Showing 138001 words to 141000 words out of 236322 words

Chapter 47 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

764

Nace ni nace ina sonta balle kazo kana gayamin mganar banza..Har Abada wannan yarinyar bata isa Imran ya sota ba Domin bata kai wannan mtsayin ba..Kuma na Rantse da Allah daya Halliceni in ka kara Cewa Inteesar taka ce sai nayi maka Dukan Mutuwa acikin gidan nan..Bazata taba zama taka ba Har Abada..!
Ya karishe Fada yana Kumfar baki,Khamis da shima idonsa ya Rufe ya Mike jikinsa na mazari ya Fara Ture Imran yana Fadin"Kaima sonta kake yi kenan..?mallan sai ka Fadamin kishi kake yi domin na Tabata? To baka isa ba Inteesar da kamilalle ta dace ba Dan iska Sauran Shaye. shaye ba..Gashi na Riketa in baka Min Duka ba wlh baka Haifu Cikin uwa da u.!
Bai gama Rufe baki ba Yaji Saukar Naushi a bakinsa yana kokarin rike hannun inteesar yaji wannan Dukan Daya sa sai da ya Duke yana Dagowa Bakinsa ya fashe sai jini Ya duba ya gani Hankalinsa ya tashi ya mike shima yakai ma Imran duka shima abaki shima nan da nan bakinsa ya fashe ganin yadda suka Fitar ma da kansu Jini yasa Zuciyar zaratan maza ta Fara Zalzal akan kishi Batare da bata Lokaci ba suka Sarke da Mumman Dambe Kowanne yana Dukan Dan"uwansa duk inda ya Samu da Karfin da Allah ya basu..
Inteeasar ta Dora hannu asaman kanta ta kwarara ihu dayaja Hankalin Megadi Dake bakin get ya Zuro da gudu ganin abunda ke Faruwa,yana kokarin Rabasu ammh ya kasa Inteesar ganin haka yasa ta Nufi Cikin Falon gidan tana Ihun Kiran sunan Daddy da Abba.
Wanda daman duk suna zaune afalon suka fara jin Hayaniya sai ga Inteesar ta shigo tana kuka tana Haki Lokaci Daya tana Kiran sunan Abba da Daddy gabadayansu suka Mike Har wadanda ke Daki sai da suka Fito,Cikin Tashin Hankali Abba da Daddy suka Isa ga Inteesar suna Tambayanta meke faruwa Cikin Tashin Hankali..
Tana kuka Tana nuna musu waje Cikin Rawan baki take fadin"Abba...Abb..Imran..!
Hankalin Abba ya tashi ya Riketa yana Fadin"Ki natsu Inteesar Ki Fadamana me ya faru da Imran din..?
Inteesar ta girgiza kai Cikin Muryan kuka tana fadin"Abba Imran suna Fada da Khamis a waje..!
Ido kowa ya zaro Cikin kidima kafin kowa yayi waje da sauri Abba kamar zai Fadi harta su Munari ba"a barsu abaya ba Baffa Kabiru da Mami Asma"u dake cikin Daki tanamai Rigiman gobe su koma Abuja sukaji kukan Inteesar suka Fito agabansu ta Fadi suna Dambe da Khamis ai Mami Asma"u kamar ta Kife Glass din Idonta na neman ya Fadi ta Fita Haraban Gida kamar ta Kifa Saboda Razama Harta Daada sai da ta Fito Falo jin wannan al"amarin Jikokinta Guda Biyu suna Fada da junansu.
Yadda suka Fita suka iske wannan Fadan ya tashi Hankalinsu Cikin Lokaci sun jigata junansu,Khamis yana da karfnsu na Sojoji Shi ma Imran yana da karfi ga Zuciya Duka Idanuwansu sun Rufe basaaji basa gani.
Abba da kansa ya Rike Imran da karfi Shida Yusuf da Sagir da Basheer Daddy kuma da Su Sa"id suka Rirrike Khamis suna sun hada ma kansu jini da majina,Matan masu Rauni sai kuka Irinsu Munari dasu Hafsah Mami Asma"u hannu ta Dora akanta tana Ihu Tana kururuwan Fadin Imran zai kashe mata yaronta Harta Sajida sai ta Fito sai kuka Baffa Kabiru Shima yana Cikin masu rike Khamis ganin yadda yake Zillo yana neman kwace kansa.
Imram ma haka yake cida yana zillo kamar wani kadan Ruwa ammh su Abba suka Dannesa.
