Showing 30001 words to 33000 words out of 236322 words

Chapter 11 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

737

Domin na Sallameki gabadaya kije Gidan da kika Zaba Fiye damu Farimcikin iyayenki na Daura Miki aure yanzu nan kuma Waliyan shi wanda kika Zaba suna waje suna Jiranki kada ki Fara Bata musu Lokaci..!
Hawayenta ne suka zubo Sharr Cikin Rawan murya tace"Abbu aure..!
Bata samu Damar karisawa ba ya Dakatar da ita yana Fadin"Aure nace don Ubanki bashi kike so ba..?har kina saba Umarni na..?Maza ki shiga ki Hado kayanki kizo ki ki wuce kafin na Ci Mutumcinki yanzu anan wajen..!
Yafada Cikin Tsawa da Umarni Safiya ta Fashe da kuka Abunda Mahaifinta yayi mata kamar bai Taba ganinta ba taShiga Dakinta ya Bita yana ta Sababin Fada Tana Tusa kayanta Cikin karamar Trolley dinta yana Tsaye kanta yana Bala"insa ta Dauki mayafinta da wayarta ta Sakamayafi ya taso ta suka Fito suka iske Hajiya Mero na tsaye tana Kuka.
Suna Fitowa ta Mike ko kallonta Alhaji Alhassan bai yi ba ya Nufi inda ta Zubar da kudin Sadakin yazo ya Tattara ya Sakama Safiya a Hannunta yana Fadin"Kije ni ba zan ce kije kiyi hakuri ba..Sai dai nace miki kada ki kuskura wani abu yasa kice zaki Dawomin gida Bazan karbeki ba Na riga na baki Zabi kuma kika Zabi Gidan da zaki yanzu sai nace Allah ya bada Zaman lafiya ga Sadakin ki nan Hakkin ki ne..Sauran abubuwan kuma Daga baya in muka Tattauna da mamarki Zaki jimu..Zan sauke hakkina na Uba gareki a karo na Biyu..Na cika na aure Tunda na aurar dake..!
Daga haka yasaki Hannunta ta jimke kudin Tana jin wani irin Tsausayin kanta me ta aikata haka..? Daga tace Yusuf take so..?menene aibunsa Da har za"ayi mata wannan auran kamar wacce bata da gata..!
Kukan ta ya Fito Sarari Hajiya Mero Ta mike Cikin kuka ta kasa Mgana,Alhaji Alhassan yace"Mero kiyi sallama da yarki..Suna waje suna jiranta..!
Hajiya Mero taji wani Bakinciki Cikin azama tataho ta Rike Safiya Tana Fadin"Wlh baka isa ba..Ba inda yata zataje..!
Tafada Cikim kuka jin haka yasa Safiya ta Fada Jikinta Tana Fadin"Mommy..!
Lokaci Daya ta saka kuka mai Cin Rai,Karamin tsaki yaja yana Fadin"Don Allah ki saketa Mero..Miye na wani kuka sai kace anyi mutuwa..? Miye na ganin Laifina abunda yarki ta Zaba kenan kuma na bata..!
Tana rike da Safiya tace"Baka isa ba..Bazan yarda ka Gurbata Rayuwar yata ba...Nima ina da iyaye da yan"uwa Zan kira su na gayamusu ina da hakki akan ya"yana Kamar yadda kake dashi..baka isa na Zura maka ido ka Lalata Rayuwar yata ba Alhassan..!
Tafada Cikim kuka Wani Shekeke ya kalleta lafin ya saka Hannu ya Bambare Safiya ajikinta yana Fadin"Ai nafi son haka ma..Kije ki kira duk wanda zaki kira..Sai dai ina mai Tabbatar miki ba wanda ya isa ya Tada wannan auran koda kuwa Goggo ce..!
Ai fadin haka da yayi yasa ta san yakai makura Tunda ya iyacewa Harta uwarsa bata isa ba to waye ya isa..?
Babu shi Tana ji Tana gani ya tasa Safiya agaba Tana kuka Tana kiran sunanta ya Fice daita yana Fadin"Ga Shaidar Daurin aure nanki Raba Biyu..Kashi Daya na mutanen Fagge Daya kuma na Yan"uwanki..Kada wani yace bai sani ba Shaida ne..!
