Showing 129001 words to 132000 words out of 236322 words

Chapter 44 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

769

yi ya Dade bai yi Uban da ya fasa yaci Ubansa..!
Tafada cikin bacin rai jin haka yasa bai kara mgana ba ya Fice Daga Falon zuwa Dakunan da suke kwana Mami Asma"u ta Tada Sajida suka kamata Ita da Umaima zuwa Dakin da ta sauka ita da Umma,koda suka Shiga sun samu Umma na Sallar Shafa"i da Wuturi kan gadon dake Dakin ta Ssuke Sajida dake faman ajiyar rai Tana Lallashinta tare da mata alkawarin auran nan bazai Tabbata ba
Umaima na gefe batace komai ba ita karama ce ta Tabbata ta Fadi wani abu wanda ya saba Ra"ayin Mami Sai Ranta ya baci Sajida kuwa tana kwance lamo acikinta Ranta Tana Fatan Allah yasa a Daura auran nan Tunda take bata taba jin bugun zuciya kamar yadda take jin kan Imran ba Daman saboda shi ne yasa Har kawo Lokacin bata ga wanda yayi mata ba sai da ta gansa ta Tabbatar da yayi Daidai da Ra"ayinta Rashin Tsoronsa da Zuciyarsa ke kara Tsumata akansa Taji gabadaya ya gama Burgeta bata Damu da mganar Mami na Shaye Shayensa ba Ta tabbata in suka yi aureta Zata gyarasa ya Daina shan komai,Tasan in ta Bude baki tace wani abu Yau Mami Asma"u sai ta kwana tan Fada kamar ta ari baki Shiyasa tayi bakam kamar Itama tana cikin Damuwa da Umarnin Daadan ne nan kuwa bata sani ba Ranta Fes yake.
Umma na gefe Kanzil batace ba sanin itama Mamin ba Ragamata Zatayi ba Tunda Har Daddyn Intee Bata Ragamai ba Umaimai Dakin da su Munari suke ta koma Zata kwana Mami Asma"u na cikin Damuwa yasa bata ma bita kanta ba.
Bangaran Inteesar kuwa Kukanta gabadaya yaki Tsayawa tana kwance kan gado tana kuka,Munari da Hafsah na Zaune gefenta sun Saka Tagumi sunyi Tambayan Duniyan nan Taki ce musu komai.
Hafsah ce ta kalli Munari tana Fadin"Ko ciwon kan nata ne ya matsa mata..!?
Munari ta Sauke Taguminta tana Fadin"Ni bansani ta kuma ta ki tayi mgana..!
Tafada daidai Lokacin da Umaimah ta Shigo ganinsu haka yasa take Tambayansu ko lafiya Hafsah suka nunamata Inteesar dake kuka Har yanzu tana Dukunkune kanta Cikin Hijabinta tana Shesshekan kuka.
Umaima ta Zauna gefen gadon Tana Fadin"Ko mu kira Umma ne..?
Munari ta mike tana Fadin"Yauwa bari nayi mata mgana..!
Jin haka yasa Inteesar ta Dago kanta Cikin Shakewar Muryan data gaji da kuka Tace"Kada ki kirata Muna..!
Munari ta jiyo tana Fadin"Saboda Mene..? Kin ki gayamana meke Damunki ammh kin zauna kina ta kuka ba Dole Hankalin mu ya tashi ba..!
Inteesar ta Koma ta kwanta Tana Juya Idanuwanta da suka koma jawur saboda kuka wani suya take ji acikin Kirjunta da wani Nauyi,kamar an Dora mata wani Dutse mai girma,Cikin Dauriya tace"Ciwon kaina ne fa zai bari in na samu Barci kada ku damu dani ku kwanta abunku..!
Tafada tana kara Dunkule jikinta Waje Daya gabadaya kallonta sukayi Cikin wani yanayi batare da sun kara mgana ba suka koma suka Zauna Jugum jugum ganin haka ne yasa Inteesar din ta Mike ta Zare Hijabin jikinta Idanuwanta na Rufewa Ta Wuce cikin Sanyi sanyi ta Fada Tiolet Domin tayi wanka ko ta Daina jin Abunda take ji acikin Zuciyarta ita Damuwarta Daya Imran bata san Wani Hali yake ciki ba,Tasan Halinsa da bakar Zuciya yana Wajen nan bai dawwo cikin Gida ba,Gashi Har 11pm ta wuce Dare ya fara Nisa.
Ganin ta shiga Tiolet ne yasa sukayi Shirin kwanciya Hafsah ta Dauki Filo da blanket ta yada saman Cafet ta kwanta Munari ta saka kayan Barci ta kwanta saman gado ita da Umaima kowa na sake sake acikin Ransa.

