Showing 18001 words to 21000 words out of 236322 words

Chapter 7 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

701

da Haiba,Akallah a Shakarunsa bazai wuce 65 haka ba,Fari ne Fatarsa mai Cike da Jin Dadi da Hutu kallon Farko zakamai kasan Jininta ne saboda yadda karan Hancinsa ya Fito Zur akan Fuskarsa.
Yana sanye Cikin American Suit Ruwan Toka ya Daure Wuyansa da Tektie, *BARRISTER KABIR HAMISU DUKKU* kenan Babban D'a na farko Wajen Daada(Maryam)
Mirmishi ya sakar mata kafin ya saka Hannunsa ya Riko Tattausan Hannunta da suke Tubus dasu Saboda Samun Hutu da kuma jin Dadi yace"Haba DAADA..taya baki da lafiya kuma ke baki kiramu ba kuma kika Hana Baba asabe kiranmu..?
Yafada yana Kafeta da Kaifaffun Idanuwansa kamar na Mahaifinsu marigayi mallam Hamisu Dukku,gabadaya ya"yan nata Zaratan mazan Duka idanuwan mahaifinsu suka Dauko Gwara ma matan sun Dauko nata Idanuwan.
Ajiyar Zuciya ta Sauke kafin ta Zame hannunta Carbin Dake hannunta ta ijiyeshi nan Gefenta saman Darduman Datake kai Cikin Muryanta mai Cike da Amo da Tsufa adan shake tace"To kabiru ko na kiraku me zakumin..? Ina da mganguna nasha..Daman jiri ne fa kawai DanaTashi jiya da Daddare ya Kamani kuma zuwa yanzu kaganni Alhamdulillah..!
Girgiza mata kai yayi yana Fadin"Ba shi kadai bane Daada..Akwai wani abu..Duk kin kara Ramewa Daadarmu taya ya kikeso mu kwantar da Hankalinmu achan inda muke Zaune muna aiki da iyalanmu Ahalin ke kuma kina nan kina ta Fama da Tunanin Dayake Haddasa miki Ciwo..? Haba Daada ya kamata ki Fahimci wani abu Tunani da Damuwa bashi bane mafita ki kuma sani Bayan Malami kina da wasu ya"yam da Jikokin da suke Bukatar ganinki a Raye Cikin Koshin Lafiya!
Jin ya famo mata inda yake mata kaikayi yasa kawai ta Fashemai da kukan Data ke rikewa Tun Dazu Tuni ya Rikice Ya Rikota yana Fadin"Haba Daada.Don Allah ki Daina kuka..Kada nima ki sani kukan..!
Yafada Daidai Lokacin da Baba Asabe ta yi sallama ta sawo kanta Dakin Dauke da Faranti Mai Dauke da Ruwa da Lemo itama Kamar Daadan take sai dai Daada Zata girmeta ba sai dai ita Baka ce mai Jiki ammh bata da Tsawo.
Ganin Daaada na kuka yasa Bayan ta ijiye Farantin Hannunta gaban Alhaji Kabir ya Zauna tana Fuskantarsa tace"Lauya sai fa kunyi wani abu akwai..Kwanakin nan sam Daada bata samin Ishashen Barci..Koda yaushe sai dai ka ganta Cikin Damuwa ko wanchan Da Dr Madina tazo ta Dubata sai da tayi mata korafin Rage damuwa da Tunani..Kayi mata mgana kila ta Rage..Ka gayamata ta Taimakemu ta kwantar da Hankalinta muna Matukar Bukatarta..!
Baba Asabe ta karishe Fada itama Tana matse kwallah Alhaji Kabir bai samu Zarafin Mgana ba Baba Asabe ta Fita da Sauri Tana kuka yau in suka rasa Daada ina Zata saka kanta matar da Tayi mata komai na Rayuwa ita da Iyalanta Tun zamanin kuruciyarta Tazo gida nan a matsayin yar aiki Daada ita da marigayi mijinta sun mata komai a Rayuwa,Duka ya"yann Daadan ita ta Renosu Domin ita Allah bai Taba bata Haihuwa ba Duk da Auran Wuri akayi mata auran ta Biyu,Dayake ita yar Minjibir ne Dake Jahar kano.Kuma ba wani Cikakkun Dangi Tunda uwa da Uba Duk sun Rasu Da Taimakon wata Hajiya Lanti mai kai mata aikatau gari gari ta Sadata da wannan gidan..Gidan Alheri da karamci kusan Shekaru Arba"in da wani abu Tana Tare da Daaada da iyalanta bata Taba kukan wanu abu ba sai dai Taje chan garinsu Minjibir takai musu alheri Daga Cikin Alheram Daada da Ahalinta Dole ta Rika Shiga Damuwa in taga Daada a wannan Halin.

