Showing 24001 words to 27000 words out of 236322 words

Chapter 9 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

699

Damka Amanar inteesar a hannunsa yace bakomai yanzu hakama Umma ta bashi Lambarta zai jirata su gama karatu su koma Gida Tare kafin ta saba Daddy yaji Dadin haka 10k ya bama Sagir ya karba yana ta Godiya Daganan sukayi sallama suka Shiga Mota suka kama Hanyar kaduna shi kuma ya wuce Department dinsu yana ta Sauri Tunda yasan an Shiga Tun Dazu!
Wayarsa ya Fito da ita yana Dubawa yana tafiya,karamin tsaki yaja ganin har yanzu bai ga kiran Imran ba alhalin tun safe yake kiransa bai Daga wayarsa ba Jiya kwata kwata basu hadu ba yadai kirasa yace ya Turamai lambar Baba Manu ya tabbata ya kai mai kudin Da sukayi mgana ne,Yasan waye Imran in yace zai yi abu baya saba alkawari zai yi din ne yana so yaji yau su Baba Manun zasu je neman auran..? Ammh bai Daga kiransa ba Shiyasa har ya karisa cikin ajin yana ta sskin tsaki.!
Abunda Sagir bai sani ba jiyan Banki Imran yaje ya Ciro kudi a Bankinsa wanda baya amfani DashivSai Lokaci bayan Lokaci,Sai kuma yaje Banki ya Cike Form yake iya Fidda kudi Gabadaya kudin bankin nashi Dubu Dari uki suka Rage bai yi mamaki ba yau da gobe bai bar komai ba yana Cire kudi Lokaci Bayan Lokaci yayi Hidimansa kanar siyan takalma,Kaya da Sauran abubuwan da baza"a rasa ba!
Sauran dawaniyar Yusuf ke gudanarsu da albashinsa in ya gagara sai ya taba kudin Dake Bankin Abba ko na Marigayi Yayansu Nura saboda Dawaniyar Abba da Likitan Dake zuwa Gida Dubashi da kuma Dawaniyar mganguna,Ammh shi baya karba ko Naira Biyar wajen Yusuf da kudinsa Daya tara lokacin Daya fara aiki a inda suka zauna yake amfani.
Bashi da Zabi Dubu dari Biyu 200k,ya ciro ya Dawo Gida a kuma Lokacin ya kira wayar Yusuf yace ya sanar ma Safiya ta Fadama Babanta mgabatansa suna tafe gobe,ya kashe nan take kuma ya kira Sagir yace ya bashi Lambar Baba Manu yana Turomai ya kirashi yafadamai sunansa yace ga kudin nan zai kawomai shi kuma yace ya bari zuwa anjuma yanzu yana gareji ne.
Haka kuwa bayan Isha"i Imran yaje yakai ma Baba Manu kudin yau ko Rakiyar Sagir bai nema ba.
Yusuf kuwa bai yi mamaki ba Sanin Halin kaninsa Duk Abunda yace zai aikata baya Runtsawa sai ya Tabbatar dashi..Safiya ya kira ya Fadamawa,Sai taji abun kamar wasa Cikin Tsoro Ta sanar ma da Mahaifiyarsu Hajiya Mero ita kuma ta sanar ma da Alhaji Alhassan bayan ya Dawo ya Cije a lebe a Fili ya Furta."Allah ya kawo su lafiya..!
Domin ya gama Shirya abunda zai yi goben da Zarar sun zo..Shi da kimarsa da mutumcinsa agari bazai bari saboda Dalilin Safiya wannan Shegen yaron Mara kunya ya Zubarmai da Daraja ba.!



