Showing 27001 words to 30000 words out of 236322 words

Chapter 10 - Gidanmu Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

Janafty   

28 Oct 2025

700

Tataba ganinsa ba sai Sau Daya sanda sukaje Dukku ita da Daddy Shima yazo shi da dansa bata dai san ko waye ba,Ta gansa alokacin ammh Tana karama bazata iya Shaidasa ba yanzu.Lokacin kuma da akayi Rasuwa anan Dukku aka Dawo aka karbi gaisuwa Lokacin Basu da Hutun makaranta Gidan Kawu Salisu tatafi abunta tayi Zamanta Saboda Nasara Domin aduniya Inteesar Bata da wata wacce ta Shaku da ita Kamar na Nasara kuma tasu tazo Daya daga ita sai Inno da Malam Babba Saboda yadda suke ji da ita sai kawunta Muda,shima akwai Biye ma Shiriritanta...
Sajida Ta fara karatun Jami"a a Base University Abuja a wannan Shekara yar Jarida take son Zama,Journalist itama Inteesar Tana so ta karanci Fanni Tsumi da Tanadi Wato Economics,Ta lula kano Inda Zata Fara Sabuwar Rayuwa.


******

Baba Manu ne da abokinsa Alh.Sadi suka Faka Motarsu a kofar gidan Alhaji Alhassan, Da misalin karfe 11am na safe Daman yasan gidan Saboda Zama anguwa Daya da sukayi da yayansa marigayi Mahaifin Sagir.
Motar ba tashi bace ta abokinsa ne Alhaji Sadi,ba kuma Domin kawu Manu ya rasa kudin da zai sai Mota ba sai dai shi Mutum ne da baya son yana Bayyana Samunsa kudi ne dashi sosai Donin gareji na kansa gareshi da yara kuma ba Laifi yana samun Rufin asiri,sai dai kuma yana da Zuciya mai kyau ko karatun Sagir Rabinsa shike Tallafe dashi kuma Lokaci bayan lokaci yana zuwa Gidan da kuma abun Arziki ko bakomai ba zai manta da Abunda Mahaifin Sagir yayi masa Ba Duk ya kasance Yaya garesa ya kafashi shine Sanadiyar daya mallaki Garejin Dayake Takama dashi.
Shi ya kira Alh.Sadi abokinsa ya gayamai komai ya kuma nemi Daya Rakashi,Shine ya bada kudi aka saka mai suka Shiga kasuwa suka Siya Kwalayrn Minti da Dabino da goro,Kawu Manu ya Rike dubu dari da Hamsi Dubu Talatin kudin nagani ina so sauran kuma na Sadaki ne.
Kawu Manu ne ya Fara Fitowa Daga Motan yana gyara Zaman Babban Rigar Shaddan Dake jikinsa Saboda zuwa neman auran nan bai Fita gareji ba haka kurum yake so ya Taimaki Imran bai san Dalili ba.
Wajen megadi ya nufa Yayinda Alhaji Sadi ya tsaya kulle Mota shima ya Biyo bayansa yana gyara Babban Rigar yadin Boyel Dake jikinsa,kamar yau ne Daurin auran.
Buga get din kawu Manu yayi yana kwada Sallama Megadi ya taso da gudu ya Bude karamar Kofar ya leko yana kallon su kawu Manu Cikin Alamun Rashin Sani.
Ganin haka yasa kawu manu yace"Kai Megida nan yana nan..?
Megadi yace"Eh yanzu ya shigo..!
Kawu Manu yace"Alhamdulillah..Shiga ciki ka Sanar dashi magabata Ne masu Neman auran yarsa suka zo..!
