Showing 78001 words to 81000 words out of 236322 words

Chapter 27 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

756

har sunan ya Bini..!
Abba ya Kalleta Cikin Dattakonsa yana Fadib"Masha Allah ai nima sunan Mahaifiyata Gareki..Daga yau kin tashi Daga yata kin koma Uwata..Allah yayi albarka..!
Inteesae bakinta Har kunne tace"Na zama Maman Daddy da Abba kenan..!
Su Munari nata Dariya ta gaida ya Yusuf ya amsa yana Kallon Safiya yace"Naga kamar kuna Sallama ne..?
Da sauri Munari tace"Gobe zata koma Gida Hutu ya Yusuf.!
Tafada Cikin nuna Rashin jin Dadinta Kada kai yayi yana Fadin"Ayyah..Munarin Abba zaki bari da kewa...Anywhy..Allah ya Kiyaye Hanya muna gaida kowa da kowa..!
Abba ma ya Karbe da cewa"Kice ina gaida Daddyn naki..In Allah ya Nufa zamu hadu..!
Inteesar tace"Zaiji Abba..Ka manta bakace agaida Umma ba..Umma Sarkin Fada..!
Tafada Tana Tura baki Munari ta Zungureta tana Fadin"Ke kuma Sarkin Shagwaba da Laifi ko..?Dariya suka sakamata Anty Safiya ta Mikamata Leda Hannunta Tace takai ma Umma Turaruka ne Dana Daki da Humra Inteesar ta Karba Bakinta Har Kunne Sallama sukayi ta karbi Jakar Hannun Ya Yusuf suka Nufi bangaransu Itama Daganan tayi ma Abba Sallama ya Bita da Allah ya Kiyaye hanya Ana gabda da kiran mganariba yasa ya tashi ya Shiga ciki Domin ya Dauro alwala,ita kuma Munari ta koma Bedroom dinta ta Dauko Mayafinta ganin ba kowa afalon yasa Inteesar ta Fice zuwa Haraban gidan ta jirata Hannunta Dauke da Ledoji guda Biyu Daya Sakon Anty Safiya ne Daya kuma na Munari ne kaya ta bata Da Hijabi Sabo ne bata taba sawa ba ya yusuf ya Dinkamatashi itama ta bama Inteesar in ta koma Kaduna in ta gansu ta Tuna da ita.
Tana Tsaye tana Mirmishi Gefe Daya Tana ayyana gobe i uwar haka tana Jikin Daddynta tana Zubamai Shagwaba kamar an ce ta Waiga sai taci karo da Imran zaune kan Mashin dinsa karan sigari a hannunsa idanuwansa suna Lumshe yana Busawa Hayakin yana Fita ta Hanci ta baki.
Tsam tayi tana kallonsa,tsausayinsa ya kamata ganin yanayinsa wanda yasa bata san sadda ta taka zuwa gabansa ta Tsaya ba ganin har ta Tsaya bai Lura da ita ba yasa ta san yayi nisa Cikin yanayin Dayake ciki.
Kawai sai ta saka Hannunta guda Daya ta Zare Karan Sigarin Dake hannunsa Daidai Lokacin daya Ware Idanuwansa akanta.
