Showing 201001 words to 204000 words out of 236322 words

Chapter 68 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

760

Gwara ya Rika mata jan ido kada ta Rainasa Daman ta Fara Rainansa.
Agurguje tayo alwala ta Fito Hijabinta ta Sanya Dake kan gado kafarta ya gani a waje yasa yace"Ke ahaka zaki Sallar..?
Kallon kanta Tayi kafin tace"Rigar fa Doguwa ce Ya Imu..!
Tafada Cikin Shagwaba Dauke kai yayi yana Fadin"U are not Serious..Oya Dauko Wani Zani ki Rufe wannan Siraran Kafafuwan naki kafin Ranki ya baci..!
Yafada Cikin Kaushinsa Kamar ko yaushe kallonsa Tayi sai ta kama kanta Kada tasha mari ganin ya koma mata Imu dinsa Sak.
Wardrope din Dakin Ta Bude ta Dauki Zanin Wani less dinta ta saka tazo Ta Bisa suka yi Sallar suna Idarwa ya Mike da Hanzari yana wani cin mgani ya Fice yana Cemata"Make sure kin Shirya da wuri..Bana son Jira..In kika batamin Lokacin kin san Sauran..Ni ba irin Ya Yusuf bane yana Jiranku kamar wani Direbanku..!
Ai Tana jin haka ta Mike ta Fada Tiolet Tayo wanka Sai da ta Fito ta Duba agogon Wayarta da Munari ta bata Jiya da Zasu tafi 7 ma Tayi a Gaggauce ta Shirya Cikinta ke kugin Yunwa Daman Tun Fara Shagalin nan bata wani ci abincin Kirki ba.
Riga da Sikat ta saka na atamfa Cikin Kayanta ne na Gida da Munari ta Hado mata,Kayan sun kamata sun mata Das.
falo ta Fito sai alokacin ta Samu Damar karema Gidan kallo Tana kara Jinjina ma Baffa Kabiru yayi kokari Sosai Kitchen ta Fada Domin samo musu abunda zasu karya Tayi mamakin ganin Harda Cefene sai dai ba Lokacin da Zata Sarrafa wani abu Gas ta kunna ta samu karamar Tukunya ta Dora Ruwan Zafi Tana kara Duba Kitchen din Tana Godema Umma da Daddy dinta da Kokarinsu akanta.
Ta Duba Taga Harda da kayan Tea,Mirmishi Tayi Munari ta Fadamata aikin Ya Yusuf ne ai kuwa yayi Taimako don inta Ya Imu ne yau da yunwa zasu Fita.
Ruwan Zafi ta Juye acikin Flaks ta Dauko Mug din Kofuna Guda Biyu ta Wanke ta Zubo Ruwan Zafi ta Kwaso kayan Tea din zuwa Falo Saman Dan Madaidaicin Dining din Dake yamma da Falon
Komawa Tayi ta Bude Store ta samu Karamin Filte ta Dibo Snak din da Umma ta saka akayi mata su Donot su Cincin su Cake da sauransu ta debo su kadan bada yawa ba Tana Fitowa Imran na Fitowa Daga Dakinsa Lokaci Daya yana gyara Zaman Net Tie din Dake Wuyansa Shigar Suit Green yayi yau Dayan Hannunsa na Dauke da Jakar Briefcase dinsa da Key din Motarsa.
Ido suka Hada Dashi Shagala Tayi da kallonsa Shi kuma bai bari ta gane Kallinta na kayatar dashi ba Sai ya Kauda kai Daidai Lokacin Data kariso gaban Dining din Tana Fadin"Gud Mrning..!
Yana Duba agogon Radon Dake Hannunsa yace"Mrning..Kin gama Shiryawa..?
Kai ta gyada Tana Fadin"Yes..Ammh ga Tea bazamu sha kafin mu Fita ba..?
Yamutsa Fuska yayi kafin yace wani abu da Sauri Tace"Nidai plz ka bari nasha Kada naje Exams ina Zare idon Yunwa..!
Dariya taso kamasa sai ya Dake ganin yadda Tayi mgana kai ya gyada mata yana Fadin"Ok.5Mn..!
