Showing 3001 words to 6000 words out of 236322 words

Chapter 2 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

706

da Maimuna ke kallonsa bai waigo ba ya Cigaba da Fadin"Mun rasaa kwarin Zuciyan da zamu karbi kaddaranmu mu Cigaba da Rayuwarmu Tamkar kowa..Tunda Kaddaran nan ta Fadamana muka rasa komai Abba ya Koma haka Imran ka koma yadda kake ni kadai ne nake kokarin Tsayuwa da Kafafuna din ma na gaza Domin Kune kwarin gwiwata da komai nawa Domin ku kadai ne ahalina anan Duniya.."Ya karishe Fada Yana Sharan kwallah

Imran ya Busa Taba mai tsawo Har sai da Hayakin ya Cushemai Zuciya ya Fara Tari da Sauri Yusuf ya Nufeshi yana Fadin"Kagani ko..?kaga irin Sakarcin ka ko..?baka da Lura ne ka rika Zuka a hankali mana Tunda ta zama ibadarka.."Da hannu ya Dakatar da Yusuf kafin ya Bude Manyan idanuwansa da suka kara zama Ja saboda Hayakin Daya taso mai Daga kai ya Nuna kansa yana Fadin"indai Ni IMRAN wanda ABUBAKAR MALAMI ya Diga kwansa ZUWAIRA Ta Haifeshi adoron Duniyanan sai na Aura maka Safiya..Ko Ubanta ya yarda ko bai yardda ba don Uwatai.."Yafada yana kara Nuna kansa da kuma Dukan Kirjinsa kafin ya Take Taban Hannunsa ya Murjeta da kafansa ya wuce yana wani Tafiyar Takama yusuf ya Shiga kwalamai kira yana Fadin"Imu..? Imu me zakayi kada ka kaje ka Karya mata Uba kamar yadda kayi ma Kawun Asmee fa..!
Imran na jinsa Mirmishi kadai yayi a Hankali ya Furta"Ka bani Shawara ya yusuf Tanque.."Yafada Lokaci Daya yana Shigewa Dakinsa Yusuf ya Dafe kansa yana Fadin"Munari meyasa kika gayamai..? Kin fi kowa sanin zai je yayi act din sa Stupit kamar yadda ya saba..!
Marairaicewa Tayi zatayi mgama ya Dakatar da ita da Fadin"Muje mu karya na kai School kin makara.."Da sauri ta Mike tana Fadin"Nayi missing din Lecture din Dr Sa"idu.."
Dinning suka nufa ya zauna Tayi Serving dinsa Tea kadai ya sha da Soyayyan Dankali itama haka basu jima ba suka tashi Daki ya koma ya Dauki key din Mota Ita kuma ta kwashi Littafanta da Jakarta da mayafinta suka Fito Haraban gidan Sun Shiga Motar kenan Yusif zai yi Rivers sai ga Imram ya Fito ya Tsuke Cikin Riga da wando Duka bakake ya saka P.Cap ga wani Bakin katon Gilashi Daya kwafa fuskarnan ba Annuri Kafarsa Sanye Cikin wani Bakin Booth din Takalmi yana ganinsu yayi kamar bai gansu ba,Bakar mashin dinsa Roba roba Dake fake a Haraban gidan ya Hau Lokaci Daya yayi mata Key ya Tada ita yana Zuba Hon Iro megadi Dake Tsaye Daman Tuni ya wangale get din sanin Hali Yanzu sai yasha mari Imran bayason Jira sai da ya Fice Daga gidan kana suka Fita suma suna Tafe Yusuf na Tunanin kada Imran yaje gidansu Safiya yayi musu Haukanshi har ya sauke Munari bai da walwala Daga nan Gida ya Dawo saboda Abba,ammh Gabadaya Zuciyarsa bata Natsu da Fitar Imran ba yasan sa Kaifi Daya ne in yace Zai yi Abu sai yayi shi yaso kiran Safiyan yaji ko yaje..?Sai kuma ya fasa Domin Cin Zarafin Da babanta yayi mai Jiya bai fatan ta sake ma ganinsa Har Abada.