Bangaran Imran kuwa bai san iya adadin Lokacin Daya dauka yana Busa Hayaki ba har sai da duka Sigarin ta kare gabadaya kana ya Hakura wani irin Turiri yake ji acikin Ransa sai yau ya kara jin Radadin Rashin Uwa ya tabbata da yau Anni na Raye da zama bango garesa ammh Saboda bai da Uwa yau ga abunda ya Faru dashi domin ya Daukesa ne a mtsayin Tozarci Abunda Mami Asma"u tayi mai Abba ba"a sakashi a Lissafi sanyinsa yayi yawa,agaban Daada da yan"uwansa Baya Daga Murya Tun farko saboda haka yasan bazai ce komai ba ammh shi Dole ne yayi mgana.
Kafafunsa ya Hade waje daya ya Saka kansa Tsakanin Cinyoyinsa ya Fashe da wani kukan Dayaji yana Tasomai Daga kasan Ransa,Rabonsa da kuka Tun Lokacin Rasuwar su Anni sai yau Zuciyarsa nada Taurin da kuka ba kasafai yake iya yinsa ba sai dai Zuciyata tayi ta kuna ammh yau yaji yana son yayi kuka kukan Rashin Mahaifiya agaresa,Kukan Rasa Anni yana Tuna Sanda Tana Raye mai kula dashi,Tana fadin Imran ka dinga shiga Mutane ka Rage wannan zuciyar taka Saboda Rayuwa in yau mune watarana bamu bane Imrana ina jiyemaka Ranar da zakayi kukan Rashina Rashin mai fadamaka gaskiya...
Haka yake jin Amon muryanta acikin kunnuwansa kamar alokacin take Fadamai sai ya kara Fashewa da kuka ammh Abun mamaki babu ko Digon Hawaye sai dai idanuwansa sun kala sun yi Jajir,Haraban gidan Tar yake da Hasken Wutar lantarki,Shiyasa Megadi dake zaune bakin get kan bencinsa yake Hangensa,Tun Lokacin Daya Fito ya gansa yana shan Tabarsa kada kai yayi kawai bai ce komai ba ya Cigaba da jin Radion sa.
Inteesar ta bata Lokaci kafin ta Fito Daga Tiolet din wanka Tayo ta Dauro alwala Domin taji barcin ya Fita Daga Idanuwanta kanta nata Sara mata ga Nauyin kirjin datake ji wanda ta rasa Dalili ta iske dukkansu sunyi barci.
Wata Rigar barcinta ta saka Riga da wando masu Taushi ta saka Hijabinta ta Daidaici gabas ta tada Salla Shafa"i da Wuturi tayi Kafin ta zauna nan inda Tayi sallar ta jingina da gado Ranta namata Daci ita ba wai wani abu ba Bata son Ya Imu ya auri wannan marar mutumcin bata Dace dashi ba sannan Cin Zarafin da Mami Asma"u tayimai yau ya bala"in sosa mata rai Bacin ran Imran bacin ranta ne in wani abu ya samesa sai taji duk ta Damu wayarta ta jawo Dake saman gado ta Duba Lokaci 12:12am na Dare jikinta yayi sanyi Tana Tunanin Ya Imran ya Dawo cikin gida ko yana Waje..!?
Wajen sako ta shiga ta Turamai

"Kana ina ne..? Plz ka dawo cikin gida Dare yayi..'!!