Da Sauri Taja Kujeran ta Zauna Tana Fadin"Bazan ma kai ba..Ya Imu kazo sha faa ba wani abu bane mai Nauyi ba..!
Bazai iya mata gaddama ba yasa ya ijiye kayan Hannunta ya Isa Kusa da ita ita tajamai kujeran Dining din ya Zauna Ta Turamai Mug din gabansa da Flaks Zata Zubamai ya Dakatar da ita yana Fadin"Barshi sha..Kada ki batamin Lokaci..!
Yar Dariya Tayi ta sakarmai ya Tsiyaya Kadan ya Zuba Madara da Bonvita da Siga kadan ya Fara kurba Filet din gabanta ta Turamai Tana Fadin"Madadin Bread..!
Kallonsa yayi kafin ya Dgo yana Fadin"what is dis..?
Inteesar ta waro ido Tana Fadin"Baka sansu ba..?tab ka bar Dadi..Ci wannan kaji..!
Ta Dauko Cake ta Mikamai Bazai iya Ture Mganar Inteesar ba yasa ya Karba ya Gutsira Da Sauri Tace"Ya kaji..?Cake ne ana shansa da Tea..!
Bai ce mata komai ba,sai da yakara Cake din Guda Biyu ya Hada da Tea din kadan ya Mike Duk Saurin Inteesar yana kallonta Tana Turawa cikin Bakin ganin ya Mike Dariya Ta basa yasa yace"Kici a Hankali kada ki tura da yawa kije kina Amai kuma..Ba Ruwana..!
Yafada yana Wucewa Jakarsa ya Dauka yana Fadin"ki Tafi dashi ma in kin Fito Exams din sai kici..!
Mikewa Tayi Tana Fadin"Am ok..Bari na Dauko mayafina da Jaka da wayata..!
Bai mata mgana ba ta kwashi Gudu Zuwa Cikin Daki da kallo ya Bita Kafin ya Girgiza kai Bata Dade ba sai gata ta Fito da bakin Mayafi da bakar Jakar sai Takalminta mai Tudu Duk Cikin kayanta na Gida ne.
Kallon Sama da kasa yayi mata Lokacin Data Tsaya agabansa Tana Fadin"Am Ready..!
Hararanta yayi Ransa na Bacin yadda Zataje Cikin maza da Gyale kuma Sikat din ya kamata Cikin Dakewarsa yace"ba hijabi ne sai wannan Mayafin..?
Inteesar tace"Wlh babu..Duka suna Kaduna Guda biyu ne kuma suna Cikin kayama na gidan mama Duka Goggo Maimunatu Gyale ta sakamin..!
Tafada Cikin Muryan Shagwabar da ya Zame mata jiki.
Karamin Tsaki yaja Kafin yace"Sako sa saman kanki..Da kika saka sa a Kafada kin manta ke da da yanzu ba Daya bane..?
Yafada yana Sakarmata ido Zatayi mgana yace"Bana son gaddama Do as I say..!
Bata da yadda Zatayi ta Warware ta Saka saman kai Allah yasa Babba ne,Makullaye ya mika mata ta saka Hannu ta karba ya Fice yana Fadin"Key din duka Doors din Gidanan ne.in kin dawo ki Rika amfani Dashi Wajen Bude get din zuwa Kofar Cikin Falo..!
Da Toh ta Bisa kafin ta Bi bayansa Shi ya Rufe Kofar Falon Tana gani kana suka Taka,wajen Mota ita yace ta shiga Shi kuma ya isa ya Bude Get din Kana yazo ya shiga Motar sai da ya Fito kana ya kara Fitowa Daga Motan ya Kulle Get din da makullin Dake Hannunsa Tunda guda Biyu ne Daya ya bata ne a Hannunta Saboda ba Lokaci Daya Zasu Dinga Dawowa ba.
Sun Fara Tafiya ya Dauki Hanyar Buk Ba wanda ya kara mgana Wayarta Tana Cikin Jaka Munari nata Kiranta bataji ba suna gabda isa ya kalleta yana Fadin"Ina za"a samu Hijabai..?
