Showing 114001 words to 117000 words out of 236322 words

Chapter 39 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

757

da Mommy ta aiko mata dashi,suna da Sauran Nama a Fridge da kayan ciki suka Hade su sukayi Ferfesu kada su bar gidan zuwa Dukku kafin su dawo ya Lalace.
Soyan kosan ya zama na Karshe ne bayan sun gaggama komai,Safiya Da Aneesa suna tajera komai Cikin kololi ita kuma Fareesatu tana ta Jera Mug,da Filet filet da Fork iya adadin mutanen da zasu yi Amfani dashi.
Inteesar da Munari da Hafsah sune ke wajen soyan kosan,inteesar na dagachan gefe saman Cabinet din kitchen din ta Haye daga Sama Sanye take da Rigar barcin munari doguwa mai Ruwan madara,mai taushi sai dai saboda Munari tafi ta kiba sai Rigar tayi mata yawa kadan karamin mayafi ne a saman kanta ta dan Ratayeshi.
Hafsah ce ke gaban Kaskon Suya ita kuma Munari na ta faman buga Kullim kosan suna yi suna Hira Jefi Jefi.
Ba wanda yaji Shigowarsa Saboda gabadayansu Hankalinsu nakan aiyukan da sukeyi ne kuma suna Hira kuma Dayake Sallamar nashi iya Saman lebensa ne ba wanda ya Jisa.
Anty Safiya ce ta ganshi Lokacin Dayake Bude Fridge ya Dauko goran Ruwa mai Sanyi yana sanye da Jallabiya mai ruwan madara,wacce bata kai kasa ba sosai Fararan kafafuwansa masu cike da gargasa suna Waje ne.
Ganin sun Hada ido da ita yasa yace mata"Ina kwana..!
Yafada yana dan Daga idanuwansa yana Karema wadanda ke Kitchen din kallo ta kasan Idanuwansa.
Safiya tayi mirmishi Lokaci Daya Tana Fadim"Lafiya lau Imran mun tashi Lafiya..?
A saman lebensa ya amsa daidai Lokacin da suka Hada ido da Inteesar wacce ta Kuramai ido tana kallonsa cike da wani Shaukin da bata san dashi ba,Kowa ya juyo yana kallonsa ganin haka yasa Munari ta gaisheshi Hafsah ma haka su Aneesa ma suka gaisheshi ba domin ya isa ba sai Domin yana da kwarjini da cika Fuska uwa uba kuma Oga Imu ne da kansa ai baza ka jira sai ya gaisheka ba..
Tundaga gaisuwar Farko bai kara amaawa kowa ba ganin haka Inteesar taki gaisheshi,Sai ma wani lamgwabe kai datake yi tana kallonsa Shi kuma Gabansa ne ya Fadi ganin saman kirjinta yana waje ne,Kuma Rigar bata da wani kauri ga Shatin saman Nonuwanta nan ta waje Jikinsa ne yaji ya fara rawa yasa ya juya zai Bar Kitchen din dauke da goran Ruwan a Hannunsa.
Daman Inteesar tana ta gefensa ta bangaran Fita ne,ita bata sani ba yazo fita sai ta zuro kafarta ta taba mai Cinyarsa da sauri ta janye tana kallonsa kankance idanuwansa yayi yana kallonta kafin yace cikin Sanyin Murya."Ke kin raina ni ko..?kowa ya gaisheni ammh ban dake ko..?
Noke kai tayi tana yar dariya kafin tace"Ina kwana..!Mirmishi kadai yayi na gefen baki yana Ficewa Daga Kitchen din bai ce komai ba.
Yana Fita Munari da Hafsah da suka ga komai suka Juyo suna kallon Inteesar dake Dariya kasa kasa suka kalli juna suna rike baki tana juyowa suka Hada ido da ita,Ganin yadda suke kallonta yasa ta bata rai ta wani Hura Hanci Dariya suka saka Harda Tafawa ita da Munari Hafsah tayi ma Munari Rada a kunni tana Fadin"Yarinyar nan akwai munafuncin datake Boye mana..!