Yafada Cikin ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????Tabbatarwa Megadi bai yi gaddama ba ya Juya Zuwa Cikin Gidan Cikin Sauri kamar zai kifa aransa kuma yana ayyana Daman Dalilin Dawowar Alhaji da wuri kenan..?Haba ko daga gani.!
Yana wannan Zencen Zuccin ya Shiga Babban Falon gidan yana Rafka sallama Daidai Lokacin da Hajiya Mero ta Fito Daga Dakinta ta Chaba ado zata Haura sama wajen Alhaji.
Sai ta Dakata jin sallaman megadi Har kasa ya Duka yana gaisheta ta amsa tana Fadin"buba ya akayi ne..?
Kansa na kasa yace"Hajiya Alhaji ne yayi baki..Sunce ace mai masu neman auran yarsa ne..,!.
Kuri Hajiya mero Tayi mai da ido kafin tace"Kenan daman da gaske zasu zo din..? Tafada cikin Bayyana mamakinta itafa ta Zata Kawai Fade sukeyi kuma data gayama Alhajin bai wani Damu ba ita azaton ta ya Shiryama hakan ne shiyasa bata Damu kanta ba.
Megadi ne yaji Tana mgana yace"Na"am Hajiya me kikace..?.
Kai ta girgiza kafin tace"Ka shigo Dasu Falon bakin Alhaji na waje..bari na Shiga na gayamai..!
Da sauri ya mike kamar ya Kifa yana amsawa da Toh ya Fice ta Bishi da kallon kafin ta kada kai ta Fara Haura Steps tsakani ga Allah Auran Safiya da yaron nan bai kwanta mata,Ya za"ayi ace Mutum ba"asan danginsa ba kuma abashi Aure aka sani ko wani mugu ne..?bari dai ta samu Alhajin Tagayamai taji me zai ce..?
Ta isa Falon nashi Cikin wani yanayi ta iskeshi Yana karantar Jaridar Dailytrust,ta yau da bai samu karantawa ba Hajiya Mero ta Shigo ganinta da yanayinta yaasa ya gane ba lafiya ya ijiye Jaridan yana kallonta Lokaci Daya yana Fadin"Mero...Meron Alhassan Me ya faru ne naganki wani iri..?
Gefensa ta Zauna Tana Fadin"Uhm.megadi ne ya shigo yace kana da baki..!
Cikin Sauri yace"Wasu baki ne..? Allah yasa dai bakin da nake zaman Dakon jira ne...?
Hajiya Mero tace"Wai Magabatan yaron nan mara asali ne wanda Safiye ke so Kamar ta mutu.Ni ban Dauka da gaske bane zasu zo..!
Da sauri ya mike yana Gyara Hulan kansa yace"Daman su nake jira..Saboda su yasa na dawo da Wuri..!
Galala ta kallesa kafin tace"Alhaji yanzu da gaske auran yarmu zaka bama wanda bamu san komai game dashi ba?
Ko kallomta bai yi ba ya Nufi Hanyar Fita yana Fadin"Nidai ba wannan mganar ba..Ina Fatan kin saka an Shiga da baki na ciki dai ko..?
Cikin Daure Fuska tace"Eh nace ya kaisu Dakin bakin ka na waje..!
Kada kai yayi yana Fadin"Dakyau ina ita Safiyan.?
Hajiya Mero tace"Tana cikin Dakinta mana..!
Bai kara cewa komai ba ya sakai ya Fice ta Bisa da kallon mamaki tana Tunanin me ya sauya Ra"ayin Alhajin..? Wanda ta sani da kansa ya kori yusuf kuma yamai iyaka da gidan nan sai dai kuma Ta hasaso Faruwan wani bu..Da kalaman da Imran yazo yayi Tun Lokacin ne taga Alhaji ya Sauya Ra"ayi..? Me ke Faruwa ne wanda Ita bata sani ba kuma Alhaji baya sota tasani din.

