Showing 90001 words to 93000 words out of 236322 words

Chapter 31 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

762

da ya"yanta yadda suke Fadan Halinta sam Inteesar batayi mamaki ba ko Daga ganin yanayinta,Daganan Hirar Mami Asma"u ya Shigo itama da ya"yanta Sai Hankali suna mgana sukace duka Laifin na Baffa Kabiru ne Shine ya Sakarmata Komai da kuma da Fifita Boko Fiye da al"adunn Addinin Musulunci,Suna labarin Halayyar Sajida kaf na Uwarta ne ta kwaso gwarama Umaima sau Dubu Sajida ga Rashin kunya ga ba kwaba sai Sangarta da Sakarci kamar wata yarinya Duk Inteesar na jinsu ita dai bata Tofa ba sai dai kawai ta Murmusa aranta Tana fadin ita Taga Rashin kunyar Sajida tun lokacin ta Gama Sanin Halinta kaf ta kuma san inda ta ijiyeta..
Sai gabda mangariba suka gama aikin white rice ne sukayi da Miyar Naman Rago sai Ferfesun kaji da Daddy ya bada kudi su Basheer suka Fita suka Siyo sai Salat da Lemon Aya da na Kankana suka Hada,Daganan kowa ya tafi yayi sallah Su Umma da su Inna Maimuna daman suna Falo suna kallo suna Taba Hira Mami kuwa da ya"yanta suna Daki basu Fito ba koda Umaima tace zata je Kitchen hanata Tayi.
Inteesar dai bata iya Sallah ba Sai da ta Watsa Ruwa kana ta gabatar da Sallah Tana Kan darduman har aka Kira Insha"i tatasshi ta gabatar ta Idar ba Dadewa taji Hayaniya afalo kenan Mazan sun Dawo daga masallaci sun Shigo kenan,Tana nan zaune bata tashi ba Hafsah tazo tayi Sallar Isha"i tace tazo su je su Taya Baba Asabe kawo su abinci Karima na Wajen tace Su Anty Aneesa gasu chan suna kwasowa jin haka yasa bata yi yunkurin Fita ba sai da Hafsah tace ta Fito suci abinci kana ta Fito duk da bama ci Zatayi ba ita abu mai Ruwa Ruwa Zata sha Shiyasa tana Fitowa Kitchen ta Nufa ta Tsiyayo Ruwan Zafi a Flaks ta Hada tea a wani karamin Mug ta Fito dashi da Cokali Tana Juyawa Daki tayi niyyar komawa Domin yau cin abincin basu Daddy suna Dakin Daada suna mgana Matan ne sai Ya"ya sai jikoki sai Tattaban kunnen Daada Dake Tsalle Tsallemsu afalon.
Har takai Kofar Dakin taji an ce"Ina Zaki..?badai bazaki ci abinci ba Inteesarr..!
Yadda ya fadi mganar ne Cikin Wata Murya yasa ta waigo Khamis ne ko ya Kureta da Mayen kallonsa kauda kai Tayi Tana Fadin"Eh am ok..!
Sai da ya wani kalletaa kasa kasa kafin yace"U are ok dame..? Me kikaci..?
Takaichi da Haushi suka kama Inteesar ba ita kadai ba Hadda da Mami Asma"u da Sajida da basu ga Dalilinsa nayi ma Inteesar mgana ba.
Rausayar dakai tayi Cikin Kosawa Tana Fadin"zan sha Tea..!
Tafada tana Dagamai Mug din Dake hannunta Zai sake mgana Mami Ta Kallesa Kafin tace"Khamis plz kaci abincinka Tace She is ok ko Dole ne..?
Tafada Cikin Halin ko in kula Umma naji batace komai ba sai chan Tace"Intee bamai cin abinci bane..Tafi daman shan Ruwan zafi in Zata kwanta.!
Mami Ta tabe baki Kafin tace"Plz Help me.. tell Him..!
Daga haka ta Tsuke bakinsa Shima bai kara mgana ba sai Binta yake yi da kallo Itama Juyawarta Tayi ta zata Shigo Dakin Sa"id ya Kirata ta waigo Cikin Girmansa yace"Ya Zaki tafi..? Da fa mun gama cin abinci zam karbi lambar kowa..Kowa kuma zai yi Sharing Cantact dinsa da Dan"uwansa..!
Yake Inteesar Tayi kafin tace"Ya Basheer plz ka bashi Cantact dina..!
Harara ya Dago ya Sakarmata yana Fadin"Ni dan aikin ki ne..?