Hafsah tace"Barta..Kuma zasu dace da Masoya..!
Suka kara Kyalkyacewa da Dariya Inteesae ta tsargu ta Shagwabe Fuska Tana Fadin"Anty Safiya ga su Munari nan basa aikin da kika saka su suna ta Gulmana..!
Anty Safiya ta waigo Tana Fadin"Kuyi dai ku gama lokaci yana tafiya..!
Da toh suka amsa ita kuma Inteesar tana yi musu gwalo,su kuma suna ta Hararanta tana Dariya sama sama.
Cikin Lokaci suka gama komai su Inteesar suka je sukayi wanka Domin sunce bazasu iya Karyawa basu yi wanka ba,jin haka yasa suma suka Shiga Domin yin wanka suyi ma yaransu kafin su Abba su fito.
Karfe 9:00am na Safe kowa ya Hallara a Falon saboda Breakfast,An shimfida Katuwar Darduma anan Tsarkar falon su ka jera komai asamanta.
Sai da kowa ya Hallara banda Imu,Har an fara karyawan Daddy ya Dago yana kallon Yusuf kafin yace"Ina Dan"uwa yake Yusuf..?
Yusuf na Kurban Tea dinsa yace"Baffa yana Cikin dakinsa..!
Ya kada kai yana Fadin"Meyasa bai fito ya karya ba..?
Yusuf yace"Bai cika cin wani abu da Safe haka ba kila sai chan da Rana..!
Kada kai kawai yayi bai ce komai ba Mami Asma"u na gefe aranta tace gwara hakan ma Domin Tun abunda ya faru jiya Tsagerancin yaron yayi mata Tsaye a saman kanta.
Inteeesar dake gefen Hafsah zaune ta Dauko Wayarta ta Shiga Messages ta Turama Imu sako.
"Ya imu kafito kayi breakfast..!
Ba dadewa ya maido mata da amasa.
"Bana jin yunwa..am ok..!
Inteesar na ganin haka ta Turamai da Sauri.
"Saboda ka cika cikinka da Hayakin Sigari ko Ya Imu..!?
Sai da yadan jima kafin ya bata amsarta,Tama kasa cin kosan dake gabanta Hankalinta na kan wayarta.
"Eh..!
Kawai yace mata Mirmishi tayi tasan bazai mata karya ba Tunda yace Eh to yasha ne,sai ta Rubutamai.
"Kana so ka mutu ne Ya Imu..?
Da sauri ya maido mata amsa wannan karon.
"Eh in na mutu Who care..!?
Tana ganin haka sai da gabanta ya Fadi da Sauri ta Rubutamai.
"Ni mana..Zan ta kuka nadaina cin abinci har nima na mutu..!
Yana kwance ne yaga sakonta sai da ya Mike zaune yana sosa goshinsa afili ya Furta yarinyar nan akwai Rigima.
Amsa ya bata da cewa"bazaki mutu ba..!
Tana ganin haka da sauri ta maidamai da amsa.
"Zan mutu mana indai kai ma ka Mutu na daina ganinka Ya Imu..!
Sai da ya dade bai Bata amsa mata ba har ta Fara sarewa sai ga sakonsa ya Shigo
"Wayace miki zan mutu yanzu..? Oya eat ur Food bana son shagwaba am not in d mood..!
Tana ganin haka sai da tayi Mirmishi akallah dai}? tasakashi yayi mgana batayi kokarin kara Turamai komai ba sanin Tunda yace baya cikin Mood din bazai kara cemata komai ba Tana kallon Wayarta Tana Mirmishi ita kadai Hafsah data Tabo Munari Tun dazu suna ta kallonta ta dago suka Hada ido Hararansu tayi kafin ta Boye Wayarta cikin karamin Hijabin Dake Jikinta,Su kuwa me zasu yi in ba Dariya ba Har sai da kowa ya Juyo yana kallonsu Daddy dake lura da Inteesar tun dazu bataci komai ba sai Danna waya take yace"Intee ijiye wayar nan ki Karya..!
Kanta a kasa tace"To Daddy..!