Daga haka ya Tasa Safiya suka Fice Daga Falon Yana tafe yana mata Fadan ba ita ta Zaba ba to kukan Uban miye take yi..?ita kuwa Tafe take kawai Tana Jimke da kudin Sadakinta a hannunta da wayarta Dayam kuma tana Faman Jan Trolley dinta.
Aharaban gidan suka iske Alh.sadi da Baba Manu su kansu sai da sukaji kamar suyi ma Safiya kuka ganin irin yadda take Shatatan Hawaye wanman wani irin Tozarci ne? Ace budurwa ba bazawara ba A daura mata aure ba wasu Mutane kuma za"a kaita ba wannan wanda zai rakata sai Waliyan Ango..?babu tsinke ballatama wani abun arziiki Gaskiya Alhaji Alhassan bai ji Dadin Rayuwarsa ba kuma Hakki da Kiwon ya"yansa sai ya kamashi.
Suna isowa gabansu ya Tura Safiya gabansu yana Fadin"Ki Duka kigaishesu..Sune wanda kika Zaban yayo Haya suka zo Neman auranki..!
Yafada kai tsaye yana kallonta kamar wacce aka Damkwafar a kasa haka ta Duka ita da kayan hannunta Tana Fadin"ina...ina..kwananku..!
Cikin muryan kuka Da Rauni Tuni Tsausayinta ya kama Baba Manu da Alh.sadi yaji kamar yayi kwallah Bai san sadda ya isa gareta ba yasa Hannu ya Dagota Tsaye Lokaci Daya yana Rike da Duka Kafadunta yace"Yata ki Daina ki Share Hawayenki..Wlh ba Domin ganin idon ki ba..Ni ba wanda yyi Hayata kan nazo Neman auranki..Ra"ayin Kaina ya sani Zuwa da kuma Dalilin kanin Mijin da kika aura..Duk da ban Taba ganin wanda kika auran ba ammh ni naji ji ajikina kin Shiga Zuru"a mai kyau da Nasaba..Sannan kuma ina da Tabbacin suma kamar kowa ne sai dai wani al'amari wanda mu bamu sani ba..Sai dai ina da Tabbacin Zaki zama Sanadiyar Gyara Zamantakewar wannan Gidan ki Cika sa da farinciki Shigowarki ya zameusu Alheri Har karshen Rayuwarsu.!.
Yau ta Taba ganinsa ammh mgangunsa sun yi matukar Tasiri acikin Zuciyarta wanda suka sakamata wani Dakewa da Juriya Bata ji ta karaya ba Tana kaunar Yusuf da Zuciya Daya kuma Tayi alkawarin sai tayi Sanadiyar dawomai da Farincikin Data lura yarasa Shi da Sauran yan"uwansa.
Da wannan kwarin gwiwan ta Dago Tana kallon Baba Manu kafin tace"Insha Allahu..!
Tafada Lokaci Daya Tana Share Hawayenta sai yaji Dadi ya Dafa kanta yana Fadin"Allah yayi miki albarka ya albarci Sabon Gidan daZaki..!
Ita acikin Ranta ta amsa Alh.sadi ya amsa afili Alhaji Alhassan kuwa baki yaTabe kafin yace"Gata nan..Nagama nawa Saura naku..Safiya ki kula kada ki kuskura kice zaki Dawon gida da wani mgana kinji nagayamiki..!
Kai ta girgiza Idanuwanta na Cika da kwallah Tace"Insha Allahu sai alheri zai kawo ni Abbu..!
Daga haka ta Rike Trolley dinta Dakyau ta Fara Tafiya tana kuka Baba Manu ya mikama Alhaji Alhassan Hannu sukayi musabaha hakama Alh sadi kafin suyi mai sallama subi bayan Safiya Harta Megadi sai yaji kamar yayi kwallah Ballatana Hajiya Mero Dake kofar Falon da Haraban gidan Tana kallon Duk Abunda ke Faruwa,Hawaye na Zubo mata kamar famfo,Suna Ficewa Daga gidan Alhaji Alhassan ya Sauke ajiyar Zuciya acikin Ransa yace"Sai yanzu Hankalina ya kwanta..!