Shagwabe mai Tayi tana Fadin"Plz Bro..plz Mana..!
Kallonta yayi kafin yace"Ok..Naji kafin ki samin kuka..!
Dariya tayi har sai da Fararan Hakoranta suka Bayyana tace"Tanque Bhaya..!
Sa"id ne yace"To in an bamu taki na Sauran fa yaushe zaki karba..?
Da sauri tace"In d mrming kafin mu tafi Insha Allahu..!
Kai ya jinjina kafin yace"Is ok..Buh ki karba kisan Is very Important..!
Kai ta gyadamai kafin ta Juya ta Shiga Cikin Dakin tana Sakin Sirrin Tsaki Aranta Tana Zagin Khamis kallo kamar Wani maye yayi ta Kallonta Haba ita fa ta kosa Gobe Tayi subar Gidan nan ta koma Tayi Shirin komawa makaranta Munari tace itama bazata Shiga School ba sai in ta Dawo su Shiga gabadaya.
Tana gama Shan Tea dinta ta Haye gado Ta gaji Barcine a Idonta Lokaci Kadan baeci ya kwasheta Sama Sama Tana jin Tashin mgangansu Daga Falon Daada.
Su kuwa sai wajen 11pm Taron ya tashi Adaran Sa"id ya Bude group din ya Karbi Lambar Kowa ya sakashi,Daga kan iyaye har kan Kanne da yayyi irinsu,Ya kuma Umarci Kowa ya Karbi Lambar kowa,haka akayi sukayi ta Sharing din Cantact din juna da alkawarin Kiran juna Lokaci bayan Lokaci,Umma daman Tana da Mami sai dai su yi Wata Biyar ba wacce ta kira Kowa acikinsu Sai ta karbi ta Inna Maimuna da Inna Bintalo yaran yaran kuma suka Karbi da junansu,Umaima ce ke bata Lambarta Cikin Dadin rai banda Sajida har gwarama Mami ta bata nuna wani abu ba Ba wanda na yabi ta kanta Ballatama ya Damu da ita banda Hafsah ba wanda ya karbi Lambarta,Sai ya"yan Inna Bintalo Daman Hadeje ce da kano,Lambar Inteesar kuwa Umma ce tayi ta badawa Mazan kuma Basheer ya basu Wannan abun yafi yima Khamis Dadi Domin Hanya mafi Sauki kenan Wajen Cimma Burinsa kan Inteesar da Tunda ya Fara ganinta Tunaninta da Soyayyarta suka yi mai mugun kamu basu barshi yayi barcin Kirki ba.,Love at first sight kenan
Su Daddy kuwa sai Wajen 12pm suka Fito Daga Wajen Daada suka ci Abinci suka Nemi makwanci Nasihohi ne Tayi musu sosai mai Shiga jiki wanda Har sai da shi kanshi Baffa Kabiru ya yarda da Kuskuransa kuma yayi ma Daada alkawarin Inshu Allahu zai gyara Daganan suka Shiga Hira da Tsara yadda Zasu Hada hannu dasu da ya"yansu su zama Zuru"a Daya ba Wariyar Launanin Fata shi ya bata musu Lokaci basu Fito da wuri ba.
Ranar Daada Tayi barcin Farincikin Data Dade batayi ba.
Washegari Tun 4am na asuba Kowa ya Tashi saboda Sammakon Tafiya,ko kafin karfe bakwai na Safe Masu Shirin Tafiya duk sun Shirya Baffa Kabiru suka Fara Tafiya Sadam wanda Zai je kano Inteesar ta karbi Lambar Matarsa Aneesa tayi mata alkwarin in ta koma kano ZAta zo Gidansu tunda tace suna Sharada Phase3 ne da Zama.
Daga sune sai Sa"id da zasu je Dutse Tare suka Tafi da Hafsah tunda Tana Wajensa ne itama sun karbi Lambar juna ita da Inteesar,karfe tara na Safe su Inteesar suka Mika Hanya sun bar Inna Maimuna na Shirin Tafiya ita da ya"yanta sai sun Biya ta Bauchi Inna Bintalo kuwa sai gobe Zata koma,gida duk yayi Shuru tunda Baki sun Watse Daada ta Bisu da addu"an Allah ya kaisu Gidajensu Lafiya kamar yadda suka zo hankalinta bai kwanta ba sai da Kowa ya Kira yace ya sauka Lafiya Har Inna Maimunatu da suka Tafi Daga baya suma sun sauka Bauchi lafiya sai dai kuma wani Haduwar In Allah ya nufa.