Tunda ta Turamai take jiran amsarsa ammh Wajen Fin Minti goma bata gani ba,Sai ta kara shiga damuwa Kiransa tayi Har sau uku bai Dauka ba Hankalinta taji ya kara tashi ta Mike Tsaye tana Tunanin ta Fita ne tagani ko kuwa A"a..?
Imran yana Cikin kukan Zuccinsa dana Sarari yaji Shigowar sako acikin Wayarsa kamar ya Share sai yaji ya kasa ya Dago kansa bayan ya Zaro wayar daga aljihun wandonsa ya Duba sai yaci karo da Sakon Inteesar wani Dum yaji acikin Zuciyar sa Ransa ya kara kuna yana Tunanin me Zata fadamai ita datake kuka Saboda Mganar Daddy..? Karamin Tsaki yaja ya goge ma sakon nata wanda ta Turo ammh ya kasa goge duka Sakonninta Haka kurum yaji bazai iya ba..
Wayar na Hannunsa take ta kira yaki Dauka sai da ta gaji da kira ta Hakura kana yaji Kamar bai kyauta ba ita Kadai ta damu dashi da Halin dayake ciki Shiyasa ya Turamata sako.

"Ki daina Damuna plz ki kyaleni..'

Haka ya Rubuta mata tana Daga Tsayen Taji shigowar sakonsa Hannunta Har rawa yake wajen ta Duba Tana ganin Abunda yace taji Hankalinta ya kara tashi a Fili ta Furta"Yana cikin damuwa Ransa ya baci.Kuma shi kadai a waje..!
Tafada Wasu Zafafan Hawaye na Biyo kuncinta batasan meke damunta Taaudsyin Imran da wani abu acikin Kirjinta da batasan ko na miye ba suka Rinjayeta ta Fito Daga Dakin Tana Sanda,Falo ba kowa shiru Duk an kashe Haske,dakuna ko"ina akulle Su Abba Tuni sun gama Tattaunawa Da Daada ta Sallamesu sun nemi makwanci Ba motsin kowa,Ahankali ta Fara takawa bayan ta Dan Taba Wayarta Haske ya kawo saboda ta rika ganin gabanta Har ta samu nasaran Ficewa Daga Falon Tunda kofar a Bude take ba"a Rufeta ba.
Tana Fitowa Haraban gidan ta Fara waige waige Karaf kuwa ta Hangosa kan Mota ya Cusa kansa Tsakanin kafafunsa Allah sarki kalleshi shi kadai Haka ta fadi acikin Ranta tanajin wani Feeling dake taso mata Daga kasan ranta kan Imran da har yau ta kasa Tantance Menene hakan..?
Jikinta a sanyaye ta Fara takawa zuwa Gabansa bai ji tahowarta ba sai dai mganarta kawai yaji.
"Ya imran..!
Tafada Cikin karyewan muryan Data Shake a kuka da Sauri ya Dago shima Rinannun idanuwansa ya Sauke Cikin nata gabadaya sai da Jikinsu ya amsa Hade da Bugawar Zuciyarsu,mamakin ganinta ya kamashi Saurin Dirowa yayi Daga saman Mota yana Fadin"Ke meya Fito dake yanzu da Tsohon daran nan..?
Yafada Lokaci daya yana Duba Agogon Fatan dake hannunsa yaga 1 saura na Dare ido ya sakamata ganin Ta faramai Hawaye Cikin Bacin ran data karaman ganin kukan ta ya Daga Murya yana Fadin"Wayace ki Fito..? Nace wayace ki fito..?..
Yafada Cikin Tsawan data Fashemai da kuka Tana fadin"Wajen..ka..nazo..!
Tafada Cikin muryan kuka Zuciyarsa ZAfi take da kukanta shiyasa Ransa ke kara baci Cikin Tsawan ya kara cemata"Ban ce ki kyaleni ba..Ni bana Bukatar kowa I don"t Need Anybody..Ki wuce ki koma Cikin Gida Tun kafin Raina ya baci na saka miki Hannu anan Wajen..!
Ya karishe fada yana so ya Danne Abunda yake ji yana Tasomai Daga kasan Ransa.
Ita kuwa kuka kawai take Ta saka Hannunta taja Hijabinta ta Toshe Bakinta ganin in ta Cigaba da Tsayiwa yana jin kukanta Zuciyarsa Zata Tsawartse saboda Bacin rai yasa ya nuna mata Hanya yana Fadin"Oya your way here..Kije chan ki cigaba da kukan naki ba sai kin zo kin fadamin ba..Nima bazan ce a auran mik...!
Bai gama Mgana ba yajita kikam ta Fadomai jikinsa da wani irin karfi Ta Rumgumesa kamkam kamar wani zai kwace mata shi Lokaci Daya tana kara Fashemai da kuka.