Dam! Gabansu ya Buga atare, Suka kurana juna ido Cikin Bugawar Numfashi da Muradi mai girma,
Ita ce tayi Saurin Janyen idanuwanta Saboda tana ji kamar Kafafuwanta bazasu iya Daukanta ba
Cikin Sanyinta tace"Ka manta na Fada maka Ita shan Taba Illah take ga Lafiyar Dan adam..?
Ko ka manta na taba Fada maka Shan Taba bata dace dakai ba..?
Har tagama mgana yana kallon Dan bakinta ko Kiftawa bayayi ita bata ma Kara Kallonsa ba ta Saki Taban a kasa ta Mutsuketa Tana Fadin"Bazan barka da ita ba..Bani na aljihunka i know akwai wasu aciki..?
Tafada Cikin Kamewa Lokaci Daya Tana Mikomai Zararan Hannayenta..
Galala yake Bin Hannun nata da Kallon Mamakinta na kamashi Cikin Dakiya ta kara Fadin"bani na aljihunka nace...Kadai san nasan ba wannan bace ita kadai ba ko..!?
Dariyarta ma yake yi acikin Ransa yana mamakin yau rana ta Farko da Mace ta Tsaya gabansa Tana bashi Unarni haka.
Yaji bama zai iya yimata gaddama ba Ya saka Hannu a aljihu ya Dauko Kwalin Taban ya saka mata a Hannu Harda Letthe din gabadaya.
Kwalin tabi da kallo kamar tana kyamkyami nan da nan Zuciyarta ta Fara tashi Daman Daurewa take,Da Sauri ta Bude ledan hannunta ta Watsashi aciki Tana yamutsa Fuska tace"Kamar itace abincinka..? Bantaba Ganinka baka shan Taba ba sai sau Daya..Plz ka bari In ba so kake Huhunka ya samu mtsala ba .!.
Tafada Tana kallon Gefe domin bata so ya Fahimci bakinta ya Cika da Miyau..
Mirmishi ya Sakarmata mai kara Har sai da ta Dago Tana kallonsa Cikin mamakinsa Saukowa yayi Daga Mashin din yana Fadin"Ban ce miki Daman zan daina sha ba..!
Inteesar ta gyara Bakinta tace"To yanzu kayi min alkwarin zaka Daina shan Taba..!
Kallonta yayi kafin yace"No..Ni bana haka ba. bazan yi miki alkwarin da bazan cika ba..Zan daina shanta Duk Ranar da Allah yace..!
Mamaki ya kamata ta Kada ido Tana kallonsa yace"Yes bana yima Mutum alkwarin da na san bazan cika ba..kuma bana so nima ayimin alkwarin da baza"a cikamin ba..Kuma ni bana karya agaban mutum saboda ya soni..Ina Fadin gaskiyatane gaban ko Waye Allah ne kadai nake jin Tsoro ba Mutum ba..!
Daga haka kawai ya wuce ta yana Tafiya Cikin Sarsassafa kafin taji yace"Kada ki sake ki mana Amai Gida..!

