Showing 54001 words to 57000 words out of 223329 words
ganka da kaya na amsa bakai zaka ganni dasu ka amsa ba”.
Murmushi ya mata cike da jin ta kuma birgeshi. Shine da kansa yay mata rakkiya har sashen Hajiya Iya. Inda a tafiyar tasu take samun damar yima gidan mai sassa da yawa kallon tsaf. A ranta kuwa raya irin jin daɗi ta masu hannu da manda takeyi. Shiyyasa akace wasu tun a duniya suke cinye rabonsu na lahira. Wasu kuma sai kaga ALLAH ya haɗa musu duniyar da lahirar duka. Ya ALLAH kasa muna cikin masu samun dukan gaba ɗaya.............✍
*_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*
Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.
*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_
*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_
*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_
*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_
*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_
Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
*_TYPING📲_*
*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*
*Page 17*
____________________
*_INA MATA ƳAN ƘWALISA BA'ABOTA SON GYARA JIKI DA FATA SUYI ƘWANAS TAMKAR WATA ƊAN DAREN SHABIYAR?!_*
_Ku marmatso kusa maza na kaiku kantin sauƙi na UMMU DUFAIL gidan sauƙi da biyan buƙatar MATA SARAKAN ado harma da MAZA ƴan ƘWALISA._
*_MATA da yawa kanso su koma Taurari ababen kallo da burgewa ga ma'abota kallo sai dai basusan ina zasu sami sinadarin kankaro wannan ƙyawu da mutuncinba._*
_To maza kuzo kusa dan Bilyn Abdull ta lalubo muku kantin sauƙi na Umm Dufail dakeda kaya masu sauƙi da gamsar da maison afani dasu_.
*_UMMU DUFAIL nada kayan gyaran jiki masu rahusa da inganci da gamsar da mai saya cikin ƙanƙanin lokaci kamar haka👇🏻😁_*
*Customers price list By Ummu Dufail FACE AND BODY*
SCRUB=2500(300ml)
Face and body mango butter=3k (250ml)
Face cream= 1800
Corretor oil/vitamin C oil=2k
Fairness skin lotion= 2500
Hot chocolate skin lotion 2500
Serum (for Nuckles )2k
Nuckles cream (stubborn)3500
Mix fruits Arabian black =soap 1800
Mix fruit glycerine soap =1900
Beetroot=1900
Coconut, milk,egg..face soap=1200
Lavender mix fruit soap =1800
Body wash =1500
cleanser=1600
Hair spray =700
Hair oil =1500
Hair relaxer =700
Hair butter 1700
Shampoo =1500
Breast=oil 2k powder 2k
Strech marks cream= 2k
Beetroot pink lips =700
Baby care soap glycerine=1k
Baby care butter =1500
Shea butter baby soap =700
Tsumin tula =2200
Tsumin zinariya =1200
Sliming tea =1500
Amarya set =25k
Liquid Arabian black soap =1900
Cleansing water =1500
*_Zaku iya bibiyarta domin gani da ido ta Handle ɗinta na istagram da facebook kamar haka_*
Ummu Dufail @ Facebook
Ummu Dufail @ instagram
Phone no: 07067943479.
_Ƴammata harma da masu auren karku bari ayi babuku. Dan gyara shine mace a wannan ƙarnin😉👍🏻_.
________________________
*Page 17*
...........Tarba mai ban mamaki da tu'ajjibi Zinneerah ta samu daga hajiya iya, harma da wasu daga cikin jikokinta dake gida ta iske a sashen. Duk yanda taso ta takura kanta saboda baƙunta da rashin sabo sunƙi bata damar hakan. Dan sai faman jera mata tambayoyi suke tamkar ƴan jaridu.
Dolenta ta saki jiki dasu dan su biyun duk sa'anninta ne. Biyu mata, Bahijja da Meenal wadda taci sunan Hajiya Iya kenan. Sai ɗaya Namiji mai suna Jamal.
Harga ALLAH Zinneerah taji daɗin kasancewa dasu, dan ta fahimci sunada tarbiyya da sauƙin kai sosai, sannan son ɗan uwansu ko yaya yake wannan trianing da akai musu ne tun asali.
Cikin katsesu Hajiya Iya dake shafa man zafi a ƙafarta tace, “Niko kun isheni da subaɗi Bahijja. Kuma barni nai hira da Innon tawa kunbi kun hana. Sai ku tashi ku kaita wancan ɗakin kuɗan ƙara gyarawa duk da dai ko jiya Rahi ta garasa ta samu taɗan watsa ruwa ta huta dan shine zai zama ɗakinta”.
