Showing 12001 words to 15000 words out of 236322 words

Chapter 5 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

705

shi nace ya Shigo kina nemansa..!
Mama tace"ai ka kyauta Sagir gashi yazomun gaisa..!
Sagir na Dariya kasa kasa ganin wani uwar Harara da Imran yake Sakarmai kafin ya Mike yana kokarin saka Budadden Takalminsa na Fatar Damisa yana Fadin"Amobe in kagama munafuncin naka Muje waje ina son mgana Dakai..!
Sagir ya mike kenan Mama Data shiga Karamin kitchen din da akayi shi da ginin Bulo an buga kwano ta sama harda kofar Katako Tana fadin"'A"a ina zaku kuma Ga Abinci na sauke Mutumin Imrana nayi Danwake..!
Tafada da Fara"arta Sagir ne yayi Saurin cewa"Mama ba Nisa zamu yi ba..yanzu zamu dawo..!
Kada kai Tayi tana Fadin"To shikenan ammh ku dawo da wuri kada ya huce kusan baya Dadi kaji Imrana..!
Dole ya Bude baki yace'To mama..!
Lokaci daya suna Ficewa Daga Gidan Imran na gaba Sagir na Binsa a Baya.
Kai tsaye kofar shagon Sagir Imran yaje ya zauna Shima sai Sagir yazauna gefensa yana Fadin"wai menene kake nema na ne..?kayi kayi mganarka yunwa nake ji yau tun safe ko Ruwa bai Shiga Cikina ba mallam..!
Kamar ba da Mutum yake mgana ba Shi Imran din ma Hankalinsa na kan Sandar dake hannunsa yana Ta Tada kasan Dake gabansa Sagir ya Kufula yace"kafa Shanyani ina da abunyi mallam..!.
Kai tsaye Imran yace"Ni kuma gani wanda bai da nayi ko..?
Yafada hankalinsa kwance batare dama ya kalleshi ba
Sai kuma sagir din yaji Kamar bai kyauta ba kada kai yayi yana Fadin"Ni ba haka nake nufi b..!
Bai gama Rufe baki ba Imran yace"What ever kai ya shafa..Zuwa nayi na gayamaka anjuma zaka rakani gidan Babanka Manu..!
Sagir ya kalleshi Cikin mamaki yana Fadin"Wai Baba manu kake nufi..?
Imran yace"Kana da wani Baban Bayan shi ne daka ke Tambayata..?
Sagir yace"Bansani ba..Kai ne in zakayi ma mutane mgana Gatse gatse..!
Mirmishi Imran ya saki kafin ya Gintse Fuskarsa yana Fadin"mutane sun fi gane irin haka ne shiyasa kake ganin ina amfani da hakan..!
Sagir yace"Bama wannan ba Me zakaje yi gidan Baba Manu..?
Har Sagir ya Cire rai da zai ce wani abu,sai kuma ya Mike Tsaye yana Tusa Dukka hannuwansa Cikin Aljihun bakin wandon Dake Jikinsa,Dayan hannu ya Zaro mai Dauke da kwalin aspen Taba sai kuma ya Zaro Lether bayan ya Zari Daya ya saka abaki ya Kyasta Lether din ya kunnata yayi mata kyakyawan zuka yana wani Lumshe ido Lokaci Daya yana Fesar da Hayakinta zuwa ga Fuskar Sagir wanda yayi Saurin Tashi yaja da Baya yana Fadin"Kaga wulakancin ka ko Imu..? Kafa san bana son warin Taba!
Imran ya kallesa da Lumsassun idanuwansa kafin yace"Kuma gashi kana abota damai shanta sai yaya kenan..?
Hararansa Sagir yayi yana Fadin"Mallam ka Fadamim me zakaje yi gidan Baba Manu..?Nidai nasan bama Haduwa kuke yi ba in yazo ballatana nace wani abu ya shiga Tsakaninku..!
Imran yayi karamin Tsaki Lokaci Daya yana Zukar Tabarsa sai da ya Zuketa son ransa kana yasaketa a kasa ya saka kafa ya Taketa ya Murjeta yana Fadin"Kai banza...Zuwa zan yi nace ya shigema Ya yusuf gaba kan mganar auransa..!
Sagir ya saki Hanci da baki kafin yace"Aure kuma? Zai yi aure ne..?
Tafiya Imran ya farayi yana Fadin"Eh..Safiya wacce mukaje gidansu jiya ita zai aura Tsohonta yace ya Turo mgabantansa to Abba ne kuma kasan dai Halin Dayake ciki,shine na yanke Shawaran neman Baba manu sai ya Nemi ko abokansa ne suje ayi mganar auran..!
Ya fada daidai Lokacin Dayake Tsayawa kofar Gidansu Sagir din Domin Tunda Mama tace Danwake take yi yaji bazai iya Tafiya ba sai yaci Duk Duniya bai ga Wanda yakai Mama iya Danwake ba ko Munari yasa tayi mai in tayi Bai iya ci sai yaji bai ka na Mama Dadi ba.