Da kallo ta Bisa Har ya shige cikin Gida Mirmishi ya kamata Miyau ta Zubar Daya cika bakinta afili ta Furta..'He is nice..ashe ya Lura ta kusa amai..!
Bata san da zuwan Munari ba sai taji kawai ta Dafa ta har ta Tsorata sai da ta Waiga ta ganta ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Har kin bani Tsoro..!
Munari tace"Hala Ya Imran kika gani..? Yanzu na gansa ya shiga gida yana Cika yana batsewa..!
Inteesar tace"Kamar wani kabewa..!
Dariya suka saka Harda tafawa kafin su kama tafiya suka Fice wa Daga gidan.
Suna tafe suna Hira har gidan Mama akofar gidan sukayi sallama da Munari akan Gobe zata zo kafin Intee din ta wuce,Sai dai Inteesar ta Boyema Munari abunda ya Faru tsakaninta da Imran haka kurum taji bazata iya fadamata ba
Haka Inteesar ta shiga cikin Gida Tana nuna ma Mama Abunda Anty Safiya ta bada akai ma Umma ta Karba tagani Tana ta Godiya.
Ranar barci barawo ne ya sace Intee Saboda Murna asuban Fari tatashi Tayi ma Mama sharan Daki ta Share Tsakar gida,Ta zo ta saka Kettle daya Tafasa ta Juye tayi wanka Kafin ta Fito Mama ta Hada mata abun kari Saboda Murna ko Yunwa ma bataji sai da Mama ta Mtsamata ne tasha Tea kadan da Buredi.
Koda karfe 11am na safe Basheer na Falon Mama shi da su Abiden yazo,Shi daman dan akida ne baya son Tafiyar Dare kuma bayason bata Lokaci shiyasa suna gaisawa da Mama yace Intee ta Fito su Dauki Hanya
Sagir ne ya Fitar mata da kayanta akwati Daya zata koma dashi,sai Sakon Mama na Umma da nasu Inno,sai na Anty safiya,bawasu kaya me da yawa ba.
Tun tana cikin gida ta Kira Munari ta Fadamata ya basheer yazo zasu tafi Munari tace gatanan zuwa sai dai Shuru Har Ya Basheer din da Sagir suka Fita waje aka gama Saka kaya a Booth Munari bata zo ba,Ita kuma Har ta kawo Falo Taga Imran ya Fita Haraban gida sai ta Labe ta Leka taga ko ya Fita sai taga yana Jingine jikin Mashinsa yana Danna Wayarsa karama bashi ma da Niyar tashi,Ballatana ta samu ta Fita kuma ta Tabbata in ya ganta bazai barta ta Fita ba.,Sai ta tsaya nan falon tana Lekonsa Gashi ta bar Wayarta acikin Bedroom dinta Inteesar nata Kira Bata Dauka ba.
Ga ya basheer nata mata Fadan su tafi bayason Tafiyar dare ga yara yazo dasu,Dole tana ji Tana gani ta Fada Gidan Gaba Tana Tura baki Domin tasan ko giyan wake tasha bata isa tace su jira zuwan Munari ba ko kuma su Biya gidansu ba Dama Daddy ne yauwa tasan shi zai mtsamai ammh yau ba Daddy bata isa ba.
Saboda Haushi ma Abiden na Hawa Jikinta ta Harareshi ta Mtsa jikin Kofa Tana Tura baki Basheer bai Damu ba Kallonta kawai yayi ya kada kai,Abida Tana Jikinsa Ta lafe ita akwai son jiki ne Abiden din ne Sarkin wasa.
Haka suka tafi Sagir na Daga musu Hannu da Mama na Daga Zaure Itama Tana Daga musu hannu Allah Sarki Sabo Turken wawa.
Munari dai Dole Daki ta koma tana Cijon yatsa,Wayarta ta Daga taga Kiran Inteesar sai tabi baya,Inteesar na ganin kiran Munari taki Dauka sai da ya Katse ta Turamata Sako.