Bayan Fitan Baba Asabe Alhaji Kabir Cikin Jimami da Damuwa ya Jinjina Hannun Daada Dake cikin nashi yace"Daada menene mtsalan ne wai..? Kinga ni bama mu kadai ba Hatta Baba Asabe bata son rasaki ballatana mu ya"yanki da bayan Rasuwar Baffa kece komai namu mu da iyalanmu yau in kika Fadi kika Mutu ina kike so mu saka kanmu..? Kafin kiran Baba Asabe Dr.Madina ta kirani Tun satin chan Daya wuce ta fadamin yadda Jininki baya kasa Daada kullum sai kara Hauhawa yake yi Ta rasa Dalili Daman ina ta Shirin Tahowa aikine sukamin Yawa Cases gareni har uku Shiyasa baki ganni ba Sai jiya da Daddare da kiran Baba Asabe ya sani Dole na Biyo Jirgi Daganan na Hawo taxi zuwa nan..!
Ya karishe Fada yana kallon Daada wacce ta ke sharan Hawaye kamar wata karamar yarinya kafin ta Dago Tana kallonsa tace"Bani da wata Damuwa sai ta Dan"uwanka Kabiru..Ace yau wajen Shekaru uku bashu ba Labarinsa Shi da iyalansa..? Anya an taba irin wannan Kuwa batan mutum ba Daya ba ba Biyu ba..Kabiru..?
Ta karishe Fada Cikin Taruwar kwallar acikin Idanuwanta.
Fesar da Numfashi yayi yana kara Nazarin yanayin Daada Daman yasan Tatsuniyar gizo ai bata wuce ta Koki..Damuwar Daada Gabadayanta ta Malami ce Shiyasani kowama ya sani.
Cikin Lallami yace"Daaad kiyi Hakuri don Allah..ki kwantar da Hankali wannan Abunda kike yi bashi bane mafita..Ina so ki Sani Malami fa ba bacewa yayi ba..Ko kuma wani Mumman Abu bane ya same shi ba fa..? Daada da kansa ya Zabi yayi nisa Damu yaje inda Bazamu taba ganinsa ba koda Mun Nemesa..Kada ki manta Dani da Mustapha mun Taka Har Chan inda suka zauna Nemansa bamu san iyaka ba mun samo Miki labarin Da kansu suka bar komai nasu Daada..Gidanshi bai saida ba sai dai sun Rufeshi Jami"ar Dayake koyarwa munje Shima ba wani bayani haka Ma"aikatun da yaransa ke aiki munje sun Tabbatar mana da Cewa Sun ijiye aiki da kansu Daada..Kuma Har yau bamu Daina nemansu ba Saboda ke Daada..Na saka a saka ido saosai duk Randa akaga wani Cikinsu na Bada Lambar a wayata a kirani ammh Har yau babu Wani labari Daada..!
Ya karishe Fada Cikin Bayyana Takaichinsa indai ya Tuna da Abunda Dan"uwan nasu ya aikata..
Cikin Sanyin Murya Daada tace"To ina zasu tafi..? Ina jin Tsoron kodai wani mumman abu ya same su..?
Alhaji Kabir yace"Ina ji ajikina babu abunda ya Samesu..Ko Satin Daya gabata naje banki..Na saka an Bincikamin account din Malami an ga ana Cire kudi Lokaci Bayan Lokacin kinga kenan Duk inda suke suna chan suna Rayuwarsu Daada Sun manta Damu da komai nasu Batare da wani Tunani ba..!
Daaada ta Girgiza kai Tana Fadin"Ban yarda Malami zai manta dani da ku yan"uwansa da asalin gabadaya ba..Kada ka manta Faruwar abunda ya Faru ya Taba kwakwalwar malami baya Cikin Hayyacinsa..Laifin na ya"yansa ne Musamman Babban..!
Alhaji Kabir cikin jin Haushi yace"Bai fa Haukace ba Daada...Ciwon Damuwa ce kawai ai Bai fita Hayyacinsa ba yasan Daidai da Rashin Daidai..Na yarda ba da son Ransa suka tafi ba Sai dai ina da Tabbacin da saka Hannun wannan Yaron nashi mai Taurin kai da Zuciya wanda kaf cikin Dangin bansan ina ya kwaso wannan Hallayar ba shine zakka a acikin wannan zuru"ar namu Daada.!
Duk Halin da Daada ke Ciki sai da ta Murmusa Cikin girgiza kai Tace'"Ba Zuciya bace Kabiru..Haka Hallitarsa yake mutum mai saurin Fushi da Fusata Akoda yaushe ina yi musu Uzuri da addu"an duk inda suke Allah ya karesu..Ni Karamar nake Tsausayi tunda itace Mace basu san kowa ba Duka Dangi suna nan Dukku,Dangin Uwarsu ai Nice nan Kabiru Tunda ni na yaye Zuwaira na Riketa har ta girma Mahaifinka ya aura ma Malami ita ina ji ajikina Duk inda suke suna chan su kadai Cikin kewa da kawa Zucci.!
