Showing 15001 words to 18000 words out of 236322 words

Chapter 6 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

698

amsa mai Cikin Fara"a Tana Tambayashi Mutanen gidan Dakyar yace Lafiya lau yana kauda kai itama ganin haka bata mtsa ma kanta ba Ta juya kan Sagir Tana Tambayansa Mama yace Tana gaishesa Daidai Lokacin da Baba Manu ya gama waya ita kuma Inna Kaltume ta mike tana cema Sagir azubo Tuwo yace a koshe yake ta kalli Imran wanda kansa ke kallon gefe yana jinsa kamar a Takure tace koshi bazai ci ba..?.Sagir ya kallesa kafin ya girgizamata kai yace mata Ta barshi kawai bata ja da Nisa ba ta Shige Daki ta basu waje suyi mgana.
Juyawa Sagir yayi yana gaida Baba Manu wanda da ga kanshi Zaka san sun Hada Jini da Sagir Saboda Zubinsu iri Dayane da kuma yanayin Dogon Fuskarsu
Amsa mai yayi Cikin Fuska Lokaci Daya yana Fadin"Ina Ita Aminan..? Ina fatan lafiya kalau take..?
Kan Sagir na kasa yace"Eh Baba Lafiyanta Kalau tace a gaisheka..?
Yana kallon Imran yana Nazarinsa acikinsa Ransa yace"Ina amsawa Daman gobe nake cewa zan leka mu gaisa kwana Biyu!
Sagir ya gyara zama yana Fadin"Baba ga abokin nawa danace maka zamu zo Tare..Imran yana so yayi mgana Dakai..!
Baba Manu ya maida Hankalinsa kan Sagir kafin ya kalli Imran yana Fadin"Topha dan Saurayi in ce dai ko lafiya..?ba wani abu Sangirun yayi maka ba..?
Imran da sai yanzu ya kallesa ya Girgiza kai yana Fadin"A'a ba mganar Sagir bane..!
Baba manu yace"To to..Ina jinka..!
Sagir ne ya kalli Imran din yana Fadin"Ka cire Takalminka ka Hawo kan Tabarman mana Imu..!
Bai kallesa ba ya gyra Tsugunnonsa yana Fadin"Nan ma is ok..!
Baba manu dai bai ce komai yana ta Tunanin wata mgana ce haka yaron da ba wani saninsa yayi ba yazo har gida saboda ita.
Bai gama mamaki ba Yaji Muryan Imran din Ciki Kaushi kai tsaye yana Fadin"Dama kan mganar Auran yayana ne...Gidan Dayake son yarinyar sun nemi Daya Turo mgabantansa Shine nazo na sameka ina so ka Shige masa gaba a Bangaran Neman auran..!
Ba wani Roko ko alfarma kai Tsaye ya Fadi mganarsa kuma bai Damu ba.
Baba manu mamaki ya kamashi ya kalli Sagir,wanda ya Sunkuyar da kansa domin bai ta cewa Sanin Halin wanda ya kawon.
Cikin mamaki yace"In shige masa gaba..? To ina iyayenku ko nace Waliyan ku..Ma"ana kanin Mahaifi ko Kanin Mahaifiya ko wani Daga Cikin Danginku..!
Imran kamar bazai ce komai ba sai Chan yace"Bamu dasu..Gidanmu mu kadai ne Dagani sai yaya na sai kanwata sai Abbanmu..Kuma shi din bai da Lafiya ne shiyasa nazo wajenka..!
Baba manu ya gyara Zama yana Fadin"To baku da yan"uwa ku din Daga sama kuka Fado..?
Sai alokacin Imran ya kara Dago kai yana kallon Baba Manu Cikin wani yanayi kafin yace kai Tsaye"Eh..!
Ba Baba Manu ba Harta Sagir sai da ya kalli Imran yana Auna masa Harara da ido Cikin Kufulwa da Rainin wayau Yaron Baba Manu yace"Kuma kace Min Eh..!