*Muna hanya..Nayi ta Jiranki baki zo ba..*

Munari na ganin Sakon sai da taji wani iri da sauri ta Rubuta mata da Amsa.
Am sorry Besty..Naso na Fito Ya Imran na gani aharaba shiyasa..Allah ya kiyaye Hanya ki gaida Daddy da Umma..!

Ta turama Inteesar wanda Tana gani sai da ta Murmusa da ta Tuna da Imran cikin Dariya ta Turama Munari..

Is ok..Ameen zasu ji..Ki kula da kanki da kowa da kowa Expecially Muradaden yayanki IMRAN..!
Tana gama Tura mata ta maida wayarta jaka tana Mirmishi Basheer na kallonta bai ce mata komai ba sanin ko yayi mgana bazata Tankasa ba Yau yasan Karansa Wajen Daddy Fada sai ya Toshe kunne.
Munari kuwa Tana ganin sakon ta Zaro ido a fili ta Furta."ni ai bazan iya Kula da Ya Imran ba Tabdijam..!

*****

Koda Inteesar ta Dawo Daddy baya gida,Umma ce Kadai sai Anty Hauwa Inteesar ta makale Umma Tana Murnan ganinta,Haka ta Rumgume Anty Hauwa Tana Murna ya basheer ta bari da Shigo mata da kayanta Murna ya mantar da ita,Shiyasa akace No place Like Home Inteesar ta Fahinci hakan
Umma ta yi mata Shinkafa da Miyar Kaza,sai kunun Aya,Inteesar ta Zauna taci ta koshi sosai,Daddy bai Dawo gidan ba sai Dare Intee ta Rumgumesa Tana Murna ganinsa shi kansa Bakinsa yaki rufuwa Saboda Dawowar yar Lelen nashi.
Ranar kusan raba Dare sukayi suna Hira,Daddy yasha Hirar Makaranta da ta Mama data Ya Sagir sai Hirar Munari da yan gidansu da sakon Gaisuwan Abba zuwa garesa.
Ta kuma bama Umma sakon Anty Safiya Umma ta Karba tana ta Godiya da Sakon Mama na Garin Dan wake,da Yaji sai Daddawa Dakakkiya da kuka da Kubewa,Haka ma Wanda ta aiko ma su Inno harda Garin Kunu Umma sai Murna take..
Inteesar sai da ta Duba ledan Kayan da Munari ta bata taci karo da sigarin data Karba Hannun Imran da Lether dinsa Saurin Dauka Tayi ta Jefa Cikin Tiolet tayi flooshing kada wani ya gani ta Shiga uku.
Inteesar Tana matukar jin dadin Hutunta agida,kwananta Hudu da Dawowa taje gidan su Nasara Ta wuni Daga gidan ta Biya badarawa ta gaida Inno da Mallam Babba sai Dare Muda ya Rakota ta Dawo gida aranar ne da Daddare Munari ta kira Suka gaisa da Umma Harda Anty Safiya bayan sun gama mgana ne Inteesar ta Nuna ma Umma Hotonsu ita da Munari da suke Dauka a makaranta Umma ta kurama Munari ido a Fili tace Kuna kama da kawarki taki Inteesar.
Inteesar tace mata haka kowa ke Fadi Umma kinsan ance kawayen juna wani Lokacin kamarsu na Rikidewa Umma na Dariya batace komai ba Suna Cikin hakane sai ga Daddy ya Shigo Daya Tambayi me suke ma Dariya Umma ta Fadamai bai ga Hoton ba Umma tace ya bari ya Huta Daganan ya manta itama Inteeesar din sai ta sha"afa.
Har gidan Ya Basheer taje ta kwana Biyu Dakyar kamar tana kan kaya ta Mtsa sai da ta koma Gida,Suna Waya da Mama Da Sagir Lokaci bayan Lokaci suna gayamata sunyi kewarta..
Munari kuma kusan kullum sai sunyi mgana da juna ta waya ko ta WathApps.
Kwanan Inteesar goma da dawowa Daga kano ta fara Zazzabi mai Zafi Wanda sai da ya kwantar da ita a asibiti.
Maleria ce ta mata mugun kamu,Sauron kano sun Debi Rabonsu Daddy nata Fadan meyasa ba"a saka mgani agidan Mama tunda akwai sauro Inteesar ta dawo da Maleria.
A dakin da aka kwantar da Inteesar din ne a kebantattacen Daki na Musamman,Asibitin kudi ne,Ya Basheer da Umma da Anty Hauwa da ya"yansu su Abiden din adakin Daddy ke ta Fada Tunda Likita yace Maleria ce ta kama Inteesar mai Zafi.
Ran Umma ya baci ta Dubu Daddy Tana Fadin"Haba Abban Intee kadaina Fadin haka fa kamar baka yarda da kaddara ba? Kuma daka ke Fadin an barta Sauro ya Cijeta Ita Ya Aminan zata zauna tana kula ita kada Sauro ya Cijeta ko..? Kuma ita da Sagir Da suke gidan Su ba Mutane bane Inteesar ce kadai Mutum Tunda yar so ce..!
Tafada Tana Bayyana Bacin Ranta Har Daddy zai yi mgana Basheer ya Girgiza mai kai ganin kada su Fara Fadansu na Fama gaban Suruka.Dole tasa Daddy ya bar mganar Ammh Umma sai Huci take ranta yagama baci.
Wasa wasa dai sai da inteesar ta Kusa Share Sati a asibiti,Saboda da taji Sauki Likita yace zai Sallameta Daddy ya Hana yace sai ta kara Hutawa kwana Shida tayi ta koma Gida Munari ta sani Tunda Data Kira Wayar Inteesar din Umma ta Dauka Ta gayamata Tana asibiti bata da Lafiya Hankalin Munari ya tashi Ta kuma tashi Hankalin su Abba bata Kwantar da Hankalinta ba sai da Taji Inteesar Ta samu Sauki har an sallamo su Daga asibiti ta Dawo gida..!