Daddy ne ya Daka musu tsawa yana Fadin"Kai meye haka.?Meke Damun ku ne..? Kuzo kuna Dambe kamar Wasu yara abunda kannenku zasu yi ku yi musu fada ammh ku da kanku Zaku Zauna kuna Fada da junanku..ku Sake su naga wanda ya kara Taba Dan"uwansa in ya isa..!
Ya fada Cikin Bacin Rai Sakinsu akayi suka koma suna maida Numfashi Imran ya Lakato jinin Dake gefen Bakinsa yana kallon Khamis yace Cikin Muryansa"Ba shikenan ba..Tabbas in ka kara maimaita kuskuran da kayi Wlh..Sai na Maka abunda yafi wannan..!
Yafada yana Haki Khamis din Shima Yana Hakin yana Lakatan jikin Dake gefen bakinsa yana Fadin"In kafasa..Ai basai na kara ba..Mu Cigaba mana Uban wa kike tsoronka..!
Yafada Cikin bacin rai kokarin kara Hadewa suke Mami Asma"u ta shiga Tsakaninsu Tana Fadin"Khamis zan ci Ubanka in baka bari ba..In shi bai da Tarbiya kai baka dashi ne..?
Tafada Cikin kuka Sai ya koma ya tsaya yana Maida Numfashi,Imran kuma kallon Mami Asma"u yake kamar yayi ta Dukanta sai dai ya Taushi kansa,shima Numfashin yake Saukewa.
Inteesar da Munari sun kamkame juna suna ta kuka Kowa abun baimai Dadi ba Mami Asma"u taja Hannun Khamis suka Nufi Falo Yusuf da Sagir suka kama Imran zuwa Cikin Falon Su Abba suka mara musu baya sauran ma Haka Daada na Falon tana Jiransu Ranta Duk ya baci Umarni ta bata Kowa ya nemi waje ya Zauna ya"yanta suka matsa gabanta.
Ta shiga Fada ta Inda take shiga bata nan take Fita ba Ta nemi jin ba"asin me yafaru Khamis ne ya iya maida mganar Imran kuwa kala bai ce ba yana Gefen Sagir yana Sauke Numfashin Alamun Fushin bai gama Sauka ba.
Khamis ko kunya yana Fadin Saboda ya Rike ma Inteesar hannu yasa Imran yace zai mai Duka Mami Asma"u Cikin bacin rai tace"Ya zata kaima Kanwar lasa ne da zai Latsa ka yaga Jini..D"ana Soja ne yasan Me yake yi..Kuma Daya rike mata hannu ina Ruwansa Wht is dey a taba hannu ai yar"uwansa ne bai kamata ya shiga ba Kowa anan Wajen yasan Imran bai da Gaskiya adauki mataki ko ni na Dauka bazam yarda adakeni kuma ahanani kuka ba..!
Take Fada Cikin Bacin rai ba Zato ba Tsammani Imran ya Dago Jajayen Idanuwansa yana kallonta kafin yace"Waht is dey a taba Hannunta..?Shi Ubanta ne ko Muharraminta da zai Rika taba ta duk sanda yaga Dama.?ba Soja yake ba ko Shugaban Sojojin Duniya ne in ya kara Tabata sai namai Abunda yafi wannan Sakarai kawai..!
Yafada yana cije bakinsa Cikin bayyana yadda Ransa ke kuna.
Sai kowa ya koma Binsa da kallo Umma Tayi kasake tana kallonsa Ranta yayi mata Fari domin da Farko Ranta ya baci yadda Mami Asma"u take nuna bakomai bane Abunda Khamis din ya aikata Hakama Daddy sai da ya Murmusa Abba zai yi mgana Daddy ya hanasa Domin kalaman Imran mganace mai kyau kuma yaji Dadinta Inteeear y'ace mafi soyuwa gareta Bazai so wani yaci Zarafinta ba ya Tabbata Indai Tana da Dan"uwa irin Imran bai mai iya cin Zarafinta bai Rama mata ba Hakama Ya Basheer aransa yana Mamakin Wasu Mutane meye na rike mata hannu? Har yana nuna ba wani abu ai koda take yar"uwansa hakan bai dace ba.
Sajida kuwa kallon Imran take shi baima san da ita ba,Tana Fadin acikin Zuciyarta Meyasa shi ya Rike ma Inteesar hannu jiya..?Shi din Muharraminta ne inda zata iya da sai Tayi mai wannan Tambayar sai dai bata da wannan kwarin gwiwan.
Daada ita kanta taji Dadin mganar Imran Dole ta hana Mami Asma"u mgana Tayi ma Khamis fadan Abunda yayi bai kamata ba kansa na kasa yace"Daada nifa bada wata Manufa nayi hakan ba..Ina son Inteesar..Kuma neman Damarta nakeyi ta amince na gabatar da mganarmu wajenku A tsaida mana Lokacin Aure..!
