Showing 102001 words to 105000 words out of 236322 words

Chapter 35 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

767

acikin kunnuwansa Ransa ne ya baci ya kashe wayar batare da yayi mgana ba Inteesar ta Rumgume wayarta Tana jin kamar Imran ta Rumgume saboda yadda Saukan Numfashinsa yasa Taji ta kasa Controling kanta.
Zama ta gyara ta sake Kiransa bai Dauka ba Sai da ta kara Kira kana ya Daga Cikin Dakakkiyar Muryansa yace"Ko waye ke kirana yafadamin kai Tsaye.. kada ya bari Raina ya baci na Bincikosa da kaina..!
Yafada Cikin Kaushinsa kamar yadda ya Saba maimakon tace wani abu sai taki ta Damke bakinta Tana Dariya Farinciki ya cikata dataji Muryansa ganin an ki mgana yasa ya Dago Wayarsa yana Bin Lambobin da kallo acikin Ranshi yana Tunanin wanene? Bai samu amsar ba yaja karamin Tsaki ya datse kiran Lokaci Daya Da kashe wayar nashi gabadaya Zai iya Zuwa Mtn office kan wannan lambar ya Tsani arainamai wayau,kuma abun
da ba"a tabamai ba Dole wani wanda yashanshi ne ko dai Sagir ne...?
Anya shine kuwa..? To in bashi bane Waye? Yusuf dai basa irin wannn Dashi Kodai Munari ce..?ai ita yana da Lambarta To kodai kodai yarinyar nan ne Mara jin mgana..? Zai iya Zama itace saboda yaga ta fara Rainasa Mirmishin Saman lebe yayi ransa ya tabbatar da itace ba wata ba zai bita a sannu zai kamata.
Ita kuwa yana kashewa ta saka Dariyan jin dadi acikin ranta tace ko bazai daga ba zata kirasa sai dai ta kara kira wayar tana kashe,ta kasa Samun shi,sai ta Hakura zuwa Gobe ta maida wayarta ta ijiye ta koma ta Kwanta Hannunta Rumgume akirjinta,Bata Dade da ijiye wayar ba sai kira ya shigo wayarta da Sauri ta dauko da Murnan ko Imran ne sai taga Khamis ne karamin tsaki taja Lokaci daya tana ijiye wayar Wani Takaichi yana kara kamata bata san Dalili ba ta tsani Khamis din,Sau daya ta taba Daga wayarsa bata Kara ba data Fahimci shine achart kuwa ya Tura mata sako ba adadi bata taba Budewa ba.
Messages kuwa ta waya ya turo ba adadi bata taba Budewa ba Bashi ke gabanta ba ita Mu"amala da ya"yan Mami Asma"u kwata kwata bazata iya ba Saboda basu da hali mai kyau har gwarama Umaima,ammh Sajidan nan ai tafi kowa Iskanci tama fi Uwarta Komai ta Damata ta Shanye,haka shekaranjiya Hafsah ta Kirata tana Fadamata Wulakancin data kirata ta mata saboda ta yi adding dinta a group din data Bude musu na mata Zallah Shine ta Fita ita kuma ta sake adding dinta shine ta fita ta Kira Hafsah a waya ta fada mgangun marasa Dadi kan kada ta kara adding dinta saboda ita bata da wannan Lokacin kuma ita ba sa"arta bace da zata Zauna tana wannan Shirmen kada ta kara mata haka bataso Daga haka ta kashe Wayarta ta kuma Sake Fita Daga group din Hafsah na gayama Inteesar taji Takaichin ba ita Sajida ta Kira ba da ta gane bata da wayau da sai ta Raina kanta ta rika ma Hafsah Fadan meyasa ma ta Sakata aciki..? Abu ne na Zumunci ba Dole aciki wanda ya dama ya shiga ayi dashi wanda bai ga Dama shi ya sani,ba wanda ya kara bi ta kanta su Anty Hauwa dasu Aneesa suna cikin Group suna Haduwa ayi ta Hiran Zumunci Inteesar ta kan Jefa mgana Daya biyu ba sosai ba.
