Showing 54001 words to 57000 words out of 236322 words

Chapter 19 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

775

Zasu je..? Abba ya kwabeta yace ina Ruwanta Tsakanin Miji da mata sai ta bata rai Tana Tura baki Abba da Yusuf suna Dariya Sanin shi yasan Inda zasu je.
Sallama sukayi ma Abba ya Rakasu da adawo Lafiya,
Wani Kamfanin saida Kayan Funuture suka Fara zuwa Tare da Safiya suka Zabi Kalan Bedroom da Falo,Dayan Bedroom din Dazai zama nasu Brwon and White sukace a Hada musu komai ,Dayan kuma da Zai Zama ko na Baki suka Hada Black and White,Sai Falo suka Hada Blue and Ash..Komai sai da aka Hada musu Harda su Cafet,kayan kallo,Sun siya Fridge Da wasu kanunun kayan Kitchen Tunda akwai karamin Kitchen a Ashashen,Ta Bank ya Tura Musu Kudinsu ya bada addreess Suka kuma Jadadda musu kayansu zai isa Kafin Su isa Gida Tare da Ma"aikatansu da zasu Hada komai sukayi musu godiya Daganan suka Shiga Kasuwa Safiya ta Zabi Kaya kama Daga less da atamfofi da Materials,Sai kayan Barci Da mayafi da Hijabi da Takalma bada yawa ya Siya mata saboda bai da kudi yace Sai sun kara Dawowa..
Suna Shagon Munari ta Kira Yusuf Take gayamai ga Masu kayan sun kawo nan yace Ta Nuna musu Shashen Dake kusa da Dakinta anan Zasu Jera Kayan Ta tayasu a Share Dakin,Munari tace ai Ta riga ta Share Dakin Bayan Fitansu Tayi Mopping Abba yace tagyara,Yusuf yace Shikenan ta Nuna musu su Jera komai suma gasunan zuwa..
Toh basu Dawo da Wuri ba Tunda sai da suka Biya suka kai Dinki Wajen Telan Da Safiya take kai Dinki Tun Tana Gida Kana suka Dawo sun Iske Tuni har kamfanin Tagama Hada komai sun Tafi..
Waje yayi matukar kyau sosai Munari ta Tayata dashi kanshi Yuauf din suka Kara gyara ko"ina Har Tv aranar aka Hadashi,Munari sai santi take Ita ta Tayata suka Kwaso kayansu Daga chan dakin suka Maidasu nan,Har Abba sai da yazo ya gani ya saka albaeka Imran ne dai bai Shigo ba,Daga bakin Koridin kawai ya Tsaya Daganan yayi Waje Shagon Sagir yaje Domin yanzu Chan yake Wuninsa,Tun Mganar nan da sukayi da Sagir na Zai bashi Sana"a Shikenan ya addabeshi Da kira wai yana Jiransa Dole yake zuwa ba Domin komai ba,Sai Saboda Sagir bai zai iya Ture alfarmansa ba, ammh ba wai Domin Ya koyi Dinki kamar yadda Sagir din yake Bukata Shi Aikinsa Daya ne aikin Banki ya Zauna kan kujera tana Juyawa dashi Lokaci Daya yana Sarrafa Computer shi aikinsa akwakwalwa yake,Bazai iya yima Sagir din gaddama ba Shiyasa yake Zuwa Sai dai Fara Zuwansa Shagon ya Takurama Yaran shagon basu da Damar Sakewa ko Hira ko Dariya in Har Imran na Shagon ba umh ba Umh ne ko Mganar Rada kayi sai yace ka Dameshi ka Fita yanzu yar Yar wakar ma da suke kunna Saboda Nishadin Dinki ba wannan Damar domin Ranar da suka Kunna Mp3 Din gabadaya Imran ya Rotsata da kasa ta Fashe,Tundaga lokacin Shagon ya Zama sai a Hankali,Yaran Sagir din Haushin Imran suke ji sai dai ba Halin su Furta Shi kanshi Ogan zai iya Bata Musu rai kuma ba komai yake yi ba
Illah ya Zauna Kawai yana bin Wuri Daya da kallo in yaji Nishadinsa ya Busa Sigari ko baka san Warinta baka isa ka Fita ba kuma baka isa ka Toshe Hanci ba Dole ka Shaki Hayakinta.
