Showing 21001 words to 24000 words out of 236322 words

Chapter 8 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

702

yarda Taje ta kwana Bata jin ta taba takama Gidajen Baffaninta,sai dai in sun Hadu gidan Daada a Dukku Shima Din bata yarda ta kwana Kafarta kafar Daddynta Shiyasa Umma tayi matukar mamaki da Intee ta Zabi kano,Sai dai kuma batayi mamaki ba ganin yadda Ta Dora ma kanta yin Jami"ar Bayeron Tun ba yanzu ba Tasan Shi kadai ne Dalilin da zai saka Inteesar Tayi nesa da gida.
Ba wanda ya kara mgana sai Umma Dake nuna ma Daddy Hanyar gidan Yaya Amina Tunda sun Shigo gadan kaya.
Sai gasu a kofar gidansu Sagir wanda ke Cikin Shagonsa da yaransa suna ta faman Dinkin yau Tun safe bai zauna ba ya Shiga makaranta bai Dade ba ya Fito Mama ta hanashi Sukunu da Murnam zuwan Inna Salaha da yarta Tun asuba tatashi ta gyara Dakinta da gidan Gabadaya tasa yaje kasuwa yayi mata Cefenan Abunda Zata Dafa musu Duk ta kasa Sukuni Shima Daya Dawo makarantar ne Mama ke shaida mai Inna Salaha ta kirata tace suna Cikin makaranta sai sun gama Zasu Biyo nan zasu kwana sai Gobe zasu Juya zuwa kaduna.
Dinki gareshi kacha kacha Shiyasa abinci kadai yaci ya Dawo Shago ya Hau keke ya Fara Dinki Sallah kadai ke tadashi
Tundazu Dayaji karan Mota sai ya kalli bakin Shagon nashi ammh Sai yaga basu bane,Duk da Kofar gidan ba kwalta bane,ammh akwai Kasa mai kyau wanda Yawan Zirga zirgan Motoci da mashina ya Shimfideta kamar an saka kwalta.
Lokacin Dayaji Dirin Motarsu yana Dagowa da Inna Salaha ya Fara Cim karo wacce ke gaban Mota itama kamar an ce ta waiga sai ta ganshi Cikin Murna ta Fara Kiciniyar Bude Murfin Motan Tana Fadin"Mun iso..Gama Sagir din Yaya Aminan chan Cikin Shagonsa yana Dinki..!
Tafada Lokaci Daya tana balle Murfin Mota ta Fito Shima Daddy Fitowar yayi yana kallon Sagir daya taso Daga kan keken ya Fito Daga Cikin Shagon Cikin Fara"a Daddy bai wani Sanshi ba,Sanin da yayi mai bai yi Girma ba Haka ba.
Sagir karisowa yayi ya rankwafa yana gaida Umma ta amsa mai Tana Fadin"Sagir idon ka kenan..? Rabona da ganinka tun zuwan da kayi gaida Inno Muda ya Kawomim kai..!
Kansa na kasa yana Sosa keya yace"Inna ai Karatu ne ke Hanani Zuwa ko"ina ..Ammh Insha Allahu da mun kamallah sai kun gaji da ganinmu..!
Umma na Dariya tace"Hakane kuma..Ga Shago nata Habaka Allah yasa albarka..!
Tafada tana kallon Shagon Tama kara ganin Cigaba Domin zuwanta na karshe bai kai haka Cika da kekuna da yara ba.
Sagir Daddy ya juya yana gaisawar ya amsa mai Cikin Sakin Fuska yana Tambayansa karatu yace Alhamdulillah Afizge Sagir ke kallonsa Haka kurum yaga kamar Fuskarsa da yanayinsa yana mai kama da wani sai dai kuma ya rasa ta ina zai kama..?
Yana wannan Tunanin Yaga Daddy ya Bude Kofar Baya yana Fadin"Inteen Daddy Fito mana..Ai mun so gidan Innam taki..!
