Showing 231001 words to 234000 words out of 236322 words

Chapter 78 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

753

Daada ta tarasu tayi ma Duka Ma"auratan Nasiha da zasu tafi harda Kukanta Domin Tana ganin kamar Kara Haduwarsu na Mutuwarta ne.
Masu Tafiya Kano Duk Tare suka Dauki Hanya Wajen Motoci Goma Sajida Tayi kuka wajen Rabuwa da Mami da Baffa Kabiru da sauran yan"uwanta Munari ma Tasha kuka ita da Inteesar haka ta kamkame Abba Da ya Yusuf Harta da Imran sai da idonsa ya Sauya ya Rumgumeta yana Shafa kanta Daga Dukku Jirgi suka Hau zuwa Abuja Ita da Inna Bintalo dasu Mami.
Suna isowa kano Mama aka Fara Rakawa Gidanta Shashenta Sai son barka Rakiyan Umma da maman nasara da Anty Uwani da Inna Kaltume Sajida kuma Mommy da Anty Saratu suka Tarbesu,Aranar suka Tafi Fagge ita da Khalil da Umma,sai Gobe zasu bi Jirgi zuwa Lagos Inteesar bata raka Ko Dayansu ba sai Hafsah,Ita da aka kaita Kusa Inna Maimunatu ta mikata Dakinta Tana ta kuka ba wanda suka kwana Kowa ya watse sauran baki suka koma gidan Abba wasu kuma Gidan ya Sadam suka koma suka kwana.
Washegari Talata Kafin su Khalil su wuce sai da suka Biyo Tanan sukayi Sallama da yan"uwa Kafin su Dunguma Gabadaya aka Rakasu Filin Jirgi Zuwa Lagos Umma da inna Maimunatu ne zasu Raka Sajida sai yayar Mami Asma"u Guda Daya.
Inteesar Tasha kuka Data Waiga ba Munari tana chan Abuja Allah Sarki Rayuwa Imran ne da suka koma Gida Yayi ta Lallashinta Tun aranar gabadaya Kowa ya watse aka bar Amaran da angwayen su samu Natsuwa,barin ma Abba da Mama,Sagir da Hafsh suma su kadai agida sun Fara Cin Amarcinsu Umma da Inna Maimunatu kwana Daya sukayi a lagos suka Jiyo Zuwa Kano Domin ai Dr.Ali argungun ya gama komai gabadaya Gidan shi ya kawatashi yace Sajida ya'tace garesa Saboda Malami kuma Shi da Iyaalan Daada ai sun Zama Daya haka suka dawo da Labarin mai Dadi sai Fatan Allah ya basu Zaman lafiya

Daga Kano Inna Maimunatu ta wuce Bauchi ya"yanta suma kowacce ta koma Gidanta Umma kuma bata Kwana ba ta koma kaduna Tunda Daddy da ya Basheer sun koma Shi da Anty Hauwa da Little Inteesar Anty Safiyama Da Imran karami Daya Fara Wayau duk sai sukaji Gidan Shiru ba Gilmawar Abba yana Barayinsa ba Munari sai su kadai Allah yasa ma ga Kirniyar imran karami.
Munari kuma Dagachan Abuja Inna Bintalo kwana Biyu tayi ta so tayi ta Koma Baffa Kabiru yace taa Tsaya ta Raka Munari Dakinta haka kuwa akayi kwanansu Uku a Abuja suka wuce Porthercourt da Rakiyan Inna Bintalo kwananta Biyu suka Hadota da sha Tara na arziki suka Sakota ajirgi sai Gombe Ta koma Gidanta Domin ta Sauke gajiyan bayan ta Kira Duka yan"uwanta tasanar dasu ta Dawo Lafiya ta Raka yarta Munari Dakinta.
