Showing 69001 words to 72000 words out of 236322 words

Chapter 24 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

759

yace"Abba da wane..?
Abba sai da ya Dade bai yi mgana ba kafin ya kada kai yana Fadin"Baffanku..Ya Kabiru..Barrister Baban Khamis da Sajida..!
Daga Yusuf har Munari ba wanda ya iya mgana saboda yadda Jikinsu yayi Sanyi balle Safiya Dake gefe aranta Tana Tunanin yanzu Abunda ya Rage ma wannan gidan kenan su Koma ga Ahalinsu kuma tayi wannan alkawarin sai ta cikashi da yardan Allah.
Sallama sukayi ma Abba suka Fice,Safiya ta Rakasu har Haraba suna Fita Daga Gidan Inteesar ta Kira Munari tace tana Kofar gidansu Sagir Tana Jiranta su Wuce sai ta Rasa me Zata ce mata tana jin kunyar tace mata ta Wuce alhalin kwanakin nan Duk Tare suke Tafiya.
Yusuf ne Dayake jin mganar Inteesar din ta Cikin wayar Domon Volume din wayar yana Cike ne yace"Ki gayamata gamu nan zuwa zamu Dauketa..!.
Cikin mamaki ta kallesa sai ya Gyada mata Kai Lokaci Daya yana Sakar mata Mirmishi da Sauri ta Fadama Inteesar din ga sunan zuwa ita da Ya Yusuf zai kaisu makaranta kafin ya Wuce Office.
Haka kuwa Akayi suna zuwa Kofar Gidan suka ganta Cikin Shirinta yau kamar sun Hada baki dukkansu Hijabai suka saka Inteesar ta Bude Bayan Motar ta Shiga sai da suka Fara Tafiya kana ta gaida Ya yusuf ya amsa mata Cikin Sakin Fuska,yana tambayanta Karatu ta amsa da Alhandulillah nan yace su Dake Allah ya basu sa"a suka amsa da Ameen Inteesar nata kallonsa Itafa Har yanayi yake mata da Ya Basheer in yana mgana.
Har bakin Department dinsu yakai su kana Ya basu 1k yace su siya abinci suka amsa suna Godiya kafin yayi Riverse ya juya ya Fice Daga makaranta ya Dauki Hanyar Ma"aikatansu Lokaci Daya yana Duba agogon Silban Dake Daure a Tsitsiyan Hannunsa.
Intee bata lura da Kolin goshin Munari ba sai da suka Fito daga Lacture Data Tambayeta sai tace mata kume wa tayi da Kofar Tiolet dinta Inteesar ta nuna Tsausayawa sosai har tana ce mata ko zasu je asibiti ne.Munari ta nuna bakomai ammh bata yarda ta gayama Intee komai ba Sai ma Intee din take bata Labarin jiya Bayan ta Dawo Daga Rakata ta ga Ya Imran da Sagir ta Shige gida da Gudu Munari Mirmishi kadai Tayi batace komai ba.
Ranar sai 5pm na yammah suka gama da Makaranta suka Dawo gida,Daga Bakin Titi suka Sauka suka gangaro Inteesar ta Fara Shigewa ita kuma munari ta karisa gida Bayan tasha Labarin zuwan Daddyn Inteesar din a Bakin Inteesar din yau a makaranta Itama sai taji tana son ganinsa ko Domin Tasan Yana Son Inteesar Shiyasa yake Shagwabata.







*Shakira..*
3/22/22, 23:06 - Ummi Tandama???i: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:JanaftyB??0
{*


}? }? }? }? }? }?}? *??T??21*

Cikin satin kaf}? Ya yusuf ke kaisu Makaranta kafin ya wuce wajen aikinsa Dayake kuma an ci Sa"a duk Lacture din safe garesu,ranar jumma"a ne kadai suka tafi da Kansu saboda sai 10am suka shiga makaranta na Safe.
