Showing 195001 words to 198000 words out of 236322 words

Chapter 66 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

751

Dawo saboda Mutane yana Gidan Sadam shima.
Sai sauran Motocin kuma zasu Dauki Sauran Mutane.
Sai Kiran su ake yi Hall din mai suna Mina Event Center fa ya Cika Damkam da Mutane su kadai ake jira,Imran na bayan Mota ya Hakimce yana jiran yaga ta ina Inteesar zata Bullo..?
Ai kuwa yayi kyakyawan gani Domin Sanda yaga su munari sun Fito da ita baki ya saki yana kallonnta baisan Sadda ya Furta masha Allah ba Saboda yaga tayi sanyayyan kyau mai Cike da sakama zuciya Natsuwa.
Har Cikin Motan suka Rakata suka Sanyata Kusa da oga Imu wanda suna karisowa ya Dauke kai kamar baya kallonsu Munari ce da Hafsah suka gaisheshi da Dakyar ya amsa.
Aransu sukace kamar Dole..?
Sai da Motar su Sa"id ta Fara yin gaba da Ta Basheer da ta Sadam kana Motar Ango da Amarya ta Daga Khalil da Sagir na gefe Khalil ke tuka motar.
Suna Kallon Imran ta Madubi suna Danne Dariya shi baima Lura dasu ba Tsabar Haduwar Intee da kamshinta ya gama Rudasa har bai san ya Riko Hannunta ba Sai ji yayi ta Dago Tana kallonsa Cikin Narkakun Idanuwanta.
Lamgwabe mata kai yayi a Hankali yace"Meyasa baki bar wayarki a Hannunki ba Ahalin kinsan zan kiraki..?
Tana Kokarin Daidaita kanta jin Yadda yake Faman shafa Hannunta Tace"Ni ban ma san inda take ba..Kamar Tana Hannun Mu..!
Dakuna Fuska yayi zai yi mgana suka Hada ido da Sagir ya Ballamai Harara yana Fadin"Munafuki i donsa na kan miji da mata Watarana sai idonka ya Tsiyaye..!
Sagir da Khalil Sai Dariya suke kwasa koda suka isa Wajen su Munari sun kariso suna Waje suna Jiransu ba Bata Lokaci Imran ya Fito Shida Inteesar ba wanda ya bashi Shawara shi yaga Dacewar ya Damke Hannun Amaryan Tasa gam Ransa na kuna in ya Tuna ahaka maza dadama zasu kallemai adon mata.
Sune kan gaba da su Waleeda da akayi ma Kayattacen shiga suna kan gaba tawagan su Munari na baya dasu Sagir da sauran gayyar suna Shigowa wajen ya Dau Sanyayyan Kidan Aure ya Dauru ga Kyali kyali na Sauka ta Ko"ina Waje ya Cika Damkam da Jama"a Imran bai saki baki ba sai da yaga Dimibin Abokan aikinsa A Wajen Har Mr Sulaiman da Mr Tunde,mamaki ya Kamashi su kuma sai dai suka Dagamai Hannu Suna Zama Inda aka Tadanar musu MC ya Fara Jawabi,Saboda Dare yayi kuma Imran ya bada Sharadin in aka Wuce 11pm Wlh zasu Nemesa su Rasa Susan Halinsa Shiyasa suka Gayana Mc ayi komai Cikin Lokaci.
Game aka Fara gabatarwa Irin dai na Mc,Tun alokacin Imran yaji ya Fara gajiya,sannan aka Umarci abokan Ango ya bada Tarihin ango Sagir da Khalil suka Fito Sagir ya Fara Bada Takaitattacen Tarihin Imran Daya Sani.Khalil ma ya karba ya bada Nashi Wanda ya sani Tun suna Lagos.
