Showing 87001 words to 90000 words out of 236322 words

Chapter 30 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

773

Kokarin ku..?yau ne ya bar gida..? Yanzu fa Kimamin Shekaru uku har da wani abu da Bacewarsa shi da Iyalansa Ammh ba wani Labari sai Faman Fadamim kike yi kuna iya bakin kokarinku..Ina Kokarin yake..?ba wani Kokarin da kukeyi kowannenku yana chan yana Harkan gabansa Kawai Shi ya Dameshi baku Damu da Dan"uwnku Daya bar gida Cikin Lalura da Raunin Rashin Daya Fuskata ba..To bari kuji na Fada muki ba iya Kokari nake so kuyi ba Sama da Kokarinku zaku yi ku dawo min da Dan"uwanku gida in ba Haka ba Nima Zaku wayi gari kunyi Sanadiyar Rasani Kamar yadda kukayi Sanadiyar Barin Dan"uwanki Cikin Ahalinsa yabar komai nashi yayi Nesa Damu saboda yadda kukayi ta Tafiyar dashi..!
Ta karishe fada Tana kara Goge kwallarta da Haban Hijabinta Kowa afalon ya kasa Motsi saboda Shesshekan kukan Daada,Baffa Kabiru da tunda aka fara mgana bai ce komai ba sai alokacin ya gyara Zama yana kallon Daddy Lokaci Daya ya maida Hankalinsa wajen Daada yana Fadin"Haba Daada wannan wani irin mgana ce ya zaki dora mana Alhakin baarin Malami gida..? Wannan ai ba mgama bace ya bar gida ba saboda komai bane sai baya son a Fadamai gaskiya sannan ya Biyema Mganar ya"yansa Har ya iya Tafiya har yau bai nemi kowa ba..Daada ki Dora duka Laifin akan karansa shi da ya"yansa ba akanmu ba..!
Mami Asma"u dake gefe tace"Nima abunda Zan ce kenan Baban Sajida What all d Bleming akan ku kuma..? Wanda ya tafi batare dayayi Shawara da kowa ba..Shi ya kamata a Dora ma Duka Laifin ai Daada..!
Inna mainunatu ta Kalleta Tana Fadin"Sam bai kamata ba abunda kuma kikayi ba Daidai bane..Bai dace Manya na mgana ba kina saka baki ba..Koda kike Matar ya kabir wannan ba Hurumin ki bane mganace ta Tsakaninsu bai kamata ki saka baki ba gaskiya...ko kuwa nayi Laifi Jama"a..?
Tafada tana kallon Daddy kai ya gyada mata kafin yace"baki Laifin komai ba Maimunatu..!
Daada ta Dago daga Sharan kwallar Tana Fadin"Kabiru ka tsawartama Matarka..Kada ta kara sakamin baki in ina mgana da Ya"yana..!
Bai da yadda zai yi Dole ya juya wajen Mami Asma"u data gama cika Da mganganun Inna Maimuna sai Harare Harare take bai mata mgana ba da ido kadai ya Kalleta alamun kada ta kara Mgana sai ta koma tayi Laushi Lokaci Daya Tana kara Rumgume Sajida Dake jikinta Inteesar Dake rumgume da Abiden tayi Tsaki acikin Ranta kafin ta Juyar da kanta Karaf suka Hada ido da Khamis ya Kureta da ido Saurin Kauda kanta tayi acikin Ranta tana Ayyana wannan kodai Maye ne wlh kurwanta kur indai itane.
Daada ta kara Gyara Zama cikin Shakewar murya tacigaba da Fadin"Zakace min kada na Dora alhakin barin Malami gida akanku Kabiru..? Musamman ma kai Domin Mustapha In yana da Laifi Kadan ne na Biye maka da yayi bai fadamaka gaskiya ba. ni kuma har ga Allah bana sanin abubuwan Dake Faruwa wani Lokacin.'