Yafada yana Bude mata kofar Motar,Sagir ya Dago Idanuwansa yana kallon wata kafa mai kyau da Tsari Cikin Cover na kamfanin Gucci ta Zurosu waje kafin ita kanta ta Bayyana Masha Allah ya Furta akasan Ransa ganinta kamar Inna Salaha sai dai ta Dauko Tsawon Babanta da yanayin karam Hancinsa sai dai Fatanta irin ta Inna Sahala ce mai Duhuwa.
Sanye take da Doguwar rigar Abaya Kirar Armani ta amsheta Tayi mata kyau sosai sai gyalen Abayan Datayi Rolling dinsa Daga Tsakiya tudun gashinta Data Tamkesa da Band,Hannunta kuma karamar Jakarta ne da wayarta sai takardunta wanda Tayi Cike cike a makaranta..
Lumsasun idanuwanta ta Lumshe Tana Bin yanayin wajen da kallo Lokaci Daya tana Shan iskar wajen kafin ta wani Dakuna Fuska Tana Fadin"Allah Daddy am Tired..!
Umma ta Harareta Tana Fadin"Kedai Raguwa ce..Baki ga yayanki bane ba gaisuwa..?
Tafada Tana nuna mata Sagir Daya gama kare mata kallo yana ganin ikon Allah katuwar Budurwa Tana Shagwaba kamar yarinya..Tabdijam wannan ne zata Zauna agidansu?akwai aiki..!
Kallo Daya tayi mai ta kauda kanta kafin ta Rausayar da kanta Tace"Umma kinsan fa in nagaji bana gane kowa..Ina yini..?
Ta fada Tana wani Yamutsa Fuska Kamar ta wurgar da kayan Hannunta Amsa mata Sagir yayi yana Fadin"Barka da zuwa kano kanwata..!
Jin abunda yace ne yasa ta Sakarmai Mirmishi har Fararan Hakoranta suka Bayyana tace"Thanks yaya sagir..!
Yaji Dadin haka Umma ce ta katse su da Fadin"Alhaji Bude Booth Sagir samu yara su shiga da kaya Ciki inteesar mu karisa Ciki nasan Yaya ta gaji da jiranmu..!
Daga haka ta wuce gaba Inteesar ta Daga kafarta Dakyar dataji sun mata Nauyi tsskani ga Allah ta gaji inda wani zai karban mata kayan hannunta Datafi kowa Murna.
Sagir ne yafito yaran Shagonsa da Hannu suka Fito suna Shiga da kayan da Daddy ya Bude Shake da Booth din Motarsa akwatunan da Kayan abinci Cike aciki haka suka dinga kwasa suna Bin bayansu Umma zuwa Cikin Gidansu Sagir.
Sagir kuwa da Daddy basu Shigo ba sai da aka gama Shiga da komai kana Sagir yamai Jagora zuwa Cikin gidan.
Suka iske su Umma a Falon Mama dan madaidaici mai Dauke da Saitin kujeru Sabbi wadanda Sagir ya saka akayi mata,Har da Cafet din ga Tibinta da Reseventa,Sai karamin Center Table a tsakiyar falon da karamin Fridge dinta Daman Daki Ciki da Falo ne sai Tiolet aciki Ko"ina Tsab Mama bata da Kazan???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ta ko kadan.
Tana ta ina ta saka da su Umma Inteesar kuma na kan kujera mai Zaman Mutum Daya ta lafe Tunda ta samu ta Zube kayan Hannunta tasha Ruwa taji ta fara Dawowa daidai.
Mama ce ta cika gaban Daddy da Lemuka da ruwa sai Kololin Abinci kansa na kasa suna gaisawa Tana Tambayan Bashir da matarsa da yaransa duk yace mata suna gaisheta ta gangaro Kan Lafiyar Daada yace mata alhamdulillah.
Mama ta juya tana kallon Inteesar da idanuwanta ke Lumshe Tana Fadin"Yata..Barci kike ji ne..? Tashi kici abinci ko wanka zaki fara ne..?naga alamar duk kin gaji..!
Umma na Dariya tace"Baki ga alama ba..Dayake kun iya Haihuwa Raguwa y'a ba..!
Mama na Dariya tace"Eh munji bakomai..Tashi ki Farayin wanka kafin kici Abinci.Kai kuma Sagir Tafi da Alhaji Dakin ka sai yaci Abincin a natse..!
