Showing 126001 words to 129000 words out of 236322 words

Chapter 43 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

748

Inteesar yanzu Mustpaha..!
Daddy ya yunkura zai mike Abba ya Rikeshi ya Dago yana kallonsa sai ya Girgiza mai kai shiyasa ya koma ya Zauna yana Huci Umma Kuwa na gefe Ranta duk ya gama baci tana ganin Sakacin Barrister sai yau ta Kara Tabbatar ma kanta ya Dade da Zama Mijin tace sai abunda Asma"u ta yanke.
Inna Bintalo ne ta Tabe baki Tana Fadin"Mganar gaskiya aduba mganar Asma"u..Ko yayane..Gwara abu mai kyau da Lalala..!
Mami Asma"u na jin haka Ta ce"Yauwa Binta daman nasan ko kowa bai Fahimceni ba ke zaki Fahimceni..Ki fa Duba Sajida fa kalleta ace Rana Daya za"a Illata Rayuwarta a aura mata Mashayi Rayuwarta ta Dauwama cikin kunci da bakinciki na Har Abada..Ina bazan bari a Cuceki ba Sajida bar kuka..!
Tafada Tana kallon Sajida dake kuka Wanda ita atunaninta kukan Mganar Daada take nan kuwa bata sani ba Sajida tana kukan yadda Lokaci Daya Zuciyarta ta kamu da son Imran sai dai Tana Hango wani al'amari nan gaba.
Daada da sai yanzu Tayi mgana Baffa Kabiru ta kalla cikin Takaichi kafin tace"To sallammmane ka Dakatar da Matarka hakanan tayi iya abunda zamu iya dauka ya kuma isa haka..Ko Tayi shuru ta koma ta zauna ko ta Ficemin daga Falo bana son ganinta!
Daada ta Fada Cikin bayyana bacin Ranta Mami Asma"u ta saki baki Tana kallonta ta Bude baki Zatayi mgana Khamis ya mike yana Fadin"Mami plz..!
Yace mata yana Riko hannunta Dole ta koma ta zauna kana ya koma Wajen zamansa Baffa Kabiru kuma bai ce komai ba,Kansa ma yamaida kasa,kamar bashi a falon saboda Yasan bazai iya Dakatar da Asma"u ba Yasan tabbas tana kan gaskiyanta ne sho kanshi bai yarda da mganar Daada ba banda Rikicin Tsufa Ina Sajida ina Imran ai Tazaran akwai Nisa kamar Tazaran sama da kasa ne.
Daada ta kada kai tana Fadin"Nayi matukar mamakin yadda na bada Umarni wanda ko ya"yana basu isa suce A"a ba sai ke Asma"u kika Mike agaban ya"yana kika ce ban isa ba kuma nayi son kai banda adalci..!
Ta karishe Fada Tana Kallon Mami Asma"u datake cika tana Batsewa.
Kafin ta Cigaba da fadin"Kuma agabanka Kabiru baka iya cewa komai ba saboda abunda tayi a wajenka Daidai ne ko..?
Dagowa yayu yana Shirin mgana ta Dagamai Hannu Tana Fadin"Ba sai kace komai ba na Riga nagama Fahimtarka..Ka nuna ban isa dakai ba Matarka ita keda iko dakai..Sai dai ina so ka sani Sajida bata fi karfin Imran ba sai ma shine yafi karfinta ba Domin Rayuwa ba ita bata isa ta taka Inda ya taka ba duk takamarta kuwa..Imran yafi karfinta da Duk Abunda Uwarta take takama dashi..!
Ta karishe Fada Tana bayyana Bacin Ranta.
Mami Asma"u tasan da ita Daada take wannan mganar Khamis sai girgizamata kai yake mganar Daada tayi ma Daddy da Inna Maimunatu Da da Munari da Safiya da Yusuf da Sagir Dadi Domin Ransu kuna yake data ke jifan Imran da kalmar dan Shaye Shaye Umma ma taji Dadi sai sakin Mirmishi take yi,Inteesar kuwa Ranta kuna yake ga Cin Fuskar Mami Asma"u ga Imu ga kuma mganar Daada.
