Showing 150001 words to 153000 words out of 236322 words

Chapter 51 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

770

wajen yaga wadanda sukayi aiki tare wasu kuma da yawa an sauya su wasu kuma Rai yayi Halinsa,wadanda suka sansa sai Turruwa suke wajen gaisawa dashi To alokacin Waye baisan Imran Abubakar malami ba kan kwarewa a aikinsa da Miskilancinsa iya Daukan wanka bama aiki Muhimmaci gabadaya Dokokin bankin shi nashi Dokar ma ya Take nasu shiyasa ba Ma"ikacin da Manaja ke ji dashi Alokacin Irinsa Saboda yadda ya maida kansa kamar wani bawa gwannati na amfana da Tarin baiwarsa da lafiyarsa.
Manajan Wajen ba"a Sauyashi ba wani Bayarbe ne Mr Tunde Abdulwasi yana ganin Imran sai da yayi wani ihu ya Rumgumesa Tsakani ga Allah sun yi Rashin Zakaran ma"aikaci kamar sa haka yake ta Fadama Imran da Khalil sun nemesa har sun gaji sun Nemi Wayarsa shuru sun ta Turamai Sako ta Email dinsa ma Shuru shi ko Imran yama manta yana da wani Email Tin bayan Faruwar abunda ya Faru ya Daina Mu"amala da Duk Abunda ya Shafi Socoal media ya koma Rayuwarsa yadda yake yanzu sai dai ammh yana ji ajikinsa kila Lokacin da Wannan Imran din zai sauya ne zai Dawo ainihin Imran Abubakar Malami A Banker,Manaja yamai Tayin Dawowa aiki kan Mstaayin da yafi na Baya Imran ya nuna mai A"a Baya Bukata Duk mganar da suke yi Cikin Rantsantsan Turacin kasar Amurka ne in kaga bakin Imran yadda yake Tsara mgana Cikin Harshen Turanci sai mamaki ya kusa sumar dakai ka Fara Tunanin Anya wannan Imran din ne mai Shan Taba..?
Khalil ne yayi ma Manaja Tunde Abdulwasi bayanin a takaice na Komawarsu Imran kano da Rasuwar Mahaifiyarsu da yan"uwansu bai ji Dadi ba ya Tsausaya musu,Ya kuma Dage Imran sai fa ya Dawo aiki ko ba anan Lagos ba zai yi waya da Manajansu na Gtbank din su Dake Reshen kano,zai Turamai Duka Bayanan Imran da Takardunsa ta Email Zasu kirashi da Zarar ya koma Zai Cigaba da aiki kamar baya bazai Taba barin wanda aikinsa ke da Mutumci Fiye da komai a idonsa ya Zauna haka ba ballatana tun abaya suna da kyakyawan alaqa da Imran din Hallayarsa na Burgesa rashin Shiga Mutane,baya da shiShishig baya Shiga Harkan kowa baya Hulda da mata sai yazo aiki ya Wuni har yammah ya tafi bai tanka ma kowa ba sai ya Zama Dole aiki ya Hadaku Mutane da yawa acikin bankin suna jin Haushinsa sai dai basu da yarda zasu yi dashi,Ko ya sani bai Damu ba Tunda bai isa yaasa su so ra"ayinsa ba Shidin Kaifi Daya ne.
Bashi da yarda zai yi ya karbi mganar sukayi Sharing din Lambar juna shida Manaja Tunde Abdulwasi,kuma bazai iya Turo Alfarma Khalil ba yana nuna Kulawa akansa.Daganan bakin Ruwa suka je suka dan Huta duk da ba wata Hira suke ba ammh yanayin yayi ma Imran Dadi yana gefe yana kallon Khalil Dake waya yana wani Narke Murya Kila da Budurwansa yake mgana Tsakani ga Allah Tsausayi ya bashi Namiji har Namiji ya Zauna Mace na Juyashi har yana neman mata kuka Duk da abaya yasan Khalil din kamar shine yana da Miskilanci Ammh jisa ya zauna yana wani marairacewa kamar zai yi kuka karamin Tsaki yaja yana kallon Daidaikun Mutanen Dake wucewa Idanuwansa yakai inda yaga wasu Beatifull Couple Duk da bai sani ba Zuciyarsa ta basa Ma"aurata ne,suna Rike da hannun juna suna Tafe Cikin Soyayya da kauna yana kallonsu yana jin wani yanayi kansu kawai yake Hangowa shi da Inteesar Tuna ta yayi sai da yaji wani Sanyi a fili ya Furta"Shababbiyar yarinya..Na kawota nan ai shagwabarta zata yi tamin..!
Yafada yana jin wani Annuri na Shigarsa Wayarsa ya Dauko ya Tura mata sakon