Sai da suka Shafe wajen Sati Biyu suna Sauke Gajiya Domin fa an sha Zirga Zirga Munari suna waya da Inteesar da sauran yan"uwanta Inteesat tasha Korafin irin Wahalan da Abokan Mijinta suka gana ma kawayenta Harda Sajida ma suna mgana Ita tabama Imran Labari yayi ta Dariya To Daman Tunda suka auri wadanan Tazuran ai sun gama yawo sai Fatan Allah ya basu Zaaman lafiya ita kanta Inteesar din ai ta gayama aya Zaginta Domin kwanakin nan kaf sai da Imran ya Famshe ita Duk Sauke gajiyan da Kowa yayi bata samu wannan Damar ba.
Allah Sarki Inteesar ita kadai ta Cigaba da zuwa makaranta kafin Transfer din Hafsah ya samu ta dawo nan da Karatu Gidansu Imran ya kara Zama Gida Saboda Mama ta kama su Imran ta Rike gam kamar ya"yanta Abba kuma yahada kan Iyalansa Waje Daya Sagir Daya kasance Dan Gida ne bai da wata Mtsala Anty Safiya na jin Dadin Zama da Mama sosai Gabadaya Renon Imran karami ya koma Hannunta ashashenta yake wuni Ta Tabbatar ita da Abba zasu kwaceshi ne Ita kanta Anty Safiyan in ba Abba ko Ya yusuf ne ya dawo ba tana Wajen Maman.
Sagir ma shi da Hafsah suna Gidan kusan kullum sai da Abba yayi musu irin na Imran yace su zauna Gidansu kada su kara zuwa kana akaji Shiru Gabadaya Imran Dayaji Labari yana ta Dariya Harda gwalo.
Munari ta Bude musu Group isu isu Ita Hafsah,Inteesar, sajida Nasara da Tasleem Nasara itama an saka Ranarta anan Kaduna Zatayi aure wani ma"aikacin NNPC zata Aura Saura Tasleem da itama Zata Fara Karatu anan jami"ar Bayaron Inteesar nata Murnan ta samu yan uwa sunan Group din SISTER"S FOREVERB??0
{,Chan suke Haduwa suna Baza Iskancin su son Ransu suna Tadin mazajensu da yarda zasu kara Zama Taurari a Wajensu da bama Juna Shawara Kowa Tana Fadin in Mijinta na kwararamata Ihun Dadi Inteesar taki cewa komai suna ta Tambayanta To ai in Ta Fada ta gama Tona asirin Ya Imu Daya Dade a Lullunbe bazata so kannensa su ji wannan mganar ba ganin Taki Fada suka Zageta suka Kyaleta ita sai dai Dariya kawai.
Ba Dadewa Hafsah ta samu Transfer ta Fara zuwa makaranta ba Depatment daya suke da Inteesar ba haka ma Tasleem data Fara zuwa sai dai kusan Kullum suna Haduwa Tasleem Direba ke zuwa Daukanta ita kuma Inteesar watarana Imran in yazo suna Tare da Hafsah ya Daukesu Dukkamsu in kuma sun tashi da Wuri kowacce Tayi gidanta Domin sun Fara Biya biyen Gidajen kansu ko na Abba Imran ya Tsawatar yace kowa ta Zauni Gidanta.
Sannu Sannu bata Hana zuwa sai dai a Dade ba"a je ba Gashi har Cikin Inteesar ya isa Haihuwa, Tana zuwa awo a wani asibitin kudi Ciki yayi Kato yayi Girman da bata iyama kanta Komai Allah yasa sun samu Hutun shiga aji Uku Daada Dataji Labarin Halin da Inteesar ke Ciki ta Kira Umma Tace tazo ta Dauke yarta ta Haihu agabanta Imran yaso ya Hana sai dai Abba yayi mai mgana Dole ya Kyaleta Daman ta Zama abun Tsausayi Ciki ya hana komai..
Umma tazo ta tafi da Inteesar ta Dawo gabanta ko kwana Goma batayi da dawowa ba ta Haihu a asibitin Barau Dukku Dake kaduna Yan Biyu ta Haifa mace da Namiji masu kama da Imran Murna Wajen Wannan Ahalin sai wanda ya gani Imran kamar ya Zuba ruwa akasa yasha a Kaduna akayi Shagalin suna Yara sukaci sunan Abba da Anni Wato Abubakar da Zuwaira kuma da Abba da Anni Za"a Rika Kiransu,Hafsace kadai tazo suna Sajida da Munari ba wacce tazo duk da sun so zuwa Munari Laulayi ne ya Hanata Sajida kuma Suna Jarabawa Domin ta Fara Karatunta Hafsah kuma Daman Tana da Karamin Cikinta..
