Showing 222001 words to 225000 words out of 236322 words

Chapter 75 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

778

Dauramata Drip tana kwance Tana Fadin"Kaico na..Kaico na ni Asma"u..Ya"yana mijina..!
Haka take ta Fada tana Kuka Hajiya Turai Jikinta ya gama yin Sanyin Ta Fita Taje wajen Justice tace ya Kira Kabiru ya Rokeshi yazo su Daidaita da Asma"u yace bazai Kirasa ya Tursasa ba Sanda yake bama Asma"u baki ai bata Jisa ba Shi ba Ruwansa abunda ta Zabama kanta kenan.





*Shakira...*
3/30/22, 20:57 - Ummi Tandama???i: *GMB2??T??30*


*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*

Asma"u ta rasa ta ina Zata farama Hajiyarsu bayanin abunda ya Faru Kunya take ji ita kanta in ta Tuna Kabiru yayi mata Allah ya isa ya Fada ya kara Fada Allah ya isa bai yafe mata ba Ta ina Zata Fara wazata Tunkara da zai saurareta Ballatana ya Fahimceta duk inda taje itace akasa Bata da gaskiya tabi son Ranta da son kanta Eh mana gaskiya ne Tana da son kamta mana in ba Domin haka ba da ta Duba Ya"yanta da Mijinta ta ijiye son Ranta da Tabi Ra"ayi da duka Muradan Mijinta da ya"yanta Kaiconta haka take ta Fada Tana kuka kamar Zatayi hauka.
Hajiya Turai ta Damu kwarai da gaske ganin haka yasa ta samu Mami Asma"u tana kwance bayan kwana Biyu Da kiran da Kabiru yayi mata Gabadaya ta Fige ta rame Ita kanta tasan bata da lafiya Jiri take gani in ta Mike duk da mgungunar Likita ammh Saboda bata cikin Kwamciyar Hankali ko sau Daya mganin bai mata amfani ba Batama sha sai Hajiya tazo ta mtsamata to gani take ko ta sha bai da amfanin Halin Datake ciki Mgani bazai Lafar da komai ba bazai Hana Wutar Nadama da kuskuran Data aikata ci acikin Zuciyarta ba.
Kwance ta sameta yaraf kamar ko yaushe kamar kayan wanki gabadaya Jikinta ya gama saki kamar mai Cutar Shanyewar barin jiki ba na barin Jiki bane na Mutuwar Zuciya ne
Kuka Take na Boye dana Sarari hawaye sun riga sun gama Samun Matsungguni akan Fuskarta Kukan Zucci kuwa Shi take kwana Tana wuni Tanayi,batare da tasan Hanyar da Zata Dakatar da hakan ba
Har Hajiya Turai ta shigo ta Zauna gefen gado kusa da Mami Asma"u bata sani ba ta Riga tayi Zurfi Cikin Tunanin Daya Zameta abun yi akoda yaushe Zafafan Hawaye suna Kwaranyomata.
Hajiya Turai Ta Kira sunanta Har yafi sau uku bata jita ba sai da ta Tabata kadan Tare da Girgizata Lokaci Daya Kafin tayi Firgigit ta dawo Cikin Hayyacinta daga Zurfaffan Tunanin Data Fada idonta ya sauka akan Hajiyarsu Saurin Share kwallah Tayi kafin ta yunkura ta mike Tana Fadin"Hajiyarmu yaushe kika shigo..?
Hajiya Turai tace"Ina Zaki san na Shigo kin Shiga Cikin Tunanin ki na Fama..?sau nawa zan Fada miki wannan Tunanin da kike yi da kukan nan bashi bane Mafita ba,Likita ya Fada miki ki Daina yawan Tunani da Damuwa saboda Jininki ya Hau sosai..!