Imran yace"Eh..Ai kaima kasan ba wanda ya Taba Fadowa Daga sama..Ballatana ka Tambayeni ko mu Daga sama muka Fado..!
Hankalinsa kwance yayi mganar Zuwa Lokacin Ran Baba Manu ya Fara Baci Cikin Hargowa ya kalli Sagir yana Fadin"Au daman da saninka ka Kawomin wannan Tsagerin yaron har gidana zai Cimim Mutumci..?
Sagir ya kwaso Rantsuwa Baba Manu ya Dakatar dashi da Fadin"Maza tashi ka Tarkatashi ku barmin gida kafin na Saba maka..ko ce maka akayi ni Mutumin banza ne..!?
Sagir ya Sadda kai yana Fadin"Don Allah Baba kayi Hakuri..Ba Cin mutumci zai maka Shi haka yake don baka Sanshi bane..Imu ka bama Baba Hakuri don Allah..!
Ya karishe Fada yana kallon Imran Din da har ya Mike daga Tsugunnon Cikin mamaki yace"Saboda mene zan bashi Hakuri..? Nayi mai wani Laifi ne..? Mgana na kawo mai ni kuma ya Tambayeni na bashi amsa do i do Something wrong..? Bana bada Hakuri a inda ban aikata komai ba Mganar aure ai Mganar alherice balle yace Mganar Shanshanci na kawomai..!
Yafada Hankalinsa kwance yana Laluban Aljihunsa Cikin Takaicin ya manta bai Fito da Tabansa ba sai dai Lether din,Karamin Tsaki yaja ya juya zai Fice Daga gidan Baba Manu ya saka baki ya kira Sunansa Tsayawa yayi kafin ya juyo Da kai ya gyada mai kafin yace"Dawo ka zauna muyi mgana..Na Fahimceka!
Yafada da Dan Sakin Fuska Domin a kalaman yaron ya gama Fahimtar sa irin yaran ne kaifi Daya marasa Tsoro,Gaba gadi basu karya ba Munafunci.
Inda ya tashi ya koma ya Kara Durkusawa Cikin mamaki Sagir ke kallon Baba Manun sanin Halinsa na Fada ammh sai me sai yaji yace ma Imran din"Wani gida ne shi yayan naka yake neman auran..?
Ajiyar Zuciya ya sauke kafin yace"Gidan Alhaji Alhassan Buhari..!
Baba Manu yayi jim kafin yace"Kardai kace min gidan Alhassan malami a jami"ar Buk Dake Zaune a Zooroad..!
Da Dauri Sagir yace"Shi Baba!
Baba Manu yace"Ai ta kwana Gidan Sauki..Ai nasam sa makotan Marigayi yaya nane Mahaifin Sagir kafin Allah yamai Rasuwa a saida gidan suka Dawo nan gadan kaya da Zama..in hakane ba mtsala Zan nemi abokina Alh.sadi sai muje ayi mganar kada kadamu kaji..!
Imran yace"Shikenan kamar me dame ake Bukata..?
Baba Manu yace"To zuwan Farko dai Kudin gaisuwa ne za"a kai sai su Minti da goro ko Dabino da Tarbarmu ko Cafet na kayan na gani ina so..In kuma zamu kara komawa bayan mun yi mgana dasu Waliyan yarinyar sun yanke Sadaki sai muje dashi da kayan Saka Rana!
Imran yayi shuru kafin yace"in naso aje gabadaya Sau Daya fa...?
Baba Manu yace"Shi Alhaji Alhassan don ya Bukaci Haka..?.
Kai tsaye Imran yace"Ko bai bukata ba..Ni haka nake so ayi.Kuma hakan za"ayi yanzu Duka da komai da komai har Sdakin ita yarinyar nawa zasu isa..?
Abun sai ya bama Baba Manu Dariya Confident din yaron Cikin Dariyan yace"Ni kuwa ina zan san Sadakinta ni ba Ubanta ba..? Sai dai muje da kudin In sun yanke na Hannunmu sun kai mu basu in kuma da kari sai mu Dawo Mu kawo Daga baya..!