Imran yayi bajinta sosai a Haihuwar Inteesar ya siyamata kyauta Mota karama 206na Murnan Haihuwan yan Biyu nan tayi jegonta Cikin Kulawar Umma da Daddy Kamar ya maidata Intee Ciki su Anni kuwa suna ganin gata Bayan Tayi arba"in bata koma Kano ba sai da ta Zaga Dangi sune har Abuja,Gidan Baffa Kabiru sai da suka Kwana Biyu suka Dawo Taje Bauchi Wajen Inna Maimunatu taje Gombe Daganan ta Karisa Dukku Burin Daada ya Cika ta Dauki Ya"yan imran da Inteesar jikokin Malami da Abubakar Sauran Jikokin Malami da Kabiru.
Har Dutse sai da Inteesar taje gidan ya Sa"id bayan dawowarta Daga Kadunna ammh shi ita da Imran sukaje suka kwana Daya suka Dawo Ta Dawo da Kwana ashirin ta koma Bikin Nasara sai a wannan karom Sajida da Munari suka zo murna ba"a mgana da suka Hadu sai Tashin Hira Gabadayansu suna da ciki banda Sajida Da suke mata Tsiyan ko Tana planing ne tace musu AllaH ne bai kawo ba Dukkansu da mazajensu suka zo bayan Biki kuma kowa ya tasa abarsa suka koma Amarya nasara ta tare agidan Mijinta Dake Malali kaduna.
Inteesar mai Taya Reno aka Daukan mata Wata yar yarinya saboda makaranta Mama ta samo mata nan kasansu take kwana wajen Inteesar din sai Weekend take zuwa Gida sunanta Hanne,Inteesar Tana Wahala sosai ga makaranta ga Renon yaran har Biyu ga Ubansu bai iya Komai ba sai fadan in anyi ba Daidai ba.
Sagir ya gama Karatunsa ya Cigaba da Dinkinsa Tunda aikin bai Samu ba suna dai Cigaba da nema.
Ashekaran suka je Lagos ita da Imran da yaran su an Turasu Seminar Gidan Abba suka sauka ba Hotel ba,Tunda Matan Lurwani maigadi suna kula da gidan ko"ina Tsab,Sati Daya sukayi kafin su gama Seminar,Su Inteesar taje Gidan Sajida suma sun zo musu Har Gidan Dr Ali argungun sunje,Bayan sun dawo Sukaje Parthecourt,Harda Sagir da Hafsah suka gano Munari suka Dawo.

******

*MURFI...*!!!
_AFTER 7 YERARS BACK..._

Bayan Shudewar wasu Shekaru Bakwai da suka gabata Ahalin Marigayi Alkali Dukku ayau ya Zama abun kwantance Baffa Kabiru girma ya kara kamasa Tun bayan Rasuwar Daada Shekaru Biyar da suka gabata ammu bata bar Gidan Duniya ba sai da Ta Dauki Jikokin Malami da Kabiru ta kuma Hada kan Zuru"arta Waje daya kafin ta bar Duniya.
Rashinta ya Girgiza ya"yanta sun yi kuka sosai sai dai kuma sun Dauki Girma da Ragamar komai akansu.
Ashekarun da suka gabata an samu Cigaba sosai ta bangaran Haiyayyafa da Karin Girma ayyukan wasu.
Imran ya samu karin Girma daga Assistan Manaja zuwa Manajan Gt brach Dake Lagos inda ya Taba aiki basu da Mtsalan gida ga Gidansu nan suka gyara ya Kwashi Matarsa da ya"yansu suka koma chan da Zama Sajida tafi kowa murna sun dawo kusa da juna duk da shima Khalil din ya samu karin girma, Shekaru Biyu da suka gabata Tunda ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????Inteesar Ta gama makarantar ta,Su da kano sai in sunzo ganin gida ga gidansu suna da Wajen sauka in sunzo garin.