Yafada Lokaci Daya Hankalinsa na Wajen Tuki Inteesar kai Tsaye tace"Kasuwa mana..!
Acikin Ransa ya maimata kasuwa Tabdijam to ina ma yasan kasuwan..?
Ganin bai kara cemata komai ba yasa itama bata kara mgana ba har suka Shigo Cikin makaranta Har Kofar Department dinsu ya kawota Ta kallesa Tana Fadin"Daman kasan Department din mu Ya Imu..?
Bai kalleta ba yace"kina so na makara ne..!
Da Sauri ta Bude Motar tana Fadin"Allah ya Kiyaye ya bada Sa"a..!
A saman lebe ya amsa da Ameen yana Fadin"Good luck..!
Ta Kada mai kai Har zata Rufomai Motar ta Tuna da Sauri ta Dawo Ta Zauna Tana Fadin"Ya Imu plz in mun gama Exam din yau nabi Munari naje Gidan Abba..?kaga duk yau baki zasu koma muyi sallama..!
Kallonta yake yi kawai bai ce komai ba Ganin haka yasa ta marairaice Tana Fadin"Plz Ya imu don"t say No..Please..!
Tafada Cikin Shagwabarta Baisan Sadda yace"Ok..!
Da Sauri ta Yada kanta Saman kafadansa Cikin Murna Tana Fadin"Tanque..So much..In ka Tashi Daga Wajen aiki sai ka Biyo mu koma Gidanmu ko..!
Kamar wani Gaula haka ya gyada mata kai Hannunsa Guda Dayan Dake saman Cinyarsa ta kama ta Sumbata Tana Fadin"Ya Imu na..See u later..!
Tafada Lokaci Daya tana Ficewa Daga Motar ta Rufemai ta Dago Tana Dagamai Hannu Baki Sake yake kallonta Gabadaya ta gama Sakamai kasala Dakyar ya Daga mata Hannu Lokaci Daya ya Tada Motar yayi kwana ya Fice Daga Wajen.
Sai da ya Dauki Hanyar Bankinsu ne ya Tuna bai bata kudin Mota ba..?kansa ya shafa yana Fadin"Su Imran miji manya..?miji ya bar Matarsa ba kudin Mota..!
Yafada yana Dariya to me ya sani na Daukan Nauyi shifa Nauyinsa kansa ba Duka yake Dauka ba Har yakai Cikon Bankinsu yana Dariyan kansa .
Intee kuma Tana waigen Neman Munari bata ganta ba ta karisa Cikin Department dinsu ta Fara gaisawa da Course mate dinsu Da suke ta mata Fatan Alheri Wayarta Take Kokarin Cirowa taji an Riketa ta baya tana Juyawa Taga Munari suka Saka Ihu atare suka Rumgume juna.
Kafin Munari taja Hannunta su samu Waje su zauna Tunda da Sauran Lokaci..
Nan fa Hira ta Tsinke Munari sai Tsiya Take mata tana kallonta Tana Fadin"Uhm..Amarsu ta angonta..ai na ganku..Aure mai Daraja wai yau Ya Imu ne da kawoki makaranta..!
Duka Inteesar ta Dagaamata suna Dariya Munari na Cemata ta Kira wayarta tace bata gani ba yana Jaka Munari sai Faman kallon Inteesar Take Tana Dariya Lokaci Daya Tace"Allah kadai yasan irin Romin amarcin da Ya Imu ya kwasa yau ya kawoki makaranta..Muma mun kusa shiga wannan karnin domin Khalil yace yana komawa zai gabatar da mganarmu..!
Inteesar na Dariya tace"Munari ana son Aure..Wai daman yace yana sonki ne..?kun dace fa..!
Tafada Bayan ta boyema Munari Wani abu bai Faru Tsakaninta da Imu ba.
Munari tace"lalle Tun yaushe...Sagir ma ya kafa Gwannatinsa Wajen Hafsah..!
Inteesar ta Zaro ido Tana Fadin"Ki bari don Allah..!