Imran ya Mike Lokaci Daya yana Fadin"Gobe in Allah ya kaimu zan kawo maka 200k..Zuwa Jibi nake so kuje gidan..!
Baba Manu yace"Wannan ba mtsala bace..Sai dai an sanar da megidan muna tafe jibin..?
Imran kai tsaye yace"Yarshi zata sanar dashi..Nagode..sai ka ganni.!
Daga haka ya juya Cikin Takunsa na Sarssarfa ya Fice Daga Gidan Baba Manu da Sagir suka Rakashi da Ido kafin Sagir shima ya mike yana Fadin"Baba sai da Safe..!
Baba manu ya Sauke ajiyar rai yana Fadin"ina ka sami wannan yaron..? Daga yanayinsa da mganarsa na gane akwai abunda yake Faruwa dashi koma ya Faru dashi Daya kara maidashi haka..?
Sagir yace"A anguwar mu suke Baba.Sune wadanda suka siya gidan Marigayi Habibu Daya rasu kwanaki fa!
Baba Manu yace"Au..Nan suke da Zama..!
Sagir yace"Eh Baba..Nima haka na gansa har muka fara abota basu da kowa anan garin koma suna dashi ban taba gani ba basu Hulda da kowa daga su sai su kawai sai ni kuma da Allah ne kadai yasan Daliln Abotanmu..!
Baba manu Dayaji Tsausayin su Imran ya kamashi yace"Allah Sarki Shi kuma Baban nasu Dayace bai da lafiya me ya same shi..? Kuma ina Mahaifiyarsu..?
Sagir yace"Wlh nima Bansani ba Baba..Abbansu dai kullum yana Daki yana kwance likita ke zuwa gida yana Dubashi kuma agidan banta ba ganin wata mace ba Daga Imran din sai yayansa Yusuf wanda shine komai nasu sai Karamar kanwarsu Maimuna..!
Baba manu na jinjina kai yace"Ikon Allah..!
Zai sake mgana suka jin Hon din Imran da karfi da Sauri Sagir ya Duka yana Saka Takalminsa Lokaci Daya yana Fadin"bari naje Baba kada ya tafi ya Barni.Labarin yana da Tsawo zan Sake dawowa sai mu Tattauna..!
Da toh kawai Baba Manu ya Bishi har ya Fice da gudu,Sai kuma ya Gyara zama yana Tunani da Nazarin Labarin da Sagir ya bashi game da Imran shidai yana ganin akwai wani abu mai Girma wanda yake cikin Zuciyar yaron kuma shike hanashi Sakin jiki Cikin mutane.
Koda Sagir ya Fita Ran Imran ya gama Baci yana Hawa Mashin din ya Fizgeta sauran kadan Sagir din ya Fadi sai da ya Rike karfen Mashin din kana ya iya Zama Dakyau Cikin Tashin hankali Sagir yace"Yanzu daman Saboda ka yi sanadiyar da zan mutu ko na jikkata ka je har gidanmu ka Daukoni..?
Imran ya saki Tsaki yana Fadin"Kamin shuru mallam..kafin na Sauya Shawara na Tsaya da Mashin din na Cikama baki da jini..!
Sagir na jin haka yayi Shuru da bakinsa Domin yafi kowa sanin Zuciya irinta Imran bamai kyau bace
Haka sukayi tafiyan ma wannan Karon Shiru har Imran din yakai Sagir din gida ko gama Sauka bai yi ba ya Figi mashin dinsa yayi Gaba Sagir ya B??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????isa da kallon kafin ya Girgiza kai kawai bai Shiga gida ba Shagonsa ya Shiga yana Duba agogon Hannunsa Tara ya wuce ya kamata su Rufe Shagon sai kuma gobe.

