Showing 6001 words to 9000 words out of 236322 words

Chapter 3 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

704

wannan Tunanin yasa Jikinsa na rawa ya matsa kusa dasu Imran yana Fadin"Kaga ba sai an kai ga Haka ba..ku Turo mgabatanku Shikenan Tunda kun nace itama ta nace sai shi.."Yafada yanawani fiki Fiki da ido na marasa gaskiya Sagir Sai da Dariya ta kusa kamashi Imran kuwa Hannunsa ya Fizge Daga na Sagir ya Tura Hannu a aljihunsa ya Dauki kwalin Tabansa Har ya karar da ita Saura Daya ya Daukota ya Jefar da kwalin ya Jawo makunni ya kunnata ya Zuka ya Fesar da Hayaki kana ya kalli Alhaji Alhassan da Jajayen manyan Idanuwansa yace"Ka kira Yayana ka sanar dashi yanzu..NAN..! Ya karishe Fada Cikin Tsawa da Sauri Alhaji Alhassan yace"Yanzu kuwa..Insha Allahu.."Yafada yana rawan Baki Imran bai Saki Fuska ba ya Taka Hargaban Safiya bai Taba ganinta ba sai sau Daya da Yusuf}? ya taba nuna masa hotonta duk da bai wani kalleta ba sosai ba,da Jajayen idanuwansa ya kare mata kallo Daga sama Har kasa Tasleem kuwa bayanta ta Labe Tana Toshe Hanci Daya lura da ita tsawa ya Daka mata yana Fadin"Ke....'jiki na rawa ta Dago kanta tana kalleshi cikin Dakiya yace"Ni sa"an ki ne da kike ganina kina Tushe Hanci..? Maza Bude Hancinki kafin ki Tunzurani na Targaki yanzu agaban Iyayenki..!"Da Sauri Tasleem ta saki Hancinta Tana rawan Jiki ta kamkame Bayan Safiya Da kanta ke Duke Tana kuka Hajiya Mero kuwa gum Tayi da bakinta batayi mgana ba Duk da itama warin Tabae ta isheta sai dai ba Halin mgana ganin yanayin Imran din ya Firgitata ta tabbata ko ita ba Shakkarta zai yi ba balle ma Dataga Shi kanshi Alhaji ya Saduda

Safiya ya kallah kafin yace"Bhabi..Stop craying...Kin auri Yayana kin gama..See u sai mun Hadu a GIDANMU.."ya karishe Fada yana wani Mirmishi kafin ya Zuki Tabarsa ya Fesa musu Hayaki kana Lokaci Daya ya Juya yana wani taku Daya Bayan Daya yana wani Rangaji ya Fice Daga gidan Sagir ya maramai Baya Megadi ya Bisu da Allah ya Kiyaye sai da Alhaji Alhassan yaji tashin Mashin din Imran kana ya iya Motsi Juyawa yayi yana kallonsu Kafin ya Fara Bambamin kunya.

"Tsayuwar mu kuke yi kukama..? Ai sai ku shiga Cikin gida...Ke Safiya ki kira shi yaron kicemai ya Turo manyansa Tunda irin Gidan da kika Zaba kiyi Rayuwa kenan ke kika sani.."Daga haka ya Saba Zaman babbar Rigarsa ya nufi Motarsa Direbansa ya Budemai Bayan Bakar prado dinsa ya Shige yana jin Zufa na ketomai Kafin Direba ya Shiga Bangaran Direba yayi Rivers Ya yi Hon megadi ya wangale get suka Fice sai alokacin Safiya ta Juya Cikin gida da Gudu Tana Dariya da kuka Tasleem ta Mara mata Baya kana Hajiya Mero da Jikinta ya gama yin sanyi da al"amarin Data gani.

Imran kuwa Har ya maida Sagir bakin Shagonsa bai ce mai kanzil ba sai da ya ijiyesa kana Sagir ya kallesa yace"Mama Tana ta Cigiyarka.."Imran yayi Mirmishi kafin yace"Kace mata Zan shigo Gobe.."Daga haka ya Bama Mashin Dinsa wuta ya wuce ya bar Sagir da binsa da kallo har ya Bacema ganinsa bai koma Shagon ba ya Nufi Gidansu Dake Jikin Shagon nashi Domin ya Dauko wayarsa da Littafansa ya Shiga makaranta.