******

*Kaduna.*

Tunda suka dawo Daga Dukku Inteesar ke shirin komawa makaranta Taso tafiyar nata ya Zama Alhamis Sai Daddy yace bari Asabar ko Lahadi sai ta Koma,bata so ba ammh bata da yarda Zatayi Ganin zaman gidan ya Isheta yasa taje gidan Nasara ta Kwana Daya gidan Ya Basheer ma ta Kwana Daya gidan su Inno ma Tayi kwana Daya Ranar Jumma"a tadawo Saboda Shirin Tafiya Umma ta mata Miya da Dambun kaji sai kayan Snkas Sai sauran Tarkace irin su madara Indomie da Complez wanda Zata tafi dashi sai kuma Dinkuna da Daddy ya Sake Dinkamata umma ma ta Dinka mata Kala Biyu duka guda Biyu iri Daya Munari tace takai ma Kala kala Daya sai ta bar wasu kayan nata agida ta Kara Dibam wasu kayan ta Hada da Sabbin Zata koma Dashi.
Suna waya da Hafsah tunda suka koma ita ke kiranta mai sonka ka soshi itama Tana kiranta Har ta bata Anty Fareesa su gaisa Ya Sa"ad kuwa shima ya Kirata sau Daya suka gaisa Tayi Saving din Lambarsa ya Sadam kuwa Kusan Kullum sai sun kirata shi da Anty Aneesa wai ko ta Shigo kano ne tace a"a Shi Ya Sadam din har kiran Daddy yayi yana Rokonsa Inteesar ta Dawo Gidansa da Zama Daddy ya basa Hakuri yace bazai yuyu inda take ma Duk gida ne ammh yayi mai Alkawarin Zai gayamata ta Rika Zuwa Weekend gidansa in ta Samu Dama da sukaji haka sukace ba komai.
Da Umma taji tace ai bakomai Tunda suna Garin Inteesar zata Rika zuwa Ita kanta Umma suna waya da Inna Maimunatu da ya"yanta Mami ce Sau Daya ta Kirata suka gaisa Sama Sama tace Tana Kotu ne Daganan basu kara mgana ba group kuwa su Ya Basheer suna Kokarin ingatansa Inteesar dai bata taba mgana ba Tana dai Shiga ta Karanta Sakoninsu,Ba Laifi su ya Sa"id suna Hira da dadddre haka in sun Dawo daga aiki Daddy ma yana mgan ba Sosai ba,Baffa Kabiru ne sai dai Turo Mrning Text da Gudnigjt ba wanda bai Ciki Harda Sajida ammh itama bata Taba mgana ba Sai Khamis ya taba mgana da Umaimah Shi khamis taji Ya Sa"id na mganar ya koma Wajen aikinsa Shiyasa aka jisa Shuru.