Shi Kanshi Sagir din yayi Nadaman Gayatton Imran din Domin ba yaransa Kadai ba Hatta shi ya Hana mai Rawan gaban hantsi ko Dinki Costumer suka kawomai Cinikayya sai dai su Fita Waje,Indai Imran na Shagon bayason Hayaniya da Takura,Sai dai ba yadda Zai yi Dashi Fada ne Kullum Kaca kaca suke Rabuwa,Bai kuma Hana gobe in Sagir yaji Imran din Shuru ya Kirasa
Har kuma zuwa yau bai kara ganin Inteesar ba,Har ma ya manta da Babunta.

******

*Kaduna..*
Da misalin karfe 8:00pm na Dare.

Shigowarta Bedroom Din kenan Dauke da Karamin mug,Wanda Ruwan Shayin Na"aNa"a,Alhaji Mustapha ne Zaune gefen gado Sanye da Jallabiya mai Ruwan Madara,Ya Zabga Tagumi da Hannun Bibbiyu Har ta karisa kusa Dashi bai sani ba,Domin yayi Zurfi Cikin Tunanin Daya Tafi kan Side Drower din Jikin gado ta ijye mug Lokaci Daya ta Zauna Gefensa Tana Fadin"Abban Intee..!
Ta fada Tana Ciremai Tagumin Sai Lokacin ya Dawo Cikin Hayyacinsa ya Fahimci Ta shigo Har tana Kusa Dashi.
Ajiyar rai ya sauke kafin yace"Bansan kin Shigo ba..!
Tace Tana Kallonsa"Ina fa Zaka sani kayi Nisa Cikin Tunani..kuma kasan yawan Tunanin illah ne ga Lafiyan Dan adam..!
Sauke Dayan Hannunsa yayi Daga Tagumin yana Fadin"Umh..Tunani ya Zama Dole Sahala..Wlh na kasa Sukuni Tunanin Halin da muka baro Daada aciki ne ke Damuna..!
Umma Ta yi shuru kafin itama Tace"Wlh nima Abban Intee..Daada ta kasa fa..Yaya malami kawai take son gani..Kaji fa Baba asabe Tana Fadin ko acikin Barcinta sunansa take kira..!
Ta karishe Fada Cikin Bayyana Jimaminta.
Alhaji Mustapha ya Sauke Twagayen Numfashi kafin yace"Ko achan Baya Soyayyar Daada ke ma Ya Malami ta Dabam ce shi din D'a ne masu Soyuwa gareta Duk yafi mu sanyin Hali Shiyasa yafi Shiga Ranta Dole Daada ta Shiga Damuwa Saboda Rashinsa Kusan kwanciyarta asibiti Biyu acikin Satin nan fa..!
Umma tace"Ni Tsorana kada Hawan jinin nan ya Fadar da ita kasan fa Mugun Ciwo ne..Daman ta Amince ko ku saka baki kai da su Hajiya Bintalo ta yarda Tabi Baban Sajida Abuja In ma Baba asabe take ji Duka su tafi Tare nan Dukkun sai a Rufeshi In Allah yasa ta Samu Sauki sai su Dawo ni aganina Chan zai fiyemata ko kobamai akwai gilmawar Wani nata agabanta nan kuwa sai dai in an Taka an je..!
Har tagama Mganarta bai ce mata komai ba sai Chan yace"Ai Daada alkwarin tayi ma kanta bazata bar gidanta Dukku Da Ranta ba..Sai dai in Gawartane ta yarda a Fitar da ita..!
Umma tace"ai kaji kuma..Allah dai ya bata Lafiya Wlh jiyan nan da muka isa Naji Tsoro Hakama Basheer yace sai da nayi kwallah Lokacin Data Rike Hannuwanku kaida Baban Sajida Tana Rokon ku ku Sadata da Malami kafin ta bar Gidan Duniya..!
Yayi kasake yana jinta Cikin wani yanayi kafin ya Mikamata Hannu yana Fadin"Bani Tea din..!