Yana Shigowa Falon ya ci karo da Yusuf sai washe baki yake Cikin Murna ya Sarke Hannayensa yana Fadin"Bro..Wai me kayi ne..?Yanzu Safiya ta kirani tace Abbanta yaje na Turo Manya..Am so Suprise Mutumin Daya gama Rantsuwan jiyanan bazai taba bani Auran yarsa ba sai gashi yau da kanshi yace na Turo manyana.."
Mirmishin Jin Dadi Imran ya saki ganin Dariya a Fuskarsa Dan"uwansa Hannunsa ya Zare kafin ya Dafa Kafadarsa yana Fadin"Imran kaifi Daya ne..Yana Cika Duk Abunda yace..So sai ka Fara Shirye Shirye ka kusa Zama ango akalla bayan Wasu Shekaru zamu samu wata mace zata karu acikin GIDANMU..!

Yana gama Fadin haka ya Sauke Hannunshi ya Wuce zuwa Dakinsa ya Shige ya Turo Kofa,Yusuf ya Bishi da kallon Kauna da Tsausayin Dan"uwansa kafin ya Girgiza kai yana Fadin"Kana Matukar Burgeni IMRAN ABUBAKAR MALAMI.."daga haka ya juya zuwa Dakin Abba Cikin Farinciki Domin ya sanar dashi Allah yayi zai yi aure wannan karan.

******

*KADUNA..*
_Area:Anguwan Sarki.._

Acikin anguwan Sarki acikin wani Tangamemen gida na Zamani Da misalin karfe 8pm na Dare wata yar Matashiyar Budurwa nagani wacce bata wuce Shekara 20 ba aduniya Doguwa ce sosai bata da Kiba Kirjinta kadai ne yake Tudu daga kasanta kuma ba wani abun kirki Sai Doguwar Fuskarta Kalar Fatarta baka ce ammh Ta samu Hutu da Jin Dadi,bata da Dogon Hanci Sai dai kana ganinta zaka Fahimci Ta Hada Jinsi da Fulani ko ta Uba ko ta Uwa tun bare ma yanayin Tsawonta da Idanuwanta Masu Dauke da gashin ido da kuma Gashinta Data Tufkeshi Har ya sauko Zuwa ga wuyanta.
Sanye Take da wata karamar Riga kamar Shimi Doguwa kanta ba Dankwali Sai Faman loda kaya take cikin wata Trolley bayan wadanda Tagama Durawa akwatuna Hudu gasunan a jere asaman Dan madaidaicin gadonta.

Har aka Bude Kofar aka Shigo Bata sani ba sai da taji Daga Bayanta ance"Auta wannan Uban kayan Duk na zuwa Kanon ne..?
Muryan wani Namiji ya Fadi hakan da Sauri ta waigo Tana kallonsa Shima kamar ita yake sai dai abun mamaki Shi Fari ne kuma ya Fita Dogon Hanci da Jikin Maza saboda yana da Dam Kiba ammh da tsawon da yanayin komai iri Dayane,Shekarunsa kuwa baza su wuce 30 aduniya ba

Zurawa Tayi da gudu zuwa gareshi ta Rumgumeshi Tana Fadin"Ya Bashir..Yaushe kazo..? Yana Mirmishi ya Shafa kanta yana Fadin"Autan Umma Kenan..Yanzu na Shigo nazo kawo su Abiden ne sun saka Rigiman wajen Umma yau zasu kwana.."Fuska Ta tabe kafin tace"Nifa ban gane musu bane..Suna so su kwacemin mtsayina wajen Umma da Da Daddy.."Yana Dariya yace"Wane su su kwace gwamnatin autan Umma da Daddy..Shalelen Ya Bashir da Anty Hauwa.."Tanajin wannan kirarin ta washe baki Tana Fadin"Shiyasa nake matukar sonka Ya Bashir..Zan yi kewarka in na tafi kano.."