Ran Baffa Kabiru ya baci cikin Fushi ya kalli Daada yana Fadin"Daada Kifa Daina dora alhakin komai akaina ki Dorashi kan Malami Da ya"yansa Musamman yaron nan nashi Kanin Yusuf Mara jin mgana ga shi yana ganin yana Daidai da kowa Tun kafin hakan ta Faru daman baya son Zama Cikin Danginsa Bazan ga Laifi in sun Tattara sun tafi wata uwa Duniya ba..!
Daada cikin tsawa tace"Yimin shuru anan wajen Kabiru kada ka kara cewa Tak..in ba haka ba sai na saba maka..!
Kowa afalon sai da yaji wani iri Baffa Kabiru kuwa kamar ya yi Bindiga haka yake ji saboda Fushi Ita kuma Mami Asma"u Sai cika take itacda yarta Don me Daada Zata Tara Mutane tana cima Mijinta Zarafin Bazata Dauki wannan Rainin ba.
Daman Tun malami nan nan Tasu bata zo Daya ba Tana ganin kamar shi ne yake so ya goga Kafada Daya da Mijinta akomai kuma alokacin Anni itama tana sakawa tana Cirewa Mai Tsada Su Asma"u ma badai ka gansu Cikin wani yanayi ba Daka gansu Zaka Fahimci suma din sun Tara kodaga Kayattacen Gidansu na Lagos Mami Asma"u tasan da Anni Zata goga acikin Dangi,saboda bata kaunar wani ya fita ita da Mijinta da ya"yanta ako"ina ne shiyasa bayan Faruwar abun Take da Zuga Barrister kan meyasa Daada take Wahalar dasu ne kan Nemo wanda basu san ina Ya shiga ba ko alokacin Dayake Ma Abba Fadan ya haukace duk itace ke Kitsamai wai yaki Daukan kaddaransa Tayaya kuma zai zo shi ya Zame musu Lalura Allah ya yita Mace mai son kanta da yawa shi kuma Baffa Kabiru yana Matukar sonta ya gama bata Dukkan Amana.
Daada ce cikin Muryan kuka Tace"In bazasu yi nesa damu ba wani mataki kake so su dauka..?Suma ya"ya ne Tamkar ya"yanku Bazasu taba Jure Zama kana kiran Mahaifinsu da Mahaukaci ba Kabiru alhalin kasan Rayuwace da Rashi ta maida Malami haka da Kaddaran da bawa bai isa ya kaucemata ba..Rashin Rai yayi matarsa Zuwaira da ya"yansa Har guda Uku Kabiru ka Fadamin ko kai ne Wani Hali Zaka tsinci kanka..? Na tabbata yadda kake son matar nan naka da ya"yanka in wani abu irin wannan ya samesu na Tabbata kai kila Sai ka Rataye kanka ma Saboda Tashin Hankali..!
Gabadaya falon sai ya Kaurevda Mganganu kasa kasa na Tuna abunda ya wuce a Shekaru uku da suka gabata Jikin kowa yayi sanyi Mami Asma"u kuwa Kallon Daada Take ta cikin Glass dinta aranta Tana Fadin"Bakin ki ya sari Danyan kashi mai Doyi Daada. !
Take fada Acikin ranta Domin Gani take kamar Daada na yi musu Mugun baki ne..
Daada kuka take harda Shasheka ganin haka yasa Daddy ya Matsa gareta yana Fadin"Don Allah Daada ki bar kuka kina Karyamana Zuciya..Ga Matayen mu ga ya"yanmu harda Jikoki bai kamata ba don Allah ki bar kukan nan ki Share Hawayenki..!
Batayi gaddama ba ta Share Hawayenta Tana jan majina tace"Naji zan Share Hawayena ayanzu..Ammh ku sani har in dai ba Dan"uwanku kuka Dawomin dashi ba bazan Daina Zubar da Hawayaena ina kuka ba..Kuma In har baka gayama Kabiru Cewa Laifinku bane game da Barin Malami gida ba Shima baZai sai na Fasa Fadin kune Sanadin Barinsa Gida Dashi Iyalansa agaban ko waye ba..!