Mami batace komai ba illah kanta Data sadda kasa Hawayenta na Diga har kan Cinyarta,Kafin tace"Ya zan yi Hajiya..?kukan shi kadai ne mafita na Na Rasa komai na Rasa aurena na Rasa Ya"yana da Duka Martabana Hajiya ya zan yi..! tafada tana Kara Sautin kukanta
Hajiya Turai kai Tsaye tace"Akwai mafita ki nemi Kabiru ki basa Hakuri ku Daidaita kanku..In ya"yanku suka ga haka suma Hankulansu zai kwanta..Nasan nima nayi kuskurre a Mtsayina ta uwa gareki ban Fadamiki Gaskiya ba sai na rika Zugaki Har Kika Tafkan wannan Kuskuran nima sai Daga baya na Fahimci Bamu kyauta ba Dagani har ke shiyasa nake so ki gyara Kuskuran ki ki same sa ki basa Hakuri ya maidake Dakin ki Daga baya sai komai ya Biyo baya..!
Mami Tasaki Mirmishin Dayafi kuka Ciwo kafin tace"Ai bazai Saurareni ba Hajiya..Gabadaya Tun bayan Faruwar lamarin Ya yanke duk wata Hanya da zai sa mu hadu..Bazai taba Saurarata ba Hajiya na Rantse..!
Hajiya Tayi shuru kafin tace"To ya za"ayi kenan..?
Gashi kuma Justice yace bazai Kira sa ba..!
Mami Asma"u batace komai ba ta koma Ta kwanta Tana jan majinan kuka,Hajiya Turai ta girgiza kai kafin Ta tashi ta Fice Cikin Nadaman Gudummuwar Data bata Wajen Kashe ma yarta aure da Lalata gabadaya Mafarkinta Tabbas itace sila in da a mtsayin ta na Uwa ga Asma"u ta bi Hanyar daya Dace da duk haka bai Faru ba Mami kuwa kuka kawai take Tana Tunanin mafita haka take Wuni ta Kwana cikin Daki bata Fita Tana Tunanin mafita da yadda Zata gyara Abunda ta bata....
Tayi ta Kiran Lambar khamis bata Samesa ba Ta Kira Wayar Sajida ta shiga ammh bata Dauka ba,sai Daga baya ta Kirata Daga yanayin Muryanta tasan bata da lafiya ammh sai tace mata taji Sauki Mami batabari Sajidan ta gane bata da Lafiya ba sai ta Boye mata adaran Jiya Ta samoma kanta mafita Batare da ta Yi shawara da kowa ba ita kadai ta Bata kuma ita kadai Zata gyara.
Bata cikin karfin jiki Jiri ma take gani Ta Riga Tama Direban da zai Tukata mgana Tun Safe ta Shirya ba wani Shiri Tayi ba Kamar ba Asma"u yar gayu ba Tuni Gilashin idonta ya kama gabansa ma bata san isalinsa ba Tana ta kanta ne Figai Figai da ita ta Fito Ta Samu Hajiya Turai ta Fadamata Zata je wani Waje sai yammah Zata dawo.
Hajiya Turai ta kalleta sai dai batayi mgana ba ta mata Fatan Dawowa Lafiya.
Daganan ta Fice Direba ya Tukata suna Fita tace mai Dukku Zataje ba Musu ya Take Mota suka Dau Hanya ta Riga ta gama Neman ma kanta Mafita Zuwa dukku shine Mafitanta zataje ta Duka har kasa Ta bama Daada Hakuri ba domin Kabiru ya maidata Dakinta ba ko Zata ga Haske a Rayuwarta Sajida tana Halin cutar da taki barin Ma a Dubata ballatana agane meke Damunta ga Khamis ya koma Wani iri,Irin yadda take aibata ya"yan wasu Kai innalillahi rayuwa ta Juya mata baya bazata iya ita Kadai ba Wlh bazata iya ba wannan Nauyin yayi mata yawa Tabbas bazata iya ba.