Ta karishe Fada Kamar tayi kuka irin na Shagwabbun yara bai samu Zarafin mgana ba wata Mata Baka mai Fadin Fuska wacce sai da ta Shigo na Fahimci inda ta Dibo Bakin Fatarta da Hancinta irin nata ne sak,Sai dai ita bata da Tsawo a Shekaru bazata gaza 40 ba Tana Shigowa ta gansu ahaka ta Tabe baki Tana Fadin"Kana nan kana Biye Shiriritar INTEESAR KO.? tun Dazu nake mata mganar ta Rage wadanan kayan taki jin mganata Ta kwashe Rabin kayanta kamar Chaj zata koma Har Abada..!
Umma ta Fada Cikin kara Bayyana mamakinta Wacce aka kira da Intesar ta Fara Buga kafa na Shagwaba Tana Fadin"to ni Umma ba Karatu zan Tafi ba..Kuma ai ance yan Jami"a fa yan gayu ne sosai Dole nima naje da kayan gayuna kada wata ma ta Rainani.."Ya Bashir ya saka Dariya yana Fadin"Hakane fa Intin Umma..Gwara kije da Kayanki Jjc Student.."Ya karishe Fada yana Dariya jin Abunda yace ne yasa ta Nakwa nakwa kamar Zatayi kuka ta Kwashi Gudu Ta Fice Daga Dakin Tana Kukan Shagwabarta Tana Fadin"Sai na gayama Daddy..Kai da Umma kun hademin kai kuna min Dariya..!

Umma ta Tabe baki ta kalle Bashir Dake Dariya tace"Kabiya ta Kitchen ka Karbi Dambun Wajen Talatu katafin ma Hauwa"u dashi.."Cikin Ladabi yace"To Umma..Angode.."Batayi mgana ta Fice Daga Dakin Shima ya Rufa mata Baya Jin Daddy na Kiran sunansa Topa Auta ta kai Sunansa yau shi da Daddy sai Allah Dariya kawai yake kasa kasa Har ya Kariso Falon.










*Shakira...*
3/22/22, 23:02 - Ummi Tandama???i: *GIDANMU..*!
_(Our House)_
*Book1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty*B??0
{

*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*

*??T??3*


"Da sallama ya Shigo Falon yana Danne Dariyansa ganin Inteesar dare Dare kan cinyar Daddy Tana ta Zubamai Shagwaba shi kuma yana ta Biye mata yana Lallashinta ga Abideen da Abida suna Tsaye gefe suna kallonta Daga duk alamu suna kan Jikin Daddy din ne tazo ta Turesu ta Haye Daman tace wajenta ne suke Neman su kwace mata.

*ALHAJI MUSTAPHA HAMISU DUKKU* ya Dago kyakyawan Farar Fuskarsa Tar da ita kamar ataba Jini ya Fito,Hancinsa Har baka yake kana masa kallon Farko zaka Shaida Tabbas Bafullace ne,Akallah Shekara bazai gaza Shekaru 58 aduniya ba Fararsa ta goge da jin Dadi da Hutu In ka kara kallonsa zaka Fahinci inda suka Dauko Tsawo da Doguwar Fuska Daga Bashir din Har Inteesar din sai dai Bashir Hasken Mahaifinsa ya Debo wanda Gashin kansa da Gemunsa suka Fara Zama Fari bakin gashin kadan ne Daga ganin sa yana da yalwar gargasa ajikinsa.

Cikin Muryansa ta Dattako ya kalli Bashir yana Fadin"Taho nan..Naji Meyasa kuka Tasa Autana agaba kuna mata Dariya kai da Mamarka..? Yafada yana dan Hade ransa ganin yadda Inti din ke kallonsa Bashir na kanne Dariyansa ya Zauna akasa Kusa da Kafar Daddy,Da gudu kuwa su Abiden suka Nufesa ya Daukesu ya aza kan jikinsa,Daga ganinsu yan Biyu ne saboda suna da Tsananin kama da juna Shekarasu bazai Wuce 3 aduniya ba yara ne kanana sai dai sun Debo Tsawon Babansu suna da Tsayi ba Laifi.

