiyasa bayan sun gama Test tayi zamanta a Hostel bata Dawo gida ba saboda Haushin Mami Asma"u take ji.

Sai ga Imran dayaje Dukku da Niyyar kwana Daya ya shantake har kwana Biyu sai dai Ranar Lahadi da Safe Bankin GTB, Reshen Jahar kano suka Turomai sakon suna son ganinsa Karfe 8:00am na safe tayimai a Office din Manaja Ranar Monday abaya bai Damu ba da aikin ba,ammh yanzu ya Damu ko Saboda mganar Daada,Khalil ya kira ya gayamai sun Dade suna mgana yana bashi Shawarwari da Kwarin gwiwa kafin suyi sallama alokacin yayi shirin Tafiya Kano da shirnsa ma ya shiga Dakin Daada yayi mata sallama Tana ta mamakin Tafiya ba Shiri yace mata wani abu ne ya taso.
Kamar kar yatafi haka Daada taji shima haka sai dai ba yarda zatayi haka sukayi sallama karfe 12, yana gombe,Daganan ya Hau Motar kano sun samu Goslow a hanya da kuma Wahalan Mai yasa basu shigo da Wuri ba sai bayan mangariba suka Shigo kano.sai dai su Abba suka gansa kamar Daga sama.


*Naji Sauki Sosai...Nagode da addu"o'inku..Allah ya bar Zumunci Ameen..*



*Shakira*
3/22/22, 23:15 - Ummi Tandama???i: *GMB2??T??13*

*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*

Ganinsa Kamar daga sama bai sa wani ya Tambayesa Dalilinsa ba,Sanin halinsa shiyasa ba wanda ya Damu daya cemai wani abu ko Abba ya saka ma Ransa ya gaji da zaman Dukkun ne Shiyasa Lokaci Daya yaji dawowa gida,ba wanda ya kawo Tunanin wani abu,Shima baice ma kowa komai ba so yake sai komai ya tabbata ya bama Abba da Yaya Yusuf a big Suprise.
Inteesar da Munari suna gidan Tunda Mama bata dawo ba,Bai bi ma ta kanta ba saboda Ransa ya baci da abunda tayimai Yayi Doguwar Tafiya ko ta Kirashi Taji lafiya ya sauka Shiyasa yayi shigewarsa Daki bayan ya barsu afalo tare da su Abba Ko kallonta ma bai yarda yayi ba ita kuwa Tana kallonsa Cikin wani Shaukin Dake Fitowa daga kasan Ranta.
Wanka yayi ya sauya kaya yayi Sallar mangariba,sannan ya fita yaje Kitchen ya Hada Tea ya Fito Dauke da Mug din kan Dinning ya zauna yasha Abunsa Inteesar da duke zaune afalon Tana ta satar kallonsa sai kuma Taga ko kallonta ma bai yi ba yana shan Tea dinsa yana Nazarin abubuwan da zai Faru gobe shiyasa yana gamawa ya mike ya Fice Daga Falon Inteesar ta Bisa da kallon kauna.
Masallaci ya nufa,Saboda yaji kamar an Tada sallah Su Abba ma sun tafi tun Dazu,koda yaje Raka"a Biyu ya samu Sauran sai da ya Rama yana cikin Masallacin Abba da Ya yusuf suka Fice Sai Sagir ne ya Jirasa ya idar suka Fito tare.
Akofar gidan su Sagir din suka Tsaya Sagir na Tambayansa ya sukayi da Daada bai gayamai ba yadai cemai komai lafiyalau Key din mashinsa ya amsa,yace ma Sagir gobe da Safe akwai inda Zashi ganin Imran din bai gayamai inda zashi ba yasa Shima bai Tambaya ba,Ba Dadewa sukayi Sallama Sagir ya Fada shagonsa Shima Imran din ya wuce gida.
Da wuri ya kwanta Saboda akwai Gajiya ajikinsa Har ya kwanta ya Tuna da Inteesar karamin Tsaki yaja kawai Mikewa zaune yayi ya Dauko Wayarsa ya Kirata alokacin bai da Riga Dagashi sai Boxer Imran ko ana Sanyi baya shiri da Zafi kwatakwata
Wayar ta shiga sai dai bata Dade Tana Ringing ba yaji ta danna mai Nomba busy,ido ya waro yana bin wayar da kallo Zuciyarsa na Zafi kamar Shine Inteesar Zata kashe ma Waya..?Shi Imran..?ko abaya ba wacce ta isa ballatana ma yanzu Dayake jin kansa Daidai da kugun kowani Dan iska Shiyasa Tun Farko baya harkan mata Saboda Raini,Inteesar ta gama Rainasa Wato saboda taga yana mata Dariya Shine Zata Kashemai waya ga Dan iska ta samu ko..? Ko ma ace yaje Wajen Sajidan ne da gaske ta isa ta Hanashi zuwa ne?Shifa Namiji ne kuma yaya yake gareta ya bata Shekaru ba iyaka in Haihuwar kaji ne zai iya Haifarta Wlh shi Namiji ne Mijin Mace Hudu wata mace bata isa ta Zauna tana Raina mai wayau ba Ko Wacece ita kuwa,Ahaka ne Sagir ke cewa yana sonta..?aikin banza in taji ma wannan mganar sai Rainin nata ma yayi yawa shifa ba macen da Zata Zauna yana bata Hakuri yana Lallashinta yana da abubuwan yi masu Tarin muhimmanci da suka fi bata Lokacinsa kan Shirme Duk yadda Ransa ke Tafasa haka ya kanne ya Cije yayi ma kansa alkawarin Fita Sabgarta Domin Tsira da Mutuncinsa sai dai yadda yake ji game da ita ya Kasheshi daya zauna yana Fuskarta Raini da wannan Wulakanci a wajen yarinyar da bata wuce yar Cikinsa ba badai shi tama haka ba ko..? uhm Fushi Ta Cigaba da yi daga yau har Mahadi ya bayyana yafita Taurin kai da Zuciya.
Duk yadda yaso barci ya Kwasheshi a wannan Daran ya kasa,sai da ya tashi Sauran Sigarinsa Daya siya a Dukku,Tun Da yaje bai wuce sau biyu yasha Sigari ba yana da Sauranta ita ya Dauko ya Dinga ban kama Cikinsa Har sai da yaji Zuciyarsa ta Cunkushe Kirjinsa da Kansa sun yi masa Nauyi kana ya Hakura ya koma ya kwanta yana Sauke Numfashi Daya bayan Daya.
Ya Dade bai yi barci ba sai chan Dayayi Ruf da ciki duk da ba kyau ammh bai da Zabi,yayi Filo da Hannayensa saman Fuska sai Lokacin ya samu barci yaso ma ya makara ba Domin Abba ya Bugamai Kofa ba sanda Zasu masallaci shi da Yusuf Dakyar ya iya tashi da jan kafa ya shiga Tiolet,in ya Tsaya yin wanka zai Rasa Salla Shiyasa ya dauro alwala yabi bayan su Abba zuwa masallaci Allah ya Taimakesa an Tada Sallar ammh ba"a kai ga Ruku"u ba,Bayan an Idar da Sallar ya Dade yana addu"an Nasara a Rayuwarsa yana addu"an Samun wannan aikin Duk da Manaja Tunde ya bashi Tabbacin ammh bazai kwanta da hakan ba ayanzu yana Bukatar aikin Ko domin cikama Daada alkawarinta,Uwa uba kuma Lokaci Yayi da komai zai Sauya ko domin ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login