Gabadaya sai Falon ya Dau Shuru Mami Asma"u baki ta saki Cikin Takaichi Tana kallon Khamis Baffa Kabiru baice komai ba Domin kansa ya Kulle,Abba ya kalli Daddy shima ya kallesa Umma ma ta Dago Tana kallon Daddy domin taga yaya ya karbi mganar sai dai Inteesar ta bata amsa Domin Cikin kuka ta Bude baki tace bata son Khamis kuma bazata auresa ba Daddy ne ya tsawarta mata abunda bai Taba mata ba Tsawa Dole tayi shuru ta koma Tana sheshhekan kuka.
Daada ta Dade batace komai ba Sai Daga Karshe tace Khamis ya Nemi so wajen Inteesar in ta amince su basu da Mtsala saboda acikin Ranta Taana Tunanin kada ta karayin kuskuran da tayi yau dinnan na Hada Auran Imran da Sajida Saboda a abubuwa su Daidaita sai dai Tun Daga jiya zuwa yau abubuwa suna Faruwa marasa Dadi wanda suka sata ta Fara Tunanin anya batayi kuskuran Hada wannan auran ba..?Tana ganin kamar wasu abubuwan marasa Dadi zasu kara Faruwa nan gaba Shiyasa ta ce Khamis ya nemi Yarda Daga Wajen Inteesar in haka ta Faru zata fi kowa jin Dadin Jikokinta sun hada kansu.
Baffa Kabiru ya mike ya nemi Izinin Daada na komawa bakin aiki gobe tace ta bama Kowa Damar tafiya gobe in Allah ya kaimu sannan mganar Sajida da Imran kuma wannan yana Wuyan Imran din.
Mami Asma"u ta Bude baki tayi mganar Karatun yarta Tana Fadin bamai yanke ma yarta Karatu Daada tace Ai ba wanda yace zai yankemata Duka wadannan Tsaran Tsaran za"ayisu Daga baya.
Daddy ya mike yace Sati mai zuwa sun yi mgana da Daddy zasu je Lagos chan gidan da suka baro dashi da Yusuf da Imran din sannan zai Tura Cv dinsa anan Jami"ar Bayero Ko Allah zai sa za"a Dace Tunda Abba ya Nuna yafi son Zaman kano Fiye da Lagos.kowa yayi na"am da mganar Daddy saboda Abba da Sauransa Tabbas Jami"a zata amfana da iliminsa Ita da Dalibai.
Kana Daga Karshe Daddy yace Imram ma ya kawo Takardunsa yana da wani aboki Dake aiki a First bank nan Resshen kano kuma Manager ne insha Allahu komai zai yi Daidai agaban kowa da kowa nan take Imran yace shi bayaso bazai yi aiki kuma baya Bukatar Taimakom kowa Sai da Abba ya Daka mai Tsawa yace kada ya kara Mgana Dole yayi shuru.
Daada taji Dadin mganar Daddy ta Dinga sakamai albarka Mami Asma"u sai Hararansa take gani take duk wannan abubuwan Dayake yi na Munafunci ne,Ta kalli mijinta Dayayi Shuru bai ce komai ba ita hakan yayi mata Daidai Kada ya ce komai Suje su karata,Gabadaya zuwansu Dukku ba Alheri bane a wajenta Gabadaya Ranta yana bace ne,Allah Allah take Su bar Dukku kamar tana kan kaya.
Daada bata yarda Taron nan ya Watse ba sai da Ta Saka Khamis da Imran suka Nemi yafiyan juna Bayan tayi ma Imran Fadan Kai ma Khamis hannu Da yayi har suka Fara kokawa ta saka Sunyi musabaha da junansu Azuciyar khamis yaji komai ya wuce ammh banda Imran Da abun ke cikin Ransa.
Koda Taron ya tashi Zuciyar kowa ba Dadi,Inteesar da su munari suka Kule Cikin Dakin duk Tambayan duniyan nan sunyi ma Inteesar taki yadda ta Fada musu komai Dole suka kyaleta.