Bayan Haihuwar su Anni haihuwanta Biyar acikin Shekara bakwai Saboda Gwarne Takeyi Data yaye shikenan sai wani Cikin taso ta fara tsarin Ilyali Imu yace sai ya gani Allah ya Taimaketa Hanne na Tare da ita tana kara Taimaakamata.
Daga su Abba karami tazo Tayi mai sunan ya Yusuf suna Kiransa Boy,Sai mai sunan Daddy Mustapha,sai mai sunan Baffa Kabiru,Sai Sagir da Imran yayi mai Takwara yana Kiransa Friend sai Karamarsu mai sunan Daada kuma mai sunan Inteesar suna Kiranta Afiya.
Ya yusuf ya samu karin Girma shima iyalai sun cika Gida,Abba tuni ya gida wani Gaton gida a sharadi phase 1 sun koma da Mama tare da Imran karami da Khadija diyarsu da suka kwace musu, an kara gyara wannan Gidan Sagir ya dawo suna zaune Tare,gidansu kuma sun bama Baba Manu ya dawo nan da Zama Sagir ya samu aiki sai dai har yau har gobe bai bar Dinkin ba domin kome ya Zama Dinkin ne Sila shida Imran suka Hada Hannu suka kara Fadada harka yanzu Manyan Shaguna sun fi goma Cike da kekekuna da ma"ikata yara sai dai Sagir ya Daina Dinkin sai dai yaransa shi kuma Oga sama oga kasa.
Shima sun tara ya"ya shima yayi ma Imran,takwara sai mai sunan Mama Amina da mai sunan Babansa Tasiu.
Munari ma ya"yanta Hudu itama Tayi ma Anni da Abba duka Takwara da Mami Asma"u da Baffa Kabiru Sajida kuma ya"yanta uku ita kuma sai Tayi ma su Inna Maimunatu kara da Inna Bintalo Daada kuwa mai sunanta Kusan kowa nada Daada agidansa.
Nasara ma da ya"yanta Biyu su ya Basheer dasu Sadam duk sun zama magidanta Girma ya kamasu Tasleem ma Tayi aure sai dai kafin haka sai da Kaddara ta Fadamata wani Lecture ya Ribace ya Lalata mata Rayuwa.
Sai daga baya ya aureta bayan ta Tsarkaka Alhaji Alhassan yayi ta kuka Saboda yasan Ishara ne Allah ya Nuna mai Koda ya Tuba.
Gabadayansu Mazan sun Hade kansu Matan ma haka Imran ya Daina shan Taba Kwata Kwata saboda Shekara Uku da suka wuce ya Kusa Mutuwa Hayakin Dayayi ta bankama Cikinsa ya Taba Huhunsa sai da Abba ya Fita Dashi Kasar Amurka Ya kusan Wata Shida akayi mai aiki kana ya warke ya Dawo Gida Inteesar har ta Fara kukan rasa Namijun Duniya sai gashi ya Warke sai dai Tundaga Lokacin ko Warin Taba bayaso shi da ita har Abada.
Su Inna Maimunatu kam sun Zama Goggon gaske Yanzu Baba Asabe suka kama Suka Rike itace makwafin Daada Gidansu na Dukku na nan da Ransa bai Mutu ba Baba asabe na Cikinsa Tare da yan aiki masu Taimaka mata Suna zuwa yin Hutu ko Sallah Duk shekara gabdaya kwansu da kwarkwatansu Baba asabe me Zata ga Iyaalan Daada..?illah dai Fatan su gama da Duniya Lafiya da Fatan Allah ya Jikan Daada da Alkali Hamisu Ameen.
Umaima tayi aure anan Kaduna Wani Dan kasuwa take aure mai kudi sosai har da Danta Daya.



*****
Lagos..

Yau din Ranar Lahadin Karshen mako ne Inteesar na kwance Tana Barci acikin Bedroom dinsu Ta Ninkaye Cikin Bargo Tana barcinta Cikin kwanciyar Hankali Da Salama Daga gani kuma barcin Sauke gajiya ne Domin jiya da Daddaran Ranka shi Dade Imran bai barta ta Huta ba.