Inteesar Tafiyarta bai samu Asabar ba Sai Lahadi Da Sassafe Ya Basheer ya Tafi kaita banda Daddy ya tashi da Ciwon Kafafu sai kawai Yace Basheer ya kaita wannan karon ma sai da Inteesar Tayi kuka sai dai suna Daukan Hanya ta Warware suna Hira da}? Ya Basheer har suka iso Misalin Karfe 11am na Safe suka isa Lokacin ko Shago Sagir bai Bude ba Tunda Daman Ranakun hutun mako bada Wuri yake Bude Shagon ba.
Sai dai Mama Taga almajirai na Shigowa da kaya sai ga Sallamar Inteesar Mama ta Fito Daga Daki ita da Sagir tana mata Maraba Rumgumeta Tayi Inteesar tana Cewa Mama nayi kewarki sosai.
Mama tace"Nima haka yata..ai tun jiya da Salaha tace zaki taho nake ta Zura ido..Tafiya bata yuyu ba sai yau..!
Ya Basheer Dake baya Dauke da akwatin Inteesar yace"Wlh Mama sai yau Allah yayi..!
Maraba ta shiga musu Sagir ya bashi Hannu suka gaisa suka Rankaya zuwa Falon Mama.
Bayan gaisawa da Tambayan Mutanen Gida Mama ta kawo musu Kunu da kosan Datayi yau da Safe Ya Basheer yasha kunun sosai Inteesar nema taci Kosan kawai.
Ya Basheer ya bama Mama 20k in ji Daddy sai Kayan abinci da suka zo mata Dashi Tana ta Godiya Inteesar kuma ana Ciki tana gyara kayanta Sai da Ya Basheer yayi Sallar Azahar yayi Shirin Tafiya Mama tayi tayi ya Ci abinci yaki wai bayaso yayi Dare Ahanya Hakanan sukayi sallama Har Bakin Mota Inteesar da Sagir suka Rakashi Sukayi sallama suna Dagamai Hannu har ya Fice Daga Layin sagir Shagonsa ya Shiga Tunda Yaransa Har sunzo sun Bude shagon sunyi Shara,ita kuma sai ta koma Cikin Gida.
Ashe Ya Basheer ba Gida ya dau hanya ba Gidan Ya Sadam yaje Daman ya gayamai zai shago kano Dawo da Inteesar makaramta da kwantance sai gashi agidan Chan suka Hade suna Hira Aneesa Tamusu lunch sukaci Sai Karfe 4pm ya bar gidan yadau Hanyar kaduna Sai da Inteesar din ta Kira Anty Aneesa ta gayamata yau ta Dawo
Shine take Fadamata Yanzu Ya Basheer ya bar gidansu Inteesar taji Haushi tace bai Fadamata zai biya ba data Bisa Aneesa tace haka yace ma Sadam dayace meyasa bai Dauko ki ya kawo ki kin ga Gidan ba Sai yace baya son ki batamai Lokaci ne.
Inteesar bataji Dadi ba ammh sun Rabu kan Insha Allahu Zata zo ko Cikin Weekend din da zai kama ne.
Suna gama Waya ta Kira Munari tace mata Ta iso Munari sai murna Kamar Zata Tsinkama Inteesar dodon kunne ta Kashe wayar Tana Mata Dariya