Tana cikin wannan Tunanin ne taji karan Shigowar sako Bata ma yi kokarin Dubawa ba,saboda tasan ko waye sai da asuba ta duba Khamis ne Yana magiya ta Daga Kiransa Tsaki Taja ta Share duka Sakonninsa bata ma Tsaya karanta su ba.
Allah yasa basu da Class din safe shiyasa tasha barcinta ta Huta sosai sai 12pm suka shiga cikin makaranta ita da Munari,achan ma makaranta Haka Khamis yayi ta Kiranta taki Dauka Har yabama Munari tsausayi ta Roki Inteesar data Dauka tace mata Wlh bazata Daga ba sai ta Kyaleta..
Tundaga Ranar Inteesar ta samun Abun yi duk dare sai ta Kira Imran ko da bazai dauka ba sai dai yana Dagawa Dukkansu suyi shuru suna jin Numfashin juna,Har ya gaji ya katse Kiran sai ya kashe kiran Tayi da Dariya ita kuma batasan ya ganota ba Ya karbi Wayar Sagir ya saka lambar ya yana Danna kira sai ga Sunan Inteesar sai ga Lambarta ta bayyana Mirmishin Saman baki yayi shi ya sani itace ba wata ba..
Yarinyar nan ta rainashi wlh ammh zai yi mganinta
Sai da sukayi wajen Sati Daya tana kiransa Ranar tana Kira ya daga tayi Shuru taki mgana shi kuma cikin Dakakkiyar Muryansa yace"Yarinyar nan kin rainani ko..?! Ni sa"an wasanki ne da zaki rika kirana kina kin mgana..? Cartoom kika maidani ko karamin yaro irinki..?
Yafada mata Cikin Kaushinsa Koda yaushe Tsoro ya kamata ya akayi yasan itace sai ta fara Kifta ido ta rasa abun cewa Mirmishi yayi kafin yace"Kina mamakin ya akayi na gano ki ko..? Duk abunda Imran yaci alwashin sani sai ya sani..!
Kifta ido take yi kamar yana gabanta ta kuma kasa cewa komai Yasan daaman bazata iya mgana ba Ganin haka yasa yace"Oya jeki kwanta Tunda baki da abun fada..Ki daina Kirana kiyi Shuru bakya iya mgana Am not a Child kamar ki ok..!
Daga haka ya datse kiran Yana Mirmishi har cikin Ransa baisan meyass ransa bai baci da duk Abunda take yi mai ba sai ma Nishadi Dayake jinsa Ciki.
Ita kuwa yana Kashewa ta Fada kan gado tana Sauke Numfashi kamar wacce Tayi gudun Tsira,afili ta Furta"ya akayi ya gano ni..? Na bani..!
Take fada tana Dariyan Nishadi.
Tunda ga ranar bata kara Kiransa ba ya dauka ba sai dai ta Kira data shiga sai ta Katse kiran,ko kuma Daya Dauka sai ta kashe Imran baisan meyasa ba baya damuwa da abubuwan da Inteesar keyi da wani ne kemai Rainin wayau nan bazai Dauka ba sai gashi ita tana yimai bai taba Daukan wani mataki ba in ta Dameshi sai ya Kirata sai ta Dauka taki mgana Shi kuma sai yace"Kin raina ni ko..?
Oya ki je kiyi karatu ki kwanta bana son wannan Shirmen.!.daga haka zai yanke kiran ko ahakan aka Tsaya He make her Night sosai,shima ana shi barayin hakane.
Ta dubasa a Wsop taga bayayi saita koma Turamai sako ta Messages sai tana Zaune ta Turamai sakon"Ya Imu kaina na ciwo..? Ya imu ina jin yunwa..?