Ba musu ta Dauko ta mikamai ya karba yakai baki Kurba Daya Zuwa Biyu ya Dakatana Yana Daidaita Zamansa Lokaci Daya yana Fadin"Baki san wani abu ba Salaha..Jiyan nan da Barrister ya kirani yana gayamin wai Dr.Zubaida Ta kirashi tace Daada na asibiti Wajenta Itama Tana gidan Baba asabe ta Kirata jikin Daadan ya tashi na Tsorata..Duka Duka ko fa kwana Hudu batayi da kwanciya asibitin ba ta Kwana Daya aka Dawo da ita gida..Ciwon Daada wlh yana Tadamin da Hankali akoda yaushe Ina Rokon Allah Duk inda ya Malami yake Allah ya bayyanashi Daada nada rai kada Sai ta Mutu Hakkinta ya kamamu..!
Ya karishe Fada yana kara Kurban Tea din Hannunsa Umma Tayi Kasake kafin Tace"Hakki kuma..? Ai naga kuna iya bakin kokarin ku Wajen Nemansa bai kamata kace in Kun gaza Hakan Hakkin Daada zai kama kuba sai dai in shi Yaya Malami Tunda ko Yaya ka Lalace Uwa Uwace Har Abada kuma Tana da Nauyi da Hakki akansa..
Bai katseta ba sai da ta gama kana ya mikata mata Mug din ta karba ta Maidashi inda ta Daukosa,Shi kuma ya Mikar da kafarsa Saman Cafet din Dake malale a Bedroom din yana Fadin"Me kika sani Salaha..? Ai Duka Alhakin Barin Ya Malami Gida da Iyalansa yana Wuyanmu ne..Musamman Barrister Domin kinsan da Zafi sosai Alokacin da Abun ya Faru Ya Maalami ya Samu Depression kan Abunda ya Faru da su Yusuf suma ba wani Hop kansu sai yake ganin kamar Rashin Hakuri ne da rashin Yarda da kaddara yasa komai ya Lalace Har Laluran tasa tana ta gaba Kullum Likitoci suna cewa ba Cigaba..Dalilin haka yasa yayi ta Fada gaskiya munyi kuskure Domin naga wani Shiri,Tv Kwanaki Wani likita na mgana kan masu Fama da irin Lalurar Ya malami yace Ciwon Damuwa ne Ba Hantara ko Fada suke so ba ajashi ajiki Lallashi da ban baki a Zauna dasu adaina bari suna Tuna Abunda Zai sakasu Tunani,arika yin Abunda Zai sakasu Farinciki akoda yaushe kuma Tsakani ga Allah Bamu yi wannan kokarin ba Mun kawo su Duk???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ku Gaban daada Mun koma Garuruwan mu,bamu yi La"akari da Daada ta Fara Manyata ba, bazata iya wani Kokari ba..Sannan iyalansa suma Raunin ya Tabasu da Har baza su iya Taimakon kansu ba Ballatana Shi Yaya Malami Ahaka suka nuna suna son Komawa Gida kuma na Tabbata Saboda Wannan Dalilin ne sukayi nesa Damu bayan sun koma Lagos Sun ga ba wanda ya Damu dasu..Na Tabbata Yusuf bazai yi Tunanin Yin nesa da Kowa ba Face mai muradden Halin nan Duk Cikin Dangin mu Imran yaron yana da Zafi Daman Chan Tun Farko Bai da Shiga Dangi Sosai sai da ya Girma ne ma Ya malami ke Tarosa in zai zo Dukku..Ina da Tabbacin Shi zai ba Yayan Shawaran Haka Shi kuma Bashi da Zabi sai ya Yarda da komai Suna ganin yin Nesa Damun din Shine mafita..Tabbas muma da laifin mu..!
Ya Karishe Fada Lokaci Daya yana Saka yatsa ya Dauke kwallar Data gangaromai Umms Jikinta yagama yin Sanyi tace"Tabbas Hakane ba"a kyauta..Rashi ne sukayi Babba..Allah ya jikan Zuwaira Ya malami yayi Shuru Dole Ya Shiga Damuwa mace mai kirki Da Sanin yakamata Ga kuma Rashin ya"ya kai yaga Jarabawa Wanda bakowani bawa bane zai iya Tsallakewa Abban Intee in Wani ne sai ya kashe kansa..!