Wannan karamcin na Gidansu Munari Inteesar na matukar jin Dadinsa Har Daddy da Umma sai da ta bama Labarin Yayan Munari ke kaisu makaranta Kullum Duk yadda kaji wani na son naka ko yana Hidima Dashi kaima Dadin haka kake ji Abunda ya Faru da Umma da Daddy kenan Shiyasa yayi alkawarin Tabbas in yazo Inteesar zata Rakashi Gidansu Munari yayi musu Godiya.
Ranar asabar ba makaranta Tun Jiya da Daddare Daman yusuf yace Safiya ta Shirya ita da Munari zasu je anguwa Shiyasa Tun Safe suka gama Duka ayyukansu bayan sun gama Breakfast suka yi Luch suka Zuba a Kula suka Rufe Kafin su dawo.
Karfe 11am na Safe suka Fita Suka bar Abba da Imran agida wanda Gudu kadai ya Fita yayi ya Dawo gida ya Shige Dakinsa Abba kuma na Falo yana kallo Yana Debema kansa kewa.
Ashe gidansu Safiya zasu je sai da suka Dauki Hanya yake gayamata Farinciki ya cikata Duk da Tana waya da Mommy da Tasleem ammh Tana Bukatar zuwa ta gansu Duk da Tasleem din na zuwa wajenta Lokaci Bayan Lokaci in Mommy ta aikota da Wani Sakon,Bata da Mtsala da su Abbu ne mtsalanta Domin Tunda tayi aure basu Taba Haduwa ba Ta taba Kiransa Sau Daya a waya yace Kada ta Kara Kiransa ta Zauna Gidan auranta Tayi ma Mijinta Biyayyah.
Sun ko ci Sa"a Alhaji Alhassan yana Gida yana Sama yana Hutawa suka iso Mommy da Tasleem suka kasa Zama Saboda Murna suna ta ina suka Saka da Yusuf da Munari Mommy kuwa Bakinta kamar zai Tsage saboda murnan ganin yarta Tayu cikar Daki wanda ganin Farko zakayi mata ka Shaida Bata cikin Wata wahala ballatana Damuwa.
Kafin kace kwabo an cika Gabansu da abinci da abunsha,Tasleem Taja Munari Dakinta Safiya kuma Tana Dakin Mommy sai aka bar Yusuf kadai afalo.
Safiya ta kalli Mommy Daidai Lokacin Datake Zama gefen Kayattacen Gadon Daya Malale Dakin tana Fadin"Mommy Abbu baya gida ne..? Naga motarsa a parking space..!
Mommy ta tabe baki Tana Fadin"Yana Nan..Bai fito bane yana sama yana Hutawa..!
Ta Bude baki Zatayi mgana Hajiya Mero ta yanketa tana Fadin"Kin mai mganar zuwa gidan kakanin naki Rijiyar Zaki da gidan Yaya Saratu..?
Safiya tace"Eh na gayamai Mommy yace Zamu je to bansani ba ko duka Tafiyar yau ta yuyu Tunda kinga Rana mai kama ta yau yake samun Hutu..Tunda Sauran ranakun sun siyar ma gwannati Lokacin su..!
Mommy tace"Hakane kam..Kudai yi kokari kuje Alhaji da Hajiya suna ta mganarki..!
Safiya tace"Tom Mommy ai Dayake ma muna mgana dasu ta waya..!
Mommy ta Mike tana Fadin"Haka Hajiya tace min..Ki je Falo wajen Mijinki kada ki barsa Shi kadai..!
Safiya tace"Mommy Abbu fa..? Bazai Fito su gaisa da Yusuf ba..?
Mommy ta bata rai kafin tace"Shi ya ma Taba Tunawa Dake ne..?ki Rabani da mganar Mahaifin da baisan Darajan Ya"yansa da Hakkinsu Dake kansa ba..Ni kuka zo Dubawa kuma nagode ku gama abunda zaku yi ku wuce ku tafi bana son ma ya Fito ya ganku..!
Safiya bata samu Zarafin mgama ba sukaji Muryan Alhaji Alhassan yana Kwalama Hajiya Mero kira atare suka Kalli juna kafin dukkansu su Kama Hanyar Fita Daga Dakin.
Suna Fitowa Falo suka iske Yusuf duke a kasa ya sauko Daga kan kujera kansa na kasa Alhaji Alhassan kuma yana Tsaye da Jallabiya yana Mazurai..