Da asuba ma sai da ya kara kafi Siga kafin ya barta ta Kwanta Shiyasa ta baro Dakinta Tunda chan suka kwana Zuwa Dakin Imran saboda bata son yaran su tashi su Dameta.
Suna Tare da Hanne domin Tare da ita suka Taho Duk da ba reno take yi ba yanzu Allah ne ya Hada Jininta Dana Inteesar Da zasu dawo lagos ita da Imran suka Nemi yardan iyayanta suka basu ita suka dawo da ita nan tare da duka yaran suka Hada suka sanya makaranta In baka sani ba sai kace Kanwar Inteesar ce Duk inda Tabi yaran Anty Hanne sama Anty Hanne kasa.
Matan Lurwanu ne megadinsu Dasuke Tare dasu anan Boyquater ke Taimakamata da aiki in yaran sun Tafi makaranta Inteesar bata aiki Tunda Imran bayaso sai dai Tana alfahari da Kwalin karatunta.
Tayi nisa acikin barcinta Taji Kiran Wayarta Dakyar ta iya Zuro Hannu Tana daga kwancen bata iya tashi ba ta Dauko Wayar Daga Side drower din gadon bata Tsaya Duba mai Kiran ba ta Daga wayar Cikin Muryan Barci Take mgana.
Dagachan BAngaran Sajida Mata agidan Khalil tace"Au barci ma kike yi..?kin manta mun ce zamu shiga Kasuwa..?kinfa san Salla ta Kusa ZAmu Tafi Dukku in bamu yi wannan Siyaytar ba sai yaushe..?
Inteesar ta yamutsa Fuska Tana Fadin"Wlh nagaji ne Sajida..Gani nan kwance ammh yanzu zan tashi..Ina Zaki kai yara..?
Sajida tace"Gidan Baba Dr mana..Kema ki kawo su nan Tunda Ubaninsu ba Yadda zasu yarda mu bar musu su ba..!
Imteesar tace"Uhm..aini sai ma na kara Tambayan da nayi mganar bai ce komai ba..!
Sajida na Dariya tace"To ai sai kije kiji da Yayana kuma Saura acre Dole sai an Fita abarsa ya Huta sosai a kula Dashi..!
Inteesar tace"Uhm..Ai wannan yayanki naki sai shi..Gabadaya ya Fara Gajiyar dani..Wnnan ma gajiyar Duk tasa ce..!
Sajida na Dariya tace"Banga Laifinsa ba..!
Inteesae tace"Muguwa Allah yasa Daran yau Khalil yayi miki mugun kamu da sai kin samu Ciiki..!
Sajida Tayi Saurin Cewa"Ba Ameen ba Gwarne ai sai Inteen Ya Imun mu..!
Inteesar ta bata rai kafin Tace"wlh ina nan a Inteen Daddyna..!
Dariya suka saka gabadaya kafin su yanke Kiran Muskutawa Tayi ta gyara Kwanciyarta Inteeear din kamar ba ita ta Haifi Zaratan ya"yan nan ba.
Bata kai ga komawa barcin nata ba Ta sake jin kiran Wayarta Idanuwanta suna Rufewa saboda barci ta Daga Kiran Tana amsawa cikin Shakewar Murya.
Hajiya Munari mata agidan Khamis Kabir Dukku tace"Ke lafiyanki kike min mgana kamar me maye..?
Inteesar tace"Ai gwara me mayen a kaina..Yayanki zai kasheni Mu..!
Munari ta Kwashe da Dariya Tana Fadin"Su Ya Imu manya..Ina zai Daga kafa ai wajen akwai danko..!
Zagi Inteesar ta Dora mata kafin Tace"Allah nifa ina jin ku ne gwara Kowa da Mijina..!
Munari tace"Uhm naki dai kika sani..Kowa ma nashi ya sani..Nifa da samun cikin nawa kamar Ya Khamis zai Haukacemin Wlh Watarana Har Tsausayi yake bani..!