Daga haka ya juya zuwa Cikin Falon Nan yaci karo da Hajiya Mero Tana kuka ya wuceta yana Fadin"Kina da aiki Mero..Waya isa ya Tada Hukuncin Allah.!
Tana jinsa ta kasa mgana sai kuka acikin Ranta kuma Fadi take"Hukuncin Allah ko Hukuncin ka..?
Daga haka ta juya zuwa Cikin Falon da gudu tana kuka ko Kwalayen Mintin Dake tsakar Falon bata bi takai ba ta Shige Dakinta ta Fada Kan gado Tana wani Gunjin kuka gabadaya ta rasa mafita ballatana ta kamo Zaren yadda Zatayi.

****
Su Baba Manu suna Tafe a Mota Safiya na gidan Baya ta saka kanta tsakanin Cinyoyinta,tana ta kuka Baba Manu na gaba Alh.Sadi na Tuki ammh an rasa mai cewa komai gabadaya lamarin ya Daure musu kai uwa uba ga Tsausayin wannan Baiwar Allah Safiya,Shiyasa suka rasa bakin Zaren kamawa.
Alh.Sadi ne ya juyo yana kallon Baba Manu kafin yace"Ina muka nufa yanzu Manu..?
Baba Manu ya sauke Numfashi yana Fadin"Mu tafi Gadon kaya..!
Alh.Sadi yace'Inda Matar marigayi Take zaune kenan..?.Baba manu ya Daga mai kai,nan da nan Alh.Sadi ya Take Mota Cikin Lokaci sai gasu a Kofar gidan su Sagir.
Firfitowa sukayi Baba Manu ya umarci Safiya Data fito ta FitoJikinta a sanyaye gabadaya Idanuwanta sun koma Jawur sun Kumbura saboda kuka,Ganin tana layi kamar zata Fadi ne yasa Baba Manu ya karban mata Trolley din,lokaci Daya yana leka Shagon Sagir sai yaga Baya Ciki sai yaransa,Nufar gidan su Sagir din yayi Bayan yace ma Safiya ta Biyoshi Shi kuma Alh.Sadi ya jirasa a waje yanzu zai fito.
Safiya dakyar take Daga kafarta hannunta Damke da Sadakinta da wayarta kamar ace kyat ta Zura da gudu sai bin ko"ina da kallo Takeyi Tana Tunanin bata taba Shigowa area din ba.
Mama Tana zaune a kofar Falonta Tana gyaran wake Bata so Sagir da Inteesar su Dawo daga makaranta bata gama abinci ba
Sama sama taji sallaman Baba manu ta Dago tana amsawa cikin Mamaki ganinsa jaye da akwati bata samu Damar mgana ba sai ga Safiya ta Shigo itama Da Hanzari Mama ta mike kafin ta samu Zarafin mgana Baba Manu yace"Amina miko Tabarma ina tare da bakuwa ne..!
Batayi gaddama ba ta shiga Ciki ta Dauko Tabarma Lokaci Daya tana Sanya mayafi ta Fito ta Shimfida musu Baba Manu ya zauna Lokaci Daya yana kallon Safiya yace"Zauna..yata..!
Jikinta a sanyaye ta Zauna agefe Kanta na kasa tana gaida Mama Ta amsa Cikin mamaki.
Kafin ta Dawo da kallonta kan Baba Manu tana Fadin"Baban Sagir lafiya kuwa..? Wannan kuma wacece..?
Baba manu yace"Sagir bai Dawo Daga makaranta bane..?
Mama tace"Bai dawo ba gaskiya..Domin daya dawo ko zai Tsaya Shago sai ya shigo..!
Baba manu yace"Bashi ma a shago Domin na leka ban gansa ba..!
Mama tace"Allah yasa dai lafiya..?
Kai ya girgiza kafin yace"Lafiya ba lafiya..Yanzu dai shi ga Yarinyar nan Ciki Amina kizo muyi mgana kana..!
Mama batayi gaddama ba ta Mike ita ta Dauki Akwatin Safiya Ita kuma Baba Manu ya Umarceta data bi bayan Mama zuwa Ciki.