Cikin saurinsa da Sassafar ya Fito Megadi na gaisheshi Hannu kawai ya Dagamai ya Nufi Falon bakinsa na Haraban gidan Lokaci Daya da sallama Kawu manu da Alh.sadi dake zaune suka mimmike tsaye da mamaki Alhaji Alhassan ya kariso yana kallon kawu Manu Domin yasansa,Farin sani Tunda Yawanci Gyaran Motarsa ko na yara garejinsa akeyimai kuma ya sanshi Dalilin yayan marigayi.
Cikin mamaki ya mika musu Hannu sukayi musabaha kafin su koma su Zauna suka Fara gaisuwa Bayan sun gama gaisawa ne Alhaji Alhassan ya Fito da wayarsa Daga Cikin Aljihu ya kira Hajiya Mero tana Dagawa yace"Ki aiko da lemu da Ruwa na bakina..!
Daga haka ya yanke kiran ya juya ga kawu Manu yana Fadin"Ikon Allah Mallam Manu..?kardai kace min kasan wannan yaron dake neman yata..?
Kawu manu yayi Dariya Kafin yace"Eh to..Banace A"a ba..Sai dai kanin yaron mai neman auran ne abokin Dana Sagir dan wajem marigayi yayana Tasi"u da suka Zauna nan kusa daku..!
Alhaji Alhassan yace"ikon Allah..Ko da naji..Domin yaron da kansa ya gayamin basu da kowa kuma nima nasaka am bincikamin..!
Kawu manu ya gyara Zama yana Fadin"Alhaji Aure ba mgNar wasa bane..Shiyasa zan gayamaka gaskiya..maganar gaskiya yaron nan bazamu ce basu da kowa ba sai dai muce haka muka gansu Rana tsaka abunda na Fahimta akwai wani Boyayyen al"amari a Rayuwar gidansu,Bazan ce ka bashi Auran yarka ba sai dai kada ka Duba wannan ka Duba Nagartan shi yaron in har kana ganin ba mtsala to ni kuma na yarda na Shige gaba kan al"amarin auran nan da yardan Allah..!
Alhaji Alhassan yayi Shuru kafin yace"Wannan bai Dameni ba..Ita taji ta gani Saboda haka Tunda nace mata A"a kuma ta Dage sai shi Zan aura mata wanda take so Taje Tunda ita ta gani ta kuma Zabi a gidan da bai Dace da ita ba..!
Kawu manu zai yi mgana ya Dagamai hannu yana Fadin"kunzo da Sadaki ne..?
Suka kalli juna shi da Alh.sadi kafin Kawu manu yace"Kwarai..Harda kudin nagani ina so da Mintin da Dabinom mu na Ganin iri..!
Alhaji Alhassan yace"Gud..Yanzu abunda za"ayi ku Dauko Dabinom da Sauran kayan..Kawo Sadakin ai bazaku koma ba sai da Amaryarku..!
Cikin mamaki suke kallonsa Alhaji Sadi ne yayi karfin Halin cewa"Amarya kuma?
Yace"Eh to me zan jira..? Tunda kunzo da komai naku..Kuma ai da Shirin Auran kuka zo Tunda kuka ci Manyan Riguna..!
Mamaki bai barsu sun kara mgana ba ganin ya mike ya Fita ya yafito megadi yana zuwa ya Tasa sa suka Dawo Cikin Falon mamaki bai barsu Kawu manu ba sai da suka ga ya zauna ya kalli megadinsa Dake durkushe yace"Zauna Dakyau Buba..Shaida Zakama Auran Safiya zan Daura yanzu..Ku miko sadakin kada ku damu ko nawa ne kuka zo dashi ku kawo..!