Ta karishe Fada tana Sharan kwallh yana kallonta bai ce komai ba sai da ya Numfasa kana yace"Kada ki damu Daada..Insha Allahu muna iya bakin kokarin mu da yardan Allah zamu dawo da Malami Cikin Ahalinsa..!
Daada taji Dadi ta kara Damke Hannayen Kabir tana Fadin"Haka nake so naji Kabiru..Allah yayi muku albarka kaida Sauran yan"uwanka..Nasan ka kirasu duk ka shaida musu Tun Safe Bintalo da Maimunatu da Mustpaha ke kirana ban Daga ba Saboda nasan aikin Asabe ne..!
Ta fada TanaFadada Mirmishinta,shima Mirmishin yayi ganin ta saki Ruwa ya Dauka ya Tsiyaya yasha ya ijiye Kofin kafin yace"Nida Mustapha kadai mukayi mgana Da Safe Daada..Nayi mai mganar tahowa mu hadu dashi muyi miki mgana kila zaki fi jin mu.Sai kuma yace min kano yake Shirin Tafiya shida mai Dakinsa zasu kai yar wajensa Zata fara karatu anan Buk kano,To yacemin yayi ta kiranki baki Daga in na iso na kirashi in bashi kuyi mgana..!
Baki Daada ta saki kafin tace"Badai wannan Sangartattaciyar yarinyar nan Mustapha zai kai wata uwa Duniya da Niyar Karatu ba..?
Alhaji Kabir na Dariya yace"Kai Daada..Takwarki ce fa...Kike Fada da ita..!
Karamin Tsaki Daada taja kafin tace"ammh kuma bata Biyo Halina ba...ayi yarinyar sai Sangarta da Sokanci ta girma ita ba yarinya ba Duk Mustapha ya bata yarinyar nan Shiyasa sam bana Shiri da ita ko nan garin bata zuwa ko Uban ya matsa sunzo Tare bata ko yarda ta kwana tasan Halina Kaniyarta nake Ci ni ba"a zuwa gidana ace za"amin Sangarta da Sakarci..!
Shidai yana ta Dariya kafin yace"Shiyasa Sajida tace Daada Rigima kamar me..!
Daada tace"Ita ma kaji wata yar Tselan uwa nan..Ita bata da Sangarta sai dai Shigen kiyuwa da Son jiki..Duk Asma'u ta gama batasu dakai..Gwara ma Umaima tafi ta kazarkazar,ammh Duka nafison mai sunan megidana Hamisu!
Alhaji Kabiru yace yana yar Dariya"Shima zaku fara fada in har yaji kina cemai Hamisun nan..!
Daada tace"Ni rabani da Fi"ilinku na yan zamani..Hamisu shine sunan kwarai ba wani Feleke ba..Yana ma ina kwana Biyu ban jisa ba..?
Yace"Yana chan Anambara inda yake aiki kila ya shiga Ruwa ne..Muma kwana Biyu bamu yi mgana dashi ba..Sajida kuma ta Fara karatu anan Base Universty ba Zama Umaima kuma kinsan Bana kinta da kulafuncin Uwa sannan itama ga makaranta ba Lokaci..!
Daada ta gyada kai Tana Fadin"Allah ya rayasu...ya kuma bada sa"a da Rayuwa mai kyau ya kuma yi muku albarka ya kara arziki..!
Ya rika amsawa da Ameen kafin ya Dora da Fadin"Nazo da kayan abinci da Dankalin Naga kamar naku yayi kasa ne..!
Daada tace"Akwai sauranshi..Kai da yan"uwanka bakwa gajiya ko Sati Biyufa ba"ayi ba Bashir dan wajen Mustapha ya kawomin kayan Abinci da kudi hakama Itama Bintalo ta aiko Direbanta dashi..Babu abunda zence muku sai Allah yayi muku albarka ya Raya muku Zuru"arku suyi ta muku hidima kamar yadda kuke yi mini..!
Alhaji kabir yace"Ameen Daada..In bamu yi miki ba wazamu yi mawa..? Ai bamu da kamarki Allah dai ya kara Tsawon rai..! Lokaci Daya yana Lalubo wayarsa daga cikin Aljihun wandonsa
Daada ta amsa da Ameen daidai Lokacin da Alhaji kabir ya Kara wayar akunni yana Fadin"bari na kira Mustapha Daada..!
Kai ta gyadamai kaunar ya"yan nata nakara Ratsata,tana fatan Allah ya cika mata Burinta na Hada ya"yanta waje Daya