Lokaci daya Tana Hararan su Hafdah dake mata Dariya kasa kasa.
Basu wani bata Lokaci wajen Breakfast din ba,kowa ya tashi su Hafsah suka Tattara komai zuwa Kitchen suka fara wankewa,Su kuma su Anty Safiya suna ciki suna Shirya Tunda ance kowa ya shirya nan da 11am zasu dauki Hanya.
Suna gama wanke wanken suka Gyara Kitchen din suka koma Daki Domin Shiryawa Munari ta kalli Inteesar Tana Fadin"Intee ya zamu yi da School yau..!
Inteesar tace"Ya kuwa..? in mun dawo zamu yi covering din inda aka wucemu..!.
Munari ta gyada kai alamun gamsuwa Inteesar ta kalleta tana fadin"Sai naje gidan Mama na Dauko kayana..!
Munari tace"Basai ki saka nawa ba..!.
Inteesar tace"A"a bazan iya ba sun min yawa salon na Dinga yawo aciki..!
Hafsah ta saka Dariya ita da Munari Inteesar ta Hararesu bata kara cewa komai ba.
Sai da ta jira su Munari suka Shirya tsab Munari ta Hada kayanta cikin karamar akwati kala Biyu da kayan barci Tunda basu san yaushe zasu dawo ba Inteesar tace su hada kayansu Waje daya Shiyasa suka Dauki akwatin kayan zuwa gidan su Mama su dauko na Inteesar su tsaya ta Shirya achan Tare da Umma suka Tafi zata leka yar"uwanta.
Suna zuwa gidan Abun mamaki suka Iske Sagir shima cikin Shirinsa na Tafiya basu Shiga mamaki ba sai da sukaji Mama na fada musu Imran ne ya Kira Sagir yace su Shirya su tafi Dukku Tare.
Umma dariya kawai tayi bata da tace akan Lamarin Imran ballatana Mama.
A gurguje Inteeesar ta Shirya Cikin Riga da Sikat na wata atamfarta Codedubuwa mai kalan Blue da Fari sai tayi amfani da bakar jaka da Takalmi da mayafi baki ta Dauko Kayanta itama kala Biyu da kayan baeci sai kananun kayan da zata Bukata suka Hada kayansu Waje Daya suna Shirin fitowa Daddy ya Kira Umma yace su dawo ana Jiransu.
Dole suka Fito da Sauri Sagir ya Tsaya Shagonsa yana sallama da yaransa,Su kuma suka tafi har da Mama data Yo musu Rakiya bakin kofar gida Tana ta addu"an Allah ya Kiyaye Hanya.
Koda suka iso duk suna Haraban gidan ne,kowa cikin Shirin Tafiya Bangaram su Ya Basheer su Inteesar suka karisa suka gaishesu kana suka karisa inda su Abba ke tsaye suka gaishesu suka amsa cikin Sakin Fuska.
Sannan suka juya suna gaida Mami Asma"u dake gefe tsaye tana Latsa wayarta tana kallon Mutane ta Cikin Siririn Gilashinta,Sama sama ta amsa musu ba wanda ya Damu da ita sanin Halinta.
Aka Fara saka kaya acikin Mota Yusuf yayi Riverse da Motarsa,zuwa Inda Abba ke Tsaye yaci Shadda Fara Tazarce yayi shar dashi,Sadam daman Da safe yaje gida ya Dauko musu kaya nashi dana Aneesa da yara dukkansu sun Dauki Uzuri a wajen aikinsu yau sai Dukku.
Awajen kowa ya hallara Imran ne kadai bai fito ba Abba ya yafito Yusuf da Hannu yana zuwa yace mai"Kira min Imran..!