Hajiya Mero ta Hade rai Tamau ta Nufeshi Tana Fadin"Gani Allah yasa Lafiya..?
Yabude baki zai yi mgana sai Lokacin yaga Safiya Dake bayan Mommy Baki ya Saki yana Kallonta ita kuma kanta ta Sadda ta karisa kusa da Mijinta ta Durkusa Tana Fadin"Ina kwana Abbu..!
Kada kai yayi sai Lokacin ya gane Yusuf ne yaron nan don da Farko Daya Sauko Yusuf din ya Duka yana Gaishessa bai wani ganesa ba, Tunda ba wani Tsayawa yake yana Kallonsa ba Koda yazo wajen Safiyar a baya.
Maida mganarsa yayi Cikin Cikinsa ganin Haka yasa Hajiya Mero ta karisa kusa Dashi kasa kasa Tana Fadin'"Yanzu ai kagane ko waye ko..?
mijin yarkace Safiya da kayi ma Auran Kaskasci Ma"ana Surukinka yazo yayi maka Godiyan Aura masa Safiya da kayi ne..Sai ka Natsu..!
Tafada Lokaci Daya tana Hararansa Tana kuma Dagowa sai ta Murmusa Tana Fadin"Ku tashi ku zauna kan kujera mana..Yusuf ai nan din ma Duk gida ne ko Alhaji..?
Alhaji Alhassan bai da yadda Zai yi Dole ya saki Fuska yana Fadin"Hakane..Ku tashi ku zauna Sannunku Mero sai ki gayamin yau muna da baki agidan nan Safiya Sannu da zuwa..!
Ba mommy ba Hatta Safiya da Yusuf Mamaki ya hanasu Motsi gefensu ya samu kan kujera ya Zauna Yusuf ya kara Ramkwafawa yana Gaisheshi ya amsa mai Cikin Sakin Fuska yana kara Nazarinsa ita Mero bata gane wani abu ba Shifa koda yayi ma Safiya wannan auran yasan me ya aura mata yayi Binciken kan Yusuf Yaro neNagari mai Neman na kansa Sannan kuma Dalilin wannan Tsagerin Kanin nashi ne komai ya Lalace Domin yayi Hannun Riga da duk abunda zai tabamai kimarsa Sai da Ya tattara Safiya ya mikamusu ya ke iya Barci Harda Minshari,bawai Domin baya son yarsa ba Taya Mutum zai Haifi ya yakita sai domin Zuwanta wannan Gidan Shine Rufin asirinsa kuma bazai iya Fitowa yayi ma wani wannan Bayanin ba Shiyasa ko Dayaje Fagge Goggo Tayi Fada kamar ta ari Baki kamar ta Dakesa shi dai sai ban Hakuri yake bata bai da tacewa Tunda aikin gama ya gama ya riga ya gamaba Goggo ba Ya riga yaShiryama Daukan Kowacce mgana kan abunda ya aikata yana Shiryen da hakan indai Boyayeyen Laifinsa bazai Fito a idanuwan yan"uwansa da Matarsa da ya"yansa ba Dama Sauran Mutanen Dake ganinsa da kima ba
Kallon Safiya yayi yana Fadin"Safiya ya Sabon Wuri..?kina Bukatar wani abu ne..?Ki Fadamin komai kike Bukata zan yi miki mishi.!
Cikin Mirmishi ta kalli Yusuf Shima ya kalleta kafin tace"Bana Bukatar komai Abbu..Komai Mijina ya Siyamin ina Cikin Farinciki a Sabon Gidan da nike yanzu..Ina Rayuwa ne Tmkar yadda nake Rayuwa a gabanku..!
Hajiya Mero Dake gefe taji Dadin amsansa sai da ta aikamai da kallon ba Haka kaso ji ba ko..?
Shi kuma sai yayi kamar bai ganta ba ya Shiga Saka musu albarka ita da Yusuf wanda yayi musu Matukar Dadi Ita da Yusuf din har ya kasa Boyuwa Saman Fuskarsu ita kanta Hajiya Mero Jin Haushinsa ya Ragu acikin Ranta.