Inteesar tace"Kidai ji tsoron Allah..Kuma naji Sajida tana Fadamin kin ma Yaya Zainab din goggo Maimunatu mgana zata zo mana da kayan Da"a A dukku..?anya Munari zan karba kada na dawo ina Kuka Ina Rokon ya Imu zai kasheni..!
Munari ta Kwashe da Dariya Tana Fadin"Banza kizauna shine auran aie..Wlh wannan nanikewar matarba ce Intee..Gwara mu sha ance in kana da kyau ka kara da wanka..Gwara mu gyara dA haka zamu katange mazan mu Daga matan Bariki..!
Su Hafsah ma duk sun ce suna so fa Ya Sagir ai shima ba Dama..!
Inteesar ta sauke Numfashi Tana Fadin"Ke dai yi a hankali kina da ciki..Ba kyau kina wannan banke banken..!
Munari tace"Ke ni kyaleni Gwara na banka..Domin na kara Rikitashi Ina nan cikin arna da yare ina Kwato mijina suna Lasan Lebe daga waje..!
Inteesar tayi Dariya Kafin tace"Ina yarana..?
Munari tace"Sun fita da babansu yawon gari tun dazu..!
Inteesar tace"Nima yanzu zan tashi kasuwa zamushiga da Sajida..!
Munari tace"Ta Fadamin dazu da mukayi waya..Yanzu har kasuwa Ya Imu ke barinki..!
Inteesar tace"Kada ma ya barin ya gani..!
Munari tace"Allah..?wato ki matse Cinya ko..?Allah Sarki Zan sauya Miki kammani an yi Laushi Ya Imu Duniya..!
Ta Fada Tana Fashewa da Dariya Zagi Inteesar ta Dankara mata kafin ta yanke Kiran Tana Dariya Munari sai Allah ya shirya Khamis ai na ganin Duniya.
Ta koma kenan Taji kuka da Haniya a saman kanta kafin ta ankara sun Hawo Gadon da Gudu Afiya ce mai kukan Tana Fadin"Ummi..Ummi..
Kinga ya Abba ko..?
Take Fada Tana kuka Mai sunan Baffa Kabiru da suke kira Baba ya rika Jaye bargon yana Fadin"Ummi ki tashi ga Ya Abba chan na Dukan Ya Boy a Falo..!
Ai jin Haka yasa ta Mike bata Shirya ba Tana kallon ya"yanta kansu Daya Afiya Dake kuka ta saka ajikinta,Sai Baba Data Dafa kansa Ta juya tana kallon musty mai sunan Daddy Dake gefenta yayi kwal kwal da ido Shi akwai Tsoro kamar Farar Kura
Cikin bacin rai Tace"Me yayi mishi Dayake dukansa..?
Kawai sai ya saka mata kuka yana Fadin"nima bansani ba Ummi..!
Sai suma Sauran su saka mata kuka Daga ganinsu a Tsorace suke suna Bala"in Tsoron ya Abba baya Musu Dakyau in ya Fara Dukan Mutum bayaji baya gani yari dan Shekara Takwaas sai Bakar Zuciya irin ta gado.
Ranta ne ya baci ta kallesu Tana Fadin"Kumin shuru..Ina Anty Hanne..?
Baba yace"Tana Tiolet Ummi..!
Karamim Tsaki taja Tana Sauki Daga kan gadon Dauke da Afiya Take fadin"Ina Abi..,?
Wannan karon Musty ne yace"Yana Study Room yace kada wanda ya Damesa..!
Inteesar ta zura Bedroom Shoe dinta ta Fice tana Fada yaran sukabi bayanta Tafe take Tana Fadin"Wato kada a damesa ni kuma azo a Dameni kenan..?
Take Fada har suka iso Tafkeken Falon suna zuwa Daidai Lokacin da karamin yaro ya saka kafa zai Taka wani yaro Dake kasa kwance bazai wuce shekara Shida ba yana kuka Anni yar Shekara Takwas Tana gefe Zaune ta Ragume Idanuwanta sun Fito Saboda Tsoro

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login