Yataka kenan zai koma cikin Gidan sai ga Imran ya fito Sanye cikin Riga da Wando baki da Fari na kamfanin DKNY,wandon baki ne yadan kamasa ta kasa sai wani katon bakin Booth din Takakmi sai Farar rigaraa mai kauri mai gajeren hannu Tana da Rubutu baki agaban rigan an saka GENTLY.
kansa kuma yasha gyara Dadan nan ya Zauna Daram yana Sheki Fuskarsa ba Fara"a ko kadan kamar an aiko mai da sakon mutuwa Hannunsa sanye da agogon Fata,Bayansa Rataye da wata Jaka baka irin ta matafiya inda ya saka kayansa da Abunda zai bukata Tunda Umarnin Abba ne bai isa ya Taallake ba ammh ba domin shi ba ya Rantse har ga Allah bamai sakashi zuwa Dukku yau.
Yusuf ya kalli Abba yana Fadin"Gama Imu din nan Abba..!
Kai Abba ya gyada kafin ya juya yana kallonsa yana Tahowa Hannunsa Daya Cikin aljihun wandonsa Dayan kuma karamar wayarsace a hannu yana Dannawa ba Abba kadai dayake Dansa ba kowa awajen sai da ya tsaya yana kallon Imran koda yanayin Tafiyarsa zaka Fahimci shi din Namiji ne ballatana Cikar Zatinsa da Kwarjinsa na dabam ne.
Inteesar dake tare da su Ya Basheer tana Rokonshi suna son zama amota Daya ita da Munari da Hafsah, bata san ta shagala da kallonsa ba sai da taji Basheer na fadamata to su shiga Motar Sadam shi zai tuka su Umma.
Kana ta iya dawowa cikin Hayyacinta Tana Sauke Nunfashi.
Imran kuwa gaban Abba ya karisa Ya gaishesu ina kwananku yace sau daya bai kara cewa komai ba ya Dauke kansa sama Daddy ne kadai ya amsa sai Abba ammh Baffa kabiru na gefe yana Waya..
Abba ya dafa kafadansa yana Fadin"me ka tsaya yi kaifa kadai muke jira..!?
Imran yace"Abba Sagir nake jira..!
Abba da Yusuf suka kallesa cikin}? mamakinsa Kafin Abba yace"Sagir kuma..?
Kai ya gyada batare da yayi mgana ba suma basu ce komai ba sai Yusuf dayace"Ka kirasa zamu wuce ne..!
Bai yi musu ba ya koma Gefe yana Kiran Sagir ta waya.
Su kuma su yusuf suka fara tsara yadda Zaman Motan zai gudana.
Abba da Daddy da Baffa Kabiru zasu shiga Motarsa Direbansa yajasu wanda ya kwana nan wajen Iro megadi.
Sai Umma da Mami Asma"u zasu hau Motar Sa"id.
Yusuf kuma zai Dauki Imran da Sagir,Sadam kuma zai Dauki Fareesatu da Aneesa da Safiya da yaransu sai Basheer zai dauki Su Inteesar.
Kowa ya yarda da Tsarin banda Mami Asma"u data bata rai tafiso tayi tafiya Mota Daya da Mijinta sai dai bata samu Fuska ba Wajen Baffa Kabiru ko yaya naka yake ai naka ne tuni sun shige Mota shi da yan"uwansa Dole itama ta shiga Motar Sa"id gidan Baya Umma ta shiga gaba abunta.
Imran bai shiga Mota ba sai da Sagir yazo kana ya yarda ya shiga gidan gaba Sagir ya shiga baya.
Motan su Abba ce ta fara fita Daga gidan sai Motar su Umma sai ta Sadam sai ta Basheer sai ta Yusuf ta Karshe,Iro nata daga musu hannu da Fatan Allah ya kai lafiya.
Da suka dawo sallar asuba Yusuf ke fadamai zasu yi tafiya na kwana Biyu kafin su dawo ya kula da gida yace bakomai Cikin gida kuwa daman sun kulle kulle ko"ina kafin su tafi.
Sai da suka Dauki Hanya kana
Baffa Kabiru ya kalli Abba yana Fadin"wanchan da naganshi Tare da Imran waye..?
Abba yace"Sagir..?abokinsa ne..!
Baffa Kabiru yace"Tafiyar ta Shafesa ne..!?