Sagir ya tako ya Biyosa yana Fadin"Anya Baba manu zai yarda kuwa Imu..?
Imran bai kallesa ba yace"Saboda mene bazai yarda ba..Aure fa akace ba wani Shashanci ba..!
Sagir yace"Ba wannan ba Kasan dai ba mganar aure ba abun wasa bane..Ya kamata ace wannan karon kun Shigo da Danginku cikin mganar Imran..!
Yafada yana Fatan Imran dinyace wani abu yau ko zai samu wata makama kan Abunda ya Shafi Imran din da bai sani ba har yau.
Ammh sai me Ko kara mgana Imran bai yi mai ya Nufi Cikin Gidansu Sagir din yana Fadin"Mallam ni ban ce kamin Tsarinka ba..in baxaka Rakani ba nasan gidan..!
Daga haka ya shige ya barsa Sagir ya Dade yana auna wasu abubuwa,Tunda yake da Imran bayan Abba da Maimuna da Ya yusuf bai taba ganin wani nasu ba ko wasu sun zo gidansu ba su kadai suke Rayuwarsu kuma Dukkansu basu yarda suyi mganar Wani nasu da kowa koshi Duk yadda yake ga Tambayan Imran bai Taba gayamai komai ba sai dai ya Taba Cemai Abba Bafullatanin Gombe ne, wanda Daman ba wanda zai kalle su yasan cewa su din ba masu Hali bane,Tabbas basu yi kama da wadanda Halin Rayuwa ta gasa ba kodaga Gidan da suka Siya suke Ciki Dankakeren gida ne,ammh bai karaya ba zaicigaba da Bin sa har ya gano Abunda yake son ganowa.
Shima jikinsa a sanyaye yabi bayansa koda ya shiga ya iske Imran zaune kan Tabarmulan da suka tashi Dazu,yana cin Danwaken da Mama ta Zubamai itama Tana gefe kan kujeran Tsugguno
Karisawa yayi shima ya Cire Takalminsa ya zauna kan Tabarman kusa da Imran ya saka Hannunsa cikin Filet din Dake gaban Imran din ya Dauki Cokali ya Debo Danwaken ya kai Bakinsa sai da ya Tauna ya Hadiye kana yace"Wato shine kazo kana ci ko ka jirani ko..?
Ko kallonsa Imran bai yi ba yana Cin Danwakensa Mama ce tace"Inafa zaijiraka Tunda kai ka Shiga wata Sabgan.!
Bakin Sagir cike da Danwake Yace"Wlh mama muna fa Tare ne muna mgana ya taho kawai ya barni..!
Mama tace"Ai kunfi kusa ba Ruwana da shiga tsakaninku Sagir..!
Tafada Tana Dariya Shidai Imran bai ce komai ba sai daya koshi ya sha Ruwa bayan ya Tashi yaje bakin makurara ya wanke bakinsa Daidai Lokacin da Sagir ke cewa"Mama Inna Salaha ta kiraki yau..?
Mama tace"Eh munyi mgana da ita Dazu take gayamin gobe in Allah ya Kaimu Megidan nata zai kawo Inteesar din da kanta har nan gidan..!
Sagir yace"nima Bashir ya kirani Dazu ina makaranta..Shi yake gayamin Baban nasu da kansa zai raka Inteesar cikin makaranta tayi Registration da wasu abubuwan domin akwai Abokansa sosai Laccharori abunda bata karisa ba yana Rokona dom Allah na Taimaka mata ta karisa..!
Mama tace"Eh nima bayanin data min kenan ina Ruwan Inteesar.."
Sagir yace"Mama gaskiya Suna ji da yarinyar nan kalli fa bama Bashir din ba Baban nasu xai bar komai nashi ya kawota..!
Mama tace"Yar gatace sosai..Ita ce fa Autan Salaha har ta Fidda rai da samun Ciki ta samu Cikin Inteesar Tana ganin gata Mussmman wajen Uban.."
Sagir na shan Ruwa baysn ya gama yace'"Ni kuwa ban santa ba..!
Mama tace"Eh bazaka santa ba Kamar sau Daya Salaha ta taba zuwa Da ita tun tana karama Tun mahaifinka ma nada rai..Duk Zuwan Datakeyi Ita kadai take zuwa gaskiya kai kuma baka}? Zuwa gidan Salaha in kaje}? kaduna gaida su Inno}? Balle kasanta kafi sanin Bashir dim Tunda shi yafi kawota in zata zo..!
Sagir ya Jinjina kai yana Mikewa Lokaci Daya yace"ina zuwa Mama in naje nida Muda ammh fa da Dadewa..!
Mama tace"Ai abunda nake nuna maka kenan yaran zamanin nan bakwa son zumunci Shi kanshi Mudan yaushe Rabonsa da nam..Ammh nayi mai uzuri yana Taimaka ma Mallam Babba a kasuwa"