Ya imu kana ina..?kaci abinci..? Allah yasa yau baka sha sigari ba..?
Na dawo makaranta nagaji Ya Imu..? Yarinta kala kala take Zubamai mai shi kuma ya kasa Dakatar da ita in ta Turomai sakon zai karanta baya ce mata komai sai tace mai ta dawo makaranta ta gaji kanta na Ciwo sai yace mata tayi wanka tasha mgani ta kwanta,in ta Tambayeshi yasha Taba..?sai yace mata Eh yasha Koda Ranta zai baci sai ya gayamata Gaskiyansa Shiyasa yake kara Burgeta Dukkansu sun Shiga Tarkon son juna batare da sun sani ba.
Ranar asabar basu da makaranta Tunjiya data dawo daga makaranta Taji Cikinta na ciwo kadan kadan sai dai bata maida kai ba bata taba Tunanin Period pain dinta bane yadawo mata wanda abaya Tana Fama Dashi sosai in zatayi kamar ta Mutu to Tana karban mgunguna sai abun yayi mata Sauki sanda Tana Kaduna sai ta shafe wata Uku Tana Period}? batayi mugun ciwon maran nan ba sai dai kadan kadan wanda bai Shahara ba Shiyasa ko Mama bata taba sani ba kuma ganin Tunda tazo bata Taba yi ba ko sau daya ba sai Mgungunanta wannan Hutun data koma gida ta maidasu.
Abun yana mata Kadan kadan ne yasa bata Dauka zai yi Tsanani ba Ranar ita tayi duka aikin gidan,Tace Mama ta Huta Jinin bai zo ba sai Zuwa Dare,Munari bata zo ba yau itama bataje ba tasan gajiya ne na makaranta sai dai zuwa gobe zasu Hadu..
Tana ganinsa tayi wanka ta gyara Jikinta tazo ta saka kayan Barci ta kwanta sai dai mai Tun tana ganin abun wasa wasa har ya Fice Tunaninta ta Fara rike ciki tana wayo Wayyo Allanta Tun tana ciki a Hankali har ya fito Fili Mama Dake falo taji Da Sauri ta shigo Ciki ganin Inteesar kan gado ahannunta kan cikinta Tana Birgima tana kuka Lokaci Daya sai ta Rude ta isa gareta ta Tarairayota Tana Sallami Cikin Kaduwa take fadin"Na shiga ni Amina Maryama meke damumki..? Meya sameki..?
Inteesar na kuka Hannunta kan cikinta Tace"Mama ci..Cikina..marana ciwo..!
Hankalin Mama ya tashi ta Rude Tana Fadin"Daman kina ciwon mara ne in zaki jini..!
Kai Inteesar ta Dagamata Bata samu bakin mgana ba..
Mama ta rasa yadda zatayi Fita falo tayi ta Kira Sagir a waya Tana Fadamai Halin da ake ciki shi kuma Lokacin suna Tare da Imran awaje sai da yagama wayar ne yake fadamai Inteesar ce ba Lafiya Tuni yaji Hankalinsa ya tashi kamar yabi bayan Sagir din sai kuma ya kasa,Ya fara Safa da marwa a waje yana Jiran Fitowarsa shi kuma Sagir yana Shiga ganin Halin da Inteesar ke ciki yasa yace Mama ta sakamata Hijabi bari ya Sami adaidaita su tafi asibiti ta amsa mai da Sauri ta Bude Akwatin Inteesar ta dauko mata Wani jan hijabinta ta kamata ta sakamata.