*Shakira*
3/22/22, 23:06 - Ummi Tandama???i: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:JanaftyB??0
{*




*??T??24*

Duk abunda ya faru Imran bai sani ba Kowani Dakika da kuma Wayewar gari Inteesar na cikin ransa yana kuma Kirga kwanaki da Ranar da Hutunsu zai kare,Domin tun yana Daukan Lamarin wasa har ya fara ganinsa da gaske ne,Domin baisan wani yanayi yake ciki ba ammh Tabbas da Tunaninta yake kwana dashi yake tashi yana jinsa kamar ba Daidai ba in bai ganta ba yana jinsa kamar ya rasa wani kuzarinsa ne da Tatafi.
ya zauna yayi Tunanin meye Hadinsa da ita da Har Tunaninta yake Hanashi Sukunu ya kasa gano bakin Zaren yanzu ya daina Tunanin Tayi mai asiri sai dai yafi Tunanin kila shine Aljanun suka shigeshi Shiyasa ya kasa Gane kansa Kwata kwana.
Afarke yake ko cikin Barcinsa Inteesar ce take giftamai abum kamar almara Ko yana zaune ne yana Kallon wani Waje Fuskarta yake gani Mganarta kuma namai amsa kuwwa acikin kunnuwansa Saboda ita yanzu ya Rage shan Sigari koda ya Daukota zai kunnata sai ya Tuna da mganarta yaji kawai bazai iya Saba mganarta ba Duk da bai mata alkawari ba sai da yaji yana son ya Daraja mganarta akalla ko bata Dawo ta gansa ya Daina sha ba ta Gansa ya Rage shanta Fiye da baya ba kuma domin yana Tsoron kada Tamai Lahani ga Lafiyarsa ba wannan baya gabansa Ya sani Shi Tuni Lafiyarsa ta Samu Tawaya.
Ko alama baisan bata da Lafiya ba Saboda ko Sagir bai taba mai Zencenta ba kuma Saboda ita yake zuwa Shagon akai akai Koda Hirarta ne yaji Sagir din yayi mganarta shi kuma ko Sau daya bai taba mai ba Shi kuma Ego dinsa bazai taba barinsa ya Tambayeshi ba.
Ko agida bai taba jin Mganarta ba Saboda baya zama cikin su Munari ce Ke da Labarinta kuma baya Sakarmata Fuska ba,ballatana yaji wani Zencenta kuma bashi da Lambarta ballatana ya Kirata Ko da ma yana Dashi bazai iya Kiranta ba Saboda yana ganin ai bashi da wata alaqa da ita Abun na Dauremai kai Ko Lokacin dayake amsa sunansa na Imran Wata mace bata taba Burgesa ba Ballatana yanzu Daya Juyama Rayuwar jin Dadi baya,Abun kunya ne babba agareahi wani ya Fahimci Halin Dayake ciki Dalilin haka yasa ya Rage yawan Walwalwarsa Fuskarsa kullum tana Hade ba Fara"a koda bai da yawan mgana ballatana Yawan Dariya Ya yusuf da Abba sun Fahimci wani abu na Damunsa sai dai sun sani koda sun Tambayesa bazai taba Fada Musu ba Imran yana da Ego gayama wani abunda ke Damunsa koda Damuwar abun zai kasheshi ne ya Gwammace ya bar abun shi kadai baya son yadda Ransa ya baci kan al"amarin ya Raba Bacin ran da wani nashi.
Shiyasa yake ta Kokarin yakice abun acikin ransa,Bayason Tunanin Inteesar din tarabi Tunaninshi Sai dai ya kasa Controlling kansa da Tunaninsa Kowani Tunaninsa da Motsinsa Tana makale acikin Ransa da Zuciyarsa Kamanninta da mganganunta sun kasa bacemai acikin Idanuwansa da Kwakwalwarsa.