*Ya kukaji salon wannan Mikakkiyar Tafiyar tamu..? Bamu ce komai ba bamu Fara Wannan Tafiyar ba har yanzu..Ku yi Kyakyawan Sharhi bayan kun yaba kun kuma danna min Kararrawar Voting ni kuma nayi alkawarin Sanya ku nishadi da wannan Labarin mai amon Sautin tafiya da Zuciyar mai karatu..*!






*Comments*
*Share*
*Vote*
*10/02/2022*
*Shakira...*
*IWA*
3/22/22, 23:02 - Ummi Tandama???i: *GIDANMU..*!
_(Our House)_
*Book1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:JanaftyB??0
{*

*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*

*??T??2*

"Daga gidansu gangarawa yayi Chan kasan Layinsu bai tsaya ko"ina ba sai Kofar wani Shago mai Dan girma inda aka Rubuta DA KUDI AKE NEMAN KUDI TAILORING CENTER ababban Allon Dake kafe a kofar Shagon.

Yana Tsayawa ya zura hannu Cikin aljihun bakin Wando Dake Jikinsa ya zaro Tabarsa da makunninta ya kunnata ya Busa ya Fesar da Hayaki Cikin Shauki kafin ya Danna Hon din mashin din da karfi kamar Zai fasa ma Mutane Dodon kunni.

Shigowarsa Shagon kenan yana Duba yaransa da kuma Sallahu wasu Dinkuna da zai basu yana da Lacture karfe 10am cikin makaranta zai shiga yana Cikin yima Babban yaransa Auwal mgana sukaji wannan Gigigitaccen hon din Imran ya cika musu kunni Dafe kai yayi Lokaci Daya ya juyo yana kallon Kofar wajen inda suka Hada ido suna kallon Juna.
Karamin Tsaki yaja kafin ya juya yana kallon Auwal yace"Don Allah Auwal kuyi kokari ku gama Kafin Dare..Yau da Daddare Hajiya zata aiko Direbansu ya karba.."Auwal ya gyada kai Daidai lokacin da Imran ya kara Danna Hon din da karfi,kansa ya kara Dafewa Cikin Takaici ya Furta"Ya illahi.."Auwal Dake Dariya yace"Oga sai fa ka Fita..In ba Haka zai cigaba ne kasan Halin yan kayanka.."ya karishe Fada yana Dariya shi da Sauran yaran Shagon wani Daga chan yana kan keke yana Dinki yace"Imran kenan..Abokin Oga ko nace Amini ayi Fada aShirya hukuma sai da Lallashi..!

Yana Jinsu bai yi mgana ba sai dan Mirmishi da yayi ya Taka ya Fice Daga Shagon yana Fitowa ya kallesa yana Fadin"Kai wai meyasa kake hakane..? Ko yaushe kazo waje sai ka bada alamun kazo.."Imran ya kalli Abokinsa SAGIR,ya zuki Tabansa ya Fesar da Hayakin kafin cikin Wata murya mai cike da gadara yace"Da kudi ake neman kudi Abokina..Taken ka kenan.."Karamin Tsaki Sagir Yaja kafin yace"Naji..Ya akayi ne..?Ya jikin Abba..?
Imran ya Sauke Kafarsa Daya Dora Saman karfen Mashin kasa yana Fadin"Lafiya..Hau muje.."Sagir ya wani kallonsa ShekeSheke kafin yace"Na hau muje..? Ina kuma..? Idanuwansa ya sakarmai Kafin ya wana Mashin Din tayi Jinjin cikin Dakiyarsa yace"Malam ka Hau muje nace ko..'?

Yafada Cikin alamun ya Fara Fusata Shima Sagir din Cikin Zafinsa yace"Ni kuma nace na hau muje ina..? Wani Wawan Harara ya Jefeshi Dashi kafin yace"Zan je na kai kanka ne Domin nayi Cininkinsa.."Karamar Dariya Sagir yayi kafin yace"Ina karyanka Wlh..Kaina yafi karfinka.."Wani mirmishin Rainin wayau Imran ya saki kafin yace"Naji..Ka hau Muje kafin Raina ya baci.."Sagir yace"Muje ina wai..?Nifa daga ganni nan Lacture gareni makaranta zan shiga.."Imran yaji kamar ya Kifamai mari Cikin Muryansa mai Cike da Amo da Zati ya kalli Sagir yana Fadin"Zaka hau ko bazaka Hau ba..?
Yafada yana Tsareshi da Jajayen Idanuwansa Sanin Halinsa yasa Sagir din ya Taka ya Hau Bayan Mashin din Dariya Imran yayi kafin yace"Da kada ka hau kagani.."Sagir yace"me zaka iya..?Kai dai Nayi niyar Hawa kawai malam..!
Imran bai yi mgana ya Taka Mashin suka Fara Tafiya Gefe Daya kuma yana Tuki yana Busan Tabansa da Dayan Hannunsa Sagir na Baya yama kasa mgana,ganin yana ta Tsula gudu yana neman kadasu yasa ya Tanka."Kai malam in ka Shirya mutuwa ne ni ban Shirya ba..fakani gefe ka saukeni sai kaje ka Tari Mutuwar kai kadai ba.."