*******

*Kaduna*

Da Ihunta da Murnanta ta Shigo Falon Tana kwala kiran"Umma..! Umma..!
Umma Dake Kitchen Tana Hadama Alhaji Tea dinsa taji Kakakin kiram suanta da Inteesar keyi ta Fito Tana gyara Daurin Zanin Atamfarta Golding Dake jikinta.
Cikin Takaichi tace"Wai ke Inteesar yaushe zaki koyi Sallama ne ba ihu ba..?
Tura Baki Inteesar din Tayi kafin ta Zube kayan Hannunta kan kujera Tana Fadin"Kai Umma ba nayi sallama ba..Ki Tambayi ma ya Bashir..!
Tafada tana wani Diddira kafa na Shagwabbanun yara.
Tabe baki Umma Tayi daidai Lokacin da Bashir yayi sallama ya Shigo,Umma ta amsa mai ya kariso Falon sai da ya Zauna ya Fara gaisheta ta amsa Tana Fadin"Ya ka baro su Hauwa"un..? Dazu yaranan sai kuka suke Shine da Babanku zai kai Inteesar gidan Inno nace ya biya da ita ta kaisu wajen Mamansu..!
Yana yar Dariya yace"Umma Rigiman yaye ce kawai..Chan ma sai Rigiman suke mata..!
Umma tace"Daman sai a Hankali..Tana ma kokari kai ne nace maka ka samo mata wacce zata rika taimaka mata..!
Bashir yace"Umma itace fa taki..Ammh nima nayi mata mganar..!
Umma tace'Ai shikenan Tunda bataso..Daman Wahala Renon yara ake jiyemata ga kuma Laulayin sabon Ciki..! Jin haka yasa bai yi mgana ya Sadda kansa kasa Domin Bashir akwai kunya.
Sanin haka yasa Umma bata kara mgana ba ta maida Hankalinta kan Inteesar Dake ta Faman Bule Lodojin Data Shigo Dasu bakinta kamar gonar Auduga saboda Murna..!
Umma tace"Ita kuma wannan ina ka samota..? Naga sai Murna take me ta samo ne?
Bashir yace"Umma Daddy ne ya kirani yace naje na Daukota gidan Kawu Salisu na Daukota..!
Umma ta Rike baki Tana Fadin"Au har chan sai taje kenan..Nifa Daga gidan ka naceta Hau adaidata ta karisa wajen Inno Tana min mitan kada Inte tatafi Batazo mata ssllama ba..Dama bai Dade da Dawowa ba sai Mitan yake Inte bata dawo ba yafa gaji wai zai kara Fita ya Daukota nace sai dai ya kiraka..!
Kafin Bashir yayi mgana Inteesar ta Daga wani maroon dim Hijabi mai kyau ta kara ajikinta Cikin Murna tace"Umma ni fa yar gatace..Kalli kiga kayan da na samo..Wadanam Hijaban Anty Hauwa ta bani kala Biyar tace na Zuwa makaranta..Wadanan Gyale da Takamim kuwa Mamarsu Nasara ta bani Kawu Salisu kuma ya bani 10k Umma Inmo ta bani Gwarin da Kuli da yawa da yaji Data Dakamin,Mallam Babba kuma ya bani 5k Umma.."
Ta karishe Fada Cikin Bayyana Farincikinta tana nuna ma Umma kayan da kudin Dake hannunta.
Umma ta kariso tana Fadin"Nagani Kin gode..Ammh meyasa baki barma Mallam Babba kudinsa ba..?
Inteesar ta Tura baki Tana Fadin"Shifa ya bani sai naki karba..Kuma ance ma raina kadan..!
Umma ta kaimata Dundu Tana Fadin"To uban nawa ne barawon..? Intesar na Dariya ta gaoce Bayan ta Tattara kayanta Tana Fadin"Nifa ba haka nake nufi ba.Ni bari ma naje na Nunma Daddy...Umma Daddy na Ciki!
Umma tace"To mara Hankali yana Hutawa kya Bari da safe ko..?
Inteesar tace"Umma da safe ba Tafiya zamu yi ba..,?
Umma tace"Kafin ku taho..Tunda ba Sammako zamu yi ba ai ba yaki bane..Ba kuma kanki Farau jami"a ba..!
Bashir ne Dake Dariyansu Tun Dazu yace"Umma Dake za"a Raka Autan Daddy ne..?
Umma tace"eh.Da nace bazani ba Tunda tace ni ba uwarta bace..Sai nace bari dai naje ko na ga Yaya Amina mun dade bamu Haduba ni ban je ba kuma ita batazo ba ko zuwanta na karshe iyakarta gidan Inno,ni kasan Lokacin bama nan mun Tafi Dukku ni da Alhaji da Inte!
Inteesar Dataji da Umma za"a je kaita kano ta Daka Tsalle Tana Fadin"Da gaske Umma Dake zamu Tafi..?
Umma tace"Ba don Halin ki ba.?Ihu ta saki kafin tace"I love u Umma..!
Ta kwashi gudu da kayanta Zuwa Dakinta Umma ta rakata da kallon kafin ta Girgiza kai tace"Kai bansan yaushe yarinyar nan zatayi hankali ba Allah ya Shirya..!
Bashir ya amsa da Ameen yana Fadib"Zatayi Umma..Bari karatun ya kamkama..!
Umma tace"Allah yasa..!
Ya mike yana Fadin"Amern Umma bari na koma ki gaida Daddy Gobe da Safe kafin ku wucen zan biyo muyi ssllama da Auta..!
Umma ta mike Tana Fadin"Shikenan ka gaida Hauwan da su Abiden..Allah ya Tashemu Lafiya..ya amsa da Ameen yana Ficewa Daga Falon Kitchen ta koma ta Sauke Ruwan Tea din Dayaji Na"a Na"a ta samu mug karami ta Zuba akai sai ta saka Siga kadan da Lemin Tssmi ta Dauka ta Fice zuwa Dakin Megidan nata.