Baffa Kabiru dayaji kunya ganin Daada ta ganosa ya muskuta yana Fadin"Ba haka bane Daada..!
Da sauri Tace"In ba Haka bane meyasa kayi shuru..?in kana so na yarda Matarka ba ita keda iko dakai ba..Ka Amince da wannan Hadin nawa..Sannan ina son a Daura auran nan Kafin kowannen ku ya koma Bakin aikinsa Gobe kenan in Allah ya kaimu..!
Gabadaya aka Zurama Daada ido Gaban Baffa Kabiru ya yanke ya Fadi ya Dago yana kallon Daada ta Hade rai ba Fara"a,kansa ya maida Wajen Mami Asma"u wacce ta Girgizmai kai da Sauri Rauninta ya bayyana bazata Jure ganin an Ruguzamata Rayuwar yarta ba.
Imran kuwa kansa na kasa bai Dago ba,yana Tunanin shi yaro ne da za"ayi mai irin wannan auran..? Me Daada take daukesa ne..?mara amfani ko wanda baisan inda kasan ke mai Ciwo bane?Kamar shi Imran ba wanda ya isa ya Wulakanta shi ko yakaskastan dashi bai nunamai kuakuransa ba Karyansa zai nuna ma Mami Asma"u tayi kuakure bazai taba Auran yarta ba Har Abada.
Baffa Kabiru bai da wata Manufa bai isa ya Bijerema Umarnin Daada ba Sai da ya Sadda kasa kafin yace"Shikenan Daada..Na Amince Allah ya kaimu goben lafiya..!
Da sauri Daada ta Saki Mirmishin Farinciki Tana Fadin'Masha Allah.Kai fa Malami me kace kan mganata..?
Abba bai da tacewa kansa ya Gyada yana Fadin"Duk yadda kikayi daidai ne ni da Imran masu Bin Umarnin ki ne..!
Mami Asma"u ta Mike Cikin Hargagi tace"To wlh in shi ya amince..Ni ban Amince ba..In dai ina Numfashi bamai Aura ma Ya"ta Dan iska Dan Shaye wanda baida Sana"ar fari ballatana na baki sai shaye shaye..!
Tafada da karfi Tana Zaro idanuwanta Waje.
Imran daya gama jin iya Abunda zai ji yakai wani limit din da Bazai iya Jurewa ba ya Mike da Sauri jikinsa na Rawa Cikin Dakakkiyar Muryansa mai Cike Amo da Zati yace"Kada ki kara Kirana Dan"iska..Ko Da'n Shaye..Shaye..Don"t Try it again..Don"t Ever Try it...!
Ya karishe Fada Jijiyoyin kansa sun Mike Radau har ana ganinsu Naman Kirjinsa na sama da kasa Lokaci Daya yan Sakin Huci mai Zafi tare da Zafin Zuciya kamar yayi Bindiga haka yake jin kansa,Hannunsa Manuniya ya Daga yana nuna Mami Asma"u dashi Cikin Alamun gargadi.
Gabadaya kowa sai ya koma kallon Imran cikin Mamaki,Umma aranta tace ai gwara yayi mganinta Haka ma Inna maimunatu taji acikin Ranta.
Mami Asma"u da Ta tsaya tana kallonsa Cikin dan shakarsa Tace"In na kara fa? Me zaka iya Mara kunya Fitsararre..?
Tafada Cikin Ingili tana Jifansa da Harara,Imran dayaji ya Fara rasa Duka Controling dinsa ya Fara Takawa zuwa gaban Mami Asma"u Cikin Dakakkiyar Muryansa yace"Sai na nuna miki Halin Dan Shaye shaye..Na kuma gwada miki Halin Yan iskan da kike Fada..!
Yafada yana kallonta Ido Cikin ido babu Wani tsoro ko Shakkarta.
Taji Tsoro saboda ganin yanayinsa sai dai kasawa ba nata bane Cikin Dari dari tace"An ce maka Dan shaye shaye..? Karya akayi ba Dan Shaye Shayen bane..?