Mami Asma"u kuwa ita da ya"yanta Tayi ta ma Khamis Fada kamar ta Dakesa sai da Baffa Kabiru ya tsawarta mata kana tyi shuru Sajida na gefe ita da Umaima Mami Asma"u ta Umarce su da su hada kayansu gobe da Sassafe zasu Dauki Hanyar Abuja
Har garin Allah ya waye Zuciyiyon kowa ba Dadi suna ta shirin komawa Inda suka Fito,Mami Asma"u da ya"yanta kamar suna kan kaya ko Breakafsat bata yarda sun Tsaya sunyi ba Ta mtsama Baffa Kabiru yayi sallama da Daada da Sauran yan"uwansa suka mika Hanya ko Sajida da Daada tace ta bari su gana da Imran bata bari ba ta Tarata suka Shige Mota sai da suka bar Dukku Taji ta Samu natsuwa kadan.
Daga Su Mami Asma"u Sai Inna Maimunatu ita da ya"yanta suka Wuce Bauchi,Sai Hamidan Inna Bintalo itama ta wuce katsina Sai Sa"id mutanen Dutse suma suka Dauki Hanya da Hafsah da suka yi kamar suyi kuka ita da Munari da inteesar Su Abba ne kusan karshen Tafiya Domin sai da Daddy daya Basheer da Umma suka mika bayan sun bar musu Inteesar zasu koma kano da ita saboda makaranta.
Suna wucewa suma sukayi Shirin Tafiya Imran dai Tun Abunda ya Faru jiya bai kara ma kowa mgana ba kamar Wanda aka Dinkemai baki Sagir har gaya gaji damai mgana ya kyalesa Kowa yayi sallama da yan"uwa banda shi,Ko Daada bai ma Sallama ba gani yake duk itace ta jamai wannan Bacin rai baima son ganinta Haraban gidan ya Fita yana Rataye da Jakarsa yana cika yana batsewa.
Abba tare da Sadam Zasu mika Tunda duka kano zasu nufa,Sadam da Imran Dake gefensa agaba Matarsa Aneesa da ya"yansu Waleed da Waleeda sai Sagir suka Fara Mikawa sai Yusuf Dake driving Abba na Gidan gaba,Sai Munari da Inteesar da Anty Safiya Dake gidan baya Imran yana ganinsu yace bazai shiga Motar ba ya gwammace ya shiga ta Sadam ba ya son ya Zauna kusa da Inteeaar Baya son ganin kwanyan idanuwanta kallonta kadai kasala yake sakamar so yake yayi yaki da koma meke Damunsa bazai bari a Fahimci Rauninsa ba.
Su Imran su suka fara yin gaba kuma sun Riga su Abba isa kano,Har Gida Sadam yakai sa har sai da yadan Jira su Abba suka kariso kana sukayi sallama ya kama Hanyar gidansa Dauke da matarsa da ya"yansa.
Tuni imran ya shige Cikin Gida ya Fada Dakinsa ya maida koda Sagir bai shiga ba Daganan yayi ma su Abba Sallama ya wuce gida Domin ya Shaida Mama, Dawowarsu Inteesar bata Bisa ba Tunda itama yanzu Gidan su Munari kamar gidansu yake Munari tabi Zuwa Dakinta gabadayansu duk sun gaji ammh Inteesar Rabin Hank????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
akinta na kan Imran Data gansa wani iri Har Sako ta Turamai kuma yagani bai bata amsa ba gabanta Fadi yake tana Fatan Allah yasa Fushin Khamis bai shafe ta ba.
Sai da sukayi wanka suka yi salla suka Huta kana munari da Inteesar suka shiga suka sama musi Abunda zasu ci.
Zuwa Dare kuma Kowa ya isa Gidansa Lafiya.
Ta wayar Yusuf Abba ya Kira Baffa Kabiru da Daddy yayi musu ban gajiya Harda Inna Maimunatu itama ta isa gida Lafiya Inna Bintalo Tana Dukku sai gobe zata koma ita.
Daddy da Abba sun Dade suna Tattaunawa kan Tafiya Lagos Sati mai Zuwa da yardan Allah Rayuwa Zata Inganta Ranar da Daddare Mama Sagir ya Rakota tazo ma Abba Murna da ban gajiya,Taga kowa banda Imran wanda tunda ya shiga Dakinsa bai Fito ba ko Sallah aciki yayi abunsa Da Mama Zata tafi ta Dunga ma Inteesar tsiyan Taga Gidan Abbanta Ta gujeta Inteesar na Dariya tace gobe Zata dawo Munari ta Daka Tsalle tace kafarta kafarta Abba yace ko"ina suka zauna Duka Gida ne shi bai da mtsala.
Washegari da Safe Yusuf ya Tafi aiki Munari da Inteesar suka shiga makaranta saboda ana ta Karatu an Wucesu Safiya kadai ce agida Tana aiki sai Abba Imran na Daki sau Daya ya Fito da Safe ya Hada Tea yasha yagaida Abba ya Dauki Ruwa ya koma Cikin Daki.