Ba megadin ba hatta su kawu manu Sai da suka Daskare Jiki ba Laka Alh.sadi da kudin ke hannunsa ya mikama kawu Manu Shi kuma ya mikama Alhaji Alhassan ya karba yana Fadin"Na wa ne anan..?
Kawu manu yace"Dubu dari da Hamsin ne..Sadaki da kudin gaisuwa..!
Alhaji Alhassan bai tsaya sauraransu ba ya kirga Dubu Dari ya Cire ya maida ma Kawu Manu Dubu Hamsin yana Fadin"Sadaki kadai nake Bukata..Don shima ya zama Dole ne..Ku matso mu Daura auran Ni zan yi ma yata Walicci Megadina zai zama Shaida Cikin ku wazai Wakilci Yusuf din..?
Nan da Kawu manu yaji ya muzanta Domin bai ma san Cikakken sunan Yusuf din ba,Sai ya Nemi adagamai kafa ya koma Gefe ya kira Sagir sai da yayi mai kira uku ya Daga Cikin Sauri ya Tambayesa Cikakken sunan Yayan Imu Batare da wani Tunani ba Sagir ya Fadamai Yusuf Abubakar Malami shi a Tunaninsa zasu tafi Neman auran ne..
Abun mamaki baya karewa Cikin Abunda bai fi Minti goma ba aka Tabbatar da Auran Safiyya Alhassan Buhari da angonta Yusuf Abubakar malami kan Sadaki mafi Daraja adaidai Lokacin ne yar aikin Hajiya Mero ta Shigo da Farantin Ruwa da Lemo ba wanda ma ya kalleshi Kowa yana ta mamakin wannan lamarin Alh.Sadi ne yaje waje Cikin Mota Megadi ya Taimaka suka Dauko Kwalayen Minti da Dabino suka Shigo Dasu.
Alhaji Alhassan ya basu Hannu sukayi musabaha kafin ya Umarci megadi Daya Dauka zuwa Falon Cikin gida ya Rufamai Baya,bayan ya cema su kawu Manu su jira Amarya ta Fito su tafi da ita..
Kawu manu yaji kansa yayi Nauyi yace"Duk wannan gaggawar na menene Alhaji..?
Mirmishi yayi yana ji kamar an sauke mai wani kaya Yana matukar Tsoron Furucin Tsegerun Yaron nan Daya barsa ya Tona mai asiri gwara yayi ya Sallama musu Safiyan ita taji ta gani..
Cikin Dariyan sa yace"To me zamu jira Tunda an Daura..? Kawai ku wuce da ita Daga baya zamu sauke hakkin mu na iyaye akanta zamu muyi mata kayan Daki Yanzu dai ta Farayin gaba Kafin komai ya Biyo Baya..!
Daga haka ya Fice Daga Falon yana Rike da Sadakin a Hannunsa..
Kawu manu ya Cire Hula yana Fifita Alh.sadi ya kallesa yana Fadin"Manu wannan wani irin Auran kaddara ne..?meke damun Alhaji Alhassan ne..,?
Shidai kawu manu bai samu zarafin mgana ba Tunanin ya tafi kan yanzu ina zai kai yarinyar mutane..? Shidai baisan gidansu Imran ba koma ya sani baya je musu kai tsaye ba Dole dai ta Inda aka Hau ta nan za"a sauka..!