Jinta Cikin jikinsa da yadda ta kamkamesa sai ya sauya komai yaji sa Cikin yanayin dayake shiga duk sanda Jikinsu ya Hadu waje Daya kukanta ya sakamai Rauni jin Dumin jikinta ya sakashi jin wani yar acikin jikinsa Tuni Zuciyarsa ta Bude ya Farajinsa kamar bashi ba,Zuciyarsa ce ta Rinjayesa yajisa ya saka Duka Hannayensa ya Rumgumeta kamkam shima atare suka ja Numfashi Cikin Bugawar Zuciyarsu alokaci Daya.
Shima indaizai Fitar da Hawayen Dayaji Dadi ya fita tsawo shiyasa kanta ya tsaya saman Faffadan kirjinsa Shi kuma ya nannadeta da Hannanyensa a saman kanta ya aza kansa ya sauke Numfashi.
Cikin muryan kuka Inteesar ke Fadin"Kada ka kara fadin haka ya Imu..!Ni bazan taba gudunka ba Har Abada..!
Kalamanta Daki daki ke shiga Cikin kunnuwansa,Yana Rike da ita cikin Wata irin Raunanniyar murya yace"A"a..Bana so naga ina sakaki kuka..Kiyi Hakuri Daady bazai aura Miki Dan iska kuma dan Shaye shaye ba..!
Yafada yana kara jinta ya Riketa kamar itace Salama acikin Rayuwarsa,Rikon yayi mata Zafin Dayasa sai da ta saki yar kara sai kuma Lolacin ya Farga da abunda ya aikata da Sauri ya Saketa ya mtsa baya yana Kokarin Daidaita kansa
Inteesar kallonsa take Cikin wani yanayin Da takasa gane ma kanta ta Bude baki Zatayi mgana kawai ya Ja Hannunta Lokaci Daya suka Fara Tafiya zuwa Cikin Falon Daada.
Ta kara yunkurin mgana ya waigo yana jan Bakinsa"Shiiii...!
Alamun tayi Shuru Dole ta maida bakinta ta kulle sai dai idanuwanta suna kan Hannunwansu da suke Hade Waje Daya tana jin wani irin Babban al"amari acikin zuciyarta Idanuwanta ta maida kansa yanayin Tafiyarsa kadai Zaka Fahimci maza na inda suke..
Tunaninta ya katse ne sanda suka Shigo Falon,sun shigo kenan Sajida Data Fito Daga Kitchen ki shi ya Fito da ita Daukan Ruwa kuma ta Kunna Hasken Falon idanuwanta Kur akan Hannun Inteesar dake cikin na Imran Cikin Faduwar gaba take Binsu da kallo.
Imran kallo Daya yayi mata bai kara ba Ita kuma Inteesar gabanta ne ya Fadi,tuna yanayin data gansu kada ta Zargesu da aikata wani abu.
Ta bude baki zatayi mgana kenan ya Saki Hannunta yana Fadin"Ki kwanta..And Stop craying ok..!
Yafada yana Tsareta da Idanuwansa masu cike da bacin rai.
Tana kallon Sajida dake kallonsu tama kasa gaba ballatana Baya bakinta ya kasa Motsi ganin haka yasa kawai ya Juya ya nufi Koridon da zai sadashi da Dakin da ya ssuka cikin Tafiyarsa ta Sassarfa da Jarumta Daga Intee Har Sajida ba wacce ya kara kallah,Bakinciki ne fal acikin Ransa,Yana jin wannan yarinyar ayadda yake jin Zuciyarsa Zai iya Kasheta bai Huce ba baima san kallonta Shiyasa yayi wucewarsa kada ma ya kara ma kansa Bacin rai.
Sagir kadai ya iske a Dakin Yayi barci Ashe sama sama ne karan Bude Kofa ya Farkar dashi da mamaki yake kallon Imran wanda ko kallonsa bai yi ba ya Tura Kofar Tiolet ya shige ya Bango kofa.
Sagir ya Sauke Numfashi kafin ya koma ya kwanta bai jima a Tiolet din ba ya Fito Dagashi sai Gajeron wando Jikinsa na Digan Ruwa Daga gani Wamka yayi,ko mai bai shafa ba ya Watsa kayan daya Cire nan kan gadon yaja Filo ya yada kan Cafet ya kwanta Ringine Ruwan jikinsa na Diga a inda yake bai Damu ba saima Hannayensa Daya goya saman Kirjinsa yana Sauke Numfashi Sama sama.
Sagir Harda Tashi Zaune yana Lekensa yana kallonsa yayi kamar bai gansa ba sai ma ya juya bayansa Kawai yana kara Hade ransa kamar bai taba Dariya ba.