Shi kuma Sagir yadda yaga Imran ya Rude ne ya kara bashi mamaki bai ma Tsaya yaji wata mgana ba ya fara Tambayansa ya jikinta..?shi kuma ya Fadamai tana jin jiki Adaidaita zai sami su tafi asibiti da Mama kai Tsaye Imran yace basai Mama taje ba Bari su samo adaidaitan sai su kaita bai iya cewa komai ba Sagir sukaje bakin Titi suka sami mai Adaidaita zuwa Kofar gidansu Sagir din kana ya shiga cikin gidan ya Iske Mama ta shirya tana Jiransa Lokacin Inteesar din taji Sauki ta Daina Rike cikin,Nan ya fadama Mama ya samo mai adaidatan yana Waje ammh Imran yace basai taje ba Shi zai rakata su kaita tare .
Mama tace taya zata barta su tafi da ita dukkansu fa Maza ne sai dai suje tare,Inteesar na jin haka tace ma Mama ta zauna saboda Dare zata iya Zuwa Insha Allahu jin haka yasa Mama bataso ba ta barsu suka tafi har Waje ta Rako Inteesar tana Rike da Hannunta,Mama dai taga Dare yayi kuma Inteesar mace ce Sagir Namiji ne Imran ma haka sai kawai ta ce bari ta Rufe gidan tare zasu tafi ba wanda yace mata wani abu..
Tunda Mama ta Rikota yake kallonta Bata ma iya Tsayuwa sai da ta Jingina da Bango Tana Halin ciwo ne ammh Ganinsa yasa taji wani Sanyi Mama ta kulle gidan ta Kamata suka Nufi adaidaita,Mama da Inteesar suka Shiga Baya Sagir da zai shiga bayan sai Imran yayi Sauri ya Shige shi kuma sai ya zauna agaban adaidaita Wani asibitin kudi Sagir yace mai adaidaitan yakaisu.
Inteesar tana kan Kafafun Mama ne da Farko ammh da Ciwo yayi ciwo ta fara Mirginawa tana Rike da Cikinta Tana kuka tana Fadin wayyo Allah zata Mutu Tsausayinta ya kamasu Mama ta kamata ta fashe da kuka Tana fadin mai adaidaita ya yi sauri Imran kuwa yana Zaune ne kamar ya Ciro ciwon jikinta ya maida akansa Rabin jikinta yana jikinsa ne,domin ta kasa Zama waje Daya Hannunta Guda ya Rike gam yana mata addu"an samun Sauki acikin Ransa.
Tana Halin ciwo ammh Rikons na Dabam ne Idanuwanta cike da Hawaye take kallonsa Cikin so da kauna mai Zafin data shigets bata sani ba...
Koda suka karisa asibitin ta galabaita Suna zuwa aka amsheta ganin yanayinta Direct gado aka bata ma,aka sakamata Drip da allurai sai barci Lokacin ta samu sauki ba kamar yadda suka zoba,Likitan yace sai dai ta kwana sai zuwa gobe sai su sallameta agaban Mama da Sagir da Imran yayi ma Mama bayanin ciwon Mara ne ya Sarketa mai Tsanani In Jinin ya Zuba sosai zuwa gobe zataji Dama,ammh ya mata alluran zuwa Gobe in ta Farka zata wartsake.
Dole Mama ta zauna ta kwana da ita Sagir da Imran sai 11pm suka koma Gida,Sagir ya Tsaya gidansu Imran ya wuce gida koda yakoma Abba da Ya yusuf basu iya Runtsawa ba Saboda susan baya taba kaiwa Dare kuma suna ta Kiran wayarsa bai Dauka ba Shi kuma yaga Kiran sai dai lokacin suna asibiti ne.
Yana Dawowa Yusuf ya faramai Tambayan ina yaje..? Bai iya karya ba kai tsaye ya fada musu Inteesar suka kai asibiti bata Lafiya sai jikinsu yayi sanyi sosai Suka Tambayesa ya Jikinta..? Yace taji sauki tana chan asibitin Daganan ya shige daki Baida wata Natsuwa bai yi wani barcin Kirki ba sosai saboda Zullumi.