Yayin Saurin katseta da Fadin"Wlh Abun Allah ya kare..Hakama likitan yace ,Wani babban Likitan kwakwalwa ne Daga asibitin ABU Zaria yace Tabbas suna kashe kansu To zasu ga basu da wani Sauran Amfani a Duniya..Wlh jikina yayi Sanyi sosai ina so na ganar da Barrister kuskuransa ammh kuma Ban samu Dama ina ganin kamar Shi Har yau Laifin Ya Malamin yake gani..!
Umma tace"Wlh kuwa ai kaji Abunda yake Fada yau..Wai Malami ya Tafi Da gangan kuma gashi yanzu a Rashinsa zai kashe Daada..!
Umh kawai ya iya Cewa ya kasa Mgana,Umma ta Mike tana Fadin"Allah ya kyauta ka Rage Tunani Don Allah mu Cigaba da gayama Allah..Insha Allahu Allah zai bayyanasa..!
Ya amsa mata da Amen,Mug din Tea din ta Dauka Tana Shirin Ficewa yace"Bashir ya Tafi dasu Abiden ne..? Naji ban ji Motsin su bane..!?
Umma ta Dakata Tana Fadin"Ai Rigima suka sakamai nace ya Tafi Dasu Wajen Uwarsu..Tun jiya basu ganta ba..!
Ya jinjina kai kafin yace"Yaran ne akwai Rigima Irin Diyarki Intee..!.
Umma ta Tabe baki Tana Fadin"Diyar ka Dai..Ni da Tunda tatafi ta yadani..Ta kira jiya muna Dukku Tana Min tsiyan ta samu Mamarta Mai sonta ba irina mai Hanata Sangartanta ba..!
Mirmiahi yayi kafin yace"Ai gaskiya ta Fada..In wani yaki ka da wuni.Wani da kwana Dubu zai soka..ai zan bar ma Yaya Aminan ita kawai ta Aurar da ita achan mu namu gayyata ne Kadai..!
Umma tace"Wa Kai din..? Dama Zaka iya ne Abba Intee..Da Ya Amina Taji Dadi..ammh Sai dai kulafuncinta bazai barka ka barmata ita ba Jifa Tafiyar ta fa sai da kafi kwana Biyu Baka Walwala in ka Dawo Gidan nan kaga bata nan..!
Yana yar Dariya yace"Ai jiya Da Daddre na kira Inteen har tabani Ya Aminan muka gaisa Ta Tambayi Daada da Jiki..Sosai naga Inteer tana jin Dadin Zaman kano da Karatun na Gabadaya..!
Umma tace"To tana samun Damar yin sagartatan son ranta mana..!
Mirmishi ya sakarmata ita kuma ta Fice Tana Mita tana Fita ya Kwashe Kafafunsa zuwa kan gado ya gyara Kwanciyarsa Tunanin da baya so shi ya Shigayi Babban Tashin Hankalinsa Rashin sanin Inda Malami yake Domin har yau suna kan nema kuma ba wani Labari Daga kowani bangare Kuma an Tabbatar musu Tunda suka bar Lagos Har yau basu kara Takawa ba..
Ya illahi ina ya Malami ya Shiga Shida iyalansa ne..?Allahu ka bayyanashi ko Domin Damuwar Daada garesa..!








*Shakira..*
3/22/22, 23:05 - Ummi Tandama???i: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:JanaftyB??0
{*

}? }? }? }? }?}? *??T??17*

*Monday*
12:12pm
BUK

"Yau ta kama Monday ko"ina kabi Sai Hada Hada ke wakana Saboda Monday Tushen aiki ne,haka yake Gudana a Tsakiyar Jami"ar Bayero Dake kano.
Dagachan Bangaran Economics Department na Hango Dandazon Jama"a Mata da Maza yan kwalisa Suna ta Tururuwan Fitowa Daga wani aji Daga Dukkan alamu Sun gama Daukan Lecture ne suka Fito,wasu Cikin makaranta suka Shiga wasu kuma Hanyar Cafteria suka Nufa Wasu kuma Masallacin Cikin makaranta suka Nufa Wasu kuma wucewa sukayi Suka Zauna Saman Kujerun Dake Zagaye da Department Din,wanda an Tanadanesu Ne Domin Zama da Huta gajiya ko kuma Karatu Irin haka dai.