Daddy ya dukar dakai yana Fadin"Gaskiya ne Daada..Ni ban Musa ba Muna da Laifin Tabbas Wajen Ya"yan Ya Malami su Daukesa Daga Cikin mu..!
Da sauri Baffa Kabiru ya Dago yana kallonsa kafin yace"Au kaima ka yarda Laifin mu ne..?
Daddy ya dago yana kallon Baffa Kabiru yace"Gaskiya ce Dole a Fadeta Baban Sajida..Na Dade ina son na Gayamaka wannan gaskiya..Alokacin da abun ya faru ba haka ya kamata mu Tafiyar da Ya Malami ba..Yana Bukatar Lallashi da jansa ajiki da kuma Nunamai Soyayyah,alokacin bai Bukatar fada ko Hayaniya domin amasu irin Laluransu Fada yana kara Karfin Tasirin Cutar acikin jikin mutum sai ya rika ganin kamar shi kadai ne,Tabbas alokacin muna da kaso mafi yawa Tunda bamu Jasa ajiki ba bamu nunamai kulawa ba sai ma Kokarin numamai ko ta Halin kakane sai ya koma yadda yake afarko kuma abun ba haka yake ba ita Cuta ce take Shiga Farat Daya Waraka sai a Hankali kuma bamu yi la"akari da Raunin Daada ba da ya"yansa kansu da suma Raunin ya Tabasu ba..bayan haka suka nemi komawa Lagos ka Amince musu bakayi Tunanin Tayaya Zasu iya wannan Rayuwar su kadai ba bayan Tafiyarsu Kaje har Gidan ka Samesu cikin Wani hali bakayi wani yunkuri domin Dawo da Rayuwarsu Daidai ba ka taho ka barsu bayan wani Lokaci aka nemesu aka Rasa tayaya bazamu dora alhakin Faruwar hakan a wuyan mu ba..? Daada uwa take garemu Hakkinta na kanmu ya Zama Dole mu yi abunda zamu yi mu Daina Sakata kuka..!
Gabadaya kalamansa ya Kashema kowa Jiki shi kanshi,Baffa Kabiru ya kasa Cewa komai Domin yasan gaskiya aka fada.
Daada kuwa Mirmishin ta saki irin na Manya kafin tace"Irin wannan Ranar nake jira....yau in ku bazaku iya ba Zan Raba aikin harda ya"yanku wasu ku nan kusan Baffan ku Malami shi yake Bima Kabiru bayan Hatsarin Jirgi ya Rutsa da iyalansa abubuwa sun Faru marasa Dadi har yayi Sanadiyar barin sa Gida shi da ya"yansa guda uku wadanda basu san sa ba Yanzu Asabe zata Dauko Hotonsu ku karba Daya bayan Daya ku duba wanda Allah yasa yayi katarin Ganin Daya Daga Cikin su Sai ya sanar damu..!
Asabe Shiga Dakina cikin Sip ki Daukomin Hoton nan..!
Ta Karishe fada ta Kallon Asabe Dake gefe da Sauri ta Mike tana Fadin"To Daada..!







*Shakira..*
3/22/22, 23:06 - Ummi Tandama???i: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:JanaftyB??0
{*


}? }? }? }?}? *??T??26*

Ba bata Lokaci sai ga Baba Asabe da Wani Hoto a hannunta an yi Elagement dinsa ta mika ma Daada,ta karba Lokaci Daya tana Kallon Hoton Cikin Raunin zuciya sai ga Hawaye Sharr sun Zubo mata hannun da Casbaha ke hannunta ta sanya tana Shafa Hoton Tana Fadin"Allah sarki Rayuwa...Zuwan da Zuwaira tayi na Karshe ne da bata kara zuwa ba Allah yayi mata rasuwa,bayan wata Karamar Sallar azumi ta kawomin wannan Hoton tace Daaada saboda ke na saka aka wanke shi aka Gyara miki shi Gamu nan dukkanmu Harda Marajin jikan ki an samu Dakyar ya Shiga Hoton watarana in kinyi kewar ganinmu sai ki Dauko ki Duba..!