Cikin Ladabi yace"Daddy ba Dariya muke mata bafa..Ita Da Umma ne tana mata Fadan Ta Dibi kaya dayawa Shine tace saboda kada taje yan Jami"a su Raina Sai fa kawai nace Jjc shikenan fa Daddy ta Fara Shagwabarta.."Ya karisa Fada Daidai Lokacin da Umma ta Fito Daga Bedroom din Dake Cikin Falon,Ta kariso kusa da Daddy ta Zauna Tana Kallon Intisar Lokaci Daya Tana Fadin"Ke miye haka..? Ko kunya baki ji ba Godai godai Dake kin Ture yara kasa ke Kin Hau Cinya ko.? Anya Inti kina so ki Girma kuwa.? Yarinya kina Girma kina kara Komawa baya koda yake ba Laifin ki bane na Alhaji ne duk ya Sangartaki.."
Ko kafin tagama Mganarta Bakin Inti ya kusa Fadowa kasa Cikin Sangarta Ta kalli Daddy Tana Fadin"Daddy kaji Umma ko..? Shiyasa nake ta Murna zan Tafi na bar mata gidan.."Ta karishe Fada tana wani Tura baki.
Umma ta tabe baki Tana Fadin"Ai chan bazaki samu Damar yin wannan Sangarta ba..Yaya Amina ba Irin Sakarkarun Matanan bane atsaye take..Ga kuma yayanki Sagir zan ce mai da kinyi wani Abu ya Zanemin ke.."Kawai ba sai Inti ta Saki kuka Kamar wata karamar yarinyar Bashir sai Dariya yake Umma ta kalleta Sororo kafin tace"Yau naga Sakalci Inti wai yaushe Zaki Girma ne..? Kin fa wuce Shekara ashirin Kina Shirin Shiga Jami"a kina Tabara Yau ko aurar dake mukayi Badi war haka kin Haihu.."Ai jin haka sai Inti ta kara Sautin kukanta Tanayi Tana Fadin"Ni ba zanyi aure ba..Kuma bazan Haihu ba.."Kai Dagajin kukan kasan na Sangarta ne Daddy ke Lallashinta yana Fadin"To daman yaushe Autana}? ta isa aure..!? Ai ba yanzu zaki aure ba sai kin kara girma...Shima sai naga Dacewar Mijin da Zaki aura wanda zai Rikemin ke ya Rika Lallabaki kamar yadda nake Lallabaki sai yayimin alkawarin kula da Hakan kana zan yarda na Bashi Autana.."Ya karishe Fada yana Shafa Kumatunta da Sauri ta Washe baki Lokaci Daya Tana Fadin"Shiyasa nafi sonka..Akan Umma Daddy..Kafi sona..Ita kuwa ssi ta cemin wai ni Shagwabbiyace.."
Daddy yace"Rabu da ita...Duk yan Bakin ciki ne.."Ya Bashir na Dariya yace'Hardani Intin Umma..? Tana wani mele baki Tace"Ni ba Intin Umma bace..Intin Daddynta ne.."Umma na jinta Tayi tsaki Tana Fadin'Nabarmai yayi ta kaya..Ni ai Bashir ne D'ana..Ni Daman ba Mamanki bace Daga Gidan Marayu Alhaji ya Dauko ki.."Baki ta Bare zata kara sakin kuka Daddy ya Riketa yana Fadin"Au kukan zaki mata..? Daman ta Fadane don ta saki kuka..Haushin kinfi sona ne Autana Rabu dasu.."
Washe baki Tayi tana Fadin"Yauwa Daddyna..Ammh zaka Kira Inna Amina kamata mgana ko..? Kaji fa umma nacewa Zata saka D'anta wai ya Rika Dukana.."Tafada Idanuwanta na Cika da kwallah Domin inti akwai Tsoron Duka.