Washegari Munari taji labari Hankalinta ya tashi ita da Anty Safiya suka tafi asibitin Da ya yusuf harda Abba koda sukaje Inteesar ta farka Taji Sauki sun iske Sagir yazo da ruwan da Zafi da kayan Tea Mama ta taimaka Inteesar ta wanke baki tana bata Tea.
Hankalin Munari ya kwanta saboda Taga Inteesar tasamu sauki Mama tace likita yace anjuma zasu koma gida tunda taji Sauki,Imran yaki zuwa asibitin tunda yaji suna chan,to suna ma asibitin aka sallameta sai Yusuf ya kawosu zuwa Gida kana ya koma ya Dauko Abba da Sagir.
Munari nan ta wuni gidan Mama tana kula da inteesar wacce taji Sauki Sosai Shiyasa tace ma mama kada ta Fadama su Daddy tasan Halinsa yanzu Hankalinsa zai tashi,Tana asibiti yana ta Kira mama ta Dauka Tace mai sun shiga makaranta ta bar Wayar agida,Sai davta dawo ta Kirashi Jin Lafiyanta kalau yasa Hankalinsa ya kwanta.
Imran Tunda yaji an sallamo Inteesar sai hankalinsa ya kwanta bai Je ya Dubata ba sai dai ya kirata a waya yayi mata sannu da jiki yace ta Rika shan ngani ita duk kunya ya kamata Saboda kowa yasan Mtsalanta..
Monday bata samu zuwa makaranta ba sai Munari ne ta leka sai Ranar Talata data samu sauki sosai ta shirya suka Tafi tare.
Ranar alhamis da suka tashi makaranta basu dawo gida ba gidan Ya Sadam suka sauka gaida Waleeda Data ke ta Zazzabi sunyi waya da Aneesan take fadamata sun iske taji Sauki waleedan har tana wasanta.
Sunyi sallar la"asar sunci Abinci Daman koda suka zo Sadam baya Gida suna Shirin Tafiya sai gashi yazo Aneesa ta dinga Kiransa ta mtsamai sai yazo yaga Munari.
Yau ta kara tabbatar ma kanta Munari ce ta Hoton nan saboda ta kara Duba Hoton wayar Sadam,Shine dai bai ganta ba saboda wayar nan tata bata tashi ba wata ya siya mata Shiyasa bai samu ganin Hoton ba,Daman Waleedan taji sauki ita Aneesan abun na Ranta ne yasa ta mtsa sai Inteesar din tazo ita da munarin don Sadam ya ganta da idanuwansa.
Tabbas Shima daya ganta Sai da yayi Shock,ita kanta Munarin taji wani iri Data gansa,Sama sama suka gaisa dasu yaja Hannun Aneesa zuwa Cikin Dakinsu.
Sai da suka Turo kofa kana ya Saketa Cikin Sauri tace"Kaima ka ga..!
Bai bari ta karisa ba ya Fiddo da wayarsa yana Fadin"Aneesa kila Wahala ce tazo karshe..Tabbas wannan yarinyar jininmu ce..!.
Yafada yana Binciko Hoton sai gashi ya gani Daidai Munari yayi Zooming yana nuna ma Aneesa lokaci Daya yana Fadin"Indai kuwa ba itace bace suna mugun kama..!
Aneesa tace"nifa inaji ajikina itace..Ka duba kaga kammaninta duk da bata kai haka alokacin ba kamminta bai bace ba..!
Sadam ya gyada kai yana Fadin"Meye sunanta..?
Aneesa tace"Maimunatu..Suna Kiranta Munari..!
Ido ya waro yana Fadin"kai..Kin manta Daman Daada tace Karamarsu ita ce taci sunan Mommy..Ina da kyakyawan Zato yarinyar Diyar Kawu Malami ne..!
Aneesa tace"Nima ina da wannan Tabbacin Tun ranar dana fara ganinta..!
Kansa ya dafe yana Fadin"Ina ne gidansu..? Kenan suna garin kano ba wanda ya sani..!