Munari tace"Ki zauna mima mun kusa Shiga Daga Ciki yarinya..!
Dariya suka saka Inteesar ta nuna jin Dadinta sosai aman take Fadama Munari in sun gama jarabawar yau Tare zasu tafi gida ya Imu ya barta Munari tace aiko kin ji Dadi kya yi Sallama da yan"uwa.
Tsaida Hiran sukayi Suka Fara Bitan Jarabawar da zasu yau duk da basu da Mtsala suna Karatin Jarabawa tun Lokacinta batayi ba Karfe 8am na Safe Daidai suka Shiga Paper 1 sai 11am suka Fito basu Zauna wani hira ba suka koma Wacce zasu shiga karfe 12am na Rana Har zuwa Lokacin.
Karfe 2pm na Rana suka Fito Shikenan sai kuma Gobe Suke da Guda Daya Daganan Inteesar da Munari suka samu adaidaita zuwa Gidan Inteesar sai Murna take kamar Wacce ta Shekara Kamar ba Jiya bane,Tabar gidan.
Koda suka isa Ya Basheer da Anty Hauwa da Anty Uwani da Maman Nasara da ita kanta Nasara sun kusa isa kaduna Harda Umaima Data Bisu Zata kwana anan Kaduna Ya Basheer zai siyan mata Tiket Tabi Jirgin kasa zuwa Abuja.
Inteesar bataji Dadi ba Domin ai tasan Daman bazai Tsaya ba Ya Basheer baya son Tafiyar Dare,Inna Maimunatu ma Ta mika Hanya ita dasu Zainab,Inna Bintalo ma ta wuce ita sai ta Biya wajen Daada Dukku.
Sa"id ne kadai ya Rage basu Tafi ba sai Sadam su yan Gida ne.
Kowa mamaki Dayaga Inteesar Munari ce ke azarbabin cewa Ya Imu yace ta Biyo ta nan in ya baro Wajen aiki zai Biyo ya Dauketa Shiyasa Abba yayi Shuru
Sai Gabda La"asar su Sa"id suka Tafi da Hafsah bayan sun gama Sallama da su Munari da suka Hada kai suna ta ma Inteesar Tsiya Harda Tasleem da itana Sallar La"asar kadai sukayi Ita tatafi Gida,Bayan La"asar kuma Ya Sadam da Tawagar Matarsa da ya"yansa suka Wuce gida,Gida ya Rage Daga Anty Safiya sai Abba Dashi ma bai jima da dawowa Daga Office ba.
Ya Yusuf bai je aiki ba Ranar yana Gida Sai da suka ci Abinci suka koshi kana Inteesar ta Tambayi Abba zuwa Gidan Mama ta kwaso sauran kayanta ya barta Munari ta Rakata Mama Taji Dadi Itama Gajiyan Biki bai Saketa ba Ta kara yima Inteesar Nasiha sosai kafin ta Dauki Sauran kayanta Saura kuma Tace Mama ta bada su kawai basu wani jima ba Saboda Abba yace Kada su zauna suka Dawo gida.
Gyaran Gidan suka Taya Anty Safiya Kafin su Shiga Kitchen suka Dora Girki,Farar shinkafa da Miya Sukayi da Nama Sai mangariba suka gama bayan sun Jera komai Saman Dining kowa yaje yin Sallah kafin su Fito su Abba suka shigo Harda Imran Daya Dawo da Sagir a masallaci suka Hadu Nishadi yake ji kamar ya Shekara baya Gidan..
Ranar Gabadaya suka Hadu Saman Dining Harda Imran da Sagir sukaci Abinci Cikin Farinciki,Bayan sun gama Abba bai yi kasa a gwiwa ba ga kara Yi Musu Nasiha sosai mai Shiga Jiki basu sukabar Gidan ba sai Wajen 9pm bayan Hankaluna sun kwanta Baki sun koma Gidajensu Lafiya..
Suna komawa Gida sun gaji sai Barci Kowa ya Nemi makwancinsa.