Daddy yaji Dadin haka Duk da ba wani yunwa yake ji ba Ammh zai fi Sakewa achan Sagir yamai Jagora Zuwa Dakinsa Dake kallon na Mama Shima yana Shimfide da Cafet da katifa Daya yada akasa sai littafan karatunsa na makaranta Dana addini sai Akwatin kayansa da Hanger Dayake Sagale kayansa na sawa sai wasu Drowers Daya kan ijiye wasu kayan Daya Dinka in yagama wadanda ba"a amsa da Wuri ba
Komawa yayi ya Daukomai Abincin Ruwan yana kara mamakin Girman Inteesar ya Dade bai ganta ba Tun tana karamarta Kamar tun wani Zuwa da Inna Salahar tayi da ita,Bata kara zuwa ba sai yau Dayake yanzu wannan zamanin ba damuwa akai yi da Zumunci yara ba In manya sukayi Shikenan,Kuma ita bata cika Bin Umma anguwa ba basa Shiri bata Daukan Sangartata Tafi Tafiya da Daddyta Shi Dayake Biye mata.
Wankan ta Shiga Daman Shi take da So,Mama da kanta ta Juyo mata Ruwan Zafin Data saka afulas,ta kai mata Har Tiolet kuma ta kwashi wayarta da Jakarta da Takardunta ta kaimata Ciki kan gadonta Sabo 6by7 na karfe wanda Sagir din yayi mata tare da kujerun Dakin nata,Sai katifa Lamba goma Sha Biyar sabuwa Dake jingine gefe sai karamin wardrope dinta mai Kofa Biyu,sai Ledan daki Sabuwa malale ga kayan Inteesar nan jere agefen gadon da akwatuna da wasu ledoji kayan abincin kuma Suna Falon Mama,Tunda Umma tace nata ne Tana ta Godiya Kamar bakinta zai Cire Umma na Fadin bakomai.
Bayan Shigar inteesar wanka ne Umma da Mama suka zama Bayan sun gaisa Mama tace"Ya wajen su Inno..? Dazu da safe Muda ya kirani munyi waya da Mallam Babba nace musu kina Tafe sukace ai jiya Inteesar din tazo tayi musu sallama..!
Umma tace"Eh Taje..Tare naso muje ammh ban samu zuwa ba..Taje har gidansu Nasara,!
Mama tace"Allah sarki..Suma munyi mgana dasu Ranar Har Yaya Salisun Yake fadamin Nasaran zata Fara karatu itama anam kadunan..!
Umma tace"Eh kasu zatayi ita..!
Mama tace"Allah ya taimaka..! Umma ta amsa da Ameen Ameen suka Cigaba da Hiransu na Zumunci.
Inteesar kuma taji Dadin wankan Datayi da ruwa mai Zafi Bayan ta Fito ta Fiddo kayan Shafanta ta Shafa ta Bude akwatinta ta Dauko wata Riga da Sikat mai gajeren hannu ta saka Saboda sune na zaman gidanta,atamfa ko wani leshi bai cika Damunta ba sai Umma ta matsa mata ko kuma taje gaida Inno ta isheta da Mita haka Daada Shiyasa bata marmarin zuwa Dukku har yau har gobe Shiyasa ba kowa ya santa ba sai dai sunanta da aka sani ba.
Bata wani cin yunwa tunda sun ci abinci kan gadon ta kwanta Tana Sauke Numfashi Lokaci Daya Tana bin Dakin da kallo Tana Hura hanci tana Shakan kamshin Turaran Wutan da Mama ta Turara dakin dashi Masha Allah komai tsab Dashi Dakin ya Burge inteesar Duk da bai kama Kafar Dakinta na Gida ba sai dai ita Ba haka iyayenta suka bata Tarbiya ba,Bata da Dagawa ballatana Girman kai Kowa Daya ta Daukeshi Umma ta Koyamata iya zama Duk inda Rayuwa ta Fada mata ballatana ita kanta umman ba masu arziki bane Har yau har gobe Mallam Babba Hatsi yake saidawa akasuwa Itace sana'arsa Mahaifinta ne mai arzikin ammh bata da Halin kyama ko nuna tafi kowa barta da Sangarta da Tabara irin na yaran da iyayansu suka Shagwaba Shima bawai na Dolanci ba Domin tasan me take yi.