Tafada Cikin Nuna iya gaskiyarta ai batama gama Sauke Numfashi ba taji Hucin Imran gabda Fuskarta kamar Walkiya ya kariso gabanta Idanuwansa Sun Rufe baima gani Dakyau Zuciyarsa ta gama Rufewa da wani Duhu har yana Hango kansa yayi Ball da Mami Asma"u da sai ta Gamu da Bango kanta ya shafe ya Tabbata bazata taba manta dashi ba.
Sai dai ya Daga hannunsa da Niyar Tureta Abba ya Mike da Sauri Cikin Abunda bai fi kiftawan ido ba ya Dakamai Tsawa"Imran...kada ka Fara..!
Yafada cikin Tsawa da Hargagi wanda ya Firgita kowa,Mami Asma"u tayi bayan Baffa Kabiru da suka Mimmikewa Cikin mamakin Imran,Imran kuwa Cak ya Tsaya yana Sakin Huci mai Zafi idanuwansa sun Juye kamar yana cikin maye,Inteesar da Munari suka kamkame juna suka Fashe da kuka Su Sadam kuwa suma Mimmikewa sukayi cikin mamaki.
Abba cikin Sauri yace"Yusuf da Sagir ku Rukemin shi..!
Yafada a Taushashe Daada Dake Zaune bata Motsa ba Illah dan Mirmishi Data saki In Asma"u ta tabata Kabiru yayi shuru ta tabbata In tayi ma Imran bazai kyaleta ba yaron Zamani ne mai ji da kuruciya Shine Daidai da ita.
Da sauri Yusuf da Sagir suka Karisa suka Rikesa daman suna Ta tsoron kada ya balle musu,Kokarin Fizge kansa yake yi suka mai Riko sosai Yusuf ya Kallesa yana Fadin"Imu..Imran kalleni..!natsu Nace maka..!
Yafada Cikin Daga Murya,kallon Yusuf din yayi yana Budemai idanuwansa Cikin Muryansa mai cike da amo yace"Na natsu fa kace..?Kake fadamin na Natsu..? To bazan natsun ba..ka sakeni nayi mganin matar nan..Nace bana son ana batamin rai Bana so...BANA SO..!
Tunda nazo na shiga Harkan wani..? Ina kebe kaina ne saboda ina Girmama yanayina..Bana so na bata ma wani rai nima bana son wani ya batamin Tayi ta mganganu akaina Cikin son ranta..Waya Dakatar da ita..?ko wayace mata ta bari bai kamata ba? Sai ni domin nagaji nayi mgana..? Wlh billahill Azim bata san Waye Imran ba yau bazan ji mganar kowa ba indai matar nan ta kara Bude baki ta Fadi wata mganar banza akaina sai na Nuna mata Kalata sai na Nuna mata ita din ba kowan kowa bace a Wajena..!
Ya karishe Fada Cikin Tabbatar da mganarsa Khamis ne ya Isa gaban Inran Cikin Fushi daman Tun dazu yana Tsaye so yake yaga Karshen Rashin kunyar Imran din in zai iya Dukan Maminsu..? Lalle da yau yagane Shayi Ruwa ne..!
Kikam ya Tsaya gaban Imran yana Fadin"Yanzu kai in aka barka sai ka Daketa..?kasan wacece ita agareni.?mahaifiya kasan kuwa mtsayin uwa a wajen D'anta..!?da zai iya zama ya Jure Cin Zarafinta Daga wani bangara..?
Yafada Lokaci Daya yana Dukan Kirjin Imran wanda ya tsaya Kikam Shima yana kallon Khamis Cikin wani Kallo na Takaichi Karamin Tsaki yaja kafin ya kwace hannunsa a wajensu Yusuf ya Saka Hannunsa ya bambare Hannun Khamis akan kirjinsa yayi irin Wurgi da Hannunsa da Zafi sai da Yayi baya kamar zai fadi kana ya Tsaya da Kafafunsa.
Cikin Nuna sa da yatsa Imran yace"Kai yaro kauce badai kai zan yi ba..Ita din wacece..?ni ba kowa bace a wajena..Ko Baffa Kabiru dake mtsayin Yayan Mahafina bai isa ya tsaya yana gayamin mganar da wanchan matan take Fadamin ba ballatama ita ba kowan kowa ba..In kai kasan Darajan Mahaifiyarka ni kuma da bani da uwa ai nasan Darajan kaina...Kauce kabani Wuri kafin ranka ya baci..!