Batayi musu ba tatashi ta Bita Sanan Daya Daga Cikin kujerun Falon ta zauna Mama ta kawo mata Ruwa ta ijiye tayi Godiya aranta Tana Tunanin kodai nan ne gidansu Yusuf din..? Ammh ai ya Taba gayamata Mahaifiyarsu ta rasu Dagashi sai kanninsa da Kanwarsa da Mahaifinsu suke zaune agidan..? To in ba nan bane gidan su waye nan..?
Mama duk ta kosa taji Abunda ke Faruwa Tana Fitowa ta Zauna Kafin ma Tayi mgana ya Rigata da Fadin"Wannan yarinyar dai da kike gani Yau mukaje Tambayan auranta Shine Ubanta ya Dauro auran kuma ya Hadomu da ita..!
Cikin mamaki Mama tace"Topha..kamar ana yaki..?to matar waye..?
Baba manu yace"Ina abokin Yaron nan Sagir..? Wayake da suna na manta..!
Mama ta Zaro ido Tana Dafe Kirji Lokaci Daya tace"Aure Imran yayi..?
Baba manu yace"Ba Imran din ba Yayansa..Na manta sunansa ko Wayake da suna ma..!
Mama da al"ajabi yagama kamata tace"Yusuf sunansa..?nifa na shiga rudu garin ya haka ya Faru..?
Baba manu ya gyara zama ya Shiga Rattabama Mama yadda komai ya wakana Tun daga farkon zuwansu Gidansa Sagir da Imran har yau da abunda ya Faru gidan Alhaji Alhassan.
Mama ta saka Salati da Salallami ta Dire Tana Fadin'"Wlh baban Sagir bansan komai game da wannan mganar ba..Yaron nan Sagir bai gayamin komai Yau Tun Safe ya tafi makaranta salaha da sukazo da megidanta kawo autan ta karatu suka Daukesa shi da Inteesar din zuwa Cikin makarantan har yanzu bai Dawo ba!
Baba manu yace"Wajen ki Zata zauna tayi karatun kenan..?.
Mama tace"Eh Wlh..!
Baba manu yace"Allah ya bada sa"a..Kin dai abunda ya faru yanzu ya zamu yi ne..?Me kika sani game da Gidansu yaron nan Amina..?
Mama ta gyara Zama Tana Fadin"Wlh bana ce maka nasan komai ba..Ni dai na san Imran din abokin Sagir ne Allah ya Hada Jininsu..Sai kuma nasan basu da kowa Daga Mahaifinsu sai shi Imran sai kanwarsu sai Mahaifinsu Dake kwance ba lafiya Domin na Taba shiga Gidan Sau Biyu na gaidashi..!
Baba manu yace"Ina mahaifiyarsu..?ina yan"uwansu da Sauran Danginsu..? Kuma laluran meye Mahaifin nasu ke Fama dashi..?
Mama tace"Wlh nidai bansani ba..Sagir dai ya gayamin yace Daya Takurama Imran din ne da Tambaya ya gayamai mahaifiyarsu ta rasu mganar Danginsu kuma Wlh shi kanshi Sagir din bai sani ba Imran din baitaba yarda ya gayamai komai ba Laluran Mahaifinsu kuma Ni bansani ba ammh Tabbas Bashi da lafiya yana Cikin Daki kwance ko Falo baya Fitowa..!
Baba manu yayi Shuru bai yi mgana ba illah Ajiyar rai Daya Sauke Lokaci Daya ya Zaro Wayarsa yana Fadin"Bari na Kira Sagir din yazo ya kira shi abokin nashi..!
Mama ta kada kai Alamun hakane din ne.
Baba manu ya kira Sagir,Shi kuma Lokacin yana cikin Makaranta ammh sun Dade da Fitowa daga Lacture,Inteesar yake jira saboda kada ya tafi ya barta bazata iya Dawo wa gida ba.
Yana Dagawa Baba Manu ya Tambayeshi ko yana ina..? Yace yana cikin makaranta nan da nan Baba Manu yace in babu Abunda yake yi ya zo gidansu gsshi yana Jiranshi
Hankalin Sagir ya tashi Dagajin muryan Baba Manu ba waasa acikinta,Gashi kuma Inteesar sun Fito Daga Lacture sun shiga wata kuma yana ma Department dinsu yana jiran Fitowar ta.