Abba yace"Imran yace yazo yamai Rakiya..D'a na kowa ne ballatana Sagir ba bare bane na gida ne yaron wajen Yayar Salaha ne matar Mustapha Dalilinsune ma kuka san inda muke zaune..!
Baffa Kabiru bai kara mgana ba Daga gani zuwan Sagir din bai mai Dadi ba Daddy dai da Abba suka cigaba da Tattauna mganarsu.
Suna Hanya sun kusa shiga Gombe Inna Maimunatu ta Kira waya tace gasu fa a dukku koda ta iso ta iske Inna Bintalo da ya"yanta sun iso sun gama Gayama Daada Komai ga Daadan nan sai kuka take tana cewa Ta kosa taga Malami ko Hankalinta zai kwanta.
Daddy yace ai gasu nan sun kusa isowa da yardan Allah har aka bama Daadan ya kara Lallashinta bai dai bama Abba Wayar ba yafiso suga juna Ido na ganin ido.

Sun tsaya a Gombe sunyi Sallar azahar wajen karfe Biyu na rana kana suka Dauki Hanyar Dukku ba Dadewa suka iso Cikin Haraban gidansu na Dukku Abba na kallon Haraban gidan yana ganin komai kamar baya babu abunda ya Sauya sai ma sauye Sauye da aka samu,Idanuwansa suka ciko da kwallah na kewar Gida da Ahalinsa gabadaya da Daada dayake matukar jin kunyar Hada ido da ita.
Sai da kowa ya fito daga Mota kana Imu ya fito yana cin mgani Sagir sai bin Gidan da kallo yake yi yana Auna wasu abubuwa acikin ransa,Da Inteesar suka Hada ido suna Shirin Shiga Cikin gidan gira ta Dagamai Kafin ta dagamai hannu kau ya kauda kai kamar bai ganta ba,nan kuwa sun yi ma juna sako ta waya Inteesar sai mai Tabara take wai ta gaji da Zaman Mota shi kuma yace ta ce a sauketa in ta gama Hutawa sai ta hayo wata Motar ta samesu achan tunda bayan Shagwaba da Rigima ita din Raguwa ce sai Dariya take dayacemata haka.
Daddy ya Riko Hannun Abba gaba gaba zuwa Babban Falon Daada.
Wanda tunda sukaji isowarsu suka Firfito falo Daada da kafarta ta Fito Tarban Abba su Inteesar suka Fara shigowa sai su Aneesa da su Umma Mazan suna Baya ya"yan Inna Mainunatu su zainab natayi musu maraba su kuma suna ta Neman inda zasu ga Dan"uwansu,sai gashi Sun shigo shi da Daddy Baffa Kabiru na Binsu ta baya,Su Basheer na takemai baya Imu da Sagir ne abaya shi yana Tafiyama kamar bazai taka kasa ba.
Inna Maimunatu ce ta fara isa wajen Abba ta Rikeshi da Murna tana kwallah ita da Inna Bintalo,Daada na Bayansu Baba Asabe na Riketa Cikin Mika Hannu take fadin"Ina Malami..Taho nan naji Duminka na Tabbatar da yau Allah ya amshi addu"ata..!
Tafada cikin murya Tsufa Dakyar ya saki Hannunyensu inna Bintalo ya Nufi Daada cikin karayan zuciya,Hannayenta ya Riko yana Fadin"Daada...Daada..ki yafemi...!
Sai Hawaye Daada ta Rumgumesa tana Shafa bayansa Lokaci Daya Tana Fadin"Har Abada banta rike ka acikin Raina ba Malami..Addu"q da Fatan alheri ne tsakanina dakai naji dadi nagodema Allah dana ganka ka dawo Cikin Koshin lafiyarka Abubakar..!
Daada ta fada Cikon muryan kuka Duka suna Tsaye cikin Tsasayawa da Fuskar farinciki.
Ta dagosa Tana kallonsa kafin ta Shafa kanshi Tana Fadin"Allah na gode maka..Zan hada kan iyalaina kafin nabar gidan Duniya..Ina yaran nan Yusuf da Maimunatu..!