Sagir yace'Mama nayi Tunanin a gyara Dakin nan sai ta zauna aciki.' yafada yana nuna wani Dakin da ke kusa da dakim mama inda take saka Tarkacenta.
Mama tace"A"a duka duka nawa Inteesar take da zan raba wajen zama da ita..Tare zamu zauna da ita adakina ga gadona ta rika kwanciyarta ni kuma sai na kwanta a katifa ba Shikenan ba.."
Sagir ya Bude baki zai yi mgana kenan yaji Imran na Fadin"Mama sai an juma ni zan wuce..,!
Ashe Tun dazu yana Tsaye ba zai ce yana jinsu ba Sanin Halinsa ba komai yake bama muhimmanci ba abunda ma ya Shafesa bai cika Bashi Damuwa haka ba
Mama ta rakaahi da Saka albarka da Sakon gaisuwa wajen Abba Sagir ya saka Takalmi yabi bayansa yana Fadin"bari na rakasa Mama..!

Yana Fita yaga Imran har ya mika Hanya Dayake da kafarsa yau ya Fito bai Dauko mashin ba Da Gudu ya Cimmai yana Fadin"Kaifa baka da kirki..Sai ka Tafi ba Sallama..,!
Imran na takunsa na Sassarfa Duka Hannuwansa na Cikin Aljihu bai ce ma Sagir kala ba suna dai ta Tafiyansu Sagir ne yace"Yanzu da Daddare zamu je gidan Baba Manun kenan..?
Bai tankamai ba sai da suka iso Get din gidansu kana Imran yaja ya Tsaya yana Fadin"Karfe 8:00pm bayan an Fito Sallar Isha"i ka Fito kofar gida bana son ka batamin lokaci..!
Daga haka kawai ya Kwankwasa Get din gidan nasu Iro megadi Da Daman yasan ko waye yazo ya Budemai karamar Kofar ya Shige shi kuma ya leko yana gaida Sagir din Daya amsamai Lokaci Daya ya juya ya Fara Tafiya yana Fadi a Fili"Imran akwai iko..kamar jinin Sarauta wannan inda Dan wani Sarki ne da anga Iko..!
Bai koma gida ba Shima Shago ya Shiga yana Duba aikin Daya bar musu yau akwai masu karban Dinki da yawa da yayi ma alkawari,Ransa ya baci ganin basu ci karfin aikim ba Dayake Sagir ya sanu manya mata ke kawomai Dinki kuma akaci Sa"a ya iya Harda Dinkin Maza Shiyasa nan da nan Shagonsa ya Daukaka Har ya mallaki yaransa na kansa ganin haka yasa bai jira su ba Ballatana yaji Hakurin da suke bashi ya Haye keke ya Fara Rage wasu ayyukan Haka yake bai da Girman kai sam yana da Zuciya da Neman na kansa ko Domin Mahifiyarsa a koda yaushe yana so yayi ma Imran mgana kan yazo ya koyi Dinki zai Ragemai wani abun Tunda babu Abunda yake yi komai Yusuf ne ke Gudanar dashi.