Aneesa tace"Bansan gidan ba Inteesaar tace kusa da inda take zaune ne..!
Wayarsa na Hannunsa yace"jeki falo ki Tsaida mun su bari na kira Sa"id a waya muyi mgana..!
Tana Kokarin Fita tace"Shi kadai zaka Kirafa..Ka mu kira mu fada yazo ba Haka bane..!
Kai ya gyada mata yana Fadin"Nasan Abunda nake yi Aneesa..!
Daga haka ta Fice ta barsa yana Kiran Wayar Sa"id kira Daya cikin na Biyu ya Daga kiran ko sallamsa Sadam bai amsa ba ya Shiga Rattafamai abunda ke Faruwa.
Yana zaune a office ne sai da ya Mike Zaune cikin Firgici yace"Sadam kada ku bari ta subuce muku.Tunda kuka Tabbatar da kammaninta da sunanta am Very sure itace.!
Sadam yace"Nima ina Tunanin haka..ammh yanzu ya kake ganin za"ayi..?
Sa"id yace"Ka kira su Kawu ne..? Sadam yace"Ba wanda na kira sai kai..!
Da sauri yace"Yauwa..kada ka fadama kowa yanzu kada kabari su tafi su kadai ka Tsaida komai ka kaisu kada kayi sanya kasan yadda Zakayi ka Shiga Har cikin gidan nasu domin ka Tabbatar da abunda muke zato..!
Sadam yace"Shikenan yanzu daman koda Aneesa ta Kirani zasu tafi..Bari na fita nace zan kaisu gida..!
Sa"id yace"Good..Yadda ake ciki ina Jiranka sai ka kirani..!
Daga haka suka yanke kiram Jikinsa na rawa ya Fice Saboda Rudewa Cikin Bedroom din ya manta da key din Motar sai da Aneesa ta shiga ta Daukomai nan yace shi da Aneensa da yara zasu kai su domin suga inda Inteesar ke zaune.
Ba wani bata Lokaci Aneesa ta Sako mayafinta,waleeda na Hannun Munari Inteesar ta riko ma Waleed hannun suka Fice ta kulle kofar Falonta.
Inteesar da Munari da yaran suna Baya su kuma suna gaba Sadam yana Driving yana kara kallon Hoton nan na wayarsa yana kara Kallon Munari ta Madubin Motarsa Har sai da ta Fara tsarguwa Tasbihi kawai yake acikin Ransa domin ya gama Tabbatarwa wannan itace Maimunatu diyar kawu Malami.
Sa"id sai kiransa yake bai dauka ba Sai dai ya Turamai sakon suna Hanya ne basu isa ba,In sun isa komai kenan zai kirasa.
Sun shigo gadan kaya Sadam ya Juya yana kallon Inteesar yana Fadin"Bari mu fara kai kawarki gida mu shiga mu gaisa da mahaifinta}? sai mudawo mu shiga inda kike zaune agaisa kafin mu wuce..!
Inteesar tace"To ya Sadam..!
Munari kuwa haka kurum taji gabanta na Faduwa kwata kwata bata yarda da zuwa gidansu ba sai dai ta kasa cewa komai.
Tafe tafe Inteesar na nuna Hanyar har Kofar gidansu Munari ya Sadam ya Zuba Hon Iro megadi ya leko cikin mamakin ganin Mota ganin bata Yusuf bane Har ya Bude musu suka Sulala cikin Haraban gidan bai Daina mamaki ba.
Imran dake duke a gaban mashin dinsa d yana gyara Wani Abu ne Daga kasa yaji Shigowar mota bai Damu Daya Dago ba azatonsa Yusuf ne shiyasa ya cigaba da Abunda yakeyi.
A parking space sadam ya faka Motarsa suka Firfito koda ya Fito idanuwansa na kan Imran dake Duke so yake ya Dago da kansa yaga ko waye..!?
Ita kuma Munari duk ta Tsure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login