"Kin manta dani ko..?

Alhalin fa ko jiya ta Kirashi sun yi da Daddare data kirassa yaki Dauka Saboda suna Tare da Khalil sai da ya Turamata sakon.

"Oya ki kwanta ki barci..Bana son Damu..!

Shine ne wai yau ta manta dashi so yake yajata da Zence.
Bata kai ga Turomai amsa ba Kiran Sagir ya shigomai ya Dauka suna mgana yana Tambayansa yaushe Zasu dawo yace bai sani ba,basu wani dade suna mgana ba ya katse kiran Saboda Hankalinsa baya kansa yana Wajen Inteeaar ne.
Illah kuwa yaga Sakonta Cikin Shagwabarta Duk da baya ganinta tace.

"Laaaa...Kai ya Imu nice ma na manta Dakai kai da kaje Lagos ka manta Dani kaga yanmatan Birni..Au koda yake ai kana da Matar Abuja Sajida.."

Sai da ma yaga Sakonta ya Tuna da Wata Sajida Tsaki yaja jin tama batamai Mood dinsa Raini yagani Kirkiri Tsaakaninsa da Inteesar Wato Shine ma ya samu yanmata ko..?kiranta yayi kai tsaye tana Dauka ya Fara Fadin"Kin raina ni ko..?Wato nine ma na samu yanmata ko..?Ni sa"anki ne Intee..?
Yafada Cikin wani Salon daya gama Kashe mata Jiki Gabadaya sai ta Fara mganarta Cikin Shagwaba Tana kanunun kuka Maimakon ya Dakamata Tsaawa yace ta Daina sai ya kasa ya samu kansa da jin Dadin Duk Abunda tayimai shi kanshi baisan Yaushe ba yadai samu kansa yana Biye ma Duk wata Tabaranta Wai kukan Shagwaba take yi basu dawo ba alhalin yace mata kwana Daya Zasu yi sai ga Imran yana mata Rantsuwan Wlh ba Laifinsa bane Daga su Daddy ne.
Soyayya mai sauya Mutum ta Sauya Imran bai sani ba ko aikin Daya amince zai koma Saboda Inteesar ne,yasan Zataji Dadi sosai,Kamar ya gayamata sai ya fasa yafi so ya bata Mamaki ne suna cikin Wayar Khalil ya zo Inda yake yana ganin haka ya katse kiran,Sai gashi ta kara Kira Bai Dauka ba sai da ta katse ya Tura mata Sakon

"Kije kiyi karatu...We tok Later bana Gida ne.."