*Ba na fara saka Lokacin Posting bane kamar yadda wasu ke Tunani ba,Ni bana Ware wasu ranakun Lokacin Posting,Ina yi duk rana alokacin da na samu dama da Lokaci sai dai in Rashin Lafiya ko ciwo ko wani Uzuri,Domin daman kana naka ne Allah yana nashi na Allah kuma shine Daidai Jiyan nan na wayi gari bani da Lafiya shiya kawo Tsaikun Rashin posting dina ajiyan..Ina ganin Comments dinku ina matukar godiya Yan Wattpaddian Voting dinku yayi kasa fa ya kamata ku kara kaimu nayi muku alkawarin Bazan baku kunya ba Insha Allahu*








*Shakira..*
3/22/22, 23:03 - Ummi Tandama???i: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:JanaftyB??0
{*

*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*


*??T??08*

"Asalin sunanta *MARYAM MUSTAPHA HAMISU DUKKU* ne Saboda taci sunan Mahaifiyar Babanta Daada yasa ake kiranta da INTEESAR.
Alhaji Mustpaha Hamisu Dukku Haifaffan garin Dukku ne na Jahar Gombe,ya kasance d'a na uku a jerin ya"yan Daada Maryam da Mahaifinsu Alkalin Kotun Musulunci Alhaji Hamisu Dukku.
Hajiya Maryam(Daada) Haifaffiyar garin Dukku ce ta uwa Data Uba Bafullatanan Dukku Ta gaba da Baya,Auran Zumunci ne tsakaninta da Megidanta marigayi Alkali Hamisu Dukku,Domin alokacin Makoci Tamkar Dan"uwa yake wajen makocinsa iyayen Daada da iyayen Hamisu Dukku sun yi Zaman makota shekaru masu yawa wanda Sanadin haka yasa suka Zama Tamkar yan"uwa wannan Dalilin ne yasa suka Hada auran ya"yansu Wato Maryam(Daada) da Alkali Hamisu Dukku.
Maryam(Daada) bata yi Zurfi a Karatun Boko ba iyakarta Sencondary Alokacin ma agidan Mijinta Alkali Hamisu Dukku Tayi Candy,Tayi aure da kananan Shekarunta,Saboda Tana da Shekara Goma sha Shida ne alokacin.
Alkali Hamisu Dukku,yayi karatun Zamani Dana Boko ya tafi Jami"ar Abu dake Zaria inda ya karanci Shari"a Low,Bayanan yayi Degree dinsa na Farko sai ya Dora bayan haka ya Hallaci Courses masu yawa akan Abunda ya Shafi karatunsa agidansu Shi kadai ne yayi karatun Boko mai Zurfi Duk da basu da yawa shi ne kuma Babba.
Yayi aiki a mtsayinsa na Cikakken Lauya ya taka mataki mataki na Rayuwa sun Fara zama da Daada a garin Dukku agidan iyayensa inda ya gada Tunda Lokacin Allah yayi ma Mahafinssa Rasuwa kafin ya samu aiki a babbar katun Jahar Gombe ya mallaki gida da Motar Hawa ya Dauki matarsa suka koma Chan da Zama..
Sun koma ba Dadewa Daada ta samu Ciki,kuma yana bata Wahala sosai Dalilin dayasa Alkali yasa aka nema mata yar aiki kenan Allah ya Hadasu zama da Baba Asabe Tun tana da Danyen Shekarunta Ita take Taimakon Maryam(Daada)da abubuwan Cikin gida,Alkali Hamisu Dukku da Matarsa Maryam(Daada) suka Rike Asabe Tamkar wata jininsu ko nace Yar"uwansu.zuwa Lokacin duka sun rasa iyayensu saidai yan"uwa da abokan arzuka.
Kabir shine Babban Dansu sai Abubakar,sai Mustpaha sai Fatima (Bintalo) sai auta Maimunatu,azuwa Lokacin da daya Tara ya"yansa Biyar ya samu Dukkan Cigaban Rayuwa,Asalin Komawarsu Dukku samun Alkalin alkalai na Babban Kotun musulunci Dake Dukku ne yasa yayi Ginin Zamani ya Tattaro Duka iyalansa suka Dawo nan da Zama Dindin Daman shi Alkali Hamisu yana da Kishim kansa yafi Sha"awar Zama a Kauyensu Fiye da Ko"ina To itama Maryam(Daada) domin duk inda zasu je basu da kamar Dukku.