*Shakira...*
3/22/22, 23:03 - Ummi Tandama???i: *GIDANMU..!*
_(Our House)_

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:JanaftyB??0
{*

*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*


*??T??5*

*Da daddare*

"Cikin Shirinsa na Fita ya Fito Daga Dakinsa Cikin Shigar riga da wando Black and white,na kamfanin Armani sai kafarsa sanye Cikin Bakin Rufaffen Takalmi na Fatar Damisa Sai hannunsa Dake daure da Bakin agogo na Fatar damisa mai kyau da yarari,Kwantacciyar suman kansa tasha gyara ta kwanta ta karama Fuskarsa kyau da Annuri Sai Bakinsa Wanda Bakin hayaki ya Fara mai dashi Duhu hakan sai ya karamai kyau da wani Haiba..
Fuskar nan nashi a Hade babu Fara"a ko kadan Key din Mashin Dinsa ne a Hannunsa yana Dakawa Sanda ya Fito Falon kamshin Turaransa na Man Daya saba amfani Dashi ya Fara ma Yusuf da Maimuna Sanar isowarsa Cikin Falon.
Ya yusuf na Zaune kan Daya Daga Cikin kujerun Falon Yana makale da waya a kunnensa yana mgana kasa kasa Cikin kwantar dakai Daga gani Da Safiya yake waya ko da wata Macen da Zuciyarsa ta gama yarda da ita.
Maimuna kuma Tana Wajen Dinning area Tana jera Warmers da Filets din Data kwaso Daga Kitchen
Tunda ya Fito ta Kuramai ido Ganinsa kamar kullum Ba Fara"a da Anuri yasa da Sauri Ta Daga murya Tana Fadin"Barka da Fitowa ya Imu..!
Bai amsa mata ba Sai ma wani kallo Daya Bita dashi kafin ya Dauke kansa Ya Juya ya nufi Dakin Abba Bata damu ba sanin Halinsa baki ta tabe kawai ta juya zuwa Kichen ta Dauko Ruwa da Kofuna,Yusuf kuma Dake waya bai katse ba ya bishi da kallo Har ya Bude Dakin Abba ya Shiga da yar Karamar sallamarsa Ciki ciki kamar wanda akace yayi ta Dole.
Har Gaban gadon da Abba ke kwance ya karisa cak ya Tsaya yana Kallon Abba Dake kwance Sambal akan gadon da ya zame masa Kamar wani Maginjini ko nace abun Dogaro ya kwana akai ya tashi akai ya kuma karishe wuninsa akai sanye yake da Farar Jallabiya a jikinsa Gashin Bakinsa da gemunsa ya cika alamun yana Bukatar a Rageshi Dogon Hancinsa ya kara Fitowa da Kyakyawan Fuskarsa ta Fulanin asali.
Kuramasa ido Imran yayi yana jin Taruwar wasu Hawaye a kwarmin Idanuwansa Durkusawa yayi agaban gadon yana kallon Idanuwan Abba suna Lumshe alamun ya samu natsuwa Cikin Barcinsa.
Hannunsa ya Riko Cikin Nashi yana Faman kokuwa da Numfashinsa Wasu al"amura da suka Shude suna kokarin Dawowamai Daki Daki yana Tuna Abba da Sadaukarwarn sa kan Iyalinsa da yan"uwansa ammh yau Dalilin Wata kaddara Kalli Halin Daya koma.
Rauninsa ne ya Fara Bayyana Kamar zai yi kuka ammh kuma bai yin ba yayi maza ya Matse Hawayensa suka koma Lokaci Daya ya Mike Bayan ya saki Hannun Abba Yana Fadin"Allah ya Baka Lafiya Abba..!
Daga Haka ya juya ya Fice Daga Dakin da Sauri Cikin Sassafarsa Daya saba akoda yaushe.