*Shakira..*
3/22/22, 23:03 - Ummi Tandama???i: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:JanaftyB??0
{*

*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*

*Jiya 16/02/2020 muka wayi gari cikin Rashi..Rashi mai girma na Rasuwar Wanda yar"uwarmu zata Aura Wato Habieb din Sadiya Sidi Said wannan rashi babban rashi ne gareta garemu gabadakidaya Ya Allah muna rokon ka ka jikan Habieb din Sidiya Allah ya kyautata Zuwansa Allah ya sadasa da Mala"ikun Rahma Allah ya jikansa da Rahmarsa Allah ka bama baiwarka Sidiya ikon da Zuciyar karban wannan Kaddaran nata Allah ya tallafi Rauninta Allah ya bata Dangana da Hakuri Ameen ya Allah*


*??T??09*


"Alhaji Alhassan Buhari Fagge Haka yake Tafiya cikin Sassarfa zuwa Shashen gidan nasa,hannunsa Rike da Sadakin Safiya,bayansa kuma Megadi ne ke Binsa Dauke da Kwalayen Cingam,da Minti da Dabino.
Bai ji yayi Nadamar abunda ya aikata ba ko kadan ba sai ma Wani Saukayau Dayaji,aduniya Alhaji Alhassan ya tsani Mutane na ganinsa da Daraja da kima,wannan kimar ta Zube,Uwa uba ga Matarsa da ya"yansa Da basu san me yake aikatawa ba ya Tabbata matukar Boyayyen Zunubansa ya bayyana Hatta Jami"ar Bayero sai ta Koreshi,Asirinsa ya gama Tonuwa Mutanen gari Dana anguwa Da suke ganinsa da kima Duk zasu daina Dalilin Safiya gwara ya mika musu ita chan su karata Tunda itataji Ta gani Shi akan Kada kimarsa ta Zube zai iya yin komai.
Bai damu ba wasu mutane ba,Inta Danginsa ne bai da Wata Damuwa ko kara ya saka a gidansu bamai Tsallaketa Saboda Shi kadai ne yayi karatun Boko agidan,Shi din Haifaffan garin Fagge ne na Jahar kano,Iyayensa Talakawa ne Futuk Mahaifinsa bashi cin yau ballatana na Gobe a baya Noma yake sai yazo ya samu Ciwon Baya ya kasa kuma Alhassan ne Babba Sauran kannen nashi Duka matane.
Karatun da ya samuyi Da Taimakon wani malami ne inda aka kaisa Almajiranci a Dala,Sai Allah ya Hada jininsu da Mallam Iliya,Wanda Da Taimakonsa ya kawo wannan matakin ya Tabbata Da yana Raye shi kadai ne zai Tsawatamai yaji to Ya rasu Da Dadewa,Goggo ce kuma Matukar sonsa Datake yi komai yayi Daidai ne ballatana Sauran kannensa mata da shi ne komai nasu Shiyasa Basu da tacewa.
Matsalan ma Daga wajen Hajiya mero ne da Danginta Yar nan cikin Kano din ne a Rijiyar Zaki. Itama Din bata isa ba shi ke da iko da ita da ya"yan da suka Haifa guda Biyu a Duniya Safiya da Tasleem..
Tundaga Falon kasa yake kwalama Hajiya Mero wacce ke Falon sama zaune tana jiran Tsammani Gabadaya yanayin Alhaji yasata Fargaba.
Sai kuma taji yana kiranta kiran Daya sa har Safiya Dake Cikin Dakinta ta jiyo Daman tana kwance ne Tana game a wayarta,Sun gama waya da Yusuf kenan yana Tambayanta ko Bakin sun zo..?
Tace bata sani ba Ammh kamar basu zo ba saboda har Abban nata ya Fita bata sani ba ta Shiga,wanka Dayake bata zuwa ko"ina Wanchan Shekara ta gama karatu Computer Sciencies ta karanta,Bata fara aiki ba sai dai Tana zuwa wani Cafe Dake nan bayansu Tana aiki dasu Duk ba wai tana musu aikin Parmanent bane,a hanyar zuwan ta ne ma suka Hadu da yusuf wata Bakwai da suka gabata.
Abban nata bai yi Niyyar ta Fara aiki ba,Shiyasa bai neman mata ba Tasleem ne kadai ke zuwa makaranta sai wannan Shekaran zata gama Candy.
Yusuf bai isa ya kira Imran ya Tambayeshi wani abu ba Domin shi bayason yawan Tambaya da Takura sai dai yafi kowa saninsa in yace Abu to ssai ya Tabbatar dashi ya Tabbata zasu zo din.
To sun gama wayar kenan Tana kwance kan gadonta Tana Game taji kiran da yake ta kwalama Mommyn nasu shi ya sakata Zabura ta Sauko Daga kan gadon tazo bakin kofa sai kuma ta kasa Fita jin Saukowan Hajiya Mero Tana Fadin"Abban Tasleem irin wannan kiran fa..? Lafiya..?