Dariya Imran ya saka kamar ta basawa kafin yace"Meyasa kake Tsoron Mutuwa abokina..? Ka manta Zaka Mutu Dolen ka..'Sagir yace"Nasan zan mutu..Ammh ina Burin kafin na Mutu na ijiye masu min addu"a kai daman bana ta kai Tunda ka Riga ka auri Taba gatanan ma ahannunka baka da mtsala.."Yana jinsa bai yi mai mgana ba ganin sun bar anguwansu yasa Sagir yace"Wai ina zaka kai ni ne..?
Har ya Cire rai da zai yi mgana sai yaji yace"Gidansu Safiya zaka Kaini..!
Sagir yace"Safiya..? Wata Safiyan kuma..? Imran yace"Safiya Buhari alhassan.."Sagir sai da ya Dafa Kafadan Imran saboda Razana Cikin Firgici yace"Budurwan ya yusuf fa kenan..? Yafada yana Bayyana Firgicinsa Dariya Imran yayi kafin yace"Sakeni Matsoraci kada kasa mu Fadi saboda Tsoron ka..!
Sagir yace"Don Allah mu daina wasa me zai kaika gidansu..?ko Ya yusuf ya aike ka..?
Imran ya saki karamin Tsaki yana Fadin"Wazai aika ?Ni Imran..Kana shan kwaya ne..Ni zan aiki kaina malam.."Sagir yace"Me zakaje yi gidansu..? Imran yace"Ka Nuna min Hanyar Gidan mallam ba Tambayata zaka Tsaya kana yi ba.."
Cikin Tsoro da Fargaba Sagir yace"Zoo road gidansu yake.."Batare da bata Lokaci ba Imran ya take mashin Har suka isa Zoo road ba wanda ya kara mgana Sagir ke nuna Hanyar gidan,Cikin Lokaci sai gasu Kofar Gidansu Safiya wanda ke Dauke da Katon Get mai Ruwan Madara Daga ganin Zubin gidan zaka Fahumci suna Rufin asiri eh mana suna Dashi Mahaifinta Alhaji Alhassan Buhari Lacture ne A BUK Dake nan Jahar kanon Dabo.
Akofar gidan Imran ya Faka Mashin din nashi Sukasauka Gabadayansu Lokaci Daya ya Juya yana Bin Gidan da kallo yana Wani Shafa Sajensa ganin haka yasa Sagir yace"Imran Me zaka yi agidan su yarinyar nan..?

Imran bai mai mgana ba Illah Tabansa daya Kara Fitowa da ita ya Kunna mata Wuta sai da ya Busa Hayakin ya Fesar kana ya Sauke kallonsa kan Sagir yana Fadin"Bafa wani abu ya kawoni ba..Kawai Kashedi zan mai da kuma Umarnin Yayi gaggawan bama Yayana auran yarsa in ba Haka ba.."Sagir Daya Zaro ido yace"in ba Haka ba mene Imu..? Don Allah ka bari kada ka Shiga gidan Mutane ka Tada wata Rigima so kake amaimaita abunda ya Faru a gidansu Asma"u..? Ka Karya ma kawunta Hannun Daga karshe ba Yaya yusuf ka bari da Shari"ar ba ina amfanin wannan Rayuwar da kaKe saka Kanka acikine..?
Yana jinsa bai taka ba idanuwansa ma na Lumshe yana Zukan Taba yana Fesar da Hayaki,Sai chan yaBude Jajayen Idanuwansa yana kallon Sagir Lokaci Daya ya gyara Tsayuwa yana Fadin"Bazan karyamai Hannu ba..? GIDANMU fa ya zaga..? Ya kira Babana Mahaukaci..? Wlh Tallahi kowaye ya nunayatsa gareni ya zagi gidanmu ya kuma kira Babana Mahaukaci sai na Karyashi in ban Nakasaahi ba Sagir.."