Wannan karon Munari bata Falon Sai Yusuf kadai Dake kan Dinning yana cin Abinci Fitowar Imran Da kokarin Fita Dayake yasa ya Daga murya ya kirasa
"Imu...!
Tsayawa yayi Lokaci Daya ya waigo yana kallonsa abincin gabansa ya Nuna mai da ido kafin yace"Ina zaka kuma ga abinci Munari ta gama..?
Yamutsa Fuska yayi kadan kafin yace"Am ok..!
Ya juya zai Sake yunkurin Fita yaji Yusuf din na Fadin"Wai ina Zakane da Daran nan kake ta wannan Uban Saurin..? Kodai kodai..?
Yafada Cikin Sigan Zolaya Jin haka yasa Imran ya juyo yana kara Hade Ransa yace"Kodai What..?
Yusuf na kai loman Shinkafa da Miyar da Munari tayi yake Fadin"Ko dai Zence zaka ne..?
Imran ya wani Kallesa Sheke sheke kafin yace"Menene kuma wani Zence..?
Yusuf yace"Nufina Tadi zaka je wajen Budurwan ka Dakayi..Domin wannan gayun ina hasashen nata ne..!
In ba domin ya yusuf bane Ashar yaso ya Dankara mai sai kuma ya Fasa ya karkace kai bayan ya Tusa Duka Hannuwansa Cikin Aljihun wandonsa yace"Abba nata barci ya ko tashi yayi Sallah..? Ya kauda Hiran Saboda bayaso Tayi tsawo Lokaci Daya kuma yana Fito da hannunsa agogon Dake Tsitsiyan Hannunsa yake Dubawa.
Yusuf ya kada kai kawai yace"bai yi ba..Kasan Dr.Ya sauyamai mgani wannan karon so akwai masu saka Barci sosai..Zuwa 9 insha Allahu zai Tashi da kansa.Ammh fa bazan fasa Fadin Zence zaka ba..!
Ya karishe Fada yana kunshe Dariyansa Lokaci Daya yana Tsiyaya Ruwa a glass Cup yasha ya koshi kana ya mike ya Zari Tissue yana goge bakinsa kafin ya Fara takowa Tsakiyar Falon.
Yana kallon Fuskar Imran din wanda yayi shuru kawai yana Kallon Yusuf din kamar ya Makeshi haka yaje ji..? Shi Imran ne zai je Tadi ko menene ma yace..? Allah ya Tsareshi..
Karamin Tsaki yaja kafin yace"Ni Imran ne zan je Zence kace ma kofar gidan wata yarinya..?Ni..Over my Death Body Wlh..!
Yafada yana wani mele baki Yusuf ya karosa gabansa Lokaci Daya yana Fadin"Common Kada ka Cika baki..Sai dai in bazakayi aure ba in ko Zakayi Dole sai ka Sauke wannan Ra"ayin naka kaji..!
Imran yace"Saboda me..? Nifa Shiyasa bana son Hada Shirgina da mata..Kasanni bana son Raini ko kadan su kuma da sunga kana Sakarmusu Fuska sai Raini ya Shigo Ciki..Ni aure bai Taba Zama Dole gareni ba sai don yana Sunnar ma"aiki in ma ya Zama Dolen zan yi auran sai na Ga wacce ita take sona zata iya Zama Dani tayi Hakuri dani kuma In har taji Tagani Shikenan Fine ammh ni kam bazan iya Lalacewa gaban Mace ina Rage Murya ba Allah ya tsari Imrana..!
Tunda ya Fara mgana Yusuf ke Dariya har yana zama kan kujera Ganin haka yasa Imran ya juya kawai ya Fara Tafiya batare Dayace wani abu ba
Gabda zai Fice Daga Falon Yusuf yace"Shikenan Imran Abubukar Malami We shall see..!
Cikin son Tabbatarwa ya juyo ya saki wani Mirmishi kafin yace"We shall see..!