Haka ya Rubuta kafin yabi Khalil wani dan Cafe inda suka Siya Coffea da lemu Anan Imran ya siya Sigari Khalil yaji mamakin ganin Imran na shan Sigari har sai da ya Furtamai Bai ce komai ba amsa Daya ya basa da cewa Life kenan.
Imran yasha Sigarinsa sosai,Saboda Tunda sukazo bai shafa ba,Har da Guzurinta yayi Khalil sai mamaki yake da Tsausayin Domin ya Tabbata Rayuwace ta maidasa haka abaya ko Kusa da ita baya zuwa.
Da suka koma gida basu ma Kowa bayanin inda sukaje ba Suma ba wanda ya Tambaeyesu..
Sai gashi bakin da zasu yi kwana daya sai gashi sai da suka kwana Hudu Tunda sai da suka jira Lurwanu ya Dawo da Iyalansa,Matan sa Biyu da yaya Bakwai irin auran Wuri ne ayi ta Tara ya"ya suka shige BQuaters Matar Buba da ya"yansu suka Tayasu gyara Komai har Cikin Gidan ma suka share suka Goge suka gyara kayan wasa kuma nasu Imran dasu Anni duk afito dasu wadanda bazasu Mori ba aka Zubar masu kyan suka Dauka sauran kuma zasu Sadakar dsshi ga Mabukata ana Gobe zasu tafi acikin Gidan suka kwana Saboda an gyara komai,Daga Gidan Dr.Isa Ali Argungun ake kawo musu Abinci Washegari Tun Safe suka Dauki Hanya bayan Abba da Dr Isa sun karbi Lambar juna haka ma Khalil da Imran sun Rabu kan in an nemesa zai gayamsa Insha Allahu.
Sai Cikin Dare suka iso kaduna anan suka kara kwana Sai Ranar Alhamis suka Dawo Kano,abun da ya bama Abba Da Daddy mamaki Har sukayi wannan Tafiyar Baffa Kabiru bai kira yaji Ya akayi ba sai dai sune suka Kirasa Daada kuwa Hankalinta kwance Koda yaushe Tana Waya da Malami Jininta ya Daina Hawa sai Dai ma yana ta kara Sauka ne.
Abba ya wakilta Yusuf ya Turama Daddy duka CV sa na Takardunsa Shi kuma ya Tuttura ma abokansa na nan Jami"ar Buk suka kuma Tabbatar da za"a dace Daman ana neman Wadanda suka kware kan Abubda Malamin ya karanta ya jira Lokaci kawai za"a kirasa.
Intee tafi kowa Murnan Dawowarsu daman Rashin ganin Imu duk ya Ramar da ita da kuma Gidan ba Dadi basu Abba Mama bata nan Taje Kaduna Bayan Tafiyan su Daddy Lagos jikin Inno ya Motsa sai sukayi mgana da Umma Maman ta Shirya tatafi Wajen kwananta uku kenan Daman Tun kafin tatafi suka dawo nan Gabadaya Saboda Taya Anty Safiya Zama.
Har ya dawo basu Hadu sunyi dogowar mgana ba sai dai sukan Hadu su kalli juna tayi mai Dariya shi kuma ya Hde rai ya Harareta,Sun Dawo Alhamis Ranar asabar da Daddare bayan sun gama Dinner gabadayansu Imran daman ba Zaman Dinner yake yi ba Tea kadai yasha sai gashi ya Fito Daga Daki ya Duka gaban Abba yana Fadamai Gobe yana so yaje Dukku.
Sun ji mamakinsa sosai Abba cikin mamaki ya kallesa yana Fadin"Dukku..?.
Kai ya gyada batare da yayi mgana ba Ya Yusuf dake Zaune gefen Abba ya kada kai yana Fadin"Dukku..? kodai Abuja mallam gayamana gaskiya..Kana son ganin Sajida ka Fake da Dukku..,,!
Kamar ya watsamai Ruwan Zafi haka yaji kallon Ya Yusuf yake yana auna in ba Domin shi bane wlh sai ya Duramai Ashariya Saboda Haushin mganarsa.
Inteesar ya kallah Dake gefen Munari da Anty Safiya itama kallonsa take Gabadaya Sai taji Ranta ya baci da aka ambaci Sajida kenan da gaske wajenta Zai je.
Kauda kansa yayi bai ce komai ba Abba na Dariya yace"Ai kamar tana makaranta bata dawo ba..Barsa kila ganin Kakarsa ne ya tasomai in yaje ya Dawo sai ya shirya yaje yaga matar tashi Lokacin ta dawo gida Tunda Ya Kabirun yace min suna Test ne..!
Har Abba ya gama mgana bai Dago ba.
Abba ya kallesa yana Nazarinsa kafin yace"Kwana zakayi in ka tafi goben..?
Dakyar yace"In Dare yayimin sai jibi zan Dawo..!
Abba ya kada kai yana Fadin"Allah ya kaika Lafiya Daada nada manyan Baki..!
Imran yaji Dadi da Abba bai kara Cewa komai ba ballatana ya Tambayessa me zai je yi wajen Daada yana Haararan Yusuf Dake Dariya ya Shige Dakinsa da Haushin Inteesar ta Kauda kai taki yarda su hada ido wai itana nan taji Haushi ne ko..?
Karamin Tsaki yaja yana jin Takaichi ya Riga yagama Shirinsa gobe sai Dukku waya ya Dauka ya Turama Intee Sako.