Acikin Masu Zaman Inteesar Tana Daga Cikinsu itama Waje ta Samu ita Kadai ta Zauna,Yau Datake kwana Goma da Fara Zuwa makarantar Bazatace ta Saba da komai ba Sai dai ta Fara Fahimtar abubuwa Dayawa Sai dai har yau batayi Wata kawa ba Ita Kadai Zakaa ganta Sai dai Tana Yada Sallama Duk inda Tajee ko Taga Gungun Jama"a Ita Haka take bata da Saurin Saki jiki da Mutane Ballatana Sabo.
Yan ajinsu Da Dama suna Lura da ita Sai dai ba wanda ya Damu Kansa Jami"a Gidan kazo nazo ne,Akwai irin su Da yawa amakarantar Wadanda Basa Bukatar Alaqa da kowa cikin Masu Lura da Inteesar Tun Shigowarta Makarantar Harda Munari Sakamakon Department Dinsu Dayane Tun Ranar da Inteesar ta Fara zuwa Take Hankalce da ita..Sai Taga Itama kamar irin tace bata Hulda Da kowa kamar yadda Take ita Kadai haka Itama Inteesar take komai nata ita kadai,Tana ta so Tayi mata Mgana ammh Sai ta kasa sai yau Bayan sun Fito Daga Lecture din 10 to 12,Zasu yi Sallah suci Abinci 2pm suna da Wani Karatun.
A idonta taganta ta Samu Waje ta Zauna ta Fito da Wani littafin Datayi Note game da abunda aka Koya musu Tana Dubawa Munari bata son Dalili ba kawai Taji Kafafunta najanta Zuwa Wajen da Inteesar Take Zaune,Sai da ta Kariso Gabanta kana ta yi mata Sallama.
Inteesar Dake Tsaka da Karatu Hankalinta yana kan Karatunta ta Dago Suka Hada Ido da Munari Sai dai Ita Inteesar ta Toshe Idanuwanta da Wani Siririn Farin glass mai kyau da yarari yau Shigar Riga da wando Tayi Wandon Ja ne plazo mai Budewa Ta kasa,Sai Wata Riga Blue mai dogon Hannu Ta kama mata Jiki sai ta Dora Wata bakar Riga mai kama da kimoni a Saman kayan ta Zarge igiyarta Daga Wajen Jikinta,Sai Red din Vail Data yane kanta Dashi hakama Taklmin kafarta red mai Tudu sai Wata Karamar Jakarta Red Colour.
Yayinda ita Munari take Sanye da Doguwar Riga Kirar Armani,Baka sai ta yane kanta da Gyalen Rigar Dayake Fara ce sai Fuskarta Tayi kyau itama Bakar Jakace ke Rataye a Kafadanta na Dama sai Wasu littafai Dake hannunta.
Lokacin da suka Kalli juna suma basu san Dalili ba sai da gabansu ya Fadi a Lokaci Daya Kuma suka kasa Dauke Ido a Kallon Juna Cikin Sanyim Murya Inteesar ta amsa ma Munari Sallamanta Lokaci Daya Tana kara Kallonta da Nazarinta.
Munari ta Murmusa kafin tace"Don Allah zan iya Zama..!?
Tafada Tana nuna Gefen Inteesar din da Sauri ta Kwashe Jakarta da Littafanta Data ijiye a Wajen Tana Fadin"Haba sai ma kin Rokeni..Zauna mana..!
Tafada Cikin Mirmishi itama Gefenta Munari ta Zauna tana Fadin"Nagode..!
Mirmishi Inteesar Tayi mata kafin Tace"U are Wlcm!
Daga haka ta maida kanta Kan Littafin Da Munari ta Sameta Tana karantawa.
Sun Dade Shuru kowa na Nazarim Kowa Ita Inteesar Bata zata iya Gane Munari a ajinsu ba Tunda suna da yawa,Ba kamar Munari Datake ankare da ita Tun Fara Zuwanta makarantar ba.
Cikin Son Takalo Mgana Munari ta Gyara Zama tana Fadin"Ammh baki Dade da Fara zuwa Makarantar nan ba ko..?
Inteesar ta Dago kanta Tana Fadin"Eh..yau kwana na Goma da Fara Zuwa kefa..? Wani Course kike yi..?