Tabbas ta fadi gaskiya ashe Watarana Zan yi kewa kewa kuwa ta har Abada..!
Daada ta Karishe fada cikin karyewan Murya kafin tace"ALLAH yajikan ki Zuwaira ya Kyautata makwancinki..Ya"yanki da kuka Amsa kiran Mahallicinku atare suma Allah ya Karbi Shahadarsu Allah ya Hadamu a aljannah Firdausi..!
Gabadaya Falon aka amsa da Ameen Jikin kowa yayi sanyi kamar yau ce akayi wannan Babban Rashin Inna Maimuna sai sharan kwallah take Saboda Tana ganin kamar yau ne komai ya faru.
Share Hawaye Daada tayi kafin ta Mikama Baffa Kabiru Hoton tana Fadin"Ku bama Matan ku da ya"yanku su gani..!
Daga haka bata kara mgana ba ta Cigaba da Jan Cashabanta Cikin Rauni da Rashin Lafiyar Jikin Tsufa.
Bai ma Tsaya kallon Hoton ba ya mikama Daddy ya karba Shine ma ya Tsaya yana kallon Hoton,Malami ya Kurama ido yana kallonsa sai yaji wata Kwallar ta tarumai a kwarmin Idanuwansa Dukkansu ne da Sallah ne suka Dauki Hoton da Ya"yan da Uban Duka Farar shadda suka saka da Hula Anni kuma dasu Asma"u suna Sanye da wani Leshi mai kyau iri Daya sai Auta Munari Dake sanye da Shadda Fara irin ta su Abba an mata aikin mata Imran ne kadai a Hoton bai saka Shaddan ba,lokacin Ya dawo Daga makaranta Ibadan Ba"a son ranshi ma yayi Hoton ba sai da Anni tace in bai Tsaya ba sai ta Sabamai Shi Sanye yake da Bakin wando da Farar riga mai Kauri Gajeren hannu Gareta,kirar Armani Yadda ya hade rai ya kalli Gefe Fuskarsa ma bata Fito DAkyau ba Zaka Fahimci baiyi niyyar Daukan Hoton nan ba Dole aka sakashi Imran kenan.
Daddy saboda Raunin Dayaji zuciyarsa tayi yasa ya mikama Inna Maimuna Hoton suka Taru ita da ya"yanta suna gani tana Fada musu Sunayensu Sai da tazo kan Imran ne ta Dago Tana kallon Daddy Lokaci Daya Tana Nunamai shi Tace"Ya Mustapha wannan banganeshi ba. ? Me sunansa na kusa da Yusuf..!?
Kafin ya bata Amsa Daada Dake ZAune tace"IMRAN kenan Miskili kafin mahaukaci ban Haushi..!
Gaban inteesar sai da ya Fadi Dataji an ambaci sunan Imran haka take Fama da Faduwar gaba Tunda ta Dawo ko sunansa ta Tuna sai gabanta ya Fadi ballatana ta Tunashi ta rasa Dalilin haka..
Haka Hoton ya Dinga Zagaya Falon Daya bayan Daya,Inna Maimunace take nuna Wadanda suka Rasu da wadanda aka nema aka Rasa Daidai Lokacin da Hoton yazo hannun su Anty Hauwa ita kuma Inteesar tatashi Zuwa Cikin Dakin da Anty Hauwa ta Sauka ta Dauko Madaran Abiden Dake Cikin Fidarsa yana Hannunta sai ya Fara Kuka Umma tace taje ta Dauko to Dataje sai ta zauna achan ta Hadamai ta Bashi yasha koda ta Dawo Hoton ya bar Hannunsu yana Hannun Mami Asma"u wacce ta mikama Umaima ita kuma ta mikama Sajida wacce ta Dade Tana kallon Hoton Imran Take kallo duk da ba sosai Fuskarsa ta Fito ba sai da akallo Daya zakamai ka Fahimci yana da wasu abubuwan da bakowani Namiji ke dashi ba ta Shagala da kallon Hoton har sai da Khamis ya taso da kansa ya karba ya Koma Wajen zamansa suna Kallo su da su Sa"id dasu Ya basheer suna kara Jimanin Mutuwar su Anni da su Asma"u Allah Sarki da yau sunan nan anan Wajen da duk abunda ya Faru bai Faru ba.