Kafin Sagir ya karbi Abun mgana yana Fadin
"Wato Soyayya Tsakanin Inteesar da Imran Wata soyayyace da Bantaba ganin irin ta ba..Makauniyar Soyayya ce da su kansu basu san sun Fadama juna ba in ance yana sonta yace Shi ba sonta yake ba ammh Kusan me..? Baya son kukanta..?baya son bacin Ranta bayason ganinta da wani kun Taba ganin Damben maza..?ku Fadamin soyayyahce ko yan"uwataka ke sawa Namiji yayi Fada kam mace yaji yana Kishin ya ganta da wani Ku Fadamin da karfi Soyayyah ce ko Yan"uwanta ka..?
Gabadaya Hall yadau Ihun Soyayyace Wlh na Love Sai Dariya da ihu da Tafi Imran Hararan Sagir kawai yake yi yakasa mgana Sagir na Dariya yace"Uhm...Harfa Rakata yana yi..
Gadin ta ma yake Wato Mr imran ya Dade dai yana Son Inteesar Daga Karshe Dayaga za"ayimai Kafa sai ya Zabura ya mike ya bayyana kansa ammh fa shi adole bai yarda yana Sonta ba Cewa yake..!
Yakasa karisawa Saboda yadda Imran ke aunamai Harara ga Ihu ya Kaure a Hall din Sagir na Dariya yana Fadin"Ammh fa soyayyar tasu ta Musamman ce..Ina wasa Dake ne..? ni Sa"anki ne..?kin Raina ni ko..? Zan Sauya miki kammani Zan yi kwallo Dake..?To Amarya Inteesar Shaawaran da zan baki a mtsayinki na kanwata Sai kin yi Hakuri kin Dage da Ninka Biyayya ga Girman Miji ga na Yaya in baki yi a Hankali ba Angon naki cikin Kwanakin nan na Amarci zai iya Sauya miki kamanni Ko kuma Gidan ku ya koma Gidan Kwallo da Mutane.!
Gabadaya aka kara Saka Tafi da ihu Imran kallon Sagir kadai yake ya auna yadda zai Yi kasa kasa dashi in suka Kebe Inteesar sai Dariya take kasa kasa yana kallonta.
Sagir ya cigaba da Fadin"To kai kuma abokina sai fa ka yi hakuri..Mata fa yan Lallashi ne duk da kace kai Allah ya kyauta ka Zauna kana Lallashin Mace..!
Khalil ya Karbe abun mganar yana Fadin"Sagir nace Ranar Lallashin bata zo bane..Nace Jama"a ku Fadama Mr Imran Ranar Lallashin bata zo bane..Sanda zai shige Dimuwa yana Fadin Baby Plz mana kiyi Hakuri..!
Ya Karishe Fada yana kwaiwayon mganar Imran ai gabadaya aka Saka Dariya wasu Harda Rike ciki Kai in aka Biyema Khalil da Sagir zasu Kullan ma da Mutane Cikinsu kuma ga ba Lokaci Imran Kamar ya Fashe Sagir da Khalil sun gama Dashi Gaban yara.
Su Yusuf Dariya kamar su kwanta yana kallon Fuskar Imran yana Dariya Nasara aka Kira tazo ta bada Tarihin Amarya Daganan aka bada Lokaci akaci akasha kana aka Fito Filin Rawa Imran duk yadda yaso ya Zille sai da su Sagir suka Fito dashi suka Rika mai barin kudi shi da Inteesar da sauran Dangi aka kuma barsu su kadai su Rausaya Imran dai ko Gyada bai yi ba sai ma Inteesar data dan juya shima bai bari ba ya Rikota yana mata wani kallo Dayasa ta Dataka sai Hall ya Dau sowa da ihu Wajen yanka Cake ma abun kallo ne Imran ai Oga ne Komai nashi na Dabam ne.