Munari kuwa Daman Tana Dakintane itama tana gyara Kayanta da mai wanki da guga ya kawo ne Sai gata ta Fito da gudu Tana Murna Abba Dake Falo Shi da Ya Yusuf suna Hira kan Yadda Harkan Tsaro ya Tabarbare a kasar nan Gefe daya kuma suna kallon NTA news na Karfe 4pm.Anty Safiya kuma na Kitchen Ta fito tana Tsalle.
Abba ya Kalleta yana Fadin"Munarin Abba meyafaru ne..?
Jikin Abba ta Fada Tana Fadin"Abba Intee ta tadawo..!
Tafada tana Washe baki karaf sai a kunnen Imran Daya Fito Daga Dakinsa sanye da wani 3Quater wando mai Ruwan madara Jikinsa ba Riga da Farko Daya fito yaso ne ya isa ga Munari ya bata wani Kyakyawan mari da sai ta kusa suma kan Ihun banzan Datake musu acikin gida sai dai sunan dayaji ne ta ambata ne yasa ya Tsaya Cak ya kasa Karisawa,Saboda yadda gabadaya Kirjinsa ya amsa Harda gangan jikinsa..
Abba dake Mirmishi ya shafa kan Munari yana Fadin"Ah Dole kiyi murna..Aminiya ta dawo ko..?ai sai tashi aje ayi mata sanu da zuwa..Nima kice ina mata barka da Dawowa..!
Da sauri Munari ta Mike tana Fadin"Yanzu kuwa Abba..Ya Yusuf ina Anty Safiya..?
Yace"Tana Kitchen..!
Gudu ta kwasa Zuwa Kitchen din tana Kiran sunan Anty Safiyan}? Abba da Ya Yusuf suka Bita da Kallo Abba yace"Allah ne ya Hada kauna Tsakanin Munari da yarinyar nan yadda suke son juna Kamar wasu yan"uwa.!
Ya yusuf yace"Sosai Abba Daman haka Rayuwa ta gada..Wani abokin ko kawa sai ya koma maka kamar wani Dan"uwanka..!
Abba ya jinjina kai yana Fadin"Gaskiya ne..tashi muje masallacin naji ana ta kira tun Dazu..!
Atare suka mike Daidai Lokacin da Imran ya koma Ciki da kallo suka Bisa Kafin su girgiza kai suna mai addu"a cikinsu ransu fita sukayi Daman sunyi Alwalarsu sun Fito da Niyar tafiya Masallaci ne labarin wani Hari da yan kiddaping suka kai kauyan Zamfara yaja Hankalinsu.
Sun Fita ba Dadewa Imran ma ya fito Bayan ya saka Jallabiya ya Nufi Masallacin Zuciyarsa sai Zafi take yi maimakon yaji sanyi Tunda wacce yake jiran da neman ganin ta Dawo sai dai ta sabamai alkawari Shiyasa yaji bama yasan ganinta.
Tasan Wahalar Daya sha Saboda rashin ganinta..? Tunda Lokacin komawarsu makaranta yayi yake Duban Hanya saboda ita a Shagon Sagir yake wuni ko zai ga Dawowarmata ammh Shuru Sai ranar yaji Munari na Fadin ba Satin zata Dawo ba Tundaga Ranar yaji Ransa ya gama baci ya tsani ayi mai alkawari a kasa cikamai baisan Dalili ba Yaji baya son ganinta kwatakwata Duk da kuwa yadda Zuciyarsa ta azalzalu da son ganinta din.
Suna Dawowa masallaci Munari ta Shirya tatafi Gidan su Sagir chan suka Hade Inteesar da sai Murna chan ta Shantare sai bayan mganariba Inteesar ta Rakota dauke da Sakon Umma Munari nata Godiya suka rabu kan sai gobe da safe Munari zata Biyo ma Inteesar su shiga makaranta.







*Shakira...*
3/22/22, 23:07 - Ummi Tandama???i: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:JanaftyB??0
{*