Tana Daga kwwncen Taji Umma na gayama Mama ta rika Zaneta in Taga zata mata Sangarta ta tsawatar mata kamar yadda Zatayi ma Sagir Mama tace bakomai Insha Allahu Baza"a samu matsala ba,Tana da kwancen Take Tura baki,Sanin Halin Umma taso ta Fito Wajen Daddy suyi Hiran bakwana Gajiya ta Hanata Tun tana Jin Hiransu Umma har barcin yammah ya kwasheta sai dai Taji Umma ta Daga mata Duka Tana Kiran Sunanta.
Bude Idanuwanta Tayi Cike da Barci Ta saukesu kan Umma Data Dauro alwala ga Ruwa nan na Diga,kan Fuskarta Hararanta Umma Tayi Tana Fadin"Kinga irin Halin naki ko..? Sai ki tashi kiyi Sallah..!
Tafada lokaci Daya Tana kokarin Sanya Hijabi ta tada Salla kan Darduman da Mama ta Shinfida mata.
Dakyar Inteesar ta iya mike Jikinta duk ya Mutu ga kasalan Data kamata ta Shiga Tiolet tayo alwala Tazo gefen Umma Ta Tada Sallah bayan ta Bude karamar akwatinta Data Jera Sabbin Hijabanta da mayafanta ta Dauki Daya cikin wanda Anty Hauwa ta bata ta saka ta tada Sallah.
Nan itama Mama ta Shigo Tayi alwalan Tayi sallah Bayan ta idaar ne ta juya tana kallon Inteesar tace"Maryam bazaki ci abincin bane..?
Inteesar taji abun wani bambarakwai Domin bamai kiranta da asalin sunanta sai Inteesar,Kai ta gyada kafin tace"Kila sai anjuma Inna Cikina ya cika..!
Umma ta karbe da Fadin"gatanan sai kin mata da gaske..Bata son Cin Abinci shiyasa kullum Zaki ganta jiya iyau Sillen kara kamar a Hureta ta Fadi..!
Umma ta karishe Fade Tana yar Dariya ganin yadda Inteesar din Ta Zumbura baki tana Dakuna Fuska ganin haka yasa Mama Jawota Jikinta ta Rumgume Tana Fadin"Kyale Sahala..In kika Tashi Zuwa Hutu na Tabbata bazasu ganeki ba..In ita bata son yar Dake ni ina so..Daman Daga Sagir sai ni agidanan naji matukar Dadin zuwan yata..!
Tafada Cikin nuna Murnanta Sai Ta bama Inteesar Tsausayi Sai ta kara Lafewa ajikinta Tana Fadin"Yauwa Mamata..Daman Umma bata sona..Nima na samu Mamata yanzu..!
Umma ta kyabe baki Tana Fadin"Kuje kuyi ta kaya..Indai wannan ne zaki dawo min ne..!
Mama tace"Insha Allahu bazamu Taba Dawowa ba sai adawowar alkhairi..!
Inteesar sai Mirmishi take Na jin Dadi Bazatace batasan Inna Amina ba,sai bata taba Zama da ita sosai haka ba wani lokacin in tazo tana makaranta sanda zata Dawo kuma Sai tatafi Gidan Inno ranar data kwana gidansu kuma Tana Dakin Umma ba wani Shakuwa Tsakaninsu sosai...
Hira suka Cigaba da yi sama Sama Inteesar an samu Abunda ake so sai ta kara lafewa Jikin Mama Kamar wata mage har tana lumshe ido,Abunda bata samu wajen Umma ita bata yarda da wannan Sakarcin ba.
Suna cikin Hiran ne sai ga Sagir ya Shigo bayan yayi sallama Suka amsa mai ya Shigo Ciki ya Duka yana gaishesu da yammah suka amsa mai sai yake fadamusu Daddy ne zai wuce masauki sai Gobe zai Dawo.