Munari tace"Course din mu Daya Economics nake karanta..!
Inteesar ta dan Saki Fuskarta Tana Fadin"Allah Sarki..Ashe ma Tare muke Kema Kwananan kika Fara zuwa kenan..?
Munari tace"Eh to ban 1 Month dana Fara zuwa..!
Inteesar tace"Kice kin Rigani Fara zuwa..Aini koda na Fara zuwa Duk anyimin Nisa da karatu..Wajen ma Class Rep ne nake karban Wasu Note din ina rubutawa..!
Munari tace"Ayyah..Ai baki da Shiga Mutane ne kamar ni da kin samu..!
Inteesar tace"Kema haka kike kamar ni..? Kwata kwata bana da Sakin jiki da Mutanen da ban sani ba Haka nake}? Nafi sabawa da Yan gidanmu Fiye da kowa..!
Munari tayi Mirmishi kafin Tace"Kamar Ni kenan..Ni kaina tunda nazo makarantar nan bani da wata kawa Ni kadai nake Rayuwata..sai yau Naji ina Sha"awar nayi miki mgana Duk da ina Lura Dake Duk Sanda kika Fara Zuwa Haka kurum naji kina Burgeni ina son nayi miki mgama mu gaisa..!
Inteesar ta Fadada Fara"arta Tana Fadin"Allah sarki..Ni kaima Da kika min mgana sai naji ina son na gaisa Dake Haka kurum Daga ganin ki yau bansan Dalili ba..!
Munari tace"Kila Allah ne ya Hada Jinimmu..Yana so mu yi kawance..!
Atare suka saka Dariya gabadayansu Cikin Nishadi Shuru yadan Biyo Baya Kafin Munari ta mika mata Hannu Tana Fadin"My Name is Maimunatu Abubakar Malami ammh Agida Abbana da Brodas dina suna Kirana Munari ne..!
Imata Inteesar din Hannu ta Mikamata suka Cafke Cikin Annuri Tace"Nice to Meet u Munari..ni kuma Sunana Maryam Mustpaha Dukku Nima Kamar ke Daddyna da kowa Agida Suna Kirana da Inteesar Saboda Sunan Mahaifiyar Daddy naci Daada..!
Gaban Munari ya Fadi jin Inteesar ta ambaci Dukku Cikin mamaki Take Fadin"Ke yar Dukku ce..?
Inteesar tace"No..Daddyna ne Dagachan.Ummata yar Kadunace..Nima a kaduna aka Haifeni Chan muke Zaune da Zama Karatu ne ya kawo ni kano ina Zaune Wajen Mama yayar Ummace..Kema Abban ku Dagachan yake...?
Da Sauri Munari ta Girgiza kai Tana Fadin"A"a..Kawai na Tambayane..Ganin Daman kina Kama da Fulani..!
Inteesar tace"Kema ai kina Kama Dasu ..Kalle ki fa Fara ni kuma Fatats mai Duhuwa ce..!
Munari Tace"Ni kuma Nafi son irin Fatarki Wlh..!
Inteesar tace"Kedai Fadi gaskiya..Farar mace alkyabban mata fa..Nima Ummata na Dauko Da Fatar Daddy ce kamar ke zan zama Saboda Farin Bafullatanin Dukkune Gaba da Baya..!
Munari ta amshe da Fadin"Ni kuma Daga Abba Har Anni Duka Fulani ne kuma Fatarsu mai Haske ne Shiyasa..!
Inteesar ta gyada kai kafin tace"Ke nan ke yar kano ce..?
Munari tace"Eh..Gidanmu na Gadon kaya..kefa ina kike Zaune..?
Inteesar tace Tana Dariya"Ikon Allah Nima ai Gidan Maman yana Gadon kayan ne..!
Munari ta cafke Cikin Murna Tana Fadin"Shikeman Daman na Fadamiki..Haduwarmu Daga Allah ne..!.Inteesar tace"Na yarda da Mganarki..!
Daganan ssi Hira ta Tsinke kamar sun Shekara da Sanin juna,Haka kowanensu ke jin wani Farincikin na yau Kadai da suka Hadu,karin Farincikin Inteesar ma Da suka Tabo bangaran Karatu ta Fahimci Munari Tasan Abunda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login