*****

Suna gabda da shiga garin Kanon Dabo Wayar Alhaji Mustpha Dukku Dake Hannun Inteesar ta Fara Neman dauki wayar ma ta Zame a hannunta saboda gajiyan Zaman Mota har barci ya kwasheta bata sani ba kiran wayar ya Tada ita Tayi Firgigit ta Farka Daidai Lokacin da Umma ke Fadin"Ke inte miko wayar Daddyn naki ana kiransa..!
Cikin Alamun barci cike a idanuwanta ta Dauki wayar ta Mikama Umma batare data ma kalli mai kiran ba Umma ta karba Tana kallonta tace"Tsiyana Dake Raguwa ce Inte..Daga kaduna zuwa kanon ne Duk kikayi Laushi haka..?.
Baki ta Zumbura wanda ya Zame mata jiki ta koma ta lafe Jikin kujeran Motan Tana Fadin"Allah Umma da Nisa sosai..!
Daddy yana jinsu hankalinshi na wajen Tuki yace"Sahala Daukan min kiran kada ya katse..!
Amsamai kiran Tayi tana Fadin"Barrister ne Mijin Asma"u..Baban Sajida..;
Tafada tana Mirmishi Tunawa da kirarin da Daddy yake ma yayan nashi duk sanda ya kira waya ko suka Hadu.
Gangarawa yayi gefen Titi yayi parking sanin mganar mai tsawo ce yace ya karbi wayar a Hannun Umma ya karata a kunni yana Fadin"Allah ya Taimaki Lauyan lauyoyi..Baban Sajida da Khamis Mijin Asma"u ma"u..!
Dagachan Bangaran Alhaji Kabir ya Murmusa yana Fadin"Mustapha Mijin Sahala..Baban Bashir..Kuma Gatan Mai sunan Daada Inteesar..!
Atare suka saki Dariya Harda Daada Dake zaune gefensa gaisawa sukayi kafin yace"Gani nan na kusa da Daada Tun dazu..Na samu na lallasheta Ammh kaima ka kara gata..!
Yafada yana mikamata ta karba Cikin Fara"a cike da ladabi ya gaisheta ta amsa yayi mata ya jiki tace"Kaifa nifa na warke ba wani abunda ke damuna..Tadin Asabe ne da baya karewa..!
Mirmishi yayi yana Fadin"Haba Daadanmu..Ai nasan ko baki da lafiya haka kike fadi..Don Allah Daaada ki kwantar da Hankali da yardan Allah Damuwarki ta kusa kwarewa Zamu dawo da Yaya Abun ki har gabanki Da yardan Allah..!
Daada tace"masha Allah..Allah ya baku iko..Allah yayi muku albarka..Ina ita Mai Dakin naka..? Ina Babban mijina Basiru..? Ko dayake ko jiya ya kirani mun gaisa harda matarsa ma ina mijin dashi sosai..Banda wannan Sangartattaciyar yar taka mai shigen sangarta da Lalaci..!
Mirmishi yayi ya juya yana kallon Inteesar data koma Barcinta yana Fadin"Kowa Lafiya Bashir yana kaduna shi na barma Harkokin namu yau..Ni da Sahala da Takwarki kuma Daada gamu mun kusa shiga kano Zamu kaita makaranta zata Fara karatun Jami"a da yardan Allah..!