Duk da Inteesar taso ganin Hoton ammh Ganinsa Hannun K???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?hamis yasa bata ma ce Zata gani ba,Da Umma ta TAmbayeta ko ta gani sai tace Eh tagani Saboda bataso ace taje ta karbo hannun wannan mai Mayen Kallo.
Bayan kowa ya gama ganin Hoton aka Maida ma Daada abunta ta karba Ta ijiye gefenta irin su Sa"id dasu Ya Basheer harda Snaping din Hoton a Wayarsu.
Daada tayi gyaran Murya Tana Fadin"Ina Fatan kowa ya ga Hoton nan ko..?
Gabadaya aka jinjinamata kai kafin ta Cigaba da Fadin"Ina neman Taimakon ku..Ba Taimakon Dai dai kun ba..kowa Dake wannan wajen ban Dauke mai ba Mazan ku da matanku ina ji ajikina Malami bai yi Nisa sosai ba yana nan kusa Damu don Allah ku saka Ido ku nuna ma abokan aikin ku Da Wadanda kuke mu"amala dasu ko Kila wasu daga cikin su sun Taba ganin Daya Daga cikinsu,na tabbata baza"a rasa wanda wata Mu"amala ya Taba Hadasu dasu ba koda Bayan barin su gida ne..!
Gabadaya aka amsa mata da Insha Allahu Sa"id ne ya Daga hannu yana Fadin"Daada in kin bani Dama Ina so zan yi mgana. !
Daada ta gyadamai kai Tana Fadin"An baka Dama Sa"idu!
Mikewa yayi Lokaci Daya yana gyara Zaman Rigar jikinsa Data Tattare saboda Zama yana Fadin.
"Assalamu alaikum da farko dai Kamar yadda wasu suka sani ni Sunana Sa"id Sulaiman ni D"a nake wajen Inna Maimunatu da Farko wani dan Shawara zan kawo mana game da Riko da Zumuncin da Daada Tayi mgama..Gaskiyan mgana akwai gyara a Tafiyar nan tamu kamar yadda Mommy ta kawo mgana ne kan cewa Dukkanmu bamu yi nisan da zamu ki Ziyartar gidajen yan"uwanmu da iyayenmu ba,Sannan da yawanmu anan Wajen bamu san juna ba Akwai Kadan da na sani ammh da yawa wasu duk ban sansu ba sai dai kawai kasan kana da wan Mahaifiya yana da Mata yana da y"ya ammh kuma bakasan matar ba bakasan ya"yan ba kuma sunan an Fito Daga Tsatso Daya,Shine na yanke wani Tunani me Zai hana Tunda nasan kowa acikin mu Daga mu yaran Har iyayan namu muna da wayar Zamanin nan Data Zama ruwan Dare ko bamu Samu takawa munyi Zumunci ba ta kafa ba akallah kowa nada Lambar kowa bayan kowani kwana Biyu Zamu rika Kiran juna awaya muna Sanin Lafiyar junamu da kuma Sanin in wani abu ya Faru..sannan abu na gaba Zan Bude mana Group a manhajar nan ta Zamani Wato WhatApps Da sunan IYALIN MARIGAYI ALKALI DUKKU Zan karbi lambar kowa zamu yi adding dinsa acikin wannan Group Kama Daga mu har iyayanmu Inda Zamu Rika Sada Zumunci a Tsakanimu in wani abun karuwa ya samemu za"a sanar Domin mu Taya wanda abun ya sama Murna in Rashi ne ma kowa zai sani Tunda duka ana Chure waje Daya sannan in ma wane bai sani ba Wane ya sani zai sanar dashi..Mganata ta Karshe shine ya kamata bayan kowani Wata Biyu a samu Ranakun karshen Sati a Dunga Haduwa ana Tattauna wasu Batutuwan da suka Shafemu ta hakane Zamu san mtsalolin junanmu sannan Shakuwa mai Karfi Zata Shiga Tsakaninmu kuma hakan zai Sanyayama Daada rai Baza tayi Fargaban ko Bayan Ranta Rabuwar kai ZAta Shigo wannan gidan ba Daga karshe ina mai Sanar da Daada ta Kwantar da Hankalinta tunda ta Shigo Damu Cikin wannan Al"amarin sai inda Karfinmu ya Kare Indai Kawu Malami na Cikin kasar nan zamu nemosa Duk inda yake mu Dawo miki Dashi Gida shida iyalansa da yardan Allah..Wssalam..!