Ya karishe Fada Cikin Daga Murya Idanuwansa sun Sauya Launi Ganin haka yasa Sagir ya Sausauta Cikin Lallashi yace"Naji Bai kyauta ba..Ammh me ya jawo haka kuma yau..? Imran yace"Raba yayana yayi da yarsa..Can u juz imaging ya yusuf na kuka fa saboda yarsa kuma sai naje gida na kwamta ina Murna..? Ina so ya gane ya Tabani Wlh zan mai gargadi in yaji Ruwansa in bai jiba Jikinsa zai gayamai ne ba Ruwana fa.."
Ya karishe Fada yana Zakuda kafadansa Lokaci Daya yana Fesar da Hayakin Taban Daya Zuka Harta Hanci ya Dumfari get din gidan Sagir ya Bisa yana mai magiya Cikin Takaicinsa ya waigo yana Fadin"Malam don Allah ka kara gaba..Haba nifa Gidan kawai na Bukata kuma ka Kawoni zaka iya karawa gaba Bai Dameni ba"Yafada kamar zai Dakeshi Sagir ya kallesa yana Fadin"Ammh ai har kofar Shagona kaje ka Dauko ni ko.?
Imran ya juya yana Fadin"Kuma Da ka gama Biyamin Bukata nace U are Free to go ko..? Sagir yayi Kasake yana kallonsa Har ya Taka Jikin Get din yayi Knooking Sai gashi megadi ya Leko Domin ganin Waye Hayakin Taban da Imran ya Fesamai ya Faramai Maraba Baya yaja yana Fadin"Bawan Allah meye hakan..?
Yafada ya kare ma Imran kallo wanda ya tsaya kyam Hannunsa Daya cikin aljihunsa Dayan kuma ya Rike da Tabarsa yana Busa sai da Lumshe ido ya Bude kana ya Sakarma Megadin wani kallo kafin yace"Alhassan Buhari yana Ciki..?
Megadi ya zaro Ido Jin sunan Megidansa kai tsaye ya Tsorata ganin yanayin Imran din Shiyasa yayi saurin cewa"Eh..Eh..yana ciki bai riga ya Fita ba.."
Imran yace"Gud..Shiga kace mai yana da Bako a waje.."da sauri megadin ya juya zai tafi Imran yace"Ji mana..! Cikin kaushin Murya Jiki na rawa ya juyo yana Fadin"Na"am yallabai.."Domim a Tsorace yake gani yayi kamar in yayiwani gardama Imran zai Fito da wuka Domin kallonsa yake kamar wani Dan Daba Duk da yayi Mishi kama da Yusuf Saurayin Daya Daga cikin yaran Gidan Jikinsa bai saki ba.

Sai da Imran ya Busa Hayakin Tabansa kana yace'In yabukaci sanin waye kace mai IMRAN ABUBUKAR MALAMI ne...Kanin Yusuf Abubukar malami.."Ya karishe Fada yana wani Shafa Gemunsa,lokaci Daya yana Lailaya Taban Hannunsa,Da gudu megadi ya juya yana Fadin"To yallabai.."Sagir Dake gefe Tagumi kawai yayi aransa yana ta addu"an Allah ya kauda Fitina yaso ya kira Ya yusuf ya gayamai ko zai yi wani abu sai ya Tuna Lambarsa Tana Karamar wayarsa ne kuma ya manta da ita agida saboda Sauri.