Wani irin waro idanu Jamal yayi tare da zabura. Haka Meenal da Bahijja ma duk sai da suka zaro idanun. Jamal yace, “Granny kina nufin ɗakin Yayanmu fa kenan?”.
Harara sosai Hajiya iya ta watso musu tana ƙyaɓe fuska. “Eh shi dinfa nake nufi ba waniba. Zuwa yake ƙasar ne da har za'a wani cigaba da faman barin ɗaki haka aljanu na dubulwa a cikinsa? Ubansama dana haifa bai tuna inda nakeba shekara guda balleshi da ke neman haɗa kusan uku”.
Yanda ta ƙare maganar cikin ɗacin rai ya saka jikinsu duk yay sanyi. A sanyaye Meenal tace, “Kiyi haƙuri Granny, mu dama zaki yarda sai mu tafi da ita sashenmu, kinga saita zauna a ɗakinmu dan ALLAH”.
“Hakan zaifimin daɗi kuwa Amina. Sai dai kuyi haƙuri nafison zamanta kusa dani akoda yaushe. Koba komai zanga fuskar Innota naji sanyi”.
Kansu kawai suka iya kaɗa mata, dan tunda ta faɗi haka basu isa jayayya da ita ba. Ko min roƙon da zasu mata kuma bazata canja ra'ayintaba. Zinneerah dai najinsu kanta a ƙasa, sai dai babu abinda ta fahimta a zancen nasu kuma. Amma ganin yanda fara'ar fuskar Hajiya iyan ta ɓace tun daga maganar ne ya saka jikinta yin sanyi itama......
“Taso muje kiga ɗakinki Sister”. Bahijja ta katse tunanin Zinneerah tana kama hannunta cikin nata. Babu musu ta miƙe tabi bayanta, Meenal da Jamal ma suka mike suka biyosu.
Kallo Hajiya Iya ta bisu dashi idanunta na cika da ƙwalla. Dan maganar nan ta tado mata da wani babban miki dake zuciyarta tsahon shekaru, wanda a shekarin can da suka shuɗe kusan biyar sun fara ganin haske, amma a wannan karon al'amarin na neman komawa baya. Dan inhar lissafinta bai ƙwace mataba kusan shekararsa ɗaya kenan rabonsa da Nigeria. A take wasu hawaye masu zafi suka fara gangaro mata. Saurin saka hannu tai ta sharesu tare da miƙewa ta nufi hanyar ɗakinta tana ɗan ɗingisa ƙafarta dake mata ciwo tinda safe.
“Sister Zinneerah lallai keɗin mai sa'a ce”. Meenal ta faɗa tana tura ƙofar ɗakin da suka iso a ɗan lungun corridor ɗin dake facing jikin ɗakin Hajiya Iya. Kafin Zinneerah ta iya cewa wani abu Jamal ya karɓe da cewa “Mai sa'a kuwa ta gasken gaske. Dan kece ta farko a tarihin gidannan kaf da zaki rayu a wannan ɗakin na Yayanmu bayan shi kaɗai dake rayuwa a cikin kayansa idan yazo ƙasar”.
Haka kawai gaban Zinneerah ya faɗi batare da tasan daliliba. Har suka shige ɗakin ita tama kasa motsawa balle ɗaga ƙafarta. Ganin hakan yasa Jamal dawowa da baya yaja hannunta suka shige ciki, duk da taso ƙoƙarin ƙwace hannun nata amma yaƙi bata dama sai da suka shigo tsakkiyar ƙaton ɗakin da batamasan yanda zata fasaltashi ba a fahimceta.
Sakin hannunta da Jamal yayi ya bata damar ɗago idanu tanabin ɗakin da kallo. Yayinda hancinta ke shaƙar mata wani irin mayataccen ƙamshi mai sanya zuciya salama. Wani irin saki gaɓɓanta sukai a lokaci ɗaya, ta zubama su Bahijja daketa yaye fararan ƙyallayen da aka lulluɓe komai na cikin ɗakin dasu saboda gudun ƙura ta hausu.
Sai da suka gama yaye komai ya bayyana Meenal ke faɗin, “Bara na ɗakko kayan shara mu tayaki ɗan ƙara gyarawan baƙunta. Kuma mufa kibar mana wannan ɗari-ɗarin Madam”.
Cikin tsokana Jamal yace, “Barta sotake mu kirata baƙauya maybe. Gwarama ki sake damu kafin su Yah Haneef su dawo gidannan gobe idan ALLAH ya kaimu, dan zasu cinyeki da bakine”.