Daada ta kyabe baki kafin tace"Uhm ai yanzu Kabiru ke fadamin nayi ta Fada Mustapha..Bani dai Salahan ita na gayamata kila tafi Fahimtata in kaine kan wannan Diyar taka bajina zakayi ba..
Yana Dariya ya mikama Umma wayar yana Fadin"Daada ce..!
Ko bai fada ba tasani Tunda suna Tare Da asuba sanda Baban Sajida ya kirasa yana Fadamasa Zencen kiran da Baba asabe tayi mai kuma bayan gama wayar tasu sun Dade suna Tattauna damuwar Daadan Dashi.
Karba Tayi Cikin Ladabi Tana gaida Daadan Da Tambayanta Jikinta Daada ta amsa ta Cigaba da Fadin"ke yanzu Salaha da saninki Mustapha zai Dauki Yarinyar nan zuwa wata uwa Duniya da sunan karatu..? Tana gaban ki ma baki iya Tankwarata ba,saboda Ubanta ya Daure mata Gindi Chan din da zaku kaita kusan dasu wa zata fara Mu"amala..? Bafa irin su Maryam ake kaiwa makaranta inda ba kwabar iyaye ba sai ta kara Sangarcewa yarinya ta isa aure ammh Sai wani Sakarci take ko yarinyar yar shekara Biyar albarka..!
Daada ta karishe Fada Cikin Fada Umma dai sai Dariya take kafin tace"Kema kya ce dai Daada..Kila ke yaji mganarki ya Daina Biyema Inte da sangantarta a kusan Koda yaushe ina gayamai aure zatayi watarana ya kamata ya Rage mata wasu abubuwan ammh daga ita har shi ba wanda ke Saurarata Daada..Mganar karatunta a kano kuwa abunda yasa na amince ba Cikin makaranta zata zauna ba Gidan Yaya Amina zata zauna Shiyasa..!
Daada tace"Yayar nan taki ta kano da Mijinta ya rasu Shekarun Baya ko..?
Umma tace"Eh ita Daada..Wajenta Zata zauna in ta samu Hutu sai ta rika dawowa kaduna Dayake ma Dan wajen Yaya Amina Sagir shima makarantar yake karatu zai rika kula da komai..'
Daada tace"To koda naji..Yanzu hankalina yafi kwanciya Allah ya Tsare ya bada sa"a..Ina ita yar Tselen uwar take ne..?
Umma tace"Gata nan tayi barci..Kinsanta Raguwa ce Daada..!
Daada tace"Nasanta kuwa..To ki ce mata nace ayi karatu banda Sakarci da Sangarta.
Umma na Dariya tace"To Daada..Allah ya kara girma..!
Daga haka ta mikama Daddy wayar ya amsa suka cigaba da mgana da Daada yana kara kwantar mata da Hankali kafin abama Kabir din su Cigaba da mgana Cikin Lokaci Sukayi sallama Kana Daddy ya Tada Motar suka cigaba da Tafiya Jefi Jefi suna Taba Hira duk akan Abunda ke Damin Daadan na Batan Dan"uwansu da iyalansa.