Hannunta ya Riko ya zaunar da ita kan Daya Daga cikin kujerun Falon kafin ya juya yana Fadin"Buba ijiye kayan hannunka..Kada ka tafi ban gama Dakai ba.!
Jikin Buba Megadi na rawa ya ijiye kayan Hannunsa ya Zube kasa yana jiran Umarni.
Hajiya Mero tabi kwalayen da kallo Cikin Faduwat gaba kafin ta maida kallonta kan Alhaji Alhassan Tana Fadin'"Nifa bangane komai ba..Wadanan kwalayen fa na miye.?
Zama yayi gefenta Lokaci Daya ya kama Hannunta ya Damka mata kudin Dake hannunsa Lokaci Daya yana Fadin"Sadakin yarki ce Mero..Yanzu nan na Daura Mata aure da wanda ta kawo..Tare da Shaidun Waliyansa daya aiko Guda Biyu,da kuma Shaidata Data Buba megadi gashi azaune..!
Yafada yana kallon Cikin Idanuwanta Cikin wani yanayi Buba megadi ya jinjina kai yana Fadin"Tabbas..Mun shaida Hajiya..Yanzu nan muka Tabbatar da auran..!
Ai da wani Sauri Hajiya Mero ta Mike Lokaci Daya kudin suka Biyota suka watse a kasa kamar Saukan aradu haka taji mganar Safiya ma Dake kofar Dakinta Tana leken Falon bata ji me ya gayamata ba sai dai Yanayin yadda Ta miken ya Fadar mata da gaba sai ta kara Sako kanta Domin Taji meke Faruwa.
Cikin wani Bacin rai ta kallesa daga Sama har kasa tana Fadin"Wani irin aure kuma..? Aure sai kace muna garin Gaba gaba Alhaji..?
Juyawa yayi yayi ma Megadi inkiya da Hannu daga haka ya Mike ya Fice Domin zamansa baida Muhalli a wajen.
Kafin ya maida kallonsa kanta Cikin Halin lko in kula yace"Auren gaske dai wanda kika sani..Miye amfanin jeka ka dawo..? Nayi mgana na Raba yarinyar nan ammh Taki jin mganata Ta rainani Ta turomin su kinga ai gwara na Aura mata shi Taje chan ta karata..!
Yafada yana zakuda kafada Cikin Karaji Hajiya Mero tace"Wlh baka isa ba Alhaji..Yata bazata yi aure a wannan gidan ba..Gidan da kace ba gidan arziki bane..Gidan Yan shaye shaye..? Inace ba kanagani yaron nan yazo yaci Zarafin mu Ammh Duk da haka kace suzo zaka basu yarka..? Wlh ban yarda ba yata ba yar tsana bace Su Biyu kadai na Haifa bazan Taba bari ka Lalata musu Rayuwa ba Baka isa ba!
Ta karishe Fada Cikin karaji wanda kaf mgangunta suka Fada kunnuwan Safiya wanda taji mganar Kamar Daga sama sai dai bata gama Fahimtar ina mganar ta Dosa ba.
Alhaji Alhassan Babatun Hajiya Mero bai Dameshi ba ya kalleta yana Fadin"Ai na ma isa Mero..Tunda har na Daura auran..Kinga ki adana mgangunki Zuwa wani Lokaci Yanzu dai ki shiga ciki ki taya yarki Hada kayanta Waliyan Mijinta suna jiranta zasu wuce da ita..Daga baya in muka zauna muka Tattauna sai musan abunda Zamu yi mata a mtsayinmu na Iyayenta..!
Yana Fada Lokaci Daya ya saka kai zai Haura sama Hajiya Mero da Zata out of Control bata san sadda ta isa garesa ba ta Chakume Rigarsa ta Baya lokaci Daya tana Fadin"Baka isa ba..Wlh Alhassan baka isa ba ba inda Safiya Zataje Domin ban yarda da wannan auran ba..!.
Ta karishe Fada Tana Fashewa da kuka Mai tsanani Kwace Rigarsa yayi yana Fadin"Mero wannan wani irin Raini ne? Ina Mijimki Uban ya"yanki zaki Chakume min Rigata..? Kada ma ki Fara wannan mgana aure na Riga na Daura kuma Wlh kinji Rantsuwan Musulmai Yau zata tafi Gidan Da ta zaba sama da mu..!
Yana karishe Fadar haka ya Tureta gefe sai da ta kusa Faduwa ya nufi Dakin Safiya wacce Rigiman iyayenta ya Tsorarata da kuma Abun ta fahimta yasa ta Bayyana atsakiyar Falon batare data sani ba Idanuwanta sun kala sunyi Jajir,kiris take jira ta Fashe da kuka aure abbanta ya Daura mata..?koda yusuf yake Zabinta ammh ai Tana so tayi auran gata da kowacce mace take yi.
Kusa cin karo yayi da ita wanda yasa yayi Saurin ja Baya yana Hararanta Lokaci Daya yana Fadin"Au daman kina jin mu ko..? Toba sai naa maimaita ba ki Shiga Dakin ki ki Hada komai naki da kikasan zaki Bukaceshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login