“Kaji munafiki, saina faɗa musu yasin”. Bahijja dake hararsa ta faɗa.
Yanda Jamal yay da fuskane ya saka dariya kufcema Zinneerah batare data shiryaba. Hakan yay dai-dai da dawowar Meenal ɗauke da kayan shara ɗakin. “Oh ALLAH, kokefa ƴar uwa. Ni kuwa an taɓa faɗa miki keɗin ƙyaƙyƙyawa ce musamman idan kina dariya?”.
Kasa bata amsa Zinneerah tayi, sai dariyar tatace ta koma murmushi kawai. Hakan datai ya saka su Jamal kwashewa da dariya a tare. Bahijja tace, “Kinga kinsatama ta haɗiye abinta da wannan bakin naki da bai gani ya ƙyale”.......
“Wai nikan sharar zakuyi ko damuna da shegen surutu?”. Suka jiyo muryar Hajiya Iya dake tunkaro ɗakin.
A take kowa ya nutsu suka fara ƙoƙarin sharar. Shigowa tai har yanzu fuskarta a dagule da ɓacin ran ɗazun. Tabi ɗakin da kallo da ƙyau kamar mai nazari. A ƙarshe ta sauke idonta akan Zinneerah dake ƙoƙarin tayasu itama. Haka kawai kuma sai taji ɓacin ran nata ya sassauta. Ta sauke ajiyar zuciya da juyawa ta fice a ɗakin.
Tsaf suka gyara komai dan an horar dasu aiki tuni. Cikin kanƙanin lokaci ƙyawu da tsaruwar ɗakin ya ƙara bayyana a idon mai kallo. Musamman da suka cire labulayen ɗakin duk suka sake canja wasu fararen tas dan dama fararen suka cire. Kaso mafi yawa dake a ɗakin kalar blue and white ne. Sai wasu colors ɗin ɗai-ɗai da ba'a rasaba. Da yawansu kuma an ɓaɓɓoyesu ma.
Idanu ta lumshe a hankali tana maijin wani abu mai nauyi dake a ƙirjinta yana narkewa sannu-sannu zuwa cikinta. Nannauyar ajiyar zuciyar da bata shirya fitartaba ta kufce mata a karon farko. Kusan a tare Meenal, Bahijja, Jamal suka dubeta. Sai dai babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu, dan sun fahimci Zinneerah bata da sakewa da mutane, gata kuma da alama akwai miskilanci tattare da ita.
★★
Ƙarfe bakwai da wasu mintuna Alhaji Kabir ya iso katafaren family House ɗin nasu. Bayan samun wajen fakin da direba yayi ya tsaya aka buɗe masa ya fito riƙe da leda a hannunsa wadda kowa yasan mai ita. Dan babu fashi kullum sai ya shigo da irin wannan ledar domin mahaifiyarsa koda iyalansa basu samu hakanba. Sanin baya bama kowa dakon ɗaukarta, shi yasa babu wanda ya tunkaresa domin karɓa. Sai dai sauran kayansa da ɗallami driver ya kwasa zuwa sashensa shi da iyalansa. Shi kuma ya nufi sashen Hajiya Iya kansa tsaye.
Ɗauke da cikkakkiyar sallama a bakinsa ya shigo falon duk da yasan a irin wannan lokacin Hajiya iya na ƙuryar ɗakinta. dan idan tai sallar magriba bata fitowa sai isha'i. Amma yanada tabbacin baza'a rasa wasu daga cikin ƴaƴansaba da basa rabo da sashen a koda yaushe.
Ilai kuwa yana shiga da fuskar Zinneerah da Meenal ya fara tozali dan sune ke facing ƙofa. A take falon yay tsit kowa ya ƙara nutsuwa. Sai Meenal ce datai saurin miƙewa ta nufesa domin amsar ledar hannun nasa. “Baffah sannu da zuwa?”.
“Yauwa uwata kune anan?”.
“Eh Baffah, munzo tarbar Sister Zinneerah ne tun ɗazun”.
Murmushi Alhaji Kabir yayi yana maida kallonsa ga Zinneerah data risinar da kanta ƙasa tun bayan amsa sallamarsa. Ya ƙaraso cikin falon sosai su Bahijja ma na masa barka da dawowa. A hankali Zinneerah ta zamo ƙasa tana faɗin, “Sannu da zuwa Baffah. Ina wuni”.
Murmushinsa ya sake faɗaɗawa da faɗin, “Yauwa ɗiyata. Welcome to Shira's family”.
“Thanks you Baffah”. Ta faɗa a hankali cike dajin kunya.