Alkali Hamisu Dukku bai bar Gidan Duniya ba sai da ya kwafa ya"yansa suka samu Wadattacen ilimin Zamani Dana Boko,Kabir Shine ya gado sa shi ya karanci Harkan Shariya,Abubakar kuma ya kasance Malamin makaranta ne kowa yasan Burinsa Tun yana karami Shiyasa Alkali Hamisu yake mai Lakabi da MALAMI..!
Bai kuma bar gidan Duniya ba sai da ya aurar da duka ya"yansa Daga matan har mazan
Bintalo Tana aure anan cikin garin Gombe,Tana auran wani ma"ikacin Fire service na Jahar Gombe kuma agidansa tacigaba da karatunta ayanzu haka Lacture ce itama anan Jami"ar Gombe Yayanta Uku Dayake bata cika yawan Haihuwa ba saboda Karatunta,Siyama da Hamida sai Hauwa"u Duka matane kuma Suna Gijajen mazajensu sunyi aure suma sun Haiyayyafa.
Sai Maimunatu Tana chan Garin Bauchin yakubu Tana auran wani Soja ne,Ita tana da ya"ya sun kai bakwai,Manyan ya"yanta itama mata ne sai Mazan Sa"id da sadam.
Sai kabir wanda ke Zaune a chan Birnin Tarayyah Abuja Yana mtsayin Cikakkem Lauyan gwannati ne,yana da mata Daya Asma"u wacce ta kasance Diyar Masu kudi ce Diya ce ga Alkalin akalai na kasa gabadaya,Sun hadu ne a wani Course Dayaje karanta a Washington,Itama taje Dukkansu Lauyoyi ne suka Fara Soyayah har takai su ga aure duk da Mtsayinta da Nasabarta Barrister Asma"u taga Barrister Kabir Hamisu Dukku kuma tayi na'am Dashi Mahaifinta bai hanata abunda take so ba Tunda su yan Boko ne abunda duk kake so Shi zakayi.
Dagashi har matarsa Lauyoyi ne masu Zaman kansa,Tsarin Gidansu tsarin Gidan yan Boko ne gaba da Baya Gabadaya Haka suka Tsara Rayuwarsu Shiyasa ko a tsarin Haihuwa ya"yansu Uku ne Biyu mata daya Namiji Babba ne Namiji mai suna Hamisu wanda yaci sunan Marigayi Alkali Hamisu Dukku suna Kiransa Khamis,Yana Chan Anambra inda yake aiki a mtsayin Sojan Ruwa Navy.
Sai kannensa Guda Biyu Sajida da Umaima wadanda Tazara ne mai Nisa a tsakaninsu dashi..Hakama Tsakanin Sajida da Umaima akwai Tazaran shekaru kamar Hudu haka.
Sai Abubakar wanda Shima yayi aure kuma shima yana da ya"ya,
Sai Lokaci Daya aka Nemehi aka Rasa Shi da iyalansa Wadanda suke a Rayuwa a lagos,Tunda Shi Abubakar din Malamin Philosopy ne a University of Lagos achan baya kafin wata kaddara ta Gitta musu wacce Tayi Sanadiyar Faruwar duk abunda ya Faru.
sai Mustapah wanda ya kasance Dan kasuwa ne,kasuwanci ya karanta Domin Shine Burinsa,yana kasuwancin sai da kayan Mota,sai kuma yana Kiwo Harda gidan gona gareshi achan kaduna matarsa Salaha itama yar kaduna ce a Badarawa,Ita yar Talakawa ne ba masu Hali ba Inno da Mallam Babba,wanda yake sana"ar sai da Hatsi,su Biyar ne agidansu Yaya bala ne Babba,sai Yaya Salisu,sai yaya Amina sai Salaha(Umma)kenan sai karamin kaninsu Mudanssir.
Auran Soyayya sukayi Tsakanin Shi da Salaha Allah ya Hada auransu yana Zaune anan garin kaduna anguwan Sarki inda ya Gina katon gida,Allah ya sakama Kasuwancinsa albarka Shima din za"a sakasa Cikin Jerin masu Dashi.
Ya"yansa Biyu ne rak aduniya Basheer shine Babba wanda Bayan Haihuwarsa har sun Fidda rai da Haihuwa bayan Shekara Goma kana suka samu Haihuwan Inteesar wacce taci sunan Daada Maryam.