*Shakira*
3/22/22, 23:03 - Ummi Tandama???i: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:JanaftyB??0
{*

*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*

*??T??6*


"Da misalin karfe 8:40am na Safiyar Ranar Laraba Daddy da Umma da Inteesar suka kama Hanyar Kano Booth din Daddy cike da Kayan Inteesar kamar wacce in tatafi sai bayan Wata Shekara zata Dawo saboda Uban kayan Data Diba akwatuna Biyar Shake da kayan sawa da Takalma sai kuma Sauran kayyakinta na Kwalama da kayan kwalliya.
Inteesar na Gidan Baya Umma ce agaba Fushi take yi Sosai bakinta kamar ya Fado Fuskarta a Dakune saboda ta Shiga gaban Mota Da zasu Taho Umma ta Rankwasheta akai ta Fito da ita tace sai dai ta Shiga baya don Ubanta Daddy ransa ya sosu ya Fara Fada yana Fadin"Salaha kina fa min abunda bana so..? Ina wani abun Duka anan Menene abun Damuwa Domin inte ta shiga gaba..? Ba yarki bace ke sai ki koma Baya ki Zauna..!
Kallonsa kawai Umma Tayi kafin ta kada kai Tana Fadin"Wlh Alhaji ba Domin agida na Haifi Inteesar fa Tsab zan ce ba yata bace An Sauyamin ita a asibiti ne..Kuma inda yau bani na Haifeta ba Kishiyar uwa nake gareta Tsab zan ce kana Fifita komai na Yarinyar akaina..!
Tafada Tana bayyana irin Takaichinta game da abubuwan da Alhaji yake yi komai Inteesar Tayi daidai ne koda kuwa abun Fada ne da Sakarci.
Shuru yayi bai ta amsa ba sai ma Juyawa da yayi bayan Motan yana Faman Lallashin Inteesar din wacce saboda Sangarta Harda kuka batayi Shuru ba sai da ya bata wayarsa Zata yi game Sabuwar Tata saboda Sauri bata Tsaya kwashe Apps din Datake da shi a acikin Tsohuwar ba Kuma ta manta ta agida Duk kuwa da yadda ta Shirya kayanta Duka.
Umma na gaban Mota ta kallesu ta watsar Da karamin Tsaki Inteesar ta kalleta Tana Tura mata baki acikin Ranta Tana ta kunkuni.
Bata kara bi ta kansu ba ta maida Hankalinta kan karamin azkar din Data Taho dashi Ba saboda komai tace zata Raka Inteesar ba din ba saboda Yaya Amina ne ta kwana Biyu bata leka ba kuma Tajata gefe ta bata Umarnin Da Zarar Inteesar tayi wani Rashin Ji ta rika saka Bulalane tana Jibganta kada ta Dauki wannan Sangartanta ta da Ubanta ne kadai zai iya da ita.