Ya Karishe fada Lokaci daya ya bangaje Khamis dake tsaye sai da yayi gefe kamar Zai Fadi Sagir ya Rikosa gaban Sajida dake makale jikin Umaimah ya Karisa Cikin kallon Kaskanci Tare da kare mata kallo Daga sama Har kasa kafin ya Nunata da Yatsa yana Fadin"Wannan abar ne kike Rigima akanta..? Ai ni ban ga mace anan wajen ba..Na Rantse ga Allah ni Imran Abubakar Malami Wannan yar taki a cikin yanmatan da zan iya maneji dasu bata aciki ko acikin Tsakiyan Shinkafa ta shiga zan saka Hannu na Tsinceta na Wurgar..Nafi Karfin yarki da Duk Abunda ta mallaka..!
Yafada yana karkato da kansa Wajen Daada kana cikkn Kaushin murya yace"Daada ki janye mganarki..Ni ban amince da wannan Hadin naki ba Ko matan Duniya zasu kare Bazan iya Auran Diyar masu som kai da son zuciya ba. infact ma batamin ba..Bana sonta bazan taba sonta ba..!
Yafada kai Tsaye Zaro ido Kowa yayi yana kallonsa Mami Asma"'u taji Tsoro yasa ta kasa wani Motsi tana Bayan Baffa Kabiru da shima ya kasa Cewa kala ballatana Fadan datafi karfinka sai ka maidashi wasa.
Ballatana Khamis da Mamakin karfin Imran ya kamasa Sagir dake rike dashi ganin yana Kokarin kwacewa yasa ya Girgizamai kai yana Fadin"Kada ka shiga wannan Fadan..Abba ne kadai ya isa ya Dakatar da Imu ammh wlh kai bazaka iya ba..!
Zallar gaskiya ya gani acikin Idanuwan Sagir yasa ya kasa Motsi.
Sajida kuwa Kukanta ne ya Karu jin Abunda Imran yace ita kuma alokacin ji take Imran yayi mata Dari Bisa Dari.
Inna Bintalo ce ta Saka Salati tana Fadib"La"ila Ha'illahu Ni Bintalo yau ina ganin Abun mamaki kai Imran Matar yayan Mahaifinka ka Daga hannu Zaka Daka..? Ashe baka da kunya da Tarbiya bansani ba..?
Kai Tsaye Imu ya kalleta Ido Cikin ido kafin yace"Eh..Ai ba uwata bace..?ko Ita din U..!!!
Bai kai Karshen mganarsa ba Yaji Abba ya Sauke mai kyakyawan mari Guda Biyu Dama da Hagu da sai da Kansa ya koma gefe yana jin Wani Radadi daga kasan Ransa Idanuwansa ya Runtse ko Dagowa bai yi ba.
Abba ya Nunasa da Yatsa Cikin Takaochi da Bacin rai yace"In ka kara cewa Tak anan wajen..Ni ba Mahaifinka bane..!
Da sauri ya Bude idanuwansa Jajir ya Sauke kan Abba zai yi mgana Abba ya Dagamai Hannu yana Fadin"Kace Tak zan ci maka Mutumci Imran..Kaji ma na Fadamaka..!.dole Imran yayi shuru Ya koma yana kokuwa da Bacin Ransa ji yake kamar ya Naushi kansa saboda Bakinciki da tozarci.
Abba ya sauke Hannunsa Cikin bacin rai yana Fadin"Ni kaina ban isa na take mganar Daada ba ballatana kai..To bari kaji na Fadamaka ba wanda ya isa ya Tada Umarninta Za"a Daura wannan auran agobe da yardan Allah kamar yadda tace sai dai in zaka Rataye kanka ne ko kuma ka sha Fiya Fiya ka Mutu karewar rashin So kenan..!
Yafada cikin Tabbatar da mganarsa kafin ya cigaba da Fadin"Kuma na Rantse in ka kara cewa wani abu kan wannan mganar sai naci maka Mutumci..Duka ka bama Asma"u da Yaya Kabiru Hakuri kafin na Saba maka..!