Atsarin Rayuwarsu Suna da Hadin kai da Zumunci a tsakaninsu kuma suna Girmama junansu Bayan Rasuwar Alkali Hamisu dukku wanda Ciwon Hakoribyayi sanadin Mutuwarsa Daga Dare zuwa safe,Su suka Cigaba da kula da Daada da kuma Baba Asabe da suka Taso suka ganta agidansu,Kabir yaso ya Dauke Daada Daga Dukku ta koma Wajensa a Abuja ammh Taki yarda tace Yarda Alkali ya Mutu acikin gidanan itama nan Zata mutu Domin ya rasu bazata Ki Burinsa na son Ta Rayuwa ita da ya"yansu a garin na Dukku ba sai dai bata da yarda Zatayi ne Tunda aiki ya Raba kowannesu Inda yake ammh Ita kam ba inda Zataje Tana Tare da Baba Asabe a garin na Dukku agidan marigayi Alkali Muddum rai.
Dole ya kyaleta Tunda ta kafe sai da yasa aka gyara gidan aka Maidashi na Zamani kowani Lokaci suna zuwa ganinta in suka samu dama.
Kayan alatun More Rayuwa kuwa da jin Dadi Daada sai dai ta bama wasu Komai na Rayuwa ya"yanta sun Dauke mata shi Taje ta Sauke Farali bata san iyaka ba bayan wanda marigayi Alkali ya kaita kuma suka je Tare,Hatta Baba Asabe taje ta sauke Farali Sau Biyu Adalilin Daada da Yayanta
Daada Tayi kokarin Hada kan ya"yanta da Jikokinta waje Daya suna zuwa mata Hutun karshen Shekara Duka matan da Mazan Domin kara Shakuwa tsakanin iyayen da kuma yaran sun san junansu da yan"uwansu gabadaya,ammh abun ya ki faskara sai da ya"yan nata su zo,ammh Ya"yansu basa zuwa sai Dai dai,in tayi mgana sai su kawo uzurin makaranta da aiki da sauransu.
Barrister Asma"u matar Kabir itace bata Shiga Mutane,Tana da Dagawa da Takama sai dai Tana da Fara"a in ta saba da Mutum,Taso tazo Daya da Umma Salaha,Suna dasawa sosai Ko Saboda yadda wata kakkarfan Shakuwa ke tsakanin mazajen nasu ne oho
Cikin ya"yanta Sajida ce kadai ta gado Duka Hallayarta Har ma ta fita sosai.
Sajida akwai Dagawa ga Takama ga Raini,Tana ganin tafi kowa Domin iyayenta sun tsaya mata sun kuma taka wani abu a Rayuwa,Yar gatace ta gaba da baya,agidansu basu san suyi aiki ba komai yan aiki keyi musu hatta da Girki kuwa,Inda Asma"u tayi kuskure kenan ko ita batace ta iya wani Girki ba Tun farkom auransu ta sakarma yan aiki Duka Ragamar Gidanta Har yau har gobe Abincin yan aiki yake ci kuma bai Taba Korafi ba saboda sun Tsara hakan Daman tun Kafin suyi auran
Khamis ne ya Debo kaf Hallayan Babansa,kuma ya Debo Hallayan Marigayi Alkali wanda yaci sunansa yaro ne matashi mai Hankali da natsuwa yana Bala"in son Tsohuwa Daada,Musamman Daga Anambara yake zuwa ganinta in ya samu Lokaci Waya kuwa Lokaci bayan Lokaci Tana jinsa kudi kuwa makudai haka yake Turomata,Duk Shekara sai ya Sauya mata Furniture din gidanta Shiyasa itama take matukar ji Dashi,Sai dai duk yadda take ji Dashi ba kai Soyayyar Datake ma kwara Daya Cikin Jikokinta ba Dukda ya kasance mai Budadden Hali da kowa baya jin Dadin mu"amala Dashi ita ahakan take matukar sonsa,sai dai Bata nunawa ba..Tunda bai Cika yawan Tako kafarsa Dukku ba sai da wani Babban Dalili Shima din sai Mahaifinsa ya Mtsamasa ne ya Tarosa suka Taho Tare,bawai bai Damu da kowa bane a"a yana Damu da Ahalinsa sai dai shiyanayin Rayuwarsa marasa son Doguwar mu"amala ce mara son Hayaniya da Zama Cikin Mutane, yana da Bambacin Ra"ayi da Mutame Koda kuwa yan"uwansa ne Shiyasa bai Cika Shiga Cikin yan"uwa ba,adangi ba wanda zai ce ya taba Doguwar mu'amala Dashi,ko da yan"uwansa da suka Fito Ciki Daya suna kuka da Hallayarsa masu Tsauri da Wuyar Fahimta.