Megadi Har Falon gidan ya Shiga Daidai Lokacin Alhaji Alhassan ya Fito Zai Fita Matarsa Hajiya Mero ta rakosa Megadi ya Zube yana Fadin"Alhaji kana da Bako."Cikin}? mamaki yace"Bako..? Daga ina kenan..? Megadi ya Kaskastan dakai yana Fadin"Yace ace maka Imran Abubukar malami ne kanin yusuf.."Alhaji ya kalli Hajiya Mero Cikin Fushi yace"Kin ji ko..? Wannan kanin Shashan yaron chan ne da SAfiya ke ta kuka Tun jiya kan nace Bata bashi.."Hajiya Mero ta karkace kai Tana Fadin"Takadirin yaron nan dai kaninsa da muka samu Labari Alhaji..? Yana Saba Babbar Rigarsa yace"Shi mana..Bari naje Shima nayi mai Fata Fata kamar yadda nayi ma Yayansa Jiya..Ni ba karamin Mutum bane da inaji ina gani zan Hada jini da Dangin Mahaukata da yan iska.."Jakarsa ta Briefcase ta mikamai tana mai Allah ya kiyaye ya Fice yana Fada Megadi Daman Tuni ya Fice kada kai Tayi Ta koma Ciki Tana Ayyana abubuwa da Dama kan Al"amarin.

Yana Fitowa Haraban Gidan ya mikama Direbansa Jakar yana Fadin"Ina yake..?Megadi yace"Yana Daga Wajen get Alhaji.."Karamin tsaki Yaja yana Fadin"To ya shigo mana..Ko ni zan Biyo sa ne..? Yafada da Dan karfi Har Imran da Sagir sai da sukaji Domin ya Taho gabda Get din ne balle ma Alhaji Alhassan irin Mutanen ne marasa mgana Cikin Natsuwa ga Sakin Murya.
Megadi ya leko waje yana kallon Imran yace"Yace ka Shigo yallabai..'Mirmishi Imran ya saki kafin ya Saki Taban Hannunsa ta Fadi kasa ya saka kafa ya Murjeta Megadi ya wangalemai karamar Kofar ya Shige Sagir na ganin Haka ya bi bayansa Suna Shiga Haraban Gidan suka Hada ido da Alhaji Alhassan wanda ke Tsaye yana gyara Babban Rigan Jikinsa Lokaci Daya yana kare ma Imran kallo Daga sama Har Kasa
Shi kuwa gidan yake Kare ma kallo afili ya Furta.."Nifa ba ganin kyale kyalen gidanka ya kawoni ba..Mgana nazo muyi kan Abunda ya Shafemu Alhaji.."

Ya Karishe Fada yana Kafeshi da Jajayen Idanuwansa Lokaci Daya ya Zura Hannu cikin aljihu ya Dauko Tabarsa ya Kunnata hayaki ya Fara tashi Alhaji Alhassan Dake tsaye Bai yi mamaki ba Daman ya samu Labarai Dadama kan Imran din a Fusace ya Tako zuwa gabansa yana Fadin"??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????Kai wannan wani irin Shashancin ne..? Kashigo Gidana kana Min Shaye Shaye..? Yafada Yana wani Kunfar Baki Domim ba Laifi Alhaji Alhassan akwai Fada.

Ko Tak Imran bai ce mai ba sai ma Tabarsa Daya kara Zuka ya Daidaici Fuskar Alhaji Alhassan ya Sakarmai Hayakin da sai da yayi Baya Cikin Firgici yana kallon Imran wanda yayi Mirmishi ya Dagamai Gira yana Fadin"Ya akayi..? Ka tabbatar yanzu.? Ba Wani Dogon Surutu ya kawoni ba..Miye Dalilinka na Hana yayana Auran yarka..? Ya fada Cikin Tsuramasa Idanuwansa Kamar yana Bashi Umarnin yayi mgana Alhaji Alhassan mamaki ya kara kamashi Sagir kuwa yana Gefe bai yi mgana ba sai addu"a yake aransa kada Alhaji Alhassan ya Fadi wata mgana kan Gidansu ko Mahaifinsu yanzu ayi mara Dadi kamar yadda Kwanaki ya Faru da abokinsa KB a Shagonsa Suna Hira sai Imran yazo wajensa Bama dashi ake Hiran ba Cikin Labarin ne Kb ya sako mganar wani Mahaukaci su dai basu yi Aune ba sai Hakorin Kb da Jininsa suka gani a kasa Imran ya Naushemai Baki da sunan wai Dashi yake da Abbansa yake kwatance Fadan da yaso har Hukuma ta Shiga Ciki Shi yayi ta bama Kb Hakurin har ya Hakura ammh da Imran yaji cewa yayi Duk wanda ya bama Kb Hakuri ya Hakura Uwarsa taci Uwatai.
Shiyasa yake ta Tsoron kada Hakan ta kara Faruwa yasan Imran kamar Yunwar Cikinsa zai iya komai ga Duk wanda ya aibata GiDANSU.