Yafada cikin bada Umarni Imran ya Dago ido yana kallon Abba,kai lalle uba ma wani abu ne Da ace yau ba Abba bane waya isa..?
Ganin ya tsaya kallonsa ne da Jajayen Idanuwansa yasa ya Dakamai Tsawa Har Jikinsa na rawa yace"Ko bazaka Duka bane ni na Duka da kaina na basu Hakurin Rashin kunyarka..?
Yafada yana Nunasa da Yatsa,Yusuf ganin yadda Abba ke rawan jiki yasa ya Isa kusa dashi ya Riko sa yana Fadin"Abba koma ka zauna zai yi Abunda kace..!
Yafada yana Rikosa,Yusuf ya kallah kafin yace"Kyaleni kawai Yusuf..!
Yafada cikin Tabbatarwa da nuna Bacin Ransa jin haka yasa ya Kyalesa ya Karisa Wajen Imran ya Dafa Kafadansa yana Fadin"Kayi Abunda Abba yace Imu..Plz..!
Bai yi gaddama ba ya saka Gwiwiyinsa a kasa Kirjinsa na kuna Cikin Dashashewar Murya yace"Ku...yi hakuri..!
Lokaci Daya yana Sadda kai Cikin Takaichi yanajin kansa kamar ma yayi Bindiga saboda Zuciya.
Mami Asma"u ganin an bata Hakuri yasa Ta fito daga bayan Baffa Kabiru Tana wanu tabe baki ganin haka Yasa Abba ya juya yana Fadin"Ina kara baku hakuri a madadinsa..Yaya Kabiru dake Asma"u ku yi hakuri ku yafe masa..!
Yafada yana Hada Hannuwansa alamun Roko Baffa Kabiru ne ya Jinjina kai Lokaci Daya yana Sauke ajiyar Zuciya Kafin yace"Is ok..!
Da haka bai kara cewa komai ba,Mami Asma"u baki ta tabe kafin tace"Uhm..Shikenan..!
Abba ya gyada kai yana Fadin"Nagode..!
Lokaci daya ya juya wajen Imran yana Fadin"Tashi ka koma Wajen zamanka..Kuma ba cewa nayi ka Fita ba..!
Yafada kafin ya kalli Sagir yana Fadin"Sagir kamasa kuje..!
Sagir na jin haka ya Rikosa yana Fadin"Tashi Imu..!
Bai yi gaddama ba ya Mike ammh Idanuwansa ma basa ganin gabansa Saboda bacin rai nan idanuwansa yakai kan Inteesar dake kuka Sai Yakara Rikicewa Kujeran dake Kusa dasu ya saka Kafa ya Daketa sai da tayi baya ta Wuntsula suka tashi a Firgece su uku ita da Hafsah da Munari suna Makyarkyata da kallo Kowa ya Bisa Abba kai ya Girgiza Shi da Yusuf.
Sagir yayi ya zauna yaki a Tsaye ya tsaya ya Harde duka Hannuwansa saman Kirjinsa ya Lamkwashe kafafunsa yana Girgizawa.
Daddy ne yace kowa ya koma ya Zauna kana Falon ya natsu bayan kowa ya Zauna Abba zai yi mgana da Daada ta Dakatar dashi da Fadin"Ba sai kace komai ba Malami..Abunda kayi daidai ne ka nuna mana Rauninka baisa ka Daina bama ya"yanka Tarbiya ba,Duk da itama Asma"u bata kyauta ba ta shiga mganar da ba nata ba sai dai Duk inda karami da babba ke Fada to Karamin ne za"a Hukunta ko da shi keda gaskiya naji Dadin Hukuncinka..!
Ta karishe fada Cikin Dattako kafin ta Dora da fadin"Dalilina na Hada wannan auran don Dinken wannan Barakan dana Hanga Tuntuni ne..Za"ayi wannan auran gobe insha Aallahu kamar yadda nace..Ke Asma"u Allah yasa kiyi Hankali..Yanzu Imran suruki yake wajenki in baki Daukesa Danki ba..Kai ma Imranu Asma"u Suruka take gareka in baka Dauketa Uwa ba..Ku koyi girmama juna saboda haka..Dare yayi kowa yaje ya kwanta ya"yana kuma zamu kara Tattaunawa acikin Daki..Allah yayi muku albarka Gabadayanku..!