Har suka isa Dukku Mami Asma"u na kuka Hawayenta basu Tsaya ba lokacin da Baba Asabe ta shigo Dakin Daada Tana Fada mata zuwan Mami Asma"u din bata gama mamaki ba sai da Taga Mami Asma"u din Tsoron Allah ya kara kama Daada da Tsoron Duniya ganin yadda Mami ta koma Daada Sai Tayi kwallah Lokacin da Mami Asma"u ta Zube agabanta ta duka ta Dafa kafarta tana kuka Tana bata Hakuri Tana Fadamata irin Halin Datake ciki da Halin da Sajida ke Ciki da Halin da Baffa Kabiru yaje yaga Khamis aciki Mami Asma"u na Kuka hawayenta na Diga saman Kafafun Daada Dake Zaune take Fadin"Ki yafemin Daaada..Wlh nayi Nadama..Na Fahimci Abunda na aikatane duka suka Dawo kaina Daada Wlh bazan iya ba nayi Rauni nayi Laushin da bazan iya Daukan abubuwanan ba ni kadai Daada Kabiru ya Kirani yamin Allah yasa isa kan Ya"yansa Daada ina zan Saka kaina..?Wlh hakkin ku ne keda Imran da Malami da su Mustapaha da kukan da na Sakaki shine yake Bibiyata ban yi Tunanun kema kamar Uwa kike gareni ba ko Tsinemin kikayi sai na Bi Duniya..Don Allah da Zatin Allah Daada Kiyi Hakuri ki yafemin..!
Daada Kwallah sai da ta Cikamata ido Ta saka Hannu ta Dago Mami Asma"u Data Durkushe gabanta Tana kuka Hawaye Shabe shabe hannu Daada ta Saka Ta Share mata Hawaye Tana Fadin"Wlh ban ta ba Rike ki araina ba Asma"u na yafe miki..Kuma suma zasu yafe miki..Ai tunda kin gane Kuskuranki bawanda zai ki karban Tubanki..Kabiru bai Fadamin Halin Daya je ya Samu Khamis ba Bansani ba..Ammh Zan Kirasa baza"a Zura ido ba su hadu shi da yan"uwansa suje su Taho Dashi Damuwace tasa ya shiga Halin Daya shiga ammh da Izinin Lahi Komai zai koma Daidai ki Daina kuka bakomai Insha Allahu..!
Mami Asma"u na goge kwallarta Tana Fadin"Bayan Damuwa harda Silar Bakina Daada nayi ta aibata Imrana Ina Kiransa da sunayej banza..yau gashi Duka sun Tabbata kan Da"ana Daada Sakayyace Allah ne ya kamani Kaico na..!
Tafada Tana Kara Saka Kuka Daada na Lallashinta Cikin Zuciyarta Tana Tsausayin Kabiru Lokaci Daya Kaddara ta Fadamai Allah Sarki yana chan cikin wannan kunar ga Asma"u Yadda ta koma Ko da wannan ka kallah Zaka Gane Allah shine gagara Misali.
Bata yadda ta Fadama Mami Har Lokacin ita Matar Baffa bane sai dai ta Lallasheta ta kuma mata alkawarin Zatayi magana da Baffa Kabiru Sajida kuma zata dawo gida Domin asan meke Damunta Mami Asma"u bata jima sosai a Dukku ba Hankalinta ya kwanta jin Daada bata Riketa aranta ba Dakyar ta Tsaya taci abinci Sama Sama Tayi ma Daada sallama Direba ya Juya da ita,Daada ta bita da kallon Tsausayi.