Daga haka ya Fice Daga Falon yana sakin karamin Tsaki ganin Bata Lokacin Dayayi alhalin shi ba Mutum ne mai african Time ba.
Mashin dinsa yaHau ya kunnata Lokaci Daya yayi Hon Iro megadi Dake kan Bencinsa zaune yana Dafa Shayinsa ya Tashi da Gudu ya Bude get din Imran ya Fice da Gudu Baki Iro ya Rike kafin yace"Nidai Allah ya kawoni gadi Wani Gida..Gidan da ban taba ganin kamar sa ba.!
Yafada Lokaci Daya yana maida get din ya Rufe ya koma ya Cigaba da Fifita Rushin Dake Cikin karamin murhin gawayin Dake gabansa mai Dauke da Karamar Butar shayi yana Dafawa.
Yana isowa kofar gidansu Sagir din yaji wayarsa na kuka,Kafin ya Cirota Daga Aljihu Sagir ya Bayyana gabansa Cikin Harara yace"Karfe Takwas din kenan..? Kasani na Fito ina jiranka kamar wani yaron aiken ka..!
Karamin mirmishi Imran yayi yana Fadin"To da wanene..? Mallam Hau muje bana so mu yi Dare sosai..!
Sagir na Hawa mashin din Lokaci Daya yana Fadin"Dare na nawa kuma..Ai mun gama yinsa..!
Imran dai bai kara mgana ba suka Dauki Hanya Sagir ne ke ta maganarsa yana Fadama Imran din ya kira Baba Manun yace maizasu zo,Imran Yana Tuka mashin din yace"Waya aike ka..?.
Sagir yace"Bangane ba..? In mukaje bai dawo daga gareji bafa..!
Kai tsaye Imran yace"Mu bisa chan..!
Sagir yace"Mganar bata kamata ayita achan ba.Agidan dai ya Dace..!
Imran yace"Naji sarkin Tsari..Kamin shuru kasan na tsani ina Tafiya mutum na min Surutu a bayana..!
Sagir ya Gimtse bakinsa bai kara mgana sai da suka isa anguwan su Baba manu dake mandawari Road,Daman Imran yasan gidan Domin In Sagir zashi Wani Lokacin Tare suke zuwa da Imran din sai dai bai taba Shiga Gidan ba sai dai ya Tsaya Daga waje Sagir din ya Shiga ya Fito Shima Baba Manun ya san Imran din Abokin Sagir ne sau Daya suka Taba Haduwa Har ya gaishesa shima Sagir ne ya Dinga Taka kafar Imran din yana mai in kiya Daya gaida Baba Manun.
Akofar gidan suka Faka mashin din kafin Sagir ya kalli Imran Daya Coge gefen mashin dinsa yace"Shiga fa zamu yi..?
Imran yace"Saboda mene.? Ya fito waje mganar bamai tsayi bace!
Sagir yayi tsaki ya wuce yana Fadin"In kaga dama kazo mu shiga in kuma baka ga Dama ba ka koma!
Daga haka ya saka kanshi Gidan ya bar Imran din nan Tsaye yana kallonsa Kamar bazai Bishi ba kuma komai ya Tuna sai ya Daga kafa ya Rufama Sagir din Baya.
Da Siririyar Sallamarsa ya Shiga Sagir da Inna kaltume matar Baba Manu suka amsa,Wanda ke Zaune kan Tabarma kusa da Sagir din mgana yake a waya.
Kamar Imran ya juya sai kuma ya Tuna Abunda ya kawosa yasa yayi karfin gwiwan karisawa ganin yadda Daga Baba Manun har Inna Kaltumen suka Sakarmai ido suna kallonsa Dayake akwai Wutan Lantarki Haske ya gauraye Tsakar gidan.
Daga nesa ya Durkusa Kamar a Dofane yana Gaishesu sau Daya ina Wuni?
Inna kaltume ne ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login