Karfe 11:34pm na Rana suka Shiga garin kano Daman Tun Daran Jiya Umma ta kira Yaya Amina ta sanar da ita gobe suna Tafe,To bayan Shigowarsu garin kano Daddy yayi waya da wani abokinsa Dake Lacture anan Buk din a Shashen Kimiya da Fasaha wato Computer Science Daman shi yayi ma Inteesar din Cuku Cukun samun Addmission din Shiyasa suna waya bayan sun Shigo yace su Fara shigowa cikin makarantar Inteesar din Ta fara Regisration din ganin Lokaci yana Tafiya har sun fara Karatu.
Shiyasa kawai suka Fara wucewa Cikin makarantar sai dai Umma ta kira Yaya Aminan ta Fadamata sai sun gama abubuwan daya kawosu zasu kariso nan ammh kwana zasu yi sai Gobe zasu koma ganin Rana tayi kuma ko gama abunda ya kawosun basu yi ba.








*Shakira..*
3/22/22, 23:03 - Ummi Tandama???i: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:JanaftyB??0
{*

*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*


}? }?
}? *??T??7*


"Tunda suka shiga cikin makarantar ake ta Cuku cuku anan sukayi sallar azahar da La"asar suka kuma ci Abinci da Taimakon Abokin Daddy Inteesar ta kamallah registration dinta Sai abunda ba"a rasa ba,basu Fito Cikin makarantar ba sai wajen Biyar da Rabi na yammah 5:30pm Inteesar ta gaji Tubus,Sai raki take yi ita kuma ba yunwa take ji ba Domin taci abinci Kawai tagaji ne so take taji tayi wanka ta kwanta ta Huta abunda ke karamata Tashin Hankali Irin jin datayi gobe ma Zata koma ta karisa ita kadai ba Daddy yaushe zata iya wannan Wahalar ita kadai .? Ta iske Jami"ar Ta bayero ba yadda Tayi Tsammani ba ashe babbar makaranta ce mai Cike da Dalibai kala kala kabilu Dabam Dabam.
Suna tafe amota bayan sun Fito Daga Cikin makarantar,Umma da Daddy suna Hira da yaba tsarin Jami"ar Inteesar na Baya tana Jinsu duk ta gaji so kawai take Tayi wanka Taji ta kwanta ko ta samu ta Huta ganin suna ta Tafiya har yanzu ba su iso ba yasa Ta Dago Dara Daran Idanuwanta Wadanda suka Cika da gajiya tace"Daddy bamu kawo gidan Inna Aminan bane..?
Tafada Cikin Sangarta da gajiya a Muryanta.
Cikin Tsausayamata ya juya Ammh Hankalinsa na wajen Tuki yace"Mun kusa Intee..Sannu nasan kin gaji anya zaki iya wannan Wahalan karatun ko mu koma gida na nema miki nan KASU ne..,?
Ya karishe Fada cike da Tsausayawa jin Abunda yace ne yasa Inteesar tayi saurin Wartsake gajiyarta Tana Fadin"A"a Daddy..Ka barni anan Nafi son Jami"ar Bayero fiye da kowacce Jami"a..Kuma Tunda na taso Daddy ban taba Fita wani garin nayi Rayuwa ba Shiyasa na zabi karatu a garin kano Saboda na kara sanin wasu abubuwan!
Daddy ya jinjina kai alamun jin Dadi Umma Dake jinsu Ta Tabe baki Tana Fadin"Ashe dai Kina da Hankali..?
Hararanta Daddy yayi kafin yace"Me kika Dauke mu..? Umma na Dariya tace"Sangartattu mana Miye ku in ba hakan ba..? Tafada Tana kallon Inteesar da Bakinta ya kusa Fadowa kasa Cikin Kunkuni tace"Daddy kaji umma ko..? Wai nice Sangartattaciya..?
Daddy yace"Manta da ita..Eh kin ji ke Sangartattaciyace wani kikayi ma Sangartanki ba Daddy ki ba..?kyaleta sai tafi kowa kewarki ko bakomai Gidan zai mata Shuru inta koma baki..!
Sanda ya Fadi haka Dukkansu sai sukaji wani iri Tabbas Bai yi Karya sai taji Dabam ita ta Haifi Intee Tasan ta da Kulafucin Gida ko Wani waje bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login