Tana Tafiya ta saka Baba Asabe ta Kira mata Baffa Kabiru Dake chan yana Faman Kokuwa da Zuciyarsa shi kanshi Tun bayan Dawowarsa Anambara Da ganin Halin da Tilon Dansa ke ciki bai da Cikakken Lafiya yayi kuka har ya Gode Allah kwakwalwarsa Ta toshe yarasa Tunanin ma me zai yi..?ballatana ya Samu Mafita Lokacin Daada ke Fadamai zuwan Asma"u bai ji mamaki ba sai dai bai Zata Zata karaya haka Cikin Sauki ba ya Dauka Bata gama ganin komai ba yanzu ta Fara gani nuna ma Daada yayi karya Take duka kukan Munafunci ne Daga baya kenan bayan ta gama Lalata komai..?shi yanzu yadda zai Dawo da Rayuwar Khamis kamar baya yake Tunani Tunda Taje ta Fadama Daada komai,Daada tace maza ya Kira yan"uwansa aje a taho da Khamis Gida yafi a barsa chan inda bai da kowa abakin Daada yaji Labarin Rashin Lafiyar Sajida shi kanshi in da Zai kwanta adubasa Wlh Jininsa ya Hau har suka gama mgana Da Daada baya Cikin Hayyacinsa Hawaye da kuka sun Rufemai jinsa da ganinsa Allah yasa yana gida kwana Biyun bai je ko"ina ba.
Sai da ya Samu Natsuwa ya Kira Abba da Daddy ya gayamusu komai suma Hankalinsu ya tashi Daddy yace Da kansa zai hau jirgi zuwa Anambara Gobe zaiTaho da Khamis Basai Abba da Baffa Kabiru sun taho ba Yace Baffa Kabiru ya turamai Address din nan da nan kuwa ya Turamai sun Rabu kan Gobe zai tafi Sajida kuma Zai je Har makaranta ya Taho da ita Gida.
Ashe abunda basu sani ba Khamis bayan ya Dawo Daga Hayyacinsa budurwansa abokiyar Watsewarsa Tasa mai suna Suzana,Ta sanar dashi Zuwan Mahaifinsa da Halin Daya Tarar dashi,Batasan Baffa Kabiru ba ammh Kamarsu da Khamis da kuma cemata da yayi shi babansa ne aranar Dayazo bayan ta Budemai kofar Falon Gidan.
Gabadaya Jikin Khamis ya gama yin Sanyi Tsoron Allah ya kamashi da wani ido zai kalli Dad dinsa..?wata amsa zai bai bashi in ya Tambayesa meyasa ya koma haka..?yace Saboda Rasa Mace..?ya koma Sabama Allah..?wannan duka ba Hujja bane ya karya Zuciyar uban Daya Dora yakini akansa Tir da Rayuwar Daya Zabama kansa Tundaga Ranar ya Tattara komai ya Watsar Tare da alkawarin Har Abada bazai kara ko Busa Sigari ba ballatana Har ya Daga wata kwalba ya Rufe babin mata da komai na Harkan Shanshanci Har Abada ya Fara Shirin Tahowa gida Domin ya Nemi Gafaran Daad ya yafemai Laifin Daya aikata.
Aranar da Baffa Kabiru sukayi mgana da su Abba da asuba Khamis ya Sauka a Filin Jirgin Abuja Taxi ya samu zuwa Gida sai dai Baffa Kabiru da Umaima suka gansa Kwatsam Allah Sarki Rayuwa Khamis yayi kuka sosai Dayaga yadda ya tafi ya bar Baya da Kura Mami Ta Dade bata gida sun Rabu da Daad Sajida Tana makaranta Cikin Halin Ciwo shi kuma yana chan yana Shanshanci Kai consa,Abakin Umaima yake jin komai Domin Sanda ya iso Dad na cikin Dakinsa sai da ya Fito ya gansa..
Haka Khamis ya Duka ya Rike Kafafun Baffa Kabiru yana kuka yana Rokonsa Gafara Tare da alkawarin ya Daina Duka Abunda yake yi Har Abada bazai koma ga aikin Daya baro ba Me ya kamata Baffa Kabiru yayi banda ya Tallafi D"ansa da Allah ya Dubesa ya Karkatomai da Hankalinsa kan Hanya Madaidaiciya ya Rumgumesa yana Godiya ga Allah Hawaye na Ziraromai bai bari Khamis din ya gani ba yayi Saurin Dauke hawayen..