Awajen Dinner ma chan na kara Hango gayyar yan GMB2BANDGROUP,da nasu Hadadden ankon Dinner din masha Allah sai Washe baki suke Daga nesa suna Daukan Intee da imu Hoto saboda suna Tsoron su karisa wajen Imu ya Fahimci Hoto suke Daukansu zasu bazama duniya yace baisan Raini zai Sauya musu kammani suna Daga gefe sun kame suna Kallo kowa Daya bayan Daya suna masu Farincikin ganin wannan Ranar da su munari da Sagir kadai suka samu Damar gaisawa sosai.
Anci an sha an sha Rawa an yi barin kudi su Inna Bintalo ana gefe atana Daukan ma Mami Asma"u Video Tana Turamata tana kara Tada mata da Hankali
Sai 11pm aka taahi Imran suka Fara Tafiya sai da suka kai Inteeear gidan Abba kana suka wuce Gidan Sadam,Suka ijiyesa Khalil da Sagir suka juya zasu Dauko su Munari ko mgana bai musu ba ganin suna Rawan kafa kan yaran zai Fada musu gaskiya su kama kansu baya son Raini.










*Shakira...*
3/28/22, 18:34 - Ummi Tandama???i: *GMB2??T??24*

*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*


Karfe 10:00am na safe aka Sada Inteesar da kayattacen dan madaidaicin Gidanta Dake Alu Venue anan cikin garin kano,Ta samu Rakiyan Mama da Maman Nasara da Anty Uwani sai su Inna Maimunatu da su Inna Bintalo da Sauran Tawagan Matan su Basheer da na Anty Safiya da ita kanta suka Sada Inteesar har saman Kayattacen Dakin Barcinta Kan gadonta na Royal bed mai kyau da yarari wanda yaji Shimfidun alfarma sai wanda ya gani bayan sun Umarceta da Tun kafin ta shiga Gidan ta Dafa Ginin Gidan ta karanto addu"an kariya da Zaman Lafiya Acikinsa da Dukkan alherai na Har Abada.
Kafin a wuce da ita Abba yayi mata Nasiha sosai da kuma Fatan Zama Lafiya Tsakaninta da Imran ya kuma Horeta da sai tayi Hakuri Sosai sanin Halin wanda Zata Zauna dashi
An kaita da Wuri ne saboda Za"ayi Walima,Atashi karfe Biyu na Rana akwai Wadanda zasu koma Gida yau Saboda ayyukansu kamar su Khalil da su Sa"id yau zasu koma Gida.
Duk wanda yaga irin Uban Dukiyan da aka Narka a wannan gidan sai kaji yana Sakama Baffa Kabiru albarka ana Fatan Allah ya bar wannan Zumuncin Har gaban Abada,Kowa sai Santin gidan yake Kitchen kuwa shima ya kawatu matuka Umma ce ta Roki alfarman a bar mata Kitchen din Ta gyara a Mtsayinta na Uwa sai aka Barmata Lalle ta Aurar da Autarta Sai wanda ya gani Kayan abinci cike da Store wannan aikin Duka na Daddy ne Ba abincin da Babu aciki Fridge kuwa Cike da kayan Cefene wannan kuma aikin Yusuf ne yasan Waye kaninsa Careless ne sosai kan Abunda ya Shafi Cin Abinci Shiyasa ya gama da Wannan Barayin ya Tabbata Cefanen zai matukar basa Wahala.
Irin su Anty Aneesa da su Fareesatu sai Daukan Hoton Gidan suke su Munari kuwa sai Faaman Daukan Hotuna suke yi ko gajiya basa yi Kowa yana Nuna Murnansa a Fili banda yan Bakinciki irin su Inna Bintalo Har Video gidan sai da ta Dauka ta Turama Mami Asma"u Tana nuna mata Irin Kudin da Baffa Kabiru ya bar nartar kan wanda ya Saki yarsa da Inteesar din da aka yi mishi auran Tura Haushi da ita.