Mama ta Mike Ita da Inteeaar Dataji Zencen Tafiyan Daddy.
Umma ma ta mike,Mama ce tace"Bazai kwana anan ba Salaha..? Tunda ga Dakin Sagir zai Ishesu sai shi ya barmai katifar Shi kuma sai ya kwanta kasa..!
Umma tace"Haka kawai Yaya Amina shi da Dakinsa yayi kwanan kasa..? Barshi yaje masauki Koma kinyi mgana bazai Zauna ba..!
Mama bataji dadi ba tace Shikenan Dukkansu suka Fita Tsakar Gida Inda Daddy ke Tsaye da Gudu Inteesar ta isa gareshi ta Rungume Tana Fadin"Daddy na..!
Shima riketa yayi yana Fadin"Intee ta..Uwata ta kaina..!
Yafada Lokaci Daya yana Shafa kanta,Kara lafewa tayi ajikinsa kamar wata mage Sagir Dake gefe aransa yace"Yarinyar nan akwai Shagwaba..!
Mama ce tace"Alhaji bazaka kwana anan ba..? Naga ai duk gida ne..?
Daddy yace"A"a Yaya Amina bari naje masauku da safe zan dawo mu wuce in Allah ya yarda..!
Bata da tacewa illah ta Bishi da Allah ya kiyayewa ya Fice Yana Rike da Inteesar Umma da Sagir suka Bi bayansu Har zaure Inteesar ta Raka Daddy tana ta mai Shagwaban gobe bazata iya Shiga makaranta ita kadai ba Wahala
Umma tayi karamin Tsaki Tana Fadin"Kada Allah yasa Ki iya..gobe da wuri Insha Allahu muna kaduna in zaki warware wannan Son Jikin naki da Rangwantanki kiyi karatu..Daman Daada ta kira waya tace abaki kina bacci tace na Fadamiki ki Dage da karatu banda Sangarta da Sakarci..!
Kafin Umma ta gama mgana Inteesar ta kusa saka kuka Ta kalli Daddy tana Fadin"Daddy kaji Umma ko..? Daman Daada nan itama bata sona.Koda yaushe tayi ta min Fada..Taci ka Fadan Tsiya..!
Umma tayi mata Dakuwa Tana Fadin"Kinga naki nan..? Wato Tacika Fada ko..? Ai Mai Biye mikin ma ta isa dashi kuma Fada take yi mai a zauna Lafiya ballatana ke..!
Ai sai Inteesar tayi kokarin saka kuka Tana Dira Kafa Daddy ya Dafa kanta yana Fadin"Kada ki bata Hawayenki Inteen Daddy..Gobe da safe ki Shirya da Wuri in xamu Wuce sai mu Biya ta makaranta inkingama Komai kin Fara Shiga lacture sai mu wuce..Ga Dan"uwaki nan sai muje Dashi sai ki samo abokin Dawowa Tare..!
Sai alokacin Ta saki Ranta Daddy ya kalli Umma yana Fadin"Sahala bana jin Dadin yadda kike Hantaran yarinyar nan fa..? Duka nawa Intee take da zaki bi ki Rika mata Fada kamar wata Babba..?
Ba Umma bace take mamaki ba Domin ita saba gani Sagir ne yake kallon Inteesar yana auna mganar Daddy wai duka Duka nawa take..? Wannan gansamemiyar Budurwance yarinya..?lalle yau yana ganin Abu xai so Imran yana wajen nan ya Tabbata da ya kusa Mutuwa saboda Takaichi.
Umma bata tsaya bata bakinta ba ta Juya tana Fadin sai Allah ya kaimu ta shige Cikin gidan Ta bar Daddy na Fadama Sagir gobe tare zasu shiga makaranta Dashi Sagir yace ba mtsala Dayake Shima yana da Lacran safe.
Shidai yana gefe yana kallon Sangarta irin ta Inteesar Dakyar ta Saki Daddy ya Fita Sagir ya Rakashi Wajen Mota sukayi ssllama kana ya wuce Shagonsa yana kara mamakin Inteesar afili ya Furta.."Mama zata sha Fama..!