Kanta yake Shafawa yana Fadin"Waneshi ya Dakarmin Auta guda..? Sha kurumin ki ni Dakaina zan kai ki Har kano gaban Innan naki na Bada Amanarki kana naja ma D'an wajen nata kunni komai kikayi kada ya Dakeki ya Lallabaki ne Saboda ke Auta ce.."Murna Ta Farayi ta Rumgumeshi Tana Fadin"Ina Kaunarka Daddyna."Kanta yake Shafawa yana Fadin"Nima haka Auta Daga ke ba Kari Intin Babanta.."Umma Dake Goge ma Abidin Baki Daya bata da Madara tace"Uhm..Bashir tashi ka Tafi gidanka kada ka Biyema wannan Shirmen na Alhaji da yarsa..Kabar Hauwa ita kadai gashi kuma kasan Halin Datake Ciki.."Yana Kokarin mikewa yace"To Umma..."
Yafada yana Mika mata Abida Data Fara Barci ta karbeta Lokaci Daya yana Fadin"Daddy zan tafi..Sai Allah ya kaimu.!
Daddy yace"Shikenan Bashir.Ya ake}? Ciki kan mganar Tafiyar Inti din..? Kunyi mgana da yaron Wajen Innan naku..?
Bashir yace"Eh Daddy munyi mgana..Lokaci fa ya tafi Tuni sun Fara Lacture ya kamata Cikin Satin nan Tatafi tayi Registration Sati na Sama ta Fara karatu gaskiya.."
Daddy ya Jinjina kai yana Fadin"Shikenan Zuwa Jibi sai muje na kaita..Insha Allahu kafin Lokacin Komai ya kamallah ko Autana..?
Inti ta gyada kai Tana Fadin"Daddy ai kagama Siyan min komai fa Abu Daya ya Rage f..? Yana kallonta yace"Menene shi Autana..? Cikin Daga kai tace"Sabuwar waya Daddy...Taya zan je da Wannan Tsohuwar wayar Jami"a ai sai su raina maka ni.."Ta karishe Fada tana wani Hura Hanci Umma ta saki Baki Tana kallonta kafin Tayi mgana Daddy yace"Hakane kuma fa..To kada ki Damu zuwa gobe Bashir zai je ya Dubo miki wata iri kike so.? Da sauri tace"Samsung Daddy..Ina sonta sosai.."Daddy yace"Shikenan Angama Intin Daddynta..!
Dariya ta saki mai kayatarwa Tana Fadin"Nagode Daddyna..!
Umma dake zaune tace"Ka biye mata kuma..? Wayata fa ko wata Biyar Batayi ba Daka Siya mata bafa..Haba Alhaji bai kamata kana Biye ma yarinyar nan ba..Yakamata ka Rika Duba Rayuwa in yau mune gobe bamu bane Haka koda yaushe Daada na Fadamaka in mukaje Gaishesu taga Inti na wannan Tabaran ko bakomai watarana Gidan wani Zataje.."Yana jinta bai yi mgana ba Illah kallon Inti Dayayi wacce ta batarai yace"Autana jeki ki kwanta kinji ko..? Sai da Safe.."Batayi Gaddama ba ta Mike Tana Fadin"Gud Night Daddy..Umma sai da Safe Ya Bashi ka gaida Anty Hauwa.."Dukkansu suka amsa mata Umma tace"Zo ki Dauki Abida wajen ki zasu kwana..'Baki ta Tura tana Fadin"Wajena kuma Umma..? Tab ni wlh A"a Shegun kukane dasu..Hanani barci fa suke Cikin Dare.."Ta fada kamar Zatayi kuka Umma tace"Allah..? Naga yadda zaki kare in kika Haifi naki..!
Inti na Dariya tace"Daddy na zai Daukan min mai Reno.."da Filon Kujera Umma taRakata dashi Inti ta kwashi Gudu Zuwa Dakinta Tana Dariya Bashir ma Dariyan yake Shi da Daddy,sallama yayi musu ya Biya Kicthen ya Gaida Talatu daya Tarar tana wanke wanke Kafin yayi mgana ma Ta mikomai kulan Umma ta gayamata ya Fice Su Umma ya karama Sallama suka Rakashi da Allah ya kiyaye ya Fice Zuwa Haraban gidan ya Shiga Motar sa Kiran 4matic ya Zuba Hon megadi ya Bude mai get ya Fice Daga Gidan ya Dauki Titin anguwan Rimi inda gidansa yake.