Ya rasa ya zai yi sai Allah ya Taimakeshi sai gasu sun Fito yamike ya isa bakin Hall din nasu sai gashi Inteesar din ta Fito Dauke da Jakarta da Wayarta sai Takardun Dake hannunta.
Tana ganinsa ta kariso gabansa Tana Fadin"La ya Sagir..?
Badai kana nan Tun dazu kana jirana bane..?
Sagir yayi Mirmishi yana Fadin"Eh mana..Kada ki Fito baki ganni ba ki fara kuka..!
Abun sai ya bata Dariya Sai data Dara kafin tace"Sai kace wata yarinya ya sagir..!
Yace"Eh mana ai yarinyar ce kada ki kira Babanki kice na barki ke kadai baki gane Hanyar gida ba.!
Inteesar tace"Laa..Zan iya fa komawa Gida dakaina Allah..Kuma ai in ina gaban Daddyna ne nake Shgwabata in ya barni ni kadai Am Mature ya Sagir..!
Mamakin Surutun yaji kafin yace"Wato Shagwabar ma Kinsan inda kike yinta ko..?
Dariya kawai tayi Tana Sunne kai Agogon hannunsa ya kallah Daya na Rana ta kusa ya kalleta yana Fadin"Daman gida nake son Tafiya an kiranibshine nake Tunanin bazaki iya gane gida ba in an tashi Ki kirani sai nazo Mu Dawo Tare..Tunda ni na gama da makaranta sai kuma Jibi in Allah ya kaimu..!
Da sauri tace"A'a kada na Wahalar dakai zan gane ba Gadon kaya ba..?in na samu mai adaidaita yana kawoni anguwan zan gane layin ina da Saurin Dauke abu akaina..!
Cikin son Tabbatarwa yace"Kin Tabbata zaki gane..?
Inteesar tace"Insha Allahu..!kai ya kada duk da haka bai yarda ba sai ya Fiddo wayarsa ya kirata sai ga wayarta na kuka acikin Jaka ganin tana kiciniyar Fitowa da wayar ne yasa yace mata"Nine na kiraki ga lambata nan ki kirani in baki gane ba..!
Kai ta gyada mai Tana Fadin"Thanks..!
Jinjina mata kai yayi kafin yace"In zaki yi sallah ki bi ayarin mata yan"uwanki zuwa masallacin Cikin makaranta in wani abu zaki siya ga Cafteria chan..Sai mgana karatu tunda an wuceki da yawa in kika Dawo sai mu Tattauna Dole sai mun samu Wani ko Wata Cikin Course mate dinki da zai mataimaka miki..!
Cikin jin Dadi ta amsa mai da haka sukayi sallama ya kama Hanya.
Minti Talatin ya bata saboda ya samu go.slow kafin ya kariso Gidan yana Shigowa ya iske Baba Manu har lokacin suna Tattaunawa da Mama Tuni ya Fita ya Sallami Alh.Sadi da Niyyar sau sun yi mgana ta waya ko sun hadu.
Yana Shigowa ya Durkusa yana gaida Baba Manu Mama ta kallesa Tana Fadin"Ina ka baromin yata..?
Sagir yace"Tana chan basu gama Lecture ba..Ammh ban barta ba sai da ta tabbartamin da zata iya Dawowa da kanta..Na dai bata lambata nace in bata gane ba ta kirani.!
Mama ta kada kai kafin tace"Allah ya dawo da ita lafiya..!
Ya amsa mata da Ameen kafin ya maida Hankalinsa kan Baba Manu Daya gyara zama yana Fadin"Ina abokin ka..?
Sagir yace"imran baba..? Ban sani ba ammh ina kyautata Zaton yana gida Duk jiya bamu hadu dashi ba..!
Baba manu yace"Kirasa a waya..Kace masa yazo nan gidan gani Ina tafe da Matar dan"uwansa..!
Sagir ya zaro ido yana Fadin"Mata kuma Baba..?
Mama ta karbe tana Fadin"Eh suna zuwa uban ya Daura auran.Kuma ya hado su da yarinyar tana nan cikin Dakina zaune..!