Da wuri Yusuf ya Dawo Daga Wajen aiki ya Siyoma Abba Sabuwar waya Saboda ya fara amfani da ita Abba yaji Dadi ya Dinga sakama Yusuf albarka suma su Munari sai yammah suka Dawo Daganan wajen Mama suka Sauka Munari ta Kira Ya Yusuf ta Fadamai yace bakomai.










*Janafty*
3/22/22, 23:14 - Ummi Tandama???i: *GMB2??T??9*

*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*


*After 1 week*
Kimanin Sati Daya kenan da zuwansu Dukku,Imran har zuwa wannan Lokacin bai warware ba Ya daina ma kowa mgana Abba ne kadai daya zama Dolensa yake Fitowa ya gaishesa da Safe,duk da kowa ya sanshi da Rashin son shiga jama"a ammh wannan karon abun nashi ya Taba zuciyar wadanda ke tare dashi,ganin ko Masallaci ya daina zuwa na kusa da Gidan su Sagir sai ya koma zuwa wani karamin masallaci na chan gaban gidansu Tunda suka Dawo Daga Dukku ba wanda yaji kalma Daya Daga Bakinsa bayan gaisuwa.
Abun ya damu Yusuf har sai da yayi ma Abba mgana Domin har ga Allah shima yaga baiken Daada akan wannan Hadin a yadda Imran yake Gudanar da Rayuwarsa auran Hadi bai Dace dashi ba kuma bai Chanchanta dashi ba.
Kamata yayi ya samu wacce yake so tana sonsa ahakan Za"a samu Riba kan Riban abunda ake nema ammh a yanzu da kunci ya kara Dabaibaye Rayuwarsa zai iya koma Fiye ma Imran din da suka sani abaya,Shan Taba kila Har ya Fara kora wasu kayan Mayen in ya Damuwa tayimai yawa Har acikin Ransa bai da yadda Zai yi ne ammh Tabbas Hadin nan na Daada ko alama bai kwantamai ba Duk da Sajidan bata da wani aibu sai dai A kallo Daya da yayi mata yasan bazata iya Zama da Imran ba bata dace dashi ba.
Abba Dayaji bayanan Yusuf shi kanshi ya gamsu kuma Daman yana Cikin Damuwar haka din ne sai dai bai bari Yusuf din ya Fahimceshi ba Sai ya nunamai ya kyalesa babu Abunda zai faru dashi Fushi yake na wani Lokaci in Abun ya sakesa zai Wartsake,Ya nuna ma Yusuf kada ya sake ya Tari Imran da wata mgana Saboda bayaso kuma abubuwa su Dawo baya Yasan Halin Imran ciki da Waje shi ya Haifesa ya kuma Tabbata shine kadai weekness din Imran in ba shi ba bai ga wanda ya isa ya Rika Lamkwasasa yadda yaga Dama ba Shi kanshi yana jin Tsausayinsa sai dai Abun nan da Hausawa kan Fadi kaki naka Duniya tasoshi hakan da yake yi Shine Daidai in Imran ya gane yana Tsausayinshi to zai yi amfani da wannam Damar yayi abunda yake so Shi kuma bazai barsa ba Yana da Sanyin Hali yana son Mahaifiyarsa da ya kwashe Fin shekaru uku bai sata a ido ba karon Farko bayan sun Hadu ta bada Unarni kan Abunda ya Haifa bai isa ya Taka wannan Umarnin ba ko shi baya Taka Umarnin Daada ballatana Abunda ya Haifa Shiyasa Daga shi Har yusuf suka Zura Mai ido Bawanda yace mai kala kamar yadda Shima bai damu yace dasu wani abu ba..
Ammh acikin Ransu suna Fata damai addu"an Allah ya sassautamai koma Miye ke Damunsa acikin Zuciyarsa.
Bayan Abba da Ya yusuf Inteesar ma tana Cikin Damuwa wannan yanayin da Imran ke Ciki Tunda suka Dawo bai kara yarda sun hadu ba Tayi ta Turamai sako zai gani zai karanta bazai bata amsa ba,Datagaji sai ta Fara Kiransa nan ma sai ta gaji da Ringing bazai dauka ba Daga karshe sai ya Kashe wayarsa Inteesar ta shiga Damuwa sosai na Rashin Sanin Halin Dayake ciki ga Karatun makaranta yayi Zafi sai ta fara Rama atsaye gata Daman ba wani kauri ba,Duk yadda taso su hadu hakan bai samu ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login