"Yayi miki kyau Tunda nine kike Turama baki kina kauda kai baki san ganina..!

Ba Dadewa ta bashi amsa da Cewa

"Eh din..Gobe zakaje kaga Amaryanka ina Ruwanka dani..!

Sai da ya waro ido Daya ga mganarta Dariya ta kamsa Yarinyar nan ta gama Rainasa cikin gatse yace mta

"Kamar kin sami ta Abuja zan sauka ko kina da sako wajen Amaryan tawa..?

Ya tura mata Sakon yana ta Dariya Har yana jin Sautinta yasan ya gama Kunno yar shagwaban kamar ya sani Dataga sakonsa sai da Zuciyarta ta Buga Saboda Takaichi da Kishi Cik?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
in Tura Haushi ta Turamai.

"Ka gaisheta..Ango mijin Amarya..In kaga Nawa Mijin ka isar mai da Sakon i Miss Him Khamis Kabir Dukku nake nufi.."

Ai sai nata yafi Zafi Daya sakon nan kamar yayi Bindiga kiranta yayi taki Dauka sai yaji kamar Zuciyarsa Zata Fito Saboda Kishi Wai Mijinta..? Lalle nema to ba sai ya zama mijin nata ya gani ba haka yake ta Fada yana Sakin Tsaki.
Itama chan bangaranta haka tayi ta jan Tsaki tana kunkuni ita kadai Daga Karshe ma barin Falon Tayi,Ta shige Ba wanda ya Lura da yanayinta sai Munari ga Dariya ga Tsausayi..
Tana shiga Daki Ta Fada kan gadi ta saka kuka ranta na kuna Afili ta Furta"To ni ina ruwana ya ma je su Tare tare achan babu Abunda ya Dameni..!
Take Fada Cikin tura Haushi Lokaci Daya ga Hawaye Munari shigowarta kenan taji Abunda Intee ke fada Ssi ta bata Tsausayi bata nuna mata taji ba ta Basar ammh Tana Lura da ita bata wani samu barci ba Bini bini ta juya ta saki Tsaki shi kanshi Imran din Rabi da Rabi ne barcin nasa kowa ya kwana da Takaicin kowa.