Alhaji Alhassan da Ransa ya gama Baci ya Fara Fada da Bambami yana Fadin"An hanashi din..? Nace an hanashi din Zaka aura masa ita ne..?ko yarka ce.?Ina ce Ni na Haifeta kuma ba wani iko da ita ba.? Ko Uban wani ya Haifamin ita ?.."Ya Karishe Fada har kumfar Miyau na Biyo bakinsa.
Imran Dake zukan Tabansa ya Dakata yana kallon Alhaji Alhassan kafin yace"Ammh dai Uban da ka zaga ba namu Uban ka zaga ba ko..? Yadda yayi mganar ne yasa Shakkarsa Ta Shiga Alhaji Alhasan ya juya kai Baiyi mgana ba Mirmishi ya saki kafin yace"Nagane..Ba Dogon Turanci nace kamin ba Malamin Kimiya da Fasaha Dalilinka kadai zaka Fadamin.."Alhaji Alhassan yace"In Kaji Dalilin sai kuma yaya..? Nace sai kuma Yaya..?
Imran ya Zakuda Kafafa yana Fadin"Sai yaya kuwa..? Iyaka in Dalilin bai min ba na saka Ka Dole ka Kira yayana ka bashi Go Ahead kan ya Turo magabatansa.."Zaro ido Alhaji Alhassan yayi kafin yace"Ni..? In hada Zuru"u da irin Mahaukata Irin Tantiranci..uwa uba ga Rashin asali da Nasaba Gidanku ba Tarbiya ba kwaba Domin Tunda kuka zo garin nan Daga ku sai Mahaifinku albarkan zaman mace ma agidan baku samu ba kuna Zaune kara Zube sai ni Saboda bani da Tunani na Dauki yata na bakku.? Ai sai kimata da Mutumcina ya...!

KAIIII...!Ihun da Imran ya Kwatsa kenan Lokaci Daya ya Daga Hannunsa sai Sauke ma Alhaji Alhassan wani Naushi wanda inda ya samesa sai ya Raunana Domin Tabbas Hakoransa na Gaba sai sun watse sai Dai Sagir ya Ceceshi Daga Hakan Ya Tare Imran Da Rikoshi da Karfinsa yana Fadin"Imran..Imu..Ka bari Don Allah..Kada ka Tabashi Don Allah.."Yake fada yana Rikesa da kyau ganin yadda yake wani Fizga Idanuwansa sun kala sun ji Jajir Tuni jijiyoyin kansa suka Daga haka yake sakin Hucin bakinciki da Hannu yake Nuna Alhaji Alhassan Dayayi gefe Tun Hargagin Imran yana maida Numfashi Cikin Muryansa mai Cike da Amo yake Fadin"Who is He da zai Fadi wata banzar mgana kan Gidanmu.? Shidin banza waye shi..? Wlh da barni da yanzu Bakinsa ya Cikada Hakoransa da Jini Kai har kana da Bakin mgana Kayi gaggawan bama Yayana Dama in ba Haka sai na Fallasaka agaban iyalanka gasunan suji su kuma Fahimci wani irin Uba ne Allah ya basu.."Ya karishe Fada yana Nuna su Safiya da sukaji Hayaniya Daga Haraban gidan suka Fito kuka kawai take Tunda Taga Imran duk bata taba ganunsa tasan sunan abakin yusuf kuma daga mganarsa ta Fahimci ko waye shi.. kanwarta Tasleem Tana Ta lallashinta Hajiya Mero kuwa Mahaifiyarsu kallon Imran take Tana kuma Kallon Alhaji Alhassan da Tunda yaji mganar Imran gabansa ya Fadi kardai yasan Sirrinsa na Neman matan Dayake yi..? In ko hakane ya Shiga uku Gwara ya basu auran Safiya daya Fallasa wannan Sirrin wanda Bayyanarsa zai yi Sanadiyar Kimarsa da Darajansa da Mutumcinsa da kuma aikinsa Dayake takama Dashi

Yin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login