Inteesar da Wuri Tayi barcin Tana idar da Sallar Isha"i Ta ci Danbun namanta da Umma Tayi mata,Ta hada da Lemo har mamana mganar bazai taso mata da Daddare ba..?Umma tace"Wannan ki kyaleta inda kika barta Shan zaki da kayan Kwadayi nan tafi auki babu abunda yake mata..!
Mama tana Dariya tace muna da lafiya ne,Inta dai Intee Kayan Barcinta ta saka ta Bi Lafiyan gado sai barci,ta bar Umma da Inna Amina suna ta Hira Sama sama take jin suna waya da Inni da Mallam Babba,Sai kuma taji Ya Bashir ya kira ta wayarta Data Manta da ita saboda gajiya Umma ta Dauka sukayi mgana har tabama Inna Amina suka gaisa.
Kusan Raba Dare sukayi suna Hira kafin su kwanta Umma kusa da Inteesar ta kwanta,Ita kuma Mama ta yada katifa ta kwanta.
Da asuban Fari suka tashi..Mama ta Fita waje ta saka musu Ruwan wanka kana tazo tayi sallah Bayan ta idar suka gaiggaisa ta kara Fita Bayan Fitantane,Umma ta karayima Inteesar fada tana Nuna mata ta Rika Taimakon Mama da wasu ayyukan Inteesar tace Insha Allahu.
Mama tayi musu abun karyawa bayan ta juyo musu Ruwan wanka Umma ta Farayi kana Inteesar,suna gama Shirya suka iske kayan Karyawansu tea da Buredi da Soyayyah kwai sai Umma datace Kosai take so da koko suka zauna suka karya atare,Suna Hira cikin Sha'awa Inteesar bata wani ci Abun kirki ba Bata iya cika Cikinta in Zata Fita wani waje ta Dade,Umma ta matsa mata sai da ta saka wata Sabuwar amtafa da Ummanta Ta Dinkamata Doguwar riga Chiganvi mai kalan green ssi tayi amfani da green din mayafi da Takalmi da Jaka.
Sagir ma yayi wanka yana Dakinsa yana karyawa sanda Daddy ya karisowa shi ya Fita yayi mai Jagora zuwa Cikin gidan suka gaisa da Mama Da Umma lokacin sun gama suka Tashi suka Fara Shirin Tafiya.
Daddy ya duka har kasa yana Damka Amanar Inteesar wajen Mama tace ta karba Tayi alkawarin Zata kula da ita kamar yadda Zata kula da Sagir.
Yaji Dadin haka ya Dire mata kudi 30k tace bazata karba ba ya Fice bai Dauka ba.
Umma ta Dauka ta bata bayan ta Hada mata da 10k tace ta Rike ahannunta Mama nata Godiya Inteesar kuma sai Hawaye kamar sallaman kenan bata Dauka haka abun yake ba da bata Zabi Karatu a Kano ba.
Har waje Mama ta rakasu tana Godiya Tana Daga musu Hannu.Umma ta shiga Gaba Inteesar da Sagir abaya wacce ke ta Sharan kwallah Daddy na gaba yana Tuki hankalinsa na kanta kamar shima ya saki kukan.
Daganan basu Dire ko"ina ba sai Cikin Jami"ar Bayero,Sagir bai Rabu dasu ba sai da komai na Inteesar ya kamallah Zata Fara Daukan karatu Daddy har bakin Hall din inda yan Department din su ke karatu suka Rakota Wato Itama Zata karanta Fanni Tsumi da Tanadi wato Economics.
Inteesar Tayi kuka kamar Ranta zai Fita ta makalkale Daddy taki sakinsa Harta Umma sai da ta sakata kwallah,dalibai suna ta wucewa suna ganin abun mamaki kuka a jami"a..? Kamar wata yar sakandiri.
Dakyar ta saki Daddy,bayan ya Share mata Hawaye,Ya lallasheta kana ta juya ta shiga Hall din Tana Daga musu hannu.
Bayan ta Shige ne Sagir sukayi sallama yace shima zai Shiga karatu ne,Daddy ya kara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login