Afalo kuwa Inteesar ce ta fara wucewa Dakinsu batare data kara Kalln gefen da Sajida take Tsaye ba,Sai da ta shige ta Rufo kofa kana ta Sauke ajiyar Zuciya tana goge Busasun Hawayen dake idanuwanta,Jikinta yayi wani irin sanyi haka ta karisa gefen Hafsah ta koma kwanta Tana jin wani yanayi a tare da ita Runtse ido tayi Ba domin tanajin Barci ba sai Domin Tana Fatan ya Dauketa,Hankalinta ya kwanta Tunda ta gansa kuma ya Dawo Cikin Gida Sai dai Hankalinta ya tashi da kalamansa,
Shi a zatonsa tana kuka ne Saboda Abunda Daddy yace..?Baisan tana kuka bame saboda Tsausayinsa da wani Lamarin data kasa gane Wani yanayi ne? Menene yasa Kirjinta ke Nauyi kan Imran..? Meyasa bata son bacin ransa? Zuciyarta na Zafi in ta gansa Cikin damuwa Bata san Dalili ba sai dai ta Danganta haka da Dan"uwanta ne sannan akwai sanin juna Tsakaninsu tun kafin su gane su din Ahali Dayane.
Sajida kuwa Har Inteesar ta Shige ta barta Zuciyarta bata gama Dokawa ba,Idanuwanta na hango mata gilmawar magijin Hannaun Inteesar Cikin na Imran dinta Zuciyarta taji tana Dokawa da karfi datayi Tunanin kodai soyayya suke yi..? Kai ina badai so ba sai dai in wani abun to kodai kodai..!.da sauri ta yanke wannan Tunanin domin ya kusa sakata ganin Jiri to ammh in ba ko Daya meye sukeyi Cikin Dare ko wa yayi barci Hannayensu Cikin na juna..?
Bata damai bata wannan amsar Shiyasa cikin Sanyi jiki ta karisa Cikin Dakin Data Fito,Dauke da goran ruwan Data Dauko Daga Kitchen Mami Tayi barci duk da Kila bataso ma Tayi barcin ba sai dai ai shi ba"acin bashinsa Umma ma kan Darduman data gama sallah Tayi barcinta Ita da Mami ne suka Hau kan gadon....
Lallabawa tayi ta Haye gado ta kwanta Tana kokarin Daidaita Tunaninta kada Zargi ya shiga Cikin Zuciyarta ya Dagulamata komai..