*******
*After 10 days*

Haka Rayuwar Auran Imu da Inteesar ya Cigaba da Gudana Kullum da Safe in Tare zasu fita Zata Dafa musu Ruwan Zafi su sha Tea kafin su Fita in kuma Batare zasu fita bata da Jarabawa da Safe shi kadai yake Fita Inteesar na kwance ma sai ya tasheta Wani Lokacin Har Yau da suke kwana Goma da aure Inteesar bata Fara Girki ba sai dai Tasha Tea taci kayan Snak,in Tana Gida domin in Ta shiga makaranta Munari take bi zuwa Gidan Chan take Wuni sai yammah Tayi in Imran ya Dawo shima nan yake Sauka sai Dare suke Dawowa Gida da sun Dawo sai barci kuma Har alokacin kowa Dakinsa yake kwana babu abunda ya Sauya.
In basu Fita tare ba Yana bar mata Kudi in Lokaci yayi sai ta Kulle Gidan ta Fita ta Hau adaidaita da Farko Har Biyama Munari Take yi Abba ya Hana yace Kada ya kara gani Imran bai ma Sani ba yana Wajem aikinsa.
Shi cin Abinci bai Damesa ba Barsa da Shan Tea da kayan Marmari Abinci sai yaga Dama yake ci shiyasa har yau bai Damu da rashin Fara Girkin Inteesar baisama san wai Ta Fara Girkin ba Ballatana yayi mata mgana Shi yana ganin akwai komai in Tana jin yunwa tasan yadda Zatayi Shiyasa bai Taba Damuwa da Rashin Fara Girkinta ba.
Kuma ba wanda ya kawo musu Ziyara ballatana yaga aikin da suke yi Daga Imran din Har Intee sai addu"a bamai Sauke Hakkin Dake kansa.
Ita bata komai sai Kwanciya in bataje makaranta sai Ciye ciye kayan snka da Shan Tea sai Tayi karatu in Tagaji Ta Danna Waya kayan kallonsu ba a Hada ba gogan Kallo bai Damesa ba...shidai barsa in ya Dawo aiki Tayi mai Sannu da zuwa ya amsa ya Shiga yayi wanka ya Sauya kaya zai Fito Falo ya zauna yana aiki Bisa Laptop aiki Dayasa yake sa ka Inteesar Wanke kayan Marmarin Dayakan Shigo dasu ta sakomai afilet da Fork karama yana aiki yana cin abunsa Hankalinsa kwance ita kuma Tana Gefe Tana Danna Waya tana Hadawa da Ciye Ciyenta ko ajikinta In Tagaji Tamai Sallama Ta Kwashi littafanta Zuwa Ciki,ko kuma Tayi waya dasu Umma wannan Kullum ta Dinga Kira kenan tana Musu Shagwaban sun ki zuwa ita da Daddy Umma tace Gotai Gotai da ita agidan yarta Daddy kuma yace Intees tasha Kuruminta in zai zo Tare zasu zo,Umma fa har hana Daddy take kiran Inteeear ammh shi ba Ruwansa Wani Lokacin suna Waje Daya da Imran in yace ina Mijinki sai ta mikamai su gaisa da Daddy Har su Taba Hira Umma sai dai ta Rike baki Tana kallon Wannan aikin.
Shidai Imran tunda dai Inteesar bata Rainasa ba Alhamdullilah..Kowa yayi abunda yaga Dama ba Takura.
Shiyasa bai Taba kallon hakan da sunan Wani abu ba yana ganin hakan Shine Daidai.
Inteesar bata Taba Zaton Imran bai daina shan Taba ba,Sai ranar Dataga yana shanta bayan ya Dawo yana Zaune yana aiki Bisa laptop dinsa Shi yama manta da ita Kakarinta yaji kawai ya Juyo yana kallonta yaga Tana Toshe Hanci Gira ya Dage mata yana Fadin"Ke nama manta Dake fa..a falon nan..Bari na bari sai na koma Ciki na kunna..,!
Yafada yana Kasheta saman Farantin Daya gama shan kayan Marmari..
Inteesar tace"nifa na Dauka ka Daina sha Kwatakwata Har ina Celerabration..!