Sai da sukaji Tashin Motarsa kana Daddy ya juyo yana kallon Umma yana Fadin"Meyasa koda yaushe kike maimaita mgana Dayane Salaha..? So nawa zan gayamiki ki Daina Ganin abubuwan da Inti ke yi a wani abu kar ki manta fa yarinya ce fa In ta girma Zaki ga Duk ta Daina wadanan abubuwan kuma kada Ki manta Sai da Bashir ya Shekara Goma sha Biyu aduniya muka Sameta alokacin da muka Fidda rai da samunta ita kadai ce Mace awajenmu menene Laifin in mun bata kulawa da gata..? Ai hakan bai Hanata zama mai Tarbiya da ilimi ba ina alfahari da ita da kananun Shekarunta ta Sauke qur'ani yanzu kan Haddatanta take,Kuma kina gani Da kuruciyata gashi Zata shiga Jami"a Alhamdulillah bata Taba Jawo mana mgana ba Salaha ni banga abun Damuwa ba.."
Ya karishe Fada yana kure ta da ido,Umma ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Uhm..Alhaji kenan wai kana Bani mamaki in kace Inti yarinyace..? Wacce ta Haura Shekara ashirin ce yarinya Alhaji..?
Cikin Halin ko inkula yace mata"To in ba yarinya bace Babba ce..? Shekara ashirib Duka Duka nawa take..? Don Allah ki Daina wannan mganar..In bamu kula da yayanmu ba..Ai samun mu ya zama na banza sai mu Daina Fita Neman Salaha..!
Sanin bazai Taba Fahimtarta ba yasa ta bar mganar ta Mike Dauke da Abida Tana Fadin"Bari na kai Abida Daki tayi Barci.."Daddy yace"Ga Abidin ma yayi barci ajikina.."Batayi mgana ba ta wuce Ciki Dakinta ta kai Abida ta kwantar kan gadonta kana ta Dawo ta Dauki Abeedin Shi ma takaishi ta kwantar ta Rufa musu bargo ta Rage musu Sanyin Ac ta kuma Rage Hasken Dakin kana ta Rufo musu kofa ta Fito Ta samu Daddy zaune in da Ta barshi ya maida Hankalinsa kan Talabijin yana kallon Labarai Kitchen ta wuce ta samu Talatu na Goge goge Sannu da aiki Tayi mata kai tsaye Fulas din Dake Kan Cabinet din kitchen din ta Nufa ta Dauki karamin mug ta Tsiyayo Ruwan lipton din Dayaji kayan Itatuwa da Ganyen Na"a Na"a ta Fice dashi Zuwa Falo Tana Zuwa Taja Center Table din Dake Tsakiyar falon ta ijiye Tana Fadin"Alhaji ga Ruwan Lipton din nan..!
Dago kansa yayi yana Fadin"Yauwa Nagode..'Daukowa tayi ta mikamai ya karba ya Fara Kurba sau Biyu yayi ya Dauko yana kallonta yace"Wata anguwa Su Yaya Aminan suka koma ne Bayan Tashin su Daga zoo road..?
Umma tace"Gadan kaya suka koma..Gidan Marigayi din da Sagir din yagada Ta koma Ciki suna zaune.."Daddy ya gyada kai yana Kurban Tea din yace"Sai nake ganin kamar Nauyi zamu kara mata Salaha..!
Umma ta kalleshi a kaikace tace"Wani irin Nauyi kuma..? Sai da ya kara Kurban Tea din yana Fadin"Kai mata Inti da zamu yi ta zauna wajenta Tayi karatu..Ga Wahalan Rayuwa ga Kuma Rigiman Diyar taki..! Umma Tayi Mirmishi Tana Fadin"Wlh ko Daya Alhaji..Bakaji da na kirata na gayamata Intisar ta samu addmission anan BUK ba..Kafin na Furta mata ina son Inti ta zauna wajenta sai dai ta rika zuwa Tana Dawo in anyi Hutu sai Tazo mana nan tayi mana Hutu ita ta Fara Cemin ammh wajena Zata zauna ki..? Kasanta da son Diya mace kuma Allah bai Bata ba Danta kenan kwara Daya Sagir..Bayan mutuwar Mahaifinsa kuma tace bata Sha'awar kara aure ba yadda su Baba Bala basu yi da ita ba tace baxata kara aure ba Shiyasa taki Dawowa ta Fara sana"arta achan tana kula da Danta har gashi yana Karatu shima kuma yana Sana"ar dole suka sakamata ido.!.
Daddy ya jinjina kai alamun gamsuwa yana Fadin"Hakan ma yayi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login