Nan da nan Baffa Kabiru ya Kira Daddy ya Fadamai ya Dakata da Tafiya Anambara ga Khamis ya Dawo gida da kansa jin haka yasa yayi Hamdala Daddy ya Kira Abba ya Fadamai Khamis ya Dawo gida Abba ma Nata Hamdala sun isa Barka.
Aranar ma Baffa Kabiru bai Fita ba yana Tare da ya"yansa Khamis da Umaima Domin ya Dauki Daraman Gyaran Duk inda ya Kuskure Domin Dawo da walwalan ya"yansa sun yanke Shawaran gobe da safe dashi da Khamis zasu je makarantan su Sajida su Taho da ita sai dai Misalin karfe Daya na Dare Sai ga wayar Mami Asma"u ta Kira Baffa Kabiru karo na Farko Bayan Lalacewar abubuwan Daya ga Kiran bai Dauka ba Tunda Idonsa Biyu Har Lokacin bai yi barci ba Mugun Haushinta yake ji Gani yake Munfuncine ba Tuban Allah da Annabi bane gani tayi ba Sarki sai Allah ta kuma Rasa komai Shiyasa ta Dawo Tana Rabe Rabe Macijiya.
Sai da yaga Kiran yaki ya kare kana ya Daga afusace ya auna mata ashariya ko Ta kyalesa sai da jinta Cikin kuka Tana Fadamai gasu a asibitin Specialist Hospital inda aka kawo Sajida bata da Lafiya Tana ta Tari da Jini Jin haka yasa Hankalin Baffa Kabiru ya kara tashi Cikin Tsananin Tashin Hankali ya Zura Jallabiya ya Fice Dakin Khamis ya shiga ya tasosa hankali Tashe yake Fadamai Halin da ake Ciki,Shima Hankalinsa ya Tashi Umaima ma Muryansu ya tasheta Daga Barcin Daya kwasheta itama jin Abunda ya Faru da yar"uwanta sai kuka Gabadayansu suka Dunguma suka Tafi.
Koda suka je sun Iske Mami Asma"u da Hajiya Turai da Justice Tafida yarkace yarkace sai kuka Take TanaTuma kamar Mahaukaciya Idanuwanta sun Kole saboda kuka Ita jenefer ta Kira saboda itace Lambar Karshe da Sajidan Tayi mgana da ita suna Kwance adaki Sanda Tarin ya Sarke Sajidan da Zafi Har ta Fita Daga Hankalinta Jenefer ita taje ta Fadama Maman Hostel dinsu ita kuma ta Sanar da kuma Hukumar makaranta aka Kwaso su zuwa asibiti bayan an Shiga Da Sajida Emergency ne Ta samu Wayar Sajidan ta Kira Mamin Ta Fadamata wanda Kurruwanta ya Fito da Justice da Hajiya Turai jin Abunda ke Faruwa yasa suka Rankayo Gabadayansu Cikin Tashin Hankali.
Ita uwa uwace ko ya ta Zama Haka Umaima da Khamis suka isa ga Mami Asma"u suka Dagota suka Rumgumeta suna Lallashinta Data kyalla ido Taga Khamis sai Rauninta ya bayyana ta Fada Jikinsa Tana Fadin"kaima ka Gujeni Khamis..Dad dinku ya sakeni Sajida Zata Mutu ta barmu Aman jini fa take..an shiga da ita Likotoci basu Fito ba Har yanzu na shiga ukuna na Lalace..!
Haka take fada Cikin kuka tana Rike Jikin Khamis da shima yake jin kamar ya Fashe da kuka Idanuwansa sun yi Jajir kukan Mami kuka ne da zai Kassara Duk zuciyar mai Sauraranta Ammh banda ta Baffa Kabiru bayan gaisawa da Justice Tafida da Hajiya Turai bai kara mgana ba sai gaisuwan abokiyar Karatun Sajida Jenefer Daya amsa ko Barayin Mamin bai kallah ba Ballatana ta saka Ran wani Rahma Daga bangaransa.