Ya karishe Fada yana komawa ya Zauna ba Daada kadai ba Kowa Dake Wajen yaji Dadin kalamansa kuma yayi Na"am dasu Daada na Mirmishi tace"Mustapah da Kabiru kunji Abunda D"anku yace ko..?kune Manya ku Zartar da Abunda ya kamata Duk abunda yace yayi Daidai yayi tunani mai kyau kuma naji Dadi..Allahu yayi muku albarka Gabadayanku daku da ya"yanku da Zuru"arku gabadaya Allah yasa yadda muka Hadu ayau anan Wajen haduwa ta gaba ace Ga Dan"uwanku agefeDaya Allah ya Bayyanasu Allah yasa suna Cikin Koshin Lafiya kamar yadda nake Fata..!
Gabadaya aka amsa mata da Ameen Jin an Fara kiran Sallar La"asar kana Daada tace"Kowa ya tashi yaje yayi Sallah..Daman Dalilin kiram nawa kenan ko ba Domin haka ba ina Bukatar ganin Ya"yana da Jikokina a kusa Dani yau gashi na ganku naji Dadi kwarai Allah ya maida ku Gidajenku Lafiya bazan zaunar daku ba Saboda akwai masu Ayyuka da yara Masu Karatu zuwa Gobe na Sallami kowa zaku iya Komawa Gidajenku Allah yayi albarka...!
Aka Shiga amsa mata da Ameen ta Mike Bayan Daddy ya Mike ya Taimakamata ta Kalleshi Shi da Baffa Kabiru Daya Mike Tsaye yana Duba agogon FAtan Dake hannunsa yana auna Lokaci ne in zai isheshi yau din Zasu juya abuja Daada ta gama batamai rai bayason ma ya kara Kwana agarin yaji tace"Mustapha kai da Kabiru in kun Idar da Sallah kuzo ina Neman ku..Asabe In kin idar da Sallah ayi Haraman Dora abinci mun cinye Lokaci anan wajen..!
Daga haka ta Juya tana Tafiya a Hankali Zuwa Cikin Dakinta Daddy ya Kalli Baffa Kabiru kafin su kada kai su Fice Baba Asabe kuwa Tuni ta amsa ta Shiga Dakinta Domin ta gabatar da Sallah Mazan ma sun bi iyayansu Waje Matan kuma Kowa ya kama Inda ya Sauka.
Bayan sun idar da Sallar ne Umma Tace Inteesar da Hafsah suje Kitchen su kamama Baba Asabe aiki Inna Maimatu harda karima da Zainabu tace suje suyi aikin gabadaya,Haka kuwa suka shiga Kitchen suka Zage suna Taya Baba Asabe aiki suna Hira Duk Rashin Sakin jikin Inteesar ta Fahimci ya"yan inna Maimunatu Dabam suke suna da matukar Kirki Shiyasa ta dan Saki jiki da su suna ta Hira Ita Karimam a Bauchi Take aure ita kuma Zainab tana auran Dan Wazirin Azare ne achan take da Zama duk adan Hiran da sukeyi ne ta ji hakan Daganan suka gangaro Hirar Inna Bintalo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login