Suma cikin hakane sai ga Munari da Tasleem sun Fito ta Duka ta gaida Alhaji Alhassan ya amsa yana wani kallonta Cikin kwarewa kasa kasa Tuni yarinyar tatafi da Imaninsa irin Kayan Harkan Dayake so kenan sai dai Tunaninsa ya Tsaya ne sanda Safiya ke Fadin kanwar Mijinta ne.
Miyau ya Hadiye mukut..Ya maida Kwadayinsa ko Ya haukace bazai yi wannan ganganci ba Ko bama Safiya ba ya Tabbata wannan Kanin na Yusuf yaji Labari sai ya Tabbatar da ya Kwaye mai Rigar Mutumcin Dayake yaudaran Mutane dashi..Da Mannau gara Hanau.
Da sauri ya gyara Natsuwarsa ya amsa gaisuwarta Cikin Fara"a da Dattako yana saka mata albarka basu Dade ba sukayi Haraman Tafiya,Yusuf ya Ijiyema Mommy 10k Abbu 10k Safiya kuma tace Abbu ya bar Tasleem ta Rakasu Rijiyar Zaki gidansu Hajiya Mero yanzu yake Fadamata Daga nan chan zasu je ba gaddama yace sai sun Dawo Hajiya Mero bakinta yaki Rufuwa ta shiga Ta Dauko ma Munari Turmin atamfa da Turare sai Turaran Wuta ta Diban ma Safiya da Humra,Sauran kuma tace takai ma Hajiya
Har Haraban gidan suka Rakasu ita da Alhaji Alhassan Ita kuma Tasleem nata Murna suna Daga musu Hannsu suka fice Daga Haraban Gidan
Sai da suka Fice kana Hajiya Mero Ta Daga Hannu Sama tace"Alhamdulillah..Allah nagode maka da Allah bai ma wani Damar Tozarta Rayuwar yata ba..Allah nake Roko ya Kareta yasa ta Zama a Haske ga Mijinta da Ahalinsa gabadaya..!
Tafada Lokaci Daya tana Nufar Hanyar Cikin gidan ko kara Kallon Barayin Alhaji Alhassan batayi ba Shi kuma da kallo ya Bita yana Mirmishi Gefen Bakinsa aransa yana Fadin kayi ki gama ne.
Suna Fita Daga zooroad basu Tsaya ko"ina ba sai kofar gidan su Hajiya Mero Rijiyar Zaki sun ci sa'a nan suka Hade da Anty Saratu tazo gaida su Hajiya sun ji Dadi sosai sukayi ta saka musu albarka basu wani jima ba suka Tafi Bayan Yusuf yayi musu alheri,Safiya kuma ta bama Hajiya Sakon Mommy Anty Saratu kuma tace Tunda sun Hadu anan tana Binsu bashi Yusuf yayi mata alkwarin Insha Allahi suna nan zuwa.
Daga Rijiyar zaki kuma Gidansu Sagir suka Sauka Yusuf Ya shiga Har ciki suka gaisa da Mama kana yace in Sagir na nan zai rakasu Gidan Baba Manu yamai Godiya,Mama taji Dadin haka Tana saka albarka Koda suka zo Inteesar na kwance tana Barci Tayi aiki Ta gaji yau har yan kayan Mama kala Biyu da Hijabai ta wanke ta Hada da nata Inears din ta wanke Shiyasa take kwance sai da Munari ta Shiga Har kurya ta Taddota Ta Daka mata Duka kana tatashi a gigice ganin Munari ya sa tatashi nan take Fadamata Tare da Ya yusuf suke da Anty Safiya Hijabinta ta Dauka suka fita ta gaishesu suka amsa mata Cikin Sakin Fuska.