Wannan kaunar ta samo asali ne da kaunar Datake yi ma Mahaifinsa ne saboda ya kasance mai sanyi Rai ladabi Biyayyah ko baya son Abu indai Daaada ta Ce abu kaza ne sai yayi shi Biyayyarsa da wannan Sanyin nasa yasa Daada ke matukar sonsa uwa uba kuma ta wanke Diyar kanwaarta Data Zama kamar itace komai nata ta Riketa ta bashi kuma ya karbs ya aura ya Zauna da ita Har Mai Rabawa ta Rabawa Duk da Ya kawo mata wacce yake so.
Shiyasa har Yau har gobe Daada bata daina kukan Rashinsa ba
Ta kamu da Ciwom Hawan jini Saboda Damuwa ya"yanta suke Wahala kan lafiyarta Musamman Kabir ya Daukan mata Likita wacce take zuwa har Gida Tana kula da ita Dr.Zubaida Cikakkiyar Likita a babban asibiti dake garin na Dukku.
Koda Daada ta tsufa Girma ya zo mata bata da Lalaci,kowa ya sani mace ce mai tsayawa akan kafarta Shiyasa bata Shiri da Sanganta da kiyuwa Sajida na yawan zuwa Hutu gidan Daada sai dai Rabuwa sukeyi ba Dadi Tun Kafin ma Hutun Sajidan ya kare.
Umaima kanwarta ta fita sanin ya kamata gata bata kiyiwa in tazo Shara gyaran Daki har girki Take Taya Baba Asabe,gidan ta koyi wasu girken girken Data koma Abuja ta gwada Ranar Diyar Lauyoyi Taga Fada kamar su Daketa suna Fadin kada ta kara Wannan kwarambanin Hannunta bai yi kwarin da Zata yi Girki ba kada ta kone
Itakuma Sajida Fadi take Tana Diyar Lauyoyin gwannati Jikar Alkalin akalai na kasa Duk da yayi Ritere,Kudi da jin Dadi sun gama Dabaibaye Rayuwa komai take kudi zasu yi mata Allah ya Tsareta da aganta tana aiki indai akwai yan aiki da kudi zasu yi mata komai Shiyasa basa Shiri da Yayanta Khamis Shima a tsaye yake a kullum yana tsawatar mata Da cewa ita macece Watarana Zatayi aure ammh Sai mahaifiyarsu da suke kira Mami ta Shiga mganar tana Fadin ya Daina Takura ma yarta yadda ta Samu jin Dadi agidan Mijinta itama Zata samu,Shidai kawai Shiru yake domin yasan Watan Watarana Zasu yi Nadaman wannan Rayuwar Bokom da Sakewan da suka Daukan ma kansu Shi Allah ya Taimakeshi Gombe yayi karatun Secondary Dinsa Bording in ya sami Hutu bai cika zuwa Abuja ba yana gaban Daada Shiyasa ya zama Dabam
Yar tsamar Dake tsakanin Inteesar da Daada kuwa bawata maiyawa bane..Duk da tafi kowa Murna da Akayi mata takwara sai dai basa Shiri saboda irin gatan da Alhaji Mustpaha yayi ma Inteesar saboda Samunta Lokacin da suka Fidda rai.
Inteesar ta shaku da Mahaifinta Fiye da kowa aduniya ko Mahaifiyarta bata Shaku da ita ba irinsa ba,Dalilin haka yasa bata da Sakin jiki da Mutane bata san kowa ba sai Daddynta sai Ummanta da yayanta Basheer sai kuwa Gidan kakaninta ta Bangaran Uwa gidan su Inno,Su da suke Biyema Sangartanta.