Abba ya juya yana Kiran Yusuf ya Taho da Sauri Munari ma haka Abba yakira Safiya itama ta kariso zuwa gaban Daada.
Daada na Hawaye ta Rike yusuf Tana Fadin"Yanzu wannan Yusufa ne..?
Kamkame hannunta yayi yana Fadin"Nine Daada..!
Idonsa ya ciko da Hawaye Ta dafa kansa Tana fadin"Masha Allah naji Dadin ganinku cikin Koshin lafiya..!
Tafada kafin ta maida Dubanta kan Munari dake Hawaye Daada ta Dafa kanta Tana fadin"Mai sunan Auta ta zama Budurwa itama Maimunatu kin ganeni..? Nice karki Daada..!
Tafada cikin karaya da tsufa jin haka yasa Munari ta Rumgumeta Tana Fadin"Eh na ganeki mana Daada..Daadam Dukku..Daadan Anni..!
Jin haka yasa kukan Daada ya Karu ta Rike Maimunatu tana fadin"Allah ya jikan Zuwaira da gafara..Allah ya jikansu ita da ya"yanta da suka rigamu gidan gaskiya..!
Gabadaya aka amsa da Ameem jikin kowa a sanyaye.
Daada ta dago da Munari daga jikinta Tana fadin"Ina yar tselen uwar nan Maryama da akace kun hadu Tuntuni baku gane juna ba..?
Munari na Dariya ganin Inteesar ta Hade rai tana fadin"Kai Daada bama kiji Dadi ba sanadina kin hadu da Baffa ba..!
Daada na Dariya tace"Naji dadi kwarai sai dai abu dayane bai min dadi ba..Yadda kika hadu da yan"uwanki baki sani ba wannan Dalilin ya kara Zaburar dani gyara wanu Gibi dna barsa a Bude insha Allahu..!
Baffa Kabiru ne yace kowa ya zauna Kada Daada ta gaji da Tsayuwa kowa ya samu waje ya zauna,Munari ta makale kusa da Daada Abba kasa ya zauna saman Cafet kusa da kafufuwan Daada shi da Yusuf.
Daada Mirmishi yaki barin Fuskarta sai Hamdala take acikin Ranta haka Yusuf da Munari bakinsu yaki Rufuwa Safiya sai waige waige takeyi Tana kallon kowa aranta Tna fadin ina Abbu yazo yaga Asali da kyakyawan Ahalin irin ahalin su Yusuf wadanda suka fisu komai na Rayuwa.
Daada ce ta ganta bata santa ba ta Kalli Abba Tana fadin"Malami wacece wannan..! Badai aure ka kara ba bamu sani ba..?
Mirmishi yayi Safiya sai taji kunya ta Sadda kanta}? Abba yakalli Daada yana Fadin"Yaushe na Warken ne Daada da zan kara aure..? Matar Yusuf ce wattani Baya ya aureta..!
Daada ta washe baki Tana fadin"Masha Allah taho nan Yata bana Jikar dake ni..!
Safiya ta Rarrafa wajen Daada ta Shafa kanta tana tasaka albarka.
Daada ta fara Wurga wurga ido tana neman wanda take son gani Sai dai bata gansa ba yana ta bayanta Shi da Sagir suna Tsaye kamar wasu sojoji sagir na son zama Imran saboda Mugunta ya hanashi.
Cikin dan Rage fara"a Daada tace"Malami ina cikon Dayan..? Ina jikana Imrana..!
Abba ya dago shima yana Wurga Idanuwansa cikin Falon hakama kowa afalon ke wurgawa sai gashi an Tsintosa chan baya kamar wani bare Baba Asabe ne Dake gefe tace"Daada gashi nan a bayanki..!
Duk da bata wani sanshi ba ammh yanayinsa yasa tasanshine Imran din ballatana ai tana jin Labarinsa Wajen Daada.
Abba ya kalli Baba Asabe yana Fadin"Baba Asabe ya bayan rabuwa..?
Baba Asabe na Dariya tace"Sai alherin Malamin Daada Tunda gaka ka dawo Ciwon Daada ya Kare..!
Yana Mirmishi yace"Da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login