Gabadaya Hankula basa kwance Fin Mintina arba"in kafin Likitocin da suka Rufu kan Sajida su Fito basu tsaya amsa ma su Baffa Kabiru Tambayansu ba sukace jictice Tafida ya Biyosu Office shi da Baffa Kabiru Matan su Tsaya a waje.
Baffa Kabiru ya Razana Dayaji bayanin Likita kan Abunda ke Damun Sajida ta Hadu da Heart problem Ciwon Zuciya Wanda har ta Fara Tabuwa saboda matsanancin Halin Datake Ciki Ta fara ganin jini in tana Tari bata zo asibiti ba har abun yayi yawa,Ammh dai yanzu ta Fita Daga Cikin Hatsarin Datake ciki sai dai Duk Abunda akasan Tana son gani ko Tana so a kawo matashi gabanta da Zarar ta Farfado in ba Haka ba zata samu Heart Attack arasa ta gabadaya.
Baffa Kabiru Haka yake sharan kwallah Da Gaske Sajida take Tana son Imran Asma"u ta rabata dashi Gashi Soyayyarsa zai Zama ajalinta Shi kanshi Justice yaji Mganar sosai Jikinsa yayi sanyi shine ya iya Fita yayi ma su Khamis Bayanin da Likita yayi musu ai sai Wajen ya kara Rikicewa Mamin Har wani Suu Tayi Zata Fadi Hajiya Turai da Khamis suka Tarota kasa takai hannunta Saman kanta ta manta asibiti suke ta Kwarara Ihu Tana Fadin"Na shiga Uku..Na Shiga uku Ni Asma"u na lalace..!
Baffa Kabiru da Ransa ya baci Tana Neman Tara musu jama"a Allah yasa ma Dare da sanin su manyan Mutane ai da ba haka ba wata Gigitattaciyar kara ya Daka mata Cikin Kaushin Murya ya fara fadin"Dillah kima Mutane Shuru..Kukan Uban me kuma Zaki mana..?kukan karya da munafunci..?ko na nadaman Dole..?duk abunda ya Faru da Sajida kece Sila...ke kika Rabata da abunda take so kika yi Sanadiyar Shigarta wannan Halin sannan kizo ki Damemu da kukanki na Banza Baki bani kin Lalace ba Asma"u Sai Y'ata ta Rasa Ranta ta Dalilinki na Rantse da wanda Raina ke Hannunsa sai nayi Shari"a dake sai kin Biyani Diyar kashemin yata da kikay Muguwa kawai azzalumuma mai Zuciyar Zalunci wacce batasan komai ba sai kanta.!
Ya karishe Fada Cikin Sakarmata Jajayen Idanuwansa da suka Rine Saboda kuka
Ba wanda iya mgana sanin ai gaskiya ya Fada Mami Asma"u jikinta na rawa da bakinta ta kasa mgana Jikin Khamis ta koma ta Lafe Umaima ta Kwantomata Tana kuka ai ita kukan natama ya Tsaya ta shiga wani yanayin da bawa bai isa ya Fassara ba.
Hajiya Turai ne cikin Damuwa tace"Haba Kabiru don Allah ka Ragama yarinyar nan mana..Tafuskanci abubuwa da yawa ko baka Ragamata ba Saboda Zaman tare ba ai ka Ragamata saboda Daranjanmu iyayenta Dake Tsaye da su kansu Yayanku gasu nan da kuma Wacce ke kwance cikin nan Cikin Kokawaa da Numfashinta..!
Ai in ma ya Bude baki yace wani abu Allah Zagin Hajiya Turai zai yi shiyasa yayi Shuru ya Dauke kansa yana ajiyar Zuciya
Sai Wurin yayi Tsit sai Jan majinan Umaima ake ji Mamin kamar ai Wutarta ta Dauke justice kala bai ce Daman ba kuma zai ce ba Wanda bai ji bari ba bazai ji Hoho ba
Dukkansu Zaman jiran Farfadowam Sajida suke Gabadayansu suna asibitin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login