Wasu ne suka samu amsa ma Daada da Ameen Mikewa tayi Daddy da Abba da suka mike tsaye suka Taimaka mata zuwa Dakinta,Inna Maimunatu da Inna Bintalo da Baffa Kabiru suka mara musu baya.
Imran kuwa shi ya Fara Fita Waje Haraban gidan kansa sarawa yake yana jin kamar ma yayi Bindiga saboda Bacin rai wato sun Dage sai anyi ko..? Lalle zasuv samu karamar bazawara kamar yadda suka Dauramai bada son ransa ba Wlh Tallahi sai ya aikata abunda bazai ma kowa Dadi ba.
Yafada Lokaci Daya yana Zaro karan Sigarinsa ya kunnata ya Haye saman Motan Yusuf ya shiga busa Hayaki ta Hanci ta baki itace kadai zata saka yaji Bacin ransa ya Ragu in ba Haka yau ba zaman lafiyaa
Achan Falo kuwa kowa ya Watse Munari ta kama Inteesar suka Shige tana Waigen Inda Imran yabi ya Fita Mami kuwa ya"yanta ta Rumgume tana jin wani Radadi acikin Ranta Yayinda Khamis yazo yana bata Hakurin ganin Harda kukanta.
Su Anty Safiya Daki suka shige Kowa zuciya ba Dadi Umma ma Dakin ta Shige Domin barci ne a idonta itafa bata ji wani damuwa ba mganin mai Son kansa kenan
Su Yusuf kowa wajen kwanciya suka Nema kowa ba Fara"a ammh kai tsaye Sadam yace yaji Dadin abunda Imran yayi ma Ma????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  mi Asma"u kila ta Daina abunda takeyi.
Badai wanda yace komai Yusuf da Sagir Tunaninsu na wajen Imu basu san Halin Dayake ciki ba sai dai Dole su kyalesa sun san ko giyan Wake suka sha Karyansu suje wajensa ahalin Dayake ciki Kadaicinsa Shine mafita da wani yaje ya Damesa sai dai suna Fatan Allah ya Huci zuciyar Mazaje...!




*Sai hakuri Team IMSARB??0
{ kuyi Hakuri..ku kara Hakuri kila Burinku zai cika agaba ammh a wannan gabar Daada ke da Filin Dagar??._??C0*




*Shakira*
3/22/22, 23:14 - Ummi Tandama???i: *GMB2??T??6*


*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*

Mami Asma"u ta Rumgume Sajida ajikinta Tana Lallashinta ganin tana ta kuka,Dago kanta tayi tana Share mata Hawaye Lokaci Daya Tana Fadin"Kalleni nan Sajida..In dai kin yarda ni Mahaifiyarki ce bazan taba bari a Rusa miki Rayuwa ta Hanyar aura Miki wannan Dan iskan ba..Ki daina kuka kinji ko My Sajida..!
Tafada Cikin son Tabbatar da mganarta ga yar Tata.
Khamis da Umaimai Dake zagaye da ita Tun bayan Ficewar kowa Daga Falon shine ya budi baki yana Fadin"Mami plz.Bana jin Dadin Abunda kike yi..Umarnin Daada ne kuma Kin Tabbata ko Dad bazai Tsallake mganarta ba ban ji dadin abun kikayi ba..Kamar yadda Dad zai bi Umarnin Daada kema Dolenki ne mganar wannan Yaron kuma am Begging u Mami ki daina Shiga Shirginsa zai iya miki komai domin baisan Darajanki ba..!
Yana mgana Mami Asma"u na Hararansa Sai da yakai Aya kana ta Saki Wani Dogon Tsaki kafin tace"Sai kawai nayi shuru a cutar dani da Rayuwar ya"ta to bazan yi Shurun ba..Mganar Dan iskan chan kuwa bazan fasa Fadin gaskiya ba duk abunda zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login