Inteesar bata san kowa a Dangi ba Domin bata zuwa ko"ina gwara Dukku ma in Alhaji Mustapha zai je takan Biyosa suzo Tare,Bata yarda ta kwana Kafarsa kafarta Duk kuwa da Mitan da Daada ke yi na bata son Shiga Cikin yan"uwanta.ita kuwa bata son Rabuwa da Babanta ne kuma tafi sabawa dashi Fiye da kowa.
Rabon Inteesar da Zuwa Dukku har ta manta saboda Korafin Daada akanta,Tayi ta cewa ta Cika Sangarta tayi ta ma Daddynta Fada kan ya Sangartata ita kuma abun Haushi yake bata yasa Daga Baya ta Daina Biyosa sai ta Fake saboda makaranta.
Ko Duka gidan Za"aje sai dai taje gidan Inno ko gidan Kawu Salisu Saboda yarsa Nasara sa"ar Intee ce kuma tasu tazoDaya
Shiyasa bata san kowa ba adangi su Inna Bintalo da Inna Maimuna sun gaji da mita sun Hakura Inteesar bata taba zuwa Gidan Daya Daga Cikinsu ba ko Za"aje bata zuwa bata son Abun mgana.
Tuni ta Dauke kafa Daga Dukku Tun Tana karamarta har saida taGirma Lokacin Data gama Candy Tana jiran Sakamako Daada ta matsa Umma ta Ce sai taje tayi Kwana Biyu achan,Daddy shi ya Lallasheta yakai ta da kansa Aranar Dataje Washegari Sajida ta iso Daga Abuja.
Inteesar bata ji Dadin Zaman Gidan Daada ba,Shiyasa Dukkun ta fita kanta Zaman da sukayi da Sajida Zama ne na kowa na Har kan gabansa Sajida girman kai da Dagawa..da nuna isa ita kuma Inteesar rashin Tsoro,itama tana ji Da gata sosai Shiyasa basu ga maciji,Daada ta Dinga Fada ita Sajida Kiyuwa da son jiki ita kuma Inteesar Da an fara mgana sai kuka Daada Tayi musu Fatata ta kira iyayansu suka zo suka Tarkasu,kowacce ta koma Gidansu da jin Haushin yar"uwanta,Sajida tana ganin kamar ita yar gata gaba da baya Diyar lauyoyi,yayanta Soja jikar Alkalin alkalai har wata adangi Zata Rainata Ina batazata yarda da wannan ba ita kuma Inteesar tana ganin ai Sajida bata fita gata ba bata isa ta taka ta ba.
Haka kowacce ta koma Gida da Korafin yar"uwanta Umma dai ta tsawata ma Inteesar din Ta nuna mata yar"uwanta ce ayayinda Mami bata tsawatarma Sajida ba sai ma Nuna ma Datake tafi Inteesar din gata nesa ba kusa ba Duk kuwa da suna Dasawa da Umma sai dai ita akwai son kanta Tana so a ko"ina akomai Ita da ya"yanta su fi kowa a Dangi Ba kuma iya Zuru"ar Hamisu Dukku ba Harta Daga Bangaranta Tana da wannan Dagawan.
Daga Lokacin kowacce ta ijiye yar"uwan nata awani muhalli na ban san kina Rayuwa ba,Basheer ne dan Dangi kowa ya sanshi kuma ba inda Kafarsa bai taka ba Tun yana Saurayinsa ma kafin yayi aure Dayake Jami"ar Bauchi yayi ya Zauna gidan Inna Maimuna Sosai yake da mu"amala mai kyau da kowa..
Inteesar kuwa bata taka kafarta Ko"ina ko Abuja gidansu Sajida Sau Daya taje Lokacin Tana karama da Tabi Daddy,daga wannan zuwan kuwa bata kara marmari ba,Lagos kuwa bata taba Zuwa ba tasan dai Tana da wani Uban achan lagos din inda yake Zaune shi da iyalansa ba kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login