Ya cigaba da faɗin, “Yaya kika barmin ƙanwata da ƙannanki da Abbanki?”.
“Lafiya lau Baffah, sunce suna gaisheka”.
“Ina amsawa. Alkairin ALLAH yakai garesu. Tashi ki zauna”.
Babu musu Zinneerah ta miƙe ta koma kusa da Meenal data kaima Hajiya Iya leda ta dawo ta zauna. Shikuma ya wuce bedroom ɗin Hajiya iyan domin gaisheta.
Tunda yay sallama a yanda ta amsa masa ya saka gabansa faɗuwa. Cikin ƴar ruɗewa ya ƙaraso ƙaton ɗakin nata itama da sassarfa. Gabanta ya zube jikinsa na rawa. “Innata mike faruwa naji muryarki tamkar baƙyajin daɗi?”.
Ɗago kyawawan idanunta da mafi yawan ƴaƴa da jikokin gidan suka gada a wajenta tai tana kallonsa. A take hawayen da taketa maƙalewa tun ɗazun suka silalo mata tare da murmushi a lokaci guda. Sake ruɗewa Alhaji Kabir yayi idanunsa shima na kawo ruwan hawaye.
Kanta ta girgiza masa a hankali tana share nata. “Hawayena basu zuba domin kai ba Kabir. Dan kai ɗa ne tamkar da dubu ga kowaɗanne irin iyaye. Nagodema ALLAH domin yayimin ni'imomi masu yawa a rayuwa da har wanda ke a nesa dani bazai ɗauka inada wata damuwa ko jarabawa nima tattare dani ba, kuma har da samunka matsayin ɗa a cikin ni'imomin. Kabir tabbas ɗan uwanka shine jarabawata. Dan ALLAH ka tayani addu'a ALLAH ya bani ikon cinyewa. A lissafin danai yau shekarar Ahmad ɗaya da watanni biyu kenan rabonsa da ƙasarnan. Yanzu ace Kabir har Inno ta rasu Ahmad ya gagara ɗakko iyalansa suzo sumin ta'aziyya. Idanma ita data nisantani dashi bazatazo ba shi bazai iya zuwaba koda shi da Modibbo ne?. Moddibo fa kansa shekararsa uku kenan rabonsa da ƙasarnan. Tunda nai maganar yay auren nan bai sake zuwaba, uwarsa kuma ta hana wannan ƙoɗaɗɗiyar yarinyar zuwa nan ɗin koda ta haihunma. To kosai na mutune zata barsu suzo su raɓi gawata......”
Ta kasa ƙarasa maganarta saboda kuka daya kufce mata.
“Innata dan girman ALLAH ki daina kuka. Kiyi haƙuri dan ALLAH, addu'arki da tamu Ahmad yafi buƙata. Kuma insha ALLAH namiki alƙawarin a wannan karon zanbi duk hanyar data dace domin maido ɗan uwana gida. Har ita ɗin da shaiɗancinta dole ta biyosa. inko taƙi wlhy sai dai ta kama gabanta inda ta fito. Amma dan ALLAH kibar kuka Inna”.
“Kayya Kabir. A baya fa kayi irin wannan namijin ƙoƙarin amma kaga ta sake sabon shiri, harshi Moddibo ɗinma da ada bayabin ra'ayinta yanzu ta sake janyesa. A zatonmu kusancin da Khalipha ya samu dasu zai kawo wani canjin sai gashi ba hakaba”.
“Insha ALLAH Inna komai zai wuce. Ai duk abinda ya saka kuka wataran zai saka dariya. Duk kuma abinda ya saka dariya wataran sai ya saka kuka. Itama ai gasunan ta haifa indai ƴaƴane ko. kuma Alhmdllh sai ya bata mafi rinjayensu maza. Itama kukan da zatayi akansu sai ya ninka naki sau dubu. Amma dan ALLAH ki daina masa kuka Inna dan shima ba laifinsa bane, anfi ƙarfinsa ne kawai”.
“Humm ko anfi ƙarfinsa kam da halima. Dan shima kaidin macen yana iske haline. Kai miyasa matan naka basu rabani da kai ba”.
Kasa cemata komai yayi sai ban haƙuri dai. Sai da yaga hankalinta ya kwanta sanann ya miƙe ya fice domin zuwa gabatar da sallar isha'i tunda ya cinye lokacin zuwa yay wankan anan.
Bai iske su Zinneerah a falonba yanzu. Da alama sun shige gabatar da sallar suma.