******

*GOMBE STATE..Dukku local goverment*
_Area:Balikaje_

A karamar Hukumar Jahar Gombe,Wato Garin na Dukku, awata anguwa da ake kira BALIKAJE yau anta tashi da sanyi sanyi kadan na Wucewar Damina da Shigowar Sanyi
Acikin anguwan daga farkon farkonta akwai wani Katafaran gida wanda kallo Daya zakayi mai ka Fahimci gidan ba fasalin ginin yanzu bane Tsohon gini ne Daya samu gyaran Masihan magina da kuma wadanda suka san Zanen Fasalta Gini yayi kyau har ya kawatu.

Tana Daga Cikin kuryan Dakinta Tana Zaune kan Darduma Misalin 9:40am na Safiyar Ranar laraba Idar da Sallar Walhanta kenan Carbi ne a Hannunta Tana ja Lokaci Daya bakinta na Motsi Wata Farar Dattijuwa ce mai akallah Shekaru 82 a Duniya yanayin Jikinta Tana dan Kiba,da kuma Tsawo Kallo Daya zakayi mata ka Shaida kirar Fulanin Dukku ne duk da Tana daga Zaune ne,
Duk da Shekarin sun ja ammh Farar Fuskarta da karan Hancinta basu Boye kansu ba..Da tsantsan kyau da Zati irin nata wanda in da zaka ka ganta Lokacin Kuruciya sai ka Tsaya Jinjina kyau da Zati irin na wannan Tsohuwar Lokacin Kuruciyarta.
Gefe gefen Fuskarta Duk Karkasan Gashi ne gashin nan yayi Fari Fat hakama Gemunta akwai Tsirarrun Fitowar gashi Haka Halittar take mai yalwar Gargasa ne hatta Hannayenta gasu nan sun kwanta Duk da kuwa Ta kwana Biyu a Duniya uwa uba gashinta kanta Dake Dunkule shima ya koma Fari Saboda Shekaru.
Sai dai aduban Farko in kayi mata sai ka Fahinci Tarin Jin Dadi da Hutu take Tattare da ita Duba da Dakin Datake Ciki da suka ji kayan alatun kawata Daki na Zamani kamar ba Dakin Tsohuwa ba
Sai dai kuma yanayin Fuskarta da yadda ta kurama waje Daya ido Zaka Fahimci Duk da wannan Jin Dadin wani abu wanda Ya Dade yana Murkusanta yana Damunta acikin ranta wanda Har ya Bayyana kan Fuskarta.

Tana Zaunen Tana Lazimi Taji Muryan Mai aikinta wacce Ta kasance kamar wata jininta kanwa gareta yanzu Wato Baba Asabe Tana Fadin"Maraba da Lauyan lauyoyi..Baban Sajida Sannu da Zuwa Lale marhaba..!
Taji Tana Fade daga Falonta,Mirmishi ta saki kafin ta Girgiza kai bata san meyasa Asabe Tafi Damuwa da Lafiyarta Fiye da karan kanta ba, Sadaukarwan da matar tayi mata mai girma ne suna Tare tun Lokacin kuruciya har yau da Girma ya kamata bata yarda da ita ba Suna zaune tare Cikin Aminci da yarda kamar yadda suka Fara Tunchan Farko.
Tasan Ko datace mata to bazata kira wani Daga cikin ya"yanta ta Daga musu Hankali ba tadai jita ne kawai tafi kowa sanin Halin Asabe..Asabe fa..Asabenta bazata Chanza ba tasan ita ta Kira KABIRUN.

Tana cikin wannan Tunanin Taji sallamarsa Cikin Muryansa din nan mai Cike da Amo da Haiba kamar ta Dan"uwansa wanda yasa sai ta waigo da Sauri Tana kara ware idanuwanta akansa Cikin Bugun Zuciya ganin ya Duka Ya Cire Takalman kafarsa sau Ciki ya Fara tako laulausan Cafet din Daya malale Dakin da Safarsa yasa ta Tabbatar ma kanta Shi kadai ne Ba Hasashenta bane kanta ta maida kawai ta Cigaba da jan Casbahanta Lokaci Daya Tana amsa Sallaman nashi a saman Labbanta.
Gabanta ya kariso ya Zauna yana Tankwashe Kafarsa Dogon Namiji ne ingarma mai Zati

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login