Mama a waya ta Kira Sagir tace mai yana ina ne..? Yace mata yaje banki ne ammh gashi nan zuwa,ba Dadewa sai gashi ya shigo har gabansa ya Fadi ganinsu yusuf ya Zata wani abu ne ya Faru da Imran domin Tun Ranar da sukayi mgana basu kara Haduwa sun yi Wata mgana da Imran din ba ya Dauke Kafa da zuwa Shagonsa sai dai su Hadu a masallaci su gaisa Sama Sama ya Raasa me yasa Imran ya Dauke masa Kwana Biyun nan sun saba Fadansu su Shirya sai dai wannan karon Abun yasha Bambam
Sai da suka gaisa kana Mama ke Fadamai Dalilin sai lokacin yaji Hankalinsa ya kwanta.
Gabadaya suka tafi Harda Inteesar Tasleem Dayake chan Rijiyar Zaki suka barta Anty Saratu zata Leka Mommy Zasu koma Tare Mama kadai suka bari gidan
Wannan karon duka Matan suka Hade a Bayan Motan Sagir na gaba yana Nuna Hanyar gidan Baba Manu.
Yusuf ya kallesa yana Fadin"Sagir ina Mutumin ka..?
Sagir ya Juyo yana Kallon Yaya Yusuf kafin yace"Kai zan Tambaya Ya yusuf...Imran na Fushi Dani ko mgana nayi mai sama sama yake amsani..,!
Yusuf ya Murmusa kafin yace"Babu abunda kayi mai kuma badakai yake Fushi ba..Sai dai shi haka yake duk Lokacin da wani ya batamai rai..Yana Hada bacin Ransa na Tsawon Lokaci sai kuma Hakan ya Horasa Shi kadai..Ni kaina sai na Bisa Dakinsa nake ganinsa baya ma son Fitowa ko Falo balle a mtsamai da mgana Abba kadai Daya zamemai Dole yake gaisawar..!
Gabadaya Tayi shuru suna Sauraransu Sagir ya jinjina kai yana Fadin"na gane..Sai dai Imran nada Wahalaf Sha"ani ina Matukar Tsausayama matarsa in bata sanshi ba Zata sha Wahalansa..!
Yusuf yace"Ko ni da nike Dan"uwansa Ciki Daya yana min Wahalar Mu"amala ballatana Mace..! Sai dai kasan soyayyar Kila sai ta Sauya shi Watarana..!
Kai Tsaye Sagir yace"Imran bai yi Beleive kan Soyayyah ba bana Tunanin hakan zai iya Faruwa..!
Yusuf yayi Dariya yana Fadin"Ai karya yake yi..Nifa ina da yakinin Mace sai ta Sauyashi Shi din banza..!
Dariya Sagir ya saka kafin yace"Shikenan mu jira mu gani..!
Ammh ina da Shakku har yanzu..!
Yusuf yace"Kajira Lokaci kawai Sagir zaka ce na Taba Fadamaka..!
Su safiya na bayan Mota suna jinsu Tabe baki inteesar tayi aranta Tana Tsausayama mai Tsautsayin data yarda ta Auri wannan ta gama kashe Rayuwarta Gabadaya Mutum na Rayuwa kamar ba Mutum ba sai Kace wani Aljani.
Suna isa gida suka kuma Taki Sa"a Baba Manu na gida Lokacin da Sagir kemai bayanin yusuf sai yaji Dadi da Sauri ya Mike sukayi Musabaha Daman Wlh Safiya na Ransa Saboda yana Tunanin shine fa yayi jagaba kan Auransu in wani abu ya Faru Allah bazAi barshi ba sai dai ganin yusuf da ita Kanta Safiyar ya Ciremai kowani Shakku Kaltume nata ina ta saka dasu Ruwa kadai suka sha Yusuf ya Ijiyemai 5k suka Fito Har waje ya Rakosu yana Godiya Lokaci Daya yana Musu addu"a har sun Shiga Mota Baba Manu ya Duka Saitin Yusuf yana Fadin"ina Murdadden kanin nan naka..?
Yusuf yayi Mirmishi kafin yace"Imran..Yana gida Baba yace a gaisheka..!
Baba Manu yayi Dariya kafin yace"Kai dai ka ari bakinsa kacimai albasa..Nasan bazai ce ba..Ganin Biyu nayi mai zuwa uku ammh na Nazarcesa kamar na Shekara da Saninsa..Ku rika Sakashi yana yawan Shan Ruwan Zamzam hakan zai Taimaka wajen Saukakamai al'amuransa..In ka koma Gida kace Baban Sagir na gaishesa..Manu nake..,!