*Shakira*
3/22/22, 23:15 - Ummi Tandama???i: *GMB2??T??12*

*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*


Da garin Allah ya waye saboda ita da Safe yazo ya Tsaya a Haraban gidan Saboda yasan suna da makaranta yau da safe so yake ya ganta kafin ya tafi.
Sai dai duk yadda yaso Inteesar da suka Fito ya yusuf zai kai su kafin ya wuce wajen aiki bata yarda ta Hada ido dashi ba,Duk yadda yayi kokarin haka yaga Idanuwanta sun tasa alamun Tasha kuka jiya da Dadaddre..
Munari ce kadai ta gaisheshi Inteesar kuwa Mota ta shige Fuskarta ba Fara"a ko kadan ta maida ma kanta wani gefe Ran Imu ya sosu yaji ba Dadi yau shine Intee bata son ganin Fuskarsa abun is so painfull acikin Ransa.
Ya yusuf ne Daya fito ya gansa Tsaye Jikin Mashin dinsa ya Hade Hannuwansa Saman Kirjinsa kamar ko yaushe Kallonsa yayi yana Fadin"Yaushe zaka wuce ne..?
Kai Tsaye Imran yace"Yanzu..!
Yafada Kan Sa tsaye Kuma Duka Kallonsa naga Inteesar wacce ta maida kanta gefe batama yarda ta Dago ba ballatana su hada ido ba duk da ta Lura ita yake kallo kuma jikinta ya bata Wadandan Kafaffun Idanuwansa suna kanta ne.
Ya yusuf yayi sakake yana kallonsa Kafin yace"Yanzu..?kuma kake Tsaye anan ba wani Shirin Tafiya..?
Imran gajiya ma yayi da mganar Yusuf ya barsa yaji da abunda ke gabansa mana bai ce mai komai ba ya Taka zuwa Cikin Falon ko waige Yusuf ya Bisa da kallo kafin ya Tabe bakinsa sai alokacin Inteesar tabi bayansa da kallo Cikin Samun Sukuni da Salamar Dake Tattare da ganinsa din Munari na Gefenta Tana Lura da Komai acikin Ranta tace Allah Sarki Soyayyah..
Yusuf shima Shigowa Motar yayi ya Kunnata yayi Riverse suka Fice Daga Haraban gidan.

Suna Tafiya ba Dadewa Imran ya Fito Cikin Shirin Tafiya yayi shigar Riga da Wando Rigar Fara ce mai Dogon Hannu Tana da Layin Baki ajikinta Sai Wandon Jikinsa baki ya kamasa daga kasa Kadan kafarsa sanye Cikin Bakin Takalmi Sawu Ciki na Fatar Damisa,Ahannunsa na Hagu sanye da bakin agogon Fata na Kamfanin Rado Kan nashi yasha gyara,Bayansa ya Rataye da Jakarsa baka ta baya kamar ta yan makaranta Bawani Kure adaka yayi ba ammh ko sau Daya ka kallesa sai ka kara kallonsa Cikar Zatinsa baiwa ce Daga Allah kwarjinsa da Kyansa kuma Hallitace ta Ubangiji Duk Takamar mace da Kudinta da Iliminta in Imran ya Tsaya a gabanta ya Kalleta ido Cikin ido sai taji ta Raina kanta da Duk Abunda ta mallaka Maza kuma yan"uwansa Dole in suka kallesa sai sun kara kallansa sun kuma Tabbatar ma kansu Babban Goro sai magogin karfe.
Ko afitowar da yayi Abba Dake kan Dining yana karyawa Sai da ya Dago ya kallesa acikin ransa yana Kirari ga Allah mai gagara Misali da ya Hallici Imran a yadda yake,Safiya ma Dake Zaune afalo bayan ta Rako Yusuf ne ta Jabe anan tana Hutawa ta kasa karisawa Shashenta Cikinta har ya Fito Domin ya Shiga watansa na Biyar,Itama Dake Zaune sai da ta kallesa ta kuma Jinjina Kwarjinsa Ya gaisheta ta amsa mai Cikin Sakin Fuska yana gaisheta Wani Lokacin In suka Hadu Gab da gab ammh fa baya Binta ya gaisheta in sun hadu shima din yana Cikin Mood mai Dadi in Ransa na bace kuwa baya bi ma ta kan kowa.