***
Sunday.
10:03am na safiyar Ranar Lahadi.

Abba ne da Ya yusuf sai Anty Safiya da Munari zaune kan Dining suna Breakfast,tunda yau din Lahadin karshen mako ne,Ya yusuf na Gida cin abinci Sukeyi batare da kowa yayi mgana ba bakajin komai sai karam Cokula da karan Mug din Tea.
Ya yusuf ne ya Kurbi Tea kafin ya maida Mug ya ijiye yana kallon Abba Dayake cin Soyayyan kwai ahankali ammh Rabinsa Hankalinsa baya kan abunda yake yi ya tafi wani Tunanin nadabam.
Ya yusuf ya gyara Zama yana Fadin"Abba badai Tunanin zaka Dawo dashi ba..?
Yafada yana kallonsa Abba Daya Sauke ajiyar Zuciya ya ijiye Fork din Hannunsa yana Fadin"Kunyi mgana da Dr..?
Yusuf yace"Eh jiya na kirashi yace...!
"Wannan watan da kaina zan je asibitin..Kuma ina Fatan ya zama na Karshe Tunda alhamdulillah na Warke da yardan Allah..!
Abba ya katesshi yana fadin hakan Yusuf ya kalli Safiya itama ta Kalleshi Kafin ya maida kallonsa kan Abba yana Fadin"Alhamdulillah Abba haka nake son ji..Allah ya kara Lafiya Gobe Kafin na wuce wajen aiki sai muje Tare In Allah ya kaimu..!
Abba ya gyada kai bai yi mgana ba Munari Dake gefe ta Tusa Dankali da kwai bakinta tace"Abba Am so Happy..!
Kamta ya shafa yana Fadin"Ki daina mgana hakan kada ki kware Munarin Abbanta..!
Kada kai tayi tana Kokarin Daukan Mug din Ruwan tea din Dake gabanta ta kurba ko abunta ta saka abakinta yawuce mata.
Abba ya Dauki Tissue yana Share Bakinsa Lokaci Daya yana Fadin"Yanzu ai nafi kowa sanin Illar Damuwa da Tunani Tunda Sanadinta yasa nayi nesa da komai nawa Ciki Harda yan"uwana da Mahaifiyata..Nasan Zafin Rashin naka sosai na kuma san Zafin Mutuwa Wanda cikin Zafinta nake har yau har gobe..Sai dai na Dauki kaddaranta nasan Mutuwa ta Allah ce kuma Kaddara Musulmi takaci..Mu kanmu Watarana zamu mutu duka munbar Duniyar muje mu Tarar dasu..Ni yanzu Addu"ata garesu Allah ya jikansu da Rahma Allah yasa sun Huta..!
Gabadayansu suka amsa da Ameen Cikin wani yanayi Abba na Shirin mikewa Yusuf yace"Abba Daman Ina son mgana Dakai..Kan Imu ne..!
Abba ya koma ya zauna yana Fadin"Meya samu shi Imran din..?
Yusuf yace"Abba kafi kowa sanin Imran na Bukatar Taimakon mu sosai..bazamu zura ido Rayuwarsa ta tafi a banza a Shan Taba ba Abba We hv to do Something..!
Abba yayi Shuru yana wani Tunani kafin ya kada kai yana Fadin"Kamar wani mataki kake ganin zamu iya Dauka kan Hana Imran Shan Sigari Yusuf...?
Kafin ya bashi Amsa Safiya ta Mike Zata bar wajen Abba ya Kirata ta Dawo Cikin Dattakonsa yace"Koma ki Zauna ina zaki..?
Cikin Ladabi tace"Abba zan koma Daki ne..Naga kuna mgana ne..!
Abba yace"A"a koma ki Zauna..Meye baki sani ba..?wannan gidan kema Kamar Gidanku ne zauna mganar Dukkanmu ta Shafemu..!
Bazata iya ma Abba gaddama ba, yasa ta Koma ta Zauna tana gyara Zaman Vail din Data yane kanta dashi.
Abba ne ya maida Hankalinsa kan Yusuf yana fadin"Umh ina jinka Wata Hanya kake ganin zata Bullemana..?
Bayan Nasihan Dakemai nima kuma inamai ita bai Daina ba..?
Yusuf yace"Eh to kamar mu nema mai Taimako wajen Malaman addini na addu"a Abba..Ko da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login