Imran sai da yayi Dariya kafin yace"Su Celebration Manya.Haka Sagir yace min jiya daya ga ina sha..Daman ai bamu yi Dake Zan Daina Shafa ba Kuma ita shanta ai Lokaci ne kuma yanzu Lokacina Duka na gwannati ne Kalilan ne nawa..
Bata Fuska Tayi bata samu Damar Mgana ba ya Katseta da Fadin"Na Rage sha sosai..Fiye da baya..Kuma in kinsan kina jin Amai u better go to ur Room..Allah in ki kayi min amai anan Wajen kinsan Sauran..!
Tura baki Tayi batayi mgana ba Shi kuma sai ya kauda kai yana Danne Dariyansa yarinyar nan in ya biyemata Tabaranta Zata Rika yimai kala kala.
Ranar da suka Cika Sati Biyu da Tarewa Baffa Kabiru yazo Kano, Saboda Imran da Inteesar bai Kwana ba Aranar ya Juya bayan ya Taka har Gidan ya Cikasu da Tarin Nasihu da Fatan Alheri Imran bai Taba jin Nadamar abun???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?da ya aikata ba Sai Ranar yaji kunya Baffa Kabiru Rana ta Farko ta kamasa anya ya Chanchanci Wannan Kyautatawar ga Baffa Kabiru..?shida ya Sakarmai ya..?
Bai Rikeka ba sai m karin kyautatawa Daya Biyo ba Imran yaji kunya saai Dai Ya yi Fuska kamar babu Abunda ya Faru Tare da Abba suka zo suka kara ganin Waje suka saka albarka.
Baffa Kabiru duk ya Rame yayi wani Iri kawai Karfin Hali ke tafe Dashi,Ga Damuwar Dayake Ciki ba Asma"u Tare dshi,Ga Khamis ba"a Samun Wayaarsa kwata kwata Ga Sajida Tana makaranta cikin Damuwa duk da bata Fito ta Fadamai ba shi ya sani wannan Raunin nata bamai Cike mata shi Sai Imran shi kuma ya Riga Yayi mata Nisa har Abada.
Wadandan Damuwan suna Ransa Kawai Karfin Hali ne da Tsabar Jaruma ke tafe Dashi yake kuma Tsaye da Kafafunsa alkawari ya Daukar ma Kansa bazai nemi Asma"u ba sai in itace ta Nemesa ba shima din Sai ya yarda da Nadamarta,ko yace bai azabtu da rashinta ba yayi karya Asma"u ai Soyayyah Ta Hadasu ba Kiyayyah ba kuma basu Taba Samun Irin wannan Babban Mtsalan ba sai wannan karom ya sani kamar yadda yake Cikin Wani Hali itama Tana Cikinsa Har kuma zuwa Lokacin bai ji Daga Justice Tafida ba Daman yasan bazai Nemesa ba Ko shi ya Nemess zai ce abunda suka yanke ma kansu Daidai ne shi bazai ce komai ba Tunda Ra"ayinsa ne.
Daga shi sai Umaima sai yan aiki suke Rayuwa Sajida basu gama Exam ba ammh yace mata da Zarar sun gama Ta dawo gida kada ma Tace Zata Zauna a makaranta ita kuma taso ta Cigaba da Zamanta a makaranta Tana Jinyar kanta ba wanda yasan Halin Datake Ciki.suna Waya da Mami Lokaci Bayan Lokaci itama Hawan ajini Duk ya Fadar da ita Karfin Halinta kawai an fa ta Fara Sarewa an Kwarari Wata na Biyu bataji Daga Kabiru ba ta Fara Saki ta Fara Zama Tana yima kanta Tunanin Ina Mafita.?shin ta ina ta Kuskure..?
Shin Tana da Son kai kamar yadda aka Fada..?tana so ta Fahimci kanta da kanta kafin ta yanke ma kanta Hakunci.
Washegarin Ranar da Baffa Kabiru yazo Ranar Monday Daga makaranta Munari ta matsama Inteesar suka Dawo Gidanta Munari ta yi mamaki Data shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login