*??T??27*


Washegari Monday tun Karfe 7:40am Munari ta biyo ma Inteesar suka Shiga makaranta basu jira Ya yusuf ba Tunda shi sai 8am zai fita BUK old Site suka nufa anan suke lectures dinsu a wannan Zangon karatun na Biyu,Zangon karatunsu na farko Gabadaya sun yishi ne a New site,sai jifa Jifa suna shiga Old site din yin wani lectures din.
Sai 5pm na yammah suka Dawo gida Daga bakin Titi mai adaidaita ya ijiyesu suka Tako da Kafarsu zuwa Cikin anguwa Inteesar ce ta Roki Munari ta shigo Ta diban mata Dambun nama da kayan Snaks din Data zo dashi Munari bata da yadda zatayi Dole ta bita suka Shiga gidan Tare ta gaida Mama kafin su Shiga Ciki,Bata wani Dade ba Saboda mangariba ta kawo jiki Abinci sukaci Tuwon Shinkafa Miyar Zogale Mama tayi Sai Inteesar ta Diban mata Dambun naman da yawa dasu Samosan da Cincin da Springrool,da Donot Tace ita dasu Abba Munari ta rasa bakin godiya Domin alkharin Inteesar gareta mai fadi ne haka Jiya Data nuna ma Abba kaya yana ta Saka albarka,Basu baro gidan ba sai da Inteesar ta kira ma Munari Umma suka gaisa Tayi mata godiya.
Da inteesar taje raka Munari ta mtsamata sai da ta shiga suka gaisa da Abba da Anty Safiya Ta nuna musu Abunda ta kara bata Abba nata Saka mata albarka Har taji kunya,Itama bata Zauna ba tayi musu Sallama Zata tafi ta Fito Falon kenan Munari ta Rakota taga Imran zaune gefen Abba Yana mai mgana ya kauda kai yana kallon wani gefe Daga alamun dai Fada Abba kemai Shiyasa Fuskarnan ba Annuri..
Lokacin Dayaji Muryanta sai da gabansa ya amsa haka Itama Tana ganinsa taji wani Sanyi ya Shigeta acikin Jikinta Lokaci Daya Duk yadda yaso kada ya Dago ya Kalleta ya kasa sai da Zuciyarsa ta Rinjayi gangar Jikinsa ya Dago yana kallonta Daidai Lokacin itama Shi take kallo,Yanzu adakin Munari ta gama Tambayansa Munari tace ita duk yau bata gansa ba yana Dakinsa sai gashi sun hadu.
Lokacin da suka Hada ido sai yaji kamar Zuciyarsa tayi Tsalle waje Daya ta Daina aiki Da Sauri ya kauda kai ya Hade rai Yana wani Dakuna Fuska ganin shi yasa Munari ta fasa Rakon da Zatayi ma Inteesar zuwa Haraban Gidan.
Ita kuma Inteesar sai ta kallesa kafin tace"Ina yini Ya Imran..!
Haka muryanta a bazata cikin Sanyinta akoda yaushe yi yayi kamar bai jita ba,Sai da Abba yace mai bai ji ana gaisheshi bane kana ya amsa yana wani Tattare giransa Waje Daya..ita dai bata bi ta kansa ba Tayi ma Abba Sallama Daganan suka Rabu da Munari duk da daman ta san Munari ta na matukar Tsorom Imran kamar Ranta bazatayi wani kwakwaran Motsi agabansa ba..
Duk da yana Fushi da ita kan taki cika alkwarin datayi mai bai Fasa ganin ta Rame ba,Kuma Zuciyarsa bata Fasa jin Dadin ganinta ba,muryanta kuwa Dayaji kamar wani Waraka ne Daga Garesa haka yake jin kansa ya rasa gane Meke Damunsa Ballatana ya Dora hakan kan wani Mizani.
Cikin Satin kaf su Inteesar basu samu Zama ba Saboda Karatu kullum in suka Shiga makaranta sai yammah Suke dawowa,Saboda sun Fara Karatu ne Gadan gadan ba zama Ga kuma assigment da suketayi akwai wadanda aka bada lokacin basu Dawo ba Shiyasa basu da Lokacin kansu sam.
Ranar jumma"a Karfe 7:30am suke da Lecture tun 7:20am Inteesar ta gama Shiryawa ta Fito kofar gida Tana Jiran Munari sun yi mgana tace mata gatanan Fitowa Tana Sanye cikin Doguwar riga atamfa Gold,mai kalan Brown sai da ta saka Karamin mayafinta Sikiws,sai bakar jaka da Bakin Takalminta mai dan Dudu sai wasu littafai a hannunta.
Sakamakon Lokacin yayi Safe ne da yawa ba Mutane sosai sai Daidai ku ne ke Wucewa sai yara masu Haraman zuwa makaranta.
Tana nan Zaune Tana kallon Shashen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login