Sagir yayi Sakace yana bin Mama da Baba Manu da Kallo Cikin mamaki kafin ya Zaro wayarsa a Fili ya Furta"Dankari...!


_Masu cewa wai auran Safiya da Yusuf kamar yar tsana..? In kun bibiya labarin zaku iya Fahimtar Dalilin da yasa Auran ya faru cikin Lokaci Alhaji Alhassan yana matukar Daraja Mutumcinsa akan mutumcinsa kada ya zube zai iya yin komai,Kuma yarda yaga Imu ya tabbata zai iya bangala Sirrinsa yayi Tirere dashi acikin Farantin ya gama yawo dashi kowa yagani kuma ya saani bazai mai Wahala ba Shiyasa ya Daura auran ya yarda Kwallon mangwaro ya Huta da guda.._??C0





*Shakira..*
3/22/22, 23:03 - Ummi Tandama???i: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:JanaftyB??0
{*

*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*

*Ina godiya masoyan GIDANMU Allah ya saka da alheri Allahu ya bar zumunci Ameen,Musamman yan gidan Gidanmu comments Section 1&2,Janaf Novella,Zauren Janafty Shakira da sauransu Tanque so much*


*??T??10*


"Lokacin da kiran Sagir ya Shigo wayar Imran yana kwance akan gado acikin Dakinsa ya gama Busa Sigarinsa har yagaji ya koma ya kwanta.
Gidan nasu ba kowa Yusuf ya tafi wajen aiki,Munari kuma Ta tafi makaranta shi kadai ne agidan,Daya tashi Dakin Abba ya leka ya sameshi yana zaune shuru Shi kadai shi ya taimakamai yayi wanka ya sauyamai kaya ya Hadamai Tea mai kauri da Soyayyan Dankalin da Munari ta soya kafin ta fita bayan ya bashi yaci ya koshi ya Doramai da mgungunansa,wanda ko Minti Goma bai yi ba ya Sulale yana Barci,wannan watan Chanjin mgungunan da Likita yayi mai kamar sun fi yimai amfani,Saboda ya na samu Ishashen Barci Kwakwalwarsa tana samun Hutu sosai Fiye da baya kuma suna ganin Chanji Sosai.
Bayan yayi barcin ne ya Fito Falo nan kan Dinnig ya Hada Tea yasha da Soyayyan Buredi,yaci ya koma Daki ya Dora da Busa Hayaki bayan ya gama ne ya koma ya kwanta sai ga kiran Sagir ya shigo wayarsa karama Kirar Nokia ce Rakani inda Zani Domin Imran bai tabaa Damuwa da sai ya mallaki Babban waya,Shi dai a kira ya Daga kawai kuma Mutanen dayake kira Daga Sagir sai Yusuf ko Munari yana da lambarta ammh ba sosai yake kiranta ba.
Cikin kasala ya Zura hannu ya Dauko wayar,ganin sunan mai kiran yasa yadan saki karamin Tsaki ya Daga kiran yana Fadin"Ya akayi ne Banzan Abokina..?
Dagachan bangaran Sagir dake kallon Baba Manu yace"Kana ina ne..? Ga Baba Manu na gidanmu yana jiranka..!
Imran ya lumshe idanuwansa kafin ya Bude su yace"Kaga mallam gajarta Zencen..Meya faru?
Domin duk da yasan mganar Neman auran yusuf haka kurum yaji ajikinsa da wani abu.
Baba manu ne yayi ma Sagir alamun Daya Fadamai Shi kuwa ya karkace kai yace"Kazo fa Domin Baban yarinyar nan Ya Daura auran Kuma ya Hado su Baba Manu da ita!
Imran bai wani ji mamaki ba sai ma wani Mirmishi Daya saki Kafin yace"Dak???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?yau..Yanzu ta na ina..?
Sagir da mamaki ya cikasa yace"Tana Dakim Mama..!
Imran ya mike Zaune yana Fadin"Gani nan zuwa..!
Daga haka ya katse kiran,Cikin Sassarfa Ya Sauko Daga kan gadon afili yake wani Mirmishi kamar na mugunta aransa yace ya Rage ma kansa aiki..Shifa baisan komai akan Alhaji Alhassan ba Daga farko sai da ya Shiga Gonarsa kudi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login