______________★
Duk yanda Alhaji Kabir yaso rintsawa a daren yau hakan ya gagara. Ba komai ke masa kai kawoba a rai sai tattanawarsa da Mahaifiyarsu akan ɗan uwansa.
Su uku kacal mahaifiyarsu Hajiya Iya ta haifa a duniya. Shine babba, sai ƙaninsa Ahmad, sai autarsu Bilkisu da ayanzu haka tana Lagos tana aure. Rana ɗaya aka ɗaura masa aure da ɗan uwansa Ahmad, wanda mafi yawan mutane sukafi sani da suna AK Shira. Ba komai yasa ake kiransa da suna AK ba sai tsanain soyayyar da sukema juna tun ƙuruciya. Kasancewar boarding school sukayi acan ake kiransa da suna Ahmad ɗin Kabir. A hankali kuma sai abokai suka koma kiransa a takaice da suna AK Shira. Mai makon Ahmad Abdul-Mutallab Shira kamar yanda shi ake kiransa Kabir Abdul-Mutallab Shira. Bayan sun kammala secondary tare suka wuce ƙasar Turkey ƙaro karatu. Cikin amincin ALLAH suka haɗa digiri ɗinsu na farko dana biyu duk a tare. Tun suna farkon fara digiri na biyu Ahmad ya haɗu da matarsa ta yanzu mai suna Hindatu. Asalin Hindatu ƴar ƙasan Nigeria yace. dan mahaifinta ɗan nanne. Sai dai mahaifiyarta ƴar asalin ƙasar Morocco ce. Amma suna zaune a ƙasar Turkey tun tanada ƙuruciya, acan ta girma tamafi sanin can matsayin ƙasarta fiye da Nigeria dan sukan jima basuzoba. Ƙyaƙyƙyawa ce itaɗin sosai kasancewarta halfcast ce. Sai ALLAH ya bata wani irin usilin ƙyau mai ɗaukar hankalin mai kallonta.
Duk da yasan ba wannan ƙyawun bane ya ruɗi ɗan uwansa ga sonta, amma shima ya taka rawar gani wajen jan hankalinsa gareta. Bayan sun kammala digirinsu na biyu suka dawo Nigeria kamar yanda mahaifinsu ya buƙata. Dan yana bukatar suzo suyi aure. Koda suka iso suka huta babu wani jan rai iyayensu suka gabatar musu da matan aure. Shi Alhaji Kabir ya amsa da hannu biyu yay godiya dan dama baida ko budurwar. Amma Ahmad ƙiri-ƙiri yace shifa yanada matar aure. Hajiya iya ce ta fara nuna rashin yardarta akan hakan amma ya nuna bamai rabasa da Hindatu dan yana mata so mai zafin gaske. Gudun samun ɓaraka yasa Marigayi Alhaji Abdul-Mutallab zaunar da Hajiya Iya yaymata nasiha harta amince badan ranta yasoba.
A take aka hau shirin biki, cikin kanƙanin lokaci komai ya kammala dan ana zuwa nemawa Ahmad auren Haindatu babu wani ja'inja aka bashi. Ansha biki na nunawa sa'a lokacin, dan Alhaji Abdul-Mutallab ya tara musu. Bayan biki duk aka kai amare garin Bauchi, harda Hindatu. Ƙyawawan halin Hindatu yasa Hajiya Iya ta fara sonta, sai kuma akazo dandanan ta samu ciki. Duk da Hindatu na karatu a jami'ar Turkey bata taɓa nuna ƙorafinta nason komawa makarantaba. Tai shiru abinta har ALLAH ya sauketa lafiya ta haihu ɗanta namiji da yaci suna Abdul-Mutallab. Amma saboda alkunya suke masa laƙani da suna Adnan, Hajiya Iya kuma na kiransa Moddibo.
Bayan haihuwarsa da kusan watanni huɗu Ahmad ya buƙaci sake komawa ƙasar Turkey dan cigaba da karatunsa. Sai dai a baɗini wannan shirin Hindatu ne. Basu kawo komai a ransuba suka amince Ahmad ya ɗauka Hindatu da dansu suka tafi Turkey saboda kowa yasanshi da matuƙar son zurfi a karatu, shi kuma a lokacin matar Kabir ta fara laulayin nata cikin ita.
Kamar wasa tun daga wannan tafiyar ganin Ahmad ya fara musu wahala. Dan ya samu aiki acanma ta dalilin mahaifin Hindatu. Sannu-sannu ƴaƴa suka fara yawaita a wannan family, yayinda ALLAH yayma Alhaji Abdul-Mutallab rasuwa. Akan wannan rasuwa kuwa saida sukai