Mami Asma"u Tun Jiya Take kwance bata da lafiya ta gama Sarewa da al"amarin Baffa Kabiru ta gama yarda ya Juyamata baya kuma bai da Niyyar Dawowa gareta,Daada da yan"uwansa sun yi musu Farraku lokacin Dataga Hoton Imran da Inteesar Awajen Dinner sai da kwalla ta kawo mata A zahirin gaskiya Imran bai da makusa ko D'anta Khamis Wlh bazai jera kafada Dashi ba Cikin Maza Dubu Sai an Tona za"a samu kamarsa anya anya ba Gaskiya bane Tana da Sonkai.?ta so kanta da yawa yasa bata Fahimci Babban goron da Allah ya Kashe yabama yarta ba sai Rudin Duniya da hujjarta mara Tushe Ballatana makama ta Ruguza komai ta Bata komai Karshenta itace tayi Biyu babu An Saki yarta Sajida Tana chan Tana Ramewa Saboda Damuwa itama Gatanan Gotai Gotai Da ita Miji ya Saketa ta dawo Gida Zawarci Itafa bata yarda ma ta Fara Kirga kwanakin Iddarta ba gani take kamar Wasa Kabiru yake zai zo ya Dauketa su koma Gida bai Saketa ba.
Da Bintalo ta Turo mata Video gidan Tagani Batace mata komai ba ta Fara Jin Haushinta Taya zata Rika Turo Mata Abunda zai Dagamata Hankali Ita kuma ba wani mganin Matsalarta Zatayi mata ba Shiyasa ta Kashe Wayarta bata son ta Dameta da Tseguminta wanda ta Saba kuma ya Zame mata jiki gwara ita Tana Gidan Mijinta kuma ya"yanta ba wacce aka Taba Saka ta zama karamar bazawara irin y'arta Sajida,kuma duk fa aje a dawo Daada uwa take ga Bintalo kuma kabiru da su Mustapaha Shakikan yan"uwa ne gareta Duk inda akaje ita ce ke cikin Bala"i ba Bintalo ba Shiyasa ta Kashe Wayarta abunda Taji ya Isheta bata Kaunar kuma ta kara jin wani abunda zai yi barazar Tafiya da Numfashinta.
Karfe 12:00pm aka Fara Walima
Malama Juwairiya Anty Safiya ta gayyato an saka Kanofi a Haraban Gidan Duk da bai da Girma sosai an Fito da Amarya Saboda Wa"azin Walimar Aure,Masha Allah Malama ta yi Wa"azi sosai kan Hakkokin mata ga Mijinta da Hakkin miji kan mata da yadda Mu mata zamu gyara Jikinmu Tare da Shawarwari ga Amarya an Raba Snks da Key Holder da Kofuna da Memo karamin Choter,Hanky da Riguna da Jaka Duka Dauke da Tambarin IMSAR FOREVERB??0
{??I0 Duk wannan aikin su Munari ne Snks din kuma aikin Umma ne,naga Tarin Mutane sosai a wajen Har da gayyar GMB2BAND GROUP suma sun Hallaci Wannan Walimar Domin Tabbatar da su Team din Imsar Forever ne.
Sai Karfe 2pm aka tashi Walimar sai aka Fara shirin gyara gidan da kuma Haraman Tafiya abar Amarya a Muhallinta.
Dr Isa Ali argungu sun zo shi da Matarsa Hajiya Barira yima Abba Allah sanya alheri aure da kuma aikin Daya samu yau zasu bi Jirgin Karfe 4pm zuwa Lagos tare da D'ansu Khalil Daga Fagge Suke daman Tunda suka iso suna chan gidan Dan"uwanta Taje Dake nan Zoo Raod ta iske Duka Gidan basa nan yayan nata kadai ta gani suka gaisa duk sun Tafi Biki.
Koda suka zo Gidan Abba ma ba Kowa sai su Imran da shi kanshi Abba Duka suna Chan gidan Amarya.