Yusuf ya gyada kai yana ta Godiya kafin su tafi acikin Ranshi yana Kara auna wasu abubuwan shifa ba Domin Abba ya Rantse mai Imran baida Aljanu ba shi kansa da Farko kallon mai Bugawar Junnu yake mai ammh yanzu kam da Baba Manu yayi mgana zai Tsaya tayin daka wajen ganin Rayuwar Imran ta Inganta kamar baya bazai zuramai ido yana da Komai na Rayuwa,ammah ya Kare rayuwarsa Cikin Wani Hali ba.
Daganan Sagir da Inteesar suka ijiye agida suka karisa suma.
Suna Dawowa abinci suka ci suka yi Sallar La"asar Abba da Yusuf kuma Daman masallaci suka tafi,Imran kuma yana Cikin Dakinsa ba wanda yaji Motsinsa kuma ba wanda ya Neme sa yaji sanin Halinsa.

*****
Washegari ta kama Lahadi ne Tun Safe Inteesar ta tashi da Murna Domin Tayi mgana da Daddy yace suna Hanya shi da Ya Basheer ammh sai sun gama abunda ya kawosu zasu zo nan gidan Maman,Gabadaya ta kasa Zama Saboda Murna Mama natayi mata Dariya Ya Basheer na son Alala shi tayi mai Abba kuma Tuwon Semo Tayi mai miyar Kubewa Bushashiya Sai wajen 1pm ta Gama komai ta shiga wanka ta Shirya ta Zauna zaman jiransu Ko abinci ta kasa ci,Mama sai Fada Take mata kan ta Rika cin Abinci ammh ta kasa ita Haka in tana Zakwadin Abu abinci ma Baya gabanta.
Duk bayan Mintina sai ta Kira Daddy taji ko sun gama abunda ya kawosu suna Hanyar zuwa Gidan Mama sai yace Mata A""a har ta gaji da kira ta Hakura tana ganin kamar bazasu zo bane Har Munari ta Kirata Tana Tamnayanta ko Daddy ya iso tace eh Yana cikin kamo sai dai basu kariso ba
Tace to bara tayi wanka gatanan zuwa,Da haka suka rabu kuma sai ta Jita Shuru karfe 3:00pm na rana Daddy da Ya Basheer suka iso ho zo kuga Murna wajen Inteesar ta makale Daddy gamgam Tana Fadin tayi kewarsa Hakama Ya Basheer ta Rumgumesa shima ya Riketa Cikin Farinciki Mama itama Murna Duk ya kamata ta rssa ina Zata sakasu haka take akwai son Yan"uwanta sosai.
Bayan sun zauna sun sha Ruwa da Inteesar ta gama jera musu aka Fara gaisawa Sagir na gefe Daman yana Shago yaga Isowarsu shi yayi musu Jagora zuwa Cikin Gidan.
Mama da Sagir suka basu Waje su gana Da Inteesar nan ta zauna tana Zubamai Shagwaba da Tambayoyin ina Umma..!? Talatuwa..? Anty Hauwa ina su Abiden ya Basheer gajiya yayi da amsa mata yayi Shuru yana cin Alalansa Dakyar ta bar Daddy yaci Tuwonsa}? yaci sosai jin Intee tayi mai,bayan ya gama ya Kira Umma ya bata sukayi mgana inda tace ta bama Dadynta sakon Dambun nama da Kayan Snkas,Roba Biyu ne Daya nata Daya na Mama nan tace ma ta kaima Mama Wayar suyi mgana nan ta Fice Tsakar gida ta Mikama Mama Wayar sukayi mgana da yar"uwanta sun Dade suna mgana barin ma mganar Kan auran Yarinyar Wajen kaw Bala ne nan da Wata Biyu.
Daddy sai da sukayi Sallar La"asar sukayi Shirin Tafiya bayan ya cika Mama da kudi Tana ta godiya kuma sun sauke mata kayan abinci Inteesar harda Lemonta Freshyo,Katan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login