*******

*Washegari*
Kano.
10:00am

Hajiya Mero ce da Alhaji Ahasaan da Tasleem zaune kan Dining din Dake Falon gidan,Suna Breakfast kowa na cin Abincinsa bakajin karar komai sai Cokali da bugawar Filet da Kofuna.
Hajiya Mero bata wani ci da yawa ba ta Share bakinta da Tissue tana kallon Tasleem tace"Tasleem tashi ki Daukomin wayata acikin Bedroom dina..!
Alhaji Alhassan dake Zaune yana Tura Dankali soyayye Cikin bakinsa,Cikin muryan Abu na Cikin bakin mutum yace"Haba Mero kina gani fa Breakfast take yi ai kya bari ta gama ko kuma ke tunda kin gama ki tashi ki Dauko Da kanki..!
Wani kallo tamai batace komai ba Tasleem ta mike tana fadin"Bakomai Abbu bari na Dauko mata..!
Shima bai yi mgana ba ya cigaba da Tusa dankalinsa yana Hadawa da Kurban Ruwan tea a wani karamin mug mai kyau da yarari.
Ba jimawa sai ga Tasleem ta Dawo da Wayar Hajiya Mero a hannunta sai da ta Zauna ta mikamata Tana fadin"Gashi Mommy..!
Karba Tayi tana Yar dariya da sai da suka Kalleta gabadayansu Lambar Safiya ta Lalubo ta doka mata Kira ta saka Wayar a Speaker ta ijiyeta nan kusa da Hajiya Alhassan saman Tebir din.
Kira Daya biyu uku Safiya Daga Chan bangaran da suke Kitchen suna aikin Abincin da su Abba sukace ayi mai yawa Saboda bayan Salar azahar in in aka gama Daura auran za"a Fito da Abincin arabama Mutane.
Gefe ta koma kafin ta Dauki Wayar Tunda gabadayansu suke Kitchen din Har da Inna Maimunatu dasu Zainab dasu Aneesa da su Munari Inteesar na Cikin Daki bata Fito ba tace kanta na Sara mata.
Sallama ta Ragada kafin tace"Mommy ina kwana..!
Momny ta amsa Tana Fadin"Lafiya lau Daugher ya kuke..? Ya Dukkun..?
Tafada tana kallon Alhaji Alhassan Daya ijiye cin abinsa yana Sauraransu Da mamakin jin ta ambaci Dukku.
Safiya Dagachan bangaran tace"Lafiya lau Mommy gamu cikin sha"anin biki kin ji Hayaniya ko..?
Mommy tace"Eh fa bikin waye..?
Safiya tace"Mommy Imran za"a Daura ma aure yau da yar"uwansa Diyar wanda Abba kebi Baffa Kabiru Barrister Dake Zaune A Abuja..,!
Mommy ta Rike baki tana Fadin"Ikon Allah kice Tuwon a maina Za"ayi..Ammh abu cikin gaggawa haka..?
Safiya tace"Daurin auran kadai za"ayi Mommy Tarewa inaga sai daga Baya..Daada ta hada abun saboda kara Hada kansu Waje Daya..Mommy kinga Danginsu gabadayansu kowa yazo da ya"yansu gidansu Babban Gida ne Mommy a Dukku su din Dangin Manyan Mutane ne Duk garin Dukku ba wanda baisan Iyalan Gidan Marigayi Alkali Hamisu Dukku ba..!
Mommy Dake sakin Dariya Tana kallon Alhaji Alhassan ta gfen ido kafin tace"Masha Allah..Naji Dadi sosai Safiya..Allah bai barin Zalunci Daman Nagodema Allah yadda wani yaso ki tozarta Allah bai bari haka ya Faru ba gaki yanzu cikin Ahalin mijinki Cikin nasaba da Karamcin da Tushe da asali in arzikin ne suma sun Taka Allah ma godemaka da kika Tsallaken Siradin Tozarci sai dai Mutum ya Tozarta..!
Ta Karishe Fada da karfi kuma da gayyah ba Alhaji Alhassan ba Hatta Tasleem da Safiya susan da wanda suke.
Safiya tace"Plz Mommy..!
Tafada Cikin shagwaba Hajiya Mero Tace"Ki gaidamin da Yusuf sai kun dawo zamu zo da Saratu da Tasleem Insha Allahu..!
Safiya tace"Tom Mommy ki gaida Abu da Tasleem sai na Kiraki..!
Daga haka ta katse kiran Mommy ta Mike Dauke da wayar tana yar waka Lokaci Daya tana Fadin"Allah ba azzalumin bawa bane..Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login