Bayan sun gaisa da Abba tayimai Allah sanya Alheri tace akaita Ta Leka Gidan Amarya kafin ta wuce Yusuf ya Dauketa Amota zuwa Gidan Tana zuwa suka Hade da Anty Safiya sai suka Tsaya suna kallon juna Baki Sake Anty Safiya Tace"Goggo Barira..!
Hjiya Mero ma ta Kira sunanta itama Cikin mamaki tace"Hajiya Mero..Ikon Allah yanzu nan Da muka Fito Daga Fagge gidanku muka Fara zuwa bakwa nan sai Alhassan kadai muka iske shine muka kariso chan Gidan Dr.Malami ai makotan mu ne,abokin aikin Dr.Ne tare sukayi koyarwa nan Jami"ar Lagos kuma mun zauna ga gida ga gida a Lagos..!
Sai kallo ya koma Sama Hajiya Mero Cikin Fara"a tace"Ikon Allah..Ai Safiya Yusuf take aure..!
Hajiya Barira ta rike baki Tana Fadin"Ikon Allah..Wato auran da Goggo Tace yayima yarsa a Wulakance batare daya Fadama kowa ba ashe ma D'an Gida ta aura Yusuf Duk Tare da ya"yanmu suka tashi. Iyalan Dr.Malami nasu Nagarta ne ni nan munyi Zaman Amana da Mahaifiyarsu Marigayiya zuwaira Allah ya jikanta Khalil kuma Hala baku Hadu bane ai abokin Imran ne yana nan Tun Ranar jumma"a
Hajiya Mero tace"Hajiya yaushe zasu Shaidasa ko ni nan ai na Dade ban gansa ba ko yazo iyakarsa Fagge baya karisowa kece dai in kika zo sai kin kariso..!
Nan fa Hira ta Sarke Hajiya Barira Tace"Ai Dayake ga Karatu ga yanayin aikinsa Banki ne ba Lokacin sun gama Sayarma gwannati..!
Nan fa Aka Tsinke da Hira Anty Safiya sai Nuna Hajiya Barira take kanwar Alhaji Alhassan ce Da goggo da Wacce ta Haifeta Inna Furare Uwarsu Daya Ubansu Daya Zumunci sosai kowa da yaji yayi mamaki matuka Har Bedroom din Inteesar Mommy ta kaita ta saka Amarya albarka Sauri Take yasa Datace Zata koma Mommy tace su tafi Gabadaya suma Daman yanzusuke Shirin Tafiya yusuf na Haraban Gidan yana Jiranta sai gasu sun Fito nan yake jin Sabon Labari yana ta mamaki haka ma su Abba sukaji Wannan mamakin da suka koma Hajiya Mero kam sai jin Dadi take irin wannan Ranar take jiyema Alhaji Alhassan Ranar da zai ji kunya,Hajiya Barira da Dr.Isa Ali argugu suna bada Labarin karamccin da Mutunci irin na Abba da Duka Iyalansa suna Fadin har suka Zauna dasu na Tsawon Shekaru basu Taba Samun Mtsala ba Shiyasa ko yanzu Megadin Dake Tsaron Gidan nasu da Iyalansa DR.Isa Ali argungu ke Biyansa Duk Wata yace ma Yusuf kada ya Damu shi ya Dauke wannan,Tsakaninsa da Abba sai Godiya anyi Zaman Amana da Mutumci
Hajiya Barira da kanta ta Kira Alhaji Alhassan tana Fadamai,Dayake Daganan Filin Jirgi zasu wuce kunya da Nadama suka kara Lullube Alhaji Alhassan ya Godema Allah baya Wajen da wani idozai kalli Yusuf da Abba..?ballatana Imran Daya gama Sanin Duka Sirrinsa.