Wajen Abba ya karisa ya dan Rankwafa ya gaisheshi Abba ya amsa Cikin Sakin Fuska yana Fadin'Bakon Daada..badai har an fito ba..?
Imran na Shafa keyarsa yace"Na fito Abba..!
Abba yace"To haka zaka tafi baka ci komai ba..?
Imran ya Girgiza kansa yana Fadin"A"a Abba bana cin wani abu in zan yi doguwar Tafiya..!
Abba ya jinjina kai kafin ya kallesa yana Fadin"To kana da kudi a Hannunka ne..,?
Imran yadan yi Mirmishi kafin yace"Kada ka damu Abba..!
Abba yace"Dole na Damu mana..Zaka gane gidan kuwa..?kadai kula da kanka kaji ko in baka gane ba ka kirani!
Imran da ya Murmusa sai da kyakyawan Fararan Hakoransa suka Bayyana ya Mike yana Fadin"Abba am not a Boy fa..?Nasan abunda nake yi..Zan kiraka da Zarar na isa Dukku ku gaisa da Daada..!
Abba yace"Shikenan Allah ya kaika Lafiya Daman mun yi mgana da ita da Safe bam ma gayamata zaka zo ba..Nasan Zataji Dadin ganinka..!
Kai Imran ya Kada bai yi mgana ba suka kara yin Sallama da Abba ya Fice bayan ya Fadaamai Sagir zai kaisa Tasha da mashin dinsa Zai bar mai Mashin din a wajensa har ya Dawo Abba yace hakan yayi nan ya fice Abba da Safiya suka bisa da Faten isa Lafiya.
Yana Fitowa ya Hau mashinsa ya Fice Daga Gidan Iro megadi ya bisa da Allah ya Kiyaye Daman sunyi Waya da Sagir Tun jiya da Daddare,kuma da Safan nan sun yi mgana yana Kofar gida yana Jiransa,yana zuwa Sagir ya Karbi Tukin Mashin din Imran ya Dawo baya ya zauna suka tafi Tasha koda da sukaje Motar Gombe suka Tarar ta kusa cika Sai Imran yace bari ya Hauta in yaje Gombe sai ya Hau Mota ta karisa dashi Dukku.
Akwai kudi a Hannunsa Sauran kudinsa Bankinsa ya Ciresu Saboda Tafiyar nan,20k ya Cire ya bar 10k agida Saboda akwai abunda zai yi dasu in ya dawo 10k ya Sako a Aljihu Saboda Tafiyar nan
Kafin Motan ta karisa cika suka Tsaya nan Gaban Motan suna Mgana Sagir ya kallesa yana Fadin"To ita Inteesar din tasan zaka tafi Dukku Saboda ita..?
Imran ya bata rai Cikin bayyanar Bacin Ransa yana Fadin"Ita Datake Fushi Dani..!.
Sagir ya kallesa cikin Mamaki kafin yace"Fushi to me kayi mata..?
Imran ya mele baki ya fara bama Sagir Labarin abunda ya Faru ya Karishe da Fadin"Kaji fa wai yarinyar nan ni zata Rubuto ma wai khamis Mijinta..?ni fa ta rainani yarinyar nan Naji dama sanda take fadin haka tana kusa dani na Daki bakinta sai yayi Jini nan gaba zatasan me zata rika gayamin Tunda ni ba sa"an wasanta bane..!
Yafada Cikin bayyana jin Haushinsa Sagir kuwa Dariya ta kamashi Har da Dukawa Imran ya Bisa da kallon Takaichi yana fadin"Kai fa Banza ne..!
Sagir ya Dago Daga Dariyan Dayake yi yana Fadin"Ban ga Laifinta bafa..wayace kace Sajida Amaryarka..? Ashe ba Dade ai kuma ta baka amsarka Daidai da mganarka..Wow..wannan Salom Soyayyar taku ta fara Burgeni kuna son juna ammh Dukkan ku baku sani ba,Inteesar Tana sonka Shiyasa take Kishin Sajida kamar yadda kake Kishin Khamis..!
Yafada yana kara Sakin Dariya kallonsa Imran yake Cikin Nazarin mganarsa Cikin mamaki yace"Itama Tana Sona..?
Sagir ya gyada kai yana Fadin"Am Very Sure..Itama Tana sonka kamar yadda kake sonta..!
Shuru Imran yayi bai yi mgana ba yana Jujjya mganar Sagir Cikin Dakuna Fuska yace"Ni ai ba sonta nake yi ba!
Sagir ya kallesa yana Dariya yace"Allah ko..?
Imran ya Hararesa yana Fadin"Kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login