Yaji kunya sanda Hajiya Barira ke Fadamasa Marigayiya Hajiya Zuwaira Kawartace sosai har Allah ya Dauki Ranta Daga Karshe ta Sanar dashi AhalinDaya bada yarsa kyakyawan Ahali ne mai Cike da Nagarta Alhaji Alhassan dai ba baki Zufa kadai ke Ketomai har suka gama mgana yana Tunanin Allah na son shi Dayake ta Nuna mai Ishara kala kala alamace Ta ya Tubarma Allah kafin Lokaci ya Kuremai in ba Haka ba ya Gujema Ranar da Duniya zata san Halinsa na Boye sai ga Alhaji Alhassan na kuka da Idanuwansa kukan Nadama da danasani Ba shakka Imran ya Cika Mutumin Kirki mai kyaakyawan Zuciya a yadda yake kallonsa bai taba Zata Har yanzu bazai iya Tona mummmunan aikinsa ba sai gashi ko alama yaron ya nuna masa yasan Abunda yake yi alokacin Alhaji Alhassan yaji komai ya Fita kansa Nadama ta Shigesa yadaukan ma kansa Alkawarin ya Daina neman mata Har Abada yana me yin Nadama ga abunda ya aikata a baya.
Khalil kuwa baisan Wainar da ake Toyawa ba sai da ya Dawo Shima Kiransa Babansa ke tayi Lokaci ya Kusa kada su Rasa Jirgi suna chan Gidan Amarya Shi da Sagir kowa yaja Wacce ta shiga Ransa yana Fadamata Sirrin Zuciyarsa Saboda Dama Daya Take zuwa a Rayuwa.
Sagir ya gama gabatar da kansa Wajen Hafsah kuma ya samu shiga kwarai da Gaske sun karbi Lambar juna khalil ma ya gama Sace zuciyar Munari Tuni itama tayi Na"am da mganar na Khalil saboda ai ya gama Haduwa Shima,Tuni suka karbi Lambar juna Duk da kowa nadashi Imran nachan sai Kiran su yake su Hajiya Barira na Jiransa Ya Yusuf zai kai su Filin Jirgi sai da suka gama Kafa Zuciyarsu sai gasu sun Dawo sai Alokacin Hajiya Barira ke nuna mai Hajiya Mero da Anty Safiya,Tasleem ma ashe kanwarsa ce Shiyasa yaga kamar ya santa Tunda shi yama Dade Rabonsa da kano yafi Shekara Bakwai.
Imran sai Hararansu yake yi Shi da Sagir saboda wani Hade kai da yaga sunayi Da yayi mgana Sai su yi mai Chaaa,A gurguje akayi sallama gabadaya acikin masu Rakiyan Har da Imran da Sagir suka shiga Motar Imran din suka Rakasu Filin Jirgi basu Baro ba sai da Jirgin su ya tashi suka Dawo a Mota Imran ya wani Hade rai Sagir ko ta kansa bai bi ballatana ma ya Tsaya Tambayansa.
Bayan La"asar su Inna Maimunatu duk suka dawo Gidan Abba sai gobe zasu Tafi su Maman Nasara kuma Gidan Mama suka yada Zango suna sai gobe zasu tafi Su Munari suka bari agidan dsu Anty Aneesa itama Anty Safiya ta koma Data Raka Mommy da Anty Saratu Tasleem dai Tana Gidan Amarya sai an juma Zata dawo.
Su suka Hadu suka kara gyara Gidan suka Share suka Turare gidan Turaran Wuta masu kamshi da Sanyaya rai Wanda Maman Nasara tazo ma da Inteesar da yaw??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a kala kala bayan na Jiki harda na Daki dana Turara gida..
Sai gabda mangariba suka yi Shirin Tafiya Fareesatu sun fasa Tafiya suma sai Gobe Mazajen nasu suka zo Daukansu zuwa Gidan Abba abar Amarya Ta Huta kafin Ango ya Shigo.
Inteesar da Farko bata Damu ba sai da Taga Tafiyar zasu yi da gaske kana ta Fara Kuka Tana Rike Munari Duk Dauriyan Munari Sai da tayi kukan Sabo hawaye shabe shabe aka Bambare su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login